Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar banza hakan yasa har zuwa lokacin ban samu mijin aure ba.

Sai da naje na dawo nake tambayar Inna yadda aka kare, ta kalleni tare da cewa.

“Kin san dai ni ba shiga harkarsu nake yi ba, ban fita ba ina dai jiyo su suna zage zage, shi kuma kawun ku Ilyasu yana tarewa Bintalo kinsan aminaine, haka suka taru suna ta rashin mutuncin su, sai daga baya ne naji ana cewa akai Hinde asibiti a zubar da cikin kafin ya fara girma asirin gidan mata tara ya tonu.”

“Ikon ALLAH kenan, Inna kinga dai yadda suka so na lalace ALLAH bai yi ba.”

“Eh shi yasa nace ku dena damuwa indai kunsan cewar baku sabawa mahalicin ku, Shi sharri dan aike ne. Gashi yau k'aik'ayi ya koma kan mashekiya, ALLAH ya kara karemu daga son zuciya.”

“Amin Innar mu.”

Daga haka na juya na d'auki abun karatuna ina kuma dubawa, su kuma can anje asibiti an basu maganin zubar da ciki tashi, Alawiyya kuma bata da cikin sai dai bincike ya nuna cewar tana dauke da ciwo mai karya karkuwar jiki shine ma yasa ta d'an fara ramewar nan ba kamar yadda take ba a baya. Hinde kuwa tunda tasha maganin nan take yin wani abu tamkar zata mutu dan Bintalo sai kuka take yi ta riga ta cire rai da rayuwar 'yarta ta, duba da yadda take sumewa tana dawowa, kuma cikin yaki b'arewa ballantana hankalinta ya kwanta.

“Wallahi kun cuce ni yaran nan, wannan daga gani aikin sihiri ne banda haka ya za'ai ace duk tambad'ewar da Mariya tayi a garin nan amman bata yi ciki ko ta samo cuta ba sai yarana. Ku duba kuga yadda tsinanniyar yarinyar can take bin makarantu tana bin samari ace itama bata da komai sai yarana dan an gansu da farin jini, wallahi ba zata zabu ba. Kaltume da Ummita kune kukai min makarkashiya.”

“Ke..ke Bintalo menene hakan? Wace irin magana ce kike yi haka?”

Cewar kawu ila saboda yaji ta ambato sunan matarsa akan sunyiwa yatanta asiri.

“Bafa zaka yi min jan ido ba ilaysu, kyar nake kallon kowa a cikin gidan nan. Kai ka manta lokacin da aka yago maka Basmah, nan kazo kana cewa Najibu ne bayan duk munsan sharri kayi masa,To sittin ta ubangiji su Ummita da Kaltume ne suka janyowa Hinde da Alawiyya.”

Bintalo ta karasa fada tana jan majina ji kake 'fyaat...'

___
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*ZATO IGIYAR TARA MATA*


2️⃣3️⃣


Kawu ila yaja bokitin sa ya zauna yana kwakwular hanci.

“Sai dai kaltume amman ummita ba za tai miki shiri ba.”

Baba Ummita dake gefe ta buga zani tana sallallami,

“Kai Bintalo kiji tsoron mai sama. Ki dena sharri, Du gidan nan akwai me bin bokaye ne irin ki?”

Baba ummita ta karasa fada tana gud’a. Usaiba ta tayata tana shewa,

“A hayye kayya kai, A nayi munajin dad’i a bari muji haushi.. Kutsin ubancan kayya kai.”

Bintalo tayi kukan kura ta cafki wuyan ummita tana gwara ta da bango,

“Sittin ta ubangiji karya kike yi. Shegiya almura, Shi yasa dan bakin halin ki akayo miki kishiya...”

Ummita ta kwace hannun ta tana yarfe shi, Domin ita batada jiki sai tsiwa, Ai kuwa ta daku awajen Bintalo,

“A hayye nanaye! Bintalo, Bintalo, Bintalo! Kowa yasan cikin shege ki kai, Aka rufa miki asiri akai auren ki sadaqah.”

Bintalo ta shatalo kafar ummita ta buga ta da kasa, Itama tai saurin riko Bintalon suka fadi tare,

“Ubanki ne ya mini? Kaji mata mai bakin hali. Sittin ta ubangiji du gidan nan keda mijin ki kune munafukai rikakkun mugaye.”

‘Ayiririri!’ Ummita ta saki guda tana dukawa,

“A hayye duniya labari, Yanzu ke har kece zaki cewa da wasu mugaye? Duk wata kutingwila dake ake shirya ta. Makira, ai gashi nan kin gani akan yayan ki.”

Nan dai fada ya kaure a tsakani, Baba usaiba sai rawa take takawa tana gud’a,

“A hayye kayya kai! A nayi muna jin dadi a bari muji haushi. Kutsin ubancan kayya kai...”

Kawu ila sai janye Ummita yake, Bintalo tana kara dankota. Cikin fada aka yagewa Bintalo jelar gashi. Ta kutuntumo ashariya ta durawa ummita tana sosa wajen,

“Kika cusge min gashi? Sittin ta ubangiji sai na karairaya ki yau.”

Haka su kayi ta fada suna yayyage kayan jikin su. Wasu daga cikin yan gidan mu suna zuga su wasu suna ko’karin rabiyar fada. Lilis su kai wa junan su, Domin Bintalo ta jibgi ummita sosai, Ita kuma ummita ta yayya kushe Bintalo a jiki. Kawu ila yaja dogon tsaki ya fice yana mita. Girgiza kai na nayi na koma cikin Daki na cigaba da nazarin wani aiki da aka bamu.

*WASHE-GARI*

Ana idar da asubahi Bintalo ta figi mayafi ta fita tun gari na duhu bai waye ba sosai. Mashin ta hau ya kai ta wani waje mai nisa. Sauka tayi ta shiga cikin wani dan karamin gidah. A kofar gidan an rubuta: Gidan Malam Mai Gani Har Hanji (Nesa tazo kusa). Mutane fal sun jeru a acikin gidan layi akeyi d’aya bayan d’aya ake shiga wajen malamin har layi yazo kan Bintalo ta shiga. Katon daki ne dauke da allunan karfe an musu rubutu, Gaban malamin kuma kasa ce fal akan buhu ya kannanade carbi a wuyan sa yana zuba gari a wata tukunya a gaban sa sai hayaki ne ke tashi a ciki. Barkewa Bintalo tayi da kuka tana face majina,

“Malam Zurqallaini mai gani har hanji temako nazo wajen ka..”

Malamin ya callara ‘kara yana ambatar wasu sunaye na tsibbu,

“Kin kawo kuka gidan share miki shi, Tabbas an sako ki agaba nagani gashi nan..”

Bintalo tasa kasan zanin ta ta fyato majina tana cigaba da shararar hawaye,

“Sittin ta ubangiji malam sun min zobe, An yiwa babbar ‘yata asiri mijin ya sake ta yace ‘yaya ba nasa bane. Sannan biyun dake gabana sittin ta ubangiji suma malam anyi musu sammu, d’aya anyi mata ciki ya’ki zubuewa ma dayar kuwa cutar kashe jiki aka sa mata malam. Gaba d’aya an nakushe mu...”

Malam ya jinjina kai yana hargitsa k’asar gaban sa,

“Saka hannun ki anan.”

Dora hannun ta tayi yace ta cire, Ya hargitsa kasar yana zana wasu kalmomi ajiki,

“Zahiri gashi nan nagani, An sako ki agaba domin so ake gaba d’aya a lalata muku rayuwar ku.”

“A hayye! Sittin ta ubangiji ahalin gidan mata tara ne. Malam duba kagani ummita da kaltume ne ko?”

Ya k’ada kansa alamun Eh yana sake dudduba kasar,

“Sune, Bakomai bane fyace dan kinyi musu zarra ne. Kinfi su cigaba a rayuwa.”

“Sittin ta ubangiji haka ne malam, Domin yarana biyun har an kusa bikin su fa. Wallahi Malam sai gashi an fasa an nemi masu neman nasu ma an rasa. Gidan da suke gina musu ma anje, Sittin ta ubangiji masu ginin gidan sunce basu san kowa ba.”

“Ai tsafi suka miki, Da jaki akai aka binne shi. Ba karamin bakin asiri bane.”

Bintalo ta dafe kirji tana raba idanuwa, Cikin rawar murya tace,

“Dagaske malam? Sittin ta ubangiji dama lamarin da ka gani kasan sihiri ne.”

“Yanzu dai abinda nake son kiyi shine, kije ki tsamo min jinin al'adar ko waccen su, ina nufin su Kaltume da Ummita sai ki kawo akwai shu'umin maganin da zan hada miki dashi idan kin kawo. Karki ce min ba zaki iya ba, saboda dole sai kin kawo tunda kika zo nan wajan.”

Mutuwar zaune Bintalo tayi a wajan, saboda bata san inda zata samo wannan abun da yace ba, hasalima bata sani ba ko har zuwa wannan lokacin Kaltume nayi ko ta dena duk da cewar bata dena haihuwa ba. Taja numfashi tare da sake matsawa kusa dashi tayi k'asa-k'asa da murya tamkar wani ne a kusa da su, ta share saman hancinta tare da cewa.

“Babu wata hanya da za'a sake min Malam? Wallahi wannan abun da kace na samo maka zai min wahala saboda bansan lokacin yin al'adarsu ba.”

Wani banzan kallo ya dokawa Bintalo wanda yasa hantar cikinta kadalawa, sannan ya janyo wani katon carbi a can gefenshi yana cewa.

“Dole sai kin kawo sannan zaki samu biyan bukatarki, sannan duk gurin da zakije suma hakan zasu gaya miki. Karki sake rik'o ta wani canjin dan ba samu zaki yi ba, tashi ki ban guri.”

Kamar zata fashe da kuka haka taji saboda tsabar tashin hankali, wannan aikin yayi mata sauri, sam bata da sanin inda zata samo abinda aka buk'ata. Ta mik'e tsaye jiki babu kwari ta kuma tarar mai mashin. Kai tsaye tayi masa kwatancen gidan Alhaji Kabeer saboda taje tayi aiki ta kuma samo musu abinda zasu sanya a cikin su ita da 'ya'yan ta da jikokinta da mahaifinsu yace ba zai karb'e su ba. Da sallama ta shiga cikin sa'a ta tarar Haj Husnah tana kitchen tana bawa Inna Rabi umarnin abinda za'a dafa. Bintalo ta gaisheta sannan ta jira aka sallami Inna Rabi ita kuma tabi bayan Haj Husnah.

“Ya aikai ne Bintalo?”

“Hajiya wani mummunan labari ne na kawo miki, sittin ta ubangiji da idanuwana naga abin.”

“Ai ke kam Bintalo ba kya tab'a kawo min maganar arzik'i sai wacce zata tayar min da hankali. Yau kuma me aka yi?”

Murmushi Bintalo tayi domin tasan duk maganar da ta kawo ko babu dad'i sai an saurareta, dan haka ta gyara tsayuwar ta tare da jan majina tace.

“Sittin ta ubangiji Hajiya basu bar miki yaron nan ba, har yau suna tare kuma bakiga yadda suke mishi ba kamar wani d'ansu, uwar ta tatseshi itama 'yar ta kwashi abinda zata kwasa, yanzu yace idan bai aureta ba zai kashe kanshi.”

Haj Husnah ta dafe faffad'an kirjinta tare da zaro manyan idanunta tana kallon Bintalo, guri ta samu ta zauna saboda wani jiri da yake neman kai ta k'asa. Ita sam ba kyautar da yake musu bace take bata mata rai, maganar auran Batoul da yake cewa zai yi shine bata so saboda yarinyar bata yi mata ba. Da hannu ta yiwa Bintalo alamar ta tafi ta bata guri, wanda da alama zuciyarta ce bata yi mata dad'i.

Bintalo kuwa tana fita ta saki dariyar keta, sannan taje tayi aikinta ta shiga kitchen lokacin Inna Rabi tana parlour tana gyarawa taje ta kwashi d'anyan abinci, su taliya da macaroni da indomie sai ledar Maggie star ta kulle a cikin buhun da take zuwa dashi. Sallama tayi musu tabar gidan tana tsinewa Haj Husnah, harda cewa idan bata yi wasa ba sai ta zama kisjiyar ta.

Haka dai aka ci gaba da rayuwa a gidan mu, Yayan mu da ya gaji shima ya shaidawa innar mu cewa zai dinga dawowa gida saboda ya dinga ganin mu. A haka wattani suka shude anata gwagwar mayar rayuwa, rashin zaman lafiya ya karu a gidan mu, kasan cewar Kawu ila da Bintalo yanzu ba'a zaman lafiya tun lokacin da aka kama Bintalo tana d'aga underwear d'in Ummita a cikin kayan wanki ta, shikenan zargi ya shiga, kuma ita Bintalo jini taje nema yayin da Ummita tace ai sace mata zata yi daman ta saba ganin undress d'inta a jikin Bintalon wai shiru kawai take yi sai yau abin ya tonu.

Ni kuwa karatu na nake yi hankali kwance domin Yayan mu yana taimaka min da wasu abubuwan ga kuma gwaggo Aminatu. Wata ranar talata ne ina makaranta bayan na dawo na tarar da Hinde ta haihu d'anta kato mai kama da Alhaji Mu'azzamu sak, ni dai tunda nake ban tab'a ganin bakin jariri ba sai wanda Hinde ta haifa. Su kuma ganin da wanda yake kama yasa suka kira Alhaji Mu'azzam suka sanar dashi, aikuwa ya rantse ya kuma rantsewa ba zai karb'a ba domin taci kud'in sa da yawa, dan haka taje tasan yadda zata yi da d'an.

Bintalo kuwa itama tace ba'a d'akinta za'a raini shege ba, rigima ta b'arke tsakanin Hinde da Bintalo.

“Kinsan Allah Hinde yaron nan gidan marayu zaki kaishi domin ba zaki ja min zagin mutane ba a gari, haka kurum ke ba aure ba ace kin haihu, ga shegen mutumin yace ba zai karbi d'an ba.”

“Kwarankwatsa dubu Babah bazan kai d'an nan ko ina ba ina son abina, haka kurum, duk bake bace kike samu a hanyar lalacewa ba. Me yasa idan muka kawo miki kayan dadi bakya cewa mu mayarsa sai yanzu da d'ah yazo zaki ce a kaishi gidan marayu, sittin ta ubangiji babu inda zan kai shi idan ba haka ba zan kaiki kotu.”

“Ke Hinde! Ni zaki kai kotu saboda baki da mutunci? Wabillahillazi kinyi kad'an yarinya, gaki ga d'an nan ai daga yau na dena nemowa kowa abinci dan uban ku, kowa ya fita ya nema da kanshi tunda abun haka ne.”

“Aiyirrrrrrr nanaye!”

Cewar Usaiba da Ummita abin ya kuma b'atawa Bintalo rai ta kuwa dinga zaginsu tana cewa suma sai sunga fiye da abinda ake yi mata ita da yaran ta. Ni kuwa tunda na shiga d'aki Inna ta dora yatsanta saman labbanta tayi min alamu da karna sake nayi mata maganar da ake yi a gidan, duk da gulma na cina haka na hakura nayi shiru dan nasan abun ne ya ishi innar mu shi yasa bata son maganar. A haka dai aka ci gaba da zama, Hinde ta sanyawa d'anta suna Ibrahim ana kiransa da Khaleel, a cewar ta gara tasa mai sunan uban shi saboda ta konawa Alhaji Mu'azzamun rai, nan gaba zata nemo har gidan iyayensa taje ta kai musu d'an. Alawiyya kuwa sai sake figewa take kasan cewar babu wadataccen magani gashi kullum cikin fad'a suke da 'yan uwanta dan basa ko rab'arta wai karta goga musu.

***Haysam kuwa gabaki d'aya ya d'auke k'afarsa daga k'ofar gidan mu, ko a hanya bana ganinsa sai abun ya d'an fara damu na, saboda ko babu komai shi d'in yana da muhimmanci a cikin rayuwata, sai dai ban san yadda zanyi na nemeshi ba hakan yasa na tattara shima na rabu dashi da niyar duk lokacin da muka had'u ma gaisa. Naci gaba da karatuna cike da nasarori masu tarin yawa wanda banyi tunaninsu ba a cikin rayuwata, na sake wayewa, kaina ya kara girma sai dai bana fad'in rai ba, a'a na zallar karatu.

A ranar da na kammala karatun degree d'ina na biyu (masters) na dawo cikin murna, a ranar ne Yayan mu shima yazo kuma dawowar da yayi yana son ya d'an jima kafin ya koma kano kasan cewar yafi sabawa da can, ga kuma sana'o'i yana ta yi babu mai takura masa bare yace yayi wani abun. Innar mu ta siyo zabi guda biyu kasan cewar tana d'an adana kud'ad'e idan Yaya ya aiko mata dasu, kuma nima idan na samu kyautar kudi daga wajan lecturers d'in mu ita nake bawa, ta siyo kayan miya tayi mana farfesu mai dad'i. Yayan mu ya siyo lemuka da buredi ya bawa Innar mu aka kasa Autar mu takai ko wane d'aki, muma muka zauna muka ci namu muna farin ciki dajin dad'i.

“Kaga su Batoul manyan gari, yanzu kuma sai neman aiki ko?”

Nayi dariya har hakorana suna bayyana, na ture ledar buredin daga kusa dani ina cewa.

“Wallahi kuwa Yayan mu, sai fatan alkairi ALLAH yasa mu samu aikin nan mai tsoka.”

“Zaki samu da yardar ALLAH, babban kwali fa gareki sister.”

Kafin nayi magana muka jiyo muryar kawu ila yana kiran Yayan mu, kai daga jin kiran kasan cewar babu lafiya. Innar mu ta kallesa tare da cewa.

“Karka yi masa rashin kunya, kabi shi a hankali bana son tashin hankali.”

“Toh Inna bari naje naji menene.”

Yana tsaye kusa da bokitin sa da alama zama yake so yayi amman yana jiran fitowar Yaya Najib, ai kuwa yana gama sauka shi kuma kawu ila ya zauna akan bokitin. Kusa da kafar bene Yaya Najib ya zauna yana gaishe da kawu ilan.

“Bana amsawa rik'e abarka munafuki, kai ni nan da kake gani na kyar nake kallon kowa a cikin gidan nan. Ashe zaka dawo?”

“Kayi hakuri kawu wallahi ina son zama ne a kusa da 'yan uwa na, kayi hakuri duk inda zanje ba zai kai nan ba duk lalacewarsa.”

Gyara zama kawu Ila yayi yana zabgawa Yaya Najibu harara kamar kwayar idon zata fad'o, ya kuma jan bokitin yana matsowa kusa da Yaya yana cewa.

“Ai dole ma ka dawo duk gidan uban dakaje, ka dauka kaci banza ne da zaka lalata min yarinya kace ba zaka dawo ba? Toh bari kaji in gaya maka, dole ne ka auri Basmah, yadda ka b'ata min 'ya haka zaka zauna da ita har tsawon rayuwarka marar mutuncin yaro.”

Cikin razana da rashin fahimtar inda maganar kawu ila ta nufa, Yayan mu ya mike tsaye baki na rawa yace.

“Ka.. Kawu wac.. Wacce Basmah???”

“Ta gidan ubanka, nace ta gidan Ubanka, banda wacce ka lalata kana da wacce ka sani ne?”

Nan da nan jikin Yaya Najibu ya hau rawa yana faman girgiza kansa tare da ja da baya, ba tare da ya sani ba har ya kusa zuwa wajan rijiya gata a bude.....

__
_Ghen Ghen!💃🏿MUN kusa shiga ainihin labarin😂💃🏿INA fatan kuna nishadantuwa da foundation din da mukayi😉 A dinga rike shekarun sbd labarin a gaba yake IN SHA ALLAH🥳🤩Parte afta parte😍🥰💃🏿💃🏿💃🏿_


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*IG😘❤️*


2️⃣4️⃣


••. ••. ••. ••. ••.

Kowa ya bud'e ido amman babu wanda ya bud'e bakinsa yayi masa magana akan inda yake nufa, ni kuma dana fito daga d'aki zan sakko kasa na zubar da burbushin biredin da muka zubar kawai na hango Yayan mu yana tafiya da baya, sauran kiris ya fad'a ciki na kirashi da sauri ina sakkowa da gudu.

“Yayan mu rijiya a bayan ka.!”

Jin magana ta yasa shi juyawa a hankali yana kallon bayan nashi, Ni kuma ban luraba skirt d'ina na take da kafata, ai kuwa na fado na dinga gangarawa har sai da nazo k'asa. 'Yan gidan mu dake lebe suna ganin yadda kawu ila ke ciwa Yaya Najibu mutunci, sai gashi nima na fado sai duk suka fito wasu na dariya wasu na min Allah ya kara yayin da wasu ke yi min sannu. Duk na kurje harma na samu targad'e a kafata ta dama. Innar mu ta sakko kasan tare da d'ago ni dan har lokacin Yayan mu bai gama dawowa cikin hayyacinsa ba akan maganar da kawu ila yayi masa. Innar mu na rungume dani ina zubar hawaye saboda na bugu da yawa, ta tsaya tana kallon kawu ila wanda yake ta faman kumbura fuska tace dashi.

“Duk ka gama abinda zaka yi akan 'ya'yan d'an uwanka, dashi da ALLAH duk suna kallon ka, Basmah kuma kaje can ka samu wanda ya lalata maka ita amman ba dai d'a na ba, kuma babu aure a tsakaninsu domin ka riga ka iskanta min yaro, ka sheganta min shi, ka tsine masa, ka aibata shi, insha Allahu ba zai tab'a auran jikinka ba bare har ka sake kulla mishi wani abun.”

Tana gama fad'a taje ta janyo hannun Yayan mu, ni kuma tana rungume dani ina d'ingishi muka haye sama, 'yan gidan mu suka bimu da ido babu wanda ya iya cewa uffan saboda sunga yau Innar tamu a kule take kowa zata iya sauke masa abinda yake damunshi.

“Ah lallai Kaltume kin rik'a, ni kika zazzage ko? Toh zaku zo ku neme mu da kanku, ba dai mune dangin 'ya'yan naki ba? Mu zamu aurar dasu, haka kuma mu zamu je nemo auran shi munafukin yaron naki, toh zaki yi nadama dan sai kinzo kin shanye duk wad'annan kalaman da kikazo kika gasa min.”

Mudai muna d'aki Innar mu na jajjamin kafata, Yayan mu kuma ya dafe goshi da alama abinda kawu ila ya fad'a ne yake damunshi. Can dai ya numfasa tare da cewa.

“Inna wannan abun na kawu ila ba wai kiyaya kawai yake mana ba harda hassada, wallahi Inna hassada ce kawai yake mana dan yaga Allah yana kare mu daga duk wani mugun baki da suke yi mana. Amman banda haka mene na cewa nine na lalata masa 'ya? Inna wallahi tallahi ba Basmah ba kadai kowace mace ban tab'a sha'awar kusanta ba bare wannan figigiyar yarinyar, Allah ya isa kuma ban yafe ba da wannan kageggen sharrin da yayi min.”

“Kuyi hakuri, kuci gaba da addu'a insha Allahu babu abinda zai sameku sai alkairi.”

Haka mukaci gaba da rayuwa, Yayan mu yaci gaba da business d'insa yana samun kud'in kashewa, nima bayan na warke daga targad'an da nayi naci gaba da yin Awara ta kuma alhamdulillah ina samu sosai. Ganin ina samu yasa Zabbau itama ta fara yin awarar itama, sai ya zamana ita a zaure take yi, duk wanda ya shigo zai siya saita tare shi tace ai ni na dena yi, a haka ta kashe min kasuwa, sai ban hakura ba saboda yanzu bana son zaman banza sai na fara yin meat pie na siyarwa, nan ma ALLAH ya kuma sanya min albarka a ciki domin matasan unguwar mu haka zasu yi ta aikowa suna siya. Ganin haka yasa na fara yin zobo ina siyo kankara ina sawa idan na kulla a leda, shima Yayan mu yana fitar min dashi can wajan aikinsa da yake zuwa, bakin ciki ya sake dira a zuciyar 'yan gidan mu ganin mun fara basu zarra dan har ledar d'aki muka sanyawa Inna muda Yayan mu, muka siyo katon bokiti na zuba ruwa yadda idan muka cika shi sai mu dad'e bamu nemi ruwan famfo ba.

•••

*GERMAN EMBASSY SCHOOL*
*ADDIS ABABA*

Gaba d’aya ta gama gajiya da jiran yayan nata. Ta fito daga owners corner din da take ta tsaya a bakin gate tana hango shi yana tafiya kamar ba zai taka kasa ba. A hankali yake tafiya yana jan jakar kanin sa dake biye dashi yana shan ice cream. Girgiza kai Jannat tayi ta dan daga murya dan kiran yayan nata. Cikin harshen Amharic na Ethiopians tace dashi,

“tolo tolo ibakihini wenidimē MM”
(Yaya Mm kayi sauri please)

Ko kallon ta bayyi ba ya bude murfin motar ya shiga bayan ya budewa ‘kanin sa gaba ya zauna driver ya jasu.

*ETHIOPIA*
(Addis Ababa)

*AMBASSADOR SALEES MUHAMMAD RESIDENCE*

Gida ne ‘kerarre wanda ya amsa sunan gidah samfarin ginin ‘kasar Ethiopia, Fari ne tas haka ma kayan furnitures din ciki duk farare ne. Wani ‘kayatattan parlor ne daya amsa sunan sa, Komai na cikin sa fari ne da silver.

Wata farar yar dattijuwar mata ce zaune a parlorn tana kallon news a tashar cnn. Center table din dake gaban ta dauke yake da kayan alatu fal akan tray, Lokaci zuwa lokaci takan dauki d’aya daga cikin fruits din ta kai bakin ta. Da alamun itace matar gidan. Domin ga babban family photo nan dauke da hotan ta da mijin ta da kuma wasu mata da maza su hudu da alamun yaran su ne.

Driver na gama parking suka firfito daga cikin Motar, suka shiga cikin gidah bakunan su dauke da sallama. Su ukun suka tafi suka rungume mahaifiyar su suna murna. Shi kuwa babban namijin hanyar sashen sa yayi mahaifiyar tasu ta kira shi,

“wedezīhi k’its’ibeti wedezīhi na”
(Zo nan yanzun nan..)

Har ya kai kafar bene

Please Login or Register in order to submit comment