Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye rediyon tana murmushi,

“ALLAH yasa muga alkhairi.”

“Alkhairin ne kuwa, Kalli abun arziki, Manemin Batoul ne ya aiko aka kawo.”

“Kai du kayan nan?”

Innar mu ta tambayi Usaiba tana bin ledojin da kallo cike da mamaki domin tun d’axu rediyo take ji, Ga kullum gidan mu cikin hayaniya yake baka bambamce fada da hira, Abun farin ciki ko na baki.

“Eh fa! Gasu nan acan acan. Hashimu ne ya bayar aka kawon ta.”

Daria na fashe da ita jin yadda baba usaiba ta fad’i sunan wai Hashimu,

“Haysam ake cewa Baba.”

Cewar Autar mu. Kada kai Baba Usaiba tayi alamun tagane, Sannan ta shiga matsar da ledojin gaban Innar mu,

“Gasu fa kaltume.”

Lekawa Innar mu tayi tana jaddada kai. Hade da rike haba.

“Anya usaiba kayan nan basuyi yawa ba? A mayar masa ko?”

Usaiba ta kece dariya tana sosa kanta.

“Kutsin ubancan kayya kai. Yasin baza’a mayar ba.”

“Innar mu wallahi nima sai dana ce masa nide bazan karba ba, Yai ta hada ni da ALLAH. Ba yadda zanyi ne da wallahi bazan karba ba. Kuma danma ya rigada ya bayar an ka...”

“Jar ubanki nace! Kaji min yar jakar uba, Yo ba dole a ansa ba. Kinfison kullum sai dai ayita cewa bakida masoya, Ko kuwa ace tarin marowata ne.?”

Usaiba ta cemin tana min dakuwa. Murmushi nai kawai na maida kai na gefe. Sake maida kallon ta tai ga Innar mu.

“Kaltume ga fa kayan.”

“Usaiba ni wallahi bani da tacewa, Ke da Batoul din dai kwa san yadda zakuyi dasu.”

“Baba Usaiba ki raba kawai. Allah badan keba kinsan kayan nan Kawu ila kwace su zai yi.”

Su Talatuwa suka kece da daria. Usaiba ta gwaggwafe ta fara raba kayan.

Mayukan shafawar da turarukan miko min su duka itada dasu atamfofin da kwalin wayar. Ta kuma bawa autar mu kiret din kwai uku ta kawo gabana. Sanan ta raba chakulet din gida uku tabani rabo biyu. Lemukan kwalin ma da biskin ta kawo rabi gaba na, Sannan ta zazzage kajin akan filet, Guda biyar ne gasassu. Guda uku ta zuba min akan wani filet ta turo shi gabana. Murmushi nai ina tunanin da Kawu ila ne yai rabon nan da kilan fukafuki zan samu. Mik’ewa tai ita dasu Larai dake tayata rikon wasu kayan.

“Nagode baba usaiba.”

“Mune da godia yar nan. Yau zamu washe bakin mu da kayan Hashimu au Hesan.”

“Haysam ne fa baba..”

Autar mu ta kara gyara mata tana daria. Dariar baba usaiba itama tayi tana sude hannayen ta,

“Ba kuma muje kasa ayi rabon wannan. Nasan anacan an kafa dandalin gulmata. Na gurji bakin shege da shegiya wallahi.”

“Sai da safe usaiba. Angode”

Innar mu ta fada mata, Tana k’ok’arin sake kunna yar rediyon ta. Matsawa nai kusa da Innar mu,

“Innar mu ga kayan fa.”

Ajiye yar rediyon tai tana kallon kayan. Cike da damuwa tace,

“Wallahi kayan sunyi yawa uwata. Nide da zaki ji ta tawa. Wayar nan da atamfofin ki bar su kar ki amfani dasu. Da safe in sha Allahu idan naje aiki sai na mayar masa ko kuwa?”

Tak’arasa fada cike da damuwa. Ni kai na kayan gaskiya yawan su sun tsorata ni. Gashi ba son sa nake ba. Kar nan gaba yace na yaudare shi abun hannun sa nake kwadayi. Amman ya zanyi ya rigada ya hadani da ALLAH ?

“Innar mu ya riga ya kashemin jiki, Ya hadani da ALLAH kada na mayar da hannun kyauta baya, Wai na dauka tamkar Yayan mu ne yabani.”

Ajiyar zuciya Innar mu ta sauke.

“Toh ai shikenan! Allah yasa hakan shine yafi alkhairi! Ameen.”

“Ameen..”

Muka amsa baki d’aya harda autar mu. Wadda tadawo kusa da ni tana jiran abata kason ta. Dak’yar na shawo kan Innar mu ta raba mana, Da catai sai dai muci ita ta k’oshi. Muna ci kunnuwan mu na matsowa. Rabon da muci dadi irin haka wallahi harna manta. Domin inde ba gidan su Fadilah ba. To sai kaduna idan munje gidan Gwaggo Aminatu.

Usaiba tun daga kafar bene ta fara shewa muna jiyo ta,

“Toh ahalin ‘Gidan Mata Tara’ ku marmatso kusa ku dandali abun arziki. Wasu sai dai su shige ‘daka su cinye su da ‘yayan su. Ahayye kayya kai.”

Tana zuwa ta baje akan taburma tana karkasa kayan motsa bakin kashi-kashi. Kashi biyar ta raba kowanne kayan, cikin sude hannu ta shiga kiran sunayen kowanne daki kamar a makaranta ana kiran rajista.

“Ke Hinde ungo naku da uwar ku.”

Bintalo dake tsaye ta buga zani tana sakin tsaki ta haye sama. Usaiba ta kece da dariya,

“Yo ai kin banza. Mutum yace baya so ba zai ci ba mana. Jar uba kayya kai.”

Ta maidawa Bintalo martani tana gu’da. Sai da tayi mai isarta kafin ta cigaba da rabawa,

“Ke Fareedah ungo naku ku da gyatumar ku Hansai, Bala rike kai da Yusha’u ne da Innatuwa. Idris ungo nan rike kai da tawagar yan dakin ku. Ungo nan Larai namu ne, Wannan na Hajara ne da Rabi ki kai musu, Rike da kyau.”

Tas tagama rabe shi, Kawu ila dake kan bokitin sa ya sake gyara zaman sa. Bokitin ma duk ya tsufa yayi tsatsa. Dake bokitin karfe ne ga alamun an kai yan walda an walde shi, Sai kace bokitin sihiri. Yaran mokota dake tsaye suka zubawa Baba Usaiba kallo suna jiran nasu kason. Burbidin ta kasa ta daddanka musu a hannu,

“Toh kuje ‘yayan sa’idunawa. Da safe kwazo ku dora daga inda kuka tsaya.”

Ta k’arashe maganar tana tsaki. Uffan ba wanda ya tanka mata domin shakkarta ake. Zagin ta kadai idan ta lailayo su ta dura maka sai kayi ciwon kai, Ba sirke haka take zagin ta. Mutinci awajen Baba Usaiba daman babu tuni su kai hannun riga. Hayewa sama tayi tana kurbar lemon ta tana wake wake da karfi,

“Kai tsakanin ‘dan Adam da kudi! Tsakanin dan adam da kudi..”

Kawu ila ya zabga mata harara ta baya, Ya duka ya dau bokitin zaman sa ya kai daki, Ya fice shagon sa ransa a matukar b’ace.

*Mun* jima muna dandalar kayan dadin nan a daki. Wayyo Allah kamar sallah. Tas na cinye nama na, Na tauna kashin na tsotse bargon na taune duddugar na had’iye. Na kafa kwalin lemon don simon da aka rubuta ajikin lemon, Na dinga tuttulawa ciki na. Ga sanyi ga dadi. Ina gama sha, Na bude ledar chakulet din. A dunkule take alawar. Na dashare hakora ina nunawa Innar mu,

“Innar mu kalli. Yasin kamar daddawa ko? Kinga yadda chakulet din take. Wayyo Allah dadi..”

Innar mu dake kurbar lemon ta tai murmushi tana juya tata chakulet din a hannu,

“Ai kuwa wallahi. Kai wannan yaro ALLAH ya saka masa da alkhairi an motsa baki sosai Allah ya bud’a masa.”

“Ameeen..”

Na amsa ta ina sake tura chakulets din a baki na mai suna ‘Maltesers. Wata bahaguwar gyatsa autar mu ta saki tana shafa cikin ta,

“Alhamdulillah! Yasin kamar a gidan yan gayu.”

Muka bushe da dariya. Mik’ewa nai Ina mika, Na d’au kofi zan debi ruwa a randa naji wayam. Babu ruwan ya ‘kare. Na dubi Innar mu dake nannade ragowar naman a takarda,

“Innar mu ruwa ya kare karfe nawa?”

Rediyon ta ta kunna ta danyi shiru tana sauraron su. Da alama so take ta gano shirin da lokacin sa , Domin ta rike komai.

“Takwas saura kwata.. Yanzu zasu yi shirin ‘Duniyar Mu A Yau.”

“Ai dare beyi ba. Bari naje na ebo mana ruwan famfo. Na randar ya kare.”

Autar mu tai hanzarin mik’ewa tana gyara zaman hijabin ta.

“Yaya zan ebo.”

“A’a ki zaman ki. Dare yayi. Innar mu bari na ebo mana ruwa.”

“Zan raka ki Yaya.”

“A’a na hutasshe ki.”

Na karasa fada ina zura hijabi na, Na dau bokitin ebo ruwan shan mu na fice. Domin idan na bari autar mu ta min rakiya toh zamu dade bamu dawowa. Domin ta dinga yimun tambayoyi kenan kala kala na duk abunda tagani akan hanya ko sunayen jikin shago...

Can gangaren famfo na nufa. Inda famfon unguwar mu yake. Akan hanya naci karo da Fareedah yar gidan Kawu Dawood ta karshe da kuma Basma yar autar Kawu ila. Ma’ana yarinyar da Hajara amaryar sa ta haifa shekaru hudu da suka wuce. Tsaki naja! Allah ya kyauta. ‘Kananan yara a dinga barin su wasarere su kadai suna yawo. Kayi magana a zage baban ka dake kabari. Har nayi gaba na dawo wajen su suna tafe hannuwan su a sarqe ko ina zasu a daren nan? oho. Na dubi Basma daga ita sai yar shimi ba ko wando a jikin ta. Fareeda kuma da riga iya gwiwa ba dankwali. Itace babba ma akan Basmah. Ita Basma shekarun ta hudu. Fareedan kuma batafi 6 ba.

“Ina zaku?”

“Atana damu ciyo.”

“Wai Ashana.”

Fareedah ta fada tana dariyar tsamin bakin Basma. Na dubi shagon ‘Galin naga akwai wuta har zasu siyo su dawo. Ko na jira su ne? Na fada a zuciata. Cikin haka na hango Kawu ila yana tafe yana watsa hannu baya yana magana shi kadai.

“Shikenan ma kuje ga Kawu can.”

Na sauke ajiyar zuciya ganin kila ya jira su siyo tunda yana wajen shagon. Tafiya sukai nima na kama hanyar debo ruwan. Basma na ganin Kawu ila ta rungume shi tana masa oyoyo.

“Maza kuje ku dawo.”

Yace dasu yai wucewar sa gidah. Suna zuwa shagon Gali ya dashare hakora, Lungu da sako ya kalla babu kowa. Ya yafuto su da hannu suka je,

“Ashana za’a bamu.”

Gyada kai kawai yai yana janyo Fareedah jikin sa. Shafa kanta ya shiga yi yana dage rigar ta sama. A hankali ya shiga rad’a mata,

“Karki fad’a a gida. Kiyi shiru zan baku kayan dadi. Me kike so?”

“Alawa da biskit da cizi da madara da lemo.”

“Tam zan baki harda karin biredi ma kinji?”

Daga kai tayi. Yayi murmushi yana tande harshe. Kofar shagon ya dan rufe yadda za’ai zaton baya nan. Ya koma ya janyo Fareeda da Basmah yana shafa bayan su kawai. Hade da lumshe idanu. Sai da ya gaji dan kansa sannan yadakko ya basu. Ya kuma dadd’akko duk abunda Fareeda tace tanaso ya zuba musu a leda yabasu. Yace suce abokin Kawu ne ya siya musu. Cike da dadi suka karba suna murna. Ya sake nana ta musu,

“Kuce abokin Kawu ne ya siya muku, Kungan shi can ya tafi. Karki fadi abunda na muku. Idan kika fada bazan kara baku kayan dadi ba. Gobe ma kuzo na kara muku na kuma baku kayan dadin..Kunji?”

Cike da murna Fareedah tace,

“Toh..”

INA zuwa na tari ruwan a famfo. Sai dana kafa kai na na sha mai isa ta sannan na cika bokiti nai hanyar gidah. Nan na kara haduwa dasu Basmah. Kai wannan yara sun cika yawo. Na fada a zuciata ina girgiza kai. Na dubi ledar hannun Fareedah cike da su biskit sai tsalle suke,

“Waya baku kayan dadi?”

“Abokin Kawu ne. Gashi can ya tafi.”

Gyada kai nayi, Domin na hango wulgin wani mutum ya wuce. Cikin gidah muka shige. Nai hayewa ta sama. Na shiga daki bakina dauke da sallama.

“Wa’alaykm Salam”

Juye ruwan nayi a randar mu. Sannan na haye kan yar katifar mu ina ko’karin bude sabon kwalin waya ta da Haysam yabani. Starcoms ce babba mai k.yau bak’a. (Kada ku manta alokacin muna shekarar 2008) Na nunawa Innar mu da autar mu sosai suka tayani murna. Cike da farin ciki da annushuwa haka muka kwanta. Ina Allah-Allah safiya tayi na kai wajen chaji. Domin bamu da wuta a dakin mu. Masifar yan gidan mu sun sa an yanke wayar dake bamu wuta.

Koda su Fareedah suka nunawa iyayen su abunda Gali yabasu. Basu dau mataki ko neman tambayar wanene ya siya musu ba. Hasalima dasu aka hadu aka cinye.

Tsit kake ji ko’ina sai munshari ne ke tashi agidan mu. Kowa yayi bacci banda dakin Bintalo da iyalan ta.. Shin ko meyasa? Oho. Lokaci zuwa lokaci Bintalo ke jera tsaki a karo na ba adadi. Hannayen ta dumu dumu a habarta ta zabga uban tagumi. Su Alawiyya sun tasa ta a gaba suna zumburar baki. Wani shegen tsaki ta sake ja. Cikin zabura ta buga hannun ta a jikin bango da karfi ta shiga nana ta,

“Kan babban bala’i. Sittin ta ubangiji ba zai yiwu ba......”

Shin ko meye ba ze yiwuba? Oho dai. Mu barwa safiya🤸🏻

•••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_




MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

_*SHAFI NA SHA ‘DAYA_*

*•**•*•**

“Kan babban balai! Sittin ta ubangiji ba zai yiwu ba.”

Bintalo tafada tana mai buga hannun ta a bangon dakin da suke jingine. Zaune suke ita dasu Alawiyyah. Sun yi jungum-jungum tamkar wa’enda ke zaman makoki. Timemiyar katifa ce taci ta koshi a dakin. Sai fankar tsaye tana ta basu iska. Kwan fitilar dakin ja ne ya haskaka dakin. Sun jeru tamkar makarantar allo. Hauwa ce kawai ke bacci tana ta jan munshari kamar bijimin sa. Lokaci zuwa lokaci Alawiyya ke sakin tsaki. Bintalo ta cire tagumin data zabga tana watsa hannu baya, Cike da kwakwazo tace,

“Anya akwai wata a kasa. Shin taya dan gidan Alhaji Kabeeru zai so shegiyar yarinyar can? Uwar ta fa agidan su take aikatau.”

Alawiyyah ta ja ajiyar zuciya ta sauke,

“Gaskia da walakin goro cikin miya.”

“Gaskia dai Baba kisan nayi. Domin ba zata sabu’ba bindiga a ruwa.”

Hinde tafada tana tura d’aurin ta gaba. Jelar gashin dokin data kara a kanta ta bayyana. Bintalo ta mike a fusace tana huci, Zata fita Alawiyya ta ri’ko ta,

“Baba ina zaki a daren nan?”

“Haba ya za’ai a kawowa shegiyar can kayan da yafi naku? Ki duba fa ki gani sai data ga naku ba dad’ewa sannan tasan yadda tai aka kawo mata. Hmm sittin ta ubangiji akwai ‘kullalliya a kasa”

“Ki bari safiya tayi Baba, Gaskia Kawu ila yasamo mana mafita kawai.”

Ta karasa fada tana janyo hannun Bintalo suka xauna akan katifa.

“Zan same shi da safe muyi maganar. Shegiya da ido ‘kwalakwala irin na mayu.”

Haka dai su kai ta maganar Batoul da kayan da aka kawo mata. Sun raba dare suna zancen da yadda xasu samo mafita. Ranar dai su Alawiyya baccin bakin ciki su kayi. Bintalo kuwa bata runtsa ba, Tana ta saqawa da warewar yadda zata lalubo bakin zaren.

*WASHE-GARI*

Da safe na tashi ina mik’a. Baki na dauke da sunan ALLAH. Na so makara ma saboda ba sallah zanyi ba. Autar mu na kasa tana wanke-wanke Innar mu kuma tana tafasa ruwan bunu. Burushi na na dakko na tatsa makilin dinmu ‘dan nera ishirin ‘dinnan na leda. ‘Kasa na sauka na wanko baki na, Daki na shiga na rataye hijabi na a saman kofar mu. Rissinawa nayi ina gaida Innar mu,

“Innar mu ina kwana?!”

“Lapia Alhamdulillah uwata. Yanzu aka tashi kenan?”

Innar mu ta fada tana tsokana ta. Murmushi nai,

“Wallahi dake jiya bamu kwanta da wuri ba. Inna akwai abunda zan taya ki dashi?”

“A’a! Kinga ruwan shayi na dora. Ga biredi nan nasa auta tasiyo a shagon Kamalu. Ga sauran naman jia nan na ‘dumama shi.”

Motsa baki nai ina kada kai. Cike da jin dadi nace,

“Tab yau za muci dabge kenan.”

Daria Innar mu tayi. A lokacin autar mu ta shigo hannuwan ta dauke da dan kwandon wanke-wanken mu. Ta wanko su tas. Ajiye su tayi ta zauna a kusa dani,

“Yaya ina kwana?”

“Gashi nan a kwanon gaban ki.”

Daria mukai baki d’aya kafin na mike na janyo kwalin wayar jiya. Jujjuya ta na shiga yi,

“Dama ace muna da wuta sai na jona kawai anan.”

Na fada ina ‘kasa da kai na, Rai na yana sake tafarfasa. Idan har natuno wai kaf gidan mu dakin mu ne kawai babu wutar lantar ki. Haka kawai akan abu kalilan su Kawu ila suka cuzgune mana wayar dake kawo mana wutar a daki. Ajiyar zuciya naja na sauke, Da alamun na dade ina tunani. Domin Innar mu magana tai tamin ganin yadda autar mu ke jijjiga kafata tana kallon Innar mu.

“Lapiar ki kuwa?”

“Ina tunani ne Innar mu.”

“kankanuwar ki dake? Ki dena kinji?”

“Toh Innar mu..”

“Toh ku matso kusa muci abinci.”

Matsowa mu kai kusa da Innar mu muka fara karin kumallo. Wai yau ni Batoul dasu Innar mu muke karyawar safe da biredi da kaza? Ga ruwan bunu da sukari. Kai wayyo dadi. Muna ci muna lumshe idanu, Yaushe rabon da mu gana da biredi ga kuma kaza? Tab dadi kan dadi. Ga ruwan shayi da sukari. Kai garin dadi na nesa! Ko da muka gama cin abincin tashi nai na shiga kaude-kaude, Na gyara ko’ina tsaf. Dan zanin gadon mu na karkade na shimfide shamilalliyar katifar mu dashi. Na share ko’ina sannan na kunna dan turaren tsinke mai kamshi. Tuni dakin yai ‘das dashi yana kyalli. Innar mu ta mike ta dau kwandon soson wankan mu ta sauka kasa yin wanka, Tana ta sauri zata tafi gidan da take aikatau, Wato gidan su Haysam.

Zabga tagumi nai ina tunanin abunda zamu dafa. Mun tashi ba ko kwandala a gidan. Ajiyar zuciya naja na sauke a hankali nake furta,

“Ya ALLAH kai ka iya kai zakai ya Allah, Kai ne mamallakin kowa da komai. Allah kasa mu futa daga kuncin wannan sarqaqiyar rayuwar. Shin meyasa yan uwan mahaifin mu na jini suka tsane mu? Meyasa suke kyamatar mu kamar ba tsatson dan uwansu ba? Ya ALLAH ka kawo karshen wannan sarqaqiyar. Ameeeen!”

Na karasa Ina mai shafawa a fuska ta. A dai-dai lokacin Innar mu ta shigo tanata sauri. Ta ajiye kwandon sosan wankan mu, Mi’kewa nai don bata wuri ta shirya. Tsakar gidan mu na leka. Can karshen bango na hango Kawu Dawood yana bacci, Matar sa kuma ta gama shiryawa ta fice nemo musu dan abunda zasu afa a baka. Girgiza kai nayi ‘kowa da abunda ya da me shi.’ Na furta ina komawa dakin mu. Innar mu ta gama kintsawa tsaf tana shafa dan turaren mu dake kan kwalla. Mace mai kamar maza kenan. Allah ya azurta mu, Na fada a zuciata.

“Innar mu har kin gama kintsawa?”

“Na gama uwata. Sai tafiya kawai, ALLAH yabamu albarkacin dake cikin wannan rana mai albarka Ameen.”

“Ameen.”

Na amsa mata ina janyo kwalin waya ta,

“Na kai chaji ko Innar mu?”

“Ya kunna injinne dan haru?”

“Gaskia kilan sai anjima.”

Na fada ina zaro ta a kwalin ta. Addua na tofe wayar da ita ina murmushi. Kamar wasa ina gwada kunnawa ta kunnu. Da chajin ta a cike sannan akwai layi aciki, Da fara’a na daga kai ina dubar Innar mu dake gyara zaman hijabin ta ajikin ta,

“Kinga Innar mu acike take ma sannan akwai layi aciki.”

“Ah Masha Allah! Toh a tsofe lapia uwata. Allah yasa rai aka yiwa.”

“Ameen! Innar mu ko na kira Yayan mu? don naga akwai kudin kira aciki.”

Sa hannun ta tai akan leben ta tanamin alamun nai shiru. Saurin daga kai nayi alamun ‘nagane’. Tunawa da nai da babu wanda yasan muna magana da shi a boye. Wayar Innar mu ma da aka sace shi yabamu muka bata, Lokacin munje hutu shema shekaru biyu baya nida autar mu . Yanzu kuwa yana kano neman kudi da karatu. Ko ya kammala yanzu oho? Sanda mu kai magana dashi ta waya karshe yace yafara karatu a sa’adatu rimi kwalejin ilimi dake kano. Dake dama sanda yana nan a babban aji biyu ya dena zuwa. Suna zuwa kano kuwa yayi SSCE ya cike kwaleji ya fara zuwa. Ko me yake karanta oho? Nasan dai suna yar buga buga da sana’ar dinkin huluna samfurin zanna-bukar su siyarwa attajirai, Sannan suna kiwon shanun Baffa Ardo, Suna kuma yin leburanci a kasuwar singa dake kano duk karshen sati.

“Me za’a dafa ne Innar mu?”

Na tanbayeta ina kauda wancen zancen. Kullin zanin ta naga ta sunce ta ciro naira dari da goma, Su kenan da ita duk sun dunkule ta mikomin,

“Ki bawa auta ta siyo kananzir na goma, Gawayin hamsin. Sittin kenan ko?”

Gyada kai nayi, Na saka hannu biyu na karbi kudin.

“Yauwa sai ta had’o da manjan talatin. Tumatir da albasan ashirin. Naga akwai tsaki, Sai ki ruda kiyi danmalele. Da daddare In Sha ALLAHU ba zamu rasa abunda zamu ci ba.”

“In Sha Allah! Toh Innar mu. Kila nima na biya na yiwa matar soja sangas dan abunda na samo sai a hada asai wani abun.”

“Toh! Allah ya rufa asiri. Bari na.....”

Bata k’arasaba sakamakon bubbuga kofar dakin mu da Kawu ila ya shiga yi ba kakkautawa. Kofar har ta ballo dama ba kwari ne da ita ba. Innar mu ta sa hannu biyu ta dafe kirjin ta. Nima na zuba ido ina bin su da kallon karin bayani shi da Bintalo dake bayan sa tana taunar cingom tamkar tsohuwar karuwa. Da alamun koma meye sun gama shirya shi. Cincirundon yan gidan mu duk sun firfito suna leken ganin yadda zata kaya,

“Zo nan ku! Ku maimata abinda idanuwan ku suka gane muku jia.”

Yusha’u da Bala suka futo daga bayan Bintalo ni banma lura suna bayan ta ba sai yanzu. Ina ganin su na tuno sun ga sanda Haysam ya riko kasan mayafi na. Yusha’u ya dashe jajayen hakoran sa wanda suka rine saboda rashin tsafta sai hamamin wari suke,

“Yasin shine nan ya riko hannun ta da mayafin ta..”

“Bangane ba?!”

Innar mu tafada cikin tsantsar tashin hankali. Kafafuwana da suka kasa rike gangar jiki na naja na zauna akan tukunya. Ina dafe kai na. Bala ya matso gaba cikin murya mai sauti ya shiga kwararo karya da gaskiya,

“Yasin atare su ke da Kaltume da Yaran gidan Alhaji Kabiru ya riko wata leda a hannun sa ya bawa kaltume ya bi bayan Batoul dake baya can, Sai...”

“Kuji tsoron ALLAH Bala.”

Na fad’awa su Bala da Yusha’u ina dafe kai na saboda ciwon daya faramin yana barazanar fadowa. Kawu ila ya dankara min harara. Bala ya cigaba da cewa,

“Toh shine sai ya riko hannun ta da mayafin ta..”

Ya karasa fada yana jujjuya idanuwa alamun hadin zancen karya. Bintalo ta saki guda,

“Ah toh sittin ta ubangiji daman nace akwai wata a kasa. Ashe lalubar ta yake.”

Innar mu ta kasa motsi tana binsu da kallo. Domin ita kanta tasan sharri akai min. Murmushin yake tayi ta gyara zaman hijabin ta,

“Sharri dai dan aike ne Bintalo, Batoul kuma ‘yar ku ce. Idan kunga dama ku yanka ta. Matsa na wuce.”

Matsawa Kawu ila yayi Innar mu ta wuce tana girgiza kai. Kawu ila ya ajiye bokitin sa daya taho dashi daga kasa ya zauna a kai yana sakutar baki, ya dube ni kamar kashi,

“Dan uban ki jikin sa kike bashi yake muku hidima?”

Girgiza kai na shiga yi, Idanuwana na fitar da ambaliyar hawaye,

“Kawu ila wallahi karya suke min. Na rantse da ALLAH bai taba min hannu ba.”

“Shegiya! Ki gayamin gaskia. Kafin na tashi na ci uban ki.”

“Kawu wallahi bai rik’emin hannu ba. Kawai dai ya riko kasan ma..”

Ban k’arasa ba Kawu ila ya sharara min mari. Tuni naga gilmawar wuta saboda tsabar zafi. Na kifa akan katifa, Kuka na shiga yi mai sauti wanda ka tsuma zuciyar duk wanda ya saurara, Innar mu dake sauka kasan bene tayi murmushi cikin daga murya yadda Kawu ila zai iya jiyo ta tace,

“Alhaki kwikwiyo me shi yaka biye, Muje zuwa.”

Tana gama fad’a ta karasa sauka tai ficewar ta. Kawu ila ya shiga zubamin fada ta inda yake shiga batanan yake fita ba,

“Y’ar iska shegiyar yarinya. Wato abun kunya kike so ki janyo mana kenan? An samo ku ta hanyar haka shine kema zaki jajibo mana? Zaki dena rusgar kukan nan ko sai na lakada miki na jaki?”

A hankali na rage sautin kuka na,

Please Login or Register in order to submit comment