Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register




••*GIDAN MATA TARA••*

A bakin kofa Alhaji Salim da senator Bilal da Alhaji Kabeer mai wafa suka tsaya, Suna jiran a musu iso su shiga ciki. Kawu ila daya mula yasha iska ya mike daga kan bokitan sa yana botsarewa, hade da sakin wata shegiyar hamma yana sosa bayan sa.

“Ko su wanne natattunne oho? Haba tun d’axu sai faman doka sallama suke, Matsiyata.!”

Haka yai ta mitar sa ya fice wajen su dakyar yana kwakwular tasono.....

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_I⃠G⃠I⃠Y⃠A⃠R⃠___Z⃠A⃠T⃠O⃠



*47*


Tsayawa Kawu ila yai yana kallon su. Shi dai yasan wa’innan mutanen ba kalar wanda sanayya za ta hada su bane.

“Bayin Allah ‘batan kai kukai ne..?”

Ya tambaye su yana sake bin kayan jikin su da kallo, Domin kallo d’aya zaka musu kasan manyan mutane ne. Kayan jikin su da yanayin fatar jikin su ma abar kallo ce. Ga wata arniyar mota da suka zo acikin ta.! Sosai ya mai dasu tv yana bin ilahirin jikin su da kallo, Senator bilal yai gyaren murya yana kallon agogon hannun sa,

“Dan Allah acikin gidan nan kake? Ma’ana kana da danganta da nan gidan..?”

Ya karasa fada yana mai nuni da karyaiyiyar kofar shiga gidan mata tara. Kawu ila ya ware idanu yana yarfe hannu,

“Bayin Allah wani ne ya janyo muku magana ko? Ai lamarin gidan nan sai a hankali, wane shegen ko shegiyar ce?”

“Subhan’Allah! Assha! Mu farin ciki ne ya kawo mu..”

“Farin ciki kuma?.....!”

Kawu ila ya maimata yana wulqita idanuwa,

“Eh! Ance duk tare kuke da sauran yan uwa ko?”

“Gashi kuma ka fada..”

Kawu ila yaba Alhaji Kabeer amsa yana yamutsa fuska. Suka kalli juna jin mamakin kalaman sa. Cikin ikon Allah sai ga Kawu Ishaq ya dawo dauke da leda fara da tumatir uku, Albasa d’aya da attarhu guda shida aciki. Da alamun cefane yayo. Yana ganin su ya tsaya yana mimmika musu hannu suka gaggaysa basu kyamace shi ba dubada yadda wasu masu kudin keyi.

“Bawan Allah kai ma acikin gidan nan kake.?”

Alh salim ya tambayi Kawu Ishaq ganin yadda Kawu ila ke raina musu hankali. Kawu Ishaq ya kada kai alamun ‘eh’ kafin yace,

“Eh anan nake ranka ya dad’e, Wani abunne?”

“Ko babu damuwa zamu iya samun waje mu tattaunawa? Ku biyu ne ko akwai sauran yan uwan ku?”

“Mu biyar ne ranka ya da’de. Maza hudu mace d’aya.”

“Masha Allah! Toh zamu dan yi magana ne daku idan babu damuwa cikon biyun naku ma zasu iya zuwa a tattauna dasu.”

“Toh babu damuwa ku shigo daga ciki ai suna nan suma.. Ilyasu muje parlorn ka ko?”

Kawu ila yaja tsaki yana sosa kwanyar kansa. Ya shiga mita agaban su bako yar kunyar bak’innan.

“Wai parlor na dan bakin munafunci. Ta ina ya zama parlor na? Ance ya zama na mallakin Najeebu! Hmm billa..”

Ashe dik sun shige bai sani ba shi kadai ne a soro ya daga hannu zai kwararo rantsuwa. Yaja tsaki yana hararar soron kai kace akwai mutum a tare dashi, Kawu Ishaq na shiga ya tura bala ya karb’o masa pure water masu sanyi a shagon Nata’ala. Ya kira Kawu Dawood da Khamis suka sakko ‘kasan suma. Sannan ya koma soro ya kira Gwaggo Aminatu ya sheda mata cewar ga wasu manyan attajirai nan sunzo gidan wai zasu yi magana dasu. Ai kuwa tace gata nan garzayowa itama. A parlorn Kawu ila suka zazzauna sai cika Kawu ila yake yana batsewa. Alhaji Kabeer ya gyara murya yai sallama hade da fara gaya musu sunayen su da matsayin kowannen su,

“Da farko dai mu wakilai ne da aka turo don nemar wa dan mu auren ‘yar ku. Kuma Alhamdulillah kafin muzo nan din, Munyi bincike akan yarinyar kuma mun sameta da halin k’warai, Mun samu yabo sosai daga gare ta. Wani abun farin cikin ma babu auren wani akanta. Ni sunana Alhaji Kabeeru mazaunin nan garin na Zaria, Dan changi ne ni kuma inada iyali na dake nan garin na Zaria, Ga Alhaji Salim alkali ne shi anan customary court dake kaduna amman anan Zaria yake zaune da iyalin sa shima. Sai Senator bilal Senator ne shi yana Abuja! Duk kanin mu mun zone a bisa nemarwa dan mu auren yar ku.. Senator bilal ‘k’ani ne ga mahaifin yaron dake son yar ku uwar su d’aya uban su d’aya, Sai Alhaji Salim shi kuma siriki ne agare su, Domin mijin kanwar su ne. Ni kuma yaro ne awajen sa.”

Kawu ila ya saki baki yana tarin mamaki,

“Neman aure fa kuka ce? Kuma nan gidan ne kuwa? Anya ba ‘batan kai kukai ba?”

Alhaji Salim ya girgiza kai,

“Banan ne gidansu Batoul ba?”

Kawu Ishaq da Kawu Dawood suka kada kai alamun Eh! Kawu ila kuwa baki ya sake hangamewa cike da mamaki,

“Ba... me?”

Su kayi shiru basu amsa shi ba kuwa, Kawu Ishaq ya dungure shi da kafar sa alamun yai shiru. Ai kuwa Kawu ila ya shiga magana ‘kasa k’asa kamar zaucacce. Kawu khamis ya numfasa kafin ya fara magana a nutse,

“Masha Allahu! Munyi farin cikin kasancewar ku a tare damu, ALLAH ya saka da alkhairi Ameen! Toh nan gidan duk yan uwa ne wanda ke zaune a inuwa d’aya. Dukkanin mu iyaye ne da ‘yayayenmu da kuma jikoki. Mu shida ne awajen mahaifan mu Allah ya jikan su da rahama. Sunana Khamis, A tare dani akwai yan uwa na kuma kanne na wato, Ishaq, Dawood sai autan mu Ilyasu gashi. Sai mace guda d’aya tak dake aure a Kaduna. Muma usulin mu yan kadunan ne. Neman abinci ne ya maido mu nan Zaria inda muka kafa ahali, Toh Alhamdulillah munji dadin yadda kuka samu yabo na kwarai akan ‘yar mu Batoul,

“Batoul ‘ya ce awajen mu. Domin mahaifin ta marigayi malam Salisu shine babban wa agare mu baki d’aya. Kuma uwar mu d’aya uban mu d’aya dashi. Ya rasu shekarun baya. Duk muna tare dasu da mahaifiyar su anan gidan dama abokiyar zaman ta itama da nata yaran...”

“Allah sarki! Allah ya jikan sa da rahama da sauran musulmai baki d’aya!”

Senator bilal ya fada yana girgiza kai cike da tausayi, Sauran suka amsa baki d’aya da,

“Ameen!”

Kawu khamis ya shafa hannuwan sa a fuska sannan ya cigaba da cewa,

“Itace ta biyu awajen mahaifiyar su, Sai yar kanwar ta Aminatu. Alhamdulillah tayi karatun boko da arabi sosai. Domin tayi saukar alqur’ani mai girma, Tana kuma da matakin digiri na biyu. Alhamdulillah tana koyarwa yanzu a jami’ar Amadu bello dake nan Zaria tana kuma zuwa tahfiz asabar da lahadi. Kamar yadda kuka ce din gaskia ne batada wani tsayayye na aure amman dai akwai maneman da yawa.”

“Masha Allahu! Lalle mahaddaciyar alqur’ani ce. Abu yayi kyau tanada kwazo gaskia. Allah ya temaka Ameen.”

Cewar Alhaji Salim. Ya cigaba da cewa,

“Toh neman alfarma muka zo, Munzo nemawa dan mu auren yar ku ne..”

“Ai tanada masaniyar zuwan ku daman ko? Ma’ana akwai maganar sa akasa.”

“A’ah gaskia! Domin banajin suna da wata alaqa dashi yaron namu fyace ta malama da dalibin ta..”

“Toh.....”

Cewar Khamis yana kallon idanun su Kawu Ishaq. Senator bilal ya cire hularsa yana gyara karin ta kafin yace,

“Muhammad Mubeen shine sunan yaron namu, Kuma dalibi ne ga ita Batoul din. Kuma banajin ta san yana son ta ma.”

“Allah sarki! Ya za’ai kenan?”

Kawu Ishaq ya tambaye su da tsantsar gaskiyar sa domin bai san ya za’ai ba. Alhaji Kabeer ya dan sake muskutawa kafin ya karbi zancen,

“Yauwa kamar yadda muka fada da farko, neman alfarma muka zo kuyi mana. Yaron mu yanzu haka yana kwance babu lapia. Kuma Allah ne mai bada lapia amman Batoul itace zata zamto silar farfadowar sa. Yana kaunar ta kauna mai tsanani wadda ta kwantar dashi ciwo. Bamusan ko tasan yana dauke da tarin kaunar ta ba gaskia. Domin bai fada a gidah ba. Ya dai suma yanzu haka likitoci na kansa. Amman Allah yana temakawa yana farfado wa da sunan ta ya tashi a bakin sa. ‘Batoul’ Toh anan aka danyi yan bincike aka gano wacece ita, Domin shi yana daga cikin miskilan mutanen nan masu b’oye abunda ya shafe su. Rashin bayyanarwar tasa shine ya haddasa masa kwanciya ciwo. Dama kuma yana dauke da ciwo wanda bayason damuwa.

“Tun yana zanin goyo yake dauke da ciwon, Domin dashi aka haife shi ma. Abune daya shafi zuciyar sa. Kusan shine ya hanashi karatu ma tun yana ‘karami, Abu kalilin ne zai sa ya tashi yaita wahalar dashi. Dan da kila ba shida wata matsala ta iya yiwuwa shima ya kammala matakin karatun da ta yiyyi..”

“Allah sarki Allah ya bashi lapia mai dorewa...Yasa kaffarane Allah ya tashi kafad’un sa. Ameen”

Cewar Kawu Ishaq. Saura suka amsa da Ameen. Akai shiru na yan wasu sakanni. Bala ya kawo musu pure water din ya ajiye a sabon tiren Hajara matar Kawu ila. Kawu ila ya hararo tiren yana kauda fuska, Kafin cikin tsukewar fuska yace,

“Yanzu ku ‘danku zaku aurawa malamar sa? Inada tabbacin ta ninka shekarun sa.”

Suka kalli juna. Su Kawu Ishaq kuwa kunya ce ta kusa cinye su tamkar wajen ya bude su fada suke ji. Senator bilal yai murmushi kawai domin ya gano hassada ce ke damun ilyasun da alamun akwai wani abu a kasan zuciar sa,

“Kada ka damu babu komai, Munji mun kuma gani muna so a hakan, Koma ace ta nunka shekarun nasa babu komai, Ai ba kansa farau ba ba kuma za’a dena a kansa ba. Kaga zai yi koyi da sunnar ma’aiki. Allah yasa mu dace Allahumma Ameen! Mu dai yanzu a shirye muke domin da kudin sadakin mu muke tafe..”

“Toh ku kuka sani domin mah...”

Kawu Ilyasu bai karasa ba Kawu Ishaq ya janye shi suka tashi. Soro suka koma ya shiga lurar da shi abunda yai bai dace ba. Kallo d’aya zaka yiwa Kawu Ilyasu ka gano bakin ciki ne zalla a tattare dashi. Ai kuwa sai ga Gwaggo Aminatu ta shigo soron sai murmushi take, Tana ganin su tasha jinin jikin ta,

“Ilyasu ne yai katobara ko??”

Kawu Ishaq ya zayyane mata komai tana jinjina kai tana dankarawa Kawu ila harara,

“Kaga Ishaq kaje ku cigaba da tattaunawa ni bari na samu kaltume da maganar, Me za’a jira ne? Ai gwara tayi auren ta. Kai kuma Ilyasu jeka ka dawo anjima dan Allah..”

“Amma Yaya..”

“Jeka dai dan Allah”

Ficewa yayi yana mita ita kuma ta haye sama. Kai tsaye ta fara duba Bintalo dake kwance kudaje sai binta suke su Zabbau na gefen kofa suna hirar su sun barta aciki basu tsaftace wajen ba. Wajen kaltume ta shiga bakin ta dauke da sallama, Batoul bata nan tana makaranta hakama Aminatu. Ai kuwa Gwaggo ta shedawa kaltume yadda ake ciki, Kaltumen ta kasa boye farin cikin ta. Abunda ake nema shekara da shekaru yazo me za’a jira?

“Duk yadda kuka tsara Yaya hakan za’ai, Amman kamar yadda kika tambaya din nagane yaron domin yasha zuwa gidan nan gaishe ta. Har kayan dadi ya kawo wa Auta. Kuma bakiga ba hidimar bikin nan duk da shi aka yiyyi. Ban dai tab’a ganin saba amman wannan yaron ma (Najeebu) yace yanada kirki wallahi..”

“Masha Allahu! Abu yayi wallahi mu dai munyi na’am. Ance wai dalibinta ne nace toh ita soyayya ina ruwanta?”

“Wallahi kuwa! Nan take fada ma ya faffadi a jarabawoyin ta kuma yanada k’ok’ari fa tace. Nace tasa kaddarar kenan. Amman dai yaya ba matsala?”

“Ta me fa??”

Innar mu tai ajiyar zuciya tana harhada hannuwa,

“Wai duba da shidin dan gidan gwamna ne mai ci na yanzu..”

Baki galala Gwaggo Aminatu ta bu’de, Can ta dubi gabas tayi sujjada tana matsawa kusa da Innar mu,

“Alhamdulillah kaltume. Ai abunda muke so kenan. Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Dan gidan Amb Salees kenan. Idan kuwa haka ne yaron ruwa biyu ne domin mahaifiyar su ance yar Ethiopia ce. Kai amma nawa Batoul murna wallahi. Mahakurci mawadaci. An ce ma wai zata girme shi, Kanin uban yace sun ji sun gani suna so a haka, Ai zai yi koyi da sunnar ma’aikin manzo SAW! Wallahi Ishaq duk ya mayar mun. Yaron nacan rai a hannun Allah wai sunan Batoul kawai yake kira, Shine suka zo neman alfarma. Ni naga dankareriyar mota mai numfashi ashe tasu ce,

“Ishaq yace min harda Senator acikin su, da alkali da wani babban Alhaji. Yace kuma fuskar su a sake daga gani suna goyon baya. Ai kudi ba karya bane kaltume, kowa yanason inda zai huta nasa su huta. Ya kika gani? Don da sadakin su wai suka zo...”

Innar mu tayi shiru tana jinjina kai, Ita dai batada matsala a daura ko yaushe domin zancen yayi na’am a zuciar ta, Sai dai kowa na duniya nada magabata, Dole ta nemi manyan ta suyi magana dasu.

“Hakane Yaya! Amman idan babu damuwa gobe da safe ISA zan tafi shema na shedawa su Baffa Ardo kar suji daga baya babu dadi..”

“Hakan yayi kaltume.. Wallahi yayi! Allah yasanya albarka da alkhairi. Ni zan tafi da Batoul din akwai yan maiduguri dake gyaran jiki a kusa damu sai a shisshiryata, Amman ba zamu sanar mata wanda zata aura ba ko?”

“Eh Yaya...”

Innar mu ta fada tana sadda kanta kasa saboda macece mai kunya. Gwaggo ta mike da kanta tasa aka kirawo Kawu Ishaq ta sheda masa da yagayawa bakin cewa daurin auren ayi shi jibi ranar jumu’ah ko da daddare ne sai ayi domin za’a shaidawa su Baffa Ardo. Hakan kuwa akayi ya koma ya fada musu sun amince amman daurin aure sai zuwa jibi wato ranar jumu’ah. Suka musu sallama, Senator bilal ya ajiye musu rafar dubu d’aya. Bakin su Kawu har kunne suka rakasu waje. Sai ga Batoul ta dawo daga makaranta sanye cikin abaya baka tayi masifar yin kyau tamkar ka saceta ka gudu. Gaishe su tayi zata shige Kawu Ishaq ya kira wota yana nuna musu ita,

“Itace Batoul din ranka ya dade..”

Senator bilal ya fadada murmushin sa yana kallon Batoul,

“TubarkAllah! Lalle son yayi sa’a. Allah ya miki albarka kinji?”

Gyad’a kai nayi domin bansan me zance ba ko suwaye hakan? Na shige ciki kai na a kasa. Da’ki na shige abuna, Gwaggo da Innar mu a daki suna ta hira nayi sallama, Gwaggo Aminatu ta rungume ni tana rawa. Nan ta shiga shedamin neman aure na akazo kuma jibi za’a daura. Bata dai gayamin waye ba tace wani ne mazaunin kaduna yana canma ba lapia zanyi jinyar sa bayan an d’aura. Haka kawai naji zucia ta ta aminta da zancen. Aure ai ibada ne, Inata kokarin hada idanu da Innar mu taki yarda nasan kunya take ji. Ni kuwa bokiti na saba na sauka kasa nai wanka na. Su Kawu Ishaq sai nannan suke danni. Na tab’e baki ina mamakin wannan sabon salon. Nai sallah bayan naci abinci. Ina yiwa Allah godia hade da neman alkhairin sa. Gwaggo Aminatu ta sauka kasa wajen su Kawu Ishaq. Ta karbi kudin hannun sa ta raba shi kashi uku, kashi d’aya ta sa aka kira masu gini ta nunna musu inda zasu dan gyaggyara a gidan mu. Kashi na biyun kuma ta aiko aka bawa Innar mu kan tayi kudin mota. Dayan kuma tace su Kawu su raba. Ni kam kallon abubuwan nake tamkar a mafarki shin wane late comer ne wannan? Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u. Kaya na na shiga hadawa a dan akwati domin Gwaggo tace ita zanbi mu tafi kaduna. Sai yamma lis muka tafi kaduna..

*WASHE_GARI*

Da sassafe innar mu da autar mu suka tafi Shema, Dama tuni ta sanarwa Najibu yadda ake ciki shima yace yananan tafe. Koda Innar mu ta samu su Baffa Ardo da zancen sun bada goyon baya dari bisa dari, Har ma sun harhada gudunmawar su mai tsoka sun bata don gudanar da biki.

*KADUNA*

Tunda muka tafi muna zuwa Gwaggo ta cicciro wasu magunguna a roba ta shiga dirka min, Ga gyaran jiki da wasu yan maiduguri suka fara min. Lamarin dai ba sauki, ciki da waje gyaran sa kawai akeyi min. Fata ta sai sheki da santsi take kamar tarwad’a.

*GOVT HOUSE*

Senator bilal ya sake karkarcewa a kujera yana duban Amb Salees,

“Wallahi yaya yarinyar tayi, Da ladabi ta gaishe mu bayan batamasan suwaye mudin ba, Kuma she’s young ma. Allah dai ya sanya albarka. Ya tashi kuwa Mubeen din?”

Amb Salees dadi ya cika shi sai murmushi yake,

“Masha Allah haka ake so, Yana ciki bamu ma gaya masa ba tukun so nake sai an daura...”

“Woah! Hakan yayi! Allah yasanya alkhairi shi kuma Allah ya bashi lapia.”

“Sun gama hada kayan lefen?”

“Eh sun gama, Naji suna set 4 inaga akwatunan ne. Kasan wata mata aka bawa kwangilar yi..”

“Hakan yayi. Allah ya temaka.”

“Ameen”

Hirar su suka shiga yi, Daga bisa ni kuma suka koma wajen Mubeen. Yana zaune akan gadon sa anjigi na masa pillow, Hannun sa d’aya ana masa karin ruwa ya sake yin haske da kyau. Senator bilal ya zauna akusa dashi yana murmushi,

“Son na Batoul... Wai wacece Batoul dinnan ne? Uhm?”

Mubeen yai murmushi kawai yana sunkuyar da kansa kasa. Senator bilal ya sake cewa,

“Ai naje na fara bincike ashe ma malamar ku ce..”

Mubeen yai saurin daga kai yana kallon kawun nasa. Senator bilal ya kada kai yana dan duba yatsun hannun sa,

“Wallahi kuwa har na ganta ma fa.. Mekyau da ita kamar kai. Ashe saboda ita ka dage sai ka koma Zaria?”

Amb Salees yai murmushi kawai ya fice ya basu waje, Ai kuwa Senator bilal ya shiga tsokanar Mubeen. Kuma yaki ya gaya masa yadda ake ciki,

“Kana sonta son?”

Mubeen ya daga kai a hankali yana kallon gefe.

“Yanzu ya zakai ance aure zata yi.”

Mubeen ya shiga kikkifta idanu ahankali ya cije yana magana ahankali,

“Uncle pls.. Wallahi inason Batoul!”

“Zan duba nagani, Idan akwai yadda za’ai. But kar kasa hope akai..kai ta addu’a.”

Daga kai Mubeen yai hawaye na zirara a idanun sa. Senator bilal ya fice yana daria kasa-kasa, Shi dama akwai shi da tsokana musanman da Mubeen don yaga shi miskili ne.

*****Ranar jumu’ah da rana aka kai lefen Batoul akwatuna set hud’u guda ashirin da 24. Komai yaji babu ce kawai babu. Zo kuga kallon kaya awajen ahalin gidan mata tara da matan unguwar. Gaba d’aya yankin ya dauka da zancen kayan da aka kawowa Batoul. Fadilah ma ya Najibu ya gaya mata wanda Batoul din zata aura amman bata nunawa Batoul din tasan waye ba. Da ita akai komai domin dama ita Mubeen din ya mata wallahi tana son sa da Batoul tun ma hakan bata kasance ba. Kawai dai tasan kawar tata tafison manyan mutane masu shekaru. Duk wasu wahalhalun kayan daki da gara Amb Salees yace su barshi dan Allah. Su kawai Batoul suke so ba komai ba.

Daren ranar kuma bayan sallar ishai aka daura auren Muhammad Mubeen Salees Muhammad da amaryar sa Zahrau-Batoul Salisu Idris Najibullah. Abisa sadaki mai tsoka, Sai a sannan mutane suka sheda dan gwamna Batoul zata aura ganin harda shi akazo daurin auren. Gaba d’aya kaduna da Zaria ta dauka da maganar. Ana dank'awa Kawu Ishaq sadakin Batoul kawu ila ya karb'e yana danna su a kasan cinyar sa. Sai huci yake kamar bijimin sa, Bayan an daura suna ta yan gaishe gaishe, Kawu ila ya sulale ya fito soro da sadakin Batoul a hannun sa yana jujjuya su, Can ya shiga duddubawa ganin babu kowa a inda yake. Yana tafe yana magana shi kadai, Ya tare mashin ya hau ko ina zashi da kudin oho? Can gidah kuwa sai neman sa ake an rasa shi gashi bai bada kudin sadakin ba.

“Wallahi saro kaya zanyi dasu, Sai nayi kudi na dawo. ‘Yayan iska kawai mutanen banza...”

Dan mashin din ya dan kalli gefe yana rage gudun da yake shararawa,

“Me kace Alhaji?”

“A’ah bada kai nake ba, Da wasu mutanen banza nake masu son ganin baya na. ‘Kara gudu mu tafi dan Allah.”

Kawu ila ya gaya masa yana hararar keyar sa. Me mashin din ya kara gudu gashi ba fitila ajikin mashin din kuma dare ne. Ga kuma babban titi ne, Ai kuwa wata mota kirar ‘daf’ ta kunno kai, Mai mashin din yayi tangal tangal zai koma gefe kawai mai motar ya danna kai ya shallara dasu gefe suka bigi wata jibgegiyar bishiya. Mutane aka taru akan su, Shi mai mashin din dai ya jijji ciwo a gwiwa da kansa, Kawu ila kuwa bai masan inda kansa yake ba, Domin kafar sa d’aya ta rabu da gangar jikin sa, Gashi ya samu raunuka a sakamakon buguwar da yai ta kai sai jini ne ke fita, fatar sa duk ta daddaudauje. Aka rankaya dasu asibiti mai mashin din sai kuka yake domin mashin din nashi ya tashi daga aiki. Shi aka tambaya inda ya dakko Kawu ila? ta haka aka gano daga gidan mata tara ilan yake. Ai kuwa babu b’ata lokaci aka je aka shedawa ahalin gidan. Hakan ne yasanya Batoul bata ji sunan wanda aka aura mata ba domin hankulan kowa ya tashi aka shiga sallallami.

Alokacin na goge numbers din su Mubeen dama sauran wanda bani da alaqa dasu. Duk lamarin nan bansan waye mijin ba, Domin ca akai ta min wanda na aura yana asibiti a kwance don babu ango aka daura auren.. Sanye nake cikin atamfa mai ratsin blue da fari na yafa mayafi fari, Nayi kyau sosai abuna. Addua naita kwararawa akan sabuwar rayuwar da zan shiga tare da wanda bansan shi ba bai sanni ba.. Duk yan gidan mu suka shirya zasu tafi dubo Kawu ila asibiti nima na mike ina gyara mayafi na Gwaggo Aminatu ta murmusa tana kallo na,

“Ina zaki ke kuma?”

“Dubo Kawu.”

“Hak’uri zakiyi Batoul, Yanzu ai ba zaki fita koina ba fyace sai da izinin mijin ki. Kiyi hak’uri kinji? zamu ce kina duba shi.”

Gyada kai nayi na koma bakin katifa ina hawaye, Yanzu shikenan kuma dik inda zani sai na tambaya? Wayyo Allah na! Gaba na ya shiga faduwa. Yanzu kenan yar koyarwar da nake yi denata zanyi? Toh ai dama haka auren yake komai dan hak’uri ne, Wata zuciar ta bani amsa. Ya Subhan’Allah! Na furta ina cije lebe na. Koda su Gwaggo Aminatu suka je asibitin suka tarar da halin da Kawu ila yake ciki abun ya basu matukar mamaki, Toh ina zashi oho? Suka tambayi mai mashin din dake gefe ana nada masa fulasta ya sheda musu yadda sukai dashi har maganganun da yai. Suka cika da mamaki, ana duba aljihun wandon sa guda biyu kuwa sai ga sadakin Batoul. Nan suka gano guduwa zai yi dasu, Sai gashi Allah ya nuna ishara akan sa. Gwaggo Aminatu ta cije yatsa tana kallon Kawu ila da wani irin kallo mai tarin ma’anoni, Dan takaici kasa tsayawa tayi ta wuto gida da kudin sadakin, Tana zuwa ta mikomin sadaki na naki karba ina jijjiga kai,

“Me zanyi dasu Gwaggo?”

“Rik’e banason taurin kai, Ai hakkin ki ne ko jari kyaja dasu.. Ilyasu ya gudu dasu sai gashi beje ko’ina ba tsautsayi ya fada akan sa. Duk nasihar da nake yiwa yaron nan baya ji ai ga irin ta nan. Babu kafa d’aya ta balle kamar ta yartsana. Bai masan wanda ke kansa ba, Duk wani abunda likitoci zasu yi sunyi yaci tura, Mutu kwakwai rai kwakwai. Ya shiga koma wai, Allah kadai Yasan ranar farfadowar sa. (coma: A period of prolonged unconsciousness brought on by illness or injury. It can be caused by a variety of problems — traumatic head injury, stroke, brain tumor, drug or alcohol intoxication, or even an underlying illness, such as diabetes or an infection. A coma is a medical emergency.)”

“Subhan’Allah buguwar da yai kenan ce ta haddasa masa shiga coma din?”

Na tambayi Gwaggo Aminatu cike da tausayi. Gwaggon ta gyada kai tana goge hawayen dake tsiyaya a fuskarta,

“Eh! Duk

Please Login or Register in order to submit comment