Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta. Bokitin zaman sa ya dakko a daki ya fito dashi tsakar gidan ya ajiye. Ya shiga zundumawa sauran kawunnin mu kira,

“Ishaq, Khamis, Dawood kuna ina? Ku sakko ‘kasa akwai magana.”

Haka yaita kwalla musu kira, Yana kuma sake tura yaran su su kira su. Ina gama wanke wanke na na dora a ka ina sharce ruwan jikin buhun sosan wanke wanken mu. Domin dashi muke wanke wa. Har na kai mattalakar bene na uku Kawu ila ya callara wa sunana kira,

“Ke Batoul kira min shegen Yaron nan mai kunnan ‘kashi wanda ya raina na gaba dashi. Kice yazo nan dan uban uban sa.”

Gyada kai nayi hade da doriyar,

“Toh Kawu.”

Ina karasa hawa na ga yayan mu na zura takalman sa a kafafun sa. Babu alamun fargaba ko ‘dar a zuciyar sa. Da alamun ma ya jiyo shi. Shi yasa ya fito daga daki don amsa kiran sa. Cikin mintina kalilan su Kawu Ishaq sun hallara a tsakar gidah ciki harda Kawu Dawood dake jera hamma ba ‘kakkautawa, Da alamun Hansatu matar sa bata samo musu abun karin kumallo ba a yawan neman abincin data tafi tun farar safiya. Ta sama nake hango su ni da sauran magulmatan gidan mu. Wasun su kuwa tuni sun sassauka kasan sun yiwa kansu wuri tun d’axu. Innar mu kuwa na kwance tana baccin ta. Da alamun acikin magungunan akwai me kashe jiki. Dadi naji data samu bacci domin da tuni idanun ta biyu za’ai wannan tashin hankalin, Abu biyu su hade mata a rai.

Daga gefe Yayan mu ya zauna akan dan dandamalin kusa da rijiya. Cike da girmamawa ya dan rissinar da kansa yana gayshe da wa’enda d’axu basa gidan lokacin da ya dawo. Wato Kawu Khamis da Kawu Ilyasu.

“Kawu Ina wunin ku?”

“La..”

Kawu Khamis bai karasa ba Kawu ila ya tari numfashin sa,

“Da bamu wuni ba zaka ganmu a haka ne? Dan uban ka. Kaga ja’irin yaro wanda ya rena na gaba dashi.”

Shiru Yayan mu yayi kansa a kasa bai tanka musu ba. Kawu ila ya ja tsaki ya sauke,

“Wato ga mahaukaci ina magana kana shiru ko?”

“Allah ya baku hak’uri Kawu.”

“Ha’kurin uban ka? Kai uban waye ma ya baka damar tako shegun kafafun ka kazo nan gidan. Ba munce ka dakata ba sai sanda muka neme ka? Wato kai kana jin kanka ka zama wani abu shine za ka tsallake maganar mu?”

“Allah yabaku hak’uri Kawu”

Yayan mu ya sake basu hak’uri a karo na biyu yana yak’e. Kawu ila ya taso zai mareshi Kawu Khamis ya dakatar dashi ta hanyar rike masa riga.

“Da hak’uri yai gabas yamma nayi dan uban ka. ‘Dan tasha ka zama ne? Dan uban ka ana magana kana washare hak’ora kana bada hak’uri. Na hada ka da ha’kurin na gunguri uban ku.”

“Sittin ta ubangiji duk mana’kisar uwar su ce. Tana ‘daka tana ji ai.”

Bintalo tafada tana watsa hannu baya. A tsaye take kamar ta hadiyi muciya a kusa da Kawu ila yadda kukasan zata koma cikin sa. Gaba d’aya a hargitse take ranta idan ya kai miliyan a b’ace yake. Yadda kukasan ta fasa kuka dan tsabar bakin cikin dawowar Yayan mu.

“Ke Karimatu! Karimatu!”

Kawu ila ya shiga dokawa Innar mu kira.

“Bata jin dadi Kawu! Tayi bacci sakamakon maganin zazzabin data sha.”

“A gidan uban ka? Matar da sassafe ta fita yawon ta zubar kace wani bata da lapia.”

“Kayi hak’uri Kawu wallahi batada lapia.”

Yayan mu ya fada yana hada hannayen sa biyu alamun ban haku’ri. Tsaki Kawu ila yaja yana sake dafe cikin sa.

“Bara na shiga bandaki na fito. Zaka fada mana dalilin daya sa ka ketare maganar mu ka dawo dan uban uban ka.”

Yana gama fad’a ya shige bandaki.

“Algungumai..!”

Bintalo tafada tana zama akan bokitin Kawu ila. Duk sauran kawunnin mu su kai shiru, Kawu Dawood kuwa na gefe yana aikin sakin hamma. Duk jiran Kawu ila ake ya fito daga bandaki aji ta bakin sa. Shi Kawu ila nacan bandaki yana katse gumi. Sakin gudawa kawai yake tsiiii. Muna jiyo sautin zubar ta har sama. Ya dau lokaci kafin ya fito yana dafe da cikin sa. Bintalo ta sauka daga kan bokitin shi kuma ya zauna yana dafe cikin sa hade da rintse idanun sa da alamun katsa masa yake yi. Cikin dauriya kamar dole ya sake duban Yayan mu,

“Dan uban ka! Akan wane dalilin za kai fatali da umarnin mu k.....”

Bai ‘karasa ba cikin sa ya sake katsawa tuni iska ta kufce masa ya shiga jera sakin wata irin tusa mai wahalar rubutawa. Sai tsami da hamamin gudawa. Ji kake,

‘Siiiit...’birr.. ‘but’but.. dadar...’

Ba shiri Bintalo taja baya tana rufe hancin ta da d’ankwalin rigar ta. Ba ita kadai ba duk sauran wa’enda ke wajen sai da suka rufe hancin su. Kawu Dawood ya kasa rike dariyar sa. Ya shiga darawa yana rufe hancin sa. Kawu ila tamkar ‘kasa ta tsage haka yaji. A kunyace ya mike yana rike wandon jikin sa ta baya. Da alamun ta fara zuba a zaunen da yake. Bandaki ya shige yan rufo kofar da karfi. Sautin futar gudawar sa ce kawai ke zuba ji kake ‘kurusss bul’bul’bul. Amman dan masifa yana cikin bandakin ma bai fasa magana ba,

“Bara na fito dan uban ka, Ka gaya min hujjar da yasa kayi fatali da uzurin mu. Kai kuma Dawood zaka gayamin abunda ya baka dariya. Zan fito duk zaku yi bayani kai da shi. Domin naga alamun kai ne ka tsayawa shegun yaran nan suke yadda suka ga dama a gidan nan......”

Babu wanda ya tanka masa, Shi dai Kawu Dawood sai da yai dariyar sa ishasshiya tukun sannan ya cigaba da jera hammar sa tamkar zai hadiye yan gidan baki d’aya. Cikin tafiyar yan kaciya haka Kawu ila ya fito daga bandaki daga shi sai rigar sa iya gwiwa, Wandon rigar a hannu yai saurin shigewa daki. Bai wani jima ba ya fito sanye cikin wasu kayan yana ‘bata rai, Ya goggoge sinadarin zuciar sa. Ma'ana bokitin karfen sa na zama. Wanda ya zama tamkar na gado ko na wani sihirin. Domin tun ina karama nasan bokitin gashi har girmana yana nan sai dai yasha walda awajen yan walda. Ya tsufa kwarai matuka. Amman ya kasa rabuwa dashi. Ni kuwa dana dube shi sai sautin tusoshin daya dinga saka d’axu nake tunawa. Zama yayi akan bokitin yana batsewa. Ya ja majina kafin yace,

“Toh zamu ‘dora daga inda muka tsaya....”

•••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*IGIYAR ZATO...💕*


_*1️⃣5️⃣_*


Kowa ya zura masa idanu. Ana jiran abunda zai ce. Waya ga ‘karamin su babban su. Yatsa yasa yana mai nuni da Yayan mu yana karkada masa shi,

“Kai ga saurayi mai jini a jika ko? Da har xamu gindaya maka sharad’i akan kada kazo sai mun neme ka, Shi ne za ka sa kafa kai shuri da zancen mu? Wato kai ‘kwankwararren marar kunya. Shin meya sa ka ‘ketare umarnin ka dawo?”

Yayan mu yai murmushi kafin ya dubi Kawu ila. Cikin gaskiyar sa yace,

“Ba ‘ketare umarnin ku nayi ba Kawu. Kawai dai nayi kewar gidah ne, Shekaru hudu ban ga mahaifiyata ba. Batasan a wane hali nake ba, Ni ma kuma zucia ta na ayyanamin abubuwa kala kala. Na kasa nutsuwa ne Kawu! Shekaru hudu na dauka bangan ku ba Kawu..”

Kawu ila yaja tsaki yana yamutsa fuska,

“Kaji makaryaci, baka ga mahaifiyar ka ba dai da yan uwan ka. Toh ka bude kunnuwan ka dakyau kaji. Kana saurare na ko?”

“Eh Kawu!”

“Toh yadda kazo haka zaka koma yanzu ba sai anjima ba.”

“Kayi hak’uri Kawu. Saboda ko gaisawa ba muyi ba da Innar mu, Tana kwance ba lapia.”

“Tabdijan! Ni kake cewa ba zaka tafi ba. Kaci uban uban ka.”

“Kayi hak’uri Kawu. Ba kin bin maganar ka nayi ba. Afuwan!”

Kawu ila yaja tsaki ya sauke, Kawu Khamis dake gefe yana aswaki ya dubi yayan mu,

“Kai Najibu tukun nama awane garin kake ne. Daka bar nan ina ka tafi? Sannan wacce sana’ar kake yi ko karatu kake yi?”

Yayan mu ya girgiza kai cikin girmamawa yace dashi,

“Dana bar nan Shema naje, Daga can kuma bayan wani lokaci sai na koma kano.”

“Me kakeyi a kanon? Sana’a ko karatu?”

Sai da Yayan mu yayi shiru na dan wani lokaci tukun sannan yace da Kawu Khamis,

“Almajiran ta na.,”

Bai karasa ba Bintalo ta shiga babbaka daria tana tafa hannaye. Gyara xaman d’ankwalin kanta tayi tana murmushin jin dadi,

“Almajiran ta. Ashe mun samu babban ‘kolo agidan? Dole a taho neman wahidin sadakayiya, Iya almajiri bara Iya. Iya ko gari ne ba suga. A hayye nanaye...”

‘Ayiriririrurururiii” Ta karasa magana tana sakin gud’a. Hade da gyara zaman gyalen ta, ficewa tayi tana nanata,

“Toh sai anjiman ku na tafi biki. ‘Dan Malam Au ‘kolon gidan mata tara idan Xaka tafi na baka na ‘dan sukari. Almajiran ta ba dadi. A hayye nanaye”

Duk sai gidan kuma ya hautsine da maganar almajirantar Yayan mu. Na dubi Yayan mu yadda yayi tsaf dashi yayi kyan gani, Idan ma almajirin ne shi menene? Ba karatu bane ba na neman duniya da lahira? Alhamdulillah da ya zama dan tasha ai gwara almajirantar.

“Almajiran kace ko? Toh awacce makarantar allon kake a kanon?”

Kawu Ishaq ya tambayi Yayan mu, Yayan mu ya sake daidaita zaman sa kafin yace,

“Makarantar allon Gwani Bukar dake unguwar bachirawa.”

Kada kai Kawu Ishaq yayi alamun gamsuwa. Kafin ya sake tambayar sa a karo na biyu,

“Naga dazu ka wuce da kaya nik’i-niki kayan menene?”

“Kawu kayana ne dana tafi dasu. Sakamakon can din ana sace mana idan mutum bai da gidan aiki.”

Kawu ila ya kece da daria har yana buga ‘kafafun sa a kasa, Sai da yau mai isar sa tukun sannan ya dubi Yayan mu,

“Waya baka kudin zuwa nan din?”

“Uwar daki na dake can ce tabani.”

“Toh kwana biyu na baka jal kayi ka koma almajirantar ka. Waya ga almajiri na’am! Zo ka karba.”

Kawu ila ya karasa fada yana kecewa da dariya, Da alamun almajirantar da Yayan mu yace yanayi ba karamin dadi suka ji ba. Domin har gaban abadan sunfi son su ganmu cikin kaskantacciyar rayuwar da babu jin dadi a tattare da ita sai wahala, kullum jiya i yau babu cigaba. A hankali ya mike tsaye ya nufi sama, ganin ya taho yasa na koma d'aki ina jiran ya shigo. Kamar wani marar lafiya haka ya samu waje ya zauna, kallo na yayi yana murmushin yak'e, alamun maganar da zai min ba mai dad'i bace. Ya kira suna na yana kallon Innar dake ta bacci.

“Batoul..”

“Na'am Yayan mu.”

“Yau zan juya zuwa kano, zama na a gidan nan hatsari ne. Inna bata da lafiya, tana bukata ta a kusa da ita, amman hakan ba zai yiwu ba, saboda zamana zai sake sanya mata wani ciwon da irin kalaman da su Kawu zasu dinga jifa na dashi. Batoul nasan kuna da hakuri, toh ina son ku kara akan wanda kuke dashi, zan koma kano yau saboda ko na amince zan zauna anan bani da wajan kwana, Allah yana tare daku, kuci gaba da hakuri wata rana sai labari.”

Yana kaiwa nan yasa hannunsa ya rik'o k'afar Innar mu, idanunsa a lumshe da alama kuka ne yake neman kwace masa amman ya hanashi fitowa. Ni kuwa tuni na fara kuka domin munga samu munga rashi, ko Yayan mu bazai d'auke mana komai na rayuwa ba, ganinsa ma kadai jin dad'i ne a rayuwar mu. Amman yanzu munaji muna gani zai koma inda ya fito saboda tsangwamar 'yan gidan mu.

“Yayan mu dan Allah ka zauna karka biye musu, munji dad'in ganinka yaya, ka daure kayi mana kwanaki biyun da suka baka dan Allah”

Cikin matsanancin kuka na karasa maganar, ya tashi tare da rik'o hannuna yana so ya sanya idanunsa cikin nawa amman naki yarda.

“Batoul rufin asirinku da nawa nake son karewa, tunda kika ga sun nuna rashin amincewar su na dawowar nan da nayi, toh lallai akwai wani makircin da zasu sake kullamin, wanda zai sa nayi nadama idan ban tafi ba. Kuyi hakuri Batoul ku zauna Allah yana tare daku, gashi banda wasu kud'in da zan iya bar muku, nima sai na fita zan samu wani abun nayi wanda zai sa na samu kud'in zuwa kano. Amman ga wasu 'yan kaya na sabulun wanka dana wanki, sai sukari da makaroni leda uku taliya guda biyu da shinkafa rabin kwano, da d'an wani wake baifi gwangwani biyu ba, nasan zaku kwana biyu kuna amfani dasu, akwai wata riga 'yan gwanjo ne guda biyu babba da karama ki dauki d'aya kiba Auta d'aya, Allah ya bawa Innar mu lafiya yasa kaffara ne, na tafi Batoul bana son ki nunawa kowa har sai na bar gidan nan.”

Wannan shine bankwanan da muka yi da yayan mu, yasa hannunsa ya share min hawayen da suke ta reto a fuskata, sannan ya juya zuwa wajan da ya ajiye jakarsa, ya rataya ya kalli Innar mu sosai kamar yau ya fara ganinta, kafin ya wuce da sauri ya fita, ina kyautata tsammanin kuka yake yi shima. Da gudu nabi bayansa amman abin mamaki har yakai kasa ya fice tamkar walkiya.

Da gudu na koma d'aki tare da zubewa a k'asa ina rera kuka, na rasa wace irin rayuwa muke yi a cikin gidan mu, kowa yana tare da 'ya'yansa a gabansa, amman mu sai neman tarwatsa mu ake yi, shin menene dalilin? Rashin uba ne ko kuwa rashin kudi? Duk na kasa ware wane ne a ciki yasa muka shiga cikin wannan azababbiyar rayuwar.

“Mai sunan uwa.”

Naji Innar mu na kirana a hankali, wacce da alama sautin kukan da nake yi ne yasa ta farkawa. K'ok'arin goge hawayen nake amman yaki tsayawa hakan ne yasa na kasa juyawa na kalleta har sai da ta kuma kiran sunana sannan ne na juya ba tare da na kalleta ba.

“Ya aka yi kike kuka? Menene?”

Na kasa magana sai wasu hawayen ne da suka sake b'allowa, ta fara k'okarin tashi zaune nayi saurin matsawa kusa da ita ina girgiza mata kai.

“Bakya hanani zama ba mai sunan uwa, barni na tashi naji matsalarki, shin ina Yayan ku?”

Ai kamar ta dokeni bansan lokacin da na bud'e baki ina shesshekar kuka ba, ALLAH sarki tuni ta fara shinshino akwai matsala, ta cije lebenta na sama tare da cewa.

“Yana ina?”

“Ya koma kano Innar mu, wallahi Inna su Kawu ila basa kaunar mu. Shin yanzu da suka hanashi zama ina suko son yaje a karb'e shi? Nan fa a k'a'ida gadon sa ne yana da iko da gidan nan amma kiri-kiri sun hanashi zama Inna, sam kawu ila ba zaiji koda k'amshin aljanna ba bare ya shig....”

“Ya isa haka, Iliyasu mahaifine a gareku dole kuyi masa biyayya. Karna sake jin kin aibata kowa a cikin zuri'arku kina jina?”

Ban amsa ba, saboda kokawar da na tsaya yi da numfashi na jin yana barazanar d'aukewa. Ta kuma kallo na tare da gyara zama tace.

“Ko bakiji ba ne?”

“Naji Innar mu”

Na fad'a dakyar kamar zan had'iye rai na. Haka muka zauna mu biyu babu mai cewa komai, kowa da abinda zuciyarsa take sak'a masa tsawon lokaci. Daga baya ne na mike na fara firfito da kayan da Yayan mu ya kawo mana, ALLAH sarki ko yanzu ya samu na motar 'oho' ALLAH kadai masani, cikin zuciyata na dinga yi masa fatan alkairi har na kammala gyara inda zan ajiye komai, daga bisani na dora mana abincin dare, duk da Innar mu har yanzu bata ce komai ba amman daka ganta kasan cewa akwai tsantsar damuwa a tare da ita.

Da daddare ana kiran sallar isha'i ina kasa ina alwala kasan cewar ko bani da tsarki ina zama da alwala, muryar Fadila ce ta katse min tunanin da na shiga ina cikin wanke k'afa. Da murna na amsa sallamar da tayi na mike ina gyara zaman hijabi na.

“K'awas kece da daddare haka?”

“Nice Aminiyar, wani labari naji shine nazo dan naji tabbaci, wai da gaske Yaya Najibu ya dawo?”

Naja dogon numfashi tare da kallon mutanan dake shawagi a tsakar gidan mu, yanayin fuskata ya canza, na ce mata.

“Kawas yazo, amman kuma ya koma tun d'azu.”

“SubhanAllah! Da sauri haka?”

“Ai kuwa dai, a can wajan da yake d'an aiki ne suka yi masa kiran gaggawa shi yasa ya koma”

“Kai amman naso ganin shi wallahi, nasan zuwa yanzu ya kuma zama babba ko?”

Murmushi nayi mai sauti ina k'ok'arin jan hannunta dan mu hau sama, sai tayi saurin dakatar dani ta hanyar rik'oni tana cewa.

“A'a daga nan ma ya isa, sauri nake yi, ki gaishe da Inna idan kin shiga daki.”

Na rausayar da kai, ganin ta juya yasa na rakata har zaure, A nan ne na tarar dasu Basma da Farida zasu fita, nayi saurin dakatar dasu ina cewa.

“Ku kuma ina zuwa da daddaren nan?”

“Shagon Gali zamuje.”

Farida ta fad'a tana cuno baki.

“Aiken ku aka yi?”

“Eh alawa zamu siyo.'”

Cewar Basma tana jan hannun Farida. Tsaki naja ganin akwai manyan yara a dakunan su, amman a rasa wanda zaije siyo musu alawa sai su dan tsabar rashin kulawa. Na kuma kallansu duk kansu vest ce da d'an pant a jikin su, nace.

“Ku kawo kud'in naje na siyo muku.”

Ai kamar na maresu, gabaki d'aya suka fashe da kuka, nayi saurin waigawa ko wani ya taho ace nice na musu wani abun, ganin babu kowa yasa nayi saurin shiga na haye sama ina mamakin sharrin yaran nan. Daki na shiga, Innar mu na zaune akan tabarmar da ta idar da sallah, autar mu kuma tana cin macaroni fara da mai da yaji wacce na dafa d'azu. Guri na samu na zauna ina jin tamkar na gaya mata, sai dai nasan gwaleni zata yi sai nayi shiru kawai ban ce komai ba.

“Innar mu na zuba miki abincin?”

“A'a mai sunan uwa, kedai ki zuba kici ni sai anjima saboda ina son gobe na tashi da Azumi”

“Innar mu baki da lafiya zaki azumi?'”

Na tambayeta ina rausayar da kai na gefe.

“Ai naji sauki sosai.”

Ban yadda ba nasan zata yi ne kawai saboda abinda ake yi mana a cikin gidan mu, za tayi ne saboda ALLAH ya shigo cikin lamarin mu. Sai naji nima dama ina da tsarki sai muyi tare amman ba dama. Zubawa nayi naci na dauki kwanukan na sauka kasa zan wanke, Kawu ila dake rike da karfen bene wanda da alama hawowa zai yi sai kuma ya dakata, ya kalle ni yana tambayata.

“Ke, ina wannan yaron mai kunnan kashi?”

“Baya nan kawu.”

Na fad'a cike da jin haushin sa, shi kuma ya sake gwaggwafewa a gurin naji kamar na koma sai dai na daure.

“Ina yaje har yanzu bai dawo ba?”

Haushi ya sake kamani, katon namiji yake cewa wai bai dawo ba har wannan lokacin karfe takwas da rabi da mintuna uku, bayan kuma mazan gidan sai sukai sha biyu ma basu dawo ba. Wata uwar tsawa da ya daka min itace ta dawo dani hayyacina, ya sake cewa.

“Idan ya shigo daga yawon nashi, ki turo min shi.”

“Kawu ya koma ai.'”

“Waye ya koma? Ina aka koma?”

Na yatsina fuska ba tare da na bari ya gani ba nace.

“Kano, yace ba zai kwana ba saboda yaga ranku duk bai so hakan ba”

“Munafuki..! Kaji wani makirci, oho dan kar ya bamu na siyan goro shine ya sulale ya tafi bayan ya cika ku da abubuwan arzik'i ko? Toh koma ciki kice da tsohuwar ku ta bada nawa ya kawo min.”

Kafin nayi kwakkwaran motsi muka jiyo hayaniya daga k'ofar gida, nan da nan Kawu ila ya juya saboda an jiyo sabuwar gulma ya fita, ni kuma na sauka kasa ina Allah wadarai da halayensa saboda kakaf babu na d'auka a ciki. Ina durkushe a wajan rijiya na jiyo muryar Yusha'u yana babbanka ashariya yana cewa.

“Ance daga wajan shagon Gali aka gansu, to wane d'an iskan ne ya lalata musu rayuwa har su biyu dan tsabar shaid'anci? Wallahi tallahi sai munyi shari'a da duk d'an iskan da aka kama ya yiwa Farida da Basma fyad'e.”


___
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*IGIYAR ZATO...💕*


_*1️⃣6️⃣_*

Yusha'u na kaiwa nan, a lokacin Kawu ila yakai inda suke, nan na jiyo wani gundumeman ashar daga cikin bakin kawu ila yana buga rigarsa da hannun hagu.

“Nace wane d'an gidan shed'aniyar ne ya lalata min yarinya?”

Ya karasa maganar yana karb'ar Basma da ake miko masa ita wacce ko motsi bata yi tuni ta dad'e da sumewa. Jikinsa yana kyarma ya fara shirin komawa cikin gida domin dai yaje ya kara tabbatarwa dan zuciyarsa sam bata yarda da abinda kunnuwansa sukaji ba.

“Ga wannan kud'in a hannunta muka gansu.”

Cewar wani matashi wanda shine ya kinkimo Basma daga inda Gali mai shago ya zubar dasu bayan ya biya buk'atar sa. Aikuwa Kawu ila ya waiga tare da sanya kafarsa ya naushi cikin matashin tare da fara zazzaga masa ruwan mafisa.

“Naci kaza-kazan ubanka, ni zaka kawowa iskanci da wulak'anci? d'ari biyun banza d'ari biyun wofi. Ni idan na kama wanda ya lalata min rayuwar yara na wallahi tallahi ko hukuma bazan sanarwa ba zan ci uban mutum.”

Yana kaiwa nan ya shige cikin gida, ni kuwa da nake bakin k'ofa ina jiyo abinda yake faruwa, jin motsin shigowar Kawu yasa na koma ciki da gudu dan kar ya ganni. A tsakar gida ya tsaya yana kiran matarsa, amman jin irin yadda yake bude murya yasa kowa ya fito daga d'aki, Yusha'u yana rik'e da Farida wacce take ta faman kuka tana rik'e gabanta.

“Me yake faru haka?”

Usaiba ta tambaya tana karasawa wajan Kawu ila.

“Wallahi wani mugun ne yayi musu fayd'e daga fitar su yanzu.”

“Lailaha'illAllahu Muhammadu rasulillahi S.A.W, fya me?”

Duk mutanan wajan suka had'a baki wajan maganar, a dai-dai lokacin na kusa shigewa d'aki naji hakan yasa ni juyowa da sauri ina kallon su ta sama. Kawu ila ya mik'awa Usaiba Basma yana faman nad'e kafar wando kamar wanda zai yi dambe, Gida kuwa ya dauki hayaniya kowa da abinda yake cewa.

“Karku zargi kowa, ni nasan wanda ya yiwa yaran nan wannan wulak'ancin, kuma billahillazi sai ya gane shayi ruwa ne. Ke Kaltume kisan yadda kikai kika fito da Najibu idan ba haka ba na lahira sai yafi ku jin dad'i a gidan nan.”

Gabana ya buga jin Kawu ila yana k'ok'arin yiwa Yayan mu mugun sharri wanda baiji ba bai gani ba, wanda ya tafi yana kuka saboda tsoran irin sharrin da za'ai masa idan ya zauna a gidan. Ashe zai tafi ne yabar mana baya da k'ura. Ashe har gwara ya zauna aci masa mutuncin da duk aka ga dama akan wannan sharrin da ake son goga masa karo na biyu.

“Kana nufin kace shine ya lalata wad'annan yaran?”

Kawu Khamis ya tambaya wanda da baiyi niyar fitowa daga cikin daki ba, har sai da yaji ance fayde akai sannan ya zabaro takalma yayo tsakar gidan.

“Kwarai kuwa, Domin maganar da nayi masa d'azu na cewar waya tambaya da har ya dawo gidan nan, toh ashe tayi masa zafi, shine ya tattare kayansa yace musu komawa zai yi can kano, kunga ni gashi nan kafin ya bar garin ya tsaya d'aukar fansa akan yaran da

Please Login or Register in order to submit comment