Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girgiza jiki agaban kowa,

“Sittin ta Ubangiji karya kake yi, Waya san sau nawa kake lalata ‘ya...”

“Karya kike yi Bintalo, wallahi tallahi wannan yaron baya kula wata ya mace ma ballanta na har yakai ga lalata. Allah ya isa wallahi. Kin kai ni karshe Bintalo..”

Innar mu ta karasa fada tana sharce hawayen bakin ciki. Kawu ila dake jingine da kafar bene ya ja tsaki yana komawa dakin sa. Kawu Dawood ne yai kokarin cewar,

“Toh ita yarinyar tafada da bakin ta abunda ya faru. Sai musan hukuncin da zamu dauka ko kuwa?”

Su Kawu Khamis suka daga kai alamun ‘Eh hakan yayi’. Kawu Dawood ya sake maida kansa ga Islaha da kanta ke a ‘kasa tana lankwasa yan yatsun ta yace,

“Ke gaya mana gaskiyar lamari, shin abunda yace shine gaskiya ko kuwa karyane shi ya kira ki?”

Bintalo tasa kafa ta take ta Islaha alamun tace Eh shine ya kirata. A hankali Islaha ta goge hawayen dake kwarara a idanun ta, cikin rawar baki tace,

“Eh Kawu! Hak’ik’a Yaya Najib shine ya kira ni, Tun ba yau ba yakeson yai la.l..lalata da ni.”

Bintalo ta saki wata uwar guda, kai kace amarya aka kawo. Cikin buga zanin ta hade da tafa hannuwa tace,

“Alhamdulillah yanzu naji zance. Daman na gaya muku shine ya neme ta.”

Yayan mu ya saki wani marayan kuka mai k’ona zucia, wanda kowa ya saurara sai ya tausaya masa. Cike da rawar baki ya tsugunna a gaban Islaha yana duban idanun ta, Wadda tai saurin kauda kai gefe.

“Is..Isl.Islaha ki dubi girman Allah ki sanar da su gaskiyar lamari, zamu mutu zamu koma ga Allah. Allah yana kallon ki, shin ni na kira ki ko kuwa kece kika neme ni?”

Islaha tayi shiru tana goge hawayen nadama, Yayan mu ya sake tambayar ta har sau uku nan ma dai amsar d’aya dince dai tabashi. Kawu Dawood yai gyaran murya kafin yace,

“Toh shikenan yanzu dai a barwa wayewar gari komai, Ke Islaha kiyi hak’uri hakan ba zata sake faruwa ba. Kai kuma Najibulla kaje langa langar ka kwana zuwa safiya zamu yanke maka hukunci. Allah ya kyauta”

Wani kukane ya kufce min jin abunda Kawu Dawood yace, Na dubi Islaha jiki na rawa nace,

“Kiji tsoran Allah Islaha, karki ga kwarjinin Bintalo, ki fad’i gaskiyar lamari.”

“Dakata shegiya, waya ce ki tsoma bakin ki? Zatai muku karya ne? Zaki matsa ko sai na sharara miki mari. Ai wallahi Idan naji hukuncin da aka dauka masa bai min ba wallahi zakuji sammaci a kotu.”

Cewar Bintalo. Ta karasa fada tana jan hannun Islaha, Innar mu dake gefe ta sharce hawayen fuskar ta, Sannan ta dubi Yayan mu cikin sakin murmushin dayafi kuka ciwo tace dashi,

“Kayi hak’uri wannan yaron. Kai dai ka cigaba da fawwalawa Allah lamurran ka, zamu tayaka da addua. Wallahi komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskiya.”

Tana gama fada ta shige daki, Nabi bayanta ina fashewa da kuka, Tsabar bakin ciki Yayan mu ko kayan shimfidar sa bai dauka ba ya fice daga gidan. Daganan kowa ya watse. Ana jiran safiya tayi aji hukuncin da zasu yanke wa Yayan mu.

*WAYEWAR GARI*

Taliyar jia na shekawa ruwan zafi muka ci. A roba na zubawa Yayan mu na tafi kai masa. Yana zaune a bakin kofar langa-langar kansa a kife.

“Yayan mu!”

Na fada ina mai ajiye robar abincin a gaban sa, dago kansa yai. Na tsorata kwarai matuka da ganin yanayin sa. Jijiyoyin kansa sun fito sunyi rud’u-rud’u dasu, idanuwan sa sun kada sunyi jajir dasu, lokaci d’aya ya zabge ya jeme tamkar wanda yayi shekararren ciwo. Murmushi ya ka’karo yana mai kokarin danne damuwar sa,

“Na’am Batoul.”

“Barka da safiya Yayan mu.”

“Barkan mu. Yasu Innar mu?!”

“Lapia lou Alhamdulillah.”

“Ga abinci nan Yaya ka daure kaci”

“Wallahi cikina a cushe yake. Amman zan ci.”

“Yauwa Yayan mu. Allah ya maka sakayya, Ya fidda kai daga sharrin su”

“Ameen ya Allah.”

Mik’ewa nai na barshi yana kokarin bude filet din da aka rufe robar dashi. Ina shiga gidah na kwaso kayan wanke wanke na sauko kasa na wanke tas. Na koma na hada gawayi na dora ruwan zafi. Tsabar munafunci ko makaranta babu wanda yaje acikin yaran gidan mu, kowanne jira yake yaji hukuncin da za’a yanke wa Yayan mu. Ta sama na hango Kawunnin mu suna ta shiga parlorn Kawu ila d’aya bayan d’aya. Anan duk suka hallara. Kasancewar nanne kadai mai parlor kuma wadatacce wanda zai dauke su. Kawu Ishaq, Kawu Dawood, Kawu Khamis, Sai shi Kawu ila din. Daki na ruga na zauna hade da janyo carbin Innar mu na shiga yin lazimin Allah ya dora Yayan mu akan su. Allah yasa su yanke masa hukunci sassauk’a.

Can parlorn Kawu ila kuwa hallara su kai, Sai da sukai yar caftar su wanda dole ne idan suka hadu sai sunyi fada. Tukun sannan daga baya Kawu Ishaq kasancewar shine babban su hakan yasanya yayi gyaran murya kafin yace,

“Toh kamar yadda kuka sani abunda ya taramu anan yau hukunci ne wanda zamu yankewa Najibulla. Shin tayaya kuke ganin za’a warware bakin zaren. Wane irin mataki ko hukunci zamu yankewa yaron nan. Kun san dai sarai Bintalo ba yadda zatai ba idan taji abunda muka yanke bai yi mata ba?.”

Kawu Dawood dake sakace hakoran sa da tsinke ya ajiye a gefe kafin ya sauke nannauyar ajiyar zucia.

“A yanke masa hukunci dai dai da laifin sa akuma yi masa sassauka. A nawa fahimtar wannan matsala da aka samu a tsakanin su abune wanda ke a b’oye wanda babu wanda yasan tabbacin gaskiyar yadda komai yake.”

Ya karasa fada yana maida kallon sa ga Kawu Khamis. Kawu Khamis ya sau siririn tsaki.

“Hakane amma ni ina ganin kawai daga shi har ita su bar gidan nan. Hakane kawai zai kawo karshen matsalar nan. Amman muddin yana nan suna zaune tare a wuri d’aya to dole sai an sake maimaita rana irin ta jiya. Amma ya kuke gani.”

Kawu ila dake kishingid’e tun d’axu yana kallon su sunata magana sai a lokacin ya dan gyara zaman sa, cikin cigaba da fifita da mificin dake hannun sa yace,

“Bangane ba Khamis, Su je ina kenan?”

Kawu Khamis ya bude baki kenan zai yi magana Kawu Ishaq ya tari numfashin sa,

“Idan na gane abunda kake nufi kana nufin ita ta tafi k’auyen su shi kuma ya koma wani wajen da zama? Ma’ana kenan yabar nan Zaria ko?”

Kawu Khamis ya jaddada kai. Baba ila ya gyara zaman sa da alamun sun tabo masa inda yake masa ‘kai’kayi.

“Wannan shine dai-dai, Tun ba yau ba nakeson shegen yaron can ya bar gidan nan. Domin naga alamun shi ke tsayawa uwar sa take yiwa mutane gani-gani, A yau ba sai gobe ba dan tselen uwa zai bar gidan nan.”

Ya karasa fada sauran na ‘babbaka daria banda Kawu Dawood. Domin shi Kawu ila yafi su rufin asiri, Don har shagon kayan masarufi yake dashi a gangare, Sannan mahaifin matar sa yanada kudi babu laipi. Kunsan yaro da kudi abokin manya, ko kaine kafu kowa kudi a dangin ku dakayi magana d’aya ta zauna kenan babu mai musawa. Shi yasa kowanne hukunci ya zartar da shi suke amfani, Kawu Dawood ne kawai baya shiga harkar sa sakamakon rashin jituwa da basa yi. Mik’ewa Kawu Dawood yai, Yayi hayewar sa sama. Nan yabar su Kawu ila dasu Kawu Khamis suna zantawa.

K’arfe sha d’aya saura kwata na ‘karasa tuwon dawar da Innar mu tasani, Ina kwashe wa na dora ruwan miya, gaba d’aya zucia ta babu dadi nake jinta, domin idan ka cire mahaifin mu daya rasu, da kuma Innar mu toh duk duniya babu wanda nake so irin Yayan mu da autar mu. Hakik’a ALLAH ne kawai gatan mu, Amma Yayan mu yana iyakar kokarin sa ganin muna cikin farin ciki ya zamto mana makara ‘dau duka. Hawaye ne na goge hade da saurin mikewa tsaye jin muryar Kawu ila yana dokawa sunana kira.

“Na’am Kawu gani nan.”

Na fada ina mai zura hijabi na. Ko takalmi ban tsaya sawa ba sanin masifar Kawu ila, Ai kuwa ina sauka kasan ya zabga min harara yana nuna ni da dan yatsan hannun sa guda d’aya na hannun dama,

“Wato tsabar raini ina kiran ki tun d’axu kina jina shine sai yanzu zaki sakko?”

“Kayi hak’uri Kawu wallahi banji ba sai yanzu.”

“Okay wato karya na shirga miki kenan? Zo nan dan uban ki. Shegiya mai idanuwa irin na jemagu.”

“TubarkAllah!”

Na fada a zuciya ta, Ina mai k’arasawa kusa dashi a tsorace. Tuni hawaye suka fara wanke min fuska. Kyakkyawan rankwashi ya sakarmin a ‘kwanyar kai. Cikin rad’ad’i na shiga sosa kai na ina hawaye, yaran dake wajen suka shiga babbaka daria cike harda Hinde dake wanke wanke. Na goge hawaye na , baki na na rawa nace dashi.

“Kayi hak’uri Kawu”

“Hakurin uban ki. Shashasha! Fita ki kira dan iskan wanki a waje kice yazo ya ji hukuncin sa yanzu ba sai anjima ba.”

“Toh!”

Shine kawai abunda baki na ya iya furtawa, naja k’afafuwa na na fita waje, cikin sa’a kuwa na hango Yayan mu shida wasu almajirai suna hira. Karasawa nai daga dan gefe nace,

“Yaya. Wai kazo inji su Kawu ila.”

Daga kai yayi, ya biyo ni a baya. Kowannen mu da abinda zuciar sa ke ayyana masa. Ni na fara shiga sai shi daga baya na. Bakin mu dauke da sallama, Kawu ila ya janyo nacaccen bokitin karfen sa daya maida shi na zaman tsakar gidah ya zauna, yana nunawa Yayan mu gefan sa daga kasa. Babu musu kuwa Yayan mu yaje ya zauna. Hinde dake hawa bene da kwanukan data wanke Kawu ila ya callarawa kira. Juyawa tayi tana zumburar baki.

“Yar hindodo mai farin jini, yarinyar gwal mai sa’ar rayuwa. Kira min babar ku da Islaha. Kice suzo yanzu suji hukuncin da aka yanke.”

Daga kai kawai tayi batare da ta amsa shi ba, tacigaba da hawa benen. Da ni ce kuwa nayi masa haka ya dinga tulata kenan kamar dabba. Amma saboda su ‘yayan da ake so ne ko fada ba ayi musu. Benen na fara hawa nima ya doka min kira cike da isa, jiki na rawa na juya,

“Na’am Kawu”

“Kira uwar ki taji yadda ake yan kewa danta hukunci.”

“Toh”

Kawai na fada na ‘karasa hawa. Daki na shiga da sallama zan fadawa Innar mu sak’on Kawu ta dakatar dani, da alamun ta jiyo shi. Cikin dan murmushin gefen baki wanda kallo d’aya za kai mata kasan tana cikin tashin hankali tace.

“Na jiyo shi Batoul. Gani nan sakkowa ‘kasan.”

Kada kai nayi alamun ‘Toh’. Sannan na juya na koma ‘kasan.

“Tace gata nan Kawu.”

Wani dogon tsaki yaja yana zabga min harara sai kace ni nayi lefin, fada ya hau yi shi kadai kamar wani mahaukacin kare ta inda yake shiga batanan yake fita ba, ya shiga dokawa Innar mu kira yana balbaleta da fada, Ni da Yayan mu dake gefe mukai shiru, idanuwan Yayan mu suka sake yin ja alamun ransa yakai kololuwar baci, Ni kuwa tsugunnawa nayi ina hawaye, domin duk sanda muke cikin tashin hankali k’afafuwa na basa iya daukar gangar jiki na. Shi kuwa Kawu ila sai ‘kara rafka mata kira yake yanata faman ihu,

“Ke kaltume, Kaltume! Ba zaki sakko ba? Ko sai na lallasa shegun dake gabana a zaune?”
—-
******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋











MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

_*SHAFI NA BIYAR_*

•••

Gaba d’aya manya da yaran gidan mu duk sun hallara a tsakar gida, Wasu a ‘kafar bene, wasu suna lek’e daga sama, wasu ta ‘d’akunan su. Kowanne ya baza hanci da idanu yana jiran jin hukuncin da aka yankewa Yayan mu. Cikin nutsuwa Innar mu ke sakkowa daga bene hannun ta d’auke da carbi tana ja harta ‘karaso inda nake tsugunne ta tsaya. A lokacin Bintalo da Islaha suka sakko suma, Bintalo na cin cingom tana fasa ‘kwan, Islaha kuma kan ta a ‘kasa tana matsa yatsun ta, kallo d’aya za kai mata kasan akwai alamun rashin gaskia a tattare da ita. Kawu ila ya janyo bokitin zaman sa na gado ya zauna yana bin kowannen mu da kallo, sai da ya mula yasha iska tukun sannan ya nuna Innar mu da yatsa,

“Ke kaltume wato saboda kin gama raina mu shine tun d’axu za’a aiko a kiraki sai yanzu kika ga damar sakkowa nace sai yanzu?”

“ilyasu kenan, Sai na katse sallar da nake na taho kiran ku? Agaban ALLAH fa nake, ai yafi gaban komai.”

Wani dogon tsaki yaja yana zabga mata harara, cikin ‘daga muryar sa ya fara magana yana mai mai da duban sa ga Yayan mu.

“Toh kamar yadda kuka sani daren jia Najibu ya nemi ya keta haddin Islaha, Saboda haka mun yake musu hukunci dai dai da laifin su.”

Innar mu dake gefe tai murmushin yake tana mai girgixa kai cike da tausayi, cikin wata irin murya tace,

“Ilyasu keta haddi fa kace? Kenan kun yadda wannan yaron ya aikata hakan?”

“Kwarai kuwa, domin rikakken namiji ne mai jini a jika, yana tashen samartakar sa, yanzu ne yake jinsa namiji sab...”

Da sauri Yayanmu ya riko kafar kawu ila yana hawaye gwanin ban tausayi, Gaba d’aya ilahirin jikin sa rawa yake yi,

“Kawu na rantse da Allah ban aikata abun da ake zargin na aikata ba, wallahi ALLAH gatanan a tsaye ko yatsun hannun ta ban taba kamawa ba, hasalima ni ba shiga harkar ta nake ba.”

Kawu ila yasa ‘kafar sa ya shure hannun Yayan mu, cikin tab’e baki yace,

“Mun rigada mun yanke muku hukunci kai da ita.”

Bintalo tayi kukan kura ta dira agaban Kawu ila. Cikin d’aga hannuwa ta shjga kwaso rantsuwa tana direwa,

“Sittin ta Ubangiji bazan yadda ba, ya nemi yai lalata da ita kuma sannan ace za’a hada a yanke hukuncin harda ita? Kaga ilyasu kasan sarai ba yadda zanyi ba, Rufa rufar da akai kad’ai a shekarun baya ta isa, kowa yasan shegun yaran nan gada su kai awajen mahaifiyar su, kalle su mana kowanne kamar sa daban, kowannen su da baban sa kenan. Shegiyar can kuwa inaga a yan gudun hijra aka samu ubanta domin kowa yasan ba...”

Bintalo bata ‘karasa ba Innar mu ta sha gabanta, hawaye suka shiga tsere a fuskar ta, Nima dake gefe na goge nawa jin sharrin shegentamu da akeyi,

“Karki kara shegenta min yara, domin kuwa kamar kowa suma nan gidan su ne, auren sunna mu kai da mahaifin su aka same su, Banda jahilcin ki ba ALLAH ne ke halittar mutum ba a yadda yaso a kuma sanda yaso? Bari kiji Bintalo tun kafin a san za’a auro ki muke tare da salis, Shin me kika sani game damu? Idan baki san nasani ba to inasan ki saurare ni da kyau, Nasan ta yadda aka auro ki, domin abun kunya ki kai, aka temaka aka hada auren ku dake ‘yar uwar su ce ke. Ko ba rufa asirin yan uwa kukai ba ya temaka ya auro ki?”

Kowa ya mai da kallon sa ga Bintalo, Ai kuwa ta zube a ‘kasa tana rusa kukan makirci,

“Wayyo nashiga uku, Yanzu Kaltume ‘k’aryar da zaki sharara a kaina kenan?”

Kawu ila dake gefe ya fara bata hak’uri yana rafkawa Innar mu harara,

“Kiyi hak’uri Bintalo, wannan zance nata ‘kage ne kawai, kowa yasan kece son ran Salisu. Ita kuwa agumi suka hada da iyayen ta ta mallaki Salis ta dole. Yara kuwa badan Aminatu tayi kanai-kanai acikin maganar gado ba ai da badasu za’a raba ba wallahi. Ki share hawayen ki Bintalo, Kowa yasan gaskia.”

Bintalo ta saki gud’a tana buga gaban zanin ta, Kawu ila yai murmushin da jajayen hokoran sa suka bayyana wanda suka rine su kai jajir saboda cin goro, Ya dubi Yayan mu dake gefan sa a tsugunne kamar kayan wanki,

“Kai Najibu, Bude kunnuwan ka ka saurare ni dakyau kaji hukuncin da aka yanke.”

Yayan mu ya daga kai, Ni dake gefe nasan ya hannu na asaman kai na na dafe ina mai zirarar da hawayen bakin ciki,

“Toh hukuncin da aka yanke shine kai Najibu zaka harhada naka ya naka ka bar garin nan, kada ka sake waiwayo gidah fyace sai mun neme ka. Ke kuma Islaha kema ki koma gidan ku, kya iya dawowa idan komai ya lafa.”

Na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara, Na dubi Yayan mu da ya kasa kuka gaba d’aya sai jajir da idanun sa su kai, jijiyoyin kansa sunyi rad’au-rad’au kallo d’aya za kai masa kasan yana cikin tsananin tashin hankali. Innar mu tayi murmushin da yafi kuka ciwo kafin ta dubi Kawu ila ta na mai cigaba da jan carbin hannun ta,

“Ilyasu na iya tafiya?”

“Eh kya iya komawa”

Sannan ya dubi Yayan mu yana mai nuna shi da yatsa,

“Minti talatin na baka kayi sallama da mahaifiyar ka da yan uwan ka da abokanan ka. Tashi ka je.”

Yayan mu ya mike dakyar yana hada hanya yabi bayan Innar mu dake hawa sama, Nima binsu nayi ina goge hawayen dake yar tsere a idanu na. Ina jiyo gud’ar da Bintalo ke saki tana tafa hannayen ta alamun duniya tayi mata dadi. Tuni gidan mu ya kacame da hayaniya kowa yana tofa albarkacin bakin sa, wasu sunji dadin hukuncin da aka yanke wasu basu ji ba. Koda muka shiga d’aki Yayanmu zubewa yayi akan katifar mu ya shiga rafka kuka, Autar mu sai hak’uri take bashi itama tana tayashi kukan. Innar mu zama tayi akan dadduma tana addu’oin ta. Duk kuwa da kallo d’aya zaka mata kasan itama tana cikin tashin hankali.

Sai da tayi addu’oin ta sosai sannan ta mike ta shiga duba cikin langunan da take ajiye kudaden wankin ta. Harhado su tayi duk sun manne da junan su. Ta shiga mik’ar dasu tana jera su d’aya kan d’aya. Yayan mu dake gefe sai ajiyar zuciya yake sauke wa yayi kukan har ya gaji. Innar mu kuwa bayan tagama hada yan kudaden ta kuma babban kad’a inda kayan mu suke taciro sauran kudin ajiyarta ta Sannan tadawo kusa da autar mu ta zauna. Cikin nutsuwa ta dubi Yayan mu da kalamai masu kwantar da zuciya ta shiga yi masa nasiha mai ratsa jiki tana yi yana hawaye, Ta k’ark’are da.

“Ka ‘kara hak’uri wannan yaron. Allah yana tare da masu hak’uri. Kuma komai na duniya rubutacce ne daga gare shi, Kasani komai nisan dare gari zai waye, Hakika ALLAH zai bayyana mai gaskiya tsakanin mu da su. Kacigaba da addua. Addu’ar wanda aka zalunta wallahi batada hijabi da ALLAH. Yana can a madakata zai yi sakayyar sa ko anan ko acan (Lahira). Allah yasa barin ka nan din shine mafificin alkhairi, ALLAH ya kare ka ya tsare ka aduk inda kake. Allah ya shiga lamurran ka, Yasa albarka a duk abunda kasa gaba. Allah ya maka albarka kai da yan uwan ka baki d’aya. Ameen”

“Aameen! Ya Hayyu Ya Qayyum.”

Muka amsa baki d’aya, autar mu kuwa har da shafawa a fuskar ta. Yayan mu ya goge fuskar sa sannan ya mike yana gyara zaman rigar jikin sa, cikin wata irin murya ya dubi Innar mu,

“Toh Inna zan tafi, Amma ina kike ganin zance kenan?”

“Toh wannan yaron ni dai tun dare nake adduoi kawo wa safiyar yau. Kuma zuwan ka Shema yafi kwanta min arai, Nasan su acan zasu zamar maka madogara, Tunda ‘ya’yan Baffa Ardo na zuwa tashi Kano, sai ku tafi tare. Kano cibiyar kasuwanci ce.”

Haka dai Inna da Yayan mu su kai ta magana, daga karshe ya amince da zuwa Shema. Na tattaro yan kayan sa na dakin mu na zuba a leda na rik’e masa. Inna ta bashi kudin ya duka hannu biyu ya karba yana godia. A d’aki ta masa adduar ALLAH ya kiyaye hanya da samun nasara, Muka amsa baki d’aya. Kafin nida autar mu mubi bayan sa, har titi muka rakashi muna yar hirar mu, duk kuwa da zukatan mu ba a nutsuwa suke ba. Cikin yan gidan mu kuwa babu wanda yayiwa yayan mu fatan ALLAH ya kiyaye hanya, Face Kawu Dawood da har naira talatin ya mika wa Yayan mu wai yasha ruwa a hanya. Babur Yayan mu ya tarar suka fara cinikin zuwa tasha. Muna daga gefe muna jin su. Sai da suka kammala sannan Yayan mu ya dawo kusa damu. Naira dari biyar ya ciro ya miko min,

“Ki Bawa Innar mu tayi cefa nen kayan azumi da za’a fara. Wannan kuma ki dau talatiin ki bawa auta ashirin. Allah ya muku albarka ya tsare ku.”

Ya karasa fada yana sake miko min naira hamsin. Na karba ina rissinawa idanuwana na fitar da ambaliyar hawaye. Hakama autar mu dake gefe.

“Mungode Yayan mu ALLAH ya saka da alkhairi. Allah ya tsare ka ya kare ka daga sharrin masu sharri. Allah kuma ya baka sa’a a komai na rayuwar ka Ameen.”

“Ameen Batoul! Ku ri’ke karatun ku duk wuya duk runtsi karku ce xaku dena. In sha Allah nima idan Allah ya buda min zan dinga aiko muku da wani alherin. Banda kula kulen samarin da zasu hanaki karatu, Banda bin wayayyun kawaye kina jina?”

“Eh Yaya”

“Yauwa! “ALLAH ya baku sa’ar karatu da nasarar rayuwa. Kuyita kauda kai dan Allah. Duk abunda zai had’a ku da yan gidan nan kada ku biye musu. Mu cigaba da hak’uri. Allah yana tare da masu hak’uri..”

Haka dai Yayan mu yaita bamu shawarwari. Ni kadai ke sauraron sa. Dan kuwa autar mu ta baje a ‘kasa tana yar carafke da duwarwatsun dake kwance akan ‘kasa. Kamar kada mu rabu haka naji. Yana hawaye muna yi. Haka dan mashin yaja shi, Muma muka kama hanyar gidah hannu na saqale dana autar mu.

.••••. .••••. .••••.

Bayan tafiyar Yayan mu abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda sana’ar sangas na kudi dana fara. Tanan muke samu mu rufawa junan mu asiri. Ga wankau da Innar mu keyi. Autar mu ma ba’a barta a baya ba domin tana yin kafutsire ta kukkulla d’aurin biyar biyar ta siyar. Abun dai sai hamdala domin kuwa mun dan samu saukin wahalhalun rayuwa. Hakan kuwa ba k’aramin rashin dadi yaiwa Bintalo dasu kawu ila ba. Domin har gaban abadan sunfi son su ganmu a tsiyace ba cigaba. A satinne kuma Innar mu ta samu aikatau a gidan Alhaji Kabeer Mai Wafa wato mahaifin Haysam wanda ke so na. Haka dai rayuwa tacigaba da garawa, Lalle ALLAH qadirun ne Ala Manyasha’u.

******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋







*MX🧕🏼**ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


_*SHAFI NA SHIDA_*


*ZARIA*

*BAYAN WASU SHEKARU*

*2008*


*GGSS ZARIA*
(GOVERNMENT GIRLS SENIOR SECONDARY SCHOOL ZARIA)

*Gaba* d’aya farfajiyar makarantar mu acike take dankam da dalibai, Kallo d’aya zaka mana kasan muna cikin tsantsar farin ciki da annushuwa. Gaba d’aya uniform dinmu mun zane shi da rubutun maka da biro. Wake wake kawai muke rairaya wa cike da jin dadin kammala makarantar sakandire da mu kai, A yau ranar Alhamis biyu ga watan afrilu shekara ta

Please Login or Register in order to submit comment