Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu itama taje.”

Cewar Bala d'an kawu khamis. Innatuwa ta saki murmushi tana taka rawa yatsunta biyu a saman hancinta ta matse shi tana sakin gud'a.

“Ahaiyeee ragas ragajab jab, haihuwa mai rana, kaji irin yaran albarka. Balele Allah ya tsundumaka a aljanna yau kam ka fito dani wallahi.”

Wannan ya sake kular da Bintalo ta dinga harbin kafafuwan su Hinde dasu Hauwa'u tana dankara musu zagi.

“Ke Hafsatu zo karbi kudin mota kema kije a madadi na tunda ba zan samu damar zuwa ba. Nima jiya da daddare malam Hamza ya bani rancenta.”

Hafsatu tayi murmushi aka fara taku cikin gadara aka nufi gurin miji. Kawu Dawood ya karkace ya zaro kud'in aljihunsa naira d'ari biyar da talatin, ya mika mata d'ari biyar d'in ta karb'a tare da zurawa cikin jakarta tana yi masa godiya. Haka suka runtuma suka tafi mota sai dai driver yace musu tunda basu cika motar ba zai tsaya ya kara dibar wasu, kawu khamis yace to dan yasan idan ba hakan aka yi ba sai an karbi kudi da yawa a gurin su kuma babu wanda zai bayar. Suna tafiya Inna da Yaya Najeebu suka fito suma, can sukaje suka shiga mota suma suka tafi. Sai da aka je can suka had'u kawu ila kuwa ya dinga surfa masifa wai inna ta raina shi amman zai gyara mata zama, tayi dariya kawai bata ce komai ba...

*2018*

*GIDAN ALH KABEER MAI WAFA*

Haysam ne ya shiga zagaye a dakin sa. Hannuwan sa saqale da bayan sa. Lokaci zuwa lokaci yakan sauke gwauron numfashi yana cije lebe. Kada kai yayi ya fita daga dakin yana jin karfin abunda zai aikata. Parlorn mahaifiyar sa ya nufa. Tana hakimce a kujera me cin mutane uku. Wata yar matashiyar yar aikin ta na matsa kafafu. Tana hango sa ta fadada murmushin ta tana rage volume din tv,

“Ka tashi?”

“Na shi Umma. Barka da safiya! Nazo da asubah ai naga baki fito ba.”

“Barka dai dan Umma. Alhamdulillah wallahi. Eh yau ban fito parlor ba dake an zabga sanyi da asuba. Ka tashi lapia?”

“Alhamdulillah Umma..”

“Meya same ka? Naga idanuwan ka sunyi jajir. Wani abun ne?”

Kallon mai aikin tasu yayi ta gefen ido. Hajia Husnah ta janye kafafuwan ta,

“Je ki hanziyya. Zan kiraki anjima”

“Toh Hajia.”

Tana fita ya koma kusa da mahaifiyar sa yana marairace murya,

“Ummah...!”

“Dan Ummah! Meya faru ne yau?”

“Ummah ina cikin wani hali Umma, Dan Allah ki dubi zance na. Wallahi ina matukar sonta Ummah.”

“Wai kake so ne Haysam? Kanata magana a baibace. Ka fito ka fadi meke damun ka. Yar gidan wanene taki ka? Uhm?”

“Ummah tace naje na nemo yardar ki tukunna..... Ummah Pls ki amince. Banason rasa ta.”

Hajja hUsnah ta cire tagumin data xabga tana kallon Haysam daya birkice. Wacece ta kuncewa kan danta noti oho. Muskutawa tayi ta matsa.

“Ban fahimce ka ba Haysam. Wacece tace ka nemo yarda ta.?”

“B..Batoul..”

Ya karasa fada yana in’ina gaban sa na dukan tara tara. Wani banzan kallo Haj Husnah tayi mai hade da shure kafar sa dake kusa da ita,

“Matsa kafin na sharara maka mari, Ashe har yanzu kai sullutu ne? Shashasha, Sakarai wanda bai san ciwon kan sa ba? Kai wai dan girman Allah wane irin bakin asiri suka maka ne uhm? Me za kai da wannan kaskantacciyar yari...”

Bata karasa ba ya rik’o kafafunta yana zubar da hawaye,

“Ummah Ki duba zance na. Wallahi Wallahi Inason Batoul. So mai tsanani ummah. I can’t take it shiysa nazo na gaya miki. Zuciya ta tana rad’ad’i ummah. Ummah karki manta yarinyar nan ma yanzu tafasa mu aikin yi. Allah ya canza musu rayuwar su. Inason ta a haka ..”

“Toh sallamamme! Sun gama da kai ai. Har kake kallon tsabar idanu na kana gayan Allah ya canza musu rayuwar su? Dan uban ka ko farcen uban ku sun dakko a kudi ne? Ana nuna ma gabas kana ga yamma?”

“Ummah dube ni mana har yanzu bansamu aiki ba Ummah. Bakya ganin hakan ma wata jarabawa ce?”

“Zaka dena kalaman nan ko sai na hanbare ka? Kai bakada zuciya ma Wallahi. Yarinyar data gama watsewa a jami’a har biyu? Nan aka kawomin zancen ta samu lecturing a jami’ar dai. Tun muna sheda juna ka rabu da figalalliyar yarinyar nan.”

“Ummah Pls..”

“Sannu bature. Na hada ka da pls din na gungurin uban ka. Banda rai ni da kaskanci me zaka debo a auren ta? Wallahi nasan layi layi ana nuna ni ga sirikar matsiyata. Tashi kabar mun waje.”

“Ummana ki yafemin. Dan Allah ki barni na auri Batoul.”

Yatsa Hajia husnah tasa a baki ta ciza tana dankara masa harara,

“Tashi ka bani waje sallamamme. Kayi duk abunda kaga dama.”

“Allah ya baki hak’uri. Allah ya huci zuciyar ki. Ki dai duba zance na Ummah.”

Yana gama magana ya mike ya fice daga parlorn yana dafe zuciar sa dake masa zugi. Yarasa wane irin kiyayya mahaifiyar sa ke yiwa Batoul. Yana fita tabi bayan sa da harara tana jan tsaki. Tacika tayi fam tamkar zata fashe. Cike da bacin rai take maimata,

“dole ka sakko daga doron *ZATON* da ka hau wallahi. Wacace Batoul? Allah ya sawake na hada zuri’a da matsiyata.”

Shi kuwa Haysam takalmi yasa ya fice daga gidan. Motar sa ya hau yayi layin su Batoul. Ata’kaice gidan su ma yai niyyar shiga sai dai ayita ta kare. Akan titi yagano ta tana tafiya. Sanye cikin bou-bou riga red and black. Ta yafa mayafin ta red. Tayi kyau kwarai dagaske. Sai zambada sauri take duba agogo. A gefan ta ya tsaya bayan yabude glass din motar. Ya dan sunkuyar da kansa yadda zata ganshi ta kuma jiyo shi,

“Yanmata na... Shigo na kai ki.”

“Ah Ya Haysam!”

Budewa tayi ta shiga bakin ta dauke da sallama,

“Ina kwana Ya Haysam? An tashi lapia?”

“Lapia qalau Mine..Muje ko?”

“Muje..”

Na fada ina mai duba takardun kan cinyata. Questions da zanyi submitting a dean office na exams din da za’a fara jibi. Lokaci zuwa lokaci Haysam ke kallo na yana mai cigaba da tukin da yake yi,

“Kinyi kyau mine..”

“Nagode Ya Haysam.”

“Yaushe zaku tashi nazo na dauke ki.”

“Kakka damu Ya Haysam. Nagode wallahi”

“No ai ni nayi niyya.”

“Kamar 5 haka IN SHA ALLAH!”

“Okay Mine. Ki jira zanzo IN SHA ALLAHU.”

Kada kai nayi ina duba agogon hannu na. Hira muke tabawa har muka karasa shiga gate din school din sannan ya rage tafiya yana gyara murya,

“Ki cigaba da sanyamu a addua Mine. In sha Allah kin kusa zama officially Mrs Haysam.”

Kallon sa nayi kawai ina kakaro murmushi. Rausayar da kai yayi yana kallo na,

“Ko bakiji me nace ba u..Uhm?”

Murmushi na sake yi wanda hushirya ta ta bayyana,

“Hajian ku ta yadda ne?”

“Sure! Why not? Tabani zab’i”

Haysam ya fada yana rintse idanu. Ya sake marairaicemin yana rage sautin muryar sa cikin so da kauna,

“Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada Mine. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i. I love you pass my mind beyond my soul. My Batoul..”

Yaja sunana cikin wata siga. Rufe fuska ta nayi ina murmushi. Ya kawoni har bakin office dina.

“Nagode Ya Haysam.”

Na karasa fada ina kokarin bude kofar najita a datse. Kallon sa nayi ya kara rage murya yana kallon cikin idanu na. Kunya ta isheni ga dalibai na wuce wa,

“You are the most beautiful woman in my life and it is the reason why I want to spend the rest of my life with you. No one can stop me from loving you. I am with you my lovely girl. I am with you my love all my life...”

Mubeen dake zaune a kofar office dinta tun d’axu yana jiran zuwan ta. Ya mike hango su da yai ta cikin motar tana dasharewa wani hakora. Ga dukkan alamu kuma saurayin ta ne. Taune kasan lips dinsa yai yana rintse idanu. Sai kaiwa da kawowa yake yi taki fitowa daga motar. Alokacin kuma Haysam ne ya isheta da kalamai sai ta bashi amsa. Ajiyar zucia ta sauke tana kallon waje wanda idanun su suka sarke da Mubeen ya zabga mata harara yana cuno baki.

“Babu komai Ya Haysam. Na..Na..Na amince.”

Haysam dadi ya cika shi ya kifa kansa akan steering yana kallon Batoul cike da soyayyah yama kasa magana. Ita kuwa futowa tai da sauri daga ciki har tana tuntub’e ta shiga office dinta ko kallon Mubeen batai ba. Ya bita office din yana mai rufe kofar. Kallon Misklin yaron nan nai ina ajiye kayan hannu na,

“Ya akai..?”

“Ayana....”

“Ayaba.?”

Na fada ina kallon sa. Girgiza kai yayi yana sauke ajiyar zuciya,

“Ina kwana..?!”

“Lapia lou”

Wata Ajiyar zuciar ya kuma saukewa na kalle shi naga ni yake karewa kallo. Shi kuma a lokacin so yake yace ta goge jambakin da ya hau saman hancin ta ya kasa. Gadan gadan ya nufe ta ta ja baya tana zare idanu. Handkerchief ya ciro a aljihun sa yana kallon idanun ta. Ta kasa motsi sai raba idanu take. Murmushi yai. Ahankli yasa handkerchief din ya goge mata saman hancin ta. Ta kalle shi tana zare idanu. Nuna mata kasan handkerchief din yai yana murmushi,

“Kar ka sake yi min haka.”

“Sorry Ma'am.”

Ya fad'a a hankali. Daga kai nayi ina kallon sa. Mekyau dashi ga nutsuwa acikin sauran students. Murmushi ya min yana zuge zip din jakar sa. Wani kwali ya ciro ya ajiye a gaba na. Kallon sa nayi alamun Ya haka? Lumshe idanu yai ya bud'e su a kaina, a hankali mai makwan ya bani amsar tambaya na sai ji nayi yace,

“You luk breathtaking Ma!”

“Lower your gaze.”

Murmushi naga ya sake yi. Ya zauna akan kujera yana zubamin idanu. Kasa jure kallon sa nayi na dubi gefe. Sake jiyo shi nayi yana cemin,

“I know you have a busy day ahead of you, but could you add me on to your to-do list?Pls Ma.”

“Me zan maka ne. Meye baka gane ba uhm?”

“Ma waye wanda ya kawo ki?”

“Banda personal questions..”

“Wai.. So pestiferous!”

“Kace me?”

“Nace kinyi kyau..”

Nama rasa amsar da zan bashi,

“Toh Nagode tashi ka tafi.”

“Mah dan Allah zan kai ki gidah yau.”

“No thanks.”

“Why??”

Mubeen ya bani amsa a marairai ce. Naja numfashi kawai na dan juya baya ina gyara gyale na saboda office din dean xani. Har nayi kofa ya riko mayafi na yana girgiza kai,

“Pls ki kara gyarawa yana yayewa mayafin.”

“And what does that have to do with you..?”

Ajiyar zuciya na sauke na gyara mayafin ina jinjina karfin hali irin nashi.

“Zan kai ki gidah Pls.”

“Nace a’a. Ni fa malamar kace meyasa ka rena ni ne?”

Sunkuyar da kansa kasa yayi. Ya girgiza kai yana kokarin saka gwiwoyin sa a kasa. Idanuwan sa sun kawo ruwa. Na bud'e baki ina kallon ikon Allah.

“please mah.''

“Meye haka? Tashi karka tsugunna meye haka? Mena maka uhm? Afuwan please.. wanda zan aura ne zai zo ya d'auke ni.”

“Kika ce me?”

Ya tambaye ni da karfi a tsawance😮 Gaba d’aya ya hautsine. 'Na shiga uku' na furta a hanakali ina ja da baya. Har bakin kofa muka kai a haka. Na tukwikwiye jiki na sai rawa yake. Domin ya fini tsawo ba sosai ba. Sai yai min rumfa ina jiyo bugun zuciar sa. Ahnkali cikin wani irin yare na jiyo sautin saukar numfashin shi akan fuska ta yana cewa,

''Dan Allah, dan girman Allah kibarni na kai ki gida.''

Bangajeshi nai zan fita ya rikomin yatsu yana kikkifta min ido. Cikin sarkewar harshe yake cewa,

''Wallahi bazan miki magana ba har muje mah, please mah ki taimaka dan Allah.''

Gaba d’aya ji na da gani na sai suka dauke na yan wasu dakikai...Kujerata na koma na zauna ina sauke numfashi, cikin raina ina cewa yau nayi gamo, daman ina jin labarin yadda wasu students d'in suke raina lecturers d'insu mata, shi yasa yawanci ba'a fiye bawa 'yan mata aikin koyarwa ba yawanci sai masu aure da zawarawa. Balle ni da nake d'anya sharaf, kuma babu wanda zai ce nakai wad'an nan shekarun. Yana can inda na baro shi a tsaye yana kallon k'ofa bai juyo ba, nima bance masa ya juyo ba domin banga amfanin yin hakan ba, nace dashi.

“Ban san me yasa kake yi min hakan ba, amman koma menene kai ka sani a cikin zuciyarka. Kabar yi min hakan domin a koma menene ina gaba dakai ya kamata kasan hakan.”

Ko motsawa Mubeen beyi ba, sai ma jinjina kai da ya dinga yi, daga baya ma sai ya fita daga office d'in ba tare da ya kuma ce min komai ba. Ko'a jikina domin ni kaina jira nake ya tafi yaban gurin dan banga abinda ya had'a mu ba bare ya takura mini. Tashi nayi na wuce office d'in Deen nayi submitting questions d'in exam, yana karb'a muka d'an yi magana dashi sannan na koma nawa office d'in. Karfe biyar nayi har na fito zan tafi naga ashe Haysam yazo, na saki murmushi tare da nufar motarsa na bud'e na shiga. Ashe duk akan idanun Mubeen wanda tun zuwan motar Haysam yaji gabaki d'aya hankalinsa ya kuma tashi, ya kasa tabuka komai ji yake kamar ya fashe da kuka, yana ji yana gani muka wuce dan yasan ko ba Haysam ba zan shiga motar su ba..

..
Kunji shiru ko? Afuwan wlh banida Lpy yanzu ma daurewa nayi. Allah ya bamu Lpy mai dorewa AMIIN👏🏻
-
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_[8/21, 7:28 PM] Nadady: *34*

*NANA HAFSAT*

Alhamdulillah komai cikin tsari da lapia aka fara gudanar da jarabawar zangon karatu na farko na daliban dake nan jami’ar Amadu bello. Ranar Friday yan level one zasu zana jarabawa d’aya daga cikin courses biyu da nake daukar su. Wato course din, The Essay in English: The Twentieth Century: Theory and Practice I.

*GIDAN MATA TARA*

Da wuri na tashi. Tunda nai sallah ban koma ba. Wanka nayo na shirya cikin wani lesi da Fadila ta mana sallar bara, Green ne da ratsin yellow. D’inkin samfarin doguwar riga ne kirar A shape. Hakan yasa na zura wani hijabi da nasiya sabo shima yellow. Ba kadan ba nayi kyau. Yar hoda na shafa kadan da man lebe bayan na bi jikina da turaruka masu sanyin kamshi. A gagguace na tsaya naci abincin safe na. Wainar fulawa ce lafa-lafa ta manja tasha kayan hadi. Naci biyu na zuba uku a yar roba na zura a jakata kan anjima naci a makaranta.

“Innar mu zan tafi.. Kinsan yau zasu zana jarabawa ta ta farko.”

“Masha Allahu! Ubangiji Allah yasa su fara a sa’a. Allah ya tsare ya kare. Sai kin dawo.”

“Amin Innar mu, Sai na dawo.”

“Toh Allah ya dawo daku lapia. Allah ya bada sa’a.”

“Amiin Innar mu.”

Mikewa nayi na fita ina ta sauri. Na gayda yan tsakar gidan mu wasun su sun amsa wasu su kai biris. Na daga kai na fita. A kofar gida naci karo da motar yan sanda tanata jiniya. Zan wuce wani police daga ciki ya dakatar dani,

“Yayata Sannu ko!”

“Sannu ina kwanan ku?”

“Lapia Alhamdulillah. Anan gidan kike?”

Ya fada yana mai nuna kofar gidan mu. Na juya na kalli cikin gidan mu ina daga kai. Gaba d’aya gabana faduwa yake. Ofisan ya shafa rantal din kansa yana cusa hannu a aljihu,

“Ilyasu yana ciki...?”

“Gaskia bansani ba ofisa.”

Murmushi yai ya juya ya kalli sauran yan uwan sa yana daga musu kai. Kutsa kai kawai sukai cikin gidan mu. Binsu nayi a baya ina dafe da kirji na. Gabana sai barazanar faduwa yake. Suna shiga suka zagaye tsakar gidan mu. Sunci magani, D’aya daga cikin su yana busa sigari ya dora kafar sa d’aya akan rijiya,

“Ina Ilyasu????”

Wani daga cikin su ya tambaya da karfi. Yan gidan mu sukai cirko cirko suna raba idanuwa. Ashe Kawu ila na cikin daki ya dora bokitin sa akan sa. Sai rawar tsoro jikin sa yake.

“Zaku fadi inda yake ko sai mun tattare ku duka munyi gaba daku?”

Bintalo ta gwalalo idanu tana watsa hannu baya,

“Sittin ta ubangiji yana daka ya b’uya. Yana jiyo ku. Ga d’akin sa nan.”

Ta karasa fada tana nuna dakin. Suka kutsa kai ciki sai gasu da Kawu ila dumu-dumu a hannun su sun mai ri’ko. Sai neman k’wacewa yake yana kumfar baki,

“Ku sake ni. Me nai muku?”

Talla masa mari d’aya daga cikin su yai a k’eya. Na rintse idanu ina tausaya masa ko meya musu oho? Yayan mu da shigowar sa kenan ya tsaya yana kallon su,

“Ah ofisa ya haka?”

“He’s under arrest. Mun kama shi da lefin cinye hakkin wani mutumi. Yaki biyan sa, Ko dai a ya biya kudaden ko kuma ya zauna agidan yari.”

“Har nawa ne ofisa?”

Ofisan ya sosa hancin sa yana kallon Kawu ila,

“Toh akwai dai fili na gidan gona da kuma wasu kudade wanda adadin su babban mu ne yasani.”

Kowa ya shiga raba idanu yana jinjina kai, Kawu ila ya bi kowannen mu da kallo yana mamakin kin bayansa da akabi.

“Ishaq, Khamis da Dawood ba zaku sa baki ba?”

Zagayewa su kai suka fice suna sunne kai, Kawu ila ya dafe kansa yana girgiza shi. Haka aka fice dashi cikin kaskanci abun tausayi. Jiki a sanyaye na fara tafiya titi. Na samu dan mashin ya kaini na hau motar makaranta. Gaba d’aya raina duk babu dadi. Komai Lalacewar naka naka ne. Hannunka baya rubewa ka yanke ka yar. Haka na shiga cikin makaranta a sanyaye. Har an fara exams din suna cikin hall.

*1k SEATERS AUDITORIUM*

Tunda suka shiga hall din Mubeen ke kallon k’ofa yana saka ran hangota shiru. Sam ya kasa samun nutsuwa ko rubutu d’aya bai ba. Fatan sa dai Allah yasa lapia. Sanarwar shigowar ta aka fad’a musu. Sannan ya sauke gwauron numfashi yana lumshe idanu jin yadda zazzakar muryar ta ke karakaina a kunnen sa. Inda take basu hakuri hade da gyara wasu questions din da aka bugo ba dai-dai ba. Tana gamawa ta sarke hannu tana bin kowannen su da kallo, Kowanne fuskar sa dauke da farin ciki yake amsa jarabawar duba da yanayin tambayoyin data basu masu sauk’i.

Ina bin takardun kowannen su amman zahiri gangar jiki na ce anan ruhi na nacan yana tunanin yadda take kwashewa da Kawu ila. Haka na k’arasa gaban Mubeen da abun mamaki da takaici sai alokacin ya fara rubutu yana sakarmin murmushi. Na dube shi na dubi answer sheet din nasa da agogo na. Girgiza kai nayi na wuce gaban wani student din. A takaice kusan atare suka gama rubutawa da sauran yan ajin. Na tattare takardun nai office dina. Ina shiga ciki Muhd Mubeen ya biyo ni,

“Ma.. Barka da rana.”

“Yauwa sannun Mu.”

“Ya..Ya akai bakizo da wuri ba?”

“Something came up.”

“Ayyah!!!! Today’s exam was..Amazing”

Har zan tambaye shi abinda yasa ya Fara rubutu a late sai kuma nai shiru ina k’ok’arin bud’e robar wainar fulawar da nazo da ita. Cikina sai zafi yakemin. Ina jin yunwa.

“Bismillah!”

Nace dashi ina bu’de ledar yaji. Lek’a wainar yayi yana yamutsa fuska.

“Ya sunan shi?”

“Bakasan wainar fulawa ba? Y’ar kalallaba ba?”

Girgiza min kai yayi yana taune lips,

“Nasan dai danwake kawai.”

Murmushi nai kawai, Saboda yanayin sa kad’ai zai nuna bai san taba,

“Wane yare ne kai?”

“Hausa Fulani da Amharic.”

“Amharic? Ethiopia ko?”

“Yes Ma! Mamana ce Ethiopian. Baba na kuma Hausa fulani ne.”

“Woah! Masha Allah.”

“Ma kinyi kyau yau.”

“Nagode! Tashi kaje karatun exams”

Kamar da bango nake haka ya kara karkacewa a kujera yana kallo na. Na kauda kai ina sake jefa lomar waina a baka.

“Ma kinyi kyau...”

“Tashi ka fita, Naga alamun ka fara renani.”

“Haba a’a! Kawai hijab d’inne ya miki kyau. Kinyi kyau ma.”

Bude baki nayi ina kallon sa. Kayan haushi Na fada a zuciata ina kurbar ruwa. Sallamar Haysam na jiyo a bakin kofa,

“Shigo ciki..”

Shigowa yayi. Sukai idanu hud’u da Mubeen . Mubeen ya watsa masa wani kallo domin bai mance fuskar sa ba. Haysam kuwa jan kujera yai ya zauna yana kallo na,

“Mine...! You luk stunning.”

Dan tari nayi alamun da mutum awajen. Sai asannan Haysam ya mika masa Hannu. Dakyar Mubeen ya bashi yana yamutsa fuska,

“Do excuse us Muhd.. Allah ya bada sa’an exams.”

Dak’yar ya mike yana min wani kallo dana kasa fahimtar ma’anar sa. Har ya kai bakin kofa ya kalle ni ciki ciki yace,

“Zan dawo anjima. Take care”

D’aga kai kawai nayi. Na juya wajen Haysam. Mubeen kuwa ya jima awaje yana sakin tsaki. Ni kuwa bayan nagama y’an abubuwan da zanyi Lokacin sun shiga wata exams din har sun kusa fitowa yasa nabi Haysam na koma gidah sabodah hankali na yak’i kwanciya da yadda aka sungumi kawu ila aka tafi dashi.

Muna tafe akan hanya Haysam na zuba min kalamai. Ni wallahi har na gaji.

“Mine sau da yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya. Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki so mai tsanani, Pls ki bani dama na fara zuwa zance, Domin fara gudanar da soyayyar mu kafin mu dora data aure?”

“Na’am..”

“Nace.. “Mine sau da yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya. Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki so mai tsanani, Pls ki bani dama na fara zuwa zance, Domin fara gudanar da soyayyar mu kafin mu dora data aure?”

“Ko Yaushe.”

Buga sitiyari Haysam yai cike da murna , Sai surutai yake yana jin dad’i. Na girgiza kai kawai ina kallon titi. Natsani yarinta wallahi....

Mubeen na fitowa daga exams yai office din Batoul. Ai kuwa ya tarar ta tafi gidah. Cike da bacin rai ya shige mota yace da direban sa,

“Muje area din limancin kona d’innan.”

Gyada kai direban yai. Ai kuwa yana zuwa ya tarar dasu daga gefen layin. Haysam ya fito daga motar ya dora hannayen sa akan motar yana zance da batoul dake facing d’insa tana dashare hakora. Wani malolon bak’in ciki ne ya taru ya tsayawa mubeen a makogoro,

“Kai ni gidah..”

“Yallabai har ka...”

“Yes muje.”

Shigewa yai suka kama hanyar gidah. Ya rufe idanun sa. Yana jiyo yadda sautin zuciyar sa ya canza. Ahankali ya lumshe idanun sa yana cije lebe.

“Ya Rabbi....”

Tun bayan sauke Batoul da Haysam yayi ya takura mata da nacin karbar soyayyar sa, Kullum cikin yi mata waya da zuwa gidan su yake. Ya kanainaye ta da soyayyar sa bata da zabi sai Na hakura ta karbi soyayyar sa. Hakan kuwa akayi. Cikin satin tuni suka kulla zazzafar soyayyah mai wahalar fassara muku.

Mubeen kuwa dakon soyayyar malamar su ke dawainiya dashi. Gashi kullum Haysam yana tare da ita ko a school. Hakan yasanya shi dan ja baya da ita sai gaisuwa kawai da yake da ita. Hakan ma dan baze iya kwana ba tare da yayi tozali da fuskar ta ba. Domin da soyayyar ta yake kwana ya tashi..

Successfully suka kammala exams din first semester. Abun ba acewa komai sai godiya ga mai duka. Domin gaba ki

Please Login or Register in order to submit comment