Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubu biyu da takwas.

_Shantu ‘kwarya dadi, kai mu karkada shantu yan uwa ai ko badan komai ba sai dan Al’adun hausa. Ya Allahu muna rokan ka, Ya Allahu muna rokan ka daka sa muci SSCE ai ko badan komai ba sai dan mu burge iyaye. Principal ma tafada, vice principal ma tafada, Allah yasa mu ci SSCE ai ko badan komai ba sai dan mu burge iyaye.🎵_

Haka dai mu kai ta bushe bushe na usur da wakokin candy. Abun gwanin birgewa. Kiran sunayen masu muk’ami principal ta shiga yi. Turyan turyan har akazo kai na wato ni shugabar daliban makarantar baki d’aya. Yara sai ihu suke yi na murnar kiran sunana. Murmushi fad’ade akan fuskata. Kai dagani kasan ina cikin farin ciki. Haka malamai suka hadamun kyauta himili guda. Har sai dana zubda hawayen farin ciki. Nasamu yabo daga bakunan malamai da dama. Alhamdulillah Allah shine abun godia. Hamdala kawai nake a zuciata har muka fito daga harabar makarantar ni da yan ajin mu. Autar mu ta tayani rikon kyaututtukan da aka babba ni. Sunana na tsinkayo Malamin Literature din mu na dokamin. Amsawa nayi ina tafiya don amsa kiran sa. Ko bai fada ba nasan Malam Tasiu yana min son son fisabilillahi bai dai fada ba. Amman na gano tuni a irin yadda yake rawar jiki a kai na. Yana tafe shima yana sosa k’eya haka muka tsaya nesa da juna kadan. Cikin sunkuyar da kai na kasa nace,

“Malam gani...”

“Sannu Malama Batoul... Yau an kammala makaranta, Shikenan za’a mance damu ko?”

Murmushi nayi, Wanda kumatu na ya lotsa, Yar wushirya ta ta bayyana. Cikin kasa da murya nace,

“A’ah Malam ai ban isa ba.”

“Hmm! Haka dai kike gani, Amman kin isa har kinyi yawa a zucia ta.”

Yak’arasa fada yana gyara tsaiwar sa, Sauran Malamai dake nesa sai kallon mu suke, Da alamun muhawara ake akan mu. Shiru nayi ban amsa shi ba. Shima bai sake magana ba sai zaro wata zungureriyar wasika da yayi a aljihun sa ya mik’o min. Na ki karba ina matsawa baya,

“Karbi mana batoul. Dan Allah karki ki karbar kokon barata. Wannan wasikar zata shaida miki duk abunda ke zuciata..”

Sunan ALLAH daya had’ani dashi yasanya bazan ki amsar takardar ba, Na sa hannu biyu na karba ina dan rissinawa. Sallama nai masa na koma cikin k’awaye na muka cigaba da tafiyar mu.

*BATOUL*

Nasan mai karatu zai yi mamakin girma na. Toh dai a lokacin shekaru na 17/18. Na kasance mai wata irin sihirtacciyar kalar fata, Domin da agidan hutu nake ma da tuni kala ta ta kara turuwa. Inada yalwar gashin kai dana gira. Baki na dan mitsitsi ne kamar na jarirai jajaye dasu. Hanci na tsaye yake a mike kamar ni na zana kaya na. Ina da tsawo TubarkAllah domin dole ka sani a jerin dogaye. Jikina a murmure kirar zatin halitta ta ta zauna daram. Duk namiji mai jini a jika ya hange ni ni Batoul dole yai sha’awar kasancewa ta matar sa. Lalle dik dan adam tare yake bai cika goma ba, Amma ni Batoul na cika tara na cif cif Alhamdulillah! lamarin sai godiyar uhangiji kawai. Yau ne ranar da na kammala makarantar sakandire inda na karanci fannin Art. Hakika ina da ‘kwazo da basira fiye da tunanin mai tunani.

*GIDAN MATA TARA*

Shigar mu gidah kenan ni da Autar mu muka hangi su Usaiba da Rabi’atu matan Kawu Ishaq su na dambatuwa a tsakar gidan mu. Gaba d’aya ahalin gidan mu sun firfito ciki harda ‘yayan ma’kota. Yadda kukansa gidan kallon kwallo haka akataru ana kallon dambatuwar da suke yi. Kawu ila na Zaune akan bokitin sa na gado yana sakace hakora. Innar mu ce kawai bata tsakiyar gidan.

“Ci uban ta Rabi”

Bintalo tacewa Rabi’atu da suke kokawa da Usaiba. Girgixa kai nayi na haura sama abuna. Ina jiyo kukan Rabi’atu. Wadda usaiba ta daga ta maka a ‘kasa. Tsakar gidan suka kece da daria. Dakin mu na shige baki na dauke da sallama.

“Wa’alaykm Salam.!”

Innar mu ta amsa tana kokarin tace taliya a mataci. Zama nayi hade da ajiye kyaututtukan da aka bani akan yar katifar mu. Dubawa nayi ganin banga sauran ba. Na shiga duddubawa ina babbanka dasu. Tunawa nayi suna hannun autar mu. Kishingidawa nayi akan katifa. Cikin gajiyar dana kwaso nace wa Innar mu,

“Innar mu sannu da aiki..”

“Yauwa Batoul. An dawo. Ina auta kuma?”

“Tana can kallon wasan kwaikwayo a kasa.”

Dakuwa Innar mu tayi min tana mai juye taliyar data tace a cikin dan foodflask din mu. Muskutawa nayi na debo kyaututtukan na ajiye a gaban ta.

“Innar mu yau mun ‘kare makaranta. Munyi candy. Alhamdulillah! Kinga kyaututtukan da aka babbani wasu ma suna hannun autar mu.”

Albarka Innar mu tasa ka min akan karatun. Tana mai duddu ba kayan cike da farinciki. Mikewa nayi domin kiran autar mu. Ina lekawa ta saman na shiga k’walla mata kira. A guje ta taho tana juyawa tana cigaba da kallon fa’dan da akeyi. Inda sabo mun saba sai afi awa ana kwasar fada a gidan mu. A kwanta washegari a tashi a dora daga inda aka tsaya kamar wasan kwaikwayo. I m

“Ke zo nan.”

Kawu ila ya kira autar mu yana mai zare mata idanuwa. Komawa tayi wajen sa jikin ta sai rawa yake yi. Yatsa yasa yana mai nuni da kayan hannun ta.

“Meye wannan?!”

“Ka..kak. Kayan Yaya Batoul ne.”

Dago kansa yayi muka hada idanu. Ya maida duban sa ga autar mu.

“Ajiye kayan ki tafi. Ke kuma zonan dan uban ki.”

Ya sallami autar mu. Ni kuma ya kira ni. Yana mai babbankada kayan kyautar da aka bani. Autar mu ta shige daki a guje ni kuma na karasa sauka kasan na tsugunna daga gefe.

“Gani Kawu..”

“Dan uban ki a’ina kika samu wannan kayan? “

“Kawu kayan kyauta ne da aka babbani a matsayi na na shugabar dalibai.”

Tab’e baki yayi, hade da zazzage ledojin. Ta farko littafai ne aciki da math-set. Leda ta biyu kuma kifin gwangwani ne guda biyar da lemon roba shima biyar. Babban dansa mai suna Yazeedu ya kwallawa kira, Da sauri yaron yazo ya tsugunna a gefe na,

“Gani Baba.”

Ledar farko mai dauke da littafan da math-set ya mika masa, Kai na kawai na girgiza ina mai jin wani abu ya tokare min wuya na tabbata na b’acin rai ne. Ina jiyo shi yana ce masa,

“Rik’e nan. Ka dau guda biyar kabawa su Mariya sauran. Maset din kuma ka dauka.”

Karfin hali. Allah kayi mana sakayya cikin gaggawa. Allah kana ganin yadda wannan bawa naka yai mana. Allah ka saka min. Haka nai ta nanatawa a xuciata domin nasan wallahi adduar wanda aka zalunta batada hijabi da ALLAH.

Cikin adduar da nake kwararawa a zucia ta na jiyo muryar sa,

“Ungo rike , Tashi ki bani waje.”

Kifin gwangwani d’aya ya mi’ko min guda d’aya da lemo d’aya, sauran kuma ya nannade a leda ya zura akan bokitin sa dayake zaune. Kifi d’aya kacal yabani acikin guda biyar da lemo d’aya shima acikin guda biyar. Abu biyu dai kacal ya bani acikin guda goma, Ban dama sauran littafan. Hawayen daya tahomin na goge wallahi badan nasan autar mu zatai kwadayin ci ba da bazan karba ba. Yahada ya cinye ya biyani a lahira. Sama na haye ina jiyo Bintalo tana dariyar mugun ta. Ina shiga daki na mikawa autar mu lemon da kifin,

“Ku raba keda Innar mu. Ya debe sauran. Innar mu har littafan da aka bani da math set ya dauke duka. Agabana ya kira Yazeedu ya mika masa wai shi dasu Mariya. Hakama kifin da lemon d’ai d’aya ya bani ya boye sauran. Shin wannan wacce irin rayuwa ce Innar mu? Narantse da Allah bazan taba yafe musu ba. Innar mu hak’uri na ya....”

Innar mu ce tai hanzarin katse ni, Ta hanyar cewa,

“Ya isa Batoul. Kar ki manta dai iyayen ki ne. Komai sukai dai dai ne. Ki dena cewa sun zalunce ki. Kina jina?”

Daga kai kawai nayi, Na juya bayana ina kuka ahankali marar sauti. Ban dena kuka ba har sai da aka fara kiraye kirayen sallar azahar sannan na mike na dauki bokitin wankan mu da soso da sabulu nai kasa. Ruwa na diba a rijiya zan shiga band’akin Bintalo ta bangaje ni ta saka bokitin ta aciki.

“Duka na zaki yi? Nace dake ni mana. Sai in san kin zama rikakkiyar mara kunya..”

Kawu ila ne ya fito daga dakin sa yana shan lemon roba ta daya kwace na d’axu.

“Menene Bintalo?”

“Sittin ta ubangiji yarinyar nan ce ta mangaje ni kawai dan zan shiga band’aki.”

Ido na zaro ganin irin rantsuwar da tai akan karya bayan ban aikata hakan ba. Ya sake kurbar lemon hannun sa sannan ya saki wata uwar gyatsa kafin yace,

“Ita da ni ne, shiyasa zata kare rashin kunyar akan ki. Ki shigewar ki zanyi maganin ta.”

“Wallahi Kawu b..”

Saurin dakatar da ni yayi yana mai nuna ni da yatsa.

“Rufemin baki. Almura da idanuwa tsuru tsuru sai kace na mayya. Zaki matsa daga nan ko sai na take kan shegiya.”

Komawa nayi baya. Kan dan simintin kusa da rijiya na zauna ina mai mamakin irin rayuwar gidan mu. Sai kace gidan haya mai dauke da yaruka kala kala. Haka nai ta tunanin kuncin rayuwar mu har Bintalo ta futo daga bandakin. Tana fitowa don neman tsokana ta karkade ruwan soson ta a fuska ta kafin ta wuce sama. Bandakin na shige nai wanka na hade da rage nauyin ciki na. Ina gamawa na haye sama. Alokacin su Alawiyya suka dawo daga makarantar su. Suma sun kammala makaranta yau. Ina jiyo Kawu ila yana sanyawa abunda suka karanta albarka. Ina idar da sallah na ciro kayan da na saka a karkashin kwallar mu. Atamfar sallar mu ce ta bara wadda gwaggo Aminatu tayi mana. Na saka ta hade da mayafin da balkisa yar kanwar Innar mu dake Shema ta bani kunce. Banyi kwalliya ba amma sosai nayi kyau. Sai kallon kai na nake ta madubi. Turaren mu dan duwala na shafa. Hade da d’aukar letar da Malam yabani.

“Innar mu zanje gidan su Fadilah na mata Allah yasanya alkhairi.”

“Madallah! Kya gaida maman tasu. Kar kiyi yamma dai.”

“In Sha Allah bazan dade ba.”

“Nima yanzu dana gama shirina zan le’ka gidan su Haysam. Ko akwai aikin da zan taya Haj Husnah.”

Ajiyar zuciya na sauke. Har ga Allah na tsani zuwa yawan aikatau da Innar mu keyi. Shiyasa na quduri niyyar yin karatu mai zurfi domin nima na samu wani mukamin ko aiki mai tsoka a gwamnati domin tallafawa Innar mu dama yan uwan mu marassa shi gaba d’aya. Sannan banason tana aiki agidan su Haysam. Duk kuwa da ba son shi nake yi ba. Amman banason tana aiki acan. A sanyaye nace,

“Toh Innar mu. Allah ya dawo dake lapia. Sai na dawo.”

Hannun autar mu na rike muka tafi gidan su Fadilah wato babbar kawata...

******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋



MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


NA HANSATU XOXO🧕🏼

_*SHAFI NA BAKWAI_*

•. •. •

Muna shiga gidan su Fadila muka tarar da baban su zai fitar da motar sa waje. Yana ganin mu yayi murmushi. Saboda yasan amintar mu ni da Fadila, Har k’asa muka dur’kusa muna gaishe shi ni da autar mu. Ya amsa fuskar sa fad’ad’e da murmushi.

“Lapia lou Batoul. Yau an kare makaranta ko?”

Kai na a kasa cike da girmamawa nace,

“Eh Baffa!”

“Toh Allah ya zaba maku abunda yafi alkhairi a rayuwar ku. Ki shiga tana ciki. Bata jima da dawowa daga makaranta ba itama.”

“Ameen Ya Rabbi Baffa.”

Mikewa mu kai daga dur’kushen da muke, Mu ka shiga ciki, Shi kuma ya ja motar sa ya fita. Aunty Nanah mahaifiyar su Fadila na zaune a tsakar gidan tana sawa Hauwa’u y’ar autar ta kunshi a yatsun hannu. Gaishe ta mu kai ta amsa ciki-ciki. Domin ita sam batason huldar mu baki d’aya da Fadila. Tafison Fadilan tayi kawance da ‘yayan masu kudi irin su. Shi yasa shekarun baya lokacin da Fadilan ke mayatar san Yayan mu. Hanata kawancen mu tayi. Sai a b’oye muke haduwa muyi hira. Fadila na jin murya ta ta futo d’aga dakin ta. Cike da murnar gani na ta washe hak’ora tana murmushi,

“Shigo Aminiyas.”

Murmushi nayi nima muka shiga cikin d’akin. Muka kafa dandalin hirar candy, kowannen mu yana bawa dan uwan sa yadda ranar yau takasance. Autar mu ta bingere a lallausar katifar Fadila, Tuni bacci barawo yayi awun gaba da ita. Fadila tayi rau-rau da idanu. Cikin ‘kasa-kasa da murya kar maman su ta jiyo ta tace dani,

“Wai ya labarin Yaya Najibu? Shiru wai ba xai dawo bane?!”

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke,

“Yana Kano! Muma mun kwan biyu bami magana dashi ba. Y’ar wayar da Innar mu ke amfani da ita ta ‘bata rannan. Mun rasa waye ya sace ta wallahi.”

Na k’arasa fada muryata na rawa. Fadila ta sake sakin wata ajiyar zuciyar. Kafin cikin damuwa tace,

“Da kaman kince min yana Shema garin su Innar mu.”

“Eh da acan yake. Toh daga baya kuma shi da ‘yayan wan maman mu suka tafi Kano neman ku’di. Kinsan ALLAH ya sanyawa Kano albarkar kasuwanci. Mutane anata zuwa neman kudi.”

“Oh okay! Allah yasanya albarka a kasuwancin nasu Ameen!”

“Ameen Tawan.”

Haka dai mu kai ta ‘yan hirarrakin mu, Har zancen samari ya shigo ciki. Fadila ta dinga tsokana ta kamar ko yaushe.

“Amiyas matar tsofi. Har yanzu kina nan akan bakan ki ko kuwa?”

Nayi murmushi kawai, Kafin cikin gaskiya ta nace.

“Fad’i ki kara, In Sha Allahu kuwa. Yo me zan yi da wanda suka bani Shekaru biyar ko ‘kasa? Wallahi basu isa aure ba. Ke ni ko wanda yabani shekaru bakwai bana fatan aura.”

Fadila ta shiga ‘babbaka daria harda rik’e ciki. Tana yi tana share hawaye tsabar dariar tayi yawa. Sai da tai mai isarta kafin tace,

“Lalle Aminyas. Ki ce kin sake ‘karo wulakan ci. Yanzu kenan wanda ya baki shekaru bakwai ma bakyasan aura? Lalle k’awata. Allah ki dena fadar haka. Hmm kilama Haysam ne mijin. Kuma kinga shekara biyar ya baki. Wai Aminiyas meyasa bakyason Haysam? Matashi dashi yaje yayo digiri d’insa a kasar waje. Shakaran jia dana had’u dashi wallahi yaketa min maganar ki Allah. Wai zai koma yayo digiri na biyu (master). A kasar Cyprus. Kuma so yake wai kafin ya tafi ya kai ku’din auren ki.”

Gwalalo idanuwa nayi ina ‘kik’kifta su cike da mamakin jin kalaman ta na karshe,

“Kai kudin aure fa kika ce? Saurayi na ne shi da zai kawo kudin aure na ko kuwa auren dole za’a min? Shi fa ya cika rigima. Dududu shekarar sa nawa?.”

Fadila ta sake kwashewa da daria kafin cikin dariyar tace,

“Shekarun sa ashirin da uku. Ai ya isa aure, Kuma in banda ke da abun ki ca yai auren fa sai ya gama masters tukun.”

Tsaki naja cike da takaici, Jin karfin hali irin na Haysam. Wai aure? Yaron da ko rabin hamsin bai kai ba (25). Cikin tunanin da nake a zuciata. Na jiyo Fadila na sake soko wani zancen.

“Allah Haysam na son ki Aminiyas. Wallahi bakiji yadda yake yabon ki ba. Wani irin son so yake miki mai wuyar bayyanawa. Na rokeki ki dena ganin ‘kankantar shekarun sa. Shi fa namiji baya kadan. Wallahi sai kiga anyi auren kakki mamaki satin farko ki ganki da ciki. Daganan zaki rena tunanin ki.”

Saurin rufe bakin ta nayi, Ina mai nuna mata Aunty da ido. Cire hannu na tayi daga kan bakin ta,

“Yo meye? Ai gaskia ne. Ke yanzu fa mun gama sakandire. Shafin sabuwar rayuwa muka buda. Kefa Aminiyas wallahi ki nada matsala. Duk samarin ki kin kore su bakya kula su. Idan an miki magana Ki ce du yarane ko kuma ke kinyi kankanta da zance. Dan Allah Aminiyas ki canza. Sai adinga miki kallon marar samari bayan kinadasu tirela tirela. Karki wasa da damar da ALLAH ya baki pls. Kinji tawaje na?”

“Naji Tawan! Yadda kika ce ai haka za’ai.”

Na bata amsa. Muka ha’da hannu muka tafa. Cikin so ta mance da dayar maganar nace,

“Ya babin karatu? Candy to aure zaki yi ko candy to ‘karo karatu?”

Yamutsa fuska Fadila tayi, Ta daga kai tana tunani kafin tace,

“Ke ni Yaya Najibu zan jira. In Sha Allah! Shine uban ‘ya’yana.”

Ajiyar zucia na sauke. Tabbas Fadila na kaunar Yayan mu. Matsalar mahaifiyar ta ba yadda zata yi ba. Kuma babu kyau tsallake maganar iyaye. Cikin son nunar da Fadila gaskia nace,

“Tawan ki tsaya ki saurare ni, ki auna maganar da zan miki a mizanin basira.”

Gyad’a kai Fadila tayi kafin tace,

“Ina jin ki.”

“Tawan kiyi hak’uri da batin jiran Yayan mu. Ki sani komai na duniya muqarrabi ne daga Allah. In dai ALLAH yayi zaki auri Yayan mu wlh ko me zai faru sai anyi. Idan kuma ALLAH yayi ba zaki aure shi ba w...”

Dakatar dani tayi ta hanyar rufemin baki. Hawaye suka fara yar tsere a kyakkyawar fuskar ta. Cikin rawar baki tace,

“D..Da..Dan ALLAH karki min fatan rashin auren Yaya. Wallahi ina son sa. Zan iya rasa farin ciki na idan har aka rabani dashi. Ya zanyi?”

“Kiyi hak’uri tawan. Ki kuma cigaba da addua. Allah zai zaba maki abunda yafi alkhairi a rayuwar ki. Zan so ki karanta wani littafi na wata writer mai suna miss xoxo. Sunan littafin SON RAI KO ZABIN IYAYE. Firdausin makarantar mu ce ta karanta mana a makaranta lokacin free period. Dake tanada waya . Kada kibi son ranki ki tawan. Kibi zab’in iyayen ki. Allah zai baki lada ya kuma sa farin ciki a rayuwar ki. Bazan mantaba a littafin yarima Aliyu yaso bijirewa iyayen sa akan ance ya auri yar uwar sa. Yak’i ya auri son ransa. Sai gashi ta zame masa masifa. Ata’kaice dai zabin iyayen da suka zabar masa Meenah sai gashi itace ta zamto wani haske acikin rayuwar su baki d’aya. Dan Allah tawan kakki bijirewa su Aunty. Allah ya zaba miki abunda yafi alkhairi a rayuwar ki, Ameen.”

Jiki a sanyaye tace,

“Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.”

Tunowa nai da wasikar da Malam Tasiu ya bani, Ciro ta nai na mika mata ina murmushi,

“Kawata karanto mana muji mai ta ‘kunsa. Malamin Literature dinnan namu ne ya bani. Wai naje gidah na karanta.”

Na karasa fada ina daria, Fadila ta karba da sauri tana warwareta, Zaro ido tayi, Hakan yasa nace,

“Karanto mana muji, Wai meyace ne? Naga kina zare idanu?”

Fadila tai murmushi kafin cikin dan daga murya tafara karanto abinda wasikar ta ‘kunsa:

_ZUWA GA MAMALLAKIYAR ZUCIA TA💞_

_FATIMATA! ZAHRA’U NAH, BATOUL! NOORAL QALB._

_ASSALAMU ALAIKI YA HABIBATY!_

_Nasan zaki yi mamakin wannan wasika tawa dama abunda ta ‘kunsa. Dan Allah kada kiyi mamaki. Domin wannan wasika zata bayyanar miki da tarin shekararren soyayya ta a gare ki. Ina fatan farin ciki zai wanzu a zuciar ki farawar karanta wannan wasika zuwa karshen ta._

_Hakika son ki ya mamaye min zucia. Son ki yayi tsamo tsamo acikin kogin rai na. Ya Habibateey ki tallafamin ki karance wasikar soyayyar nan duka._

_Na dade ina kallon taurarin samaniya yayin da naga wacce tafi kowacce haske,_

_Sai naga bakowa bace na ke gani ba sai ke masoyiyata! So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina! _

_Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar mace sai ke! Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai!_
_Yarda da amincewarki gareni sune zasu tabbatar da soyayyarki tagaskiya a gareni! Dan Allah ki tallafawa zucia ta ki karbi kokon barar soyayya ta._

_Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nake bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata! Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata, _

Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, Tare da lullu6a da qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki sai naji tamkar yanayin zafi! Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata!

_DAGA ‘KARSHE_

Ko kinsan kece abu na farko da nake
roqon samu? Wallahi ko iyalina basu kai matsayin ki a zucia ta ba. Wallahi nafi son ki akan matata. Bata min halacci. Bata kula dani, Abinci ma sai taga damar dafawa. Ki temakamin ki aure ni ki maye gurbin soyayyar da nake miki a zuciata.

_NI NE NAKI:_
_TASI’U BALA_

Tana gama karantowa ta shiga babbaka daria, Naja tsaki ina cigaba da firfita da d’ankwalin hannu na. Cikin b’acin rai nace,

“Allah ya sawwake masa, Duk namijin da baya yabon matarsa wallahi bashida hali, Sannan makaryaci ne, domin kai ma haka zai kai mata zancen ka, Wannan ai rashin adalci ne. Fisabilillah ya zaiyi da ni? Gani yake yi fa da wannan kalaman zai mallake ni ko?”

Fadila ta kad’a kai tana daria. Sai da tai mai isar ta kafin tace,

“Gaskia bai kyauta ba. Ni ya ban haushi ma. Misali ace tana yi masa hakan ma, Sirrin su ne menene dalilin sa na gaya miki?”

“Oho masa. Idan ma yana kai sunana wajen Allah In Sha ALLAH bazan zama mallakin sa ba. Allah kuma ya sakawa matar sa karyar da yake yi mata.”

“Toh Ameen dai.”

Haka dai muka cigaba da hirarra kin da suka shafe mu. Mun jima muna tattaunawa kafin na mike hade da tashin autar mu. Tayi fitsari ta wanko bakin ta da idanun ta, muka tafi gidah bayan Fadila tamana rakiya ta koma. Daga nesa na hangi Innar mu tana dawowa, Haysam a bayanta rike da leda a hannun sa. Nayi saurin juyawa kar ya hango ni.’ Amma autar mu da bata shiru ta tsalawa Innar mu kira. Hakan ya karkato da hankalin sa ya ganni. Ai kuwa ya biyo baya na. Ina gaba yana biye da ni. Nagaji na tsaya ina kauda fuska ta gefe. Nacin Haysam yayi yawa wallahi. Zuciyar sa kamar kare ya cinye, Sam baya boye soyayyar daya kemin ko a idanun waye. Ina jin sa yana wani furta sunana cikin soyayya a hankali acikin wata irin siga. Cikin turo baki gaba na amsa ciki ciki ina gaishe shi, tunawa da nai da dokar da Innar mu ta kafamin ta dole sai na dinga gaishe shi ai ba sa’ana bane.

•••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_*


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(SABON TAKU)_

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

•. •. •.

_*SHAFI NA TAKWAS_*

Ido cikin ido ya ‘kuramin idanu yana min wani irin kallo, Kasa jure wa nayi na fara matsawa dan guduwa. Saurin rik’o ‘kasan mayafi na yayi yana wani

Please Login or Register in order to submit comment