Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tazo ita ce mai jinya. Abie ya wadatasu da komai na rayuwa, burinsa Raiyana ta warke ras, kafin ya 'dauki mataki.
Wahida ganin yadda Raiyana take abu hauka tu'burin ya saka taji mugun tsoro tana son tace akaita wajan malamin dan tasan zai warkar da ita, amman tana jin tsoro.
Jaddatu zaune tana shan shayi tana masifa.
Abie na zaune gefenta sanye da wasu fararen kayan 'yan Pakistan, ya yi wani irin kyau sai fitinannan 'kamshi yake tashi ajikinsa.
“Wai shin Abdul dole ne sai ka zauna da MATAR nan bazaka sawwaqa mata ba? Nagaji da shigo mana gida da ake wlh, ni ina gudun wani mugun abun ta aikata ya koma mata.� Hanan ta ce“Yo da fa Ummi me kike tunani? Dan Allah Ya Abdul ka sallameta.�
Abie ya harari Hanan ya 'dora yatsar shi bakinsa.
A tausashe yace“Ummi don Allah kiyi hkr komai zaiyi daidai, Allah ya bata lafiya duk abinda mutum zaiyi ya duba gaba akwai abinda yasa bazan sawwaqa mata ba yanzu, na fiso ta dawo hayyacinta na sakata jikina na nuna mata hanya idan tabi gaba zataji da'din rayuwarta, da wanda zata kuma rayuwa da shi, dan mutum ya aikata ba daidai ba bai kamata ka 'dauki tsatsauran hukunci cikin fushi ba kabi komai asannu, naji zafin abinda tai sosai amman akwai abinda na duba sona da take shine ya jefata wannan rayuwar yanzu idan na 'kyamace na mata Koran kare, cikin ciwo idan ta warke zatayi abinda ya linka na baya wanda inada tabbacin 'karshenta bazai kyau ba duk wanda ya furta ma kallamar so ka girmamasa aduniya duk da ta yi kuskure babba, amman wlh na yafe mata Ummi tinda ga abinda ya sameta wannan izina ne ga 'yan baya.�
Jaddatu ta ce“Wai me tayi ne? Kana nufin wani abun ta maka?�
Hanan zatayi mgna yay saurin cewa.
“Ummi bari idan na dawo daga Australia zamuyi mgna, anutse, likacin baby ummina na Espagne.�
Jaddatu ta ce“Ai kai kasani da zurfin cikin tsiya, yaushe ne Rahma zata koma wajan karatun?�
Abie ya shafi sumar kansa yana murmushi qasa2, ya ce“Jibi insha Allahu ummi.�
“Allah ya kaimu.�
“Ameen.�
Ya amsa yana miqewa ya haura sama.
Auntie Saro wacce tazo wucewa dan zuwa kitchen taji dukkan abinda Abie yake bayani, tsananin tashin hankali da tsanar 'kanwarta ya marfaketa lokaci 'daya. Duqewa tai 'kofar kitchen ta rushe da kuka tana rufe bakinta.

Tsaye take tsakiyar falonta waya take cikin nutsuwarta, ta 'kurama tafkekiyar Tv da take manne da bango kyawawan 'kananun idanunta.
Sanye take da riga da siket coffee brown, kayan 'yan Ethiopia.
Siket 'din ya 'dan kamata 'kugunta wanda yaba hips 'dinta da bom-bom 'dinta damar bayyana, daga 'kasa sai siket 'din ya baje, rigar ta 'dan kamata daga sama hakan yasa 'kirjinta wanda yake cike da dukiyar Fulani ya zauna daram cif-cif cikin rigarta Masha Allah.
Gashinta da yake 'dauro jelar har gadon bayanta, ta 'daura 'dan mitsitsin 'dan kwalin kayan Iya tsakiyar kanta, hakan ba qaramin kyau ya 'Kara mata ba, wuyanta sanye da sarqar zinari haka kunneta sai zobe guda 3 cas ajere yatsun hagum 'daya diamond irin na Abie 'daya gold me rubuce da sunanta 'daya azurfa ta 'kwaran.
Sai siri-sirin abin hannu wanda suka kasance na zinari kowane tsintsiyar hannunta na 'dauke da guda shidda sai 'kyalli suke 'kafarta ta hagum sanye da sarqar qafa ta gold wanda takeda wasu tsakiyoyi masu tsananin kyau da haske.
Awannan lokaci dole ne duk wani cikakken namiji idan yaga yadda Rahma ta 'dauki wanka da tsadaddun abin da tsara kwalliya yaji yanada burin ta kasance mallakinsa, gata 'yar shar dole ka ji kana son mallakarta.
'Dan guntin murmushi ta saki ta 'dan taka 'kafarta da 'dan 'karfi sarqar 'kafarta ta bada wani irin sautin 'Kara cakasssss.
Cikin harshen turanci ta ce.
“No! Anee ba ki gane bane wlh abin ya ban mamaki sam bansan ya akayi na shagalaba har hutuna ya qare ban koma ba, amman harda laifin Abiena shine ya shagwa'ba ni, amman munyi mgna ya ce jibi insha Allah zan tafi nayi missing Espagne sosai.�
Ta 'karashe mgnar cikin Jan numfashi ta kalli Latifa ta ce“Shiga bedroom ki gyara.�
Ta nufi hanyar fita.
Latifa ta ce“Uwar 'dakina yau idan kin fita ahaka bakin titi wlh bazan kaffara ba sai kin ha'da hatsarin motoci bila adadin.�
Rahma ta juyo tana waro fararen 'kananun idanunta, batayi mgna ba sbd wayar da take ta fice abinta, tana son mgna da Abie akan tafiyar Anee na bata labarin jibi suke fara jarabawa.

*Hospital*
Ja'afar cikin shigar 'kananun sosai kayan suka fito masa da cikakkiyar halittarsa, sun masa mugun kyau, sai baza 'kamshi yake, yana zaune gefen gadon Ibtisam ita kuwa tana bacci, yayin da iyayan nasu suna waje azazzaune.
Wayarsa hannunsa karatun Qur'ani yake, yana karanta suratul Rahman.
Motsi yaji alamun ta farka,yay saurin kallonta yaga ta qura masa manyan kyawawan idanunta, wanda suka riki'de sukayi jajir, sai zarosu take.
Sansanyan murmushi ya sakar mata, ya na 'ko'karin kamo hannunta yaji saukar abu da baisan ko meye ba, kan goshinsa tiss kakeji goshin ya fashe jini ya fara tsartuwa.
Sake 'dagawa tai da niyar buga masa tana sheqa dariya, sai ga Dr Salis ya shigo ya nufo wajan aguje ya na fa'din.
Kana kallo ka riqeta mana......�
*'Yar Ajin Tubarkallah🥰*

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/28/22, 13:28 - Buhainat: ```D A```

```41&42```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_


“Haba! Ja'afar ya zaka biye mata, ka sakata gaba kana kallo zata illata ka. Duba yadda goshinka yake fitar da jini, ita fa ba ruwanta bata san me take ba, amshe pls. Toh wa ma ya kawo kwalbar lemo kusanta ya ajiye?�
Ja'afar yay saurin damqe hannunta mainlafiyar, wanda kuma shi ne yaqe ri'ke da kwalbar, yay saurin matseta jikin bangon gadon yana son amshewa.
Kokowa suka fara, tana 'kurma ihu iya 'karfinta, tana wawuransa cizo.
Mal Adamu da Tanko Laraba Karime wacce tazo yau dan ganin jikin nata,da su Harisu aguje suka shigo 'dakin, sukaga abinda yake faruwa.
Dr ya ce“Karkuyi mgna dole ya kuyi zama da ita, sbd shi ne mai jinyarta ta haqiqa.�
Kallon ikon Allah suke barin Mal Adamu wanda yama 'dansa Ja'afar farin sani,wajan jarumta da 'karfi dan tabbas Ja'afar yama 'kato bugo 'daya mai kyau sai yakai 'kasa, amman ga shi yana 'ko'karin kasawa wajan mace.
Ja'afar kuwa ganin fa da gaske idan ba 'karfin ya sakawa Ibtisma ba toh tabbas zata 'barar da shi, shi kuma tausayinta yake.
Sosai ya saka mata 'karfi ya amshe kwalbar ya beqawa Dr Salis, ya riqeta gam sai fizge² take tana son cizonsa ta 'karfi yaqi bata damar yin hakan.
Cikin 'kasa² da muryasa kamar yadda ya saba mgna ciki² yake amsawa Dr tambayar da yay masa tin shigowarsa.
“Dr ni ne na shigo da ita nan cikin asibiti na siya ina bu'katar abu mai sanyine, ban san ya akayi ta janyo kwalbar, ban ankare ba karatu nake.�
Ya fa'da yana mata kyakkyawar runguma tsam cikin 'kirjinsa ya saka mata 'karfi duk yadda taso 'kwacewa ta kasa sai dukansa take tana kuka tana yagonsa, ta koma 'kyal'kyala dariya.
“Pls Dr yi mata allura ta koma bacci.�
Ya 'karashe mgnar yana tallabe fuskarta da dukkan hannayensa, ya 'kura mata idanu cike da tsantsar tausayinta da sonta.
Manyan idanunta masu matu'kar haske da kyawu wanda suka riki'de sukayi jajir ta qara zarusu tana masa wani kallo tana zum'buro baki tana son mgna ta kasa.
Laraba ta fashe da kuka tana fa'din.
“Ni kam an nakasa min yarinya shi kenan, wlh Ja'afar bazan ta'ba yafe maka ba...�
Tanko ya daka mata tsawa yana fa'din.
“Fita waje Laraba.�
Karime ta ce“Laraba ki kasance mutum mai tawakali da Allah, addukan abinda ya sameki ba ki 'dora alhakin akan wani ba.�
Sai lokacin Ja'afar ya lura da iyayansu a 'dakin, yay saurin janye Ibtisam daga jikinsa yana riqe hannunta. Dr Salis ya ce“Kuje waje pls.�
Bayan sun fita Dr Salis yama Ibtisam allaru take bacci ya 'dauke, sai lokacin Dr yama Ja'afar dressing 'din goshinsa, yana masa fa'da.
“Ja'afar sai kayi taka tsantsa ka lura dan ita ba ruwanta ko wuqa zata iya caka maka aciki ganinta dai daine.�
Ja'afar ya ce“Ok Ngd zan kiyaye.�
Wajan iyayansa ya dawo ya 'dan zauna ka'dan yacema su Harisu su tafi gida zanje ya canza kaya sbd jini ya taba kayansa.
Mal Adamu ya ce“Sai kana lura Ja'afar.�
Kai ya jinjina ba tare da ya yi mgna ba suka nufi gida.

Ja'afar sosai yake gudu saman titi, har sai da Harisu ya ce“Malam ka bimu asannu karka juyemu a saman titi.�
Lips 'dinsa ya cija ka'dan bai ce komai ba, daman sun san bazai ce 'din ba.
Dab da zai karya kwanar da zata sadasu da layin gidansu ya hango wani yaro bazai wuce 'dan shekara 10 ba, kana kallon kasa shuwa arab ne, da sanda alamar ma makahone yana sanye da jallabiya fara tafara 'daukan datti.
Ganin gadan-gadan ya nufi titi ga wani mai mashin daga nesa alamar gudu yake sosai.
Ja'afar ya taka birki da mugun 'karfi ya bu'de motar aguje ya nufi wajan yaron.
Cikin zafin nama ya finciko yaron wanda mai mashin 'din yay nasaran buge gefen kafa'dar Ja'afar sosai yaji zafi ya jure yana riqe da yaron wanda ya sanya kuka sbd mugun tsoron da ya ji.
Mai mashin 'din kuwa bai tsaya ba shegen ya arce sbd yadda yaga Ja'afar bazai tsaya ba ya masa bugun mutuwa.
Jama'a sai sannu suke masu, Ja'afar da gutun larabcinsa da ya fara koya masa mga.
“Bari kuka tinda Allah ya kiyaye amman ka daina fitowa kai 'daya kaji? Toh kai baka gani me yasa ka fito? ina ne gidanku na kaika?�
Yaron ya ce“Kanada kirki ba dan kaiba da na rasa wani abun daga sassan jikina ko na mutu ma, ngd yayana kaji, gidanmu ba nisa nan bayane ka tsallakani zan iya zuwa.�
Ja'afar ya yi mamakin yaron da ya masa hausa, ya kama shi ya 'dauko masa sandarsa ya tsallakasa sai da ya kaisa har kan layin da ya nuna yace nan ne layin gidansu ya koma ya shiga mota.
Yahuza ya ce“Kaga da kai an kashe ka abanza kali har ka gwalje.�
Ja'afar ya ce“Ba komai bakaga amarsu ta fashe min goshi daman.�
Yay mgnar cikin raha, har mamakinsa sukayi dan sunsa ba wani mgna yake da sakin fuska ba.

Auntie Saro sam ta manta za'a iya jinta tin tana kukan a'boye har ya fito fili.
Ummu Adnan ta fito daga kitchen tana tambayarta.
“Saro lafiya kuwa?�
Cikin kuka ta ce“Lafiya lau kawai ina tausayin Raiyana ne Allah bata lafiya.�
Ta fa'da tana meqewa.
Jaddatu tagani tsaye da sandarta.
“Haba! 'Yar nan kokuma kinyi mana la'be ba, kinji abinda Abdul yake fa'da, dan Allah bar kukan. Karki damu insha Allah zataji sauqi akwai malamin da maganinsa warkada masu manyan aljanu Abdul ya ce zaizo ya dubata.�
Jaddatu tana 'karashe mgnar tana tafiya tana kallon hanyar bene ganin Abie tsaye ya fara taka stairs yana waya ya ri'ke 'karfen benen, sai murmushi yake.
Jaddatu ta ce“Hanan wannan yayan naki yau kam acikin nisha'di yake fa!�

Auntie Saro kunya taji ta ce“A'a wlh banji komai ba Ummi.�
Jaddatu wacce tin tuni ta bar corroded 'din kitchen, kai ta ka'da dan ta jiyota.
Hanan tai dariya ta ce“Ai haka mukeso wlh ya kasance cikin farin ciki Ummi.�

Abie 2 ne ya shigo bakinsa 'dauke da sallama.
Jaddatu ta amsa ya gaisheta cikin girmamawa yanama iman wasa.
Jaddatu ta ce.
Ya wajan masu jikin? Ni kuwa uwar Ibtasam take kowa tanada cikakken hankali kuwa Abdul?
Abie 2 yay murmushi ya ce“Ummi kinsan irin abun nan ba kowane yake tawakali ba, gani take yaron shi ya hurema 'yarta kunne ta baro gida.
Yauwa Ummi ga ruwan addu'ar nan aba Raiyana.�
Ya 'karashe mgnar yana hango Abie 1 na 'daga masa hannu alamar ya jira shi.
Kafa'da ya maqale ya miqe yana murmushi ya musu sallama iman ta bisa suka fita, Jaddatu na saka masa albarka.
Hanan ta ce“Ummi kije ki bata ruwan addu'ar mana.�
Sanda Jaddatu ta buga mata duk da ta goce sai da ta sameta.
Ta ce“Ahir 'dinki ki kiyayeni bari mijinta yazo shi ya ga ya iya.�
Auntie Saro taje wucewa taji dole ta toshe kunnenta ta fice.

Anutse ta sauko kai tsaye ta nufi sashen Abienta, tana tafe tana waya cike da nutsuwarta.
'Kofar ta murda ta shigo falon ta fara rarraba idanu zatonta Abie na falon.
Ganin baya nan ta zube saman sofa tana yamutsa fuska idanunta hanyar bedroom 'din Abie.
Can 'kasa da harshen larabci ta furta.
“Shiiiiiiiit! Anee pls ki daina min mgnar Rafeek, ya cika fitina banson damuwa shiyasa nai blocking 'dinsa, na daina aiki da duk wani layina da ya sani, har sai na dawo sbd kinga asharu'dan Abie bazanyi samari ba har sai na kammala karatuna, shi nakeso ya ban dama da kansa, inada tsananin biyayya wa Abiena, sbd yadda yake jini fiye da komai da kowa na duniya ni 'daya tak Allah ya basa aduniya, meye anfanin sa'bamasa ko 'kin masa biyayya matsayinsa na mahaifina? Wlh shiyasa ban yarda nayi saken da son Rafeek zai kaini wajan da zan sa'bawa Abie nah ba, pls karki kuskura ki basa number na sharesa abinda jibi nake dawowa.�
Ta 'karashe mgnar cikin mugun gajiya da doguwar mgnar da tai tana mida numfashi da sauri².
Daga can kuwa (Espagne) wacce aka Kira da Anee zaune take saman sofa fara ce itama sosai kana kallonta kasan balarabiya ce, tanada 'kiba ba kamar Rahma da take mai 'dan jiki ba, sai kayan alatu.
Murmushi Anee tai cikin harshen turanci ta ce.
“Ok.. Ok! Habibty na jinjina yadda kike son Abienki kina masa biyayya Allah yasa da mun kammala karatun mu kina meqa Rafeek matsayin miji ya amshe shi da hannu biyu.�
Rahma tai fari da 'kananin idanunta masu matu'kar kyau ta ce“Amin habibty Anee, insha Allahu zai amshe sa bazai qisa ba, balarabe jansin sane.�
Sosai suke hora hara 'yan shirun suka zo.
Anee jin kamar halin shirun na Rahma ya motsa dan yanzu daga uhmm sai umm-umm take cewa da Anee, shiyasa Aneen tai mata sallama tana qara godiya akan lokacin da aka bata.
Rahma ta shiga 'daukar hotuna sai da tai kusan guda ashirin, ta ajiye wayan, saman center table, ta miqe ta nufi bedroom 'din Abie tana kiransa cike da sangarta.
“Abienah! Kana ina? Wollah tin yanzu ina kewarka.�
Ha'daddan bedroom 'dinsa ta bu'de ta shiga, wani irin sanyin Ac da masifaffan 'kamshi suka kawoma 'kofofin hancinta farmafaki, wanda ya sakata jin wani irin yanayi mai da'din gaske, baccin da yake cin idanunta taji lokaci 'daya tana buqatar yinsa.
Ahankali ta ce“Uhmm! Abiena kana jin da'di fa! Irin wannan 'kamshi ya ha'du da sanyin Ac.�
Ta 'karashe mgnar tana shiga tsakiyar bedroom 'din.
Sam bataga alamun Abie ba ta kasa kunne bathroom nan ma shiru ba 'karan ruwa, sai ta tuna watarana yana shigewa cikin Bathtub ya jima kafin yay wanka dan ta sha shigowa tai ta jiransa idan ya fito tai masa qorafi ya ce kwanciya cikin bathtub yay.
Baki ta zum'buro gaba ta ce“Bari ma naje lambu nasha iska Abie ban iya jiranka na tafi anjima zamuyi mgna akan tafiyata jibi munada jarabawa fa!�
Ta 'karashe mgnar tana tafiya, dan zatonta Abienta na bathroom.
Anutse ta fara taka stairs, hancinta ya jiyo mata 'kamshin Abienta.
Kan da take 'dagowa ta hangosa yana taka stairs cikin kuzarinsa alamar sauri yake ya hayo.
Kasancewar mai kwana² ne kuma ita farkon saukowane. 'Kananun kyawawan idanunta ta firfito waje tana mai cike da mamaki ashe Abien baya 'bangaransa.
Tai saurin juyawa daman stairs biyu kawai ta taka, baya ta koma saman ta la'be a corrode 'din wani 'daki wanda daga shi sai sauka 'kasa.
Tafe yake yana waya cikin nutsuwarsa da kamewarsa.“Ok Abraham Ngd sosai da wannan temakon, yanzu sauran awa 4 jirginmu ya tashi, kaga kenan malamin bazai isko ni ba, tinda kace lallai kafin ya ya iso tsakiyar dare, amman amasa tarba mai kyau abasa masauki zuwa gobe zanyi mgna da Jaddatu sai amasa jagora ya dubata amman duk abinda za'ayi ayishi acikin jama'a, Allah ya kawosa lafiya zan barmaka komai duk abinda za'ayi, Allah yasa adace.�
Ya kai 'karshen mgnar dai dai ya 'karasa hayowa ya shiga rarraba idanunsa sakammakon 'kamshi Rahma da ya baibaye dukkan 'kofofin hancinsa.
Rahma tana la'be tana leqensa yana nemanta still waya yake cikin dadda'dar muryasa, bai daina wayarba bai daina rarraba idanunsa ba nemanta, sbd jikinsa ya basa tana kusansa la'bewa ta yi.
Wayar ya katse yana fa'din.
“Hakan ya nuna Baby bakida gaskiya akwai abinda kike 'boyemin kar na gani shiyasa da kika jini kika la'be koh?�
Ya 'karasa mgnar yana nufar corrode 'din da yafi zargin nan ta la'be.
Wayarsa ta 'dauki ringing ya 'daga yana dafe goshinsa ya furta.
“Ya Rabbi! Mu'az afuwan dan Allah! Ban 20 minutes insha Allah zan fita yanzu da kaina zuwa wajanku, ya hkr da jama'aginin dai ya kusa kammaluwa.�
Wanda aka kira da Mu'az daga can ya amsa da, Ok yalla'bai sai kazo wlh ya matsa yana son ganinka ko yaje can gidan naka ba'a barinsa shiga, shine yaji nan hospital 'dinka ne ake ginawa amman yazo yafi sau ashirin bai sameka ba, kuma an hanasa numberka, dan ko ni gaskiya yalla'bai na hanasa sbd mutane yanzu abin tsorone.
“Abie ya shafi sumar kansa yana sakin murmushi ya ce“No! Karka damu Mu'az ya jirani ina zuwa yanzu.�

Rahma ta zauna da'bas ta lumshe idanunta taji wani irin fa'duwar gaba, ga mugun sanyi na ziyartarta adukkan ilahirin wata 'kofar gashi ta jikinta, wanda hakan yaba ilahirin jikinta damar 'daukan sanyi ba kamar tafin 'kafafunta da tafukan hannunta.
La'bbanta suka motsa ta furta.
“Abiena har kasan inda nake Ayanzu? Pls ka fahimceni ban 'boye dan ban yarda da kaina ba, daga wajanka nake zatona kana toilet...�
Jin fitinannan 'kamshinsa ya baibaye 'kofofin hancinta, hakan ya tabbatar mata Abienta na kusantowa gareta, sbd 'kamshin yafi na 'dazu mamaye hancinta.
'Kan'kame jikinta tai idanunta arufe ta ce“Pls Abie kayi hkr kaji.�
Ta 'karashe mgnar tana beqa masa hannunta alamar ya tayar da ita.
Awarwaron hannunta suka bada sautin 'Kara yayain sarqar 'kafarta ta shiga 'Kara cakasss dalilin 'kafar da take bubbugawa irin tana shagwa'ba.
Jin shiru Abienta bai Kama hannunta ba, ya saka da sauri ta bu'de idanunta ta ga ko dai baizo ba ya yi fushi da ita.
Da sauri ta maida idanunta ta rufe tana janye hannunta ta fara yarfawa, awarwaron suna bada sautin 'Kara, ta fashe da kuka tana fa'din “Innalillahi! shi kenan na jawa kaina mgna............!�
*💃�'Yar Ajin Tubarkallah🥰*

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/28/22, 13:28 - Buhainat: ```D A```

```43&44```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_


Abie ya har'de hannayensa saman 'kirjinsa, ya kafeta da narkukkun idanunsa, cike da mugun mamakinta yadda ta dun'kule waje 'daya kamar me jin sanyi, ta dage tsakaninta da Allah tana gabzar kuka, tana rattabo masa bayani.
“Ni kam shi kenan don Allah Abiena kayi hkr na tuba, wlh ba dan naji mgnar ka bane, nazo corridor 'din nan dan na 'buya. daga wajanka nake zatona kana bathroom, lambune zanje ina tafe 'kamshin ka ya farmaki hancina, ina 'daga kaina na hango ka, ganin kamar waya kake mai mahimmanci shine na 'buya idan ka gama sai na zo gareka.�
Ta kai 'karshen mgnar tana ha'de kai da guiwa tana 'kara sautin kukan.
Abie wani sihirtaccan murmushi yay, ya matso ya tsugunna gabanta, kamar zai shige jikinta sai ya 'dan matsa gefe.
Dab da kunnenta ya kai bakinsa, ahankali cikin wata sihirtacciyar muryasa mai taushin gaske, ya furta.
“Ok.. ok! Baby naji bar kukan, kin san ban jure kukan ki? Toh meye ma na kukan Baby ummina?�
Ya 'karashe tambayar, yana bin dukkan jikinta da wani irin sihirtaccan kallo. “Wow! Babyna wanka ya yi kyau.�
Sanya tattausan hannayensa yay ya 'dago kanta, dab da fuskarta yake fa'din “Shiru baby please, kinga yadda kikayi kyau kuwa? Kin zama kamar 'Yar 15 years ba 18 years ba baby ummina.�
Ya 'karashe mgnar yana zama 'kasan ya shigar da ita cikin 'kirjinsa mai fa'din gaske, ya kwance 'dan kwalin kanta ya barbaje dogon gashin kanta wanda yasha gyara da maiyuka masu tsada yana wani irin fitinannan 'kamshi, ya shiga shafawa anutse yana sumbatar gashin, yana sakin murmushi, ha'di da buga bayanta alamar lallashi.
Rahma tai shiru ta daina kukan tana sauke ajiyar zuciya wata irin nutsuwa na shigarta, ga wani sanyi da yake ratsa zuciyarta, gefe dadda'dan turaren jikinsa mai masifar tsada, 'kamshinsa ya gama kashe mata jiki,tai luf abinta har sake 'kam'kameshi take, tana lumshe idanunta sbd da'din yadda yake sosa mata gashin kanta.
Bakinsa ya kai dab kunnenta, ya fara mata mgna cikin siriryar murya, wanda tsinin la'bbansa ya kasance yana gugar fatar kunnenta, tai saurin 'kam'kameshi tana 'yar dariya.
“No! Baby bar dariya mgnar gaskiya muke, zan miki tuni akaro na uku kinada miji, akwai igiyoyu guda uku akanki, tin kina 'yar 'yar shekara 12 aduniya, ki kiyaye kisan irin shigar da kikeyi, yanzu da hakan za ki fita lambu ki gilma 'kartin ma'aikatan gidan su na kallon ki?�
Ya 'karashe tambayarta yana 'dago da fuskarta wadda take cikin tafin hannunsa, ya zuba mata rikitattun idanunsa, ya na ha'de fuskarshi tam! Alamun ba wasa.
Ya shiga tattara mata dogon gashinta irin na asalin larabawa.
Rahma 'kurr ta masa da idanu, tana nazarin mgnar Abie, sai ta kasa jure kallon nasa ta sadda kanta, ganin Abien ya birkice mata lokaci 'daya sai ya zame mata tamkar wani matashin saurayi 'dan shekaru 30, duk da daman bazaka ta'ba cewa ya kai shekaru 50 aduniya ba, sbd jin da'di ga hutu da ya gama ratsa shi.
Tunanin mgnarsa ta shiga wai tanada miji tin tana 'yar 12 years, ta kula wanda idan bazata manta ba, wannan shine karo na uku,amman yafi shekara bai mata mgnar ba sai yau sbd yasan ba wani mazan take kulawa ba, sannan bata shigar da za'aga ko fatar wuyanta bare bayanta.
Kanta ya fara 'daurewa shin da gaske yake ita 'din matar aure ce? Ta ya zai 'daura mata aure da wanda bata saniba? Kuma tin tana 'yar shabiyu, kenan yanzu shekarunta 6 tanada aure? Sannan ba shawarata? Duk da tai qarama lkcn batan meye aure ba.
Shin yaushe ne ma ashekaru 6 ya 'daura mata auren? Dan yanzu ta shiga wasi-wasi ganin mgnar yau ta banbanta da na shekarun baya, tin batada wayon kirki, yake yawan fa'da mata tanada aure, ta riqe martabarta mijinta yana tafe gareta sai ta kammala karatunta. amman tinda ta zama cikakkiyar budurwa sau 3 kawai ya mata mgnar.
Da sauri ta 'daga kanta kamar an tsikareta.
Idanunsu ya sarqe cikin juna.
Jurewa tai idanunta cikin nasa ta damqe hannunsa, sosai ta fara mgna.
“Abiena, idan ban manta ba, wannan shine karo na uku tin fara zamana cikakkiyar budurwa kana tunatar dani inda miji, amman sai bayan shekara kake fa'damin, wanda hakan yake sakawa na manta na shagala, duk da zuciyata na gayamin banida mijin kana gayamin hakane amatsayina na 'yarka domin na kare martabata da martabar gidanmu...�
Dogon numfashi taja ta 'boye kanta cikin 'kirjinsa wanda jikinta ya 'dauki mugun 'bari sbd yadda ta ga Abien ya kafeta da idanu yana sakin 'kayataccan murmushi, sai kawai kasala ta saukar mata.
Cikin fizgo numfashinta wanda yake 'ko'karin barin gangar jikinta, ta ce.
“Abie nasan bazaka ta'ba cutar daniba, sai dai ta ya kasan inada miji ka bari nayi soyayya da wannan baqin yaron arashin sanin nayi? Sannan kasan inada mijin ranan ka isko ina bacci ka shiga kwararo min da addu'a Allah ya ban miji nagari mai tsoron Allah wanda zai riqe maka 'yarka bisa amana, toh me yasa kayi addu'ar nan um Abiena?�
Abie ya numfasa cikin ra'da ya furta.
“Baby lokaci na tafe, wannan duk mai sauqine babyna randa na miqaki 'dakin mijinki, zan miki bayanin komai, na kuma miki alqawalin randa kika ha'da idanu da mijinki idan har bakya sonsa kinji bazaki iya zaman aure da shi ba zan saka ya sakeki ki kawomin za'bin ranki na aura miki Ok babyna?�
Rahma ta 'dago cike da farin ciki ta ce“Allah da gaske Rabin raina Abie?�
“Wallahi da gaske Rabin Raina ummina, nayi alqawalin sanyaki farin ciki na miki duk abinda kikeso daga nan har na bar numfashi.�
Ya 'karashe mgnar yana 'daga mata gira 'daya ha'di da wani 'kayataccan murmushi wanda ya saka duk ta birkice tama kasa sanin da wa take tare.
Cikin diriricewar da tai ta maqale masa sosai ta manna masa kiss saman goshinsa muryata na rawa ta ce“Ngd Abiena ina sonka kaji.�
'Yar dariya mai 'kayatarwa yay, wacce ta sake rikitata ta sakar masa kukan shagwa'ba.
Ganin kamar ta diririce ta shiga wani yanayi wanda shi yasan meye ya miqe da ita tana jikinsa yana fa'din “Na tuba ummina shiru please. �
Shiru tai

Please Login or Register in order to submit comment