Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nazo na tafi asatin masifar ta sauka a 'kauyenmu basubar kowaba sai masu kwana gaba.
Na shiga tashin hankali kusan mahaukaci nazama banma San 'kashashen da na shiga Neman Aymana ba, har Sudan naje har Nigeria naje na watsar da karatun Abu wasa tin ina saurayi nake yawon duniya inada shekaru arba'in da 5 nazo 'kasar nan banda yawon bara babu abinda nake banda wajan kwanciya sai kango idan ruwan sama yazo haka yake kusan qarewa akaina sabida 'dakin zana ne gareni shekaruna 4 anan ayanzu inada shekaru 49 aduniya wlh ban ta'ba sha'awar aureba sbd nasan ba mai aurena, sbd talaucina na zama tsohon 'karfi Rana tsaka Allah ya ha'dani da Rahma yarinyar albarka ta temakamin tamkar ta sanni.�
Ya 'karashe mgnar yana kuka.
Abie ya rungumeshi yana buga bayansa ya ce“Alhmdllh! Haqiqa Allah shine sarki gagara misali wanda baida abokin taraiya, 'kudurar ubamgiji yawa gareta Allah qarawa Annabi daraja. Abdulmajid! Rahma da kake ganinta 'diyar Ummu Aymana ce.�
Wani irin juyi Abie2 yay yana kallon Abie cike da mamaki, Abie ya ce“Wallahi nine wanda ya ceto Ummu Aymana daga Iran na.kawota Morocco.�
Wani irin kuka Abie ya fashe da shi ya rungume Abie yana fa'din.
“Don Allah kirawota na rungumeta naji gumin 'diyata jinina dangina families na da ta ragemin aduniya, Abdulmajid Allah ya biyaka da gidan Aljannatul Firdausi, wlh zan iya rantauwa irinka Baku kai gomaba a duniya ba, ba banza nakwjin yawan fa'duwar gaba akan 'diyar albarka da farko na 'dauka da sonta na kamu, amman ashe ba haka bane son da nake mata naji ya babanta da son aure ashe jini nace.�

Abie ya ce“Please kabar kukan godiya zakama Allah, ba kuka ba barci take bari naje na tadota.�
Abie ya 'karashe mgnar yana sakinsa ya miqe ya fice.
Sosai ya yi mamakin 'kofar falo a bu'de kai ya girgiza ya wuce bedroom.
Kwance take ta k'udundune cikin blanket tana shara baccinta.
Blanket 'din ya janye ya sanya hannunsa ya cicci'beta sama yana juyi da ita, yana sumbatar ta a wuyanta yana fa'din.
“Oya my baby bu'de idanunki yau ba baccin safe, bu'de na baki labari.�
Rahma tai miqa ajikin Abie tana bu'de kyawawan 'kananun idanunta, wa'danda suke cike da bacci ta kalleshi ta kwa'be fuska ta ce“Wayyo Abie bacci pls.�
Ta 'karashe mgnar cikin jin kunyar miqar da tai, ta kauda kanta sbd kallon da Abie yay mata ya kashemata jiki.
“Uhmm! Babyna ki daina min wannan miqar wlh zanyi wani abun. Albishirnki?�
Rahma ba tare da ta kalleshi ba ta ce“Goro.�
Kiss me na fa'da miki.�
Ashagwa'be ta ce“Abie kunya nakeji wlh.�
Sauketa yay ya zaunar da ita saman bed, ya rankwafo ya tallabo fuskarta ahankali yana qara kusanto da fuskarshi dab da tata yana mata wani irin kallo, wanda yasa taji duk gashin jikinta na tashi atsorace ta ce“Abienah me zakayi.�
Dai dai lokacin ya kawo bakinsa dab da nata cikin kasalalliyar murya ya shagwa'be ya ce“Babyna bakinki zan Sha pls.�
Zatayi mgna taji har ya tura mata la'bbansa duka cikin bakinta ya kamo 'kungunta da hannun 'daya.
La'bbansa kawai yake goga mata acikin bakinta yana sauke mata hucin numfashinsa yana hura mata iskar bakinsa.
Sai taji ya kamo harshenta yana tsotsa anotse yana murza 'kugunta.
Idanunta alumshe Sam batayi yunqurin hanasa ba, tanajin yadda yake wasa da harshenta yana bata yawunsa had'iya kawai take tanajin kissing 'din kamar zata makance dan da'di, amman kunya ta hanata Kama masa.
Hannunsa taji acikin rigarta ya kamo mutumin yana shafawa.
Idanu ta bu'de tana son zare bakinta yaqi, kallo 'daya ta masa tai saurin runtse idanunta tana sauke numfashi.
Dole ta barsa yay wasansa son ransa ya barta.
Dariya taji yana mata lokacin da ya saketa ya zauna kusanta kamo kanta ya yi ya 'Dora bakinsa saman kunnenta ya mata ra'da yana shafa wuyanta zuwa kanta.
“My heart ke 'dince special mugun sonki nake kina burgeni komai naki na daban ki dinga hkr da Rabin ranki haka fa zamu rayuwa cikin so da kauna ki Saba da fitina ta zan koya miki ba maganar kunya, oya canza kaya muje wajan Abie 2 na nuna miki wani Abu.�
Ya 'karashe mgnar yana tsotsar 'kasan wuyanta.
“Wayyo Abie ka bari wlh nauyinka nakeji.�
Dariya yay ya ce“Uhmm! Da zaran na baje kulina an wuce wajan idanu zan bu'de miki My Babyna.�
Da kansa ya canza mata kaya, jallabiya ya saka mata ya yane mata kanta da mayafi ya sunkuceta ya goyata bayansa.
Kanta ta tsinta da 'yar dariya ta maqaleshi.
Tafiya yake yana mata hira amman ta kasa basa amsa sumar kansa take shafawa idanunta arufe ta ce“Abie baka tsoron Ammi ta ganmu?�
Ashe Rayyana na la'be duk tsotsar da Abie yama.Rahma akan idanunta, lokacin da ya haura saman ta bu'de 'kofarta da niyar zuwa wajansa ta gaishesa ganin ya nufi 'dakin Rahma ta bisa dan taga lafiyar Rahma ganin jiya kamar batada lafiya.
Abinda ta ga Abie yanama Rahma ne ya girgizata taji duniyar na juya mata ta toshe bakinta tana tsaye tana kallonsu kamar dole sai da suka gama yana shiryata ta fito ta sauko ta la'be 'kofar 'dakinta tana kuka tana tunanin me zatama Rahma ta huce.
Daidai 'kofar falonsa taga ya ajiye Rahma ya ce“My Baby tsaya na 'dauko laptop. �
Rahma ta 'daga masa kai ya bu'de falon ya shiga.
Raham murmushi tai tana binsa da kallo har ya shige.
“Rahma!�
Rayyana ta kirata da 'karfi.
Juyowa tai ta Saki fuska tana amsawa da “Na'am ammi ina kwana? Kedawa kike kuka?�
Rayyana ta ce“Nida ubanki Yar kutumar uba shegiya munafuka tsohuwar karuwa, ashe iskanci kuke keda uban naki shiyasa kikaqi karatu kika dawo kuka tare kuna zina shikuma shiyasa yaqi sauke nauyina ashe 'diyarsa yake ci yan buro uba shego yan iska.�
Rahma ta zaro 'kananun kyawawan idanunta waje wanda sukayi ja tsabar b'acin rai tana fa'din.
“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!...�
Bata rufee baki ba Rayyana ta yi kukan kura ta damqo wuya Rahma ta shaqeta sosai tana kishinta ta ce“Na rantse da Allah sai na kasheki dan ubanki karuwa kwartuwa me bin mazan mutane.�
Rahma tsoro ya cikata abinka da 'yar hutu bata Saba fa'daba ita yadda zata 'kwaci wuyanta ahannun Rayyana take qoqari ta kasa ga shi bata Iya ihu sbd shaqar da ta mata bata wasa bace.
Abie na fitowa ya yi mugun gani ya Saki laptop aguje ya isa yana fa'din.
“Innalillahi wa'inna ilahiri raji'un, shi kenan ta kashemin ita.�
Wani irin mari ya gaurama Rayyana wanda take taga wuta na gilmawa ta Saki Rahma tana 'kurma ihu.
Rahma wacce take neman sumewa sabida azaba ta tafi luuuu zata fa'di Abie ya tareta ta fa'do jikinsa ya 'dauketa sama ya jefata bayansa ta qamqameshi tana sakin kuka Mara sauti ta ce“Abie mutafi ka 'boyeni kasheni zatayi dan Allah kaini wajan Jaddatu.�
Abie ya ce“No! Babyna bari naci ubanta tukun ashe ita 'din ba 'yar arziqi bace.
Ke kin isa ki ta'bamin matata mafi daraja, kinsan wacece Rahmata gareni? Duk tuggun da kika shirya baya bai isheki ba yanzu rayuwarta kike nema? Ashe tuban muzuru kikayi? Ai dama hali ajikin rai, Toh jeki na sakeki saki uku bani ba ke wlh na fasa miki duk abinda zan miki, yanzu nakeso kibar min gidana kafin nasaka amiki korar kare. Baku iska kun rabani da Ruhina ba, abadant ita 'din tawace.
Azzaluma da ni kika buga kin tsira amman Baby tafi 'karfinki wallahi.�
Yana gama maganar yasa ya tafi.
Rayyana wani irin ihun kuka take tana fa'din.
“Wlh baka isaba zama daram agidan mijina akan kwartuwa zaka korani...�
Wani irin baya² ya yi ya dawo ya harbi bakinta da 'kafa sai ga jini.
Rahma ta qamqameshi tana kuka.

Tafiya yay yana kiran waya.
Rahma ta warce wayar ta kashe.
“My baby bani wayata.�
Kuka ta sanya amsa ta ce“Ka barta na yafemata Abienah, don Allah karka 'bata ranka ina lafiya Abie.�
Shiru yay yana taka steps.
Sai da yaje dab da Inda za'a yi hangosu daga falon ya saukota ya rungumeta yana dubata ya shafi fuskarta ya ce“Ina yake miki ciwo babyna?�
Rahma ta tsura masa idanu sonsa kawai yake 'dawauniya da ita.
“Babu Abie dan Allah tinda dai ba abinda ya sameni ka rabu da ita ta tafiyarta kar akamata pls Baby.�
“Ok naji Babyna oya muje wajan Abie 2.�
Hannunsu maqale cikin na juna suka sauko ba kowa a falon daman kuma yasan sai wajan 9 ko Jaddatu ta fito. ummun Adnan da Latifa ya 'kwalama Kira.
Sai gasu daga kitchen suna shirya abinci breakfast.
Zubewa sukayi suna gaishesa ya amsa.
“Ku shiga Ku sanya Raiyana gaba ta fito umarni na Baku idan taqi Ku Kira Meerah na can sama hawa na 2 ta temaka muku Ku fito da ita har harabar gida.�
Cikin girmamawa suka amsa suka nufi sama,Abie yaja hannun Rahma suka fice zuwa wajan Abie 2.........


_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/30/22, 21:21 - Buhainat: *Yauwa lokaci ya qore akwai sauran labari, bazai yiba na kammalashi a page biyu ko uku dan haka mu ha'du bayan sallah insha Allahu, wlh aikin gyara gidana zanyi gobe da jibi, Ngd kuyi hkr dan Allah.*


```D A```

```89&90```


Aslm please wlh ba Editing ina uzuri sosai idan kukan typing errors afuwan.��


Rayyana kuwa tinda su Abie suka barta, ta zube wajan bakinta na fitar da jini, sai biegima take, tana bori sai sambatu take tana fa'din.
“Wallahi Abdulmajid ban sakuba, shin wai ya akayi naji yana cewa matarsa? Agidan uban wa uba ya ta'ba auren 'yarsa..? Kan buro uba wallahi ba'a isa ba, duk duniya ba mai rabani da mijina, wlh ban sakuba, Saki uku lokaci guda azaman Saki guda yake, dolene ka maidani 'dakina naci uwar shegiyar munafukar yarinyar nan, daman can shiyasa bana sonta sabida ina kallon idanunta naga tana ruwan karuwai munafukai, wayyo Allah na!! Jama'ah kuzo an sakeni Saki uku wlh bazan bar gidan nan ba akan karuwa...�
Meerah ce taji ihun da kukan daga can ta bu'de 'kofa ta fito, ta sauko gudu sauri² ta iso wajan Rayyana tana fa'din.
“Subahanallahi! Auntie me ya faru?�
Tana qoqarin Kama Rayyana.
Cikin zafin nama ta miqe ta wanke Meerah da mari ta ce“Uban babanki ya faru shegiya munafuka, sai naci uwarku keda munafukar karuwan uwar gidanki...�
Latifa da Ummun Adnan ne suka iso suna fa'din.
Haba! Auntie me kikeyi hakan?�
Takalmin 'kafarta ta cire ta jefa musu tana kuka ta ce“Karku ta'bani ni wallahi duk na tsaneku ace duk kuna gidan nan bakusan me akeba? Abie da Rahma suna iskanci bakuda labari dan na kamasu ya sakeni Saki uku wlh ban sakuba ina sonsa...�
Latifa ta ce“Au sharrin da za ki k'ulla musu sbd ya sakeki? Ai wlh yamun daidai dan nasan ba kin tuba dan Allah bane...�
Rayyana ta ce“Ke! 'Yar aiki zanci ubanki ki tsaya a matsayanki na 'yar aiki nan ba huruminki bane.�
Bugo ta kaima Latifa, Latifa ta tare ta 'dauketa da mari ta hanka'data ta ce“Ai tinda Yalla'bai ya cika aiki alqur'an ba sassauci Ummun Adnan kuka mata mufitar da alqaqai wa za ki buga? Tab ni wlh sai muyi damben mutuwa ban tsoronki, Meerah shiga 'dakinta na da 'dauko hijabi mu cika aikin oga sbd nasan bazata fita da 'kafarta ba.�
Aikuwa Rayyana na ihu Latifa ta riqe 'kafafunta sabida shegen 'karfine da ita.
Ummun Adnan da Meerah suka Kama hannayenta tana ihu suka 'dagata sama suka nufo 'kasa da ita.
Jaddatu da Hanan tsaye suna kallon hanyar bene.
Jaddatu ganin su Latifa da Rayyana kamar sun 'dauko kayan wanki, Jaddatu ta ce“Lah! Me nake gani ni Rahmatu? Latifa meyake faruwa?�
Latifa suna tafiya ta ce“Oga ya ce“Muje mu fito da ita mu rakata har filin gidan, wai ya koreta taqi tafiya.�
Jaddatu ta ce“Kai Masha Allah Abu ya yi kyau, wani mugun abun ta shuka musu asaman ko?
Rayyana kan atafi bari kiji Rahma matar Abdul ce ba 'yarsa ba ayau zan saka ranan tarewansu, muguwa azzaluma kinso 'bullo mana ruwa Allah ya jiqanmu, Aqara gaba abarmin yarana su hutu yanzu lokacin hutunsu ne ya 'dauki abarsa su tafi yawon bu'de idanu, agaishemin da dandab'asa duk da ita ba irinki bace.�

Rayyana ihu take tana kuka ta ce“Allah ya isana kun ha'inceni ban yafeba...�
Latifa ta buge mata baki suka jata suka fice da ita tana ihu.
Hanan ta girgiza kanta ta ce“Allah kyauta wane wulaqanci yafi wannan? Rayyana banso kukayi rabuwar rashin arziqi da Ya Abdul ba.�
Jaddatu ta ce“Yo ai ba 'diyar arziqin bace, dole anuna 'dan hali muje muyi kwanciyarmu kan abin kari ya kammala.�

Komawarsu 'daki daman ihun ya tashe su.
Duk nisan gate sai da suka kaita har bakin gate suka ajiyeta suka juyawarsu.
Rayyana irin kallon da taga Ana mata yasa ta fice daga gidan tana kuka.

Abie 2 na zaune ya zubama qofar falon idanu, su Abie suka shigo da sallama.
Abie ya amsa yana hawaye ya warema Rahma hannayensa.
Hannun Abie ta matse tana kallonsa ta ce“Abienah naje wajan Abie2 ? Me ya samesa yake kuka?�
Abie ya matsa hannunta sosai cikin nashi, ya mata ra'da akunnenta.
“My Baby my heart eh jeki, shi ne yayan Ummul Aymana, congratulation my baby naji da'din samun jinin mahaifiyarki zaku rayu tare.�
Rahma ta qamqame Abie ta ce“Ngd ngd ngd Rabin raina.�
Ta sakeshi ta fashe da kuka da gudu ta nufi wajan Abie2.
Jikinsa ta fa'da ta 'kam'kameshi tana kuka, ta ce“Allah sarki Abie2 nah ashe dai Abien nawane, Alhmdllh! Allah na godema zan rayu da jinin mahaifiyata, Abie2 ina sonka don Allah ka kasance tare da mu har abdan bazan barka ka koma Iran ba bare akashemin kai. Naso na rayu da ummata nasan macace me kirki zata riritani zan mata shagwa'ba zan dinga tsokanarta na zubawa da gudu tana bina tana ku kamomin ita yarinyar nan batajin magana fa! Wlh ina son ummina ina son Abbana ina son Mustapah, ina son Abienah amman son Abienah ayanzu na daban ne duk son da nake musu na ha'damasa shine kowa nawa sai yanzu da na sameka Abie2, kai zan ba rabin 'kaunar Abienah.�
Abie2 shima kukan yake ya rungumeta ya ce“Nima bazan tafi ba 'diyar albarka muna tare insha Allah, Abienki shine uwarmu shine ubanmu dole ki masa son so amman ai shine mahaifinki ko.�
Abie zama yay gefensa ya tallafe kumatunsa da tafukan hannunsa ya zuba musu idanu yana kallonsu kamar Tv, bai hanasu kukan su ba sunata sambatunsu.
Rahma ta basa dariya sabida ta kasa amsa tambayar da Abie 2 ya mata.
Numfashi yaja yay gyaran murya ya ce.
“Toh dai kukan ya isa haka pls ai Baby bazata amsa maka tambaya ba, bari na baka tarihin ha'duwata da Ummul Aymana...�
Abie nan ya tsakura masa labarin Aymana na ha'duwarsu da soyayyarsu da sadaukarwa da yama Aliyu zuwa haihuwar Rahma da basa ita da sukayi da 'daura aurensu da Abbu yay da kashe shi da Naja'atu tai, da dalilin zuwansa nan.
Abie2 ya ce“Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abdul Majeed sannu kai kam na daban Allah ya halicce ka acikin mutane, wlh bansan Kalmar da zan gayamaka ba, komai ka wuce akiraka tsakanina da kai kawai nayi ta maka addu'a da fatan alkahir har numfashina yabar gangar jikina, ban ta'ba murna da farin ciki ba irin na yau naji da'din 'diyar albarka matarka ce ba namijin da ya cancanta ya zauna da ita matsayin mijinta sai kai, kaine uwata Kaine babanta yayanta 'kawarta komai nata.�
Abie ya murmusa yana jinjina kansa, ya kamo hannun Rahma ya zare wayarsa cikin hannunta, yana latsawa.
Rahma ta kalleshi ta kalli Abie2.
Abie2 Yay murmushi ya ce.
'Diyar albarka 'dagani na wanko fuska�
Rahma janye daga jikin Abie2 tana goge fuskarta.
Hanyar bedroom ya nufa.
Kallon Abie tai yana waya.
“Hello yauwa a ha'doma komai na breakfast akawo mana 'bangaran Abie2.�
Katse kiran yay, ya danna number Abby morocco.
Ringing biyu aka 'daga.
Da hannu ya yafito Rahma yana 'daga mata gira, yana mata nuni tazo kusansa.
Kanta ta kauda ta 'daga kafa'da ta ce“Naqi awajan babana nake.�

'Yar dariya yay yana kallonta cike da so ya fara amsa wayar.
“Hello Abby! Baku taso ba?�
Daga can Abby ya amsa da.
“Ai jirginmu sai 10 na safe zai taso insha Allahu, ina rigiman manka?�
Abie ya ce“Gatanan ta ha'du da babanta ta shareni ina kiranta.�
Yanayin da ya yi mgna ya sanya Rahma juyowa ta kalleshi tana girgiza kanta.
Abby yay dariya ya ce“Wani uban kuma?
Abie ya ce“Wlh dattijon da yake gidana ashe yayan Ummu Aymana ne, daman najima ina zargin hakan ban dai tabbatar bane.�
Abby ya ce“Masha Allah naji da'di yarinyar mu ta sake samun gata.�
Sunyi 'Yar hira yaba Rahma wayan akunyace yau ta gaisa da Abby ba kamar daba, har yana tsokanarta.

Abie2 na fitowa Latifa na shigowa da 'katon tray shaqe da kayan breakfast, da sallama.
Leda ta shimfida saman carpet ta ajiye tray'n atsakiya ta gaishe da Abie2.
Abie ya ce“Yauwa Latifa fatan kunyi aikin da na baku?�
Cike da ladabi ta ce.
“Eh Yalla'bai ai tin yaushe har 'kofar gate muka kaita.�
Abie ya jinjina kansa ya ce“Masha Allah Ngd tashi kije.�
Rahma da kallo take bin Latifa har fita.
Abie ya ce“Baby sakko mu karya, ha'dama.�
Baki ta zumb'uro ta sauko kusan Abie2 ta zauna ta ce“Abie2 kaga Abie ya saka na kori ammi ai bai kyauta ba ko?�
Kallonta Abie 2 ya yi cike da mamaki ya kalli Abie wanda ya zubama Rahma idanu yana mata kallon mamaki.
Abie2 ya ce“A'a baka kyauta ba me ta yi?�
Abie ya harari Rahma ya ce“Uhmm! Wlh kashemin ita ta kusa na isko ta shaqeta da bana kusa ai shikenan.�
Abie2 ya ce“Subahanallahi bata kyauta ba.�
Rahma ta ha'da musu tea me kauri ta zuba musu farfesun kan rago kubus gefe ga soyayan dankalin turawa normal ba kwai.
Akunyace take ci sabida kallon da Abie yake mata.

Can ciki kuwa Jaddatu baccinsu suke cike da nutsuwa.
Yayin da Rayyana tana can kamar mahaukaciya sabuwar kamu.
Gidan nasu ta fa'do aguje tana ihu da kururuwa, Auntie Saro a kitchen tana ha'da breakfast taji ihun Rayyana.
Fitowa tai ta ce“Ke! Lafiya me ya faru na shiga uku.�
Rayyana ta riqe Saro tana kuka ta ce.
“Ya sakeni Saki uku kawai dan na kamasa da 'yarsa suna alfasha wlh kamasa nayi yana tsotsarta, kawai dan na fa'data da bugu ya sakeni, don Allah Auntie ki temaka min na koma ina sonsa.�
Saro ta ce“Ta faru ta qare nasan za'a rini bakyajin mgna 'kun'kurus tafaru ta kaqare, amman 'karya kike koda kin kamasu na yarda akwai 'boyayyan al'amari, ba wai yana alfasha da ita bane, wannan mutumin baka shedar 'dan Adam amman wlh ban yarda zai aikata zina ba, duk wanda ya kiyaye dokokin Allah da wuya ka sameshi cikin masu aikata alfasha, bare babban zunubi irin wannan.�
Rayyana ta ce “Ya ce wai na isa na kashe masa mata uwarsa ta cemain wai Rahma matarsa ce ba 'yarsa ba, 'yan aiki aka saka suka min 'daukar 'yan wanki suka fiyo dani waje, yaushe Rahma ta zama matarsa?�
Saro ta kamo hannunta suka shiga ciki zaunar da ita tai ta kawomata ruwan sanyi ta bata Tasha ta kamo hannunta ta ce“Abinda zan gayamaki anan shine kiyi hkr ki cire Abdulmajid aranki wlh najima da ciremiki shi arai, da nasan abinda kakiyi zaiyi wuya yaci gaba da zama dake daman irin ranan nan ya miki tanadi dan haka wlh karki kuskura kice zakibi malamai sbd ba aure tsakaninku Saki ukune kiyi hkr ki dage da istigfari ki tsarkake zuciyarki wlh za ki samu muji kiwa Allah ki Santa zuciyarki hkr ina jiye miki aikin da nasani irin wanda kikayi kwanaki ki manta da rayuwar da kikayi da shi ki fuskanci gabanki yanzu ki Kama kanki don Allah, daman can ALLAH ne ya 'kaddara akwai aure tsakaninku amman ai ba sa'an aurenki bane, sai dai kashhh! Damar da ya baki kikayi wasa da ita dan haka shawarata kiyi hkr ina jiye miki aikin da na Sani wlh idan kika je kika gingimo babban aiki ba hannuna ba 'kafata kiyi tawakali da mabuwayi gagara misali sai komai yazo miki a sauqi.�
Rayyana sosai jikinta ya yi sanyi ta share hawayen fuskarta ta ce“Na miki alqawali zanyi aiki da shawaranki duk da ina masifar sonsa zan jure na Kama rayuwa sabuwa yanzu na kuma yarda ni ce na janyo kome ya faru dani zanyi qoqarin gyarawa.�
Saro ta rungumeta ta ce.
“Naji da'di sosai Allah ya shige mana gaba adukkan lamarinmu.�
“Ameen.�
Rayyana ta amsa, nan ta kwanta sbd ciwon kan da take Saro ta tafi ta qarasa girkinta.
Can gidan Abie kuwa cikin farin ciki aka wuni,su Jaddatu da suka samu labarin Abie2 yayan Ummin Rahma ne, Rahma tana kusan Jaddatu wuni guda sai dai ta kasa sakewa irin na da, Abie kuwa ya fita sha'aninsa zuwa companynsa, su Meerah kuwa anata girke² tarbar baqi.

*Niger*
Misalin 'karfe 6 na yamma.
Ibtisam zaune, can gefe abinta tana qanqaran faratanta, har yanzu 'kirjinta zafi yake mata, haka la'bbanta basu idasa sacewa ba kamar yaune ya mata muguntar.
Tsaki taja ta ce“Mugun banza Allah sai ya saka min, ban yafe ba.�
Laraba dasu Karime akan kunnansu abinda data fa'da.
Karime ta ce“Wlh zakici ubanki wannan mugun halin bazaki kaiki ko inaba sai nadama, kibi a sannu fitinanniya kawai.�
Laraba kam batace uffan ba dan tana mgna Karime ta ce ita ta koya mata.
Taslim ta ce“Aunty Ibtisam anata shiryaki kina baqin hali wlh duk kyan amarcin naki zai zube ai.�
Miqewa tai daman tana sanye da hijab ta ce“Na tafi gidan Dadda nan gidan ba mai 'kaunata.�
Karime ta ce“Ai za ki dawo jeki Allah kiyaye.�
Aydah ta biyo bayanta suka tafi.
Dab zasu karya kwanar gidan sai ga Ja'afar saman mashin yana tuqi yana waya sai murmushi yake, sanye yake da 'kananun kaya.
Sauran ka'dan ya bugeta yay saurin taka burki ya 'dago da niyar basu hkr dan baima lura da suba.
idanunsu ya ha'de waje 'daya.
Take Ja'afar ya ha'de fuska kicin² yana mata shegen kallon rainin wayo.
Ibtisam kuwa gabanta ya fa'di, tsoronsa ya shigeta ga wani irin kwarjini da ya mata, ya yi masifar kyau.
Kanta ta sadda k'asa tana Jan hannun Aydah zasu wuce.
Aydah ta ce“Yaya Ja'afar ina wuni lah! Gidanmu zaka? Mu kuma zamuje gidan Dadda.�
Ja'afar ya Saki fuska ka'dan ya amsa gaisuwar ya ce“Aikenku akayi ne?�
“A'a Auntie ce kawai zataje shi ne zan rakata.�
“Ok.�
ya ce yana kallon Ibtisam, ya ce“Wa kika tambaya? Ko zaman kanji kike?�
Kallo 'daya ta masa ta sadda kanta 'kasa tana wasa yatsun hannunta ta ce“A'a zanje amsa abune�
“Koma toh gida wlh na sake jin labarin kin fito kinsan halina, ware anan 'yar rainin hankali. Aydah na hanata Ku koma gida kinji yarinya me hankali, ki gaishemin da Nadra da Taslim.�
Ibtisam ta saci kallonsa ta juya suka koma gida, ya kunna mashin 'dinsa yay gaba.
Da kuka ta shigo gidan tana fa'din“Yanzu Ana gani wannan baqin mugun zai kasheni da basin ciki baza'a raba aurenba.�
Karime ta jefa mata takalmi ta ce“Anqi araba dan ubanki keda shi mutu ka raba uwad mugun hali. Aydah ya akayi kuka dawo?�
“Umma da Ya Ja'afar muka ha'du ya koromu gida ya ce ba'a zuwa gidan Dadda wa ta tambaya tinda ba aukenta akayi ba mu dawo gida.�
Laraba ta ce “dakyau wlh yayimin daidai.�
Ibtisam d'aki ta shige tana turo baki.

Inna suna zazzaune Deluwa na girki anata hira.
Ja'afar ya shigo da sallama da qatuwar leda ahannunsa, ya beqama Inna Hansatu.
“Kai Masha Allah har an gama 'dinku nan?�
Ja'afar ya ce“Eh innata ai Saidu bai wasa da cika alqawali, ki cire naki ki ba umma nata ga na Baaba a ajiye masa bari na watsa ruwa.�
Ya fa'da yana sauke numfashi ya juya zuwa 'bangaransa.
Deluwa ta ce“Allah ya maka albarka Ja'afar ya tsare manat kai gabanka da bayanka.�
Ya amsa da “Ameen umma.�
Innah aka ranga'da gudu“Allah saka maka da alheri baqin buzuna.�
Maimou ta ce“Wlh da nasani daman can nakai.�
Deluwa ta ce“Su Sadiya kuwa can suka kai Ja'afar ya tamabyo musu.�

Ja'afar yana fitowa daga wanka Ana kiran magarib yay alwala ya tafi masallaci.

*Gabon*
Bayan sallar magarib Aishatu ta sulale ta tafi gidan Rabi'ah.
Zaune take atsakar gida ta yi tagumi ta rasa abinda yake mata da'di arayuwatar,kamar amafarki taji sallamar Aishatu.
Da sauri ta 'dago kanta ta kalli hanyar shigowa gidan, ta ga ita ce.
Mamarta ta ji ta amsa sallamar.
Cike da jin kunyar Aishatun, tana fa'din.
“Aishatu kece agidan namu? Sannu da zuwa wuce ciki mana.�
Aishatu fuska sake ta amsa kamar ba komai, ta nufo wajan Rabi'ah wacce ta kasa motsi kamar ruwa ya cinyeta.
Dakyar ta miqe tana cewa“Mushiga ciki.�
Aishatu ta bita abaya ba tare da ta tanka mata ba.
Kai tsaye 'dakinta suka shiga, ta nuna mata gefen katifa.
Zama tai ta ce“Ya jikin? Allah ya raba lafiya, yauwa ba wai wata alaqa ta kawoni wajanki ba, a,a nazo na tunasar dakene, karki kuskura ki amince idan Ma'aruf yazo miki da mgnar zubar da ciki, kiji tsoron Allah kibar cikin nan ki haifeshi ba'a San me abinda aka Haifa zai iya zama ba, nan gaba, dan haka kuji da zunubin zinar ma, na barki lafiya.�
Rabi'ah tai saurin riqe Aishatu tana kuka ta ce.
“Don Allah Aisha ki yafemin, naji kin yafemin ki sake yafemin.�
Karki damu ai ni baki cuceniba, kanki kika cuta, wlh ba komai na yafe miki, duk meson

Please Login or Register in order to submit comment