Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

latsawa waya sai da ya shigo tsakiyar falon ya 'dago kansa.
Karaf idanunsu ya sarqe waje 'daya.
Kansa ya kauda yana fa'din.
“Ya Rabbi! Yarinyar nan anya doctor Moha ya dubata sosai ta warke?�
Koda ya yazo saitinta baiyi yinqurin mata mgna ba,ya wuci ya nufi 'kofar fita.
Muryata ya ji tana gaishesa.
“Balarabe ina wuni?
Abie ya amsa bai waigo ba, ya ce“ki kirani da Abie sbd ni babanki ne ko bakiga nakai sa'an Tanko ba? Ko ba komai na haifi 'diyar da ta fiki shekaru.�
Ya 'karashe mgnar yana bu'de 'kofar zai fice.
Aguje ta iso wajansa ta 'dora hannunta saman handle 'din kamar zata shige jikinsa ta ce“Ni dai wlh Babana ya girmaka yaushe zaka haifeni ni dai wlh bazan ce Abie ba, Balarabe zance sam baka ruwan tsofi, kai ya kamata akiraka 'dan matashin dattijo wlh, ni dai don Allah Balarabe ka kaini hospital kalli hannuna ciwo yake.�
Ta 'karashe mgnar ashagwa'be kamar zata shige jikinsa tana matsar 'kwalla.
Abie da sauri ya matsa gefe yana kiran sunan Allah sbd yanzu ya karanto meke dawainiya da ita.
“Ok.. OK! Ban waje na wuci bari na kira Dr.�
Tana matsawa yay saurin wucewa.
Ibtisam ta dorqushe nan tana sakin kuka tana fa'din.
“Ba wanda zai fahimci me nakeji akansa wlh ba laifina bane ba.�
Tanko da yake tsaye a'kofar bedroom 'dinsu yana kallon komai, baki 'daya kunya ta rufesa baima San yanzu ta inda zai fara ba.
Isowa yay ya duqa ya 'dago Ibtisam ta miqe.
Ganin Babanta hankalinta ya tashi jikinta ya 'dauki rawa sai taji fitsari na son ku'buce mata.
Bakinta na rawa zatayi mgna Tanko ya buge bakinta yajata har bedroom 'dinsu.

Laraba tana linke kayansu Tanko ya jefo mata Ibtisam.
Laraba ta ce“Toh me kuma ya faru?�
“Wallahi Laraba na fara tirr da aureki, kinga irin tarbiyar taki ko? Kinga abin kunyar da take son janyo min, babban mutum irin Abdulmajid zata tsaya tana neman raina masa hankali, idan ba dalilin dalili ba ina na isa na zauna inuwa 'daya da shi. Wlh yau 'din nan ba gobe ba zamubar 'kasar nan.�
Ya fice fuuuu rai a'bace.

Ja'afar yana zaune a compound 'din gidan jikin wasu flowers.
Abie nan ya isko shi.
Cikin girmamawa suka gaisa, Abie ya ce“Ja'afar je ka fito da Ibtisam sai direba ya kaiku hospital ta ce hannunta na ciwo.�
Tanko ne ya iso wajan naso.
Abie ya ce“Daman kana wajan kaima?�
Tanko ya ce.
“Abdulmajid tinda yarinyar nan ta warke don Allah kawai yau mu juya zuwa gida, kuma jirgin Niger direct ba sai mun koma chad ba.�
Abie ya ce“A'a ai dole sai goben ni zan wuce Espagne wajan baby kwana 'daya zanyi sai na isko ku Chad akwai hira zamu tattauna akan karatun Ja'afar dan Allah ka hkr muje tchad.�
Ja'afar yay godiya ya miqe ya tafi kiran Ibtisam.
Tanko ya ce“Toh ba damuwa duk yadda kace haka za'ayi Allah ya kaimu goben.�
Abie ya amsa da “Ameen.

Tinda Tanko ya fita Laraba ta balbale Ibtisam da fa'da.
“Wai make faruwa? Ko so kike ki kashemin auren?“
Ibtisam tana kuka ta ce“Wlh A'a Anna ni bansan meke damuna ba ki min addu'a kawai bana fatan sanadina Baba ya sakeki insha Allah zan kiyaye.�
Laraba ta ce“Koma meye kibarwa Allah shine masanin sirri da gaibu kinji?�
Kai Ibtisam ta gya'da tana kuka.
'Kofa aka 'kwan'kwasa Laraba ta ce“Tashi kije.�
Miqewa tai jiki ba 'kwari ta bu'de 'kofar.
Hannunta yaja suka nufi bedroom 'dinsu.
Rungumeta yay ya ha'deta da bango ya tallafo kanta yana tambayarta da ido menene.
Kai ta girgiza.
Hannunta yaja suka zauna bakin bed ya rungumeta jikinsa, ya riqe fuskarta yana lashe mata hawayen fuskarta.
Akunne ya ra'da mata.
“Me yake damunki fa'damin zan temaka miki?�
Kuka ta rushe da shi ta qamqameshi.
Kwantar da ita yay ya mata rumfa, ya ha'de face 'dinsu ya 'dora bakinsa saman Nata ya zura hannunsa cikin rigara ya shiga nuna mata wani irin rikitaccan salo wanda ya taso mata da mugun feeling, yadda yake murza nipples 'dinta, yana shafar marata da cikinta zuwa cibinta sai meqa take tana ha'diyar yawunsa da yake shayar da ita.
Ja'afar abinda bai mata jiya ba sai da ya amta yau wani irin salo mai gigita mace sai ga Ibtisam tana masa kukan da ta rasa na me tana qamqameshi, ta sakar masa jikinta baki 'daya yana jiyar da ita da'di wanda bata isa ta kwatanta shi ba.
Jin tayi released ya zaro bakinsa daga can yana murmushi jin yadda take kiransa Mon Amour.
Sai da sukayi wanka ya canza mata kaya da kansa ya rungumeta tai luf jijinsa idanunta arufe cikin zazzaqar muryasa ya mata ra'da akunnenta.
“Mon cœur! Meke damunki? Muga hannun da yake ciwo.�
Lamo tai cikin jikinsa bata iya mgna ba sai da ya sake tambayarta ta ce“Na warke.�
Hancinta yaja ya sake rungumeta tsam 'kirjinsa yana shafa kanta.
Kiran Maghreb ne ya saka ya janye daga jikinta, har ya yi alwala ya tagi masallaci bata miqe ba ta yi tagumi ta rasa meke mata da'di, ko amafarki bata ta'ba tunanin zata so wani ba bayan Ja'afar sbd mugun son da ta masa amman gashi da aurenta ta kamu da matsaneciyar 'kaunar Abie wanda batajin zata iya dainawa duba da yadda takejin 'kaunarsa har cancan 'kasan zuciyarta.
Zoben yatsarta da akace shi ya saka mata take kallo tana zubar da hawaye tana qamqame zoben,tanajin tabbas mutuwarta ta kusa sone 'kaunace wacce take cikin jini da 'bargo take masa bata San ya zatayi ba.
“Balarabe ya zanyi wallahi tallahi bazan iya rayuwa ba kai ba.�
Sai da ta gama sambatunta ta miqe ta shiga ta 'dauro alwala, ta fito tazo ta tayar da sallah.

Acan Espanol
Rahma suna shigowa gidan saman sofa ta zube, tana maida numfashi ta runtse kyawawan 'kananun idanunta, zuciyarta babu da'di bata jure fushin Abienta.
Meerah tazo tana musu sannu da zuwa, ta ce“Madam Rahma akwo miki koda tea ne me kauri kisha kafin kiyi wanka kuyi sallah na jera abinci a dining? �
'Kananun idanunta ta bu'de ta girgiza kanta “No! Meerah ki barshi ngd.�
Anee ta ce“Wlh baki isa ba Meerah kawo mata tea me kauri.�
Meerah ta ce“Toh an gama wlh bata son cin abinci.�
Anee ta kamo hannayen Rahma ta 'kura mata idanu ta ce“Haba! Rahma me ya yi zafi haka? Tinda aka kiraki awaya kika canza duk bakida nutsuwa da sukuni meke faruwa? Ko Rafeek ne bakya so har haka?�
Rahma ta sadda kanta ta ce“A'a Abie nah ne, fushi yake dani, sbd yaji Rafeek ya kirani da Baby cute nafi zargin hakan.�
Sam batajin da'di Abienta na fushi da ita ba.
Anee ta gane Rahma ba qara min so takewa Abienta ba bata iya samun nutsuwa
Idan Abien na fushi da ita.
Anee ta rungumeta tsam tana lallashinta, ta ce“Karki damu Abienki na sonki bazai ta'ba cutar da ke ba, tinda har ya ce miki idan kinada mijin idan bai miki ba zai rabaku ki auri wanda kikeso ai ba matsala yanzu zan fahimtar da Rafeek akan mgnarku ya yi hkr zuwa wani lokacin.�
Rahma ta girgiza kanta, “A'a Anee wlh koda ace wanda yafi kowa tsufa aduniya ya kasance makaho kurma Abie ya auramin zan zauna da shi na masa biyayya har 'karshen rayuwarmu, bazan iya bijirewa Abiena ba, kinsan 'kaunar da nake masa? Wallahi bana fatan na ba'kanta masa rai sam bana iya jure fushinsa akaina, kawai Rafeek yay hkr Allah ya basa wacce ta fini.�
Ta 'karashe mgnar cikin shasheqar kuka. Dan tana sonsa ba yadda zatayi ne shiyasa take baya² da lamarinsa.
Anee ta rungumeta tsam tana jin tausayinta da na Rafeek sbd tasan ba qara min so yake ma Rahma ba.
Meerah ta kawo tea 'din Anee ta sakata ta sha sai da ta shanye tass tana ha'da zufa.
Wanka ta shiga tana fitowa ana kiran sallar Maghreb tare da Anee sukayi sallah, suna kammalawa bayan sunyi azkhar suka fito falon.
Meerah tai serving 'dinsu.
Rahma bai fi spoon 3 ba ta yi ta ajiye spoon tana 'daukar cup glass wanda Meerah ta cika mata da lemon zallar strawberry sai ra'ba cup 'din yake tsabar sanyi, ta kafa bakinta sai da ta shanye, ta ajiye tana 'daukar wayanta ta latsa lumber Abie.
Ta gaji da ringing ba'a 'daga ba.
Goshinta ta dafe tana sauke numfashi.
Anee ta cika cikinta dam suka dawo falon, ganin yanayinta ya sanya Anee ta shiga bata labari me da'di sai da ta 'dan sake jikinta kadin Anee ta ce “Muje ki saka direba ya mayar dani gida.�
Rahma ta marerece ta ce“Please mu kwana gobe sai mu wuce school. �
Anee ta maqale kafa'da ta ce“Wlh bazan kwana ba haka kawai kinsan Ya Zahara da fa'da muje kawai asaukeni.�
Rahma ba yanda ta iya ta raka Anee har gida suka jiyo.
Abie 2 Rahma ta kira suka Sha fira tana tambayarsa jikin Raiyana ya bata labari, amman bai ce ita ce ta musu asirin ba, ya dai ce mata ta warke ta kirata ta mata barka.
Rahma cikin farin ciki ta Kira Raiyana.
*Chad*
Zaune suke a falon Raiyana ta ra'be dan ko ta saka baki a hira Jaddatu ajiye hira take ta 'dauko wata.
Jin ringing wayarta ya saka ta duba ganin lumbar ba suna ta 'daga tare da sallama.
Rahma ta amsa tana fa'din.
“Ammie barka da arziqi Ashe kin warke?�
Raiyana ta saki kuka tana fa'din.
“Ummi qarama ki yafemin dan Allah ki gafarceni wlh na tuba zan riqeqi da amana ki tayani roqon Abienki karma ya rabu dani.�
Rahma ta ce“Subahanallahi! Haba! Ammi ni wlh baki min komai ba! Kuma idan ma kin min toh na yafe miki, Abie kuwa insha Allah kuna tare bazai sakeki ba! Toh me kika masa ma? Bari zan kirasa ki daina kuka dan Allah.�
Raiyana sosai taji sanyi aranta ta share hawayenta ta ce“Ngd sosai Allah ya miki albarka.�
Rahma ta amsa da“Ameen ammi ki gaishe da kowa sai anjima.�
Jaddatu bata ma kalli inda take ba Hanan ce take bata hkr akan ta daina yawan kukan 'yan aiki na jinta.
Jaddatu ta ce“Ta baya ga wasa kenan.
Ai gaban 'yan aikin baqaqen aljanun suka fa'di munanan aikinta wannan me zai dameta dan sunji kukanta tana Neman gafara wajan wa'danda ta cutawa...�

Abie 2 bayan sun kammala cin abinci dare ya kira Abie 1 lokacin ya raka baqin da yay suna bakin gate bai 'daga kiran ba sai da suka tafi.
Da sallama ya fara.
Abie 2 ya amsa ha'de da gyaran murya ya ce“Abdulmajid! fatan kuna lfy ya me jikin?�
Abie wajan wasu fararen kujeru ya isa ya zauna yana amsawa da.
“Lfy lau Alhmdllah ya kowa na gidan? Gobe insha Allah suke shigowa amman ni sai jibi zan biya wajan Ummi.�
Abie 2 ya ce“Masha Allah! Abdulmajid kayi hkr dan Allah ka sassautama matarka tayi nadama naga tana son zama dakai fiye da komai arayuwarta.�
Abie ya numfasa ya ce“Toh har na dawo zamuyi mgna insha Allah. �
Hira suka ta'ba sukayi sallama.
Yana dates kiran kiran Rahma ya shigo.
'Dagawa yay tare da sallama.
Ashgwa'be ta amsa ta kirasa.
“Abie Rabin raina idan na 'bata maka rai ka yafemin ko na samu sassauci azuciyata.�
Abie yay murmushi ya ce“Uhmm! Baby cute ko? No! Baki 'batamin raiba amman zamuyi mgna idan na iso gobe oya ki kwanta da wuri kinga tin sassafe kike tafiya school. Fatan kinci abinci?�
Shasheqar kukanta yaji cikin kunnensa.
Idanunsa ya lumshe yana shafa sumar kansa ya furta.
“Ya ilahi! Babyna mene um?�
Cikin kuka ta ce“Daman nasan kaji shine duk ka bi ka tayar da hankalinka ka tayar min da hankalina, Sam banida walwala banida sukuni komai baya min da'di sakammakon Abiena na fishi dani, ya hana kasan nutsuwa ya hanani.�
Ta 'karashe mgnar cikim shasheqar kuka.
“Am Babyna kina jina?
Kai ta 'daga kamar yana ganinta.
“Yauwa kiyi shiru maza kije kici ka cikinki dam da abinci ki Sha ruwa ko lemo me sanyi ki nutsu na hkr na daina fushin gobe idan nazo zamuyi mgna OK baby love? �
Ashagwa'be ta ce“Toh Abie kace ka yafemin, sannan kamin murmushi kace min baby Ummi I love you. �
Abie dariya ta 'kwace masa harda riqe cikinsa yana 'kyal'kyala dariya.
Rahma kuka ta sakar masa yanajin sautin yadda take buga 'kafafunta 'kasa.
Cikin dariya ya ce “Ok..OK! Babyna zan fa'da na yafe miki I love you baby ummina ruhina.�
Yadda ya fa'dan ya saka Rahma jin wani irin yanayi tin daga 'dan yatsar 'kafarta zuwa tsakiyar kanta, idanunta ta lumshe ta qamqame jikinta waje 'daya tana sauke ajiyar zuciya wadda sautinta ke fita da 'karfi yana ratsa dodon kunnen Abie ta waya.
Asanyaye ta ce“I love you too Abienah Rabin raina, yauwa sai mgnar ammi nah.�
“No! Babyna sai nazo zamuyi yanzu ina busy good night ki ci abinci OK? �
Kai ta jinjina tare da amsawa“Toh Abienah.�
Kiran ya dates yana sakin lallausan murmushi.

Musalin 11 Ja'afar zaune gefen bed yana waya dasu Harisu cikin nisha'di yana gayamu su gobe zasu taso.
Ibtisam sai turo baki take wai ya hanata bacci.
Bayan ya gama yay shirin bacci ya hauro gadon ya rage hasken 'dakin ya kwanta, ya matso jikinta ya sanya hannayensa ya zagaye 'kugunta ya tura fuskarshi tsakanin wuyanta yana jujjuyawa ya Kira sunanta cikin wata irin murya.
'Kam'kame jikinta tai tana sauke ajiyar zuciya.
Murmushi yay bai mata komai bakinsu kawai ya ha'de yana mata wani irin fitinannan kissing wanda ya zautar da ita ta rungumeshi 'Kam tana maida masa martani, har bacci ya 'dauke su.

Washegari cikin shirin tafiya suka ta shi, Abie ya saka an zagaya gari dasu sunyi kalle² laraba idanunta kamar xasu fa'do waje sayayya sosai Abie ya musu yana taka tsantsa da Ibtisam sbd yadda take qoqarin shige masa shiyasa wajan siyayyar yaqi shiga wajan yana mota Pa 'din Abie ne yake biye dasu.
Tanko ganin irin ku'din da Abie ya kashe musu harda kuka ya riqe 'kafarsa yana masa godiya.
Misalin 'karfe 1 na rana jirginsu Ja'afar ya 'daga zuwa Chad Abie shi kuma nasu 2 na Rana ya 'daga Australia.

Espagne
Rahma yau ta ci sa'a 'karfe 3:30 na yamma suka dawo daga school.
Murna ta hanata zaune ta hanata tsaye, da kanta tinda tai sallar la'asar ta shiga ma Abienta girkin da ta San yana so fiye da sauran abinci.
Sai da ta kamamla komai Meerah ta shiyar kan dining area ta shiga wanka.
Bayan ta yi sallar Maghreb Wata irin kwalliya ta cancara wuyanta da kunnen and hannunta ta zuba gold haka yau ta canza sarqar 'kafarta ta saka ta diamond har tafi waccan kyau da tsari.
Riga da wando na Pakistan ta saka maroon sunyi mata masifar kyau wani irin 'kamshi take na ban mamaki, ta tufqe gashinta ta Saki jelar har gadon bayanta, ta yafa mayafin kayan.
Meerah kanta da take mace ta yaba kyan da Rahma tai da tsarin surata, sosai take mamakin tsantsar 'kaunar da Rahma takewa mahaifinta kamar dai saurinyata ko mijinta irin wannan girkin da 'daukar wanka.
Zaune take tana duba lokaci.
Zabura tai ta ce“Wayyo na makara zuwa airport maybe muje kusan tare, Meerah na tafi sai na dawo.�
Ta 'karashe mgnar tana tafiya abinda taji a Tv yasa tai saurin dawowa baya ta qurama Tv 'kananun idanunta masu matuqar haske da kyau tana kallon labarun da ake, cikinta taji ya hautsuna zuciyarta tai wata irin bugawa lokaci 'daya taji duniyar na juya mata idanunta suna lumshewa kafin ta fahimci sauran bayani ta sulale nan 'kasa sumammiya...

_💃�'Yar Ajin Ma Sha Allah🥰_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/12/22, 00:27 - Buhainat: ```D A```

```57&58```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

Meerah da take fitowa daga kitchen idanunta suka sauka akan Rahma ta zube 'kasa.
Aguje ta nufi wajanta tana salati, ha'di da kiran sunanta.
Gabanta ta zube tana 'dagota tana girgizata ha'di da kiran sunanta.
“Rahma me ya sameki? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!�
Duk ta ru'de ta rasa ya zatayi da Rahma.
Idanunta ya sauka akan Tv ganin irin labarin da ake, lokacin ana sanarwa jirgin da ya taso daga Australia zuwa Singapore ya fa'di, sai jirgin Turkey wanda zaije Istanbul shima ya fa'di.
Agigice Meerah wacce sam bata fahimci garin da akace ba tsabar ru'du jin ance ya taso daga Australia, ta 'kwalla ihu mai firgitarwa wanda ya haddasa me gadi da securities Rahma suka nufo hanyar falon aguje hannunsu riqe da bindigogi.
Ki shin 'kofar suke kamar zasu 'ballata.
Meerah ta kwantar da Rahma ta nufi 'kofar aguje ta bu'de.
Aguje suka shigo suna tambayarta menene?
Agigice take nuna musu Rahma da Tv tana fa'din.
“Ya mutu itama ta mutu.�
Wajan Rahma suka nufa, tana kwance kamar gawa.
Me gadi ya ce“Ki kawo ruwa da sauri.�
Robar ruwan da take ajiye saman center table ta 'dauko ta 'balle murfin ta zubama Rahma tana kuka.
Bata motsa ko gezau babu alamar zata farfa'do.
Securitien ta me suna Adeel yay saurin sunkuyawa ya cicci'beta ya ce“muje hospital karta rasa ranta.�
Meerah haka ta bisu aguje ba ko 'dan kwali akanta.
Rungume take da Rahma abayan motar tana kuka har suka isa ha'dadd'iyar privet hospital dan a'kasar ma sai wane da wane yake zuwanta.
Cikin gaggawa aka amsheta aka shiga emergency da ita.
Temakon gaggawa suka shiga bata domin su samu numfashinta ya dawo.
Meerah ta kira Anee ta gayama tana kuka ba'a rufe 30 minutes ba sai ga Anee itama kuka take suna leqen Rahma ta 'kofar glass anata fama akanta har yanzu bata farfa'do ba.
Securities hankalinsu ya yi mugun tashi jin jirginsu Abie ya yi hatsari.
Misalin 9 na dare jirginsu Abie ya diro 'kasar Espagne.
Haka kawai yakeji fa'duwar gaba sam baya jin da'din zuciyarsa.
Shigar larabawa ce tsaf ajikinsa tamkar balaraben saudiya, kallo 'daya zakawa kayan jikinsa kasa na manyan ku'dine tin daga takalmin 'kafarsa har zuwa agogon gold da yake 'daure atsintsiyar hannunsa.
Farin glass ne manne akan fuskar shi.
Cikin nutsuwa yake sauko daga cikin jirgin, yana 'ko'karin canza layi.
Rahma ya kira tanata ringing ba'a 'daga sakammakon sun baro wayan agida.
Direban Rahma ya kira bugu 'daya ya 'daga cike da mamaki, nan ya sheda masa sun iso lfy azo 'daukarsa.
Nan ya shedama Adeel suka tafi 'daukansa cikin fa'duwar gaba, basu San irin tashin hankalin da Abie zai shiga ba jin 'yarsa hospital har yanzu bata farfa'do ba.
Daga airport kai tsaye hospital suka nufa.
Abie ya ce.
“He! Ina zamuje ne?�
Adeel ne mai 'karfin halin cewa.
“Yalla'bai kayi hkr...�
Ya basa labarin komai.
Wani irin juyawa kan Abie yake yana kira sunan Allah, hankalinsa amugun tashe.
Suna zuwa Abie ya nemi abarsa ya ganta, amman har lokacin ba damar ganinta, haka ya dinga kai kome ya rasa me yake masa da'di.
Misalin 10 na dare Rahma ta farfa'do tana wani irin fizge² da ihu tana kiran Abie.
Likitocin tsaye kanta, allura suka mata nan take bacci ya 'dauketa.
Doctor yana fitowa Abie ya taresa da rawar jiki yana tambayarsa.
Zofa ya goge, da harshen turanci ya ce“Muje office�
Zaune suke Abie na fuskantar Dr.
“Yalla'bai zuciyar yarinyar nan tayi mugun bugawa sakammakon razana da abinda taji ko ta gani ya gigitata, har ya hasasa mata suma wanda ta kwashi sama da 4 hours kafin mu samu ta farfa'do, dan haka akiyaye 'bata mata rai, yanzu tana bacci da zaran ta tashi zata farka normal, ga magugun da za'a siyi ta sha su tsawon sati gudu insha Allah komai zaiyi normal. �
Baki 'daya Abie baida wata nutsuwa bare kwanciyar hankali, tinda yaga Rahma kwace agadon asibiti, sai ga shi yanzu ana mgnar zuciyarta ta buga duk sakammakon taji jirgi ya yi hatsari tin bata tsaya taji wanda zaije wata qasa bane ba.
Numfashi ya sauke ya ce.
“Ok Dr ngd bari zan siyo magugunan yanzu, sai akaini wajanta.�
Fita yay, sukayi mgna da Adeel, ya fita ba jimawa ya dawo da magugunan masu masifar tsada.
Doctor ya nunama Abie yadda zata sha sannan ya ce da ta tashi ayi qoqarin bata koda tea ne amman abari ya huce karta Sha da zafi sosai.
Abie ya tura direba da Meerah gida ta 'daukoma Rahma kaya Kala biyu ta tawo da kayan tea da komai harda girgin da Rahma ta shiryawa Abie.
Zaune suke sun sakata gaba bacci kawai take Abie na riqe da hannunta wanda baida drip, yana aikin murzawa yana shafa fuskarta.
Kallon Meerah da Anee yay ya ce.
“Dare ya yi kuje gida ku kwanta Ku huta, Anee a fara ajiyeki sai su Meerah su isa gida OK?�
Tana share hawaye ta ce.
“Toh Abie Allah ya bata lafiya, gobe zan shigo daga makaranta.�
“Ameen�
ya amsa suka tafi.
Dr ya sake leqowa ya dubata ya fice Abie ya rufe qofar ya shiga toilet ya 'dauro alwala ya fito ya gabatar da sallolin da ake binsa.
Koda ya idar nafila ya shiga, wadda sai 2 na dare ya miqe bayan ya yi doguwar addu'a Allah ya ba Rahma lfy.
Bakin gadon ya zauna ya rankwafo yana kallon kyakkyawar fuskarta.
Drip yaga sauran qiris ya qare ya cireta ya matsar da ita ka'dan ya haye gadon ya shigar da ita jikinsa sosai ya lullu'besu da tattausan bargo wanda Meerah ta kawo.
Wata irin ajiyar zuciya yaji Rahma ta sauke tana qara shigewa jikinsa ta tura fuskarta 'kasan wuyansa tana sauke numfashi anutsu irin baccin yana mata da'di.
Zagayeta ya yi da hannayensa yana buga bayanta ya manna mata kiss agoshi ya qura mata idanu yana jin mugun tausayinta.
Ahankali ya furta“Babyna da kin mutu ina tunanin ba lallai na jimaba zan biki, baki tsaya kinji da kyau ba Abienki kawai kike tunani har kunnuwanki suka jiyo miki jirgin da zaizo Espagne ne.�
Kanta ya shafa ya tallabo fuskarta ya kirata cikin ra'da.
“Baby ummina!�
Ina alluran da aka mata, sosai take aiki bacci take ta qamqameshi.
Tofeta yay da addu'ar bacci ya kulle idanunsa ba jimawa bacci ya sace shi.

A can kuwa 'kasar Tchad.
Jirginsu Ibtisam misalin 8 na dare ya sauka, Yahaya direba da Abie 2 and Mal Adamu sukazo tarbansu.
Ibtisam sosai gidan ya burgeta dan yafi ma na Australia tsaruwa da kyau.
Bayan sunyi wanka sunci abinci Tanko ya nemi izinin suje gaishe da Jaddatu, Abie ya musu jagora har falon.
Jaddatu ana zaune ana jan casbi suka shigo, da sallama.
Ibtisam da manyan hotunan Abie da Rahma ta fara cin Karo akowane kusurwar bango wasu suna tare rungume da juna wasun kowa daban sai Jaddatu da wani kyakkyawan tsoho balarabe sai wani guda sun kusa su goma suna cikin anushuwa.
Ibtisam tsirawa hoton Abie da Rahma ido tai, yadda suke 'kam'kame da jina suna dariya.
Tsaki taja 'kasan le'be duk da kuwa taga tsantsar kamarsu da Rahma, baki ta murgu'da ta janye idanunta daga kallonsu.
A'kasa suka zube suna gaisheta.
Jaddatu cikin sakin fuska ta amsa tana kallon Ja'afar da yake yanzu ya iya larabci ta ce.
“Barka da arziqi Ja'afar, Ibtisam ya jikin? Allah ya 'Kara sauqi na tayaki murna amman don Allah ki kiyaye ko gaba karki sake yinqurin guduwa sbd za'a miki auren dole, idan kin tsayawa kin gayawa Allah tabbas zai miki maganin komai.�
Ja'afar ne ya fassarama Ibtisam tinda dukkansu bayan Abie 2 da Ja'afar Tanko da Adamu and laraba da ibtisma ba mai jin larabacin.
Ibtisam tai 'kasa da kanta cikin ladabi ta ce“Ngd ummi Allah ya saka da alkhairi.�
Laraba ma godiya tai jin yadda Jaddatun take fa'dawa 'yarta gaskiya.
Hanan ta ce“Ya Abdul sai ya wuce wajan 'Yar lelensa ko? Amman ya ce gobe zai zo.�
Abie2 ya girgiza kansa ya ce“Da wuya har mugani.�
Dariya sukayi.
Latifa ta ajiye musu lemo da ruwa kayan motsa baki anata hira abin gwanin ban sha'awa hira Ja'afar ne me fassarawa.
Rayyana ce ta sauko ganin harda Ja'afar ta zube tana neman gafarasa.
“Wlh ba komai na yafe miki Allah ya yafemu baki 'daya.�
Da “Ameen suka amsa, sun jima sosai kafin su miqe Jaddatu ta ce“Ja'afar Ibtisam da mamarta ga bedroom can hanyar kitchen su zauna kafin Abdul 'din yazo su wuce.�
Ja'afar yay godiya ya fa'dawa Laraba sukayi godiya nan aka ha'dasu da Latifa kasancewad tana jin hausa ita ta kaisu har'dakin da zasu zauna.

Ja'afar bayan sun koma 'bangaran Abie2 yamusu sallama yace zaije gidan Baba Tsalha ya kwana wajansu Harisu ya yi kewarsu sosai.
Fatan alkhairi suka masa ya tafi.
Ibtisam ta baje saman bed tana qarewa 'dakin kallo tana jinjinawa wai nan wajan saukar baqine toh ina wa 'yan gidan gaskiya masu ku'di na morewa inji Ibtisam.
Fuskar Abie take mata gezu sai tsaki take ja taji haushin ganinsa da balarabar yarinyar nan.
Laraba ta ce“Ibtisam dan Allah ki ajiye hankalin ki,kinji?�
Kai Ibtisam da 'daga sbd tasan duk abinda zatayi dan sugane bazasu ganeba gwara ta barma zuciyarta.

Baba Tsalha ganin Ja'afar awannan daren ba qaramin farin ciki yay ba, kamar ya goyasa yana tayasa murnar samun lafiyar Ibtisam.
Yahuza ya ce“Wai Ja'afar kaga yadda ka zama kwana ukune ko nawa har ka canza baqar fatarka tana sheqi.�
Harisu ya kauma Ja'afar duka ya ce“Ba dole ba 'kasar waja ai akwai da'di ga Hutu ga amarya agefe.�
Ja'afar bai ce musu uffan ba bayan murmushi haka suka kwanta awannan dare cike murnar ganin Ja'afar.

Acan Espagne misalin 'karfe 4 Rahma ta farka tana fizge² tana kuka tana kiran

Please Login or Register in order to submit comment