Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kudi kuma? Tab Allah ya kyauta..”

Cewar Baba Ummita. Ta ja majina tana karkada kai hade da sake cewa,

“Yarinyar nan Hinde ita ta ja Mari shiga bankadaddiyar hanyar nan...”

Baba Ummita ta karasa fada tana kwararawa Hinde kwandon tsinantaka. Likitan ne ya shigo d’akin da sauri yana wa Bintalo yan gwaje-gwajen. Bintalo ta sake sakin wata kara tana nanata,

“Kud’i na! Kud’i na a asusu shud’i da ruwan toka dana ruwan zuma.. Sittin ta ubangiji sai an fito dasu.”

Likitan ya tsaya yana kallon Bintalo kafin ya haska wani abu a idanun ta yana girgiza kai,

“Baiwar Allah daga hannun ki sama ko kafar ki..”

Bintalo tayi tayi ta kasa. Gaba d’aya ta kasa motsa wani sassa na jikin ta, Lamarin fa tamkar almara. Mu kai jungum jungum muna kallon ikon Allah.Ajiyar zuciya likitan ya sauke yana duban mu,

“Ina mijin ta?”

“Mijin ta ya rasu dr! Nan dik yan uwan sa ne da ‘yayan sa..”

Gwaggo Aminatu ta fada jikin ta a sanyaye. Likitan ya ka’da kai,

“Manya biyu daga cikin ku su biyo ni ofishi na..”

Yana gaba su Gwaggo Aminatu da Kawu Ishaq na biye dashi. Suka je office d’insa ya xauna yana zayyane musu abunda ya samu Bintalo ya karkare da,

“Toh kuyi hakuri! ta samu mutuwar ‘barin jiki a bisa muguwar faduwar da tayi kuma tanada ciwon sukari. Bayan nan jinin ta ya hau shima...Ta samu hauhawar jini.”

Salati suka fara yi gaba d’aya jikin su yayi sanyi. Sun jima kafin su dawo wajen mu. Inda Kawu Ishaq yace mu tafi gidah ai Bintalon ma sallar su xa’ai. Ai kuwa da yamma aka dawo da ita a nannade acikin tabarma tamkar kayan wanki, Sai surutu take ita kad’ai tana dadara hakoran ta..

“A hayye yau ga gaye ba makilis. Sittin ta ubangiji dole afito mun da yara na su uku, Shud’i da ruwan zuma da ruwan toka...”

Haka Bintalo tai ta surutai abun tausayi wallahi. Ni kam har a sujood sai dana mata adduar samun lapia da bayyanar ku’din nata. Haka muka kwana a gidan nan bacci barawo ne ya d’auke mu. Domin surutan da Bintalo ke zubawa dole su hana mutum runtsawa.

*WASHE~GARI*

Wajajen sha biyu da kwata saura Ruma tayi sallama tana kwalawa Bintalo kira da alamun batada masaniyar abunda ya faru,

“Bintalo sakko ki karb’i xubin su Shehi na gangaren kasuwa da Mati mai gidan biredi.. Har zan taho muka had’u da shegiyar nan. Nace ah ladiyo anyi abun kai. Wallahi nagaya miki sai ta shiga sunne kai tana sosa dudddugaggen kwakwidon kanta. Yanzu dai zo ki karbi kudaden mutanen nan. D’auka ya kusa zuwa kai na.. Nasan kina nan kina aikin susar takashi.. Bintalo!”

Na rike haba ina ayyana yadda Ruma zata yi idan taji babu kudaden nan. Gashi jia ake fad’ar Mari da Hinde ne suka sace su suka tafi dasu ikko suka musanya mata asusuwan. Baba Ummita dake shararar hawayen barin Mari ta sharce majina tana kallon Ruma,

“Ruma bakisan abunda ya faru bane?”

Ruma ta dora hannuwa a kirji tana ware idanu,

“Waye ya rasu?”

“Mari da Hinde sun gudu an neme su an rasa... Kuma”

“Kuma me?”

“Bintalo ba lapia tasamu mutuwar barin jiki.”

“Toh fa subhanAllah. Tana ina?”

“Tana dakin ta...”

Cewar Baba Ummita! Kowa yai shiru ya kasa gayawa Ruma gaskiar lamari. Ruma ta haye sama tana yan sallallami,

“Sannu Bintalo! Dankari Mak’ari! Sannu! Ina asusun suke na tafi dasu kawai tinda ke ba lapia.?”

Bintalo na hangen Ruma ta fashe da kuka tana kikkifta idanu. Ruma ta zauna a gefe tana rufe hancin ta. Ganin yadda Bintalo tayi face-face da katifar tayi fitsari akwance sai zarni kuma su Zabbau basu gyara ba. Ruma ta muskuta tana kallon Bintalo cike da tausayi,

“Garin yaya haka tafaru Bintalo? Ko akan tafiyar su Hinden ne...?”

Bintalo ta fashe da wani kukan tana k’ok’arin girgiza kai alamun a’a. Ruma taja ajiyar zucia ta sauke tana dudduba lungu da sakon da zata gano asusuwan.

“Sannu Bintalo! Allah ya sawwake. Dama akace idan baka mutu ba ba agama maka halitta ba. Ko a dad’a ko a rage ka... Ina asusun suke ne?”

Zabbau ta shiga harhada yatsu tana kallon Ruma ta gefen ido,

“Kiyi hak’uri baba Ruma..”

“Uhm babu komai zabbau! Allah zai tashi kafadunta ai ku za’a bawa hak’uri yanzu.”

“Ba wannan ba..”

Ruma ta kada kai alamun son jin bayanin gaba. Zabbau tasa hannunta akai ta shiga sosa wa tana in’ina..

“Baba Ruma walle talle bankin kudi dai an sace hi..”

Ruma ta mike tana sosa kunnenta,

“Kika ce me?”

“Ca nai an sace su. Walle babar mu batada masaniya akai. Mari da Hi...”

Ai bata karasa ba Ruma ta zube tana firfita fuskar ta da takalmi alamun ta shiga kololuwar balai. Gumi ne ya shiga tsattsaga a ilahirin jikin ta. A zuciye ta mike ta cakume wuyan Bintalo tana jijjigata gefe d’aya kuma ruwan balai da zagi take zuba mata,

“Kutmelesin kan babban bala’in bolar jakara. Billahil lazi ba yadda zamu yi ba. Kai idan gidan nan zaku siyar na rantse da Allah sai kin biya kudin mutane. Munafuka, Algunguma, Munasura, Yar bakin ciki da hassada. Har zaki kwanta cutar karya bayan kin cinye kudin mutane?...”

Bintalo ta shiga kakari saboda yadda Ruma ta shaketa tana jijjigata. Gaba d’aya yan gidan mu kowa ya fito yana kallo wasu suna leken dakin nasu. Alawiyyah ta fashe da kuka tana janye Ruma. Cikin zafin nama Ruma ta dauke ta da mari tana huci,

“Idan kika kara rik’e ni sai na hallaka ki wallahi. Kaga yan iskan mutane, Ayi muku dare kuyi ma mutim rana? Ringidi-ringidi gantalalliyar mahaifiyar ku tazo ta same ni na temaka mata. Na shiga na fita na samo mata ta zama uwar adashe. Sai data bari an tara himilin kudi za’azo min da maganar banza? Ni za’a damfara wai kudi an sace?..”

“Walle talle baba Mari da Hinde ne suka sace..”

Zabbau ta fada tana rausayar da kai. Ruma taja tsaki tana d’aure mayafin ta a kugu cike da balai ta watsa hannu baya tana buga zani,

“Kalar ku kalar mahaifiyar ku, Algungumai marasa amana. Ni zakuyi wa baraki? Wallahi sai anfito da kudaden mutane. Ba yadda zanyi ba. Ke Bintalo kinsan na dameki a rashin mutinci na shanye billahil lazi.”

Kawu ila ya jinjina kai yana bata hak’uri ta watsa masa kallo tana kada masa hannuwa,

“Da hak’uri yai gabas yamma nayi bakin munafiki. Munafukan banza da wofi. Wallahi sai kun biya ni kudaden mutane. Babu abunda ya dame ni. Kudaden mutane ba zasu ciwu ba. Yan iska marassa mutinci..”

“Ahayye kayya kai! Naci biredi na yage leda hehehe! Banci naninba nanin ba zata ci ni ba. Ilyasu da bintalon dai keda hakkin biyan ki tunda sune iyayen su..”

Baba usaiba ta karasa fada tana dukan cinyarta. Kawu ila ya dankara mata harara yana mai da kallon sa ga Ruma,

“Baiwar Allah babu ruwana wallahi! Bintalon dai itace zata biya ki ko kuma Ummitan mahaifiyar Marin.”

Baba Ummita ta buga tsallen albarka tana buga kirji,

“Da Mari aka kawo ni gidan nan? Ni kadai aka wanko daga wajen budar kai aka kawo ni, Billahil lazi sisi na ba zaiyi ciwo ba. Kai ne ubanta meyasa bakasa ido akanta ba? Kai zaka biya wallahi.”

Kawu ila ya shiga cire yar sharar rigar sa zai daka baba Ummita kenan Gwaggo Aminatu ta shigo cikin gidan mu tana tsawatar musu...


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[8/31, 10:34 AM] Miss Xoxo: 𝓜𝓐𝓓𝓐𝓜𝓔___𝓨𝓔𝓡𝓦𝓐🧕🏼



*45*


“Kai Kai Kai! Haba ya isa. Wallahi tun daga bakin titi ake jiyo hayaniyar ku, Ku yanzu fisabilillahi ba zaku dena wannan abubuwan ba? Wannan wacce irin rayuwa ce kuka d’orawa kan ku? Allah ya sawwake..”

Haka taita nanatawa har ta hawo bene. Ta dubi Kawu ila dake kokarin mai da rigar jikin sa,

“Sannu ilyasu! Da wa zaku daku?”

“Da Ummita ne Yaya.. Ta renani. Agaban mutane take min rashin kunya.”

“Ba haka bane Yaya. Shine nan ike cewa wai da ni za’a biya Ruma kudin da aka sace.”

Baba Ummita ta fada tana dankarawa kawu ila harara. Gwaggo Aminatu ta jinjina kai tana kallon Bintalo,

“Tab sannu Bintalo. Allah ya baki lapia. Yanzu kudaden da kuke magana angano wanda ya sace su ne?”

“Eh Mari da Hinde ne Yaya..”

Kawu Ishaq yabata amsa yana cire tagumin daya zabga. Ruma taja tsaki tana jijjiga kafadu,

“Billahil lazi sai an biyani kudaden mutane. Babu abunda yasha min kwalar riga.”

“Baiwar Allah ke kuma wacece?”

“Ni ce wadda tai silar samawa bintalon zama uwar adashe. Kuma ina cikin masu zubin, Shine zaku zo da wata bazawarar magana wai kudade babu? Wallahi ba za’a damfare ni ba. Kudi yadda suke cis sai an fito dasu.”

Gwaggo Aminatu ta zabga tagumi tana kada kai,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Wallahi sai dana bawa Bintalo shawarar tadena ajiye himilin kudaden nan agidah saboda tsautsayi. Kai ya SubhanAllah!”

“Oho dai! Can ta matse muku a matse matsin matsalolin ku. Ita tace zata iya ta dage sai da aka bata. Mu dari ne keyin adashin nan. Kinsan himilin kudaden da aka tara kuwa? Na rantse da Allah ko mutuwa Bintalo zata yi sai an biya kudaden nan a yau.”

“A yau fa kika ce? Baiwar Allah duk cikin mu nan bamu da masaniyar sanda kuka gama maganar adashen ku. Da ita ku kai komai, Ko kotu akaje wallahi bamu da lefi.”

Gwaggo Aminatu ta bata amsa tana murmushi, Ruma ta sake jan wani tsakin a karo na ba adadi tana jijjiga kugu,

“Oho dai. Yanzu dai ya ake ciki. Yanzu zaku harhado ku bayar ko sai da yamma? Dan a yau za’a biya mu kudaden mu. Ko mu kai kara folisitehen..”

Gwaggo Aminatu tayi shiru kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya,

“Idan nace miki zamu iya hada kudaden ku mu baki na miki k’arya wallahi, Saboda babu wanda zan tursasa ya biya abunda ba dolen sa bane kowa yana ji da kansa. Saboda haka zamu yi meeting da yan uwan mu gasu. Duk yadda ake ciki zamu kirawo ki kiji. Allah ya kyauta..”

Ruma ta kwararo rantsuwa ta dire tana karkada hannuwa,

“Wallahi kudade ba zasu sha ruwa ba. Yadda suke sai an biya su tas, Marasa mutunci..”

“Dakata baiwar Allah! Yanzu zamu iya nannade hannuwan mu mu barki ke da ita domin sanda kuke abinku ba masaniyar wani acikin mu. Zancen a had’a kudi a biya ma wallahi bai taso ba. Domin babu wanda zamu yiwa dole bama wannan ba bamu mai k’arfin iya biyan ku wannan kudaden. Kede yadda ake ciki kyaji kawai.”

Ruma ta buga zani tana dankarawa Bintalo harara ta karasa kusa da ita tana huci,

“Bara na miki yadda zaki fi ganewa bakar algunguma, Sittin ta ubangiji sai kin biya ni kudaden mutane. Shegiya maras mutunci wadda ba Allah a ranta. Muguwa uwar bakin hali, Kishiyar ki da yaranta kin sasu agaba kina musu mugunta da zagon kasa sai gashi a kanki komai yake k’arewa kinsamu mutuwar barin jiki. Wallahi inde kudi basu fito ba sai kin biya ni ko da tsiya-tsiya...”

Tana gama fa’da ta fice tana huci tana sake nanata,

“A kuma kirawo ni anjiman dan billahil lazi kudade ba zasu ciwu ba.”

Gwaggo Aminatu ta girgixa kai kawai tana kallon kowannen mu,

“Shi yasa ake cewa idan zaka gina ramin mugunta gina shi gajere saboda zata iya kasancewa kai zaka fada. Idan ka gina shi mai zurfi ma kai zaka fada, Ya kamata ace kuyiwa kanku karatun ta nutsu, Rayuwar nan ba matabbaciya bace wallahi kana zaune lokaci kankani zaka jika cikin rami ba ranka an shafe ka a rayuwar duniya. Akan me zaka tsaya kana jifan dan uwanka da sharri? Shi fa sharri wallahi dan aike ne duk inda zai je ya dawo sai ya koma kan ka ko wanin ka,

“Abinda kuke bakwa kyautawa musanman Bintalo da kai Ilyasu. Ku duba ku gani gaba d’aya acikin gidan nan rayuwar ku biyu dinnan tafi ta kowa watangariri. Ilyasu dubi kwana ki yadda shagunan ka suka kone gaba d’aya jarin ka da abunda ka mallaka ya lalace. Tun yaran nan na kaltume na kanana kake tsangwamar su da kyararsu, Ka kori Najibu ni banda masaniya ma sai daga baya. Wai zai afkawa kanwar Bintalo yanzu gashi Najibu ya zama wani abu a rayuwa yayi karatun sa ya samu aiki har yayi aure da gidan sa. Islahan da kuka ha’da baki da ita ina kwanakin baya akace tayi cikin shege an zubar har anzo daurin aurenta aka fasa?,

“Yanzu wa sharrin ya komawa? Bayan nan Ilyasu kaita had’uwa da masifu na rayuwa baka daddara ba ka sake matsawa Batoul ka hanata zama da samarin kwarai, Ka kore su tas. Kana jajibo mata wasu daban. Ta haka ka ha’du da gamon ka. Satin ka uku a chaji ofis ilyasu. Duka ba wanda ba’a maka ba. Da gande-gand’e aka samu aka futo da kai. Kasan ya akayi? Toh bari kaji dakunan ka guda biyu da parlor an siyar, da su aka biya maka bashin kudaden da Alhajin ke binka.. Domin wanda muka harhada bai isa ba.”

Kawu ila ya dafe kirji yana ware idanu,

“Siyarwa fa kikace Yaya, uban uban waye ya siya?”

“Zage ni Ilyasu nagode.”

“Ba zagin ki nake ba Yaya. Meyasa za’a siyar min da hakk’i na ba tare da masaniya ta ba?”

“Amma bakada mutinci ko kad’an Ilyasu, Wa kake jira ya biya maka da? Banda ma zumunci da zuciyar musulunci ka isa mu biya maka? Toh a tak’aice dai da mu kai shawarwarin mu ba mafita yan kudaden da muka ha’da basu taka kara sun karya ba. Agaban shedu akai liman hamza da barrister kb. Muka roki Najeebu dan gidan Kaltume alfarma ya siye daki mai ciki da parlorn, wancan wanda babar su basmah ke ciki kuma shima muka mai kudi Najeebun ya siya muka biya maka bashin da marigayi salisu ke binka muka bawa iyalan sa gadon su...”

Kawu ila ya zube a kasa yana zunduma ihu,

“Inaaa ba zai yiwu ba wallahi..”

“Wallahi mai yiwuwa kuwa ta yiwu, Banda abinka da bamuyi maiyiwuwar ba mun ro’ki yaron ya siya kai ka isa ka fito daga chaji ofis d’inne? Wallahi akotu zasu maka ka. Yaro dan arziki dan kirki ma da yace shi kar ace ya siya saboda ya bar maka ka cigaba da zama har karshen rayuwar ka. Kawai dai daku na mallakin sa ne.”

Kawu ila ya shiga birgima yana koke koke. Ni abinma ya daure min kai? Don wallahi bansan da maganar nan ba kwata kwata banida masaniyar Yayan mu ne ya biya kudin wajajen. Gwaggo Aminatu ta shiga fiffita da mayafinta. Saboda yadda aka taru aka rufar mata akai. Gashi dakin ba iska.

“Sannan kema Bintalo da sannu kike girbe abinda kika shuka, Duk kulle kullen da kike akan kaltume tun bata hayayyafa ba harta fara hayyayyafa yaran ta har suka girmaa suka mallaki hankalin kansu baki dena ba, Yanzu yau ina Najeebu shin meya zama a rayuwa? Kun kore shi yayi hak’uri yai karatu ya zama wani a rayuwa gashi har yayi aure. Batoul gatanan kaf gidan nan babu wanda ya kamo ko farcen ta ne a ilimin addini dana boko, Gashi nan aiki take da sannu gashi nan itama ta zama wani abun. Duk abunda kike kulla musu akan yayan ki yake karewa daga ke har ilyasun,

“Ba sharrin da baku yiwa Batoul ba akan ciki da sauran su, Sai gashi Hinde da Alawiyya su suka fara kwaso abin kunya, Alawiyyah ta samu cutar shan inna, Hinde kuma harda rabon ciki gashi nan ta haife shi. Zabbau ma gashi nan mijin ta ya saketa har saki uku yace yaran kuma ba nasa bane. Yanzu dubi abunda ya faru dake Bintalo duk fa Allah ne yake sakayyar sa tun anan duniya. Bama wannan ba daga ke har ilyasun gaba d’aya ‘yayan ku bame cikakkiyar tarbiyya. Ace wai har Mari da Hinde sun san zaman kansu agidan karuwai? Suna bada jikin su ana zina dasu? Kuma su kawo muku kudi ku amshe? Nan fa zan taho gidan nan kwana ki motar mu ta baci mun tsaya a gareji sai ga Mari a tsakiyar maza tana shewa suna babbaka daria,

“Nazo na maka magana Ilyasu kace min wai tana temaka muku ne shiysa. Yanzu ai ga irinta nan. Kwadayin ku ya kai ku ya baro ku. Sun kwashe kudaden Bintalo sun tafi lagos zaman karuwanci. Duk inda kuka fita dole a nuna ku ana zund’en ku. ‘Yayan ka tara Ilyasu kowanne da bakin ciki da yake cusa maka, Yazeedu da shafi’u sun zama barayi, Mariya ta zama karuwa ta shahara ma tabar garin, Narata yarinyar nan kunce bata dawowa gida sai dare itama. Walidi kuma ya gama renaku kana fada yana mayar maka ga shaye shaye, Basmah an mata fyade itama duk akan rashin basu ishashiyar tarbiyya ne. Kuna barin su suna fita ko’ina cikin dare, Ya kwakwume muku su ya musu fyade itada Fareeda danma Allah yasa anmata aure ita,

“Ga wasu yaran kanana kana dasu duk mata, Furera, Bushra, Mardiyya. Yayan ka mata shida rigis ga maza uku kowanne da bakin cikin da suke sanya maka, Haka kema Bintalo naki gaba d’aya ma mata ne. Amman dukkanin su bana kirki ciki harda Hauwa’u itama naga ta zama kamar Hinde. Gaba d’aya ku duba ku gani rayuwar ku data yayan ka dik abunda kuka shuka ne kuke girbar sa. Matan ka sun guje ka kowacce zaman yayan ta take, Yaran ka suna ciyar da kansu. Yanzu ku dubi Bintalo ha’ula’i ne da ta samu kanta aciki duk kuwa da tata qaddarar kenan amman ai komai yana da sila. Toh haka rayuwar take wallahi kana ji da kanka ma yaka kare ballatana kana d’aukar hakkin wani, Haka abun yake wallahi inde zalunci kasa a gaba toda sannu zaka girbe shi tas. Saboda shi zalunci ko yaya mutum ya zubda hawaye ko ya kai karar ka wajen Allah to fa adduar nan batada hijabi ga mai sama sai yayi sakayya ko anan duniya ko a lahira,

“Yara goma sha tara ne agidan nan cif amman gaba d’aya yaran kaltume ne suka fita zakka kama daga tarbiyya, Ilimi da kuma sanin yakamata. Wallahil azim shiysa rayuwar su ke tafiya dai dai kullum ci gaba suke yi. Nasha kiran ku a’boye ku Ishaq da khamis da Dawood na muku magana akan ku tsawatar ku tsayar da lamarin nan duba da nidin ba anan nake ba amma kukai biris, Duk shiysa komai ya shafe ku tunda da sanin ku ake komai ku zauna yaro karami acikin mu yana juya ku saboda yana da dukiya ko? Yanzu ina dukiyar tasa! Kudin ma kun juya masa baya saboda yana cikin halin rashi yanzu, Shiysa ku kanku rayuwar taku data yayan naku gatanan itama sai a hankali ne. Ishaq yaran ka biyu mata Larai da Talatuwa suma har yanzu ba wanda yai aure acikin su, Ba karatun ba bokon sai neman magana a unguwa. Kai kanka baka da tsayayyen aikin yi sai jiran shago,

“Kai ma Dawood hakan take kai a komai ma ba abunda ya da meka ciki harda bawa yayanka tarbiyya kuwa. Tun sanda ka rasa aikin ka ka zama tamkar sullutu wai abincin cefane ma sai matar kace zata futa ta nemo. Yaran ku kunki tsayawa ku inganta rayuwar su, Fareedah da ita aka hada akai wa fyade donma Allah ya temaka kun aurar da ita, itanma dai ance ta kamu da ciwon yoyon fitsari. Fareed kuwa yana biyewa su yazeedu suna daukewa mutane kaya da kudade. Sam ba tsari a lamarin shin wannan ba hakkin wanda kuka sa agaba bane?,

“Khamis kai ma duk tare kuke har gwara ma Dawood shi bai cika magana ba, Amman shirun ma ai lefi ne. Yanzu dubi kwanaki nan akace Yusha’u ya sace kudin bintalon ashe shi da yaran Ilyasu ne. Bala ma ya zama dan chaburos? Kullum yana tafe yana tangalin maye.. Shin dan Allah ku gayamin rayuwar ‘yayan waye ke tafiya a mizanin gaskia? Me suka muku kuka tsane su haka? Shin wannan wacce irin tsantsar qiyayya ce? Gwara kowa ya sani. Tun da ran salis kuka tsani ya auri kaltume duk dan yafi samin alheri acikin ku, Kuma alokacin mahaifanta sune masu hali. Iyayen mutunci da karamci suka ri’ke ku a garin nan tamkar wanda suka haifa, Ya nemi auren yarsu suka bashi ba tare da sun hana ba saboda karamci irin nasu,

“Akai auren kuka tsawwala mata, Shekarar farko kuka fara yanyana maganganun juya ce bata haihuwa. Kuka sa ala dole ya auro Bintalo, Kuka uzzura kaltume ta tatafi gidan su ashe da shigar ciki ta dawo ta haife danta kukace ba dan Salisu bane na shege ne, Hakama haihuwar Batoul itama kuka shegenta ta, Me suna na ce kawai ta haife ta anan. Amman kowacce haihuwa sai taje gidan su saboda tsabar uzzurawa da mugunta irin taku. Sai ‘karairakin maganganu kuke yi wai ‘yayanta shegu ne. Wallahi tallahi kuji tsoron ALLAH musanman Bintalo da Ilyasu. Duk ku kuke fara haddasa komai,

“Bayan Bintalo ke kin manta halaccin da akai miki aka auro ki. Abun kunya fa kika aikata har an zauna daurin auren ki aka fasa. Aka dubi zumunci muka rufa miki asiri Salisu ya auro ki. Amman tunda kika shigo gidan nan kike neman raba shi da matar sa ta sunnah, Wai har kike shegen ta yaranta da neman fidda ta daga gidan ta na sunnah. Abar dai kaza cikin dakin ta domin tashin tashi na bata da dadi, Sai mu kwana mu wuni ana maida zantuka kuma dik marassa dadi. Duk dai gashi nan kowannen ku yana ganin sakayyar kaltume da yaranta akan sa. Kuyi gaggawar neman yafiyar su. Wata kila Allah ya dube ku da idon rahama idan suka yafe muku, Sannan maganar kudaden adashe kuma bansan yadda zamuyi ba dake ba Bintalo, Abunda nasan zamu iyayi shine kawai zamu sanarwa yan uwanki, Sannan zamu harhada kayan dakin nan yan gwangwan su siya, Zamu baki yan awanni keda ragowar yaran ki kuyi shawara dasu, Nan dakin da rabin na tumunin takarbi idan da akwai wanda zai siya a gidan nan toh sai mu siyar masa, Muma zamu harhada dan abunda aka samu sai abawa matar, Idan kinada wasu ajiyayyun kudaden ko kadarar suma ki kawo a biya su. Ke kika san yawan kudaden mu ba sani mukai ba, Bara mu baku wuri. Ke Zabbau da Alawiyyah ina Hauwa’u kuzo kuyi shawara da mahaifiyar ku. Sanda Allah yasa su Hinde suka shiryi suka dawo sai asan yadda za’ai.. Allah ya rufa asiri. Mu basu waje ko?”

Gwaggo Aminatu ta karasa fada tana mikewa tsaye. Na sharce hawaye na ina girgiza kai. Tabbas an jima ana zaluntar mu agidan mu. Sai gashi yanzun d’aya bayan dayan su suna gani akan su dakan yayan su. Lalle Allah buwayi ne gagara misali. K’asa Gwaggo Aminatu suka sauka ita dasu Kawu ila dake mitar yayan mu ya sai wajen sa. Ni kuwa d’aki na shige zucia ta cike take da maganganun gwaggo Aminatu.. Ba a wani d’auki lokaci sosai ba Zabbau ta sauka wajen su Gwaggo. Ina ga sun yadda da yadda gwaggon ta tsara, Domin tuni Alawiyyah ta zura mayafi ta kira yan gwangwan sukai wa kayan dakin Bintalo kudi suka dauke su duka suka biya kudin. Gwaggo ta kira Innar mu kasan mai suka tattauna oho naga dai Innar mu ta dauki kudaden ta na cikin kwalla ta koma. Daga nan kuma suka hawo saman inda gwaggon take sake cewa,

“Toh Alhamdulillah kamar yadda na fada d’axu mun gama magana, Dakin da Bintalo da Kaltume yake a matsayin tumunin takabar su yanzu na roki kaltume ta siye shi ya zama mallakin ta. Sannan ni na siya dakin nan na Bintalo agaban shedu ga kudi a account dina, Sannan zan kara wasu wanda nai niyya saboda zumunci. Ishaq da Khamis ma sun bada dubu biyu

Please Login or Register in order to submit comment