Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_.............DA RABO_



*01*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM


*Dedicated to my Trio*♥


Cikeda risinawa matashi mai kimanin shekaru 30 a duniya ya d’ago yana duban Dattijon mutumin mai kimanin shekaru 58 zuwa da tara kana yace “But Daddy.....”

Katsesa yayi da fad’in “No SAMEER I don’t want to hear anything, what’s gotten into you Son.... Haba Sameer ni nasan ba haka na tayar dakai ba... Abinda nakeso da kai ka tashi ka tafi gidan Uncle d’inka ka basa hak’uri sannan ka d’auki matarka ku tafi magana ya k’are....”

Jinjina kai yayi kana yace “Ok Daddy I’ll do as you say....”

Murmushi Dattijon yayi kana yace “That’s my boy Allah ya maka albarka....”

“Ameen Daddy...” Ya fad’i yana k’ok’arin mik’ewa had’ida fidda wayar salulansa daga aljihu....

Satan kallon sashen da Mummynsa ke zaune yayi aiko banda uwar harara babu abinda take aika masa.... K’arasawa ya d’anyi had’ida risinawa kana yace “I’m sorry Mummy... I promise this will never happen again in shaa Allah.....”

Jinjina kai tayi kana tace “I hope so, Ace aure ko wata biyar mai kyau bakuyi ba an soma samun sab’ani irin haka ai babu dad’i... Dama naji batu mai dad’i kaji koh...”

A hankali ya jinjina kai kafin ya fice daga parlorn....

Motarsa ya nufa ba tareda ya kula da Malam Sallau dake gaidashi ba...

Ya jima k’ofar gidansu Siyama yana tunanin ta yanda zai soma bada hak’uri don sam hakan ba d’abi’arsa bace idandai ba ma iyayensa bane, a hankali ya rintse idanunsa had’ida furta “Goodness! Where do I start....”

K’aran da wayarsa tayi ne ya sanyasa zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa daga d’aya b’angaren Sultan yace “Doc we’ve an emergency here at the hospital, Sameer we need you right away....”

Shafe goshinsa ya d’anyi kana yace “Is my presence really necessary, just do what you can, I’m dealing with another problem here...Please...” ya k’arashe yana lumshe dogayen idanunsa masu yalwan suma....

Fuzar da iska Sultan yayi kana yace “Sameer it’s a boy.... He suffered a multiple deep burns... I’m afraid he’s dying...” Ta cikin wayar yake jiyo sautin kukan yaron wanda k’unan wuta ya masa babu dad’i, cikin sauri Sameer ya juya kan motarsa yana fad’in “I’ll be on my way....” Cikin sauri ya karya kan motar had’ida ficewa daga gidan mai gadi na faman d’aga masa hannu alamun a sauk’a lafiya....

****

*Kano*


Cikin sanyin jiki suka shigo parlorn ko wacce tayi jigum jigum, budurwa mai kimanin shekaru 23 a duniya ne ta soma yab’e baki tace “Wllhi Allah Abbah shi yake biye Mamani take abinda taga dama, haka kurum mata ta tayar da bori wai zata tafi tabi MA’ARUF ni so nake wata rana a barta ta gwada fita nemansa ace yau shekaru 26 babu mutum babu labarinsa toh ta ina zaka soma nemansa, sai anyi magana ace tsufa ke d’awainiya da ita, mtsww...” Ta k’arashe tana jan tsaki....

D’ayar mai kimanin shekaru 19 tace “Wllhi Adda Nabila ni bana ganin laifin Baffah Wali idan ya fice mata a giya, kiga dai duk jikokin gidan nan rankatataf d’inmu ban cire kowa ba harda ke mai sunanta bata damu da kowa ba kullum damuwarta Ma’aruf yaron da tun yana shekara 4 ya b’ace sai anyi magana itada Mamy suce INDA RAI DA RABO, Allah na tuba da ace yana raye tsawon shekarun nan ai da ya bayyana mana....”

K’aramar cikinsu mai kimanin shekaru 16 tace “Ahtoh sai anyi magana tace Babban Jika... Mu da yake Yayanmu uwa d’aya uba d’aya ma bamu kaita damuwa b.....” Had’iye kalaman nata tayi cikeda k’unk’uni tana duban wacce ke faman narka mata mugun kallo da alama bata jima da shigowa parlorn ba

“Aunty Zulfah ina yini....”

Gaba d’aya sauran biyun suka juyo suna duban sashen da k’anwarsu ke gaisuwa....

Ganin yanayin Addar tasu wacce ke sanye cikin kayan Bautar K’asa ya sanyasu shan jinin jikkunansu....

Ba tareda ta amsa gaisuwar tasu ba fuska a tsume tace “Mamy fah...?”

Nabila mai bi mata a haife ne tace “Suna can sashen Mamani suna bitan karatunsu na aikin lallashi...”

Girgiza kai kurum Zulfah tayi kana ta nufi k’ofa zata fice Mas’udah mai bin Nabila a haife tayi saurin katseta da fad’in “Allah Aunty Zulfah Mamani abinda take yayi yawa naga dai idan da akwai wanda b’acewar Yaya Ma’aruf zai damesa bayan Mamy da Abbah toh ya kamata ace sai kece tinda ranar da aka haifeki ranar Yaya ya b’ata....”

Nabila ta k’arada “Shiyasa Mamani tafi tsanar Addah sama da kowa a jikokinta a nata tunanin sanadiyar haihuwar Addah Yaya ya b’ata...”

“Ya isheku haka...!” Zulfa’u ta katsesu kafin taci gaba da fad’in “Ku bazakuyi hankali ba, ana cewa yaran Abbah sunfi kaf yaran gidan nan tarbiya amma kuna nema ku shafawa iyayenku bak’in fenti... Sai mai idan Mamani ta nuna damuwarta kan missing grandchild d’inta, badai jikanta bane toh ina ruwanku, idanku baku damu dashi ba sabida baku sanshi ba sai ku k’yaleta ita ta nuna damuwarta, wllhi kunji na rantse kar na sake zuwa gidan nan naji kuna k’anan maganganu kan wannan al’amari kunajina koh...”

Ciki ciki suka amsa kafin Marliya k’aramar cikinsu ta k’arada “Aunty Zulfah yau ina kika baro Kausar naga baki kawota nan gida ba yau....”

Harara kurum Zulfah ta watsa mata kafin ta fice ta nufi sashen Mamani....

****

*Kaduna*


Fitowarsa kenan daga surgery wayarsa dake bisa teburinsa ta d’au ruri.... Dafe kansa yayi ganin mai kiran ba kowa bace illa Mummynsa sannan ta kirasa yafi sau a k’irga, shaf ya mance bai kashe wayar salulansa ba sanda zai shiga aikin domin kuwa akasarin lokuta idan zai shiga aiki kashe wayarsa yake donma kar a nemesa....

A hankali ya d’aga wayar had’ida zama cikin kujeransa....

Kafin ya sami zarafin magana Mummy ta soma balbalesa....

“Sameer ya maka kyau, nace ya maka kyau... Da ka fice zaka gidan Hajiya Faridan gidan uwar wa ka tafi....? Shine sabida tsabagen wulak’anci zaka barsu suna jiranka, ko kasan cewa harta Alhaji Madi bai fice ba ya tsaya jiran zuwanka amma ka kama ka watsa mana k’asa a idanu.... Ya maka kyau Sameer nasan haka zakayi wllhi da ban bari an baka auren Siyama ba....”

Tinda ta soma magana bai katseta ba har saida takai aya, a hankali ya soma fad’in “Mummy calm down please, this isn’t good for your blood pressure.....”

A hasale ta kuma cewa “Don’t ask me to calm down, jininan ma ya hau mana duk ba kaine sila ba....”

A hankali ya shafi goshinsa can k’asan mak’oshinsa ya furta “Goodness..!” A fili kuwa cewa yayi “But Mummy cikinku babu wanda ya damu yaji daga gareni, babu wanda ya damu if I’m also suffering, Mummy this isn’t easy for me either.... Kin sani Mummy kinsan ina son Siyama kuma auren soyayya mukayi.... Kwana biyun nan bansan meke damunta ba... Amma koma meye na miki alk’awari I’ll save our marriage cos I still love my wife, l love her so much...” Ya k’arashe cikin sanyin murya....

Jinjina kai Mummy tayi cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa D’an Albarka haka nakeson ji maza ka wuce gidan Uncle Madi d’in daga asibitin zanyi waya wa Hajiya Faridan na sanar da ita aiki ne ya rik’eka a asibiti amma gaka nan zuwa....”

Bai iya amsa Mummy ba har suka ida wayar, mik’ewa yayi had’ida d’aukar wayarsa da key ya nufi duba patient d’insa kafin ya fice...

Sam baisan Siyama nada kishi haka ba, ya kamata ta fahimci yanayin aikinsa da kuma za’a iya kiransa emergency ko wani lokaci.....

A farfajiyan gidan ya iske Alhaji Madi zaune saman kujeru na shak’awata jarida rik’e a hannunsa, don haka kai tsaye cikeda risinawa ya nufi sirkin nasa kuma amini ga Daddynsa...


Daga can d’an gefe ya durk’usa kana ya soma gaida sirkin nasa.... Fuska babu walwala ba kaman yanda ya saba masa d’inba ya amsa...

Sameer ya d’anyi gyaran murya kana yace “Uncle dan Allah ayi hak’uri bana gida Siyama ta fice kuma koda na kira layinta bata d’aga ba amma In sha Allah hakan bazai k’ara faruwa ba...”

Cikeda k’osawa Alhaji Madi ya amsa da “Allah sa kada hakan ya kuma faruwa, a dinga kulawa Sameer, kasan cewa muna tsananin k’aunar Siyama kuma bamu k’aunar ganin kukanta, sanin kanka ne Sameer my children are my life, I can do anything for them ko menene, Siyama da Khalid sune farin cikin rayuwata ka fahimta...”

A hankali Sameer ya jinjina kai kana yace “Ayi hak’uri Uncle za’a kiyaye In sha Allah....”

Alhaji Maina ya kuma jinjina kai had’i da bud’e shafi na gaba a jaridar tasa kana yace “Ka k’arasa ciki ka samu matar taka....”

Cikeda risinawa ya kuma mik’ewa had’ida godiyawa Alhaji Maina kafin ya nufi sashen Ammi mahaifiyar Siyama....

“You know what sis... I think you’re been too impulsive....”

Matashin Saurayi mai kimanin shekaru 26 ya fad’i yana mai duban Addar tasa wacce ratansu shekara guda ne tak....

Pillow dake gefenta ta d’auka ta jefi dashi kana tace “You stay out of this Khalid... Ni ba sa’arka bace...”

Fitoda manyan idanunsa masu rikita ‘yanmata yayi kana yace “Oh really Sis.... Alright, fine, ni shawari kawai nake badawa, stop being so paranoid, your husband would never cheat on you, I know Sameer so well, kuma da kika aureshi kin mance wanene shi, kin mance wa kike aure...? Well, Incase you forgotten Sister, he’s a Doctor, a surgeon for that matter... Emergency zai iya faruwa ko wane lokaci kuma za’a kirashi, so sister dear you’ve to get this through your head.... Ok...” Ya k’arashe yana janyo bakin gelan kitson kalaba manya dake zube kanta...

Duka ta kai masa yayi saurin kaucewa a daidai sanda sukaji sallaman Sameer....

Daskarewa Siyama tayi had’ida lumshe idanu sakamakon jiyo k’amshin mijinta da tayi wanda tayi kewarsa a kwana guda tak...

K’arasawa Khalid yayi yana fad’in “Yauwa gwara da Allah ya kawoka, you better take your wife with you before she breaks all my bones da wannan hannun nata....”

Murmushi kurum Sameer yayi kafin ya mik’awa Khalid hannu sukai masabaha...

Bayan sun gaisa Khalid ficewa yayi ya bar ma’auratan guda biyu...

Kaman munafuki ya k’arasa cikin parlorn yana mai sand’a idanunsa kan matarsa tsan tsan k’aunarta na d’awainiya dashi....

Saida ya k’araso har gabanta kafin ya zauna shima dirshan saman babban carpet na alfarma da aka k’awata parlorn dashi..

Sameer baiyi wani aune ba ya rungume matarsa da hawaye ke gangaro mata, murya can k’asa cikin sigan lallashi yake furta “Hey it’s ok Partner I’m here now...”

Aiko kaman jira take tayi bursting cikin kuka...

Lallashinta yaci gaba da yi yana bata hak’uri.... “Honey I’m sorry... I didn’t mean to hurt you, but Partner ya kamata ki fahimci yanayin aikina, ko wani lokaci za’a iya nemana cikin gaggawa, Honey I thought you were the one encouraging me before, have you forgotten already, kin mance ke kike cewa taimakon mutane nake naci gaba da aikina a lokacin da iyayenmu suka buk’aci nayi aiki a company d’insu.... Partner I thought kin shirya ma faruwan irin hakan... Babu dare d’aya da zan fice surgery na barki ba tareda naji pain d’in barinki da nayi ba.... I love you so much Siyaam, I love you with every fiber of my being....” Ya k’arashe fararen dogayen idanunsa cikin nata hannayensu rik’e cikin na juna...

A hankali tasa hannu ta goge hawayenta kafin tace “But Partner we just got married amma ace bakada time d’ina, yaya kake tunani zanji... Shin ka mance a daren aurenmu saida aka kiraka on emergency, watanmu biyar da aure amma ban tab’a samunka complete na sati guda ba, Partner I love you and I hate sharing you with anything or anyone else....”

Dunk’ule hannunsu ya kumayi waje guda kana ya simbaci hannayenta idanunsa naga kyakkyawan fuskarta yake fad’in “I love you more Honey, and this time around I’ll make it up to you, zan d’auki hutun aiki.... Let’s go for a vocation, anywhere... Wherever you like, maybe sai muyi honeymoon d’in da bamuyi ba...”

“Are you serious Partner...?”

Jinjina mata kai yayi murmushi bai gushe saman kyalkyawan fuskarsa ba ...

Rungumesa tayi tana fad’in “I love you so much Partner...”

Khalid da Ammi ce suka sauk’o parlorn tare yanda suka tadda ma’auratan a haka...

Tuni annuri ya cika fuskar Hajiya Farida yayinda Khalid dake faman danna wayarsa ya maida dubansa ga Siyama yana mai furta “Wow look who’s smiling now... Ammi I think the couple have already resolved their problems....”

Banda harara babu abinda Siyama ke aika masa, cikin turo baki take furta “Ammi ki shiga tsakanina da yaron nan ni ba sa’arsa bace.... Besides no one ask you to interfere....” Ta k’arashe tana kuma watsa ma Khalid mugun kallo...

“If you really think so, then you should’ve resolved this at your house ba sai kinzo nan gidan kina bud’e mana sirrin aurenki ba big sis....”

“How dare you..!!” Ta fad’i sanda ta nufesa a guje...

Gwalo shima ya mata kafin ya fice daga parlorn a guje yana fad’in “Catch me if you can.....”

Ammi dake faman rabasu dole ta k’yalesu had’ida maidoda hankalinta ga Sirkinta dake durk’ushe wajen.....

***

*Kano*

*SameenaAleeyou📚*
[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_..............DA RABO_



*02*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



*Dedicated to my Trio♥*



Cikin sautin kuka dattijuwar matar mai kimanin shekaru 74 a duniya taci gaba da fad’in “Duk kece sila Halima, kece sila.... Sakaci da gangancinki yasa kika d’auki yaro k’arami mai shekaru 3 rak a duniya kika tafi dashi kasuwa bayan kinsan kina d’aukeda juna biyu kuma haihuwa na iya samunki ko wane lokaci.... Dama so kike ki b’atar min da jika kuma burinki ya cika kin salwantar da Ma’aruf bazan kuma ganinshi ba ni Hanne....!” Ta k’arashe tana mai ci gaba da kuka wiwiwi had’ida warware bakin zani tana rufe fuskarta....

Lami abokiyar zaman Mamy ce ta k’arasa ta kamo Mamani had’ida zaunarta saman sofa tana aikin ci gaba da lallashi, Karima da Dilje kuwa matan Baffah Wali da Matar Baffah Sirajo gaba d’aya yab’e baki sukayi had’ida ficewa sim sim don sun gama kallon show dama abinda yakaisu kenan yayinda Zulfa’u ta k’arasa ta rungume mahaifiyarta dake tsaye kaman ruwa ya shanye hawaye na kwaranya mata...

Aiko kaman ance Mamani ta d’ago sunayin idanu hud’u da Zulfah ta mik’e tana ci gaba da tururi take nuna Zulfah da d’an yatsa tana fad’in “Me wannan annobar take a nan... Fice mun daga d’aki tun kafin kisa wani iftila’in ya kuma auka min, wannan yarinya haihuwarki musiba ne... Da ace ba’a haifeki ba jikana Ma’aruf da yana nan ina taredashi... Fita annoba mai farar k’afa shiyasa mijinki ma ya kasa juran zama dake aure kullum na tangal tangal, haka kurum an cuci jikana an lanjama mashi annoba da sunan mata....”

Ba Zulfah kawai ba harta Mamy saida taji kalaman Mamani har cikin k’ahon zuciyarta, duk hak’uri irin na Mamy batasan sanda ta bud’i baki ta soma fad’in “A gaskiya Mamani kar ki sake jifan d’iyata da munan kalamai irin haka, Zulfa’u mutum ce kuma d’iyace kaman ko wata d’iya cikin gidan nan, sannan ko kad’an babu laifinta cikin abinda ya faru hasalima abun a tausaya ma rayuwarta ne tinda duk randa akace shekarar haihuwarta ta zagayo sai ta tuna ranace data kasance bak’in rana ma wannan zuri’a, idan bazaki lissafa Zulfa’u cikin jikokinki ba inaga bai kamata ki cireta daga cikin ahalin gidan nan ba.... Kiyi hak’uri idan kalamaina ya maki zafi......”

Banda sallallami da tafe hannaye Mamani bata komai fad’i take “Aaa Halima kin rik’a kawai ki sha d’amara ki dokeni sai nasan kin cika matar Alk’ali....”

“Mamani ni ba nufina kenan ba, Zulfa’u nake dubawa....” Ai bata kai aya ba Mamani ta fashe da kuka sosai tana fad’in Lami tayi maza ta kira mata Alk’ali a wayar Salula.....

Zulfa’u kuwa rik’o mahaifiyarta tayi suka fice daga sashen...


Zulfa’u ta dubi mahaifiyarta dake faman zuban hawaye a karo na biyu, kusanta sosai ta matsa kana ta kamo hannayenta “Mamy dan Allah ki daina kukan nan haka, na sani kina hak’uri da Mamani amma kici gaba don na tabbata akwai ranarda hak’urinki zai zame miki alkhairi don shi bai tab’a zama sharri ba....” Ta k’arashe cikeda kwantar da hankaliwa mahaifiyar tata....

Sauk’e ajiyan zuciya Mamy tayi kana tace “Zulfah shin sunsan ciwon da nake d’auke dashi cikin zuciyata samada shekru ashirin da shida, Ma’aruf d’ana ne, ni na d’auki abuna tsawon watanni tara a cikina sannan na haifeshi na kuma raineshi.....” Kukanta ya tsananta sanda taci gaba da fad’in “Shin bama wannan ba, meye naki a ciki da za’a tsangwameki a kafa maki k’ahon zuk’a, baga uwar mijinki ba baga Kakarki ba.... Zulfa’u ki yafeni dan Allah duk ni na jefaki cikin wannan rayuwa na k’unci da kika tsinci kanki ciki....”

Cikin sauri Zulfah ta rungume mahaifiyarta tana mai k’ok’arin maida hawayenta take fad’in “Mamy ki daina fad’in haka dan Allah, haka fah Allah ya k’addara kuma kada ki mance bawa bai isa yayi ma kansa abinda Allah bai masa ba, Mamy idan kina fad’in haka ni kuma yaya zanji...? Dan Allah ki dinga kwantar da hankalinki mu ci gaba da Addu’a INDA RAI DA RABON Yaya ya bayyana zai bayyana kinji koh Mamy.....”

D’agowa tayi tana kallon d’iyar tata wacce tun tasowarta ta zame mata garkuwa abin dogaro hak’ik’a duk wannan k’unci da take fuskanta tunda Zulfah ta mallaki hankalinta ta zame mata majingina abokiyar shawari, fatanta Allah ya yayewa Zulfa’u duk wasu damuwan da take ciki kama daga danginta zuwa mijinta, hak’ik’a Zulfa’u yarinyace mai tsananin hak’uri da jin k’ai, A hankali Mamy ta furta “Ubangiji ya miki Albarka Zulfa’u yasa Khausar ya kasance mai jin k’anki kaman yanda kikejin k’aina....”

A hankali Zulfah ta amsa da “Ameen Mamy...” cikin zuciyarta kuwa ma iya cewa zuban hawaye yake don har wannan lokaci kalaman Mamani basu daina yawo a kwanyarta ba...

Suna a haka sukaji sallaman Aunty Lami.....

Fuska cikeda damuwa Aunty Lami ta zauna daga gefen abokiyar zamanta Mamy tana dnnarta da bata hak’uri gameda abinda Mamani ke mata cikin gidan...

Su Nabila dake zaune parlor suna ganin Aunty Lami ta shigo suka kasa kunne donsu sam sunk’i jinin Aunty Lami, ansha basu labarin irin zaman rashin jituwa da sukayi da Mamy a baya amma yanzu wani jan Mamy a jiki take saikace ba kishiyoyi ba, harta yaran Mamy jansu take a jiki Nabila uwar ‘yan bala’i ita ke tinzira sauran k’anne nata suk’i sakin jiki da Aunty, Mamy kuwa sosai take masu fad’a tace su daina d’aukan maganganun su Aunty Dilje abinda ya riga ya wuce ya wuce, Allah yana shirya bayinsa a duk sanda yaso, Zulfa’u ce kurum takan saki jiki da Aunty Lami amma su Nabila Mas’udah da Marliya kam inaa sai Mamy tayi da gaske ma sukan shiga Sashen Aunty Lami, haka Mamy zatayita masu fad’a da nasiha tana nuna masu ko don rashin haihuwa da Allah bai baiwa Aunty Lami ba su dinga zuwa wajenta suna d’ebe mata kewa sabida sud’in sune ‘ya’yanta tinda sune ‘ya’yan mijinta.....


Daga gida kai tsaye gidan Baffah Ado dake bayansu kad’an ta biya d’aukan Khausar, Hajiya na hankince a tsakar gida ita dasu Naja’atu k’annen Hafiz mijin Zulfah, sallamanta ne ya katse masu hiran tasu, daga can bakin tabarman ta d’an durk’usa tana gaida Hajiya, kaman koda yaushe ciki ciki ta amsa mata, Naja’atu da Sahariyya kuwa kallon arziki bata ishesu ba, sanin koda zata kwana a wajen bata gaishesu ba sud’in bazasu gaisheta ba, cikin sanyin muryarta tace “ Naja’atu ina yininku...?”

Da k’yar Najah ta amsa Sahariyya kanma earpiece d’inta ta saka taci gaba da bin wak’ar dake faman tashi cikin wayar....

Zulfah bata kuma bi takansu ba ta dubi Hajiya tace “Hajiya dama nazo d’aukan Khausar ne....”

Wani uban kallon wulak’anci ta watsa mata kana tace “Lallai Zulfa’u kin rik’a.... Kin wani kwaso k’afa wani wai kinzo d’aukan Khausar, naga idan kin kaita ma Halima sai lokacin da sukaga dama su maidata, auho wato ga mayu zamusha jininta, toh bazaki tafi da ita ba, idan kin mance na tuna miki nan gidan Uban Khausar ne kuma muke da iko da gadara da ita ba Halima da danginta ba, ki tashi ki ficemin Khausar bata nan sun fita dasu Ummi.....”

Tinda ta soma magana kan Zulfah ke k’asa, cikin kwantar da murya tace “Hajiya kiyi hak’uri Babanta ne yace idan zan koma gida na taho da ita....”

“Toh nace bazaki tafi da ita ba Zulfa’u, harni zakiyiwa gada kan d’iyar d’anah, aikin banza aikin wofi ke wato ga ‘yar boko mai bautan k’asa koh... Shiyasa na k’yamaci aurenki da d’anah wayasani gantalin mi kike tafiya da sunan bautan k’asa, wllhi wllhi Zulfa’u kinji na rantse idan ina raye bazan tab’a barinki kiyi tarbiyan Khausar ba, kuma koba dad’e koba jimawa auren da Ubanninku suka k’ulla tsakaninki da d’anah sai an warware... Annoba dangin tsiya.....Tashi ki fice mun....” Ta k’arashe tana mai janye b’angaren tabarma da Zulfah ke zaune bisa wanda saida ta dungura k’asa, su Naja’atu abin nema ya samu suka kuwa kwashe da shewa....

Hawayen da Zulfah ke rik’ewa suka shiga gangaro mata, a hankali ta mik’e ta fice daga gidan farin hijabinta duk ya b’aci da hawaye.....


*SameenaAleeyou📚*
[25/11, 16:42] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_


*03*



*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



*Dedicated to my Trio♥*





A hankali ta zame hannayenta dake cikin ruwan wanke wanke kana ta saci kallon gefen da Hajiya ke zaune hankalinta yayi nisa wajen tsinewa Zulfah da zuri’arta itada yaranta su Sahariyya....

A can bakin layi ta hangeta tana neman a daidaita, cikin sauri ta k’arasa idanunta na zuban hawaye sabida tsananin tausayin Aunty Zulfah, batasan sanda ta rungumeta sabon kuka na zuwa mata ba, mamaki ya ishi Zulfah jin yanda ta rik’eta tana kuka wanda ko ba’a fad’a maka ba itama nata tarin k’uncin take fitarwa....

K’ok’arin daidaita kanta Zulfah tayi don idan k’arami nayi kai a matsayinka na babba sai kayi k’ok’arin samun k’warin gwiwa...

Rik’eta tayi kana tace “RAIHANAH ki daina irin wannan kukan kanki zaiyi ciwo.... Mai suka miki yau kuma...?”

Budurwa mai kimanin shekaru 17 da ta kira da Raihanah share hawayenta ta shigayi kana

Please Login or Register in order to submit comment