Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce“Ai fa sai kayi hkr ta zage yalla'bai shine masalaha.�
Abie ya ce“Ok cire toh.�
Kallonsa tai tana maqale hannunsa 'kirjinta kamar tasan me ya ce, ta furta.
“Ok cire toh.�
Ta saki wata 'katuwar dariya, ta zare zoben hannun ta sanya babbar yatsarta ta dama bata shiga ba ta sanya ata tsakiya ta mata yawa.
Kai ya girgiza ya ce“Ki saka ahannun hagum....�
Ji yay ta 'daukeshi da mari cikin sanyin da jikinta ya yi na allura. Ta ce“Ki saka ahannun hagum.�
Idanu suka zazzaro Abie yay murmushi ya kamo hannun nata ya zare zoben ya mayar mata yatsar hagum.
Dariya take harda riqe ciki.
Abie yay tagumi yana kallon hukuncin Allah. Dr ya saka aka samo abinci wanda Abie ne ya bata ta cikin lalami da biye mata, tana ci tana qyalqyala dariya, sai kuma ta roshe da kuka.
Kamar tsawon minti 40 bacci ya 'dauketa ta 'dora kanta cinyar Abie wanda zai zame Dr ya ce“Hkr zakayi fa, tinda har tana yarda ka ra'beta duba fa batasan mahaifinta ba.�
Bayan baccin ya yi nisa ya janyeta ya miqe, sam baida wani sukuni.
Malam Adamu addu'a ya mata suka fito.
Office Dr Salis.
Abie ya fuskanci Dr ya ce“Yanzu ya ake cikine?�
Dr Salis ya ce“Idan kana ganin fitar taku waje zai fi ba damuwa zan bincika muku babbar hospital wacce ta 'kware wajan irin ciwonta sai Ku fara shiri.�
Abie ya sauke ajiyar zuciya ya numfasa, ya na 'dan lumshe manyan narkakkun idanunsa, ya furta.
“No! 'Bangaran nan banida matsala zanyi waya da doctor Moha 'kwararran likitan 'kwaluwa ne, a babbar asibitin Australia, shine ke kula da 'bangaran masu ta'bin hankali, zan masa bayanin halin da take ciki sai mu fara shirin tafiya.�
Bayan sun gama tattaunawa suka nufo gida kowa zuciyarsa ba da'di halin da Ibtisam take ciki babbar matsalace arayuwarta, sai fatan samun sauqi.

'Bangaran Ja'afar kuwa, bayan yazo gidan yay parking, ya fito yana kiranta.
Lokacin tana falo zaune Jaddatu nata mata tsiya.
Rahma ta murmusa lokacin da ta ga sunan Habibynta na yawo saman screen 'din wayar.
Picking call 'din tai tana manna wayan kunneta tare da sallama.
Ja'afar ya amsa yana fa'din na 'karaso, bari na gaishe da Baabana kafin ki fito.�
Rahma ta shagwa'be murya ta ce“Basa nan Habiby sunje hospital.�
“Ok fito toh.�

Jaddatu ta kalli Rahma tana miqewa fuskarta 'dauke da murmushi, ta 'dagama Jaddatu gira ta ce“Ya dai? Anata kallona?�
Daga haka tasa kai ta nufi hanyar fita daga falon.
Jaddatu ta ce“Allah zai mana maganin komai insha Allahu.�
Hanan ta ce“Allahu ya sha'a.�

Da murmushi 'dauke akan fuskarta ta isa dab da shi ta tsaya tare da sallama ta nuna masa hanyar zuwa falon baqi.
'Kayataccan murmushi ya sakar mata, suka jera zuwa falon.
Abie da yake tsaye yana kallonsu sai da suka gefta shi ya girgiza kansa ya koma ciki ya 'dauko ruwan addu'a.
Suna shiga falon Ja'afar lumshe lumsassun idanunsa ya na shaqar dadda'dan 'kamshin falon, ya furta.
“Qalbina irin turaren wutar nan zakina sakamin agidana.�
Ya 'karshe mgnar yana zama.
Murmushi tai ta 'dauki wani ha'dadd'an cup glass ta tsiyaya masa sansan lemon 'ya'yan itattuwa ta beqa masa ta zauna 'dan nesa da shi.
“Ngd Qalbina, amman zan fara koya miki hausa sbd ba kowa ya iya English a family namu ba.�
'Yar dariya tai tana rufe fuskarta.
Kur'bar lemon yay ya ajiye cup 'din ya fuskanceta murya a tausashe.
“Qalbina ya mgnar auren namu? Kiga gwara ayita tin su Baabana suna nan.�
Rahma cikin siririyar muryarta mai zaqi ta ce“Karka damu Habibyna za'ayi wlh na matsu ayi mutafi Espagne har na gama karatuna, idan kuma can zamuyi rayuwarmu Abiena baida matsala.�
Fuskarta yake kallo murmushi 'dauke kan fuskarshi ya ce.
“Yauwa my Qalbi A'a bazamu zauna acan ba, Niger zamu zauna ok?�
Ta waro idanunta zatayi mgna sai ga Abie 2 ya shigo da sallama.
Rahma ta miqe tana fa'din.
“Oyoyo Abie 2.�
Murmushi yay ya zauna tsakiyarsu kamar yadda ya saba.
Ja'afar ya gaishesa.
Cikin fara'a ya amsa, ya 'dora da cewa.
“Yauwa 'diyar albarka beqo min cup ga ruwan addu'a kusha sbd aurenku.“
Cikin zumu'di da jin da'di Rahma ta ce“Wow! Abie 2 ka gama mana komai mun gode.�
Ta 'karashe mgar tana beqa masa cup 'din. Amsa ya yi ya zuba ma Rahma ya beqa mata ya ce“Shanye duka fa!�
Ba musu ta amsa ta shanye, ya zubama Ja'afar ba musu ya amsa ya shanye tare da bismillah.
Wani irin jiri suka din gaji atare, wanda sai da suka dafe Kansu.
Abie ya riqosu dukkansu yana tambaya.
“Lafiyar ku kuwa? Ku karanta AMANAN RASULU da KURSIYU da YASIN, da
LA'ILAHA ILLAHUWA WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDA WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIR (10).�
Kai suka jinjina suka fara karantawa cikin ransu, sannu ahankali suka fara jin jirin na sakinsu, amman sai sukaji dukkan jikinsu ya 'dauki mugun zafi da ra'da'di sosai.
Abie ya qara musu ruwan suka sha yana addu'ar Allah yasa kafin kwanaki asirin ya sakesu sbd ya yarda da addu'o'in 'dari bisa 'dari.
Abie ganin irin yanayin da suke ciki ya dafasu ya ce“Ja'afar jeka gida zuwa gobe sai kazo. 'Diyar albarka je ki kwanta ki huta.�
Ba musu suka miqe ya kama hannunsu suka fito Rahma ta shagwa'be.
“Habibyna sai munyi waya ka kularmin da kanka.�
Kai ya jinjina mata sbd bazai iya mgna ba.
Sai da ya shiga mota Abie ya rakata har 'kofar falonsu ya juya yana mai farin ciki sbd yaga alamun nasara.
Ja'afar yana zuwa gida ya 'bingire bacci.
Rahma hakan ce ta faru bedroom Jaddatu ta shiga sbd jirin da yake 'dibarta bazata iya hawa saman bene har na 2 ba.
Koda su Abie suka dawo basu iskosu ba, nan Abie 2 ya basu labarin abinda ya faru.
Sosai kowane yaji da'din labarin Tanko addu'a yake Allah yasa Ja'afar yay gaggawar dawowa haiyacinsa.
★★★
Cikin kwana biyar Abie ya gama mgna da Dr Moha daga Australia, har an fara shirin tafiya,wanda Abie ya baiwa Tanko wadataccan ku'di ya koma Niger ya 'dauko Laraba zuzo a musu passport.
Rahma da Ja'afar kuwa har yanzu su na son junansu amman ba sosai ba irin nada, abin ya fara ja baya.
Daga Abie 1 har Abie 2 and mal Adamu, ba wani mai 'kwa'kwaran barci dare suke bi kullun cikin fa'dawa Allah suke, sbd canji ya fara zauwa.
Ga manyan malaman da Abie ya rabawa ku'di anata saukar Qur'ani ana yanka raguna anata sadaka, har tuyar wainar hatsi ake, Ana rabawa sadaka, toh komai sai lokaci ya yi.
Ja'afar ya fara maida hankalinsa wajan Ibtisam, abin har mamaki sukeyi, duk da har yanzu bai sakuba.
Ibtisam ana nan dai ba wani sauqi sai wajan Allah, karyata ce take qara sauqi bata fiye yarda da mutane ba sai Abie shima nesa da nesa dan yawan 'daukeshi take da Mari, bawan Allahn hakan bai hanasa temaka mata ba, sbd shine kawai take yarda ya bata abinci.

*Niger*
Tahoua
Laraba ta rabka tagumi tana kallon Tanko.
“Haba! Laraba wai kin fini son Ibtisam ne? Ai bawa baya tsallake 'kaddarasa. amman ki sa ni komai ya faru da ita mune sila, mu muka janyo mata wlh ni basan she'dani da ya shiga kaina ba har na amince zan bama Jamilu 'diyata.�
Laraba ta ce“Wai yanzu ina zamu bar yaranmu har rai biyar? Gaskiya Tanko bazan jeba tinda kace ma bata gane mutane kaje kawai zan dage mata da addu'a, ko kutafi da Dadda.�
Ta qarashe mgnar tana share hawayen takaicin kanta da ta siyama 'yarta larura.
Tanko ya ce “A'a dole sai dake wanka da sauran abubuwan da ya kamata ke zakina gwada mata, ni ya zanyi da ita¿ yaran can zasu koma wajan Dadda har mudawo.�
Kirane ya shigo wayarsa yana dubawa ya ga Karime ce daga Cameron.
'Dagawa yay tare da sallama.
Karime ta amsa ta ce“Shamsu ya ake cikine har yanzu baku wuce Tchad bane?�
Tanko ya ce“Gobe insha Allah zamu wuce, gatanan tana son gardama wai bazata jeba.�
Karime ta ce“Na rasa meke damun Laraba wlh, ban ita.�
Tanko ya bata wayar ta amsa tana kum'bure² ta gaisheta.
Karime bata amsa gaisuwar ba, ta ce“Laraba bakida hankali, yarinyar ba lafiya an turo kije ku tafi yaran sai zauna wajan Dadda amman kin ce bakya zuwa?�
Laraba ta ce“Toh ni ko naje me zan mata sbd Allah? Banda takaici ya nemi kasheni.�
Karime bata sake mgna ta katse kiran.
Tanko ya amshi wayar ya sake kiran Karime suka tattauna.
Gidan Dadda ya tafi daga can ta biyo shi tazo ta wanke Laraba tass ta 'dora da cewa“Wlh tallahi idan bakiyi shirin tafiya ba, ayau zan saka Shamsu ya yi aure sutafi da amaryar ta kular masa da 'yarsa.�
Laraba hankalinta ya tashi ta fara kuka ta ce“Ai duk basu fahimceni bane ni bawai naqi zuwa bane, wlh ina baqin cikin zuwa naga halin da Ibtisam take ciki ne.�
Ba Dadda Tanko ma sai da abin ya basa dariya.
Ai kuwa zuwa dare su Taslim suka harha'da kayansu sai gidan Dadda. washegari su kuma suka tafi, yaransu na kukan halin da yayarsu take ciki.

Inna zaune ta cika ta yi famm sbd takaicin abinda Ja'afar yay musu, ashe yarinyar na wajansa?
Deluwa ta ce“Hansatu ki daina damuwa komai da kika gani na faruwa adoron duniya rubutacce ne.�
Baki ta ta'be ta ce.
“Wlh abin yaban haushi sosai kinsan matar can da baqin surutu wlh sai ta gauraye garin Tahoua duk girmansa, tana cewa 'danmu ya 'boye mata 'yarta har hakan ta faru da ita.�
Deluwa ta ce“A'a da wuya kema don Allah kiyi shiru, Allah ya tsare gaba, ita kuma ya bata lfy...�

*Gabon*
Aishatu zaune an ca'ba kwalliya ana jiran me gida, wanda ko jirginsu bai taso ba.
“Uwani!�
Cikin girmamawa uwani ta iso ta zube gabanta tana fa'din.
“Ga ni hajiya.�
Aishatu ta ce“Yauwa idan kin kammala jera komai ki 'dauki basket 'din nan kije Nura ya kaiki ki kaiwa Rabi'ah, kiyi sauri ki dawo fa!�
Cikin girmamawa Uwani ta ce“Toh hajiya an gama.�
Aishatu ta ce“Oh! My god! Nace ki daina cemin hajiyar nan aunty Aisha kawai ya isa.�
Uwani ta amsa da
“Toh� ta miqe.
Aishatu ta kira Rabi'ah tana dariya ta ce“Toh ah kwa'daitu yanzu Uwani zata kawo miki, daga nuna miki abubuwan da na girkawa Ma'aruf kin rikice, sai na fa'da masa na ce kina 'kwalama gidansa.�
Ta 'karashe mgnar cikin dariya.
Daga can Rabi'ah ta yatsina fuska tana hararan wayar, dakyar ta tattaro nutsuwa ta qaqalo murmushi ta ce“Ayyah! Ai na ha'da miyau ne gwara kawai ki ban nima naji da'dina.�
Dariya sukayi atare.
Aishatu ta ce“Wai Rabi'ah kinga wasu ha'dadd'in lafaya da jakukuna and takalma na Tchad da Ma'aruf ya turo min hotonsu ya siyamin. Da dogayan riguna.�
Rabi'ah sai da ta kusa ha'diyar zuciya tsabar baqin ciki, harda tari ya sarqeta.
Dakyar ya tsaya ta ce“Ƙawata pls zan kiraki anjima.�
Ta katse kiran.
Miqewa tai tsaye ta fara zirganiya.
Number Ma'aruf ta kira bugu 'daya ya 'daga kiran.
Kuka ta sakar masa mai cike da kissa.
Ma'aruf wanda yake cikin jirgi su na dab da tasowa ya qyalqyale da dariya ya ce“Allah ya baki hkr idan nine bari zanji dake komin dare sai na zo munyi ido hu'du.�
Ashagwa'be ta ce“Me kake so na ajiye maka pls gayamin na girka yanzu?�
Cikin tsokanarsa ya ce“Duk abinda zuciyarki take so ki girka idan dai son gaskiya ake min abin zai kasance irin wanda nakeso ne.�
Dariya tai ta ce“An gama Mon Cheri.�
Wata number Ma'aruf ya kira bugu biyu aka 'daga.
Dariya ya busshe da ita tamkar ba acikin jirgi yake zauna ba, ya ce.
“Kayan suna dab da zuwa fa! Kuma masu ingancine...�

Abie 2 killun sai ya karanta Kursiyu 'kafa 5 ya tofa ajikin dabino ya ba Ja'afar da Rahma suna ci idan sun cinye sai ya 'kone 'kwallon.
Abie zaune cikin hamshaqin falonsa, sanye da wani yadi marar nauyi milk da ganin 'dinkin kasan dan kasan na shan iskane agida akayisa.
Ya yi wani irin kyau Masha Allah, kwarjininsa da haibarsa kwance kan fuskarshi, wacce ya manna mata farin glass.
Laptop ne gabansa yana dannawa cup 'din coffee agefansa, yana kur'ba.
Fuskar shi bazaka ta'ba gane halin da yake ciki ba farin ciki ko akasin hakan.
Wayarsa ta 'dauki ringing ya kalli screen 'din wayar.

Kansa ya dafe cikin taushin murya ya furta.
“Ya Rabbi! Ba 'kasar da zan iya fita a wannan yanayin bayan Australia.�
Wayar ya 'daga ya fara da sallama atausashe.

Rahma tsaye cikin shirinta tana sanye da doguwar riga ta ha'dadd'an tsadaddan lace, black yanada adon purple, hakan ya fito da hasken fatarta ta yi masifar yin kyau, matuqa, ta murza 'daurin zahara buhari, ta fesa turare ta mai azabar 'kamshi, 'dan 'karamin Jajayen la'bbanta ta qara goga musu lipstick, abin gwani ban sha'awa.
Kyawawan fararen 'kananun idanunta ta juya farr tana sakin 'kayataccan murmushi.
Wani madedecin mayafi black ta 'dora saman kafa'darta ta 'dauki wayarta ta nufo falonta.
Tv ta kashe ta fice.
Ta saukowa bene na 1 da Raiyana sukayi kici'bis zataje wajanta.
Raiyana ta beqa mata robar strawberry tana fa'din.
“ummi irin wannan gayun ina zuwa haka?�
Rahma ta 'dan yi 'karamin murmushi ta ce“ Ngd ammi bari na dawo sai na shanyeta zama 'daya.
Wlh Ja'afar zaizo zamuje hospital ya yi fushi wai banje naga Ibtisma ba, kuma ai ya kamata naje sbd Abiena ne ya mata sanadin halin da take ciki.�
Raiyana ranta ya 'baci matuqa amman ta danne haushin tai yaqe ta ce“Hakane kuma amman sai kinyi da gaske fa ina gudun mahaukaciyar yarinyar nan ta amshe miki shi fa!�
Rahma ta yamutsa fuska ta ce“Wlh ni kam kwana biyu banajin kishinsa Sam shiyasa ma zanje na dubata.�
Bata jira komai, ta nufi hanyar bedroom 'din Abie.
Raiyana ta biyota aguje tana fa'din.
“Ummi kawo mana na ajiye miki har ki dawo.�
Rahma ta ce“A'a naqi ki shanye.�
Ta kwasa aguje ta banka 'kofar falon ta shige ta maida 'kofar ta rufe tana dariya 'kasa². Aguje ta nufi Abie tana fa'din.
“Wayyo Abiena ammi zata amshe min strawberry nah.....�
Uhmmmm!😔😟🚶��♀�

_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
2/24/22, 16:51 - Buhainat: ```D A```

```37&38```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_


Abie yana waya mai mahimmanci, yaji shigowar Rahma da gudunta, tana kiransa.
Kansa ya 'dago ya zuba mata narkakkun idanunsa.
Kusansan ta zauna ta 'dora masa robar strawberry'n saman cinyarsa, ta kwantar da kanta saman kafa'darshi, tana maida numfashi.
Hannunsa ya sanye ya shafi fuskarta yana buga bayanta alamar lallashi.
Lamo tai tana kallon 'dan 'karamin bakinsa da yake mgna cikin nutsuwa yana sakin murmushi.
“Ok insha Allahu zanyi qoqari Bilal Thank u bye.�
Ya jira har wanda ya kirasa ya kashe wayan daga can, (sbd al'adarsa ce baya kashewa mutum kira sbd ya tsani akashe masa.)
Strawberry'n ya 'dauka ya na jijjuyawa, yanajin Sam bai yarda da shi ba, ya ajiye saman center table 'din gabansa, ya 'dago Rahma yana jan kumatunta yaja siririn hancinta, ya ce“Babyna wa ya biyo ki? Ina za ki kikayi kwalliya haka?�
Ashagwa'be ta ce.
“Ammi ce, Abiena ba na gayamaka zamuje hospital ba da Ja'afar?�
Murmusawa yay ya ce“Oh! Sorry Babyna.�
Sajansa ta shafa tana kallonsa 'kurrr.
Gira ya 'daga mata zaiyi mgna Raiyana ta shigo da sallama, ba'kin cikinsu kamar zai kasheta.
Abie ya amsa yana kallon Rahma ya ce“Alamu sun nuna bacci kikeji Baby shiga bedroom 'dina ki kwanta.�
Kukan sangarta ta sanya masa tana diddira 'kafa.
“Ok tashi kije.�
Rahma ta ce“Naqi mgnarka zanbi Abie Rabin Raina.�
Ta 'karashe mgnar tana miqewa zata nufi bedroom ya kamo hannunta ya ce“Yauwa Baby ummina jeki Ku tafi bazan ta'ba hanaki abinda kike so ba.�
Cikin murna tai kissing 'din hannunsa tana Jan dogon karan hancinsa ta ce“Ngd Abie Rabin raina. Ammai ki 'karamin godiya bye.�
Ta 'dauki wayanta da handbag 'dinta zata 'dauki strawberry ya damqe hannunta ya mata wani kallo tai saurin 'kasa da kanta tana murmushi ta ce“Toh Abie ka 'boye min har na dawo I love u bye.�
Ta tafi tana 'daga musu hannu.
Raiyana masifa da bala'ine yake cinta.
Abie aikinsa yake a laptop, jin har Rahma ta fita Raiyana ba amsa mgnar da ta mata yasa ya 'dago ya kalleta akaikaice cikin kamilalliyar murya shi ya ce.
“Hajiya Raiyanatu ya dai?�
Cikin masifa daman saura 'kiris take jira ta ce.
“Ban saniba karku raina min hankali, ko a'kasar arna soyayyar da take tsakaninka da Rahma ta 'kazamta indai har kai ubantane da kakawota duniya. Ka fa'damin gaskiya Rahma 'diyarka ce ta cikin ka, ko 'diyar dangi dan na fara zargin ba kai ka haifeta ba, wlh akwai ayar tambaya, sai kace kai ka'dai ka ta'ba haihuwa aduniya...�
Wani mugun kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sanyawa bakinta linzami. Amman da yake masifar kishinsa na cinta kawai ta sake cewa.
“Abdulmajid! Ka fa'damin Rahma 'diyarka ce ko 'yar ri'ko?
fa'damin ni wannan munafucin da kuke na soyayyar 'boye ya isheni, gwara Ku fito da ita waje kuyi aure ni da ita mujera....�
Yadda ya mur'de mata la'bba da wata irin tsawa da ya mata shi ya katseta daga mgnar da takeyi.
“Tashi ki ban waje, sai kije ki nemo mata wani uban, wlh saura 'kiris ki kaini bango taraki nake nasan duk halin da kike ciki.�
Miqewa tai rai amatuqar 'bace ta ce“Da 'yar halak kake mgna.�
Ta juya fuuuuuu ta tafi.
Goshin sa ya dafe yana mai jin tsanarta har cikin ransa sbd ya gama ganota tsaf ita ce ta ha'da Ja'afar da Rahma kawai dan tana zargin Rahma ba 'yarsa bace.
Guntun murmushi ya su'buce masa yana shafa sumar kansa.
Robar strawberry ya ce“Ko anan ya ci ki gane Allah yana tare da masu gaskiya wato kin kuma shiryo wata masifar ki bata ta ci ko? Ai duk motsinki akan idona lokacine baiba insha Allahu da kanki za ki tonawa kanki asiri.�

Rahma tana saukowa 'kasa ko zama batai ba Ja'afar ya kirata yazo.
Jaddatu na kur'bar shayi Rahma ta rungumeta ta ce“Zan fita Jaddati sai min dawo.�
Jaddati ta ce“Hanan ta shi maza duk Inda zasu sanya 'kafa kema ki saka.�
Hanan ta miqe ta ce“Bari na shirya.�
Rahma ta ce“Uhm! Me aka 'daukemu munafukai ko me?�
Jaddatu ta ce“Kusan hakan ne ban yarda da ke'bewarku ba dan kiji.�
Rahma ta girgiza kanta ta kira Latifa.
Rusunawa tai ta ce“Uwar 'dakina ga ni.�
“Yauwa Latifa je kimin gyara ki canza zanin gado awanke toilet, ki mopping ko ina.�
Latifa ta amsa da “Toh�
Ta miqe.
Hanan ta fito cikin shiri ita da 'yarta Rahma ta miqe tana ha'de ranta.
Jaddatu tai dariya batace komai ba.
Ja'afar zaune gaban Malam Adamu ya rusunar da kansa, sanye yake da shadda ruwan kwai dinki zamani ya yi kyau sosai.
Cikin dadda'dar muryashi mai fitar amon da'di ya ce“Baaba don girman Allah atafi dani inda za'ayiwa Ibtisam mgani pls.�
Mal Adamu ya ce“Wai kai Ja'afar mune ka maida marasa hankali ko meye? Kace Rahma kake so yanzu kuma kwana biyu ka maida hankalinka wajan Ibtisam kana nufin dukkansu kake so?�
Ja'afar cikin ladabi ya ce“Eh Baabna hakane.�
Ran'kwashinsa Mal Adamu yay akansa, ya ce“Ba ruwana wlh idan bakayi aniya ba, idan sun tafi wajan magani da kai zamu koma niger.�
Abie 2 ya ce“Ni abinda ban ganeba Ja'afar wa kafi so tsakanin Ibtisam da Rahma?�
Kai tsaye Ja'afar ya ce“Wallahi Abie su dukkansu ina son su....�
Mal Adamu ya ce“Tashi bamu waje shashasha.�
Sallamar su Rahma ce ta katse mgnar ta shi.
Kusan Abie ta zauna tana gaishesu.
Malam Adamu ya amsa cikin fara'a yana tambayarta.
“Ina Abienki?�
“Yana ciki Baba.�
Abie 2 ya ce“Hanan harda ke za'a tafi ko?�
“Eh Abie harda ni.�
Sallama suka musu yayin da suka fito dankkansu.
Rahma kusan Ja'afar Hanan da Iman na side 'din baya, Ja'afar yaja motar suka fice, sunata hirasu cikin nisha'di.

Raiyana tana shiga bedroom 'dinta takira Wahida, tana 'dauka ta saki kuka ta ce“Wlh komai na neman wargaje min, wlh ina son Abdulmajid bazan so na rasa shi ba, amman wlh na tsani Rahma nan sai naga bayanta.�
Wahida daga can ta ce.
“Matsalata dake rashin wayo, shiyasa burinki ba lallai ya ta'ba cika ba, sbd duk mai gajan hkr bai fiya cin ribar duniya ba, tuntuni kin 'bata rawarki da tsalle. Yanzu kin tabbata taci strawberry da na kawo miki?�
Raiyana ta ce“A'a wlh ta bama Abien ajiyarsa kinga da nuna wani abu awajan zai zargi wani abun shiyasa na basar.�
“Good ki saka musu ido don Allah bari haukan nan kar ya qarasa ganoki kinga yanzu ma dan malam na aikin shashatau ne yasa bai iya lura da wani abun, bari zanje yanzu yay mana bincike ko zai ganewa ita 'din 'yarsa ce, dan kina cewa ki fito yanzu zai zargi wani abun.�
Raiyana ta ce“Ngd naji da'din kasancewarki 'kawar arzi'ki.�
Sallama sukayi tai jifa da wayar ta kwanta tana tunanin mafita, tin kafin ta kwa'be mata.
Dr Salis ya kaisu har room 'din da Ibtisam take.
Kwance take tana baccinta.
Ja'afar ya sakata gaba yana kallonta ya riqe hannun mai lafiyar.
Rahma ta ce“Allah sarki baiwar Allah jita kyakkyawa da ita, a ba'kar fatar ma ita fara ce. Allah ya baki lfy.�
Hanan ta ce“Ameen.
Rahma ta kalli Ja'afar ta zum'buro baki gaba ta ce“Saketa mutafi ko¿�
Dr ya ce“Ai kuwa idan ta tashi mai rabasu sai Allah.�
Ja'afar addu'a yay mata ya gyara mata kwanciyarta suka fito.
Wajan me taxi suka shiga suka gaishesa Rahma ta basa ku'di da addu'ar samun sauqi.
Dr Salis ya ce“Ai shi zuwa monday zamu sake shi.�
Daga asibiti sai da sukasha yawonsu motar securities na biye dasu.

Wahida zaune gaban Malam tana kallon yadda yake baje qasa afaifai, yana siddabarunsa.
Sosai ya bada gaskiya akan binci ken da yake yi.
Kallon Wahida
ya yi ya ce“Mgnar gaskiya tsakanin Abdulmajid da Rahma na kasa ganin komai banda wasu taurari masu matuqar haske da nake gani. Amman da fatan ta ci strawberry da na baki yau da safe kika kai?�
Wahida ta zayyane masa komai kamar yadda Rayyana ta fa'da mata.
Wasu kwalaban turare manya guda 2 ya bu'de ya shafe babban casbi nan mai dubu ya shafa agoshansa da fatar idanunsa ya shiga wasu irin sabbatu yana Jan dogon casbin nan.
Sai da ya kwashe awa 1 ahaka ya 'dago ya kalli Wahida ya ce“Tabb akwai babbar 'kura sbd sihirin jikin Rahma da Ja'afar yana dab da karyewa, sbd ba qaramin tashi tsaye akayi akan lamarin ba. Hanya 'dayace ba 'boye-'boye Raiyanatu ta amince na sadu da ita na ha'da maniyi da nata na mata wani gaggarumin asiri wanda inada tabbacin sai ya kamasu su dukkansu sai yadda tai dasu.�
Wahida ta ce“Toh ba matsala zan mata bayani anutse idan bata amince ba ita ta sani.�
Tana fita ta Kira Raiyana ta mata bayani.
Raiyana ta ce“Wlh tsoro nakeji bazan iya aikata zina ba tin farko kinsan duk mugun halina ban sha'awar aikata zina banda aure bare inada miji kamar Abdulmajid bazan iya ba wani kaina ba.�
Wahida ta ce“Nasan hakan shiyasa nace kiyi shawara.�
“Wahida ya sake wata dabara bazan aikata zina ba gaskiya, gwara na hkr nifa atsorace ma nake sbd ya gama ganoni fa sabi'de shagu'be da yake min, yana min magana me harshen damu.�
Wahida ta ce“Ki dai bi asannu ki koyi hkr da siyasa.�
Sallama sukayi ta koma ta sanar da malam abinda Raiyana ta ce. Malam ya ka'da kafa'da ya ce“Ku ta shafa�.

Ja'afar lokacin da yay parking da mota Abie ya fito yana sanye da farar jallabiya milk colour, ya 'dora hirami kansa, tafiya yake cikin nutsuwarsa yana waya ya doshi rumfar shaqatawa. Sai baza 'kamshi yake wani irin annuri na fita kan fuskar shi, baza ka kalleshi kace akwai abinda yake cin zuciyarsa ba, sai baza uban 'kamshi yake.
Ja'afar hango Abie ya saka ya kalli Rahma ya ce“Muje na gaishe da Abie na wuce gida, kinga Baaba Tsalha ya kirani wai nazo zamuyi mgna.�
Rahma ta sakar masa murmushi ta ce.
“Ok muji Habibyna.�
Hanan ta ce“Uhmm! Ba ko kunyar suruka ko?�
Ja'afar fitowa yay yana murmuahi ya bu'de Rahma 'kofa, Raiyana ta fito tana riqe da hannun Iman suka nufi wajan Abie wanda yake cikin rumfar shan iska.
Ummu Adnan suka hango ta kai masa kayan motsa baki ta fito.
Da sallama suka shiga ha'daddiyar rumfar wadda take fitar da 'kamshin Franni.
Abie ya amsa sallamar yana fa'dda'da fara'ar shi, ya na amsa gaisuwar Ja'afar ya kamo hannunsa ya zaunar da shi kusan sa. Ya ce“ Baby ba shi lemo mana. Ja'afar ya mai jikin? Tana bacci ko?�
Ja'afar ya ce“Eh Abie.�
Abie ya 'dora iman cinyarsa ya ce“Baby Abunki ya kusa zauwa, ke Hanan ya tin jiya yana kiranki bakya 'dauka?�
Ya tambayeta yana hararenta ya madai idanunsa kan Rahma.
Wacce ta zauna kusansa ta 'dauki cup 'din da yasha lemun inibi ta shanye sauransa ta ajiye cup 'din ta 'dauki wani ta tsiyayama Ja'afar ta beqa masa.
jingina kanta da kafa'dar Abie tai tana kallonsa, suna mgna da Hanan amman idanunsa akanta yana hararenta. Ashagwa'be can 'kasa² ta ce“Abiena bacci nake ji.�
Abie suna mgna da Hanan bai katseba sai da ya idar ya ce“No! Bazaki ba Baby.�
Ja'afar ya rusuna yama Abie sallama.
Rahma ta sumbaci kumatun Abien ta miqe ta tafi raka Ja'afar.
Hanan tana dariya ta ce“Wannan yarinyar taka Abie rigimammace.�
Murmushi yay ya ce“Toh ya na iya Hanan.�
Hirasu suka shiga tsakanin ta Wa da

Please Login or Register in order to submit comment