Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan a kauye yake tuni yayi aure ya ajiye irin su. Toh na rantse da abinda raina yake hannunsa sai na wulak'anta Najibu, sai ya san wanene ilyasu, sai ya gane kuranshi yabar ganin ya fara tara gemu, wallahi k'asa-k'asa zanyi da shi.”

Yana ta surfa masifa, su kuwa iyayen yaran banda koke-koke babu abinda suke yi, suna ta faman cewa sun shiga uku sun lalace ga Bintalo ta hana aje asibiti, a cewar ta idan suka je kotu za'a kai maganar kuma daga nan shige nan an lalata musu suna, gara a bari har Najibullah din ya dawo sai a dauki fansa. Da wannan shawarar sukaki kai yara asibiti sai ruwan dumi da suka sanya su aka basu magunguna Basma kuwa tamkar ba zata yi rai ba saboda an yi mata kaca-kaca abun babu kyan gani.

Ni kuwa d'aki na shige tare da zama jikina banda rawa babu abinda yake yi, na kalli Innar mu wacce idanunta ke kafe waje guda, tsoro ya kamani duk a tunani na bata numfashi saboda banga wani gurin numfashi a jikinta yana bugawa ba. Na rarrafa tare da kai hannu na tabo kafadunta, sai naga ta kalleni ba tare da tayi motsi ba. Autar mu ta shigo da gudu kasan cewar itama tana k'asa, tazo ta fad'a jikin Innar mu tana kuka, duk muka koma kanta muna tambayarta abinda yake faru da ita.

“Innar mu jini a jikin Farida, Inna kuka fa take yi tana cewa zafi, wayyo Inna Basma zata mutu tana ta yin wani abubuwa”

Magana take yi, amman jikinta sai rawa yake daga ganinta kasan bata da nutsuwa. Inna ta sake janta jikinta tana shafar bayanta, cikin dauriya da k'okarin kai zuciyarta nesa tace mata.

“Ya isa haka, ba zasu mutu ba kinji ko? Amman kema ki dena sauka kasa da daddare kinji ko? Saboda kar kema abinda ya same su ya sameki kinji Auta na?”

Ta dinga d'aga kai tana sauke ajiyar zuciya, ni kuma na koma gefe tare da sanya hannu a hab'ata ina hawaye, cikin rai na ina hango lokacin da zasu tafi siyan alawa. Kamar na gayawa Innar mu abinda suka min d'azu da nace su kawo na siyo musu, sai dai nayi shiru saboda nasan haka zata ce min karta sake jin na yi maganar cewa naga fitar su, musamman ma da yanzu suka sake dora zargi akan Yayan mu.

A ranar dai bamu samu isasshen bacci ba, saboda tashin hankali ana ta fama da Basma wacce ke suma tana dawowa. Shi kuma Kawu ila ya addabi mutane da ashariyar da yake ta dannawa Yayan mu da besan ana yi ba. Tun daga wannan abun da ya faru, sai tsana da tsangwama suka sake yi mana yawa, jikin Innar mu kuwa ya sake tsananta amman babu wanda yayi yunkurin cewar zai kaita koda chemist ne bare a kaiga asibiti. Kullum nice nake zuwa gidan su Haysam a matsayin Innar mu, ina yin aiki na dawo na gyara dakin mu nayi girki domin yanzu ko ragowar abincin ma Hajiya Husnah tace a dena bani.

*BAYAN WATANNI TAKWAS*

Bayan watanni shida jarabawar kare sakandiren mu ta fito, cikin hukuncin ALLAH takarduna duk sunyi kyau muna ta murna nida su Innar mu, sai dai babu halin ci gaba da makaranta duk da cewar ina son haka. Samari kuwa sai dai nace sambarka domin zuwa suke yi waje na neman aure amman da Kawu ila yaga saurayin yana da abin hannu sai yaje yayi min sharri, daga ranar ba zan sake ganin kowa ba. Kullum addu'a ta shine ALLAH ya bani abinda yake alkairi, Gashi duk wad'anda suke zuwa d'in irin shekarun d'in da zan iya aure ne, amman Kawu ila sai dai nace Allah ya shiga tsakanina dashi, domin duk korarsu yake cikin hikima ba tare da mutum yasan sharri yake min ba.

Kamar kullum kasan cewar tunda na fara aiki a gidan su Haysam sai Inna ta dena zuwa sai dai ni naje. Yau kam ina kare aiki na nazo zan tafi gida naga Haysam a tsaye jikin motar Abban su. Ina kallonsa amman saboda karya tsaida ni sai nayi saurin wuce shi, amman taku uku zuwa hud'u ya tare gabana yana sakin murmushi.

“Gaskiya mine, kina bani wahala duk da cewar ance abinda zaka samu baka samun shi ta sauki. Duk wannan saurin na menene?”

Na kauda kaina gefe domin kallonsa yawa yake min, sai naji duk na tsargu idan ya kafeni da idanunsa.

“Mine ki gaya min yanzu me zaki yi tunda kin karbo takardunki, Aure ko karatu?”

Nayi shiru domin bansan me zanyi ba, babu kudin tafiya jami’a, mijin auran kuma suna zuwa ana b'atani a gurin su, to mai zance dashi? Sai naji ya sake min magana.

“Kinga dai ni tafiya zanyi k'asar cyprus saboda Hajiya ta matsa kan cewar ba anan zanyi karatuna ba, wallahi mine bana son na rasaki shi yasa nake son jin menene ra'ayinki a yanzu?”

Kallansa nayi muka had'a ido nayi saurin kawar da nawa gefe. Yatsuna biyu nasa ina jan karan hancina kafin daga bisani na gyara tsayuwa nace dashi.

“Duk biyun ina so, sai dai a yanzu babu abinda zance dakai, saboda ban san abinda Allah zai shirya min ba”

“Toh mine ki tafi kiyi karatu mana? Nasan har lokacin na dawo sai kawai muyi aure ko?”

Nayi wani guntun murmushi mai cike da takaici, toh da ina da ikon komawa makaranta zan tsaya bata lokaci ne, amman dan ya raina min hankali shi zai tafi k'asar waje karatu, ni anan din ma karatun neman gagagarata yake amman yake min wannan maganar. Cikin son katse hirar domin na gaji so nake naje na huta nace masa.

“Toh zanyi.”

Na fada cikin gatse, amman abin mamaki sai naji yace.

“Good girl! Toh yanzu zansa a nemar miki inda zaki yi Jamb, insha Allahu duk inda kika samu gurbin karatu zan dauki nauyin ganin komai ya tafi da ikon ALLAH, mine karki zato ko wani tunani akan wannan abin da zanyi miki. A'a nayi miki ne fisabillahi, badan na dage sai na aure ki ba. Kije ki fara shiri zanzo muje kiyi registration din Jamb din idan an fara.”

Bansan tun lokacin da na bud'e hakora nake faman farin ciki da murna dajin wannan kalaman na Haysam ba, sai naji kaso d'ari cikin kin da nake masa ya ragu sosai, a yanzu ji nake tamkar na rungumesa dan murna. Cikin jin dadi na dinga zuba masa godiya har sai da dakan shi ya gudu cikin gida, sannan na juya da sauri nima nayi gidan mu dan zuwa sanarwa da Innar su. Koda naje na bata labari itama tayi murna da farin ciki, ta dinga sanyawa Haysam albarka tamkar yana wajan. Haka na dinga baza kunnuwa dan naji lokacin da za'a fara Jamb din, ai kuwa lokaci nayi Haysam yayi min magana, aka yi komai aka gama.

Kaduna mukaje muka zana jarabawar jamb d'in mu tare da rakiyar Haysam da wata kanwar abokinsa wacce itama zata zana jarabawar. Bayan wata biyu dai komai ya fito. Alhamdulillah na samu gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake nan Zaria. Wato ABU ZARIA. Lallai ALLAH qadirun ne ala manyasha’u, Domin fannin dana keso shina samu, wato digiri a fannin zallar turanci. B.A ENGLISH. A dai-dai wannan yanayin ne shima Haysam aka kammala shirye-shiryen tafiyarsa karo karatu, shima kuma sai da ya tabbatar ya bar komai da zan tafi makaranta ta a hannun babban abokinsa mai suna Suraj. Lokacin da yazo yi min sallama sai da naji tausayinsa, naji tamkar nayi masa alkawarin zan auresa, sai dai idan na kalleshi na kuma tuna shekarunsa da kadan suka wuce nawa, gashi in mace ce ko a yanzu za'a iya yi min aure, sai naja guntun bakina nayi shiru ina binsa da addu'ar fatan alkairi.

Tunda ya juya ya tafi bai sake waigowa ba, shikenan ko sai yaushe zamu sake had'uwa? Naji zuciyata nata tambaya. Yana da kirki, yana sona da gasken-gaske, sai dai harga ALLAH Haysam yayi min yarinta a matsayin mijina, bana son nayi aure na raina miji na, nafi son na auri wanda ya girme ni, wanda kallona kawai zai yi idan nayi laifi na gane abinda yake nufi, ba wanda zai min kallon warning ba nayi zaton sa'ana ne ba. Na koma gida ina murmushi domin tuna kalmarsa ta karshe da ya gaya min.

_''Kisa a ranki cewar Namiji baya kad'an mine.''_

Daga haka naci gaba da harkokina, duk lokacin da ake neman wani abun na makarnta Suraj zaizo har gida ya sanar dani, da haka har lokacin fara karatu na Yayi. A satin da zan fara karatu na debo yan kaya na duka na wanke su tas. Suna bushewa na hada su a leda, Hijabi na na zura na dauki yar ledar kayan,

“Innar mu bari naje gidan su Fadila na gogo kayan nan. Kinga na huta idan zani makaranta kawai sawa zanyi.”

“Hakan yayi! Allah yasa ki fara a sa’a. Kar dai ki kai yamma.”

“Ameen Innar mu! In Sha Allahu bazan jima ba.”

“Yaya sai kin dawo.”

Autar mu ta fada tana cigaba da cin ragowar diddigar awarar da Baba Usaiba ta bata.

“Yauwa autar mu. Kar fa kije ko’ina.”

“Tam Yaya.”

Ficewa nayi daga daki, Tsakar gidan mu babu kowa da alamun suna ‘daka, Gidan su Fadila na nufa zuciya ta ‘k’al da ita, Gaisawa mu kai da Aunty Nana ta amsa ciki-ciki tana yamutsa fuska. Dakin Fadila na shiga bakina dauke da sallama, Tana gani na ta mike muka rungumi juna.

“Aminiyas yanzu nake zancen ki a zucia ta.”

“Allah sarki tawan! Allah yabar mu tare har gaban abadan.”

“Ameen”

Ruwa ta kawomin da cincin. Ci nayi na rage sauran aleda zan kai wa su Innar mu. Dan bama iya cin abu bamu ragewa juna na komai kankantar sa. Cire hijabi na nayi na sauka kasan carpet.

“Tawan ‘dan bani ayon din gugar ki na goge kayan nan.”

“Tafiyar tazo ne? Oh yanzu shikenan sai mun ganki.”

Murmushi nayi ina yayyafa ruwa a shaddar da Yayan mu ya dinka mana shekarun baya, Maje gaba akai mana shi yasa sai yanzun tayi cif cif ajiki na.

“Haba tawan ai In Sha Allahu had’uwa ba zata gagara ba. Da yardar Allah kuwa, Ga kuma waya ma zamu dinga hirar mu.”

“Ai na taya ki murna Aminiyas, Duk fa cikin sa’oin mu da mu ka zana jarabawar jamb babu wanda yaci, Amma ke Allah ya datar dake kinci har kin samu admishon a fannin da kike so. Ubangiji Allah yasa ki fara a sa’a Aminiyas.”

“Kinsan komai rubutacce ne daga Allah tawan. In sha Allah kuma naku yana nan tafe.”

“Ameen ya Allah! Ya labarin Yaya kuwa?”

“Yana kano abunsa inajin yanzu ko yana shekarar karshe ta kammala N.C.E d’insa.”

“Masha Allahu! Ubangiji Allah ya kara bashi nasara ameen.”

“Ameen..”

Haka dai mu kaita yan hirarrakin mu har na kammala goge kayan nawa dama ba yawa ne dasu ba. Na zura a leda ta raka ni har gefen layin mu. Na karasa gidah baki na dauke da sallama.


*GIDAN MATA TARA*

Zaune Bintalo take a mattakalar bene itada Innatuwa matar Kawu Khamis. Gefen bandaki kuma layi akai, Su biyar cas suna jere jiran wanda ya shiga ya fito. Sallama na sake yi a karo na biyu ganin babu wanda ya amsa wacce na fara yi. Nan ma shiru su kai suka cigaba da hirar su. Sama na haye abuna ganin yadda suke bin ledar hannu na da kallo.

Baki na dauke da sallama na shiga dakin mu. Innar mu na kishingid’e tana jin rediyo, Autar mu kuma tana yar carafke da duwatsun ta a kusa da randa. Zama nai a kusa da autar mu ina bubbuga baya na bayan na ajiye ledar kaya na akan katifa,

“Innar mu sannu.”

“Sannun mu! Har kin gogo?”

“Eh wallahi. Ai dake ayon din nasu mekyau ne kuma wutar da karfi.”

“Masha Allahu! Allah yabada sa’a.”

“Ameen”

Kayan jiki na na rage, Mun dan taba hira da su Innar mu kafin na mike na dora dumamen tuwon da matar soja taba mu jia. Munci munyi nak muka dasa hira har lokacin bacci yayi bacci ya dauke mu.

••••. •••••. ••••. ••••.

Dan kudin da Gwaggo Aminatu ta bayar aka kawomin da shi na shiga kasuwar layin mu nayi yan saye sayen makaranta dai dai namu na talakawa. Shagon gali na biya don auno omo dan aune. Yana zaune a benci ya dora wata yarinya a tsakiyar cinyar sa. Na dubi yadda ya cakwaikwaye ta yana mata wasa sai bangala daria take. Sai dana dubi yarinyar sosai na gano yar gidan Haladu Mai Guga ce.

“Humaira!”

“Na’am.!”

“Tashi kije gidah abban ku na kiran ki.”

Na fadi haka don kawai ta tafi gidah. Hankali na sam bai kwanta da Gali ba. Kad’a Kai tayi ta tafi gidan su da gudu.

“Matar Manya!”

Gali ya fada yana lashe lebe. Harara na wurga masa ina mika masa dari biyun hannu na,

“Ungo bani omo rabin rabi da sukarin hamsin da bota yar leda guda biyu.”

“Yanzu kuwa Hajjaju! Dan Allah ki dinga murmushi kinfi kyau.”

Ya karasa fada yana mikomin, Wafta nayi na fice abuna. Gidan matar soja na biya na mata sallama sannan na wuce gidah kai na tsaye.

*GIDAN MATA TARA*

Ina shiga naja baya nai turus, Domin gaba d’aya ahalin gidan mu rankataf suna tsakar gidah, Kawu ila ne a tsakiyar su sai zunduma ashariya yake wai an balla masa hannun bokitin zaman sa, Baki na dauke da sallama na shige zan haye sama ya kira sunana cikin kwakwazo,

“Ya ki nan. Dan uban uban ki zo ki gayamin wane iskancin ki kai aka samo miki jami’a har an biya miki zaki fara zuwa.? Kaga shegun yara yan iska wanda basu san halacci ba..”

“Jami’a? Jami’a fa kace ilyasu.! Tab sittin ta ubangiji zina take aikatawa. Uban waye ya biya mata?”

Bintalo tafada tana kururuwa, Hade da buga zanin ta...


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_*


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(TAKU NA BIYU)_


ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE, ME SO DAN GIRMAN ALLAH YA BIYA YA KARANTA HANKALI KWANCE😘❤️

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*1️⃣7️⃣*


“Zina fa ki kika ce, Kutsin ubancan kayya kai! Ke Bintalo kiji tsoron ALLAH.”

Cewar Baba Usaiba da ta fito daga kan layin bandakin da suka jeru, Bintalo taja tsaki tana watsa hannu baya,

“Yo karya akai? Bata yinne? A wannan zamanin wane garan saurayin ne zai dinga yiwa budurwa hidima haka? Sittin ta ubangiji sai dai wanda bakin uwa ke binsa.”

Baba usaiba ta ja guda ta saki tana buga zanin ta,

“Ahayye kayya kai, Yo inda haka ne Alawiyyah ma da Hinde bin mazan suke d...”

Bata karasa ba Bintalo tayi kukan kura ta cafki wuyan ta, Tuni fada ya gaure a tsakani, Kawu ila yaja bokitin zaman sa ya zauna yana saka ce baki. Kankace me? Gida ya kara taruwa da mutane, Almajirai da ‘yayan ma’kota duk sun shigo kallo, Baba Usaiba sai ‘daga Bintalo take sama tana naka ta da ‘kasa, Dariya ta tahomin na danne kawai nayi sama ina godewa ALLAH da hakan tafaru, Da tuni Kawu ila ya dinga sheganta ni. Duk kuwa da nasan yanzun ma ban tsira ba, Da sun gama casuwar zai kirawo ni ya dora daga inda ya tsaya.

Daki na shiga da sauri ina dariyar da tun d’axu na rike ta, Innar mu dake jan carbi a gefe ta dago ta dube ni,

“Dariyar me kike ne?”

“Bakyaji na da Kawu ila yanzu?”

“Uhm uhm! Na dai jiyo hayaniyar sa d’axu yana kiran yaran gidan nan ‘d’ai dai kan an karya masa hannun bokitin zaman sa.”

“Ai gwara da aka karya.”

Na fada ina murmushi, Dakuwa Innar mu tayi min na zauna agefen ta, Autar mu na gefen katifa tana sakin munshari domin ita akwai bacci idan ta samu waje.

“Innar mu ga yan kayayyakin fa.”

“Masha Allahu! Sai ki harhada su waje d’aya kada ki manta wani abun”

“Toh! Ga wannan makilin ne na siyo mana naga namu ya kare, Wannan kuma gari ne na auno shima kwa sha idan babu abinci, Ga gawayi shima na siyo da sauran canji.”

“Kai ai da abun makarantar kika siya, Toh angode Allah ya saka da alkhairi, Allah kuma ya baku sa’ar karatu. Ameen”

“Amin Innar mu.”

Mi’kewa nai na shiga harhada yan kayayyaki na a leda bacco, Dama ace akwai akwati da aciki zan zuba komai nawa, Ina gama hadawa na kara kintsa dakin mu na tattare komai. Waya ta na dakko na shiga daddan nata ina goge sakonni mara sa amfani, Shafi’u Gangare shine sunan da nazo kan sa a wurin shigowar sak’onni. Bazan manta ba shine saurayin da nayi na karshe wanda Kawu ila ya tare shi bansan wane irin sharri gaya masa akai na ba amma tundaga ranar bai sake takowa inda nake ba. Sakon na kara karantawa,

“Ashe haka kike? Tir da halin tsatson ku wallahi. Meyasa ba zaki gayamin gaskiyar lamari ba? Ki farga ki canza yanayin rayuwar da kika dora kan ki, Shine mutinci.”

Sake karantawa nai ina cizan lebe na na kasa, Toh shin wane sharrin Kawu ila ya gaya masa akai na? Me hakan ke nufi? Shin *ZATON* da yake ganin an same mu ta haka gani yake kenan fasikanci nake aikatawa? Ajiyar zucia naja na sauke. Na goge sakonnin dukkanin su, Domin duk tarin su akan hakanne, Kowanne da kalar abun da yake rubuto min. Goge nambobin su nai gaba ki d’aya na ajiye wayar a gefe ina tunanin ina mafita?

“Batoul! Batoul! Batoul!”

Kawu ila ya shiga kwararawa suna na kira, Mi’kewa nayi daga kwanciyar da nai ina mika. Hijabi na na zura na sauka kasan. Shi kadai ne a kasan sai yara dake wasa a gefe, Da alamun an gama fadan kowa ya watse. Na dubi Basmah dake kusa da Buhari almajiri ko pant babu a jikin ta. Kuma mahaifiyar ta na kallon ta domin su basman na daga gefen kofar dakin. Ita kuma Hajarar na kishingid’e a wajen kofar tana fiffita. Girgiza kai na nayi cike da Takaici,

“Kawu gani..”

“Ina fa! Ga ni dai, Basarakiya ranki ya dad’e.”

Murmushi nai jin bakar maganar da ya yabamin,

“Kawu bacci ne yafara dauka ta sai daga baya naji kiran ka.”

Yamutsa fuska yayi yana sosa hancin sa, Ya curo tasono yana cilloshi waje na, Naja gefe karya fadomin akai, Kawu ila ba karamin katsami bane. Kuma nasan da biyu yayi haka. Ban gama maganar da nake a zuci ba na jiyo shi,

“Shegiya mai idon jemagu yanzu ke harnan kyankyami na kike? Ke da ke aikata zina kina bawa samari jikin ki suna biyan ki kudi? Tasono kuwa uban kowa yana ‘kwakwulewa, Shegiya almura da ido tsuru tsuru.”

“Allah ya baka hak’uri Kawu, Ba kyankyamin ka nake ba.”

“Oho dai! Zaki gayamin uban da ya biya miki makaranta ko kuwa?”

Ajiyar zucia nayi, Na cire tagumin dana zabga,

“Kawu wallahi ina ranar da nake ta cemaka zanyi magana da kai kaki saurara ta?”

“A ubanki? Yaushe akai haka?”

“Ranar da zan tafi gidan aiki da safe kwanaki?”

Tsaki yaja yana wurgomin harara. Nayi murmushi kawai ina cigaba da lankwasa hannu na kafin na cigaba da cewa,

“Toh sai na samu Kawu Ishaq na gaya masa cewar an samamin gurbin karatu a jami’ar Amadu bello dake nan zaria.”

“Uban uban wanda ya sama miki karatu nake so inji. Yanzu ke har kin isa ki je jami’a? Dan uban ki agidan nan wa kika ya shiga jami’a?”

“Kawu naga su Hinde suma sunyi jamb din basu ciba..”

“Na had’aki da jamb din na gunguri uban uban ki. Zaki gayamin wanda ya biya miki karatun ko sai na lallasa ki awajen nan?”

“Kawu Haysam ne ya samamin..”

Sallallami Kawu ila ya shiga rafkawa yana tafa hannaye, Alokacin Bintalo ta fito daga dakin ummita da alamun lab’e take dama. Zaro idanu tayi tana bubbuga kafafun ta. Cikin tsantsar kidimewa ta rafka salati tana tafa hannuwa,

“Wannan yaro ya kawo kansa, Sittin ta ubangiji sun kai sunan sa an magance shi. An daiji kunya wallahi.”

Nayi murmushin yak’e kawai ina jiyo su suna aibata ni, Kawu ila ya kwaso rantsuwa ya dire yana wallacewa kan babu jami’ar da zani, Gaba d’aya sai sauran y’an gidan suka firfito, Ana kacaccala maganar zuwa na jami’a da bada jiki na da nake yi wai maza na amfani dani.

“Yo dubi jikin ta mana, Duk ya saki alamun ana tattabeta.”

Cewar Bintalo tana dungure min kai, Na dubi jiki na bansan sanda na saki wani marayan kuka ba, Baba Usaiba ta sakko da gudu tana karkadawa Bintalo hannnu,

“Kutsin ubancan kayya kai, Kiji tsoron ALLAH Bintalo, Yo du gidan nan akwai wanda ya kai Alawiyya da Hinde sakakken jiki ne? Nonuwa sun rafke suna reto alamun a...”

“Sittin ta ubangiji sai nayi maganin ki yau Usaiba..”

Bintalo ta lailayo ashariya ta d’urawa usaiba, Itama ta lailayo ta rama, Sai ruwan ashar ne ke zuba daga bakunan su, Na goge hawaye na ina takaicin irin rayuwar gidan mu.

”Ke de Usaiba ki fito kice kawai bakin cikin goshin su Alawiyya kike, Yo Idan ba haka ba ke meye naki aciki? Ta kira Larai ne ko Talatuwa da zaki dinga shiga abinda babu ruwan ki.”

Cewar Ummita matar Kawu ila tafarko, Wato aminiyar Bintalo kaf gidan mata tara. Baba usaiba ta kece da dariya tana kururuwa,

“Kutsin ubancan kayya kai! Wa zan wa bakin ciki? Alawiyya ko Hinde? Duk cikin su babu budurwa, Gaba d’aya sun gama yawo a kwararo kaf garin nan babu wanda bai sani ba, Yaran da ake dibar su suna fito Kaduna.”

Usaiba tafada tana sakin gud’a. Bintalo ta shatalo kafarta ta fad’i a kasa ta hau ruwan cikin ta, Dake kakkarfa ce Usaiban tuni ta janyota itama ta maida ta kasa ta shiga dukan ruwan cikin ta. Sauran suka sa dariya. Dai dai shigowar Gwaggo Aminatu dake kaduna. Tana gaba yaran ta biyu na biye da ita abaya, Dayan yana rike da madaidaicin akwati, Dayan kuma ya rik’o wasu ledoji shake da kaya, Suna ganin ta suka dena fadan, Ta shiga bin mu da kallo gaba ki d’aya tana girgiza kai,

“Gidan Mata Tara kenan, Ashe har yanzu baku girma ba? Fada ai an barwa karnuka su dinma basu cika yi ba.”

“Yaya sannu da zuwa!”

“Sannun mu ilyasu, Kana nan dai da nacaccen bokitin nan? Dan Allah ka jefar dashi haba!”

Gwaggo Aminatu tafad’a tana firfita da gefen mayafin ta, Daria kawu ila yayi yana sosa keya bai ce mata komai ba, d’aya bayan d’aya manya da yaran gidan mu muka shiga gayda Gwaggo Aminatu. Amsawa tayi cike da fara’a.

“Ina wuni Ya Naseer? Ina wuni Ya Faysal?”

Na gaishe da yaran Gwaggo Aminatu wanda ke tsaye suna kallon mu. Ya Naseer shine na biyu a yaran ta shi kuma Ya Faysal na hud’u ne, Sauran duk mata ne, Biyu sunyi aure, Biyu suna karatu. Amsawa su kai da fara’a kowanne a fuskar sa,

“Batoul meya faru na gan ki a tsugunne kuka kike yi?”

“A’a Gwaggo! Abune ya fadamin ido na.”

“Karya take yi, Yaya yarinyar nan da kike gani fasika ce.”

Salati Gwaggo Aminatu taja tana kallon Kawu ila,

“Haba Ilyasu? Kasan me kace kuwa?”

“Toh Yaya jikin ta take baiwa wani yaro dan gidan Alhaji Kabeeru Mai Wafa shine bayan sun gama tambadancin su ya nema mata makarantar jami’a.”

Tsaki Gwaggo Aminatu tayi tana girgiza kai, Cike da bacin rai tace dashi,

“Dan ALLAH ilyasu ka dinga yiwa bakin ka linzami, Maganganun da kake fada sam basuda ce ba, Kai sauri ka roki gafarar ubangiji da ta yarinyar nan. Shin me zaka gayawa ALLAH ranar lahira? Shi fa *ZATO* ba abune mai kyau ba, Kuma har gaban abadan inde ba gafarar yarinyar nan ka roka ba wallahi sai ALLAH ya kama ka da aibata tan da kake yi. Maganganu marassa dad’in ji, Sam basu da kan gado, Shi fa *ZATO* wanda kakewa kallon haka daban me aikatawar kuma da baka ganin

Please Login or Register in order to submit comment