Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗin,
“Batoul...Batoul... Ki saurare ni pls.”

Dr Affan yai murmushi yana dudduba kwayar idanun Mubeen,

“Mubeen kana jin mu? Ka farka ga Batoul din a kusa da kai..”

A d'arare Nace, “Ya tashi d’axu fa.. “

Na basu amsa ina ja da baya. Duk kallona sukai da mamaki,

“Mubeen din? Ya tashi mikewa sosai kuma?”

Nace, “Eh, amma kuma sai ya koma ya kwanta.”

Gyada kai yayi ya cigaba da dudduba shi, Ni kuma ina gefe lokaci zuwa lokaci nakan kira sunan sa kamar yadda suka umarce ni. Cikin ikon Allah kuwa ya shiga bude idanun sa yana sauke su akanmu mu duka, yanda yake kyakykyaftasu zai baka tabbacin dishi-dishi yake kallonmu, a bazata mukaji yace,

“Ma..! Kece dagaske?”

Baya naja a tsorace, su Doctor kuwa sai suka sanya dariyar farin ciki.

Ya yunkura yana sake maimaita sunana da kokarin son mikamin hannunsa da kyar. Kasa motsawa nayi, amma ya d'an bani tausayi, dan haka na kada kai, ina juyarwa gefe kadan, ‘Wai Mubeen ne mijina?’ ni jin lamarin nake tamkar a mafarki. Gaba d’aya ya maida ni kamar mudubi, kallo na kawai yake ko kifta idanu bayayi. Cikin haka mahaifin sa ya shigo shida sauran mutanen d’axun. Sunji dadin yadda suka same shi ya farfado, daxuma har ya mike kamar yadda dr Affan ya sheda musu.

Yanda yaketa kokarin son naje garesane ya saka Dr Affan fadin, “Mrs Mubeen zauna kusa dashi Please”.

Tamkar zan fasa kuka haka naji, ga kunya kamar na nutse cikin kasa saboda mahaifinsa da gayyar mutanen da suke tare, amma a mamakina sai naga su ko'a jikinsu......

“Daughter zauna kinji, karkiji komai”. Maganar papa ta katse shakkuna.

Zama nai gefensa tamkar mai jin tsoro, kamar jira yake kuwa ya sakala hannunsa cikin nawa carab, duk da babu wani karfi tattare dashi. wani iri naji a raina, wai nice yau hannun Mubeen da nawa cikin na juna?, jin abin nake tamkar a mafarki....

Yanda yake ta kokarin son dora kansa saman cinyatane ya saka dr Affan fad'in na taimaka masa ya dora din, nikam lamarin Mubeen ya fara girmar wayona, banida zabin daya wuce bin umarni kodan kunyar idon mahaifinsa, haka na taimaka masa kansa ya dawo saman cinyata, ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yana lumshe idanu, murya a sanyaye ya furta,

“Thanks Ma..!”.

Ban iya koda kallonsaba balle na motsa, sai ajiyar zuciyar da Papa ya sauke shima ta sakani jin tausayinsu, lallai suna k'aunar Mubeen sosai.

Karin ruwa aka sanya masa hade da wasu allurorin a jijiyoyin sa. Har aka kammala komai kamar yanda dr Affan ya sanar sai kuma gobe idan Allah ya kaimu, yace,

“Mrs Mubeen kiyi hakuri har barcinsa yadanyi nisa, dan yanzu kina zame jikinki zai iya farkawa”.

Kaina na jinjina masa a kunyace.





ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*IGIYAR ZATO.....💞*
(Eternal_love)

*50*

*KADUNA*

Haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya a wannan gida, ina kokarin danne zuciyata wajen jinyar Mubeen da basa dukkan kulawa, hakan nama ahalinsa dadi sosai, Shi yasa suma suke bani dikkan kulawa.

Rashin kunyar Mubeen itace kawai ke batan rai, zuwa yanzu duk yanda zan canjama yaron nan fuska kona d'aure akan karya tab’ani baya jina sai yayi, musamman ma idan zan bashi abinci yafi min duk iya shegen daya gadama. Sai dai ina kokarin dannewa saboda rashin lafiyarsa, ga Doctors dinsa sun shinfidamin dokoki akan yanda zan bashi kulawa kodan dai-daitar komai.

Alhamdullahi yanda nake kokarin bin dokar tasu kuma ana dacewa, dan akwanaki goman nan dana dauka tare dashi jikinsa yayi kyau sosai, zuwa yanzu har dan fita yakanyi harabar gidan yasha iska.

Duk yanda naso sabawa da bakin al'amuransa nakasa hakan, sai dai nasihar Gwaggona tana dakatar da dukkan yunkurina akan komai.

Tunda na tashi a safiyar yau da tunanin maganar komawata makaranta na tashi, dan hutuna ya kare. Abin mamaki sai juya zancen nake a raina da tunanin yanda zan tinkari Mubeen dashi. Cikin kullawa da kwancewa na gama kimtsawa daga shirin da nakeyi, dan wanka na fito, ina cikin fesa turare ya shigo dakin da sallama.

Amsawa nai, sai dai ban juyaba dan ina kallonsa ta cikin mirror. Yanda na hango idanunsa na yawo a jikina duk sai naji na takura, nadan hade fuska dan banason raininsa, sai dai dana tuna kuma maganar komawata majaranta saina dan sake kadan...

Ajiyar zuciya na sauke a hankali jin ya rungumeni ta baya, tunanin dana tafi baisa naji sanda ya iso gareniba, ya dora kansa saman kafadata yana gogamin gashin sajensa a wajen. Take tsigar jikina ta hau tashi, nai kokarin ture hannunsa dake kan cikina amma na kasa hakan.

Ta cikin mirror muka hada ido, nadan hararesa shi kuma yay min murmushi mai cike da ma'anoni da yawa, cikin sanyaya murya yace,

“Tsaurin idonki yayi yawa Fateemah, bantaba ganin matar dake harar mijintaba sai ke”.

Shiru nai ina maimaita sunan Fateemah daya kirani dashi, sai naji kamar ba sunanaba, dan tunda nake a duniya zan iya cewa babu wanda ya taba ambatar sunan da hakan..

Sake katsemin tunani yay da cewar,

“Kinason kiji labarina Mah!?”.

Samun kaina nai da daga masa kai alamun amsawa. Yay murmushi tare da sumbatar wuyana, sannan yace,

“I love you”.

Ban tanka masaba, danshi wannan kalmar ya maidata tamkar me a harshensa, a yini yakan fadamin ita sama da sau goma, duk da ni banajin son nasa amma inajin dadi, sai dai nakan kanne bana nuna masa naji dadin dan karya samu lagona.

Hannuna yaja zuwa bakin gadon, ya zauna sannan ya dorani saman cinyarsa. Da sauri na kalle shi inason sauka amma sai ya rikeni da kyau yana girgiza kansa.

“Dan Allah karkice zaki tashi kinji My Fikre”.

Ban tankashiba, na dauke kaina ina mamakin solon fitina kala-kala na Mubeen.

Hannuna daya kama cikin nasa ya murza yace,

“Mah! Kin zama tawa ni kadai, sai nake ganin Kamar mafarki... Ina kaunar ki fikre!”

“Meye fikre?” ‘Na fada inadan juyowa na kallesa.

Sai da ya dagan gira daya da wani salo sannan yace,

“My love.... Ko bakyaso?”.

Shiru nai ban tanka masaba, saima dauke kaina daga sashensa da nayi. Yace,

“Toh ki zaba d’aya: Babe, Love, Beautiful, Princess, Buttercup, Cutie pie, Dreamgirl, Lovebug, Sunshine, sweetheart, Precious..”

“Banason ko d’aya.. Bani labarin da kace.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana sake narkar da idanun sa akai na, Hannun sa d’aya na aikin murza hannu na.

“Kiyi hak’uri da neman aure na da ya zamto tilashe akan ki, Da farko dai ina dauke da ciwo ne wanda dashi aka haife ni, Tun ina zanin goyo nake shan wahala. Wanda na samu hakane alokacin da Mamma zata haife ni shekarun baya, (Preeclampsia is a condition during pregnancy where there is a sudden rise in blood pressure and swelling, mostly in the face, hands, and feet. ||If the preeclampsia remains untreated, it can develop to eclampsia, in which the mother can experience convulsions, coma, and can even die. However, complications from preeclampsia are extremely rare if the mother attends her prenatal appointments.),

“An haife ni da ciwon zucia, Ga ciwu ka kala kala, Ko yaushe muna hanyan asibiti tun ina kankani dan dai Allah yayi da sauran kwanaki na agaba, Ga chronic ulcer da nake da ita, Fikre idan zan lissafo maki ciwukan dake damu na zamu kwana mu wuni anan, Yawan ciwukan dake damu na yasa banyi karatu da wuri ba, Dana fara karatu ciwo zai hanani na dena karatun, Ya zamto kawai anamin home school har na girma nazo na fara online university Manchester na dena, Daga nan na fara AIU (Atlantic international university) shima months nayi na dena, Daga baya dai nayi Boston University Online shima na dena ciwo ya tashi, dana warke na fara Drexel University Online shima ciwo na worsen, Daga karshe kuma nayi Arizona State University Online shima ciwo ya tashi kawai na dena gaba d’aya ma. Nayi shekaru bana fita koina, Sai daga baya nake bin driver mu dakko kanne na a German embassy school wato mashkur da Aeedah. Jannat kuma tana high school duk aciki.,

“Ina ta shan magani a hankali har ciwukan ya lafa muka dawo nigeria. Papa yace na fara nan Ahmadu Bello a time din ma na nuna banaso nafison home school ko na kara applying online. Papa yace A’a! Ashe Allah yayi zan hadu da ke. Ina son ki fikre, Ina kaunar ki wanda kalamai sunyi kadan wajen nuna soyayya ta agare ki, Kin daukeni a matsayin ‘kankanin yaro saboda kinga ina karkashin ajin da kike koyarwa ko? Toh ba komai bane yasa hakan face wannan lalurorin na rashin lapia. Su suke maidani baya a komai na rayuwa, Kiyi hak’uri da auren ‘kanin ki kamar yadda kikace din bayan dai baki girme min ba...” ‘Ya kare maganar da kumshe dariyar shak’iyanci ’.

Na zabga masa harara ina yatsina fuska,

“Harara ta kike? Ai shi namiji baya kadan.. Allah Fikre kibar cika baki hmm!”

Kwatsam haysam ya fadomin a rai na, Domin shine ke gayamin kalmar haka a shekarun baya. Mubeen ya sake yin rau-rau da idanu kafin ya cigaba da cewa,

“Fikre! No matter how many challenges come in my life, I will face them without difficulty if I have your support.I am taken by the most beautiful woman in my life. I Love you!..”

Shiru nayi ina sauraransa har sai da ya gama magana sannan na sauke numfashi, naji tausayinsa kwarai amman ban nuna ba a fuskata. Shikam idanu ya tsuramin tamkar yaune ya fara ganina, da alama dai yanason jin wani abu daga bakinane, amma saina dauke kai abuna naki cewar.

Ya langabe kai kadan yana sake kafeni da wadannan idanun nasa masu saka dukkan gashina mikewa batare dana shiryaba, can kuma ya dafe tsakiyar kirjinsa yana faman rintsa ido. Yadda naga yana janyo numfashi da kyar ne yasa ni saurin matsawa kusa dashi hankali na a matukar tashe, jan numfashin ne ya tsananta tsoro ya kama ni ban san lokacin dana sauka a jikinsaba na zauna a bakin gadon tare da sanya hannuna na dora a inda yasa nashi din.

“Sannu Mubeen, zuciyar ka ce ko kirjinka?”

Na tambayesa cikin sanyin murya mai tattare da jin tausayin halin da naga ya shiga tamkar zan fashe da kuka.

Kasa magana ya yi, sai hannunsa da ya dago da kyar ya kwantar min da kaina a saitin kirjin nashi inda yake masa zufin. Ya na iya, dole nayi luf saboda ina tsoran kar wani sabon abin ya faru akansa bayan ana ganin nice maganin warakarsa, kar naje kuma na zama sanadin mutuwarsa gabaki daya.

Jinai ya saki wata sassanyar dariya cikin kunnena, nai saurin dagowa na kallesa da mamaki. Gwalo yaymin tare kashe ido daya ya nuna kasa da babban danyatsansa.

Fahimtar shakiyancine ya sakashi yin hakan saina hararesa na yunkura zan tashi. Saurin kamo hannuna yayi ya maidoni muka fada a gadon tare yana dariya. Kokari kwacewa nake amma na kasa, gashi yasa kafa ya danne tawa,

“My fikre wallahi zuciyarki gulmammiyace, anason dan yaron nan ana kaiwa kasuwa”.

Ture shi nake sonyi amma na kasa, ya kuma matseni yana dariyarsa, cikin kunnena yace,

“Fadamin tun yaushe kika kamu?”.

“Ban saniba, ni wallahi bammasan ya akai ka rainaniba har haka Mubeen?”.

Dariya ya sake kwashewa da ita fiyema data farko, wadda nikuma ta sakani kuluwa da sabon haushi. Juyowa nai sosai garesa zanyi magana cikin masifar da ni kaina ina mamakin yanda na iyata a yanzu kawai bawan Allahn nan ya hade mabinmu waje daya. Duk yanda naso kwatar kaina na gaza, dan Mubeen duk yanda na rainashi yafi karfina, tunma ina gwada dan karfin nawa harna koma nai luf ina karbar sakwanninsa.

Tafiya tayi nisan da gaba dayanmu munfita hayyacinmu, ban tashi fargaba saida naji yana neman wuce gona da iri. Dan karfina na tattara na turashi, kasancewar shi yayi laushi saina samu nasara. Nai azamar juya masa baya wasu hawayen takaici na gangaromin a fuska.

Ina jiyosa yana sauke numfashi da sauri-sauri mai alamun murmushi, ban sake gigin juyawaba na cigaba da hawayena a haka.

“I love you my Fikre”.

Na jiyo muryarsa yana fada a hankali.

Banko motsaba, sai sauran hawayena dana goge, ‘gaskiya Mubeen ya bala'in rainani’ na faɗa a zuciyata batare dana san maganar ta fito filiba.

Jinsa kawai nai ya kwantomin a baya yana fadin,

“Ni na isa raina malamata, kawai dai kinsan nima a gida nine malamin”.

Hannunsa naso turewa amma saina gagara, maganar malanta da yayi kuma ya tunamin abinda ke raina. Shiru mukai na tsahon lokaci, kowannema a ransa yana daukar dan uwansa ko yayi barcine. Babu zato mukaji kiran sallar karfe biyu.

“Mah kin makarar dani banyi sallah da wuri ba”

Mubeen yayimaganar cikin kunnena’. Janye jikina nai daga nasa, bai hananiba kuwa. Sai da na sakko daga gadon na kalle shi ina daga girata cikin dauriya da danne kunyarsa da nakeji ta cikamin kirji.

“Kafin nazo gidan waye yake sawa kayi salla? Ko kuwa dan ni yau kaga mun kwanta gado daya a tare shine zaka ce min haka?”.

Sai kawai naga ya saki murmushi yana lumshe idonsa, na harareshi ina nufa cikin toilet.

Ina shiga na maida kofar na rufe sai na jingina, kaina na dafe tare da kirjina, ina jiyo dariyarsa daga nan, wani haushi ya sake kamani, nai kwafa ina nufar yin fitsari nai alwala.

Idanu na zaro tare da jin wani takaici, sai kawai naji hawaye na zubomin, wai yanzu nan nice dan yaron can zai saka yin wanka? ‘Na shiga uku ni Batoul’ kawai sainaji kukan dayafi na farko karfi ya zomin.

Babu yanda na iya, dole na cire kayan jikina nai wankan tsarki, rufe kofa da naji tun dazunne ya sakani ji a jikina yabar dakin, dan haka na fito kaina tsaye.

Ajiyar zuciya na sauke ganin bayanan, na zauna ina goge gashina a gaggauce danna samu nai salla.

“Mah! Kema sai da kikai wankan kenan”.

Wani masifaffen faduwa gabana yayi, zuciyata kamar zatai zallo ta fado kasa saboda kunya da takaicin Mubeen , bangama dawowa hayyacinaba na ji ya zare karamin towel din hannuna ya dora saman kaina yana cigaba da tsane ruwa, sai faman jiyo sautin murmushinsa nakeyi. Bakina kam yagama mutuwa rumus yau, ko kallonsa naki yarda nayi harya kammala ya sakamin doguwar riga.

“Tashi muyi salla, mun makara da yawa”.

Yanzunma ban taka masaba, bankuma kalleshi ba amma na mike dan muyi sallan. Bayan mun idar ya juyo yana kallona da wani murmushin, tamkar na nutse a wajen haka nakeji...

“Wai ‘dan yaron nan ya zama surikine yau Fateemah?”.

Maganar Mubeen ta daki kunnuwana, Harara na dago na dalla masa ina yunkurin mikewa daga wajen. Saurin kai hannunsa yay ya jawota ta dawo ta fada jikinsa.....

Muryata na rawa nace,
“Mubeen banason abinda kakemin, sakemin hannu”.

Kin saki yayi. saima sumbatar goshina da yayi, yace,

“Allah idan kika cigaba da cikamin baki mai gaba dayama zanyi ki tabbatar na girma niba yaro bane”.

“Innalillahi” na shiga ambata da sumbin al'ajabin Mubeen da tsagwaron tsaurin idonsa na rashin kunya.

“Sorry Mah! nayi shiru”.

Ya fada a hankali cikin kunnena.

Shiru nai masa ban tankaba, shima sai bai sake maganaba yadai zubamin idanu kawai kamar wata tv.


*_Washe gari_*


Tun a jiya dana samu Mubeen yabar dakin muka koma yar wasan buya, naki yarda mu hadu, nama kulle dakina nakuma bar key a ciki yanda bazai iya budewaba, yamin kiran duniya da knocking naki na bude, daga karshe dole ya hakura ya kyaleni, Amman dan naci sai da ya dawo washegari ala dole na bude.

Kamar kullum ina tashi nayo wanka nabi lungu da sako na shafa turarukha, Wata bou-bou rigar lace na saka. Na dan tsaya ina shafa hoda kadan gudun maik’o. Ta mudubi na hango Mubeen yana kallona tashin sa kenan daga baccima daga gani. Na turo baki gaba ina yatsina fuska dan na manta na bude dakin da asuba na fita dakko ruwa kitchen.

“Ina kwana....?” na fada cikin dauke kaina

Lumshe idanu yayi ya bude yana taune lebe hade da sakin murmushi,

“Fikre! Barkan mu da safiya.. Meyasa bakya tashi na kullum sai ki ta tashi kina riga ni yin wanka?”

Ya karasa fada yana langab’ar da kai da karasowa inda nake. Na tabe baki ina cigaba da zizara kwalli acikin idanu na,

“Idan zaka shigo dakin mutane ka dinga neman izini dai”

Dariya yayi data bayyana hakoransa sosai yana fadin,

“Saikace wani kwarto , nida dakin matata kuma”.

Ban tanka masaba, saima saurin barin wajen da nayi, nama fita a dakin.

Tana fita Mubeen yayi murmushi yana nufar bandaki. Na dawo dauke da shayi naji motsin ruwa a bandaki, ban kawo wanka yakeba nadai zauna kawai ina shan tea din, dan da yunwa na kwanta yaron nan jiya yajamin kin cin abinci. Yadan jima sannan ya fito daure da bathrobe.

Saurin dauke kaina nayi tamkar ban ganshiba, yace,

“Kinyi kyau..”

“Nagode..” na fada batare dana kalle shi ba dai.

Tsulum sai gashi a gaba na yana shafa kwantaccen gashin kai na dana hade shi wuri d’aya da ribbon. Na lura yanason gashi, Bayan idan santsi ne dakyau nasa yafi nawa. D’ankwali na dauka zan daura ya rike yana zama a saiti na,

“Ki bar kan ki a haka... Kinji?”

Kasa masa musu nayi na kad’a kai kawai ina cigaba dashan tea dina. Mik’ewa yai yana murmushi ya jima yana taje sumar kansa, Kafin ya zauna a kasan carpet yana tankwashe kafafu bayan ya zira jallabiya a jikinsa.

“Fikre.. bani abinci yunwa nakeji”

Ka’da kai nayi na kakkai masa abincin dana shigo dashi a tire gaban sa,

“Toh a bani”

Yana iya haka na zage Ina bashi domin in dai shine zai ci to ba zai shi da yawa ba barin shi zai yi. Amman inde nice zan bashi to zai ci sosai wani lokacin harda ‘kari. Tas ya cinye na hada masa tea yasha.

“Mubeen..”

Saurin dagowa yai ya kalle ni. Na dan kalli gefe ina jujjuya maganar a zucia ta,

“Dan Allah inason komawa school.”

Ware idanu yai sai kuma ya hade rai yana turo baki ni abinma daria yaso bani na danne nima,

“Kaji? Dan Allah.”

“Meyasa kikeson komawa Zaria kingaji da ni ne?”

Girgiza kai nayi,

“A’a! Kawai inason na cigaba ne.”

“Hankali na ba zai kwanta ba Fikre! Ace ina kaduna matata kuma tana Zaria, Amma zan gayawa su papa”

“A’a kabarshi kawai.”

Na fada jiki na a sanyaye. Taune k’asan leben sa yai yana sanya hannu na acikin nasa, Yana son yimin wasu salo masu birkitamin lissafi a wasu lokutan,

“Fikre ina sonki, So mai tsanani. Banason kiyi nisa da ni, Nasha wahala kafin na mallake ki. Banason kiyi nisa da ni ko yaya wallahi.. Idan su Innar mu ki kai missing sai muje mu gayda su, Sai muje kuma school din ko?”

Kada kai nayi kawai jiki na yai sanyi.
Sai da yaci abincin sosai sannan yacemin ya koshi, tashi nai na tattare kwanikan na fita dasu, ina dawowa na iske baya dakin.

Zama nai abuna ina kokarin kunna wayata, sai gashi ya shigo cikin kananun kaya, yayi kyau sosai, amma saina dauke kaina tamkarma ban ganshi ba.

Wayar ya zare daga hannuna, sannan ya kama hannun ya mikar dani tsaye, ya dakko wayar sa akan gado hade da bude drawer ya dakko min hijabi,

“Saka muje wajen su papa..”

“Ga mayafin kaya na nan agefe sai hijabi.”

Nabi zungureran hijabin daya bani da kallo,

“Eh a haka zaki sa Allah! Duk sun tashi sun sa miki mayafai shara shara. Ni wallahi bana son su.”

“Toh ni inason kaya na ahaka.”

“Toh ni banaso, Ai dai ni zakiwa kwalliyar ko? Toh inde ni da ke ne ko dankwali ba sai kin saba amman inde zaki fita daga kofar nan to hijab zaki sa. Zan karo miki wasu.”

Na kalle shi cike da karfin halin jin kalaman sa. Karbar hijabin nai na zura. Na isa gaban mudubi na dakko maroon Jambaki zan saka kenan Mubeen ya karb’e yana ajiye shi,

“Meye hakan? Bani kaya na.”

“Fikre bar jambakin nan ba sai kin saba.”

“Mubeen meyasa kake haka ne? Fisabilillahi ya za’ai na tafi haka kamar wadda aka tono a rami ba dan jambaki. Dan Allah bani.”

“Ga Vaseline nan ki shafa ya wadatar.”

Banbi takan sa ba nai ficewa ta na barshi a tsaye yana daria. Da sauri ya karaso ni yana rikemin hannu, Na hadu da gamo na haka naita kiciniyar kwacewa amman yak’i saki na. Saboda rashin ta ido har parlorn Mamma Ahlaam muka k’arasa a haka hannun mu saqale dana juna. Na zare nawa dakyar ina matsawa can gefe bayan mun gaysa dasu.

“Ga abinci can a dinning.”

“Tab mun koshi, wallahi Fikre ta bani dankali da kwai da kunu ga tea harda soup na hanta kinji ciki na kuwa..”

Mamma Ahlaam tai murmushin jin dad’i, Ni kuwa gaba d’aya kunya ta ishe ni.

“Ai kuwa kayi kiba ba laipi. Alhamdulillah! Gwara kai ta ci ai ka samu ka maida jikin ka.”

“Ki mata magana ma wallahi sani fa take a gaba sai na cinye da yawa Mamma.”

Haj Ahlaam tayi murmushi kawai tana cigaba da danna wayar ta, Mubeen yai ta neman maganar sa har papa ya dawo muka gaysa nide duk kunya ta kamani. Anan muka wuni har dare muka koma sashen mu. Wanka nayo na haye kan gado can karshe ina dudduba waya ta. Daga nan bacci mai nauyi ya d’auke ni. Mubeen na ganin tayi bacci ya lallaba ya shige jikin ta yana sinsinar wuyan ta da k’irjin ta, Ga hannun sa d’aya na karakaina a ilahirin jikin ta. Ita kuwa Batoul ji take tamkar ana mata tafiyar susa sai kara bankaro jiki take tana susa, ta nan Mubeen ya samu ya rage zafi yana murmushi..

*WASHE—GARI*

Da safe muka shirya driver yaja mu zuwa Zaria, Sanye nake cikin doguwar rigar atamfa da hijabi blue kalar kayan. Gaba d’aya rai na a bace yake akan takurawar da Mubeen yake min tasa hijabi da sauran su. Dan sai da muka kwashi fad’a ma kafin mu taho, Tunda muka taho yake neman magana ban kula shi ba. Naci jambaki ja ya gauraye labbana, Haka muka karasa kofar gidan mu, direban ya sauka a hanya Mubeen ya karasa damu. Yana gama parking nasa hannu zan bude najita gam,

“Bude min na fita..”

“Idan naki fa?”

“Dan Allah fa nace..”

“Goge jambakin ki tukun..”

Hawaye ne ya tahomin na shanye ina dudduba tissue babu, Kasan atamfar jiki na na dago zan goge ya dakatar dani,

“Ungo nan goge..”

Juyawa nai da nufin kallon sa kawai ya hade bakin mu waje d’aya.. Wata irin sweet and passionate sumba mai zagaye jini da bargo ya shiga min, Cikin wani salo na daban yana yi yana dakatawa yaja numfashi ya cigaba, Daga goge jambaki sai abu yaso ya faskara, Inata janye jiki na ya rike ni gam yana cigaba da budurinsa. Wasa wasa tun ina irgen sakanni har na fara na mintina. Tun ina mamaki har lamarin ya fara bani tsoro ganin ya danna wani madanni kujerar da nake tayi baya ya rankwafo sosai yana kallon fuska ta, Nai saurin rufe idanu na ina rufe bakina,

“Wayyo dan Allah! Kabari..”

Murmushi yai ya koma ya zauna yana kifa kansa a sitiyari fuskar sa na kallo na. A hankali cikin lumshe idanu yace dani,

“Zan shigo daga baya...Kije”

Saurin kada kai nayi ina gyara zaman hijabi na na shige da sauri ko takan wayata ban bi ba.....

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻__Could this actually turned into something real? Shin ya zata kaya ne da zukatan masoya biyu wanda suke da banbance-banbance a tsakanin su? The class of the have and the have not??? Suraidah 'yar gidan wani babban oil tycoon ce. Muhammad Mahboub kuma d'an gidan talakawan talak ne. Shin ya zata kaya ne da

Please Login or Register in order to submit comment