Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ina jan majina saboda murar data kamani lokaci daya, hannu na nasa na shiga goge hawaye na ina nanata,

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”

“Dan ubanki ina wayar daya baki?”

Cikin kuka na cusa wayar acikin rigata. Ganin zai ‘kwace ta,

“Gatacan Innar mu ta tafi mayar masa.”

Kad’a kai yayi yana kwafa. Bintalo ta shiga sakin gud’a a karo na ba adadi. Cikin shewa tace,

“A hayye! Dama da walakin wallahi. Sittin ta ubangiji da ganin yawan kayan nan kasan ba banza ba. Ashe sai da ya rabe ki sannan ya baki. Y’ar iska.”

“Allah ka sakamin. Allah kana gani. Allah kamana sakayya da wa’innan bayin naka azzalumai.”

Na shiga fada a hankali ina goge hawayen fuska ta, Kawu ila ya mike tsaye yana karkada hannuwa,

“Karki bari na sake jin ko ganin haka ta faru. Sannan karya kara tako kafar sa yazo gidan nan dan wallahi zan mugun sab’a miki. Shashasha, Sakarai. Daga ganin su Alawiyya sunzo da kayan dadi shine zaki bada jikin ki don a baki? Kaga karamar y’ar iskar yarinya. Ina ke Ina tsatson gidan Alhaji Kabeeru Mai Wafa? Ki cigaba dasa ido ko bakin ciki akan abunda aka basu. Wallahi zaki nadamar sani na a rayuwar ki. Da ido tsuru-tsuru kamar na mayu.”

Yana gama fad’a ya sauka kasa, sauran na biye dashi. Bintalo kuma ta shiga yada magana tana zunden Usaiba dake yiwa Talatuwa kitso. Ci kanki batace mata ba. Da alamun tama ta take yi. Mikewa nai na debi ruwa na shafa a fuska ta. Inda ya mare ni harya kumbura da shatin hannun sa. Autar mu dake rakub’e a gefe ta rungume ni tana bani hak’uri. Murmushi nai kawai ina goge mata hawayen dake zuba a idanun ta,

“Ungo rik’e ki siyo kananzir na goma, Gawayin hamsin. Sai manjan talatin da tumatir da albasa na ashirin. Kiyi sauri ki dawo karki zauna wasa.”

Gyada ka tayi ta karb’a da gudu ta fice. Murhun mu na gyara yadda data kawo zan dora komai. Na d’akko tsakin ina tsince shi, Zuciata cunkushe da bakin cikin rayuwar gidan mu. IN SHA ALLAH zan tambayi Innar mu ko da akwai dalilin da yasanya aka tsane mu haka. Ba jimawa autar mu ta kawo komai. Cikin kankanin lokaci na kammala mana. Na zuba na Innar mu a yar kular abincin mu. Mu kuma na sa mana a filet muka ci. Ina gamawa na fuce makwabtan mu can gidan matar soja don yi mata sangas (some gaps) Mun jima ana mata dake ‘kanana ne. Sai bayan magriba na koma gidah, Lokacin Innar mu harta dawo. Na mata sannu da zuwa hade da ciro dari biyun kud’in sangas na mika mata,

“Gashi Innar mu.”

“Toh uwata! Angode Allah yayi albarka. Sai asiyo wani abun aci ko?”

“Eh mai sauk’in dafawa ba.”

“Toh taliya za’a siyo kenan? Amma fa ba mai sai dan kad’an Innar mu.”

Innar mu ta dafe habar ta tana tunanin abinda za’a siyo. Taja ajiyar zucia ta sauke,

“Yanzu idan akace a siyo taliya ma kudin man a zaune yake da kayan miya. Gaushin ma ya kare ko?”

“Eh Innar mu”

Na bata amsa ina matse hawayen dake neman zubo min.

“Dan Allah ayi y’ar kanannidaddiya (Indomie)kawai.”

Autar mu tafada tana murna. Innar mu tai murmushi,

“Abincin yara zaki ce. Toh ita nawa take?”

“Nera ashirin ce Innar mu.”

Autar mu ta fada cike da jin da’di. Innar mu ta mikomin dari biyun. Na karb’a ina zura hijabi na. Autar mu harta fice tana murna.

“Ta nawa zamu siyo ne?”

“Asiyo ta dari ko? Da safe sauran darin ayi karin kumallo da ita.”

“Toh Innar mu sai mun dawo.”

“Allah ya dawo daku lapia.”

“Amin..”

Ficewa mu kai ni da autar mu. Shagon Gali muka je, Yana tsaye yana kulla gishiri a leda. Yana ganin mu ya dashare baki, Hade rai nai saboda banason raini. Muna aji biyar a firamare ya rubuto min leta wai so na yake. Ni da shi bansan wanda ya girmi wani ba. Amma tsabar cika ido wai ni yake so.

“Bamu Indomie guda biyar..”

Dakkowa yai ya zuba a leda yana mikomin,

“Gashi aunty na.”

Karba nayi ina cuno baki na domin nasan da biyu ya fa’di haka. Biskit ya debo yana mik’awa Autar mu. Girgiza kai tayi tak’i k’arba domin Innar mu ta hana ta kar’bar abun hannun mutane. Hannun sa yasa zai riko nata nai saurin janye ta ina zabga masa harara,

“Akan wane dalilin zaka bata biskit ba d’aya ba ba biyu ba.?”

Ina karasa fada na zabga masa harara. Ina jan hannun Autar mu muka fice ganin yadda yake kallon ta yana murmushi yana wani tande baki. Tsaki naja na sauke..Mtscew’

“Dan iska, Sai kace maye.”

“Yaya menene?”

“Babu komai! Kar ki kara zuwa shagon Gali siyo abu. Ko ya kiraki karki je ke bama shi kadai ba da sauran mutane. Kina jina?”

“Eh Yaya.”

Gida muka shige. Innar mu na kishingid’e tana jin rediyo. Sannu da zuwa tai mana ta cigaba da sauraron shirin da take. Gaushin na fifita dake da dan sauron wutar tuni ruwan kai ya tafasa na zuba indomien. Cikin kankanin lokaci na gama na juye mana a tire. Hannuwa muka wanke muka fara ci. Tas muka cinye, Autar mu kuwa hadda sude tiren. Na tattare kwanukan na sauka na wanko su tas. Na tashi autar mu data fara gyan-gyadi na kai ta tayo fitsari. Muna dawowa kuwa ta bingere tafara bacci. Matsawa kusa da Innar mu nayi ina matsa mata kafafu a hankali kai na na kasa,

“Innar mu...”

“Na’am Uwa ta.”

“Innar mu kiyi hak’uri dan ALLAH. Shin akwai dalilin da yasan ya aka tsane mu a gidan nan? Cin kashin da ake mana yayi yawa Innar mu. Na rokeki ki, Dan ALLAH Innar mu... Nagaji ne, Zuciya ta tana *ZATON* wani boyayyen lamari. Dan ALLAH Innar mu ki gayamin akwai dalilin da yasa basa son mu ?A matsayin mu na yayan dan uwan su na jini?”

Ajiyar zuciya Innar mu ta sauke. A sanyaye ta dago daga kishingid’en data ke. Cikin wata irin murya mai wahalar fasaltawa ta fara magana,

“Toh uwata kinyi magana. Wadda dama nasan komai daren da ‘dewa wannan ranar zata zo. Kamar yadda wannan yaron (Najibu) shima ya nemi sanin haka a shekarun baya. Itama kuma auta da Lokaci yayi idan har ina raye zan sanar mata. Idan kuma rai yayi halin sa toh na rokeku daku sanar da ita. Idan kuma komai ya dedeta kafin lokacin hakan falillahil hamdu. Haka akeso dama, Kina jina ko?”

D’aga kai nayi ina sharce hawayen dake y’ar tsere a fuska ta. Innar mu ta kara nisawa kafin ta cigaba,

*MAFARIN KOMAI:*

___
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

_*SHAFI NA SHA BIYU_*

*•**•*•**

*MAFARIN KOMAI*

“Kamar yadda kuka taso kuka ji sunan mahaifina Malam Rabi’u Shema. Ya kasance yana da mata biyu. Mahaifiyar mu kinsan sunan ta kika ci, Muna kiran ta da Inno. Itace kuma matar mahaifin mu ta farko. Sai matar sa ta biyu Iyalluwa. Mu bakwai ne duka ‘yayan baban mu. A b’angaren mahaifiyar mu mu hudu ne. Yayan mu Abdullahi shine ‘dan fari kaf gidan mu, Sai Yayar mu Halimatu. Sai ni dake mabiyar ta, Sai dan autan mu Baffajo wanda yaci sunan Baffa Ardo kawun mu. Iyalluwa kuma nada ‘yaya uku: Bello, Yafendo da kuma Usmanu,

“Mahaifin mu kafin rasuwar sa ya kasance manomi ne, Kuma shine mai bada shawarar Mai gari. Mai garin yankin namu kuma yayan mahaifin mu ne. Uba suka hada, Uwa kuma Kowa da tasa. Shi mahaifin mu d’akin su d’aya dasu Baffa Ardo. Mahaifiyata wadda kikaci sunan ta kafin rasuwar ta, Ta kasance tana sana’ar saye da sayar wa tana kuma yin kosai da koko, Babu lefi gidan mu ana zaman lapia da kaunar juna. Kowannen mu yana bin nagaba dashi. Akwai biyayya gaskia,

“Asalin kakannin kakannin mu fulani ne na jaub’awa. Kuma ance Sheman ma zuwa kakannin mu su kai, Ma’ana tsatson mu daga wani yanki suka taso sukazo Shema suka kafa ahalin su. Mahaifin ku kafin rasuwar sa ya had’u da ni ne abisa tashi da suke yi shida yan uwan sa. Ma’ana suje wannan gari su kafa kasuwancin su idan rani tayi su koma wani garin su kara yin wani kasuwancin. Lokacin da suka zo Shema a wajen mai gari suka sauka kafin mahaifin mu ya nema musu wajen da zasu zauna. Anan shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakanin mahaifina da naku. Saboda yafi sauran yan uwan sa sauk’in kai da son jama’a. Hakan yasanya yan gidan mu ke son sa. Aka dauke shi tamkar ‘da. Har sai da takai ta kawo an ajiye masa kwanon abinci a gidan mu. Safe, rana, dare sau uku cass ake bashi abinci. Har yakai ya janyo abokan kasuwancin su suna zuwa suyi ma inno d’inmu cinikin koko da kosan da take na siyarwa,

“kafin a baka auren d’aya daga cikin tsatson mu sai an gudanar da wasu al’adu kafin a yadda a baka ‘dayan mu. Mahaifin ku ALLAH ya dasa masa soyayya ta a zuciar sa. Tun ina d’aukar sa a matsayin yaya na har na dawo nima na fara son sa. Muka fara soyayya cikin so da shakuwar juna. Bazan manta ba a lokacin yan uwan sa sun kyamaci ne a matsayin wacce yake so. Ganin daga k’auye nake kuma mu ba masu rufin asiri bane. Al'adar Shadi na daga cikin al'adun mu da suka shahara. A duk shekara muna taruwa domin gudanar da gagarumar gasar a kowanne rassa na arewacin Nijeriya. Mun kulla soyayya dashi har ta kai yaje wa da mahaifin mu zancen. Saboda kaunar da mahaifin mu ke yi masa shida Baffa Ardo da Baffa mai gari. Hakan yasanya kawai aka bashi ni batare da ya gudanar da al’adun da muke yi ba, Mai gari yayi shela kan ya bada aure na ga wani da yayiwa alqawari shekarun baya. Ba ajima ba kuwa aka kawo goron aure na aka sanya rana. Babu dogon zance akayi biki. Alokacin mahaifin ku sun sayi wannan gidan da muke ciki,

“A shekara d’aya akai bikin mu da sauran ‘yayan baffanin mu. Zagayowar wata shekarar duk suka hayayyafa ni kuwa ban taba batan wata ba. Mun zaga ko’ina ance lapia ta lau haka ma shi mahaifin ku, Haihuwar ce dai ALLAH be kawo ba. Daga baya mahaifiyar mahaifin ku ALLAH yai mata rasuwa dama tuni mahaifin su ya rasu shima. Tun daga lokacin yan uwan mahaifin ku wutar ki na tak’ara ruruwa a zukatan su. Sun tsane ni tsana mai tsanani idan muka cire Aminatu da Dawooda shi dama bai cika magana ba. Dangin mahaifin ku su kai ta kananan maganganu kan ni juya ce bana haihuwa ga matan yan uwan sa nan da aka samu a lalle tare sun hayayyafa. Wato Usaiba matar Ishaq da ummita marar ilyasu. A tare suka haihu d’aya da rana d’aya da yamma. Larai da safe Usaiba ta haife ta, Mariya kuma da Yamma aka haife ta. Makirci da manakisa babu wanda ba a shiryamun a gidan nan Allah ne kawai yake kare ni. Har ta kai an hadamun wani tuggu wanda hakan yai sanadiyyar komawata gidah. Sabuwar shekarar da muka shiga aka tafka mana rasuwa, Baffan mu ya rasu da wata biyu inno dinmu ta rasu itama bayan wata biyar kuma iyalluwa ta rasu. Hak’ik’a mun shiga matsatsi da kuncin rayuwa, wa zan kai wa kukana? Wadanda zasu sharemun hawaye na duk Allah ya karbi rayukan su. Ban koma gidah ba sai bayan watanni biyar, Na koma najj wani sabon lamarin kuma,

“Mahaifin ku an bashi auren yar kanwar kakan sa dake kauyen kode ta jihar kano kauyen lahadin makole. Naci kuka kwarai har sai da yayar mahaifin ku tazo daga kaduna gidan aurenta ta kwantar mun da hankali kan cewar bawai dan bana haihuwa bane zai auro ta. A’a kawai dai rufa mata asiri zai yi ita wadda zai auren ya kuma kara karfin zumuncin su. Shi da ita sun bani baki sosai haka dai na hakura ya karo auren. Tazo ta tare, kullum burin ta shine had’ani rigima da mahaifin ku, Tsegumi, Gulma da hassada ciki harda makirci babu wanda bata yi mun. Shekarar farko ta haihu ta samu diya mace wato yayar ku zabbau dake aure a kod’e. Na sha bakaken maganganu daga kawunnin ku. Na rufe kunnuwa na cigaba da zaman aure na. Sai bayan shekaru biyu zama yaki da’di, Baffa Ardo yasa bello ya d’akko ni ya kai ni gidah cikin ikon Allah ina komawa gidah da wata d’aya da rabi na fara wani irin ciwon ciki komai na ci sai na amayar ana min gwaji akace ciki ne. Da akai aike aka fadawa mahaifin ku kwarai yayi murna a daren yataho Shema. Amma yan uwan sa kawunnin ku kenan sukace basu yadda ba lalle ba cikin sa bane. Dakyar dai da yardar ALLAH na dawo gidan nan. Ai kuwa ni da wannan yaron munsha muzgunawar rayuwa, Akai ta shegan ta shi ana aibata mu suna ware shi acikin yara ana kyamatar sa,

“Allah ne ka’dai ya raya shi da kuma kwanan sa agaba. Ba don haka ba kala kalar muguntar da aka yiyyi masa da mai karar kwanane da yara su....”

Innar mu na kaiwa nan tayi jimm tana jinjina kanta, Siraren hawaye suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta. Cikin muryar rarrashi na shiga bata hak’uri,

“Kiyi hak’uri Innar mu. In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, ALLAH zai inganta rayuwar mu muma da yardar Allah.”

“Ameen.”

Innar mu tafada tana sharce majinar da ke tsiyaya a hancin ta. Saboda tsabar kukan da take yi tuni mura ta kamata. Ajiyar zuciya taja ta sauke tacigaba da cewa,

“Tun bayar haihuwar wannan yaron ban sake wata haihuwar ba har Bintalo ta sake haihuwa inda ta haifi Alawiyya, Nan ma dangin mahaifin ku su ka kara yo min caa. Daga baya cikin ikon ubangiji bayan haihuwar Alawiyya da shekaru biyu da wata d’aya lokacin mahaifin ku sunje tashi Bintalo ta sake haihuwa inda ta haifi Hinde. Ni kuma cikin ikon ALLAH na je Shema bikin Atuwa yar Baffa Ardo, A cikin watan shekarar ala fara fadan musulmi da arna dinnan. Ashe da shigar ciki, Ni kuma haka Allah ya qaddara min samun ku. Har ciki ya tsufa ba hanyar sanarwa da yan uwan mahaifin ku. Nan Allah ya albarkace ni da samun ki, Baffa Ardo shi yayi miki huduba yasanya miki sunan mahaifiyar mu. Uwata in k’ark’are miki zance dai sai aka sake sheganta min ke akaro na biyu bayan na wannan yaron. Mahaifin ku yayi mai yiwuwa don tabbatar mu su kudin jinin sa ne, Fafur sun ki yadda. Ban kara wata haihuwar ba sai bayan shekaru bakwai. Cikin Aminatu auta ne kawai na haife shi anan gidan. Ita dinma ca su kai basu yadda da shi ba. Mahaifin ku da Aminatu sune kadai su kai mai yiwuwa don ganin sun nusar dasu cewar kuma ‘ya’ya ne kamar kowa amma hakan yaci tura. Har ALLAH ya karbi ran mahaifin ku a har kullum addu’ar sa da cikar burin sa baya wuce yaga ya cire mummunan *ZATON* da suke akan ku ba. Ni kuma banason na kwashe ku na tafi da ku Shema, Kinga zanbar baya da k’ura kenan, Domin har gaban abadan mutan garin nan zasu yadda da *ZATON* da ake muku. Fatana a har kullum shine ALLAH ya ganar da ahalin gidan nan su sakko dagga *IGIYAR ZATON* da suke muku. Ai dole dai idan muna tare dasu su maye muku gurbin mahaifin ku. Amma da na tafi daku, duniya zata fara yamadidi da kiran ku ‘ya’yan mace. Allah dai ya samu dace duniya da lahira. Ameen!”

“Ameen Innar mu.. Hak’ik’a labarin nan ya dimauta ni, kuma an sha gwagwarmaya dake kin tsaya tsayin daka akan mu. Allah ya warware wannan sarqaqiyar yasa su gane turbar gaskiya. Ameen.”

Haka dai mu kai ta zantuttuka da Innar mu, Sai da dare yaja sosai tukun sannan muka kwanta, Zuciata cike take fal da labarin mu da Innar mu ta bani.

*WASHE GARI*

Washe gari da asuba da kyar na farka, saboda dad'ewar da mukayi da Innar mu akan tarihinsu da take bani. Ina mutstsike idanuwa tare da murzasu da hannayena guda biyu saboda kaykyayin da suke min, a haka na mike tsaye, wata irin hamma na saki kai kace yanzu nake shirin kwanciya baccin, amma ba komai bane sai irin na yarda jikina yayi wani irin tsami. Bokiti na d'auka da ragowar ruwa a ciki saboda naje na tsarkake jikina, dan naji duk na b'aci daga kasa na, kasan cewar bana amfani da pad sai d'an tsimma saboda rashin kud'in siyan kunzugun. Innar mu na kalla wacce ke zaune tana lazimi akan tabarma tana gyangyad'i, na saki d'an murmushi tare da girgiza kai ina jin kaunar mahaifiyar tamu har cikin zuciya ta.

Fitowa nayi ina kallon lungu da sako na saman benan ko zanga wani, ganin babu kowa yasa na dan lek'a k'asan benan. Da sauri na k'arasa sauka k'asan saboda hango usaiba na zuba ruwa a buta, wanda da alama ban d'akin take son zuwa itama, zan iya barinta ta shiga, sai dai wannan karon nima sauri nake yi domin idan na bari ta shiga sai randa hali yayi saboda dad'ewar da take yi a ban d'aki idan ta shiga. Ina jiyo ta tana mita daga bakin k'ofar, ni dai ban ce komai ba har na gamana fito sannan ita kuma ta shiga.

Sai dana gama shiryawa tsab, sannan na tashi na d'ebi wankin mu duka, K’asa na sauka da sabulun wanki na shiga dirje mana kayan ina sab'ewa a ruwan d'auraya, k'ugu na sai radad’i yake min amman haka na karasa wankin dakyar. A inda zan shanya su na fara tunani ga masifar 'yan gidan da suke yinta babu gaira babu dalili. Shanya su nai a k'afar bene da jikin bangon benen tsakiya, na nufi sama da bokitan da nayi amfani dasu. Ina shiga d'aki, na tarar da Innar mu da autar mu sun cure guri guda Autar mu tayi bacci akan taburmar da tai sallah Innar mu kuma ta kudundine da hijabin ta. Idanun ta sun kad’a sunyi jawur. Da alamun zazza’bi ne ya rufeta daren jiya..

“Innar mu ina kwana?! Subhanallahi! Innar mu jikin ne? Sannu ya jikin naki?”

“Lapia Alhamdulillah uwata.. Na tashi ai naga bakyanan ina kikaje ne?”

“Wanki nai Innar mu. Naga kayan sun taru da yawa. Zazzabin ne?”

Na karasa fada ina taba kafafunta dake rawar sanyi. Jikin yai ‘kau. Ya dau zafi sosai. Daurewa tai ina hankalce da ita. Ta rik’e hab’a tana jinjina kai,

“Du wannan wankin ke kadai? Ca nai fa ki bari zamu yi tare. Ai yayi miki yawa ke kadai.”

“Babu komai Innar mu. Na kammala ma harna shanya su.”

“Masha Allah! Toh angode ALLAH yayi miki albarka.”

“Ameen Innar mu! Allah ya azurta mu muma mu dinga bayarwa ana wanko mana. Ko mu sai injin wanki irin na gidan matar soja.”

Dan murmushi Innar mu tayi. Tana rintse idanu cikin ciwo.

Gabaki d'aya jikinta ya sanyaya daka ganta kasan cewar akwai abinda yake damunta, wanda ba wai a iya fuskarta yake ba, a'ah har can cikin zuciyarta take jin ciwon. Bata iya kallo na ba, muryarta a sanyaye tace dani.

“Babu wani abun da zaku iya sarrafawa kuci yanzu, kuyi hakuri ku daure har naje gidan aiki naga ko ALLAH zai sa na samo muku koda k'anzo ne kuci.”

Na kalleta da mamaki a fuskata jin tana ambatar fita, bayan jikinta kamar garwashin wuta yake. Duk da cewar wankin da nayi ya kuma sanya min wata azababbiyar yunwa, hakan hakan bai zai sa na bar mahaifiyata da take halin rashin lafiya ta fita aikin wahala ba. Na sanyaya murya dan na kwantar mata da hankalinta ina cewa.

“A'ah Innar mu kiyi kwanciyarki, keda baki da lafiya ya za'ai kije aiki.”

“Dole ne naje na nemo muku abinda zakuci uwata, idan ban fita na nemo ba, waye zai kula ku dan bakuci ba a cikin gidan nan?”

“Innar mu ki kwanta, bari naje gidan ruwa naga ko ALLAH zai sa na samu wacce zan yiwa kitso, abinda na samo sai muyi amfani dashi”

Na gama fad'a ina sake kai hannuna jikin k'afar Innar mu ina sake jin yanayin jikin nata, gidan ruwan da nake fad'a zanje can ne bayan gidan su Haysam, inda ake buga musu ruwan leda wato (pure water) na bada sari, a jiki akwai wani gidan mai d'auke da mata uku, nan naso zuwa ko ALLAH zai sanya suce ayi musu kitson, amman Innar mu tace.

“Uwata kiyi zamanki, hurumin samar mana da abinci baya wuyanki yana wuyana. Ki zauna gurin 'yar uwarki zanje na dawo yanzu, ai zan iya zuwa.”

Babu yadda na iya dole na rabu da ita, ina ji ina gani ta mik'e da kyar tana rintsa ido alamun kanta yana tsananin bugawa. Tashi nayi na d'akko mata hijabi ta karba tasa sannan ta yi min sallama ta fita daga cikin d'akin namu. Ina jiyo lokacin da kawu ila yake ce mata.

“Toh garin ya waye za'a tafi yawan ta zubar ko? AlLLAH ya kiyaye ba uwar ba 'ya'yan tur da irinku.”

Banji muryar Innar mu ba, hakan ne ya tabbatar min da cewar bata kulashi ba, saboda idan da sabo wannan kalaman sun riga sun zauna a zuciyar Innar mu. Na mik'e tare da fara gyara d'akin namu, ina gamawa na koma na kwanta tare da zaro wayar da Haysam ya bani sai faman kallonta nake yi.

“Ke Batoul! Batoul.!”

Na jiyo muryar Bintalo daga kasan bene tana ta kwad'a min kira kamar wacce na karbarwa bashi. Kamar karnaje saboda nasan yanzu kasan cike yake da 'yan gidan, kuma idan har na sauka duk wani wulak'anci a gabansu za'a yi min shi.

“Ko bazaki zo bane ni na zo?”

Na sake jiyo muryar Bintalo, ko yaranta bata iya yiwa wannan kiran da take yi min. Na juya tare da maida wayar inda nake b'oyewa na aje, sannan na fito ina mistsike ido kamar a lokacin ne na tashi daga bacci. Da hannunta take mun alamun na sakko, na kalli mutanen dake gurin kowa na harkar gabansa, sannan na sauka kamar wacce babu kashi a jikin ta.

“Kaga sarauniyar mata, ana tafiya kamar yar gidan wani sarkin.”

Cewar Bintalo tana tsaye ta rik'e kugu jira kawai take na gama sakkowa, cikin rai na nayi murmushi domin ba zan bari wata kalma tasu ta bata min rai ba a yau.

“Kawu Dawood ina kwana?”

Na gaida shi kasan cewar yana zaune ne a kafar bene yana asuwaki, ya amsa min ba tare da ya kalleni ba, don shi bai fiye yin doguwar magana ba sai dai duk abinda ake yi yana ji tankawa ne da kuma kallo ba zai yiwa abin ba. Na gaida duk wad'an da suka cancanci gaisuwa a gurin, wasu sun amsa min yayin da wasu suka share ni tamkar ba dasu nake ba, saboda kawai basu dauke ni a bakin komai ba.

“Kitso nake son kiyi min mai kyau, zanje biki da anjima.”

Wani irin bakin ciki ya tokare a wuya na jin abinda take son nayi mata, babu wani lallami ko daddad'ar kalma, a'a cikin gadara da bada umarni haka take min kai kace itace tayi nakuda ta. Shirun da taji nayi mata ne ya sake bata damar yin magana a karo na uku cewar.

“Ko ta hana ki yi mana ne iye?!”

Nasan Innar mu take nufi, dan haka nayi saurin girgiza kai alamar bata hana ba, sai dai fuskata a cunkushe take saboda na tsani yiwa matan gidanu kitso domin kana yi kana shan takura gashi ba godiya

Please Login or Register in order to submit comment