Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaske Hajia. Wallahi kin bani kunya da har akan wannan maganar kikazo nan gidan. Dan kine mai taurin kai. Da har zaki gindaya masa sharadi yasa kafa ya shure zancen ki. Nan yake zuwa yana mata nacin auren sa. Yace kin amince harda doriyar za’azo akawo kudin aure. Ki tambayeta gatanan dai dai da sakan d’aya bantaba son ta dashi ba wallahi. Saboda mahaifiyar sa ba sirikar kwarai bace. Saboda haka daga yau Hajia ki tsawatarwa dan ki. Kada ya kuskura ya kara zuwa wajen Batoul. Kada ya kara tako kafar sa nan gidan da sunan batoul. Alakar mu dashi ta yanke. Alkhairin daya mana Allah ya biyashi ya bashi mata tagari wadda tafi Batoul a komai. Itama Allah ya bata wanda ya fishi. Allah ya hada kowanne da rabon sa. Ku rike arzikin kudin ku. Mu rike talaucin mu da wadatar zuciyoyin mu. Ke Batoul yo wankan ki wuce sama. Allah ya sawwake.”

Kai kuma ilyasu idan tunda kai ne sheda ina fatan ka saurari duk abubuwan da nace? Ka zamo sheda Batoul har gaban abadan tayiwa Haysam nisa...”

Tunda Innar mu ta fara magana har ta gama idanuwan yan gidan mu awaje suke. Domin Innar mu bata cika maida martani ba sai dai idan abu ya kai kololuwar ba’ci shine xata maida martani mai zafi. Kowannen su yai shiru ciki harda Haj Husna dake sandare a tsaye. Haka ta tsaya tai ta kumfar baki tana gatsine gatsine kafin ta fice tana mita. Ni kuwa bandaki na shige nai wanka zuciyata cike da dadin yadda Innar mu ta wanke mu agaban kowa. Koba komai itama Haj Husnan zata san dan nata baya gaban mu. Allah yasani naji haushin Haysam amman nasan so ne yasa ya fadamin ta amince. Kuka na nai marar sauti na haye sama. Yinin ranar kai na banda ciwo babu abunda yake. Mubeen ma har gidah yazo ya turo a kirawo ni saboda tsabar bashi da kunya. Yai ta aiko yara naki fita. Daga karshe ya turo aka kawomin jakata da waya ta. Daren ranar nan haka naita sak’e-sake a zuciata ina kuka ina gayawa Allah ya zaba min abunda yafi alkhairi. Haysam ya kirawoni yafi a kirga. Dana gaji na kashe wayar gaba ki d’aya. Gaba d’aya satin banje makaranta ba. Mubeen yaita shataletalen zuwa gidan mu ko sau d’aya ban fita ba. Domin shima haushin sa nake ji. Saboda ya renani reni me tsanani da har zai dubi tsabar idanuna yace yana so na.. Ni kuma haka Allah ya qaddara min rayuwa ta?

••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[8/28, 9:32 PM] Miss Xoxo: 𝓜𝓐𝓓𝓐𝓜𝓔_𝓨𝓔𝓡𝓦𝓐🧕🏼


*43*


*Tunda* wannan abun ya faru na nisanta kai na daga Haysam da kuma Mubeen. Duk abunda zai janyo haduwar mu da d’aya daga cikin su na nisanta kai na dashi. Da makarantar ma na fara fashi sosai. Sai da Innar mu ta tsawatar min tukun sannan nake zuwa. Gidan mu kuwa yawancin kullum sai sun yadamin magana kan yadda Haj Husnah ta kare magana zagi. Tun abun na damu na har yazo ya dena. Nai ta addua har Allah ya cire min shakuwar mu da Ya Haysam a zuciya ta. Kullum sai yazo gidan mu ya aiko kirana bana fita hakama waya sai yai ta kira bana dagawa. Sakonni kuwa kusan kowanne minti sai ya turo. Ganin yadda yake batawa kansa lokaci yasa na shirya sako na tura masa sannan na toshe shi (blocking) ba damar ya kira ni ko turo min sa’ko.

“Assalamu Alaika wa rahamatu Allah wa barakatuh! Ya Haysam barka da dare. Ina fatan kana cikin k’oshin lapia? Ya Haysam da farko inason na miko dimbin godia ta a gare ka. Duk abunda na zama a rayuwa kai ne tushe. Kai ne ka zamto tsani na rayuwa ta. Badan kai ba da banzama abinda na zama ba ayau. Nagode kwarai da abubuwan arzukan da ka yiyyi mana. Kalmomi sunyi kadan wajen nuna dimbin godiar mu agare ka. Fatan mu a kullum shine Allah ya biya maka bukatun ka na alkhairi, Allah ya kare ka daga sharrin masu sharri. Allah ya saka maka da gidan aljanntul firdaws. Ni batoul inayi maka fatan alkhairi a rayuwar ka, Abu na biyu shine zan baka hak’uri. Dan Allah kayi hak’uri ka yafemin, Inaso mubi umarnin iyayen mu.. Duk wanda yabi zabin iyayen sa hakika zai ga dakyau. Allah ya baka wadda tafini komai wadda zata soka ta kaunace ka har k’arshen rayuwar ka.... Bissalam!”

Ina gama karantawa na goge shi tas na kashe wayar tawa baki d’aya. Form din islamiyyar da zan shiga ta matan aure na dakko na shiga cikewa. Ranar asabar da lahadi kawae akeyi kuma da safe. Gwara na shiga na ragewa kai na damuwa idan na shiga cikin mutane.

*GIDAN ALH KABEER MAI WAFA*

*Zaune* Haysam yake ya tsurawa screen din wayar sa idanu ko k’iftawa bayayi. Ya kikkira wayar Batoul taki shiga sannan ko d’axu yaje gidan su taki fitowa. Gaba d’aya ya rame ya zabge yayi baki tamkar bashi ba. Damuwa tayi masa yawa, Ya rasa mai yasa Batoul din ke masa haka, Meya canza ta oho? Screen dinne yai haske alamun sak’o ya shigo saurin budawa yayi yana karantawa. Haj Husnah na gefe tana hankalce dashi. Gumi ne ya shiga ketowa Haysam sanda ya fara karanta sak’on. Ya daga kasan rigar sa yana sharce gumin dake kwararo masa. Da sauri ya mike zai fita Haj Husnah tasha gaban sa,

“Zauna babu inda zaka je. Dawo ka zauna.”

“Ummah.. Batoul! Batoul ce Umma”

“Ban isa na saka ba kenan?”

Kansa ya dafe idanun sa sun cicciko,

“Ba haka bane Ummah! Batoul ce ta turomin wani sako wai tanaso mu rabu da juna. Dama kuma ta dena futowa Idan naje gidan su Ummah. Bata daukar kiran da nake mata bare kuma ta maidomin da duk sakonnin da nake aika mata..”

Tsaki Haj Husnah taja tana turo daurin d’ankwalin ta gaba,

“Eh kai ma ka fita harkar ta..”

“Ummah saboda me?”

“Saboda haka muka yanke hukunci da mahaifiyar ta.”

“Ummah gidan su kika je?”

Haysam ya tambayi mahaifiyar sa yana ware idanu hade da zubewa a kasa tamkar wani karamin yaro. Haj husnah tayi murmushin mugunta tana hura hanci,

“Eh gidan su naje..”

Salati Haysam ya fara jerawa yana kwararawa mahaifiyar sa magiyar ta janye furucinta. Haj Husnah ta karo sautin kallon da take tana gyada kai alamun film din na tafiya da ita. Tasa kafa ta shure hannuwan Haysam daya dora a kafafunta yana rok’on ta a gurfane.

“Ummah! Ummah dan Allah! Dan girman Allah umma...”

“Wallahi zan sharara maka mari. Dan bakin munafurci inajin ka da mahaifin ka kana gaya masa ya nemar maka auren ta. Toh indai na isa da kai a matsayi na na wadda ta dauki cikin ka na wasu watanni ta haife ka, Na shayar da kai har girman ka. Inde na isa ina kuma da kima da mutinci a idanun ka inason ka rabu da figalalliyar yarinyar can...”

‘Figalalliya? Yarinya dimir-mir da ita?’
Haysam ya furta ahnkali ashe Haj husnah ta jiyo shi ta saki murmushi mai sauti tana kada k’afafuwa,

“Inde irinsu kake so gasu nan a dangi birjik. Ga sadiyya yar aminiyata maimuna yarinyar nan kamar ita ta kera kanta kuma ubanta commissioner ne. Ga lulu yar Haj Bushra komai yarinyar nan ta hada ance bana zata zama likita, Ga asmau yar kawun ku.. Bama wannan ba da zaka kwantar da hankalin ka kabi zab’in da nake so wallahi daka warke. Domin yar gidan Amb Salees nakeson hada ka da ita. Sakarai..”

“Ummah banason su. Ni wallahi Batoul nake so ummah. Dan Allah kiy..”

“Billahil lazi zan kantsama maka mari, Kaga ja’irin yaro kafaffe. Wallahi zan daga maka su idan dai ba zaka bi magana ta ba. Ka tashi kaje babu ni babu kai.. Kaje gaka gata nan..”

Ta karasa fada tana mai nuni da k’irjin ta. Nanda nan hankalin Haysam sai ya sake dugunzuma, Ya rarrafa ya kifa kansa a kasan k’afafunta,

“Na tuba Ummah! Kiyi hak’uri ki gafarce ni dan Allah... Kiyi hak’uri ummah kinji?”

Wani shegen murmushi Haj husnah tayi tana shafa sumar kan Haysam,

“Ya wuce auta na.. Tashi ga magani can akan dinning table kasha sai ka kwanta. Kaji?”

Gyada kai Haysam yayi yana sharce hawayen dake kwarara a idanun sa. Maganin ya dauka ya shige dakin sa ya barke da wani sabon kukan mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara. Shin ya zeyi zai bijerewa mahaifiyar sa ne ya nemi soyayyar zuciar sa? Dafe kansa yai da hannuwa biyu yana zubar da hawaye da majina. Lamarin dai ba sauki.

•••X••O••X••O•••

*GIDAN MATA TARA*

Dawowata kenan daga Islamiyya naci karo da Mubeen a kofar gidan mu yana danna wayar sa. Yana hango ni ya kuramin idanu,

‘Dan iska..’
Na fada a hankali ina canza hanya. Ta can baya na biyo ina sake hade rai na amman hakan besa yaron nan ya dena kallo na ba. Ga wani munafukin murmushi da yake yi. Can na hango su Bintalo da Ruma suna tahowa suma zasu shiga gidah, Na shiga tafiya ahankali domin mu shige a tare dasu, Bintalo sai watsa hannu baya take tana dadawa takashin ta duka, Gaishe da Ruma nayi zan shige ciki na jiyo muryar Mubeen na magana,

“Ma..”

Gudun kar su Bintalo su gano wani abun yasa na tsaya ina murmushin yake. Bintalo ta zaro idanu tana kallon Mubeen,

“Dan bature sake dawowa kayi yau ma?”

Gyada kai Mubeen yai yana murmushi. Bintalo ta watsa hannu baya tana mai buga tsakiyar zanin ta,

“Tab sittin ta ubangiji kai kam angama wankewa an baka kasha. Wannan sururucewa har ina? Tun bikin Najeebu kake zuwa gidan nan. Kai bakada mafadi ne?”

Mubeen ya girgiza kansa yana murmushi. Ruma ta janye hannun Bintalo suka shige ciki. Mubeen ya marairace fuska zai yi magana na shiga karkada hannuwa cike da fada na dube shi,

“This should be the very last time da zaka kara tako kafar ka zuwa gidan nan, Sannan ko a makaranta kada ka kara zuwa wuri na kaji na gaya maka. Ka goge number dina kada ka sake kirana ko turomin sak’o.. Wallahi zan mugun sab’a maka. Kaje ka nemi dai-dai da kai mana sai ni? Ko an gaya maka mulki ko sarauta na siyan soyayyah? That aside! Ni ba sa’ar ka bace kana ji na? Na girmeka sannan kai dalibi na ne. Wannan wane irin reni ne fisabilillahi???”

Kallon sa nayi yadda ya tsaya yana kallo na ko motsi bayayi, Ya rame kome yasa oho? Ahankali cikin wata irin murya yace,

“Ma lefi ne? Shin lefi ne don dalibi yaso malamar sa? Kuma kinata zancen shekaru ni kinsan shekaru na ne? Bama wannan ba haram ne soyayya da wanda ka girmewa? Age da shirme ne figures ne fa Ma... Dan Allah ki tausayamin Ma.. Wallahil azim saboda soyayyar da nake miki yasa na kayar da kai na a courses dinki saboda banason na dena ganin ki.. Tun bansan ki ba zuciyata ta san dake. Aduk sanda naga gilmawar ki ko wajen daya shafe ki wallahi sai bugun zuciata ya canza... Ina sonki Ma..”

“Kanada hankali kuwa?”

“bani dashi inde akan soyayyar ki ne..”

Wai ni yaron nan ke gayawa wa’ennan kalaman? Billahil lazi ya gama renani. Naja ajiyar zuciya na sauke ina tunanin abinda zan gaya masa,

“Toh ka nemi sa’ar auren ka. Saboda nakusa aure..”

“Ai ba’a daura ba.. Har yanzu ba wanda yasan mijin ki.”

“Toh inaso ka sakko daga *IGIYAR ZATON* zaka mallake ni. Domin ni da kai ba tsaran aure bane. Ka cire *ZATON* samu na a zuciyar ka kana jina? Kai fatali da duk wasu waswasi da zuciar ka ke ‘kissima maka ni a ranka...”

“*IGIYAR ZATO*?????”

Ya tambaye ni yana murmushi, Na dage gira ina yamutsa fuska,

“Tabbas *IGIYAR ZATO* saboda ka hau *IGIYAR ZATON* abinda ba taba samu zakai ba kana jina? Domin ka hau doron wahala, Igiyar da ba matabbaciya bace. Ka hau *IGIYAR ZATO* toh kayi gaggawar sakkowa daga kai domin ni Batoul ko a mafarki bazan taba soyayya da irin ka ba..”

“idan kuwa hakane bazan taba sakkowa daga *IGIYAR ZATON* son ki dana hau ba. Kece first love dina. Da son ki nake kwana nake tashi, Akan ki gwara na rasa komai na dana rasa ki. Har na gwammace nayi nisa da gidah akan nayi nisa da ke.. Son ki ya rigada ya gama mamaye ilahirin jiki na da ruhi na,

“My love is forever yours. Come rain and sunshine, I will treat you like a diamond and will never let you stay a mile from me. Saboda haka ki sakko daga *IGIYAR ZATON* ba zaki mallakamin soyyayar ki ba. Even if you are far away from me, you will never leave my heart even for a second, My love for you will blossom until my dying days because I have felt purpose and I want to show you, love...”

Jiki na babu abunda yake idan banda rawa. Wannan wacce irin musiba ce? Gaba d’aya jijiyoyin kansa sun fito sunyi rud’u rudu. Zaure na shige ya biyo bayana yana janyo min kasan hijabi, Kasa kallon idanun sa nai. Saboda yanada wasu irin sihirtattun idanu masu wuyar fassarawa.

“Cikamin hijabi....”

“Ma.. Meyasa bakya sona uhm.?”

“Sakarmin hijabi kafin na sab’a maka Mubeen”

“Is it not okay to fall over heels with you ?Uhm?”

“Na shiga uku... Dan Allah ka ky’ale ni..”

“Dan Allah Batoul....Ki so ni ko dan kadanne. I promise to be an excellent lover..”

“Karka sake gayamin irin wadannan kalaman. Ka nemi sa’ar yin ka dai-dai kai kana jina? Kuyi duk abunda zaku yi. Idan kuma aure kakeso to ka gayawa iyayen ka su maka..”

“Hmm’ ma kenan! Ni dama ai da aure nake son ki.. Kuma nan kusa babu daukar lokaci. Babu wacce zuciya ta ta aminta da ita fyace ke.. Amman wait Can’t I date you? Am I that unlikable? Uhm? Ina son ki so mai tsanani.. Dan Allah ki karba kokon barar soyayyata..”

Dogon tsaki naja cike da takaici na dube shi,

“Ka gama?”

Daga kai yayi jiki a sanyaye. ‘Kofa na nuna masa da hannu ina sake hade rai,

“Fita toh! Karka kara tako kafar ka zauren gidan nan da sunan zuwa waje na kagane?”

Shiru yayi yana kallon kasa, Nai ‘kwafa ina shigewa cikin gidah gaba d’aya ya dagula min lissafi. Da yan iskan kalaman sa masu ratsa mutane. Na juya na kalli zauren ina hararar sa. Murmushi yai ya fice yana jefa muk’ullin motar sa sama yana cafewa. Sama na haye na shige daki raina a jagule. Zama nayi a kusa da Innar mu ina sakin ajiyar zuciya,

“Innar mu...”

“Na’amm me sunan uwa!”

Numfasawa nai na shiga raba idanuwa ina harhada hannuwa,

“Innar mu acikin...”

“Na’am acikin me?”

“Innar mu acikin dangin mu na Shema babu wanda za’a iya had’amu aure dashi...?”

Innar mu ta mike daga kishingid’en da take tana rage sautin rediyon ta,

“Meyasa kikace haka uhm?”

Hawayen danake makalewa ne suka shiga zubomin, Allah yasani na gaji wallahi. Abunda Haysam yamin yanacin rai na. Ga yadda yaron nan ke uzzuramin. Ga maganganun da yan gidan mu ke gasamin, Hakama yan unguwa na kirana da sunaye kala kala. Fisabilillahi ya zanyi da rai na??

“Innar mu bakomai kawai gani nake ta hakan ne zan samu mijin aure..”

“Bar kuka uwata, Share hawayen ki. IN SHA ALLAH! Mijin ki nanan tafe, zaki yi aure nan kusa keda duk wanda basu yi ba. Da aure da mutuwa da haihuwa dik lokaci d’aya ne uwata. Wallahi baka wuce lokacin ka, IN SHA ALLAHU! Allah zai zab’a miki mafificin alkairi. Mijin ki na zuwa nan kusa mai sunan uwa. Wani jinkirin alkhairi ne... Bar kuka kinji?”

Daga kai na nayi na shiga share hawaye na ahankali ina jin k’arfi acikin zuciya ta. Kalaman Innar mu sun tausasamin zuciya ta..

••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_[8/31, 10:34 AM] Miss Xoxo: 𝓘𝓖𝓘𝓨𝓐𝓡____𝓩𝓐𝓣𝓞💞



*44*


Tunda wa’ennan abu suka faru ashe zukata da gangar jikin mutane uku ba acikin nutsuwa suke ba. Muhammad Mubeen yafi kowa jigata domin baida koshasshiyar lapiar da zuciyar sa zata jure rashin wani abu da yake so. Haka yaita watangaririn neman ganin Batoul amman hakan yaci tura. Shine a tafe kullum zuwa gidan su Batoul amma bata futowa. Gashi Bintalo ta sashi agaba. Muddin tagan shi haka zatai ta sukar Batoul awajen sa. Shi kuwa sai yai shiru har sai tagaji tatafi. A kofar gidan su yake kusan yini duk weekends idan zata islamiyya harta dawo yana hangen ta. Daya hanta hankalin sa zai dan kwanta sai ya tafi gidah. Gashi ko a makaranta bata bari su hadu. Kiran wayar duniya da tura mata sak’onni idan yayi bata dagawa. Ko ta whatsapp tayi blocking’ dinsa sam ya dena ganin statuses dinta da display pictures. Abun na damun sa kwarai matuka, Har ta kai ya fara rashin lapia a tsaitsaye...

Toh haka ma bangaren na Haysam lamarin ba sau’ki, Damuwa tai masa yawa tamkar zaucacce. Kodah mahaifin sa yai masa maganar gidan su yarinyar da yake so sai yace dashi an bada ita gudun karya tsallake maganar mahaifiyar sa. Mahaifin nasa bai kawo komai a ransa ba yai masa addu’ar Allah yabashi wata ta gari. Amman kullum Haysam sai yayi kukan bakin cikin rasa Batoul da yayi na har gaban abadan. Haj Husnah kuwa dadi kashe ta ganin zancen Batoul dai babu shi. Tuni ta fara cuku-cukun yadda zata hadu da matar gwamna wato mahaifiyar Muhammad Mubeen.

Batoul kuwa gaba ki d’aya ma abubuwa ne suka taru su kai mata yawa musanman yanzu da babu wata kawarta da tayi ragowa wadda batai aure ba. Uwa uba ita kadai ce yanzu tarage ba tai aure ba dubada yammatan gidan mata taran kowanne da nasa a hannu yawancin su.. Gashi ‘yayan Gwaggo Aminatu mata biyun da suka rage bikin su za’ai a satin. Sati na zagayowa Gwaggo ta turo da buses guda biyu aka kwashe su sai kaduna. Anan sukai kwanaki har uku ana gwangwaje bikin yaran na Gwaggo Aminatu.

*GIDAN MATA TARA*

Tunda aka kammala bikin yayan Gwaggo Aminatu muka dawo gidah sai na kasance tamkar bani ba wallahi. Na rasa mai yakemin dadi? Zanje makaranta na dawo gidah, Asabar da lahadi kuma naje Islamiyya. Ko hira ban cika yi ba acikin su Innar mu. Nafi karatu ko na janyo wayata na shiga whatsapp na dan karanta littattafan da marubutan online keyi.
**** Ranar wata sanyayyar asubahin asabar an tafka ruwan marka-marka muka tashi da tashin hankula har biyu a gidan mu. Tashin hankali na farko shine an nemi Mari da Hinde an rasa. Kaf Zaria babu inda ba’a cigita ba basa nan. Anje gidan magajiyan tasu ma nanma basa nan. Tashin hankali na biyu kuma an sace asusun kudaden da Bintalo ke ajiyewa na mutane. Tun asubahi ta suma ake kwara mata ruwa taki farfadowa. Gaba ki dayan yan gidan mu mun taru akan Bintalo ana kwarara mata ruwa amman bata farfado ba. Cikin haka sai ga Kawu khamis da Dijangala wato shugabar matan gidan magajiya tare da wani ‘dan daudu yaci dauri sai kace mace. Kawu khamis ya zauna a bakin rijiya yana tsatstsafe gumi,

“Fada musu yadda ake ciki malam..”

Dan daudun yai fari yana cokalo daurin d’ankwalin sa gaba,

“Malam fa kace? Ka dube ni ka kira ni Malam? Ka dena ragemin matsayi. Sunana Sahura nice baby..”

Ya k’arashe maganar yana yamutsa fuska hade da watsa hannu tamkar mace. Dijagangala dake gefe ta dubi Bintalo dake sheme,

“Itace babar Hinde?”

“Itace...”

Kawu ila ya bata amsa yana sake kwararawa Bintalo gugar ruwa a fuska. Dijangala ta yamutsa fuska tana bin kowannen mu da kallo,

“Toh Mari fa?”

“Ya tace...”

“Toh abisa binciken da mu kai mungano Hinde, Mari da kuma wasu daga cikin yammatan mu sun tafi birnin ikko (lagos) domin samun manyan alhazawa.”

“Lagos?” Na maimata a hankali ina girgiza kai. Ashe Kawu Khamis ya jiyo ni.

“Kinsan da zuwan nasu ne..?”

Saurin girgiza kai nayi,

“A’ah Kawu.. Kawai dai kwanakin baya can zan tafi makaranta naga Hinde da Marin a zaure naji kuma sun ambaci lagos.”

Yan gidan mu suka shiga rafka salati da sallallami. Kawu Ishaq ya numfasa kafin yace,

“Toh aina suka samu kudin zuwa ikkon?”

“Gaskia ban sani ba. Amman dai kudade masu yawa suka nemo kila. Saboda sai sun kama daki acan ga kudin abinci.. A gaskia bamuji dad’in tafiyar su ba muma. Saboda suna d’aya daga cikin y’ammatan mu dake janyo mana manyan mutane.”

Dijangala ta fada tana mik’ewa tsaye. Kawu khamis ya k’ada kai yana cire aswakin bakin sa,

“Toh kinga mahaifiyar Hinde dake sheme dinnan?”

Dijangala ta daga kai tana bin Bintalo da kallo dake sheme a kasa,

“Toh wallahi uwar adashe ce itace ke ajiyar kudaden yan adashe na yankin yan kasuwa. Ta neme asusun ta rasa gaba d’aya an kwashe. Shine ta suma.”

“Toh fa! Allah ya sawwake. Sury nice tashi mu tafi..”

Dijangala ta fada tana duban dan daudun. Mikewa yai yana botsarewa kamar mace,

“Toh bayin Allah da alkhairi. Allah ya dawo mama dasu lapia. Yan uwana ina lalle da gyaran kai idan zaku yi..”

Cewar dan daudin da suke kira da sury nice. Ni kuwa sakin lebe nai da saleba ina kallon sa. Abun mamaki baya karewa a duniya. Gardeden namiji amman ya maida kansa mace. Ficewa su kai suna shewar su.

Bintalo kuwa tamkar babu rai a tattare da ita. Cikin ikon Allah Gwaggo aminatun da aka kira aka sanarwa halin da ake ciki ta iso hankalinta a tashe. Ba bata lokaci aka kinkimi Bintalo akai asibiti da ita. Alawiyyah da zabbau sai kuka suke yi suma. Likitoci sunyi mai yiwuwa ganin Bintalo ta farfado amman hakan yaci tura. Likitan ya cire safar hannun sa yana kallon mu,

“Wai shin meya faru da ita haka ne? Kawai yanke jiki tayi ta fadi?”

“Dakta tsaya kaji! Baiwar Allahn nan uwar dashi ce. Tana ajiyewa yan kasuwa kudaden adashin su. Wanda idan karshen shekara tayi duk suka dauka zasu babbata kaso mai tsoka. Toh wallahi sai aka dauke kudaden a ma’adanar su. Dama kafin nan an nemi yar ta anrasa. Toh asubahin yau kuma sai ta nemi kudaden bata gani ba. Shine muka jiyo karar ta ta yanke jikin ta ta fadi.. Alawiyyah haka ne ko?”

Kawu khamis ya tambayi Alawiyyah yana kallon likitan. Alawiyyah ta fyace majina da hawayen dake yar tsere a fuskar ta,

“Eh Kawu! Tana ta neman inda ta ajiye bata gani ba. Ta tattambaye mu muka ce wallahi bamu gansu ba. Ashe wai an dauke su ne aka musanya da wasu ba komai acikin su. Kawai muka ji ta saki Kara ta yanke jiki ta fadi..”

“Toh acikin dakin ku take ajiyar kenan?”

“Eh dakta..”

“Toh agaskia hakanne ya janyo mata da babban tashin hankalin da zuciyar ta ta kasa dauka. Yanzu dai sai ta farfado xamu san abinda zamu mata. Amman dai ga ruwa nan an sa mata mun kuma yi mata allurori. Allah ya bata lapia.”

Likitan na gama magana ya kade rigar sa ya fice. Sam Bintalo bata farfado ba sai wajajen yamma ta bude idanun ta ahankali amman ta kasa motsa kowanne sassa na jikin ta. Dakyar take iya nanata,

“Kudi na! Kudi na a asusu shud’i da ruwan toka da na ruwan zuma... Sittin ta ubangiji sai an fito dasu.”

“Kai wannan mata kina ji da kan ki kina maganar

Please Login or Register in order to submit comment