Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bud'e masa k'ofar, Mubeen ya shiga gidan baya ya zauna. K'ok'arin shiga driver yake suka ji muryar Amb Salees yana magana.

“Ya zai tafi shi kadai? Kasan fa bai san ko'ina ba a can, kuma a irin wannan lokacin da nake cikin campaign dole sai yaran nan suna fita da masu kula dasu, ba wai ina cewa mutanen sune zasu kula da shi ba. A kallah dai muma muyi wani abun sai ALLAH ya dafa mana.”

“Na fahimceka ranka ya dad'e, amman yanzu kam karka damu zan taya shi shiga wasu guraran.”

Driver ya fad'a yana d'an rissinawa. Amb ya jinjina kai, sannan ya karasa wajan Mubeen dake zaune a cikin motar yana game a cikin wayarsa.

“Mm.'”

Ya d'ago yana kallon mahaifin nasa cike da girmamawa, ya kuma ki bari ya had'a ido dashi.

'”Allah ya tsare kaji? Nasan bani da matsala da kai, but be very carefull.”

Kai ya d'aga sannan driver yaja suka tafi. Shi kuma Amb ya shiga mota shida mutanansa suka nufi kaduna yin wani taro su da magoya bayanshi.

Cikin ABU suka nufa, Mubeen ya sakko bayan sunyi parking. Tunda ya fito mutane ke kallonsa maza da mata, shi kuwa babu abinda ya damesa domin bai ma san suna yi ba kasan cewar idanunsa kasa suke kallo. Kai tsaye admin block ya nufa, yana shiga dai-dai lokacin Batoul ta fito daga office din wani HOD. Mubeen yaji zuciyarsa na harbawa, nan da nan ya d'ago kai yana d'an jujjuyawa tamkar mai neman wani abun. A hankali ya juyar da kansa gefen hagu, dai-dai lokacin ita kuma Batoul ta wuce ta gefensa na dama tana sakarwa Haysam murmushi. Mubeen dake tsaye ya juya dama sai dai baya ganin komai da yake sa shi fad'uwar gaba, hakan yasa shi rintsa ido yana karanta hasbunallahu wani'imal wakil.

Kai tsaye office d'in wani dean ya shiga, ya jima a ciki dan kamar ba zai fito ba, ashe da ya shiga kwanciya yayi sai da yaji kirjin nasa ya lafa sannan ya fito yana wani yatsina fuska. Can cikin school d'in ya zazzaga, 'yan mata da sauran samari sai kallansa suke yi, wasu suyi masa maga amman sai ya kasa koda sakar musu fuska, ko d'an murmushi kasa yi yayi saboda rashin sabo. Yaje ya gama zazzagawa sannan ya nufi mota suka koma gida.

Batoul kuwa sun jima ita da Haysam a tsaye, bayan sun d'an yi gaisuwa take tambayar sa mai yasa bata ganinsa, ya shaida mata cewar baya garin ne yayi tafiya. Tare suka taho a motarsa abinsu gwanin ban sha'awa tamkar wasu sababbin amare, ya kalleta bayan ya d'an rage gudun da yake yi yana cewa.

“Mine har yanzu baki bani damar fitowa ba, ko dai banyi miki bane?”

“Sam ba haka bane Yaya Haysam, idan nace bakai min ba toh wa nake son yayi min? Kuma karka manta ka zama wani babban jigo a rayuwa ta. Yaya Haysam mahaifiyar ka bata san mu'amular mu, musamman irin wacce kake son mu kulla shin ya zan yi na amince maka nazo zuciyata ta rikirki ce. Na baka dama kaje ka karbo mana yarda da amincewar iyayenka, ni nawa basu da matsala, ALLAH ya tabbatar mana da alkairi.”

Wani irin sanyin dad'i ya ziyarci zuciyar Haysam, ya kalli Batoul sosai kafin yace.

“Insha ALLAHU yadda kika bani dama a yanzu baki wani gaddama ba. Suma wannan karan zasu bani goyan baya.”

Murmushi nayi masa dan ko a raina banji cewar zamu iya yin aure da Haysam ba, gashi na tsani mahaifiyar sa tun lokacin da ta yi mana rashin mutunci. A zuciyata na dinga addu'ar ALLAH karya tabbatar da wannan abun, dan har ga ALLAH na kasa mantawa da abinda Hajiya Husnah tayi mana. Kafin mu karasa unguwar mu, nace ya sauke ni saboda kar wani ya ganmu yaje yayi mana sharri. Nayi masa godiya bayan na sauka daga motar na wuce, ina jinsa har sai da na karya kwana sannan ya tashi motar shima ya wuce gidan su. Ina komawa gida na sanar da Innar mu duk yadda muka yi a makaranta, sannan na sanar da ita ranar da za'a yi mana interview da screening tayi min fatan alkairi.

•••••; •••••; •••••;

*ABU*

Saukarta kenan daga keke napep, sanye cikin riga da zani rafa na wani green d'in lece da ratsin milk na zare a jiki, tayi amfani da mayafi milk jaka da takalimi suma duk milk color tayi kyau sosai. Mai napep din ta tsaya ta bawa kud'in sa, dai-dai lokacin motar da aka kawo Mubeen tayi parking a saitin su Batoul wacce ke sanya canjin da aka bata a cikin jaka. A hankali ya fito daga cikin motar ya tsaya, dai-dai lokacin Batoul taje ta wuce ta gefensa tare da bula masa mayafinta da take gyarawa ya gogi kumatunsa.

Kallonta yayi amman baiga fuskarta ba kasan cewar ta wuce. yaji kirjinsa ya ci gaba da bugawa, hakan yasa shi ya fara bin bayanta ba tare da ya san yana yi ba. Driver d'in sai magana yake masa amman baiji ba, mutane sai kallansa suke yi sun d'auka tare suke. Sai da Batoul ta shiga office sannan ne hankali da tsantsar bugun zuciyar Mubeen suka tsaya. Ya kuma neman ta inda yake jin bugun amman ya kasa gano manufar zuwan shiga riki cin.

Dafe kansa yayi tare da lumshe idanunsa na tsawon lokaci. Muryar driver d'insa shine ya dawo dashi cikin nitsuwarsa inda yake tambayarsa ina zashi bayan ba nan ne hanyar department d'in su ba. Bai ce komai ba sai karb'ar kayan karatunsa da yayi sannan ya juya ya tafi. Har ya zauna yana tunanin wadda ya gani, wacce yana kyautata tsammanin itace take sanya shi jin bugun zuciyar nan, amman abin da yake daure masa kai shine, tun fa ranar da suka fita yawo shida 'yan gidan su ya fara ji, gashi yazo makaranta abin ya tsananta, kodai wata ce take bibiyarsa?. Shi dai a ranar yaji lectures ne kawai amman idanunsa basu dena hango bayan matashiyar da ta dinga jansa a sihirce ba. Bai san wane department take ba, uwa uba bai san yanayin fuskarta ba bare nan gaba ya gane ta.

Ranar alkhamis shine ranar da zan fara lecture, bayan na gama shiryawa cikin wata atamfa brown da ratsin orange a jiki, na d'auki orange d'in mayafi na yafa sannan nayi amfani da black flat shoe da jakarta da na zuba komai da zan buk'ata a ciki, na kalli Innar tare da cewa.

“Wallahi ina gabana fad'uwa yake yi, anya zan iya gabatar da lecture d'in nan a gaban zafafan students?”

“Uwa ta zaki iya mana, ai da koyo aka san gwani, kiyi ta addu'a insha Allahu zaki iya.”

Ta fad'a cike da karfafa min guiwa, na jinjina kai tare da d'aukar turaren da Yayan mu ya siyo mana na shafa, na juya zan tafi sai gashi ya shigo d'akin, yayi murmushi tare da cewa.

“Weldone sabuwar lecturer, kinga yadda kikai kyau kuwa?”

“Yayan mu nifa fargaba ta fara min yawa, wallahi gani naje yi tamkar ba zan iya yin lectures d'in ba.”

Yayan mu ya tuntsure da dariya, hakan yasa ni turo baki ina kallansa.

“Yayan mu dariya ma zaka min ko?”

“Sorry k'anwata, kece da abin dariya, menene abin jin tsoro sai kace wata 'yar kauye? Ki daure daman komai na farko ai sai ya tsorataka, amman karki bari zuciyarki ta karaya. Kiyi addu'a idan zaki fita, sannan in zaki shiga lecture d'in nan ma kiyi addu'a.”

Sai naji kwarin guiwa ganin yadda duk suka karfafa min zuciya, na kallesu tare da yin dariya har hakorana suka fito nace.

“Zan iya, nima yanzu naji tabbacin zan iya, sai na dawo, ina alfahari daku baki d'aya.”

“Ya Batoul ki siyo min abin dad'i.”

Cewar autar mu, na amsa mata da 'toh' sannan na wuce na fita ina ta addu'a. Da kawu ishaq muka had'u yana jan ruwa daga rijiya, na gaida shi bai amsa ba sai kallo da ya bini da shi yana tab'a baki, ganin abinda yake min ne yasa ni fita ba tare da na kuma bi ta kan kowa ba. Sai da na fara zuwa office na zauna har zuwa lokacin ya cika wato karfe takwas, na dauki jaka ta na wuce venue d'in da zanyi lecture d'in. Baki na dauka da sallama, da basmala na shiga, kai na a k'asa na kasa kallon kowa har naje na tsaya a wajan da ya kasance gurin tsayuwar duk wani mai gabatar da jawabi. Na ajiye jakata sannan na d'ago kai tare da dora idanuna akan d'aliban.

-
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*IGIYAR ZATO.....💞*


*30*

Sallama na fara musu, Da farko muryata ta fara rawa, Amman daga baya sai na fara bayani dalla-dalla. Sunana da gurbin karatu na na fada musu cikin harshen turanci,

“Assalamu Alaikoum sunana Batoul Salisu idris Najibullah, Kuma ni ce malamar ku ta wannan course din. Da farko kafin mu tsunduma cikin abunda ya kawo mu. Zan fada muku gurbin karatu na dama sunayen darussan da zan d’inba d’aukar ku. Nayi karatu na na degree anan makarantar bangaren B.A English kamar ku. Inda na dora da degree na biyu a jamiar dake kaduna. Alhamdulillahi bayan wasu lokuta kuma Allah yasa na fara koyarwa akan ku. Inda zan dinga koyar daku subjects/courses, ‘History of English literature. Da kuma The Essay in English: The Twentieth Century: Theory and Practice.’ Wato courses biyu kenan..

Tunda ta shigo yaji yana neman rasa tunaninsa duk kuwa da cewar bai d'ago ya kalleta ba, ya sake rintsa ido yana karanta hasbunallahu wani'imal wakil. Tunda ta fara magana Mubeen ya nemi ji da ganin sa ya rasa na 'yan wasu dakikai, Gaba d’aya bugun zuciar sa ya tsanan ta. Zazzakar muryar ta sai karakaina take a cikin kunnen sa. Wani irin shauki yaji yana d'iban sa akan yaje gare ta. A hankali yasa hannu ya dafe saitin zuciar sa. Da k’yar ya iya d'aga idanuwan sa ya dora su a saman fuskar ta. Ya cigaba da mata wani irin kallo tun daga kan yatsun ta zuwa fuskar ta. Kasa dauke idanun sa yai daga gare ta yana mata wani irin mayen kallo. Saurin sunkuyar da kansa yayi yana istigfari. Gaba d’aya baya jin bayanin da take yi. Muryarta ce kawai ke masa yawo a kunnuwan sa, Yayin da kyakkyawar fuskar ta ke bayyana a idanun sa.

Ni kuwa gaba d’aya yana yin yadda yan acikin suka bani nutsuwar su yasa naji dadi na cigaba da kwararo bayani na,

“Yau zan fara daukar ku course din; The Essay in english: The 20th century(Theory and practice). Ranar Friday’s kuma zan dinga daukar ku course din: History of english literature. Kafin nan zan fa’di doka na, Banda latti, Banda shige da fice idan ana lectures sannan banda yawan magana, Sai abu na karshe attendance dole ne shi da presentations. Kuna jina?”

“Eh...”

Suka fada da karfi, Gaba d’aya mazan ajin sun sake bada nutsuwar su ganin ta budurwar malama gata yar kyakkyawa. Ai kuwa wani daga cikin su ya daga hannu zai yi tambaya. Alokacin Mubeen yai saurin juyawa yana masa wani irin kallo, Domin Haka kawai yaji bayason yaron yai magana da ita.

“Ma’am shekarun ki nawa? Sannan matar aure ce ke ko budurwa?”

Yana fad’an haka gaban Mubeen ya yanke ya fadi. Tsura mata idanu yai dake seat din da yake shine na farko dayake kallon podium din da take a tsaye. Murmushi kawai Batoul tayi kafin cikin dakewa tace,

“Na wuce shekaru ashirin sannan bani da aure amma an kusa..”

Mazan ajin suka sa ihu suna tafi. Mubeen ya bata rai yana dankarawa wanda yai tambayar harara. Batoul kuwa na gama introducing na course din ta fice kan nextweek za su fara shiga kundin darasin. Da sauri Muhammad Mubeen ya bi bayanta hannun sa d’aya dafe da saitin zuciar sa. A hankali cike da nutsuwa take tafiya, So yake ya tabbatar da salon sabon takun zuciar sa. Waya take yi da Yaya Najibu alokacin batasan ma yana biye da ita a baya ba,

“Eh wallahi Yayan mu, Yaran basu da matsala gaskia. Eh nagama musu yau kawai na fada musu course outline d’inne. Ameen Ya Allah Yayan mu. Yauwa sai na dawo..”

Murmushi Mubeen yai yana shafa kansa. Ko kad’an bai damu da yadda mutane ke binsu da kallo ba. Idan har ba sani kai ba zaka dauka a tare suke. Ja yai ya tsaya a bayan ta lokacin da take kokarin shiga office din ta. Juyawa tai jin motsin mutum a bayan ta. Karaf idanuwan su suka hadu. Kowanne sai da wani abu ya ziyarci jikin sa. Kasa dauke idanun sa yai daga kanta. A hankali ya fara kokarin bude baki ya mata magana amman ya kasa. Shigewa tai ciki ya bi bayanta. Zama tayi akan kujera bayan ta ajiye laptop din hannun ta akan desk. Dagowa tayi ta kalle shi a karo na biyu.

“Baka iya gaisuwa bane?”

Murmushi yai yana sake sunkuyar da kansa kasa. Zuciyar sa kuwa tamkar zata fito ta fadi saboda tsabar yadda take bugawa. Kallon sa Batoul ta sake yi tana dan hade rai,

“Baka jina ne?.”

Girgiza kai kawai yayi ya juya ya fita. Ita kuma ta zauna tana dudduba wasu syllables. Yana fita ya dena jin yadda bugun zuciar sa ke dokawa idan yaga wulgawar malamar tasu. Mota ya shige ko takan sauran lectures din da za’ai bai bi ba. Jingina yai da kujerar motar yana lumshe idanun sa. Gaba d’aya duk wani motsi da ganin sa ita yake gani. Kama kasan lips dinsa yai yana ciza. A hankali ya zaro wayar sa yana danna recording din muryar ta da yai sanda ta fara lectures. Tamkar mai ciwon lebe a hankali dakyar ya furta kalmar

“Ayana..”
(Beautiful flower)

Ya karasa fada yana jingina wayar a k’irjin sa hade da lumshe idanu yai murmushi. Direban dake jan motar ya tsaya yana kallon sa ta mudubi,

“Oga ba lapia kuwa?”

Girgiza kai Mubeen yai alamun a’a. A haka suka karasa gidah. Lokaci lokaci Mubeen kan saki murmushi shi kadai.....

Kodah Mubeen ya koma gidah gaba d’aya sai walwalar sa ta ‘karu. Mahaifiyar su ta kasa shiru sai data tambaye shi ganin ya zauna a parlor yana murmusawa lokaci zuwa lokaci,

“Mm da alama wani abun farin cikin ne yasame ka ko?”

Murmushi Mubeen yayi yana sosa girar sa da yatsa daya. Beyi magana ba, Hakan yasa Mamma Ahlaam yin shiru kawai tana girgiza kai. Mikewa tai ta shiga kitchen. Bata jima ba tafito da tray dauke da abinci. Ajiye masa tayi akan center table din dake gaban sa.

“Mamma a ‘koshe nake.”

Ya karasa fada yana rausayar da kai, Sam bayason cin abinci tamkar wani dan karamin yaro. Sa shi tayi a gaba da lallami har ya fara ci. Cikin haka Amb Salees ya dawo. Shima ya zauna yaci abinci, Suna tab’a hira lokaci zuwa lokaci shi da Haj Ahlaam. Banda Mubeen da ke danne danne a wayar sa.

“Mm ya school din? Tayi ko kana nan akan bakan ka na kai bakason ta?”

Wayar sa ya ajiye akan table yana kallon mahaifin nasa. Ajiyar zuciya ya sauke domin haka kawai yaji kuma bayason ya dena zuwa.

“No papa zan cigaba da zuwa.”

Amb salees da Mamma Ahlaam suka kalli juna cike da mamakin abinda Mubeen yace. Sam basu taba kawowa zai yi saurin sakkowa haka ba. Du bada idan ya tsani abu ya tsane shi kenan har gaban abadan. Idan kuma yanason abu to duk rintsi sai ya mallake shi. Shin ko meyasa ya sauya ra’ayin sa? Amb Salees ya jinjina kai yana daga kafada,

“Masha Allah! Toh Allah yasa albarka a karatun naku. Kaga hakan shine dai dai, Na fito takara za’a ga ‘dan ciki na bai je waje karatu ba kamar yadda sauran yan siyasa keyi. Toh Allah ya bamu nasara gaba ki d’aya..”

“Ameen Papa.”

Mubeen ya fada yana tsotsan kasan lips dinsa. Amb Salees ya kurbi ruwan gaban sa kafin yace,

“Toh har an gama lectures dinne ka dawo gidah?”

Girgiza kai Mubeen yai alamun A’ah.

“Toh this should be the last, Ka dena fashi. Saboda attendance is compulsory and ...”

Ai tuni Mubeen ya dena jiyo muryar mahaifin nasa, Take sautin muryar Batoul ta shiga yawo a kansa. Inda take musu maganar attendance compulsory ce. Sai lumshe idanu yake hade da kara jinginar da kansa a kujera.

“Ina fatan kana saurara?”

Sai a sannan Mubeen ya farfad’o daga day dreaming din daya tafi. Saurin kada yayi hade da mik’ewa ya tafi sashen sa. Yana shiga dakin sa ya wurgar da wayar sa akan gado. Ban’daki ya fada yayo wanka hade da alwala. Sallah yayi yadan taba karatun qur’ani kafin ya sake mikewa ya haye gado ya kwanta. Tuni bacci daddad’a ya dauke shi, cike da mafarkin Batoul wadda batasan ma yanayi ba. Wayaga karfin hali soyayya da malamar aji.

*GIDAN MATA TARA*

Ina gama abubuwan da zanyi a makarnta na dawo gidah. Gaba d’aya a gajiye nake wallahi. Lalle lecturers suna k’ok’ari wallahi. Rana d’aya har na fara fita daga hayyaci na. A gajiye likis na shiga layin mu. Tun daga farkon layin mu nake jiyo kwakwazon yan gidan mu. Allah ya kawo mu. Na fada a azuciya ta ina girgiza kai. Da sallama a baki na na shiga gida. Gaba d’aya a hautsine tsakar gidan mu yake. Ba babba ba yaro an zagaye Bintalo da Kawu Ishaq sai surfa zagi take yi tana buga zani hade da watsa hannu baya,

“Sittin ta ubangiji hak’uri na ya kare. Idan ita Kaltume ta bar maka toh ita taga zata iya. Ni kuwa sai ka sallame ni a satin nan. Idan kuma ka ‘ki. Toh Sittin ta ubangiji dole ne ku tattara naku ya naku daga dakin nan tunda ba mallakin ka bane.”

Kawu Ishaq ya daga hannu alamun ban haku’ri. Bintalo ta buga tsallen albarka ta dire, Hade da kwararo zagi da rantsuwa kan bazata yadda ba.

“A hayye nanaye! Yau ga gaye ba makilis, Sittin ta ubangiji isyaku ba yadda zanyi ba. Shekara da shekaru kana zaune ka gaje daki tamkar wanda akace an bar maka? Sittin ta ubangiji hak’uri na ya kare.”

Tana gani na tayo kai na tana susar takashi hade da dada masa duka. Ta watsa hannu baya tana nuna Kawu Ishaq,

“Kinga Batoul idan kaltume ta barwa isyaku rabin dakin can a tumunin takabarta shikenan. Ni dai yau dole ayi mai yiwuwa ko dai ya biya kudin hayar dakin ko kuma ayiwa daki kudi ya bani hakk’i na aciki. Sittin ta ubangiji nagaji.”

Shiru nayi domin na rasa ta cewa. Duba da ko Innar mu ta bar masa kason ta ba burge su za miyi ba. Kuma muma kadarar mu ce. Saboda me zamu bar masa? ‘Karawa me karfi- karfi kenan. Saurin girgiza kai nayi alamun a’a. Ina kokarin fara hawa bene. Bintalo tayi guda tana buga zani,

“A hayye nanaye! To isyaku kaji dai ko? Itama kaltume bata bar maka nata kason ba. Kai ne ka tattago aure kana zaman zaman ka. Toh yanzu dai tunda Rabi’atu bata ‘yaya ita ka’dai ce kawai ta koma dakin usaiba s..”

Ai bata ‘karasa ba Baba Usaiba dake gaban rijiya tana janyo ruwa ta saki guga ta fada ciki. Cike da masifa hade da kwakwazo baba usaiba taje gaban Bintalo,

“Kutsin ubancan kayya kai. A hayye kayya kai! Kin taba ganin inda kishiyoyi suka zauna a daki d’aya? A gidan uban wa ake haka?”

Bintalo taja guda ta saki tana yarfe hannu,

“A hayye yau ga gaye ba makilis. Kwarai kuwa, Sau nawa ma idan miji fatararre ne? Dakin da kike shi ne mallakin sa. Kuma dududu yaranki nawa ne? Su biyu ne jal sai ke ku uku, sai uban Iyali hud’u kenan. Sai ita Rabi’atun ku biyar kenan. Sittin ta ubangiji sai dai ku gwamatsu haka.”

Baba usaiba taja dogon tsaki cike da takaici ta cakumo wuyan Bintalo suka haura da dambe. Nai hayewa ta sama ina dariya. Domin wani lokacin sai diramar fad’ar su tasa ka murmusa ko kayi dariya. Dakin mu na shige. Akwai wuta fanka sai wulwulawa take yi. Innar mu ce kadai ta kishingida tana jin rediyo, Autar mu kuma da alama ta tafi Islamiyya. Gaida Innar mu nayi tayimun sannu da zuwa. kayana na shiga ragewa ina bawa Innar mu labarin makaranta. Hijabi na zura na dauki kwandon kayan wanka na nayi kasa. Suna nan suna fada har lokacin dana fito daga wanka. Anan na hango Bintalo tayi kukan kura ta shige dakin Rabi’atu tana watso kayan dakin waje tanayi tana surfa masifa. Sai gumi ne ke reto a fuskar ta,

“Sittin ta ubangiji dole ne yau ko dai ku bar dakin nan ko kuma ka biya kudin hayar dakin. Ai kaci moriyar dakin mun maka hak’uri..”

Kowa yayi shiru yana binta da kalllo ciki harda Kawu ila dake kan bokitin sa, Ya zabga tagumi yana sakacen hakoran sa. Girgiza kai kawai nayi na haye sama abuna cike da mamakin tijarar Bintalo. Itace maganin su.


X•••. O•••X•••O

Ranar juma’a da wuri na tashi tun farar safiya. Domin a ranar zan yiwa yan level one lectures din course na biyu da zan dinga daukar su wato ‘History of English literature..’ Wanka na na falla na turara kayan da zansa akan kabbasa. Dake jumu’ah ce shigar doguwar riga nayi baka ta abaya. Sosai nayi kyau. Yar farar hoda na shafa kadan hade da jan jambaki. Na zura zobe na hade da ‘daura agogo a wutsiyar hannu na. Kunshin da nayi daren jia ya kara turuwa yayi maroon sosai. A tsaitsaye na sha kunu da fanken da Innar mu ta ajiyemin agaba na. Laptop dina na zura a jaka ta hade da sauran littaifai na.

“Innar mu zan tafi..”

“Toh me sunan Uwa ta! Allah ya tsare ya baku narasa Ameen.”

“Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum Innar mu.”

Ficewa nayi daga dakin da sauri Ina mai duba agogon hannu na ganin zan makara. Bintalo na hango tana janyo ruwa a rijiya. Ta sha goyo asusu da zani na adashen da take ajiyewa a baya tamkar dan karamin jariri. Dariya ce ta kufce min na shiga darawa, Dagowa tayi ta dube ni tana wake-waken ta,

“Meya baki dariya ke kuma?”

Dena dariyar nai ina karasa sakkowa daga bene,

“Baba goyo naga kinyi..”

Watsa hannu baya tayi dayan kuma tana sosa takashi.

“Ke sittin ta ubangiji dole na sab’e abuna na goye, Har ‘daka aka biyo sahu aka sace shi satin baya. Gida fal cike da ‘barayi da iyayen barayi ga fatararru da masu nakashasshiyar zuciya, a hayye yau ga gaye ba makilis! Sittin ta ubangiji dole na goye kudin mutane.”

Murmushi nayi kawai na fice, Domin dana tanka abun kai na zai dawo. Tinda maganganun da ta fada dasu Kawu ila take da Kawu Dawood da Kawu Ishaq. Ina fita na samu mashin na haye ya kai ni wajen lodi nan ma ba jimawa mota ta daga sai makaranta...


*MUHAMMAD MUBEEN...*

Tashin sa kenan daga bacci, Yana duba agogo yaga ya kusa latti. Cikin sauri ya fada bandaki yayi wanka. Shigar ‘kananun kaya yayi samfarin Calvin Klein. Da sauri ya faffesa turare ya goga chapette a jajayen labban sa. Parlor ya fita hannun sa dauke da notepad da biro. Amb Salees ne kawai a zaune yana karatun jarida. Da alamun Mamma Ahlaam tana kitchen. Jin yadda parlorn ya cike da k’amshin girki,

“Papa! Good morning.”

“Morning Mm! Ya jikin naka ashe jiya da zazzabi ka kwana?”

Murmushi kawai Mubeen yayi yana kallon agogon hannun sa,

“Bara naje na kusa latti..”

“Kaji sauk’i ne har xaka tafi sch? Abincin fa?”

“E..”

“Toh! Allah ya dawo da

Please Login or Register in order to submit comment