Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na uku ya juya ya koma yana jan kasan lips dinsa, Harara mahaifiyar tasu ta dankara masa. Dan murmushi yayi yana sosa ‘keya, A haka wani dattijo ya shigo da alamun mahaifin su ne. Da sauri matashin saurayin ya bashi hannu suka gaysa yana mai sannu da zuwa da harshen hausa,

“Papa sannu da dawowa.”

“Yauwa Muhammad. Ya school?”

“Alhamdulillah!”

Muhammad Mubeen ya fada yana kallon mahaifiyar tasu,

“Mamma can i?”

Ya karasa fada yana nuna kafar bene alamar ya tafi? Kad’a kai tayi tana girgiza kai. Sama ya haye da sauri yana cire agogon dake daure a wutsiyar hannun sa. Su kuwa sauran yaran bararrajewa su kai suna hira da iyayen nasu, Suyi da yaran Amharic wani zancen kuma su yi da Hausa gwanin ban sha’awa.

**Tsaye take a kitchen kusa da gas cooker, dan wake take sakawa d'ayan tukunyar kuma kwai ne take dafawa, mai aikin ta kuma tana gefe domin a ka'ida duk wani abunda mai gidan yake son ci matar gidan itace ke girka masa idan ba haka ba toh ba zai ci komai ba har sai ya fita wajan harkokinsa. Muhammad Mubeen ne ya shigo, Sanye yake cikin kananun kaya, ba tare da yace komai ba ya zaro cokali yaje kusa da Maman tashi yana taya ta jefa d'an waken a cikin ruwan dahuwa.

“silezīhi wede tachi weredu?”
(An sakko kenan?)

Yayi murmushi kad'an ba tare da yayi magana ba, daman tasan hakan zata kasance dan haka bata damu ba suka ci gaba da sakin d'an waken har suka gama. Kallonsa ta d'an yi shi kuma ya juya zai fita tace masa,

“migibuni le’irisiwo mesit’eti ālebinyi?”
(Zaka ci ne na zuba maka?)

Yanzu ma girgiza kai yayi alamun a'a bazai ci ba ya kuma sanya kai ya bar cikin kitchen d'in, shu'umin yaro ne wanda miskilanci ya yiwa yawa, sam baya kaunar magana

*SHIN WANENE AMB SALEES MUHAMMAD?*

Ambassador salees muhammad ambassador ne dake wakiltar Nigeria a kasar Ethiopia. Ya kusa retiring ma saboda permanent ambassador ne bana appointing ba. Cikakken dan usulin kaduna-zaria ne. Babban ‘dah ne ga marigayi Alhaji Muhammad Mai Taya. Su uku ne jal awajen iyayen su. Shine babba sai kanin sa Alhaji Bilalu wanda senator ne shi dake wakiltar wani yanki a jihar kaduna, Sai kanwar su Rahilah wadda ke aure a Zaria kuma awajen ta mahaifiyar su take. Mahaifin su Allah yayi masa rasuwa tun shekarun baya.

Amb. Salees babban mutum ne wanda ya rik’e mukamai da dama a kasar Nigeria dama ketare, Matar sa tafarko Allah yayi mata rasuwa bata taba haihuwa ba . Bayan rasuwar ta da wa’ensu shekaru aka bashi mukamin Ambassador for peace dake wakiltar Nigeria a kasar Ethiopia. Anan ALLAH ya hada ransa da sakatariyar sa wadda musulma ce yar kasar Ethiopia mai suna ‘Ahlaam Bnt Jauhar’ Har ALLAH yayi da rabon aure a tsakin su ya aure ta. Shekarar farko ALLAH ya albarkace su da samun ‘yaya hudu. Maza biyu mata biyu.

Muhammad Mubeen shine ‘dan su na farko, Sai Jannat wadda taci sunan mahaifiyar Amb Salees wato Inna Hauwa. Sai Mashkour da kuma autar su Aeedah. Gaba d’aya yaran sai su kai ruwa biyu, Sun dakko yanayin fatar mahaifiyar su da yanayin gashin kanta, Sai tsayi da siffar jikin su irin na mahaifin su hausa fulani. Sun kasance tun sanda aka haife su acan suke. Hutu ne kawai ke kawo su Nigeria. Hakan yasanya suke jin hausa sosai domin acikin Nigerian embassy din suke, Kuma akwai ma'aikatan da suke aiki anan suma da matan su da yaran su, Shi yasa suka iya hausa kamar wanda aka haife su a kano. Amma sunfi yin yaren kasar ta Ethiopia wato yarukan Amharic da Oromo.

A yanzu haka Ambassador Salees ya fara musu shirye shiryen komawa ‘kasar Nigeria domin yanason yayi takarar zama gwamnan jihar kaduna..


____
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*YEFIK’KIRI TARIKI....💞*


*2️⃣5️⃣*


*LIMAN KONA*

*GIDAN MATA TARA*

Yana gama yi min albishir d'in da ya kawo min na mik'e cikin tsantsar farin ciki na rungumesa Ina tsalle da kafafuwa na. Innar mu dake zaune tana cin tuwo sai murmushi take yi tana girgiza kai fuskarta kunshe da murmushi na tsantsar farin ciki.

“Yayan mu naji dad'i kwarai da gaske, wallahi lokacin da ka karb'i takarduna banyi zaton zan samu ba. Na gode Yayan mu ALLAH ya baka mata ta gari, ya baka mai kaunarka kilama kawata ce matar.'”

Dariya yayi domin ya gane wacce take nufi, bata san yaje gidan su Fadilan ba ya yi magana da mahaifin ta amman yace masa ya d'an jirkinta, shi kuma yaje ne saboda ganin yadda ko b'oye soyayyarsa yarinyar bata iya yi, shi yasa kafin ya fara zuwa gurin nata ya fara tuntub'ar shi kamar yadda addini ya gindaya.

“Kedai kiyi min addu'a kawai, ba sai kince kila ba. Yanzu ranar Monday zaki fara zuwa dan shugabar makarantar tace daman suna da buk'atar malamar turanci a wasu ajujuwan.”

“Aikuwa zanje da wuri ma kuwa Yayan mu, kaima Allah ya baka babban abin yi yadda zaka gatanta mu da yawa.”

Duk suka yi dariya, auta dake rubutu a cikin littafinta ta d'ago tana kallansu tace.

“Ni dai Yaya barrister zan zama yadda zan dinga yankewa su kawu ila hukunci idan an kaisu k'ara.”

Duk muka rike baki had'e da zaro idanuwa waje, Inna kuwa harda dafe kirji tace.

“Auta karna sake jin wannan maganar ki rufawa kanki asiri, kina ganin daman ke kadai ce wacce basa yiwa komai saboda ke a cikin gidan nan na haifeki. Toh ki yi shiru da wannan shirmen naki kafin yaji ki kema ki shiga cikin bakaken addu'o'insa da yake mana.”

Baki ta turo da alama haushin fad'an Inna taji, sai tayi shiru bata sake tofa mana baki ba har lokacin kwanciya bacci yayi ta kwanta. Yayan mu ya d'auki tabarmar da yake kwanciya a nan k'ofar d'akin mu, ya d'auki zannuwan da yake shimfid'awa shima yaje ya kwanta. Washe gari da tashin hankali muka farka, domin tun dare aka kira kawu ila cewar shagonsa ya kama da wuta babu abinda yayi saura a cikinsa. Ya dawo gida ya dinga surutai kamar wani arne wanda bai san kaddara ba, yana kuka 'yan uwansa da matansa suna ta bashi hakuri amman yaki yin shiru.

“Har ni za'a yiwa bakin ciki saboda anga bana fita yawan maula, ban dogara da kowa ba bare a kawo min rai ni, shine za'a kona min shago? Toh wallahi ba zan yadda ba sai an biya ni aheee!”

“Ka zauna kanata zance sai an biya ka, toh waye ya kona maka shagon da har kake zaton zai biya ka?”

“Kece, aradun Allah ke ce Bintalo, saboda babu wanda yake sakawa kayana ido idan bake ba matsiyaciya.”

“Ahaiyyyeee carkwai! Yo ilyasu har kana da arzikin da zai tsole min ido ne? Karka manta fa munsan shafe-shafe munsan kala, Sittin ta ubangiji yanzun nan sai na b'alle maka tazuge a tsakar gidan nan Waye bai san cewar gadon su Najibu bane ka hau kai kayi dumu-dumu akai ba, shine yanzu dan asiri ya tonu zaka ce nice na kona shago. Ayyirrrrrr nanaye caca's..”

Zuciya ta d'ibi kawu ila, ya habb'arar da bokitinsa dake ajiye a gefe ya nufi inda Bintalo ke karkad'a kugu. Tana ganinsa ta ciro d'ankwali tayi damara, cikin rashin sani taji ya sauke mata yatsunsa guda biyar a saman kumatunta, ta saki wata gigitacciyar kara tare da zubewa a gurin tana ihu. Nan da nan gidan ya sake rikicewa, su Zabbau da Alawiyya suka yo kan kawu ila zasu rufar mishi, Yayan mu da ya fito daga band'aki yayi saurin yar da butar yaje ya tare su.

“Ka rabu damu Najib muje mu rage masa hakoran bakinsa, mu zai dokarwa uwa? Toh yau zamu nuna masa muma fa shugon ne yabar ganin shima ya iya.”

“Kuyi hakuri dan Allah, ko babu komai shima uba ne a wajan mu baki d'aya, nasan zafin abinda ya faru ne yasa shi aikata wannan d'anyan aikin, da kuma yanayin yadda take bashi amsa. Kuyi hakuri karku tab'a shi.”

Yaya Najibu ya samu ya lallab'a su Zabbau, shi kuma kawu ila ganin an hanasu sai ya fara kumfar baki yana cewa.

“Daka rabu dasu ai naga iya inda rashin kunyar tasu ta tsaya, yara marasa tarbiya an tsotsa a Mama marar tsabta. Bar su kuzo ku doke ni sai na tabbatar da iya tarbiyarku tsinannu 'yan...”

Bai samu damar k'arasawa ba sakamakon kofin da Hinde ta cilla masa a keyarsa. Kai gidan mu sai dai addu'a amman sam babu tarbiya a cikinsa. Nanfa aka had'u aka dinga dambe tsakanin su Zabbau yaran Bintalo dasu Yazeedu yaron kawu ila gidan ya sake rarrabewa kowa da nasa b'angaren da yake goyan baya. Innar mu ta fito daga saman ta leko ta kira Yayan mu da yake ta faman k'ok'arin rabo tace ya dawo ciki, dan idan komai ya lafa tasan Bintalo da kawu ila zasu iya jonewa azo a barshi a ciki bayan shi rabon fad'a yaje.

Ganin abun yaki karewa ne yasa kawu ishaq zuwa kiran 'yan sanda, aka zo aka tsawatar musu sannan aka ja musu kunne kan cewar duk wanda ya kuma cewa wani ne yayi masa kaza toh za'a kaishi gidan yari ko waye a cikin gidan mata tara. Wannan abun ne yasa aka yi shiru, sai dai fa kullum kawu ila sai ya zazzagi wad'anda suka kona masa shago, ya koma komai sai da kyar ake yi, gashi da mata biyu kowa jira yake ya kawo masa. Ni kuwa littinin na zuwa na shirya tsab na fito zan tafi Private school din da Yayan mu ya samo min aikin koyarwa.

A ranar da naje principal d'in makarantar *NAWAL MODEL NURSERY AND PRIMARY SCHOOL* tayi min interview, taji dad'in yadda nake bata amsa sai tace zan dinga koyar da 'yan aji uku na primary, kud'in da zasu bani kuma dubu ashirin. Nayi murna da godiya cikin raina ina sanya musu albarka. Naje classes d'in da aka bani nayi introducing d'in kaina sannan na koma female staffs room na zauna na fara rubuta planing book saboda idan nazo gobe nasan abinda zanyi musu.

Tunda na fara teaching d'in nan babu wanda ya sani a cikin gidan mu, duk a tunaninsu wani karatun na kuma dorawa, har kawu Dawood na cewa dan ALLAH na karance duk duniyar karna bar komai. Basu tashi shan mamaki ba sai da na fara jin alert sannan ne suka ankara da abinda nake yi, saboda cimar mu ta canza, sannan na bawa matayen gidan wato iyayen naira d'ari biyu-biyu su kuma kawus duk na bisu da d'ari biyar-biyar a bisa umarnin Inna wai na sanya albarka ne bayan kuma basa sanya mana d'in....

*KADUNA NIGERIA*

Dirar su a jirgi ba jimawa driver yaje airpot ya d'auke su, kai tsaye ya nufi Zaria dasu inda nan ne suke da gida. Unguwar Bomo suka sauka cikin wani katafaran gida wanda kai daga ganinsa kasan cewar mamallakin gidan wani kusa ne a cikin wannan k'asar tamu mai tarin albarka. Driver na gama parking kowa ya fito daga cikin motar amman banda Muhd Mubeen, yana zaune kawai yana danna waya, sam ba zaka fahimci a wane irin yanayi yake ba, amman tabbas cikin zuciyarsa bai so aka dawo k'asar nan ba, dan yasan 'yan uwa da dangi zuwa zasu yi tayi gidan suna cika su da hayaniya.

“Muhd Mubeen, fito mana.”

Papan u ya fad'a yana bude murfin side d'in Mubeen din, yayin da ya zura wayar cikin aljihun jeans d'insa yaki bari su had'a ido da mahaifin nashi saboda kwarjini yake masa. Yana gaba papan su na biye dashi, dama tuni sauran suka wuce ciki. A parlour ya zauna kan kujera yana dafe goshi saboda jin sa yayi yana bugawa alamun ciwo zai yi.

“Kaje kayi shower kazo kasha maganinka tun kafin yazo ya kwantar da kai.”

Papan su ya fad'a yana kurawa d'an nasa ido, da alamun sun san matsalar shi tunda gashi har magani yake dashi. Sam baya son tafiya mai nisa indai tafiyar mota ce ko mashin ko jirgi, duk lokacin da yayi sai ciwon kai ya saukar mishi, yafi son tafiyar k'asa ko keke, wannan kam duk inda kace yaje zaije haka halittarsa take, iyayen suna kyautata zaton nan gaba zai dena musamman da yanzu suka dawo k'asar su, suda Ethiopia sai dai idan zasu family d'in mahaifiyar su.

A hankali ya mik'e ya nufi side d'in shi, komai tsab dashi babu abinda zai nema ya rasa a cikin d'akin nashi. Kaya ya cire ya shiga bathroom, ruwa ya kunna a heater sannan ya fito jikinsa daure da towel hannunsa rik'e da kayan da ya cire, wani d'an karamin d'aki ya shiga ya nufi wajan washing machine ya bud'e ya saka kayan a ciki ya kuma fita zuwa bedroom d'insa. Wardrobe ya bud'e nan ma akwai kayansa a ciki sabbabi dal, ya d'akko vest da boxer short ya ajiye akan gadon. Ya jima zaune a bakin gado kafin ya mik'e ya kuma shiga cikin bathroom d'in ya shiga cikin kwamin wanka tare da kunna shower ruwan yana zuba a jikinsa.

Ya jima a bathroom d'in kafin ya fito ya shirya cikin farar vest da boxer yasa turaruka a jikinsa sannan ya nufi parlourn side d'in nashi ya kwanta akan kujera, wani textbook ya gani akan hannun kujerar ya dauka yana dubawa. Can b'angaren kuma suna can jiransa ake ya fito yasha magani yaci abinci amman shiru, mahaifiyar su ta kalli autar ta tace.

“hīdi talak’i wenidimihini dewilileti, met’itomi migibuni inidībelana mediḫanītuni inidīwesidi nigerewi”

 (Je ki kira Ya MM kice yazo yaci abinci yasha maganin sa.)

Mikewa Aeedah tayi hannun ta da teddy bear dinta ta tafi kiran yayan nasu. Sashen sa ta shiga tana kwala masa kira,

“Assalam alaikoum! Yayya Mm mamma said you should comman eat and take your med, right now.”

Ajiye littafin yayi yana yamutsa fuska, Shi dama basa shiri da abinci. Da hannu yai mata alama da taje yana zuwa. Mikewa yai ya koma dakin sa ya zura wando wanda ya kai masa zuwa gwiwa. Hannuwan sa zube cikin aljihun sa ya nufi parlorn yana yamutsa fuska, Ran sa a jagule yake. Gaba d’aya sun hallara a dinning area suna jiran fitowar sa. K’arasawa yai yaja kujera ya zauna yana tsotsan kasan lips dinsa,

“Me za’a zuba maka?”

Cewar Mamma Ahlaam mahaifiyar su. Wadda ke nuna masa abincin. Binsu yai da kallo yana sake hade rai, A hankali kamar mai koyan magana ya rik’e haba dakyar yace,

“Mamma na k’oshi fa.”

Tsaki taja tana zabga masa harara, Amb Salees dake gefe yai murmushi yana ajiye jaridar hannun sa,

“Ka ci ko yaya ne Muhd Mubeen. Kaga ba kada lapia, Ka daure ka dinga cin abinci kana jin dai abunda dr Amelia tace.”

Kad’a kai yayi ba tare da yace komai ba, Yasa hannun sa ya faten dankali. Tana zuba babban cokali d’aya ya dauka da sauri ya ajiye a gaban sa dan kada ma ta kara wani. Tamkar magani haka ya dinga cusa shi yana shan ruwa. Suna ta hirar su banda shi. Don inde miskili kake nema number d’aya to Muhammad Mubeen yafi kowa. Yana gama cinyewa ya mike yana goge bakin sa da tissue,

“Maganin fa?”

Amb Salees ya tambayeshi yana ‘ballo masa maganin. Ya dora akan plate ya mika masa yana nuna masa ruwa a gefe. Dauka yai yasha ya koma sashen sa. Wunin ranar sir bai futo ba, Abincin dare ma bai ci ba sai tea.

*WASHE-GARI*

*UNGUWAR BOMO*
*AMB SALEES MUHD RESIDENCE*

Yana futowa daga wanka daure da bathrobe ya shiga goge curly gashin kansa da towel. Sai daya shafa mai ya sanya turarukha sannan ya zura jallabiya kawai yana kara feshe jikin sa da turare. A lokacin k’anwar sa Jannat tai knocking dakin ta shiga,

“Rise and shine big bro! Ina kwana?”

Kallo d’aya yai mata ya cigaba da taje sumar kansa. Matsawa ta kara yi kusa dashi tana kallon sa ta mudubi,

“Ya Mubeen! Wai kazo kaci abinci.”

K’ada kai yayi alamun Toh. Kafin ta fita harya rigata.

“Papa, Mamma ina kwana?”

“Alhamdulillah!”
Amb Salees ya fada yana karasa cike wasu takaddu.

“t’ewati! t’ēnahi inidēti newi?”
(Lapia! Ya jikin naka?)

Mama Ahlaam ta tambaye shi tana kawo masa tray din abinci gaban sa. Murmushi ya mata kawai ya karbi plate din ya ajiye agaban sa. Kunu ya debi a cup kawai yasha. Ya balli maganin sa yana kwantar da kansa a jikin kujera. Amb Salees ya mika masa wata takarda da pen,

“Rike ka cike na school dnka ne.”

“School?”

Ya tambaye shi yana kallon takardar. Kad’a kai mahaifin nasa yayi yana cigaba da cike sauran takaddun. Yamutsa fuska Muhammad Mubeen yai yana karanta takardar, Dakyar a hankali kamar mai ciwon mak’ogoro ya dubi mahaifin nasu,

“Papa! Ba home school? Ko na...”
Ya kasa karasawa yana kallon paper tamkar ya yaga ta.

“Home school kuma Muhammad? Nan fa ba embassy bane. Zaria ne, Cike ka mikomin banason a dau lokaci.”

Cikewa yai ya mika masa hade da mikewa zai koma daki Amb Salees ya tsaida shi,

“Dawo, Touring Zaria za’ai yau.”


“But..”

“No buts Muhammad shirya muje kai ake jira.”

“inē k’emīsi nenyi”
(A shirye nake.)

Ya fada yana ficewa daga parlorn. Farfajiyar wajen motocin yaje ya tsaya yana dafe kansa, A haka suka fito suka shisshiga motar su Jannat harda camera. Shiga yai yana cije lebe. Unguwoyi suka fara bibbiyawa Amb Salees na gaya musu tarihin unguwoyin da shekarun da akayi su a takaice. Uffan Muhammad Mubeen bai ceba har suka karasa unguwar Limancin kona. Anan ne ya daga kai ya kalli unguwar yana dafe saitin zuciar sa dake masa wata irin bugawa ta daban. Har suka karasa gidah bai dena bugawa ba. Dakyar yake iya lumshe sexy sleepy romantic eyes dinsa yana rintse jajayen labban sa... Sosai yake mamakin sabon yanayin da bugun zuciar sa ya canza..


..
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼[7/26, 8:31 PM] +234 904 419 1709: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*HELWA....💞*


*62*

*LIMANCIN KONA*

*GIDAN ALHAJI KABEER MAI WAFA*

Bintalo na tafe tana kwaso rantsuwa tana direwa ita kadai, Sai watsa hannu baya take tana magana a hargitse. Dayan hannun nata kuma tana dukan takashin ta ta baya.

“Yar kundun ubar tsutsa, Sittin ta ubangiji kwalbar mursaleta zan siya na gwaggwuda miki duka.”

Haka ta karasa shiga cikin farfajiyar tana dukan takashin ta, Daga wajen filawoyi ta tsaya ta dan dubi koina kafin ta daga zani ta kaikaice ji kake,

‘Sittt..’

Tana gama sakin tusar ta mai shegen doyi ta karkade zanin tana rufe hancin ta,

“Kai, gumama! Sittin ta ubangiji aiken dan waken jia ne da alalar hinde.”

Sai data bari ta huce sosai sannan ta karasa cikin gidan tana doka sallama hade da cire mayafin ta ta rataye a bakin kofa. Ta corridor ta hango Alhaji Kabeer Mai Wafa yana sakkowa daga k’afar bene. Murmushin fuskar ta ne ya fada’da. Inna Rabi dake tsaye tun shigowar ta ta tsaya tana duban ta da kyau. Tun ba yau ba ta lura Bintalo na neman shisshigewa Alhajin. Ai kuwa mutuniyar ku ta kara bankaro kirji tana kara rambada gyatuma radau din bakin ta. Parlorn ta karasa da sauri tana rage sautin murya,

“Alhaji ina kwana? An tashi lapia?”

“Alhamdulillah sannu!”

Ya bata amsa yana zura takalmin sa sau ciki . Tsayawa tai tana kallon sa harda su lumshe idanu. Ya dan kalle ta yana mamakin tsaiwar da take. Sosa kai tayi tana kara dashare hakoran ta,

“Ya akai?”

“Uhm uhm w...”

“Ke! Meye haka? Me kikeyi anan?”

Cewar Haj Husnah wadda ke sakkowa daga sama tana taunar cingom. Bintalo ta shiga inda-inda tana nuna kofa. Alhaji Kabeer ya girgiza kansa kawai yana duban Haj Husnah.

“Haj ni zan fita. Na gaya miki Amb Salees yazo gari ko?”

“Eh haka kace. Can zaka je yanzu?”

“Eh zan biya ta can. Saboda akwai kwangilar gini da zamuyi magana dashi, Kinsan a gidan sa na bomo yake. Toh shine yake so a fara gina masa wanda zasu zauna anan cikin gari area din Hanwa low-cost.”

“Kai Masha Allah! Shine mai matar sa yar Ethiopia ko?”

“Eh...”

Ya bata amsa yana duba agogon wutsiyar hannun sa. Murmushi Haj Husnah tayi tasa hannu d’aya tana gyara masa karin hular sa,

“Komai yayi dai-dai Abban su. ‘Yayan sa nawa ne yanzu? Ta farkon data rasu bata taba haihuwa ba ko.?”

“Toh godia nake Umman su. Eh bata taba haihuwa ba. Wannan ‘yayanta hudu. Maza biyu mata biyu.”

“Kai Masha Allahu! Sai a daura zumunci. Babban ‘dan na....”

“Hajia sauri nake yi. Kar na tsaida shi kinsan manyan nan. Idan na dawo mayi magana.”

Alhaji Kabeer yai saurin katse ta yana mai ficewa daga parlorn da sauri. Rakiya ta masa. Bintalo dake tsaye kamar gunki ta cire hannun data sa abaki tana susar takashi. Sam ba taji dadin bata mata lokaci da Haj Husnah tayi ba. Da tuni tayiwa Alhaji magana ta sanar masa zuciar ta. Wayaga k’arfin hali. Cikin murtuka fuska Haj Husna ta koma parlorn tana jera kwan cingom. Zama tayi a kujera tana karkada kafafuwa. Bintalo ta fara jan kafafuwan ta zata fita ta kira ta a tsawace,

“Zo nan Bintalo. Munasura! Ina zaki ko guduwa zaki yi?”

Bintalo ta koma tana sadda kanta a ‘kasa. Haj Husnah taja dogon tsaki tana kwallawa Innar Rabi kira,

“Rabi, Rabi, Rabi..”

Da azama inna Rabi ta shiga parlorn hannun ta dauke da ludayi.

“Me kike yanzu?”

“Hajia abincin Haysam nake dafawa.”

“Ok yayi kyau. Dan Allah karki masa me magi irin rannan.”

“IN SHA ALLAH! Hajia.”

“Kina nan Bintalo tazo yau?”

Bintalo ta shiga raba idanuwa tana kallon Inna Rabi, Inna Rabi ta kad’a kai alamun Eh. Kafin cikin sauri tace,

“Ina nan Hajia. Wani abun ne?”

“Sanda Alhaji yana nan. Sunyi wata magana da ita?”

Inna Rabi ta girgiza kai,

“Gaskia bansani ba ko sunyi. Da dai tare muke a kitchen da ita. Toh sanda Alhajin ya sakko kuma sai naga ta shiga parlorn. Toh bansan ya su kai ba kuma.”

Hajia Husnah tayi murmushi hade da yiwa Inna Rabi alama da hannu da ta tafi. Bintalo ta shiga zare idanu. Dayan hannun ta kuma tana sosa takashi. ‘Das ta ‘dada ma takashin duka hade da dukawa ta soso wajen sosai. Haj Husna ta taja tsaki tana jifanta da harara,

“Meye haka?”

“Sittin ta ubangiji wata yar kundin uban tsutsa ce kecin zarafi na a ‘duwaiwai. Mursuleta zan cusawa shegia ta mutu sa..”

“Kina jina? Kada ki ‘kara takomin shegiyar k’afar ki gidan nan. Daga ya...”

Bintalo ta zube a kasa tana kururuwa,

“Wayyo ni Bintalo yar marainiya. Hajia kiyi hak’uri. Sittin ta u..”

“Karki wata rantsuwa. Bara kiji ma nayi miki yadda xaki gane kema, Sittin ta ubangiji zama na dake ya ‘kare daga yau. Ki tattara naki ya naki ki tafi. Mai gidana kike so ina hankalce da duk shige da ficen ki. Ina ke ina miji na? Dube ki dan ALLAH. Wata sad’od’o dake ba gaba ba baya. Sai kaje namiji, ‘kirji kamar silifas. ‘Kazama baki da aiki sai susar takashi. Saboda tsabar kazanta. Ficemin daga gida yanzu kafin na rufe ki da duka.”

Haj Husnah ta karasa balbalawa Bintalo fada tana huci. Bintalo ta shiga runtuma ihu jin kalaman hajian na karshe. Hawaye na zuba majina na kwarara haka Bintalo ta kara gwaggwafewa tana bawa Haj Husnah hak’uri,

“Kiyi hakuri Haj. Kinga an gama lalata min rayuwa ta data ‘yayana. Babbar ‘yata mijin

Please Login or Register in order to submit comment