Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

DA MUTANE.. SHI KUWA MAROWACI YANA NESA DA ALLAH, KUMA YANA NESA DA MUTANE, kyauta takan juyar da Makiyinka ya zama masoyinka. Takan zama dalilin samun tsaro acikin dukiyarka. Sannan zaka samu addu’o’i da fatan alkhairi daga dubunnan Jama’a,

“DAUKE CHUTA DAGA MUTANE : Wato dena chutar da mutane. Manzon Allah (saww) ya gaya ma Sayyiduna Mu’azu bn Jabal (ra) cewa yin hakan ma sadaka ne. Wato ya zamto kai baka chutar da kowa. Manzon Allah (saww) yace duk wanda yake chutar da makobcinsa ba zai shiga Aljannah ba.Ita chutarwar takan zamanto ta hanyar Mummunar magana, ko mummunan kallo, ko kuma yin wani abu a aikace don chutar da wanj ko wasu. Kuma Makobtan nan sun hada da Makocinka na gida ko wajen aiki ko kasuwa ko wajen zama, ko kuma kishiyarki wacce kuke zaune tare.

“KYAUTATA MAGANA : Kyautata kalmomi yayin magana da mutane shima yana daga halayen kwarai. Idan zakayi magana da mutane kayita cikin girmamawa da karramawa da mutuntawa. Allah Madaukakin Sarki yace “KU GAYA MA MUTANE KYAKKYAWAR MAGANA, Manzon Allah (saww) yace : “DUK WANDA YA KASANCE YAYI IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA, TO YA FADI ALKHAIRI KO YAYI SHIRU,

“HAKURIN ZAMA DA MUTANE : Dole in mutum zai zauna da Jama’a ya zama mai hakuri da juriyar dauke chutarwarsu. Idan ka zama baka da hakuri, to tabbas kayi babban rashi. Domin hakuri shine mafi girman abinda zai janyo maka kyakkyawan sakamakon alkhairin duniya da lahira. Manzon Allah (saww) yayi ma Sayyiduna Abu Hurairah wata babbar wasiyyah. Yace masa “YA KAI ABU HURAIRAH, LALLAI NE KA KULA DA KYAWAWAN HALAYE, Sai Abu Huraira (ra) yace Ya Rasulallahi menene kyawawan halaye? Sai Annabi (saww) yace masa “SHINE KA SADAR DA (ZUMUNCIN) WANDA YA YANKE MAKA, KAYI AFUWA GA WANDA YA ZALUNCEKA, KUMA KA BAMA WANDA YA HANAKA

“YIN AFUWA DA KYAUTATA ZATO GA MUTANE : Tabbas da ache mutane baki dayanmu zamu zama masu yin afuwa da kyautata zato kamar yadda Annabi (saww) ya karantar damu, tabbas da mun samu nasarori da dama. Yin afuwa ga mutane yana janyo ma mutum samun daraja awajen Allah. Hakanan kyakkyawan zato yakan janyo samun kusanci da Allah. TAWADHU’U (QANKAN DA KAI) : Yana daga cikin halayen girma. Duk masu daraja agun Allah zaka samesu masu Qankan da kansu ne acikin mutane. Amma masu girman kai, Manzon Allah (saww) yace ba zasu shiga Aljannah ba. (Allah shi kiyayemu).Gaba dayan wadannan halayen har da ma wasunsu, sune irin halayen Manzon Allah (saww). Shi yasa Ubangijinsa (SWT) yace masa :

“KUMA HAKIKA KAI KANA BISA WASU DABI’O’I MASU GIRMA,Kyawun halaye babu abinda ya fisu amfani aranar Alqiyamah. Domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “MAFI YAWAN ABINDA YAFI SHIGAR DA MUTANE ALJANNAH SHINE TSORON ALLAH DA KUMA KYAWUN HALAYE, Awani wajen kuma yace, BABU ABINDA YAFI NAUYI AKAN MIZANI FIYE DA KYAWUN HALAYE, Awani wajen kuma yace :

“SABODA KYAWUN HALAYE, MUTUM YAKAN RISKI DARAJOJIN NAN NA MASU AZUMI DA QIYAMUL LAYLI: To Kinga wannan duk riba ce ga masu kyautata Halayensu. In dai har kina son ki samu Wadannan darajojin, to mai zai hana tun yanzu ki gyra halayen ki? Ki zama mai hakuri da ladabi da bin iyaye da Tawadhu’u da juriya da kyauta da sakin fuska ga kowa da kowa kina jina?
Allah ya taimakemu. Allah ya Qara mana son Manzon Allah (SAW) da koyi da halayensa. Ameeen”

Kan Hajia Husna a kasa tana tsiyayar da hawayen nadama. Muryar ta na rawa tace,

“Insha Allahu baba! Nagode Allah ya saka da alkhairi.”

“Amin.. Jeki ki kama wa mahaifiyar taki aiki.”

“Toh baba.”

Ficewa tayi tana jin wani sanyi na ratsa ta, shi kuwa Malam shehi murmushi yayi ya janyo y’ar wayar sa data sha nadi da kyauro ya latsa lambar alhaji Kabeer ya kira shi ya sheda masa cewar yanason ganin sa. A satin kuwa yaje zaria suka yi magana ta nutsuwa dashi. Aka maida auren sa da Hajia husnan, Sai satin gaba ta tattara ta koma zaria tamkar ba ita ba, Ta zama marar magana kullum cikin lazimi take, ita yanxun da ace Haysam bai yi aure ba to ko yar aiki alhajin zai aurawa Haysam babu ruwanta, Domin duniya ta koya mata hankali. Anan ta jiyo Haysam din ya samu aiki ta dalilin surukar gwamnan kaduna, wato Batoul da tai hanyar samuwar aikin nasa.. Hajia Husnah ta kara yin nadama sosai da yadda da qaddara. Domin d'an hakkin daka rena shike tsole maka idanu. A baya kaltume mahaifiyar Batoul din tace Insha Allah Batoul xatai wa Haysam nisa kuma sai sun samu alkhairi ta b’angaren ta. Sai gashi tun ba’aje ko’ina ba Allah ya tabbatar da hakan. Har gida taje ta bawa Kaltume hakuri sannan tayi mata godiya na zamowar Batoul silar tafiyar Haysam kasa mai tsarki da shaidar zama a can din din din.

Toh dama haka duniyar take. Na gaba ya koma baya duniya makaranta. Duk wanda ya hau IGIYAR ZATON ‘daurawa da rayuwar duniya ya sauke domin ba matabbaciya bace. Yau ka zamto cikin halin rashi, gobe Allah ya daga ka duniya ta sanka, Ka zamto cikin masu dukiya. Toh haka lamarin yake! A kullum dai bawa ya fawwalawa Allah lamurransa shine dai-dai. Domin zai ga dakyau kuma mafificin alkhairi...👏🏻

*PARIS.*

Gaba d'aya mun canza daga ni har shi munyi wani mugun fresh kai daka ganmu kasan cewar muna cikin hutu, gaba daya na kuma yin haske jikina ya yi luwai-luwai tamkar an saka ni a inji an wanke ni, to bani da wani fargaba yanzu babu tunanin rashin abinci ko masifar yan gidan mu, ba zuwa lectures bare fargabar zuwa school d'in. Yadda naga komai na jikina yana canzawa ne ya kuma kayatar dani, shi kanshi Mubeen sai tambaya na yake menene sirrin nace masa Paris.

Fitowa ya yi daga wanka jikin sa daure da towel hannunsa rike da karami wanda zai tsane jikin nashi, na bisa da kallo domin zuwa lokacin wani irin sihirtaccen so nake mishi wanda a hankali ya dinga shiga da salo, kulawa, tarairaya, bege, kauna tatacciyar soyayya marar sirke da Mubeen yake nuna min a koda yaushe sune silar jefani cikin soyayyar shi, na manta da cewar shi dalibina ne, na manta da cewar shi sa’ana ne domin ina yi masa kallo irin na mazan da nake burin aura.

Mubeen matashi ne amman komai yake yi irin na kamilallun manyan magidan ta yake, idan ya yi min wani abu sai na ganshi tamkar babana ko wani babban mutum mai daraja da na sani, ganin yadda na kura masa ido yasa shi karasowa guri na yana riko min hannu yace.

“Kinata kallo na kizo kiyi aikin lada.”

Nayi murmushi kawai tare da karbar towel din na shiga goge masa ruwan jikin nashi. Mai yaje ya dakko ya kuma miko min na karba na shafa masa ganin zai tashi yasa na riga shi tare da cewa.

“Ka jira na karasa maka ai ka gama komai.”

Bina ya yi da ido ganin yadda jikina yake jujuyawa sai faman murmushi yake yi. Wajan sababbin kananun kayansa na tsaya ina tunanin wanda zan ciro mishi, sai faman cilla kayar ido nake sama da kasa, can kuwa ido na ya sauka akan wasu riga da wando jeans blue da red d'in t-shirt sai undis na juyo na taho, ganin yadda yake yi min wani shu'umin kallo yasa na kauda fuska dan shi yanzu zai iya samu sauya wani sabon wankan.

“Tashi ka shirya.”

“My Fikre anya ba zan hakura da fitar nan ba?”

“Yafi maka kam, Daman ni ba so nake ka fita ba.”

“Me yasa?”

“Saboda kawai bana so.”

“Gaskiya akwai dalili haka kawai ba zaki ce karna je ba.”

Na hada rai tare da tsuke fuska ina cewa.

“Toh kuwa sai dai muje tare.”

Tashi ya yi tsaye tare da rungume ni yana juyi, tun ina dariya har na fara jiri kai na ya fara juyewa ina cewa ya bari shi ya dauka wasa nake masa sai da yaji ni luuuuu na fada kirjinsa kamar marar laka sannan ya ririko ni tare da kwantar dani a kan gado.

A hankali ya shiga kiran suna na amman shiru, yadda yaga ina sauke numfashi ne ya tabbatar masa da cewa bacci nayi, ya sauke ajiyar zuciya tare da gyara min kwanciyar yana murmushi. 'Ashe ma ko kwalliya ta ba zata gani ba' ya ayyana a cikin ransa. Kayan yasa ya gama feshe jikinsa da turaruka sannan ya dauki wayarta ya dauki hoto kusan guda uku harda wanda ya yi a kusa da ita ya ajiye tare da sumbatar goshinta ya bar dakin.

Can yawon shi ya tafi sai dai bai wani dade ba saboda yasan idan ta farka zata ne meshi. Yana shiga kuwa ya tarar bata kwance, ya duba bathroom nan ma babu ita duk inda yasan zai duba a part d'in su ya duba ba Batoul. Hankalinsa ya tashi matuka ya fara fita hayyacin sa ya fito zuwa reception d'in hotel d'in cike da tashin hankali.

“My wife.. Mata ta.. Ban ganta ba.. Please ku taimaka min dan Allah.”

Gabaki d'aya yaso ya haukace musu a wajan, suka dinga bashi hakuri akan zasu nemo masa ita. Yana dagowa kuma sai ya hango ta tsaye a bakin ruwa babu abinda yake damunta. Ko kula ma'aikatan da suke tsaye akan shi bai yi ba ya nufi gurin kamar zai fadi. Yana zuwa yayi mata wata bahaguwar runguma ta baya yana faman sambatu.

“Me yasa kikai min haka? Kin tayar min da hankali my Fikre sauran kiris na haukace da ban ganki ba, please karki sake fita ban sani ba.”

Da wata uwar harara na bishi bayan na juyo mun had'a idanuwa, duk sai na ganshi a firgice amman naki sassauta masa, rai na a bace nace.

“Waye ya fara tafiya ya bar wani? Kai ne ka fara tafi bayan ka gama wujijjiga ni, shine yanzu zaka zo kace karna kara, to kaima karka kara.”

“Fine naji. Taho mu shiga ciki.”

“Ni ka bar ni anan.”

“Ya ilahi my Fikre kizo muje akwai abinda zan nuna miki.”

Ganin ya dage ne yasa na bishi muka koma dakin. Sake rungume ni ya yi yana sumbata ta nayi masa biris sai can kuma yace.

“Baki ga kwalliya ta bane?”

“A ina?”

“A wayarki mana.”

“Ohh na gani mana but bakai kyau ba ai.”

“For real?”

“Yeah.”

Habarsa ya rike yana shafa kwantaccen sajensa na kallesa tare da turo baki nace.

“Abinda yasa bakai kyau ba saboda bangani ba da ido na, sai da ka gama wujijjigani kasa nayi bacci sannan ka wani saka ka tafi.”

“Ohh haka ne? Toh albishirinki”

“Goro.”

Nayi maganar ina sake kwanciya a jikinsa.

“Zamu bar Kasar nan soon insha Allahu ai mun dandana ko?” Cike da farin ciki nace dashi.

“Alhamdulillahi dama nayi missing d'in su Innar mu da Mamma.” Murmushi kawai ya yi yana shafa gashin kai na..

•••X••O••X••O•••

*Ranar* asabar da yammaci Kawu ila ya farfado daga coma daya shiga, Sai dai fa ya zama abun tausayi. Domin gaba d’aya tunanin sa ya goge, Ya manta wanene shi? dama sunan sa a ta’kaice. Kafar sa d’aya a gundule an nannade ta da bande ji, Hakama rabin kansa sa ya samu rauni sosai, Idon sa na hagu shima ya tsiyaye. Dole ka tausaya masa domin gaba d’aya ya zama tamkar sabon tab’i, Yawu ne kawai ke dalala daga bakin sa. Allah sarki duniya..

Duk yan uwan sa sun zagaye shi suda sauran tawagar gidan mata tara! Haka Hinde da Mari sai zare idanu suke, Domin satin baya suka dawo bayan an zazzabga adduoi Allah ya karkato da hankulan su suka dawo gida amman ba ko sisin kwabo a tare dasu. Gaba d’aya sun jeme sun zama wasu iri, Hakan yasanya Gwaggo Aminatu yiwa limamin masallacin jumu’ah maganar bada su hinden auren sadaqa ga wanda yayi niyyar auren su, Domin ceto su daga fadawa kogin halaka...

Kawu ila yasha adduoi kafin hankalin sa ya fara dawowa, Sannu ahankali ya dawo. Yayi kukan dana sani tamkar ransa zai fita daga jikin sa, Ya nannemi gafarar yan gidan baki d’aya, Musamman su kaltume da Najibu.

Da daddare muna zaune ina jikinsa muna kallon wani Korean drama sai ga kiran wayar yaya Najeeb, cikin sauri na daga tare da cewa.

“Yaya na kuma babban uba ina mai sunan Abba na?”

“Lafiya lau kanwata, ina mai gidan naki.”

Na kalli inda Mubeen yake matse dani nace.

“Gashi nan yana gaida kai.”

"Ina amsawa a mika min gaisuwar ban girma."

Nayi murmushi kawai domin duk abinda yaya Najeeb yake cewa Mubeen yana ji. Yayan mu yace.

“Daman muna asibiti ne shine kawu ila yace yana son ya roke ki yafiyar abinda duk ya faru a baya gashi nan bari na sata a handsfree kiyi masa magana tun da ya fara samun bakin sa yake ta kiran sunan ki.”

Wasu hawaye suka ziraro min na kasa cewa komai har yayan mu ya kara wayar a kusa da bakin kawu ila. Allah sarki muryarsa a hankali duk wannan hargagin babu shi, muryarsa kadan-kadan yana neman ya fiyata ina hawaye Mubeen yana share min kafin daga karshe mu katse wayar dan yadda nake kuka harda shasheka hankali na duk ya kara tashi da alamuran duniyar nan.

A ranar dai da kyar Mubeen ya lallaba ni nayi bacci saboda duk na damu gani nake tamkar ba zai yi rai ba, abubuwan baya suka dawo min, harda bokitin zaman sa da yanayin yadda yake shigowa gida da fitarsa da yadda yake kira na idan ya tashi.

Daren ranar Allah ya karbi ran Kawu ila, Yayi kwanan keso da safe aka kaishi makwanci. Hakika ahalin gidan mata tara sun shiga dimuwar mutuwar Kawu ila, Sosai sun koka da mutuwar tasa. Don kwana biyu kafin rasuwar sa har yar sandar dogarawar sa ya dakko ya fito tsakar gidah akai ta wasa da dariya dashi. Mutuwar ta girgiza su ciki harda Bintalo dake ganin saura ita. Ta nennemi yafiyar su Itama tana kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara,

Bayan futar su ummita daga takabar marigayi Kawu ila suka harhada yana su suka bar gidajen ranar alhamis, dake ranar talata aka daura auren su Hinde da Mari, Talatuwa.

Toh fa abubuwa da dama sun faru kamar tashin ahalin gidan zuwa ga gefen unguwa cikin dandatsetsan gidan da gwamna yayi musu sauyi, Domin yayi musu gyara sosai a garin ciki har da yin babban titin da zai kaika kaduna, Wanda yinsa ne yasa aka rushe gidan mata tara. Domin daga kan gidan aka fara shimfidar titin. Gida je marassa bene(bungalow) masu dakuna uku da faluka bi biyu kowanne da gate dinsa aciki ga kuma babban gate da ake rufe gidajen gaba d’aya da za’a iya kiran su da estate aka yi musu kyauta bayan ya biya su ku’din wancen daya rushe..

Bangaren da akaiwa Bintalo dai Zabbau ce aciki da sabon mijin ta da aka daura musu aure, Domin Bintalo tuni tasa aka tattara ta aka maida ita k’auyen kod’e dake lahadin makole ta kano. Ta nannemi yafiyar yan uwanta kancewar gwara ta mutu acikin su..

Sashen Marigayi Kawu ila kuma yayan sa maza ne aciki, Matan kowacce uwarta ta tafi da ita. Innar mu kaltume kuma tana sashen ta Itada autar mu Aminatu da yar autar Baffa Ardo qibdiyya wacce ta dawo wajen Innar mu da zama na dindinin. Lamarin dai sai godiya ga mai duka, Domin dukkan matsatsi yana tare da sauki, Alhamdulillah duk wani ruguntsumin kwamacala na gidan mata tara a yanzu ya zama tarihi. Kowa ko’karin farantawa Innar mu yake, Domin tayi musu nisan da har gaban abadan ba zasu taba kamota ba. Alhamdulillah! Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u. Tabbas duk wanda yai hakuri da sannu zai ci ribar a gaba.....

Toh masu karatu kunji dai yadda ta ‘kar’kare da rayuwar gidan mata tara... Allah ya shiga lamurran mu, Allah kada ya kawo ranar da zamu zalunci wani ko mu bishi da sharri, Domin shi sharri dan aike ne duk inda yaje dole ya dawo wurin ka ko wanin ka. Allah ya biya mana bukatun mu na alkhairi. Yasa miyi kyakkyawan k’arshe! Allahumma Aaameen💞

**
*JEDDAH*

Tun da jirgin mu ya sauka a airport din jiddah nake kalle kalle. Ashe dama Makka zamu zarto mubeen yace dani gidah zamu koma? Wani farin ciki ya sake lullube min zuciya ta lokacin da na fara hango gilmawar larabawa. Wai ni Batoul ni ce a kasa mai tsarki? Hawayen daya gangaro min na goge,

“Stud-muffin!...”

Na fada a shagwabance ina turo baki,

“Kinsan ni ba ruwana wallahi a gaban kowa zan tsotse wannan bakin..”

Hararar wasa na jefa masa, Ya mikomin hannun sa na sakala nawa ajiki. A haka muka shiga mota ta kai mu masaukin mu. Ruwa muka watsa kafin Mubeen yasa akawo mana abinci,

“Sakko muci...”

“Wannan abubuwan? Na k’oshi gaskia”

“Ai kuwa baki isa ba! Jalamah. Su Ka'ak ne fa da Kabsa sai Jareesh / Harees.”

“Ni nakoshi...”

Mubeen ya mike ya dawo kusa dani yana kallon idanu na,

“Nace muje asibiti kince bakomi shawara ne....”

Shiru nayi ina lumshe idanu, Turaren jikin sa ba karamin fusgata yake ba. Janyo shi nai ina cusa kai na acikin kirjin sa. Hade da murza hanci na ina sake bude kofofin hanci na. Mubeen ya sake makalkale ni dama abunda yake so kenan ya kwantar dani yana kallon idanu na,

“Whole-world! Meke damun ki ne.. I’m loving the new you!...”

Ban amsa shi ba na kara rungumo shi ina sunsunar turaren jikin sa ba karamin dadin sa nake ji ba,

*KINGDOM OF SAUDI ARABIA🇸🇦*
(MECCAH}

Cikin dare na tashi Mubeen ina fashewa da kuka,

“Ya Salam! Fateemah na! Meya faru? Waya tabamin ke! Ni ne? Uhm?”

A rude ya shiga tambaya na yana dudduba jiki na.

“Babu komai... Zanci dan Allah”

“Mezaki ci? Me kike so?”

“Kosai.. Stud muffin zanji kosai..”

“Kosai kuma Fateemah na! Yayy..yaz..Yazanyi yanzu.”

“Ni wallahi kosai nake so. Na cikin mai me zafi.”

Mubeen ya mike yana kunna side lamp. Ya maida rigar sa yana kallo na,

“Bara naje na dudduba ba za’a rasa ba a wajajen cin abinci na hausawan mu. “

Ahankali na cigaba da kuka na domin ni yanzu nafi bukatar kosan akan komai. Ya jima kafin ya dawo da kullin ledar kosan jikin sa har rawa yake ya ajiyemin, Hannuwa biyu na shiga dauka ina dumawa a baki na abun tausayi.

“Sai me kuma..? Uhm?”

Ban amsa shi ba har na gama ci tas na gyatse hade da hamdala.

“Nagode stud muffin...”

“Fateemah na! Baki taba cewa kina sona ba? Meyasa? Shin akwai wani makusa atattare dani da bakya so? Dan Allah ki sanarmin...”

Girgiza kai nayi gaba d’aya komai nasa burge ni yake. Amman na rasa meyasa harshe ne ke nauyi a duk sanda zan furta masa ina sonsa nima.. Murmushi kawai na sakar masa na shige ban’daki. Nayi wanka na zura rigar bacci. Daki na koma na haye gado, Banga Mubeen ba ko yana shan iska ne awaje? Gyara kwanciya nai kafin wani lokaci tuni bacci ya sace ni.. Cikin dare na farka naga Mubeen a kusa dani jikin sa sai rawar sanyi yake. Ya dau zafi rauu. Idanun sa sun kad’a sunyi jajir.

“Subhan’Allah! Meya faru da kai? Baka da lapia ne?”

Kada kai yayi yana janyo ni jikin sa,

“Zazza’bi nake yi love.”

“Tashi muje asibiti to.. Sannu!”

Magungunan dake gefen sa ya nunamin,

“Na siyo d’axu dana fita dinnan..”

“Dama can ka tafi? Sannu!”

Na fada muryata a raunane. Gaba d’aya jikina rawa yake. Tarin ciwukan sa, tsoro na d’aya kar Allah yasa d’aya daga cikin ciwon sa ne ya tashi. Tunanin abunda zan masa na shiga yi, Can na tuno wani film dana gani lokacin da wata budurwa ke tallafawa saurayin ta yana zazza’bi. Rintse idanu na nayi. Na shjga cire kayan jiki na, A hankali na zame duka na shige jikin sa. Sai ga bawan Allah yana sauke ajiyar zuciya. Duk da rashin lapiar dake damun sa hakan besa ya biya buk’atar saba. Cikin wani salo wanda ya gigitani ya tsunduma ni a kogin dadi.

“Zan sha ruwa love.. Kin karar min da ruwa..”

Ban kula shi ba na janyo gorar ruwa a gefe ina mika masa, Ya girgiza kai yana nuna baki na,

“Na bakin ki nake so..”

“Ka cika fiti na wallahi. Ni dai ban iya ba.”

“Tsaya na koya miki to..”

Kafin nai magana ya dan gyara zaman sa yana cije lebe. Hannun sa ya daura akan gorar ruwan yana kaita baki na. A dai dai kunne na ya shiga radamin,

“Sha amma kakki shanye fa... Sha ki barshi a bakin ki..”

Na had’iye wani tokararren abu a mak’ogoro na ina girgiza kai,

“Shikenan Idan bakiyi ba babu ruwana keda daukar zunubi. Mijin ki ya saki abu kin ki..”

Sha nayi na barshi a baki na ina rufe idanu na. Ahankali na ji saukar tattausan leben Mubeen akan lebe na, Can kuma ya zura harshen sa cikin baki na. Wani irin deep french kiss ya shiga yimin yana shan ruwan ahankali. Na hadiye ba shiri ina kauda fuska.”

“Ban koshi ba..”

“Rik’e kasha ai ni ba robar bace..”

“Ki bani pls.. Har zazzabin ya fara sauka fa.”

Kurba na sake yi na barshi a baki na. Salon wannan shan nasa yafi wancen. D’aya hannun sa akan albarkatun kirji na. Ga muguntar da yake yi acikin baki na.

“Fateemah na.. Kin zamo ta musamman daga cikin mutane na musamman da na tab’a haduwa da su a rayuwata, kin shiga zuciyata kin zauna ta yadda ba zan iya mantawa da ke ba har abada. Komai naki dabanne da sauran mata! Ina fata da burin kasancewar mu tare a daula mafi tsari da kyawun burgewa wato Aljannatul frdwas..”

Ya zare bakin sa ahankali yana maida numfashi. Amman har yanzu yana yawo da hannun sa ajiki na,

“Bacci nake ji.. Kaji?”

“Bana Manta lokacin da Lecturer din mu na media history yake yi mana Dictation kowa yana rubutawa haka ni ma ina rubutawa. Bansan cewa ba abinda Malam yake faɗa nake rubutawa ba , sai bayan ya kammala na duba naga saƙonnin soyayya nake rubutuwa Izuwa gare ki sahiba ta , alokacin ne na tabbatar da irin son da nake yi miki,

“Hakika ke ta daban ce a gare Ni hakan yasan ya naji ina sonki. Wasu suna cewa bamu da ce ba Ni kuma ina cewa ƙarya ne inaji a jiki na Wata Rana zaki zamo tawa Insha Allah. Gashi kamar wasa munyi aure, Muna kwance a gado muna making... love da my love. Fateemah na Ina kaunar ki! Shi so na gaskiya ba ya taɓa canjawa daga yadda ya kafu a zuciya tun asali, sai dai a samu masoyan sun canja daga yadda suke tun fari,

“Ko da a ce mun tsufa, idaniyata ba za ta daina ganinki a matsayin wannan kyakkyawar macen ba, zinariya mai kyawun sura, Fateemah Ina kaunar ki!”

Jinsa kawai nake, Gaba d’aya Bacci nake ji wallahi. Ya hanani ta hanyar sake maidani dayan barin yana kallon idanu na,

“Fateemah na! A koda yaushe ina fatan nasara ta kasance a tare da ke, na kasance mai yin fatan kasancewar farin ciki a cikin zuciyar ki a safiya ko rana, amma shin zaki iya tinawa da wani abu wanda zuciyata ke muradin samu daga gare ki? Zawjatiii! Ba komai bane face ki mallaka min zuciyar ki ta hanyar sanya ni a cikinta ni kadai ba tare da kin hada ni da kowa ba, Dan Allah ki karbe ni a matsayin mijin ki,

“Tonight I want to slowly kiss my way from your lips down…the only question is how far down will I go? I couldn’t get enough of you Love! Ina kaunar ki Fateemah na.. I love you so much. No matter where our lives take us I will always be by your side.”

Inason na mayar masa da martanin inason sa nima amman harshe na yai nauyi. Hannuna d’aya nasa ina shafa sumar kansa, Lumshe ido ya shiga yi a hankali yana hade bakunan mu waje d’aya. Ya labarin zazzabi? Tuni ya sauka, Sai ya zamto ni ce me zazzabin shine mai rarrashin...

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[9/15, 10:36 PM] Miss Xoxo: *_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_*


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(TAKU NA BIYU)_

_Wattpad: missxoxo00_
_YouTube channel:Alkalami Tv_

_*55_*

*_KARSHE || FINALE🥰😘💫*_


_*DEDICATED

Please Login or Register in order to submit comment