Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TubarkAllah. Idanuwana farare ne tas da su kamar ruwan madara, kwayar idanu na kuwa burawun ce sosai, sai yalwar gashin gira domin saura ka’dan su hade da juna, baki na dan mitsi-tsi ne jawur dashi kai kace jambaki na shafa, hanci na dogo ne sosai, ga kuma tawadar ALLAH a gefan hancin wanda ya kara kyawun fuska ta, Inada yalwataccen gashin kai tubarkAllah tamkar ni na kera abuna, har gadon bayana yake zuwa. Shekaru na goma sha hudu a dunia, inada sa’oina sosai a gidan mu, Wanda suke kula-kulen samari kamar tinkiyoyi. Idan kaga layin da ake a kofar gidan mu za kwi mamaki. Na kasance ina da dinbin samari, Sai dai basa kulani saboda rashin ganin fuskar hakan. Sannan Yayan mu ya hanani kula kowanne daga cikin su. Hakan ba damu na yayi ba domin nima banida ra’ayin kula samari yanxu. Nafison sai nayi karatu sosai, kuma inada burin auren wanda ya girmemi ni sosai domin agani na sunfi hankali da nutsuwa.

Duk abokanan Yaya Najib kallon yara nake musu, har a sujjada nake rok’on ALLAH karya sa na auri wanda ya girme mini da shekaru biyar, nafuson na auri wanda ya bani shekaru goma da yan kai saboda wasu dalilai na dana barwa zucia ta. A karamin aji na biyu nake a jiniya sakandire, wadda ake kira da gwanmen gels jiniya sakandire sukul, shekaru na sha hudu a duniya, banida burin da nake so na karanta irin karantar bangaren zallar ingilishi. Kuma har farfesa nake so na zama a fannin.

Gidan mu ya kasance mai dakuma tara aciki, kuma Idan ka lissafa matan auren dake ciki su tara ne, Hakan shi yasanya yan layin mu dama unguwoyin gaban mu, yiwa laqabi da gidan mu 'Gidan Mata Tara'

Wannan shine takaitaccen tarihin gidan mu dama nawa a tak’aice.

*WASHE-GARI*

Tun asubar fari dana tashi ban koma ba, bandaki nai hanzarin shiga nayo wanka na, saboda ban’daki d’aya ne kawai a gidan mu, kuma har layi ake yi akan sa. Ina gama wanka na na tado autar mu itama na sab’e mata jikin ta. Innar mu ma tayo nata bayan mun gama kintsawa. Uniform dinmu na zaro mana a karkashin kwallar da muke ajiye kwanukan abincin mu. Domin anan nake mana ninkin guga sai na zura su a leda na dora kwallar akai sai kuga kuma sun ninku tamkar an goge shi. Rogowar dumamen shinkafar jia muka ci, na koma gefe ina azkhar, Innar mu kuma tagama nata tuni, ta kunna yar rediyon ta tana jin labaran jamus. Autar mu kuma ta kishingid’e tana bacci, daria taba ni yadda ta kanannade tana baccin ta da yar ledar littattafan ta a hannu. Gyara mata kwanciyar nai yadda zata ji dad’in baccin ta. Haka dai nai ta jira har rediyon hannun Innar mu suka sanar da ‘karfe bakwai da ‘kwata’. Mikewa nayi na dan diga turaren ‘dan duwalar da shi kadai ne turaren mu na shafe jikina dashi. Tashin autar mu nayi ta kara wanko bakin ta da fuskar ta. Innar mu dake gefe ta mik’o min naira talatin,

“Ungo ki dau ashirin din ki barwa auta goman, ALLAH ya bada sa’ar karatu mai amfani.”

Rissinawa nayi na karba cike da girmamawa,

“Mungode Innar mu ALLAH ya ‘kara bud’i.”

“Innar mu mungode..”

Autar mu tafada tana rufe bakin ta sakamon hammar data taho mata, da alama baccin bai gama sakin ta ba.

Haka dai na tasa keyar ta muka fara sauka a bene, a lokacin su Alawiyya ke wanka, kamshin soyayyan kwai sai tashi yake daga dakin su. Da alama dashi zasu tafi makaranta. Nida autar mu ne kawai ke yin makarantar gwamnati. Su Alawiyya firabet suke zuwa duk tam dubu d’aya da dari biyar. Makarantar su d’aya da Fadila babbar k’awata. Ina ta jan hannun autar mu muka tafi makaranta, har ajin su na kaita sannan na wuce namu ajin. Koda aka fito birek awara da wainar fulawa na siya mana ni da autar mu. Goman ta kuma muka sai ruwan biyar da alawa. Ana tashin mu muka dauki hanyar gidah, Muna tafe a hanya ina bitar haddar Ashmawin da za’a karba an jima a islamiyya. Tun a kofar zauren kofar gidan mu muke jiyo hayaniyya, kai na na dafe da hannun dama ina girgiza shi, shin yau ko da suwa ake dambatuwa oho? Muna shiga na jiyo muryar usaibatu maman su Larai tana lailayo ashar tana durawa Bintalo. Nan dai suka hau gumirzin fada, Baba ila dake tsakar gidah ya janyo bokitin karfe ya zauna akai yana duban su da kallo. Sunne kai nayi a ‘kasa na fara hawa bene, muryar Baba ila na jiyo yana doka wa suna na kira,

“Batoul, Ke Batoul...”

Gaba na ya fadi jikake ‘ras, Shin menayi ni kuma?! Cikin rawar baki da jiki na fara komawa kasa ina nanata,

“Na’am Kawu...Gani!”
_______
******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*IGZ*

*SHAFI NA: UKU*

•••

“Zo nan dan uban ki.”

Wani abu ya tokare min a wuya na, Na rasa mai yasa ala dole sai sun zagi Abban mu aduk lokacin da zasu mana fad’a. Jiki ba ‘karfi na ‘karasa kusa dashi na tsugunna tamkar mai neman gafara.

“Gani Kawu.”

Da alama bai masan meyasa ya kira ni ba, Domin sai cixan lebe yake alamun tunani. Babu abinda nayi masa wallahi, Kawai dai neman yadda zai dake ni yake yi ko tozarta Innar mu.

“Ruwan tuk’a tuk’a zaki ebo mani, kwarankwatsa idan kika da’de baki kawo ba sai na lahira yafi ki jin dadi.”

Na ‘kara kasa da kai na ina kukan zuci, duk ga yara nan ciki harda almajiran gidan amman babu wanda zai ebo masa ruwan sai ni? Ga yunwa dake addabar ciki na sai kukan agaji yake. Rankwashi ya sakar min a kai na nai saurin dafe wajen,

“Toh kawu a me zan ebo maka?”

“Tambaya ta kike? Lalle figegiyar mahaifiyar ku ta kara lalata ku.”

Mik’ewa yayi daga kan bokitin da yake zaune ya shiga zundumawa Innar mu kira ba ‘kakkautawa,

“Ke Kaltume, Kaltume, kina ina ne? Zaki fito ko sai na raunata shegiyar yar nan taki?”

Innar mu dake sallar nafila tai hanzarin sallamewa, cikin sauri tafi to tana dafe kirji,

“Kawun su, ya akai? Lefi ta maka? Dan Allah kayi mata hak’uri.”

A dai dai lokacin Usaiba tai kukan kura ta cakumi Bintalo tana yage dankwalin kanta, Tun d’axu suke fada.

“Shegiya mai kan ‘kwakwido.”

Cewar Usaiba ta fadawa Bintalo tana tsurtar da yawu a gefan Bintalo, Bintalo ta kece da daria tana nuna Usaiba da hannu,

“Shegiya wada, tamkar a kife ki da kwando, da ido aciki munafuka.”

Baba ila yaja tsaki yana nuna su da hannu,

“Ku fitar min a hanya, ko nai sanadin barin mutum anan gidan.”

Innar mu dake saukowa daga bene tafara girgiza kanta tana mai cewa da baba ila,

“Kayi musu hak’uri sharrin shed’an ne.”

Kawu ila ya kece da daria, hade da tafa hannaye kamar mace, Cikin kasakantaccen kallo ya dubi Innar mu,

“Toh munafuka algunguma, Sa’idinawa ana ruwa kuna irgawa masu bacci da ido d’aya.”

Innar mu tayi shiru kanta a ‘kasa, Bintalo ta buga zanin ta tana sakin gud’a,

“Kuji min annamimiya, Ke har kina da bakin magana? Dangin mayu uwar shegiya, acike nake da ke wallahi kika kuskura wata kalma tafito daga bakin ki sai na daka shegiyar yar ki.”

Innar mu tayi shiru kanta a ‘kasa, na goge hawayen da ya fara tsere a fuska ta. Wai shin yaushe zamu dandani farin ciki ne? Wannan wacce irin musibace ace yan uwan mahaifin ka na jini su dinga kyamatar ka suna la’antar ka.?

‘Ya ALLAH ka nuna min ranar da zan mai dawa su Kawu ila martani, domin nagaji da rashin ‘kauna da tozarcin da suke mana shekara da shekaru. Ameen ya hayyu ya qayyum.’

Na fa’da a zuciata ina mikewa tsaye.

Bokitin da ya mike akan sa na d’auka na fice cikin sauri, Usaiba dake gefe ta ja tsaki tai hayewar ta sama tana mai jifan su da munanan kalamai. Har naje tuk’a tuk’a na dawo ina jiyo muryar kawu ila yana zuba magana da alama da Innar mu yake domin ina jiyo ta tana bashi hak’uri, A soro na tsaya ina mai baje kunnuwana don jiyo zancen su,

“Ki jawa shegiyar ‘yar ki kunne, dan billahil azim idan ta sake nanata hali irin na yau sai nayi maganin ta. Kina jina ko?”

Innar mu tai hanzarin ka’da kanta alamar Eh kafin tace,

“Toh Kawun su! Insha Allahu ba zata kara ba, ayi mata uzuri.”

Hawaye na na goge, ina takaicin banyi komai ba, amman kusan kullum sai an laqaba min sharri kawai don Innar mu ta kaskantar da kanta taba su hak’uri, shi yasa duk wata bolar su akan mu suke zuba ta. Shin a haka zamu dawwama cikin bakin ciki? Cikin zucia ta na shiga nanata,

‘Ya Raheem sa’adneey min kullu amr!’

Har bandaki na kai masa ruwan, sannan na koma bakin kofar dakin sa,

“Kawu! Ga ruwan na kawo”

“Annamimiya! ‘Bace min daga bakin kofa.”

Jiki ba kwari na mike nai hayewa ta saman mu. Cin karo nayi da Alawiyya ta yab’a jambaki a baki tana kwarkwasa, Bintalo dake gefen ta tana gyara mata mayafi tai bake bake a matattakalar benen da zan wuce. Na tsaya ina jiran ta wuce,

“Meye kike bin ta da kallo? Zaki ‘kasa da idanun ki ko sai na zuba miki mari?”

Matsawa nayi nesa dasu kai na a ‘kasa, Kawu Dawood ya fito daga dakin su yana aswaki, shi gaskia ba shida hayaniya irin tasu Kawu ila, Kawai dai shi matar sa ce zata nemo abinci ko da kuwa bara za tayo, babu inda zashi kullum yana kwance a daki tunda aka kore shi daga wajen aikin sa, cikin tab’e baki ya dubi Bintalo,

“Hayaniyar menene haka kuke yi?”

“Hayaniyar da akai ai da yawa, wacce daga ciki?”

Ya tofar da yawu ya cigaba da kuskure bakin sa kafin yace,

“Hayaniyar yanzu, Meyasa waccen yarinyar ke rakub’e a gefen ku? Ki bata hanya ta wuce mana.”

“Oh shegiyar can? Take Alawiyya tai a kafa ta kuma nemi ta bangaje ni kan naki matsa mata ta wuce..”

Ware idanuwa nayi jin sharrin da Bintalo ta hadamun. Cikin rawar murya nace,

“Kawu Dawood wallahi ban aikata ko d’aya daga ci...”

“Wuce ki tafi.”

Ya fadamin batare da yaji karashen magana ta ba, rabawa nayi ta gefan su na wuce dakin mu. Ina shiga na tarar da Innar mu tana lazimi, autar mu kuma tana aikin da aka basu a makaranta. Kayan makaranta na nacire na d’aura zani, wanka kawai nakeso nayi idan naci abinci. Kwanon gabanta Innar mu ta matso dashi kusa dani, budewa nayi ina murmushi, garin kwaki ne da mai da yaji. Na wanko hannu na a tukunyar bayan mu sannan na fara handama shi a baka bayan nayi bismillah. Ina gama cinyewa nai hamdala, nacaccen hijabi na na zura na dauki robar sosan wankan mu da sabulu irin ‘danyaka ‘dinnan na naira ashirin. Na hada da bokiti na sauka kasa don yin wanka. Da mutum acikin band’akin, hakan ya sanya na zauna a dandamalin kitchen din ‘kasa wanda matan Kawu ila ke amfani dashi. Bude kofar bandakin akai, na daga kai na don ganin wanda zai fito. Innatuwa ce tafuto wato matar Kawu Khamis, sai baje hanci take yi da alamun kashi tagama kasayarwa.

Shiga nayi bayan nayi adduar shiga bandaki, Wanka nayo nima na dan karkace na sau kashi na wanda dakyar yake fitowa sakamakon garin da naci, saman mu na haye, na shafa mai hade da sanya kayana dake karkashin kwallar mu, hijabin islamiyya na zura na dau yan littafan da muke yi, nayiwa Innar mu sallama kan sai na dawo, Tare da yiwa autar mu kashedin kar tayi latti. Saboda manya mu karfe uku muke tafiya yara kuma sai karfe hudu.

Ta gidan su Fadila na biya, a bakin gate din su muka hadu da ita tana sanya hijabi, Tana gani na ta dashare hakora, nayi murmushi ina tsaye a bakin kofa,

“Tawan..”

Fadila ta fadamin tana mikomin jakar ta, karfa nayi na rik’e ina jujjuya littafan hannu na,

“bestie ya kike? Kice yau baki makara ba kenan.”

Daria tayi tana harara ta,

“Dalla na dinga makarar kenan? Yauwa na taho miki da lessons din da akai mana yau, Idan aka fita free period sai na koya miki..”

“Nagode bestie! Allah ya bar zumuncin mu har gaban abadan.”

“Ameeen!”

A tare muka tafi, hannuwan mu saqale dana juna, Idan ka ganmu dole ne mu birge ka saboda yadda muke ba amintar mu hakkin ta, hakika Fadila ta xarce aminiya ta zama hamimiya kuma yar uwata ta jini mai son cigaba na, duk karatun da ake musu a makarantar su sai ta koya min, sannan tanada lesson teacher dake zuwa har gidah ya koya mata karatu ranar asabar da lahadi, shima dik sai ta koya min, B’angaren Islamia ma duk abunda bata gane ba ina koya mata, kasancewar ni ce monitan ajin mu sannan nafi kowa kokari da hazaka ba yabon kai ba. Idan kayan dadi suka yi a gidan su sai ta kawomin nata rabon, bama b’oyewa junan mu komai, mun kasance muna bawa junan mu shawara duk sanda hakan ya kama.

Akan hanya muka hadu da Haysam, wato d’aya daga cikin samarin dake nacin so na, Ina ganin sa na bata fuska na shiga zame hannu na daga na Fadila saboda nasan dole sai ta tsaya tasa munyi magana dashi ala dole. Haysam matashi ne mai jini a jika, dan shekaru goma sha tara, yanada kyau da kamala, sannan ‘da ne ga Alhaji kabeer wafa, wato manajan chanjin kud’i na b’angaren Zaria. Banason Haysam saboda ‘dan masu ku’di ne ni kuma yar talakawa ce, bayaga haka ma banason kula kulen samari ga kuma sharadin Yayan mu daya hanani kula kowannen su. Saboda na tsaya na fuskan ci karatu na sosai. Tundaga nesa Haysam ya tsuramin ido yana bin kallo na tundaga kan yan yatsun kafata zuwa kirji na da fuska ta,

“Dan iska..”

Na fada ina cuno baki na gaba ina sake k’ok’arin kwace hannu na daga na Fadila ganin yadda take masa murmushi alamin ya matso kusa ga ni. Kin sakin hannu na tayi, Hakan yasanya Haysam tunkaro mu yana taune leben sa na kasa.

“Batoul!”

Yakira sunana yana sakin murmushi, na kauda kai na gefe ina sake hade fuska ta, Ganin hakan ya sanya shi mai da kallon sa ga Fadila,

“Aminiyar mu, ya kike?”

“Lapia lou saurayin mu. Ya gidah?”

“Alhamdulillah fa! Islamiyya zaku ne?”

Ya tambayeta yana mai sake maida kallon sa fuska ta.

“Eh wallahi can zamu.”

“Nazo nayi rakiya?”

“Meze hana? Bismillah!”

Jerawa mukai dashi muna tafiya, Fadila na tsakiyar mu suna hira, lokaci zuwa lokaci yakan sako sunana ko zanyi magana, Ni kuwa shiru nayi naki tankawa har muka k’arasa makaranta. Sallama su kai da Fadila ya tafi gidah mu kuma muka shjga ciki.

“Ki dena abunda kike Allah! Menene makusar Haysam? Meyasa bakya son sa? Akan wane dalilin zaki dinga garashi tamkar taya? Haba Batoul! Ki dena yiwa samarin ki haka Allah. Wasu ma ido rufe suke neman masoyan ke kuwa kin samu damar ki a hannu kina neman ta kubce miki, kiyi tunani tawan.”

“Bestie kenan, Duka-duka shekarun mu nawa? Sannan ko ajin farko na siniya sukul bamu shiga ba, bayaga haka Haysam dan masu hannu da shuni ne, Banason hada kai na da wanda suka fini a komai, har a addinan ce a har kullum so ake ka kalli na ‘kasa da kai ba wanda yake saman ka ba ya kere ka. Sannan sahibin ki ma wato Yayan mu ya hana ni kula samari.”

Fadila ta fad’ad’a murmushin ta jin na ambaci masoyin ta.

“Hakane kuma. Toh Allah ya zaba mana mafificin alkhairin sa Ameen.”

“Ameen”

Aji muka shige, aka fara tilawar karatu kafin Ya Sayyadi ya shigo. Haka dai mukai ta tilawa sannan aka kada kararrawar sallar la’asar. Sallah muka fita muka yo sannan muka koma aji, Malam yabi daliban ajin mu d’aya bayan d’aya ya karbi haddar suratul Yasin da Ashmawi. Ya fita sai Malamin dake mana Bulughul Maram da Buhgayatul Muslimeen ya kara mana, daga ‘karshe mukai Sira da kuma Usulul Thalatha.

•••••. ••••. •••••. ••••.

Haka dai rayuwa ta cigaba da garawa, Safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u. Yau da dadi gobe babu, A haka dai akai mana hutun karshen aji, a daddafe muka je Shema k’auyen su Innar mu ni da autar mu mu kai hutu. Ana’i sauran kwana ki biyu za’a koma makaranta muka dawo. Dan kudin da muka samo a Shema dasu Innar mu ta yanka mana sabon inifom aka dinka mana, ta sai mana takalma na makaranta da safa yar gwanjo. Takuma yi mana dan tsince tsincen kayan abinci, Ciki har da rabin buhun gawayi da taliya yar aune, dari ukun kai kuma ta auno kananzir da manja, nera darin kai kuma ta bani kan na ajiye mana kudin birek ne na makaranta ni da autar mu har tsawon kwana ki uku. Dama gashi ni na shiga babba aji na uku na jiniya sakandire, Autar mu kuma ta shiga ajin firamare na uku. Haka dai muka shiga rufawa juna asiri don ciyar da kan mu.

Ranar wata asabar muka tashi da tashin hankali, Domin ogan su Yayan mu wato mai wurin kanikancin su ya sayar da wajen ga wani mutumi inda za’a mayar da wajen filin yin biki na kudi dake ‘katon waje ne. Gefe kuma wajen wanke mota. Yayan mu yaci kuka ko ince munci kuka duk kanin mu, Innar mu kuwa muryar ta har dashe wa tayi tsabar kuka. Kasa zuwa makaranta muka yi ni da autar mu. Yayan mu mai share mana kukan mu yanzu shima abun a taimaka masa ne. Tsawon kwana ki uku muka dauka bama zuwa makaranta. Islamiyya kuwa munma ajiye babinta a gefe, domin bamu da tabbacin samun kudin biyan islamiyyar na wata wata. Yayan mu ya buga ko’ina amma babu aikin yi, domin duk inda yaje nema sai ace sai ya kawo takardar kammala sakandire tukun.

Da dare tare muka hadu muka ci kwadin tafasa da Innar mu ta samo a gidan da take wankau. Sannan muka dora da taliya da mai da yaji, Innar mu ne gefe tana jin rediyo, Mu kuma mu da Yayan mu muna hirar mu. Har lokacin bacci yayi, Yaya ya dauki yar taburmar sa da net ya daura a tsukukun kofar dakin mu ya kwanta lokaci d’aya bacci yai awun gaba dashi, Cikin dare fitsari ya ishe ni na mike daga kwancen da nake daure da zani na zira hijabi na dauki cocilan mu na shiga haska gabana dashi, a hankali na tsalle Yayan mu na sauka bandakin ‘kasa na shiga zurara fitsari na ahankali ina rufe bakina sakamakon bahaguwar hammar da naketa saki wadda kallo d’aya zaka min kasan bacci ne a idanu na. Ina gamawa nai tsarki na fito daga bandakin baki na dauke da addua. Ina hawa bene mu kai kicibus da Islaha kanwar Bintalo wadda tazo daga kauyen su, Ta kasance tana mutuwar son Yayan mu. Gashi Yayan namu ko kallon ta bayayi idan suka hada idanu ya zabga mata harara. Hango Yayan mu nai ya tattare kayan kwanciyar sa zai fita waje, Da alamun takura masa tashiga yi. Ni dai daki nai shigewa. A hankali a hankali nake jiyo nacin da Islaha ke yiwa Yayan mu,

“Sakarmin hannu dalla malama”

Da sauri na fito daga daki ina kallon yadda Islaha ta rike hannun Yayan mu dumu-dumu acikin nata. Sai zabga mata harara yake yi yana kokarin kwace hannun sa taki sakin sa. A dai dai lokacin Bintalo tafito daga daki kallo d’aya tayi musu ta daura hannuwan ta akai, cikin sakin wata irin shegiyar ‘kara tace,

“ihuuuuuu Gardiiiiiiiiii”

Ai bata rufe baki ba mutan gidan mu suka fara firfitowa daga dakunan su, kankace me? Anyi cincirondo kowa yana kallon su Yayan mu, Islaha daure da zani ba dankwali a kanta, Shi kuma Yayan mu sanye yake da wando dogo babu riga ajikin sa, sakamakon zazzafan zafin da ake zubawa yasa tun da zai kwanta ya cire yashiga cikin net.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un..!”

Itace kalmar da Yayan mu yake ta furtawa, lokaci d’aya hawaye suka shiga yar tsere a fuskar sa. Nima na goge nawa hawayen tare da tsugunnawa, sakamakon rawar da kafafuna suka shiga yi sun kasa daukar gangar jiki na tsabar tashin hankali. Na dubi Bintalo dake sakin wani makirin murmushi tana tafa hannuwa,

“Shege wan shegiya ‘dan shegiya! An tsotsa a mama ai dole a nuna hali, Toh ‘karshen tuka-tuka tik, Allah ya kama ka. Tun ranar da yarinyar nan tazo gidan nan kake bibiyar t...”

Bata karasa ba Innar mu tayi hanzarin shiga tsakanin su, Ta kwace hannun Yayan mu daga na Islaha, cikin rawar baki da jiki tace.............
——
******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋




MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


_*SHAFI NA HUDU_*

•••

“Ya ishe ki Bintalo, Banason tashin hankali shiya sa bana biyewa ayi dani idan hayaniya ta kaure a tsakani. Saboda haka kada ki ‘kara sheganta min yara, ‘ya’yana yan halak ne. Allah ya isar mana idan har kika kara aibata su. Banda bina da ‘yayana da sharri ba abinda kika iya, Allah ya tsare mu daga miyagun halayen ki...”

Tunda Innar mu tafara magana har ta gama gaba d’aya kowanne acikin yan gidan mu mamaki ne dankare a zukatan mu, idanuwa muka zuba mata ni kam harda ‘kyak’kyaftawa ko mafarki nake, domin tunda nake bantaba ganin Innar mu ta maida wa wani martani ba fyace yau. Da alamun an kaita mukura, dadi ne ya mamaye ni ganin tafara samawa kanta ‘yanci. Na dubi Bintalo yadda ta daskare a wajen tana kikkifta idanuwa, da alamun maganganun da Innar mu tayi sun shammace ta. Cikin tunanin dana tafi na sake jiyo Innar mu tana yiwa Yayan mu magana,

“Wannan yaron (Saboda ‘dan fari ne) Inaso ka gayawa kowa yadda ku kai da yarinyar nan data bika da sharri.”

“Innar mu wallahi kawai ina kwance a cikin net na jiyo ana kiran sunana, Sai kawai na mike tsaye ina kallon gabana ganin mai kiran nawa, Ashe ita ce. Tasa hannu kenan zata bude min net din na mike tsaye gaba d’aya na tattare tabamar tawa da net din zan koma langalangar almajirai, Toh a lokacin ma na hango Batoul ta dawo daga kasa da alamun bandaki taje. Bayan shigar Batoul daki ke da wuya kawai naji ta rik’o min hannu, nai nai ta sake ni ta’ki, Nasa d’ayan hannu na kenan zan fincike sai Bintalo tafito daga dakin ta tana kurma ihun gardi, Wallahil azim hakan akayi. Daman tasha tara ta a koina ne tana gayamin kalaman so. Gata nan a tsaye idan ‘karya nai mata.”

Bintalo tayi kukan kura tana

Please Login or Register in order to submit comment