Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cin abuncin ya iso yaja kuje ya zauna, ya bu'de plate.
Sosai sukaci alfatat 'din wanda yaji niqaqen nama, suka Sha lemon inabi.
Abie ya bata magani ta Sha suka dawo falo suka zauna Rahma ta canza channel, Abie ya shirya ya tafi makarantar su Rahma, ita da Anee su na zaune suna hirasu harda Meerah.

*Tchad*
Misalin 'karfe 8 na dare Ja'afar zaune gaban Mal Adamu, suna mgna Abie 2 na gefe, casbi ahannunsa yana ja.
Ja'afar sanye yake da 'kananun kaya, wanda suka masa kyau, kasancewarsa namiji me qirar qarfafa, sun fito da mur'daddan jikinsa sai baza 'kamshi yake.
Mal Adamu ya ce.
“Wlh har na rasa bakin da zan godema bawan Allah'n nan, ya kaiku 'kasar waje neman magani an dace yanzu kuma takardun karatunka yake nema dan samomaka aiki ko cigaban karatunka? Allah ya masa albarka ya karashe da dukkan abin sharri.�
Abie 2 da Tanko suka amsa da “Ameen.�
Ja'afar ya ce“Eh Baaba inaga karatun yake so cigaba, ni kuma sam ya fita araina gwara kawai aikin 'kasa² dai-dai ruwa dai-dai tsaki. Yanzu idan yazo dole tare zamuje Niger tinda takardon na can.�
Mal Adamu ya ce “Toh toh ba laifi Ja'afar Allah ya maka albarka.�
Tanko ya ce“Mal Adamu inaga idan muje ayi biki sai kawai yazo da matarsa, ko ta zauna can idan ya yi 'yan watanni sai ya dinga zuwa, inaga zaifi ko?“
Ja'afar ya kalli Tanko da sauri sai dai ya sadda kansa.
Mal Adamu ya ce“A'a wannan ba mgna bace, ya za'ayi biki yabar matarsa ya taho? Ai insha Allah tare zasu taho Allah ya tabbatar mana da alkhairi.�
Suka amsa da “Ameen.�
Abie 2 yay gyaran murya ya ce.
“Abdulmajid ya ce ku qara hkr Rahma batajin da'di tana kan shan magani, da zaran ta gama likita ya qara bincikar lafiyarta zasu dawo.�
Mal Adamu ya ce“Allah sarki, Allah ya qara mata lfy, ya maidosu lfy.�
Abie 2 da Tanko suka amsa da “Ameen.�
Ja'afar ya miqe ya musu sallama ya fito yana karka'da 'dan makullin motarsa.

Ibtisam ya hango tana zagaye tana kalle² a compound 'din gidan.
Cike da mamaki yake kallonta, yana nazarin anya yarinyar nan tana lafiya lau kuwa?
Ganin ta nufi rumfar shaqatawa ya tsaya yana kallon ikon Allah har ta shige ta zauna.
Wajanta ya nufa fuska ba walwala, yana takunsa mai cike da 'kasaita.
Kallonta yay ta sadda kanta tana wasa da zabon hannunta, bata ma san ya shigo ba.
Cikin tsawa ya ce“Ke! Tashi koma ciki uban me kikeyi anan?�
Ibtisam firgigit tai ta dawo daga duniyar tunanin Abie.
Kallonsa tai ta ga yadda ya tamqe fuska ba alamun wasa.
Baki ta zum'buro gaba ta ce“Haka kawai nazo inajin yanayi me da'di sai ka korani...�
Wata iriyan damqa yay mata ya miqar da ita tsaye, wadda ta sanyata sakin ihu jikinta ya 'dauki rawa ganin yadda fuskarsa take amurtuke.
Cikin mugunta ya matse 'kugunta da kakkausar murya ya ce“Maza wuce ciki ni sa'anki ne?�
Ya tambaya yana murza mata fatar baki, ta saki kuka tana girgiza kanta ta ce“Don Allah kayi hkr zan shiga gidan.�
Hanka'data yay waje cikin tsawa ya ce“Wuce na sake ganin kin fito ahaka ke marar kunya.�
Da gudu ta nufi cikin gidan, tana kuka.

Tsuki yaja ya tafi ya shiga motarsa ya fizgeta aguje ya nufi gate yana huci, yana 'kudirtawa tabbas sai ya mata horo me tsanani zata dawo hayyacinta.

Zazzaune suke afalon anata hira Rayyana wacce taje cikin farin ciki sbd wayar da sukayi 'dazu da Rahma awayar Abie jin yadda Rahma ta sake tana bata labarinba, suna tafe har ita cikin satin nan, ta kwantar da hankalinta Abie na sonta bazai rabu da ita ko meye ta mata ta yafe mata.
Shi ne fa Rayyana taji hankalinta ya kwanta dan tasan Rahma 'yar lelen Abie ce tinda tana sonta toh Abie ma zai sota. Ta zage tana basu labarin wata kakarsu wacce take Sudan, idan kana son kaci dariyata ka samo kyankyaso koda mataccene ka ajiye wajan da zata gani har rawar banjo take tsabar tsoro.
Idan ta fa'da da larabci sai ta fassara da hausa sbd Laraba wacce ta dage tana tiqar dariya, oh! Mutane basu iya samun waje ba.🤔
Jaddatu ikon Allah take kallo yadda Rayyana ta saki jikinta tana bada labari, ita ko kunyar abinda ta aikata bataji, har ta manta.
Hanan dariya take harda riqe cikinta ta ce“Wlh Rayyana da ace anan garin take ko dan naga rawar banjo zamuje mu samo kyankyason mu ajiye agabanta.�

Rayyana ta ce“Wlh Hanan anyi muguwa kice rawar banjo kike son gani?�
Dariya sukayi Jaddatu ta ce“Kai wlh mutane ba kunya ko ka'dan koda yake ance tabarmar kunya da hauka ake na'deta.�
Rayyana ta gane da ita take ta basar da ita taci gaba da labarinta.
Ibtisam ce ta shigo tana kuka.
Laraba ta ce“Ke fa bakida hankali wlh meye haka kike musu ihu agida? Kinsan dai jajayen mutane basa son hayaniya dan Allah ki bari.�
Jikin Laraba ta zube tana rage kukan nata ta ce’Yo ba wancan mugun bane ya mur'demin hannu haka kawai ban masa komai ba, dan naje wata rumfa mai shegen kyau na zauan.�
Rayyana ta ce“Waye Ibtisam?�
“Ja'afar mana.�
Rayyana ta ce“Oh! Abin na masoyana ba ruwana qila akwai abinda kika masa.�
Jaddatu ta ce“Me ya faru ne take kuka iyayan jin hausa?�
Latifa da take 'daukar tray'n da ta yanko Jaddatu kankana ta gintse dariyartatai maza ta wuce kar abin ya shafet.
Rayyana ta gane sarai Jaddatu habaici ta mata ta fa'da mata abinda Ibtisam ta fa'da.
Jaddatu ta ce“Wannan yarinyar zatayi ruwan marasa kunya qila ta masa rashin kunyane ai kome bazai gagareta ba tinda ta iya biyosa daga wata qasa tin kafin aurensu.�
Rayyana dai bata sake mgna ganin Ibtisam da Laraba suna kallonta sai kawai ta waske ta ce“Ta ce qila kin masa laifi ne.�
Ibtisam ta miqe idanunta akan hoton Abie ta nufi hanyar kitchen inda 'dakinsu yake tana share hawaye, tana kisima wani qudiri aranta ta nan kawai takejin zata iya samun Abie.

*Gabon*
Har goma na dare Aishatu bata farfa'do ba daga dogowar suman da tai, hankaalin iyayanta da 'yan uwanta ya tashi. Ma'aruf daman ba'acewa komai, shi hankalinsa qololuwar tashi ne yay, ko baqin ruwa har yanzu ya kasa Sha, hajiyarsa ba yadda batayi da shi ba amman yaqi ya ce sai yaga tashin Aishatu.
Amman doctor ya basu tabbacin zata farka akowane lokaci.
'Bangaran Rabi'ah kuwa tinda take bata ta'ba tsanar kanta da bin mazan da take ba sai yau, ji take kamar ta da'bawa cikinta wuqa amman idan ta tuna makomarta wajan Allah sai ta fasa.
Tinda ta dawo daga sallah sai istigfari take taji har Abadan bazata sake zina ba ta tuba da zuciya 'daya ta fasa dukkan halaiyarta, abinda ta yanke ta qudurta aranta tanaga shine daidai shi zatayi, bata ta'ba sanin cin amana idan an kamala haka take sai yau ta yi tirrr da Allah wadaran halaiyarta.

*Espagne*
Anee sai da sukayi sallar isha sukayi lunch kafin Rahma ta saka direba ya kaita gida.
Har lokacin Abie bai dawo ba, Rahma ta cika da kewarsa ga bata san inda ya ajiye mata wayanta ba!
Koda yazo ta yi fushi dakyar ya lallasheta sai da ya Kira mata Jaddatu sukayi fire sosai da Hanan kafin 'yan Morocco su ummiterh daga qarshe Rayyana.
Misalin 12 na dare, hadari ya ha'du sosai garin sai wata irin cida ake ga tsawa mai figitarwa.
Rafeek kwance saman lafiyayyan gadonsa yana juyi banda tunanin Rahma ba abunda yake, adaidai wannan lokacin, mugun sonta yake kamar me, ga shi yana kiranta baya samunta.
Sake gwada kiran number nata yay duk da yasan ba lallai ta shiga ba.
Cikin sa'a ya ji wayan na ringing ya zabura ya miqe zaune cikin farin ciki.
Dai-dai lokacin Abie na kwance saman 'katon Royal bed 'dinsa ya shige cikin lallausan bargo, yana latsa wayan Rahma, kiran ya shigo.
Sunan Rafeek ya ga yana yawo saman screen 'din wayan.
'Kirjinsa ya ji ya buga dammm!
Picking call 'din yay, baiyi mgna ba, ya kara wayar kunnensa.
Daga can Rafeek ya sauke ajiyar zuciya,cikin sansanyar murya mai da'di ya kirata.
“Baby cute! I miss you I love you, ya jikin naki? Wlh na kasa bacci tunaninki na azabtar dani, 'dazu na matsawa Anee ta rakoni gidanku taqi, hope kinji sauqi? Pls ki ban dama na bayyana wajan Abie sbd naga baida wata Matsala wlh ina sonki ina son mallakarki nan kusa, hello baby cute kina jina kuwa ko network ne?�
Abie tsabar tashin hankali har zufa take tsatsafo masa duk kuwa sanyin A/C da yake cikin 'dakin zuciyarsa wani irin tsalle take tamkar zata faso 'kirjinsa ta fito waje, hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi sam bai san abin na yaron ya kai haka ba!
Wayar ya kashe baki 'dayanta, yana ciza jajayen lips 'dinsa, yana jin wani irin 'daci acikin bakinsa.
Wayarsa ya janyo wacce take ajiye akan bedside drawer, hannunsa na rawa ya Danna wata number ya kira bugu 'daya aka 'daga.
Dai-dai lokacin da zaiyi mgna ya ji Ana bugun 'kofarsa da 'karfin gaske.
Jin muryar Rahma tana kiransa tana shasheqar kuka yay saurin jifa da wayar hannunsa ya miqe jikinsa na rawa ya diro daga saman bed 'din ya nufi 'kofar...!
Washhhh! Wlh ina ciwon kai nai muku typing 'din nan.

_Rahmerh ladingo😉_


_*🤲�Ya Allah ka jiƙanmu kayi mana rahama badan halinmu ba.��*_
3/16/22, 11:30 - Buhainat: ```D A```

```65&66```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉�300N +22796515805*_

```WANNAN PAGEN SADAUKARWANE GA MUM SAYYED DA MMN ABDULWAHAB AND KHADIJA WLH NAJI DA'DIN COMMENTS 'DINKU NA JIYA TNX SO MUCH ACI GABA DA GASHI GUYS, YANZU AKA SOMA ANZO WAJAN.😉```
Kofar Abie ya murza key ya bu'de hankalinsa atashe.
Kafa'dunta ya riqe yana girgizawa, “Babyna me ya faru dake? Tsoron tsawa ko Baby?�
Rahma ta girgiza kanta ta fa'do jikinsa tana qamqameshi gam, jikinta sai rawa yake, tana kuka ta ha'da uwar zufa.
Arikice ya 'dago fuskarta yana bubbuga kumataunta, ya tsura mata idanu, yana tambayarta “Baby menene? Me ya faru dake pls nutsu ki fa'damin kalleni tare kike da Abienki ba abinda zai sameki insha Allah. Menene Baby?�
Rahma ta qamqamshi gam ko 'kwa'kwaran motsi ta hanasa, sai kuka take.
“Oh! Ya Rabbi! Baby tsoron ruwane ko cida? Nasan dai ba wani zai iya shigo mana gida ba, toh menene Baby? Oya muje 'dakin naki mugani.�
Ya qarashe mgnar yana qoqarin 'ban'bareta daga jikinsa, taqi ta maqaleshi gam.
“Baby ki tsaya mana karki kadamu, nutsu ki min bayani OK? �
Kai ta 'daga ya janyeta daga jikinsa ya kama hannunta don su shiga bedroom 'dinta ta'ki ta qamqameshi.
Cak ya cirata sama kamar 'yar baby ya nufi bedroom 'dinta da ita.
Cikin kuka ta ce.
“Abie kar muje 'dakina wlh tsoro nakeji awajanka zan kwana mummunan mafarki nayi, wanda ko 'kasar arna abin baya faru kuma bazai ta'ba faruwa ba.�
Ta 'karashe mgnar cikin kuka.
Abie galala ya saki baki yana kallonta ya tsaya da tafiyar cak, fuskarta ya tsirawa idanu, cikin kwantar da murya ya ce“Ok fa'damin wannan wani irin mafarkine baby? Kina nufin bakiyi addu'a ba lokacin da kika farka kika dinga kuka da famar kiran Abie?�
Ya mata tambayar yana 'dago ha'barta ya ce“Kalleni Baby.�
Yadda ta ga fuskar shi ba wasa ya sanya ta ha'diye kukanta tana kallonsa ahankali ta motsa la'bbanta ta ce.
“Wlh nayi addu'a Abienah kawai na gigice da mafarkin ne.�
“Ok fa'damin wane irin mafarkine? Fa'damin idan ba haka ba sauka kije 'dakin ki kiyi addu'a ki kwanta bi khair insha Allah. �
Rahma ta qara maqaleshi ta sadda kanta cike da jin nauyin Abien ta bu'de 'dan 'karamin bakinta ahankali ta ce.
“Abie zan fa'da maka, wai mafarki nayi ni da kai muna cikin wani irin 'kawataccan lambu, ko ina franni ne tsanwa shar, wasu irin dawakai farare tass na zagaye damu, sai wasu mata masu farin kaya suna hidima damu, da wasu yara maza kyawawa biyu basu fi shekara 3 ba, sai wata 'Yar baby 'yar wata 10 amman tana tafiya irin ta yaran da basu jima da koyan tafiya ba, amman akwaita yawo ko ina shiga take a lambun, haka duk inda zaka tafi kana maqale da ita ko ina gashinta har gadon bayanta, kamarmu 'daya da ita, wai kuma inada cikin tsawon wata 4 duk bamu san da shi ba sai yau anata zabga ruwa babyn ta fita aguje sakamamakon Meerah da ta bu'de 'kofar ta manta bata rufe ba, ta fice hankalina atashe na bita aguje sbd tsoron karka ganta ka 'batama kowa na gidan rai, amman yarinyar ta min nisa ruwan haka ya dinga dukanmu dakyar na kamota tana kyalkyala dariya.
Ba'a fi awa 'daya ba zazza'bi ya rufeni hankalinka a tashe mukaje asibiti gwajin farko akace inada ciki wata 4 sakammakon razanar da nayi ina cewa ban yarda ba ya ina goya zanyi ciki wallahi bazan yarda ba sai an zubar, daidai wajan akayi wata irin tsawa na tashi a bacci, don Allah Abie kayi hkr da lafazina wlh abinda ya firgitani kenan duk da nasan sharrin mafarkine amman na ru'de naji tsoro sosai ne.�
Ta 'karashe mgnar cikin shasheqar kuka tana kallonsa cike da tsoron hukuncin da zai 'dauka 'kilama, dukanta zaiyi, ya ce ta haukace.
'Kananun kyawawan idanunta ta xaro waje cike da mamaki tana kallon ikon Allah, ganin Abienta na sakin 'kayataccan murmushi wani irin zallar farin ciki take gani akan fuskarshi idan batayi 'karya ba sai ta ce rabon da taga irin wannan murmushin akan fuskarshi tin tana 'yar shekaru 12 tin Jaddi Cheri, sunan da take kiran abdulwahab mahaifin Abie kenan.
Mamaki sosai Abien yake bata lokacin da yake sumbatar kumatunta, ya zura hannunsa cikin rigarta yana shafa lafaffan cikinta yana kallonta.
Wani iri ta dingaji a 'dan gigice ta riqe hannunsa ta marerecewa, idanunta ya fara tara ruwa ta kirasa“Abie Rabin raina.�
Juyawa yay ya shiga bedroom 'dinsa ya murza key ya nufi 'katon bed 'dinsa da ita har yanzu yana shafa cikinta yana wani irin murmushi sam labarin ya mantar da shi tashin hanklin da Rafeek ya jefasa.
Rahma ta lumshe idanunta tana tura kanta cikin 'kirjinsa tana shaqar dadda'dan 'kamshin sa tana sauke ajiyar zuciya.
Tsakiyar gadon ya kwantar da ita, ya nufi fridge wanda yake nan cikin bedroom 'dinsa, ya bu'de ya 'dauko fresh milk me sanyi wacce ya siyo 'dazu ya 'dauki cup ya tsiyaya sai da ya cika cup 'din ya rufe sauran ya maida fridge ya nufo gadon.
Zama yay ya 'dagota tana kallonsa ya tallafo fuskarta ya kafa mata cup abaki.
“Oya Baby sha kiji sanyi azuciyarki zan fa'da miki fassara mafarkinki.�
Ya 'karashe mgnar yana sakar mata tattausan murmushi, wanda ya sanya jikinta qarasa mutuwa murus.
Hannunta ta 'dora saman nashi ta fara sha anutse, tasha fiye da rabi ta janye bakinta tana langwa'bar da kanta.
“Abie ya isa.�
“No! Baby shanye ji cikin ki kwalam ba komai, laifin Baby Ummu Aymana ne (Fifie)
Ta sanya mamarta ruwa ya daketa harda zazza'bi daga nan aka gano 'kaninta ko 'kanwarta Allah masani.�
Ya 'karashe mgnar yana murmushi hannunsa saman lafaffan cikinta yana shafawa anutse, still idanunsa cikin nata yana bata fresh milk 'din.
Baki 'daya Rahma 'kusosun kanta sun kwance ta rasa gane kan Abie 'dinta 'karshe idanunta ta kulle ta shanye fresh milk 'din, ya kwantar da ita ya mayar da cup saman fridge, sai lokacin idanunsa suka sauka akan wayarsa wacce aka gaji da Alo² aka kashe.
Sumar kansa ya shafa ya 'dauki wayar da take yashe saman carpet yay 'yar siririyar dariya ya kashe wutar 'dakin ya, kunna ta gefen gado ya hauro saman bed 'din ya kwanta nesa da Rahma yana murmushi yay dialing number 'dazun, yana kiran Rahma “Babyna zo nan.�
Ashagwa'be ta rarrafa jikin Abie ta shige jikinsa luf ta qamqameshi.
Blanket ya ja musu ya rufesu ruf kansu kawai ya bari awaje, hannunsa 'daya ya sanya ya zagayeta 'dayan manne da wayarsa.
Bugu biyu aka 'daga.
Murmushi ya saki me taushi ya ce“Afuwan ihun Babyna ne ya rikitani 'dazun hope kana lafiya? Pls Tarno flight gobe zuwa Tchad insha Allah nake so?�
Daga can wani kyakkyawan baturene babba zai kai warin Abie ya maida masa cikin harahen nasu.
“Ok Abdul an gama 'karfe nawa?�
Abie ya murmusa yana kallon fuskarta ta 'dan hasken 'kwan gefen gadon ya 'daga mata gira ganin ta kafesa da idanu, ya ce.
“Da yamma muyi kwana hanya ya kasance na samu sallar juma'a jibin insha Allah a Tchad. �
Tarno ya amsa da “Ok an gama yadda kakeso hakan zayi kun gama samun flight amman kwana Canada zakuyi.�
Sallama sukayi da Abie.
Wayar ya kashe baki 'daya ya ajiye saman bedside drawer, ya sake shigar da Rahma jikinsa ya kirata can 'kasan maqoshi, dab da fuskarta har hancinsu na gamuwa, suna shaqar numfashin junansu.
“Baby Ummin Abienta!�
Rahma wani yammm ta ji ta sake qamqameshi ashagwa'be ta kirasa.
“Abie nah! Ka fassaramin mafarkin kaji?�
Hancinta ya sumbata ya tallabo fuskarta suna kallon juna, bakinsa dab da kunnenta cikin kwantar da murya ya ce“Ruhin Abie mijinki kikayi mafarki kuma nasan insha Allah cikin tarin yaran da zaku haifane Allah ya nuna miki ukun da cikon na hu'dun.
Ni shaquwar da take tsakaninmu ce ta sanya kikaga fuskata amman azahiri mijinki na sunna kiga gani.�
Rahma ta sauke ajiyar zuciya ta shafo sajan Abie ta tura hannunta cikin sumar kansa me taushi tana caku'dawa, ashagwa'be ta ce “Abie naga hotonsa pls Rabin raina kaji?�
Ta 'karashe mgnar tana sumbatar goshinsa tana kallon jajayen lips 'dinsa tai saurin 'dora bakinta saman nashi ta sakar masa Sumba ta janye tana kwantar da kanta saman kansa ta kirasa “Abie nah!�
Sai ta rushe da kuka.
Abie ya furta “Ya Ilahi! Babyna menene? Taho zo nan.�
Ya 'karashe mgnar ya 'daukarta dukkanta ya 'dorata saman faffa'dan 'kirjinsa ya 'kam'kameta yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, ya tura hannunsa cikin dogon gashin kanta yana yamutswa asannu.
Ra'da ya mata akunnenta“Abinda kikeso na tare dake Baby shima sonki yake kamar zai mutu sbd masifar sonki da 'kaunarki, gobe zamu wuce bazan sake baki waya ba sai kin tare, kina son ganin mijinki?�
Asakalce ta 'daga kanta tana tura hannunta cikin gashin kansa.
“Ok yaushe kikeso?�
Ra'da ta masa akunnensa “Wayyo Abie Rabin raina duk kunyarka nakeji ni bazan iya gayaba ka sanya min rana da kanka.�
Murmushi yay ya kamo hannunta ya sumbata yana cizon 'karamar yatsarta ta saki 'yar qara tana 'kyal'kyala dariya ta qamqameshi.
“Nan da kwana 6 insha Allah zai bayyana gareki OK? Ko kinfi son sai bayan biki? Nafiso ki gansa idan kinji bai miki ba zan rabaku na baki farin cikin ki.�
Rahma taji damm! Gabanta ya fa'di dan ji take rabuwa da Abie kamar rabuwa da numfashinta ne, amman tasan dole zata rabu da shi ji take inama ace Ab'ie ya halata gareta, gani take Abienta yafi dukkan mazan duniya komai da ake buqata wajan namiji, ita hakan take ganin Abienta.
Daurewa tai ta yi murmushin yaqe ta ce“Allah ya kaimu.�
Hancinta yaja ya ce“Ameen Baby ummina.�
Manne suke waje 'daya Abie na shafa gashinta ha'di da Sosa mata ta yi luf samansa, tanajin daman su dauwama ahakan, tana jinjinawa Ammi Rayyana ta yi dacen miji.
Hannunta ta tura cikin gashinsa tana shafawa.
Saukar numfashinta ya ji alamun ta yi bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya fara qoqarin kwantar da ita taqi ta maqaleshi.
Dariya yay ya sake mata masauki a 'kirjinsa, yana shafa bayanta, ya karanto musu addu'ar bacci.
'Karfe 3 na dare ya farka daga dadda'dan baccin da ya sace shi, ya samu ya janye jikinsa daga nata ya shiga bathroom ya 'dauro alwala.
Sallar nafila da ta zame masa jiki ya yi bayan ya idar ya yi karatun Qur'ani wanda saida aka Kira sallar asubah ya rufe Qur'anin ya miqe ya gabatar da sallar raka'atanil fajir yana idarwa yay addu'a ya miqe ya gyarama Rahma kwanciya ya sumbaceta a kumatu ya lullu'beta, dan ta yaye zanin rufar taje qarshen bed 'din duk girmansa.

'Karfe 6 ya dawo daga masallaci.
Zaune ya iskota saman darduma sanye da jallabiyarsa milk colour ta yafa mayafinta tana karatun Qur'ani.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ji da'di har ransa.
Kai tsaye saman bed ya wuce ya kwanta yana 'daukan remote ya rage gudun A/C.
Idanunsa akan Rahma yana sauraron dadda'dar muryata, suratul Yasin take karantawa.
Tana kai 'karshe tai addu'a ta shafa ta miqe ta linke darduma ta mayar dasu ma'ajiyarsu har Qur'anin.
Kallon Abie tai tana langwa'bar da kanta ta gaishesa.
“Abie nah Sabahul khair.�
Abie ya beqa mata hannu ta taho da sassarfa, ya kamata ta hauro saman bed 'din ya janyota jikinsa ya rungume gam ya sumbaci goshinta ya ce“Baby kin tashi lfy? Ya rigima da shagwa'ba magen Abienta�
Kai ta 'daga masa tana 'yar dariya.
Lullu'besu yay da blanket ya ra'da mata “Muje na ha'da miki tea sai muzo mu kwanta.�
Ashagwa'be ta ce“A'a Abie ai kasan sai da rana nake breakfast, kafin mu tashi Meerah ta gama mana komai, ko naje na girka mana?�
Hannunsa ya'dora saman lips 'dinta yana shafawa ya ce“No! Baby oya bacci.�
'Yar dariya tai ta shige jikinsa ta cusa kanta kafa'darsa tana shaqar qamshinsa.
Haka wani irin dadda'dan bacci ya 'daukesu manne da junansu.

A can kuwa 'bangaran Rafeek ya shiga tashin hankali jin Rahma ta kashe wayarsa adaren ya Kira Anee dakyar ta samu ta lalla'bashi, akan gobe zata rakashi Gideons da yamma idan ta taso daga makaranta.

*Gabon*
Har garin Allah ya waye Aishatu ba farfa'do ba, dukkan illahirin families 'dinsu hankalinsu tashe yake.
Banda baqin ruwan tea da hajiya take matsawa Ma'aruf ya sha ba abinda yake iya sakawa acikinsa. Kwana ya yi yana sallah yana istigfari akan babban zunubin da ya aikata na zina.
Misalin 'karfe 3 na yamma, 'yan gidansu duk suna waje azaune Ma'aruf ya kasa ya tsare yana bakin gadon Aishatu azaune, yana riqe da hannunta me drip yana zubar da hawaye.
Motsi ya ji hannun ya fara ya kalleta agigice cikin murna har ya bu'de baki zai kirata sai ya tuni ayanzu ba wanda ta tsana bata son gani sama da shi.
'Ko'karin janye hannunsa yake cikin nata dan ya danna 'yar na'uran da zata janyo hankalin likitocin.
Ya ji tana furta.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ya Allah karka tasheni daga wannan dogon baccin da nake idan dai har gaskiya ne abinda ya faru ba mafarki nake ba ya Allah ka 'dauki raina na huta...�
Ma'aruf ya rufe mata baki yana kuka ya ce“Aishatu don Allah bu'de idanunki muyi mgna kiyi hkr karki tonamin asiri na rantse miki da Allah ban ta'ba zani ba sai jiya itama wallahil azeem bansan yadda akayi ba nayita ki yarda dani don Allah ki bu'de idanun...�
Wata irin bangaza ta masa idanunta arufe tana qara rufesu.
Ta sake hanka'dashi wanda sai da wajan cs 'dinta ya amsa ta saki ihu tana riqe wajan cikin kuka ta ce“Fita anan na tsaneka bana son ganinka wallahi idan baka fita ba zan zan baka mamaki na tsaneku tsana mafi muni macita amana azzalamai, daman kai na jima ina fa'da maka kai mazinaci ne kana musamin Allah ya isa tsakanina daku, ina 'dan cikina? Kun kashe shi ku?�
Ta tambaye shi cikin tsawa har yanzu bata bu'de idanunta ba, sai wani irin numfashi take ja jikinta na wani irin 'bari tamkar me farfa'diya.
Ma'aruf na'uran ya danna da 'karfi sai ga likitoci sun shigo aguje.
Temakon gaggawa suka dinga bata allurai Dr ya mata nan take bacci ya 'dauketa.
Dr ya dinga ma Ma'aruf fa'da.
“Me ka fa'da mata wanda ya haddasa jininta sake hawa? Wlh sai kunbi ahankali ayi nesa da abinda bata 'kaunar gani.�
Ma'aruf ya share hawayen fuskarshi ya ce“Ok Dr insha Allahu za'a kiyaye Ngd.�
Wajan iyayan nasu ya fito yana sheda musu ta farfa'do amman an mata alluran bacci. Hamdalah sukayi duk suka 'dunguma 'dakin da take suka mata addu'a.
Hudah da Kabeera sunzo dubata har kuka sukayi jin an ciro yaron bai qarasa isa haihuwa ba.

Rabi'ah zaune ta rabka tagumi tana zubar da hawaye tana mgna qasa-qasa.
“Don Allah Aishatu ki yafemin nasan na tafka kuskure mafi girma, cin amanar wadda ta yarda dani, mu hu'du muka tasa amman cikinsu kifin sona da yarda dani fiye da Hudah da Kabeerah, amman nice me 'kyashinki da ha'intarki, naqi aure sbd yadda kika 'kwa'daitamin mijinki kike 'kodashi da yabonsa sai naji duk duniya banda wanda nakeso sama da shi.
Wani 'bangaran Aishatu kece kika janyo akaso 100 kaso 90% laifinki ne ni laifina cin amanarki, da son abinda duniya da ya min yawa har na fa'da bin maza, har yau na kasa samun hamsha'kin me ku'di daidai Ma'aruf, abinda ya saka kenan na biyo masa ta bayan gida, ki yafemin Aishatu don Allah. �
Ta 'karashe mgnar cikin kuka, Rabi'ah kuka na gaba....

*Tchad*
Tin bayan la'asar Ja'afar suka zo nan gidan Abie wajan iyayan nasu suna fira cike da nisha'di.
Sanye Ja'afar yake da wani yadi me kyau milk colour ya yi kyau sosai sai baza 'kamshi yake.
Cikin tsokana ya ce“Baaba ya kamata a'danaka a motar nan gaskiya har Abie 2 ma.�
Abie 2 yay

Please Login or Register in order to submit comment