Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

marairaice fuska sai kace karamin yaro,

“Batoul! Dan Allah ki tsaya ki saurare ni.”

Allah daya hadani dashi yasa na tsaya ina ‘kwace kasan mayafi na hade da doka masa harara. Cike da bacin rai nace masa,

“Kada ka kuskura ka ‘kara tab’a min mayafi.”

“Kiyi hak’uri ki tsaya ki saurare ni dan ALLAH.”

“Ina jin ka..”

Na fada a gatsine, Domin teburin Haladu mai shayi dankare yake da samarin unguwar mu. Sai lek’owa suke suna hangen mu ciki harda mazan gidan mu, Wato su Yazeedu da Shafi’u ‘yayan Kawu ila. Nasan kuma sai sun kai masa rahoto.

“Ashe yau kun gama makaranta ko?”

“Eh”

Na bashi amsa ina lankwasa yatsun hannu na na dama. Hannun sa d’aya yasa yana shafa gemun sa. Nai murmushi kawai gemu ba gemu ba sai wani iyayi yake yi kamar wani babba. Cikin maganganu na da nake a zuci na jiyo shi yana magana,

“Allah ya sanya albarka a karatun naki. Yanzu zaki bude wata chapta din rayuwar ki. Zaki cigaba da karatu ne ko...?”

Bai karasa ba yasa hannun sa yana sosa keyar sa, Sa rai nasan kunya yake ji ya furta ko aure zanyi? Cikin nutsuwa nace dashi,

“Duk abunda ALLAH ya zabar min shi zanyi.”

“Masha Allah! Kinyi magana mai kyau Mine..”

Wai Mine sai kace wata mallakin sa, Na fada a zuci ina murmushi, Yaron nan ya gama rai na min wayo.

“Pls Batoul ki bani dama na fara zuwa zance wajen ki...”

Wata uwar harara na dankara masa ina kyakkyafta idanuwa,

“Kace me?”

“Nace ki bani dama na fara zuwa tadi wajen ki..”

“Tab Ya Haysam kenan! Ai ban isa zance ba.”

Ware idanuwa yai yana sake motsawa kusa dani. Nai baya kadan. Cikin rawar baki ya dube ni,

“Mine! Please ki tausaya min.. Wallahi na matsu.”

“Tame fa?”

Na tambaye shi ina neman ‘karin bayani.

“Ta fara zuwa zance wajen ki.. Wallahi inda akwai gaban matsuwa nayi.”

Ajiyar zuciya nai, Domin narasa ta yadda zan fito ‘karara na nuna masa ni bana ra’ayin sa. Gashi ya tsare ni da mayen kallon sa, Sai bin ilahirin jiki na yake da kallo kamar wata mutum-mutumi.

“Ya Haysam zanje gidah sauri nake yi.”

Na karasa fada ina nuna gidan mu. Murmushi yai wanda hushiryarsa ta bayyana. Ya shafa kansa kafin yace,

“Toh yaushe zanzo kenan? Saboda zan koma Cyprus ‘karo karatu, kuma..b..Banason na tafi ba tare da ‘kwakkwaran magana a tsakanin mu ba.”

Nayi murmushi kawai, Lalle zancen Fadilah dagske ne. Dak’yar na iya daga kai na dube shi kafin cikin nutsuwa nace dashi,

“Duk yadda ake ciki zaka ji abakin Fadila”

“Meyasa ba zanji a bakin ki ba uhm.. ?Batoul..!”

Ya karasa fada yana jan k’arshen kalaman sa.

“Ya Haysam bari na tafi gidah. Innar mu na jira na.”

Ina gama magana na shige gidah na barshi a tsaye batare dana bashi amsar tambayar da yai mun ba. Domin narasa ma mai zance masa. Ina leken sa ta zaure naga ya mike yayi titi hannayen sa zube acikin aljihun wandon sa na jins. Girgiza kai kawai nayi na ‘karasa shiga gidah na haye sama.

*GIDAN MATA TARA*

Usaiba matar Kawu Ishaq da Hansatu matar Kawu Dawud sune a tsakar gidan mu suna hira, Gefe kuma Innatuwa ce matar Kawu Khamis da Hajara amaryar Kawu ila wadda ke baje akan tabarma tana afka kalba a baka. Cikin ta yafuto sosai, Zata iya haife shi a kowanne lokaci. Wato haihuwa ta biyu bayan ta Basmah babbar ‘yarta. Wadda ta haifa shekaru hudu baya.

Tunda na shiga da’kinmu na kafa kofin ruwan randar mu a baki ban cire ba sai da na shanye ruwan tas. Domin ‘kishiruwa nake ji sosai. Gefe na zauna ina ajiyar zucia,

“Innar mu sannu da dawowa..”

“Sannun mu Batoul. Ya Auntyn su Fadilan?”

“Lapia lou Innar mu.”

“Haysam din ya tafi? Yaron kirki tunda ga gidan su ya dakko min ledar nan ya rako ni wallahi, Akwai hankali da nutsuwa.”

Shiru nayi ina ninke mayafi na.

“Ko baki ji mena ce ba?”

“Angode masa. Ya tafi, Yace wai zai koma ‘karatu.”

“Eh haka hajiyan su ke fada wai zai yi digiri na biyu a ‘kasar waje.”

“Eh haka yace. Muma ALLAH yabamu ikon cigaba da karatu Innar mu. Ilimi da dadi yake . Ina so naga ina koyarwa a jami’a ace na zama wata nima, Ana damawa dani a fannin ilimi.”

“Allah ya tabbar da alkhairi uwata.. Allah ya baku nasara a rayuwar ku Ameen.”

“Ameen Innar mu..”

Muka hada baki muka fada gaba d’aya harda autar mu dake zanen gidah a littafin ta.

“Innar mu mai zan dafa?”

“Ai inaga ba sai anyi abincin daren nan ba. Kinga hajiyar su Haysam ta zuba min abinci ishashshe. Har Haysam din ya riko min. Yake tambayar ki. Nace kingama makaranta yau.”

Na dubi ledar da take nuna min. Baka ce an kulle saman ta. Yanzu duk aikin da take musu ba zasu iya zuba mata ko a kwano bane sai leda? Allah ya yaye mana wannan ‘kuncin rayuwar. Allah ya kawo mana haske a cikin lamurran mu. Ameen! Yak’e nayi na zauna kusa da ita ina matsa mata kafafunta.

“Sannu Innar mu.. ALLAH dai ya nuna mana lokacin da zamu ji dadi a rayuwar mu. Allah har abun matsa kafafu zan siya miki. In sha ALLAH!”

“Ameen Uwata Ameen”

Dake wani lokacin haka take kirana saboda sunan mahaifiyar ta naci wadda ake kiranta da Fadimatu_Zahrau. Yan kwanukan wanke-wanken mu na sauka dasu. Ina wankewa autar mu na ‘dauraye wa. Cikin haka su Alawiyya da Hinde suka shigo, kowacce da ledoji a hannun ta. Sai Hauwa a bayan su tana biye dasu da wata ledar. Bintalo ta sakko a guje daga sama. Daga ita sai ‘d’aurin zani, Kanta ba dankwali, ‘kuda-kudar kwanyar diddigaggen gashin ta duk ta fito. Kawu ila ma ya fito daga dakin sa hannun sa ri’ke da bokitin da yake zama akai. Washe baki yayi yana kallon ledojin hannun su Alawiyyah. Saboda tsabagen gulma da annamimancin sa. Da kuma son cin zarafin mu a kullum shi yasa ya dena zuwa shagon sa yana zama. Sai yaro ya samu mai zama masa. Shi kuma kullum yana gida yana neman magana.

“Sannu ‘yayan albarka. Masu farin jini da dimbin alkhairi. Yau kuma me muka samu? Nan duk kayan murnar kare makarantar ne?”

Cewar Kawu ila, yana tafa hannaye sai kace mace. Bintalo sai raye raye take tana murna. Hinde ce kadai ta daga masa kai alamun Eh, Alawiyya kuwa fasa ‘kwan cingom tayi hade da zama a gefan Hansatu matar Kawu Dawood.

Gud’a Bintalo ta hauyi tana buga zanin ta. Ummita matar Kawu ila dake gefe ta karbi ledar hannun Alawiyya tana zazzage wa akan taburma. Bota ce guda d’aya sai biredi mai yanka yanka leda biyu da kwamfulas sachat babba guda d’aya. Ledar hannun Hindatu kuma kek ne na Oasis guda uku da lemon roba guda biyar. Sai ledar hannun Hauwa kuma lemon ‘bawo ne da ayaba. Yadda kukasan duniya aka kawo haka Bintalo ta dinga shewa tana goranta mana,

“Ahayye nanaye! Kaga masu farin jinin yan gida d’aya. Ga kaya nan na motsa baki na dubunnai, wasu kuwa sai dai su ciji yatsa babu masu kawowa, A hayye nanaye..”

‘Chassss’ suka hada hannaye suka tafa da Ummita matar Kawu ila domin itace aminiyar gulmar ta itada mijin ta Kawu ila.

“Tab! Gaskia sun kashe kudi, Nera tayi kuka anan yasin. Kalli kek dinnan sai gidan yan gayu ake samu.”

Kawu ila ya karasa fada yana jujjuya kek din hannun sa. Hada kayan wanke wanken mu mu kai muka fara hawa bene dasu,

“Zo nan mai idon jemagu..”

Kawu ila ya kirawo ni, kin juyawa nai domin harga Allah natsani yadda yake tankamin halitta ta.

“Zaki zo ko sai na zo na damki wuyan shegiya?”

Juyawa nai na fara sauka autar mu kuma ta haye sama harda tuntub’e. Nesa dashi na tsaya ina kallon ‘kasa.

“Bak’in ciki kike yi musu ne?”

Kamar daga sama na jiyo muryar sa, Wai bak’in ciki? Na nanata a zuciya ta. Toh mezan yi wa bakin ciki? Kayan da samarin su suka fita dasu suka siya musu ko kuma samarin nasu wanda yan gidah d’aya ne zan yi bakin ciki? Nama rasa wanne irin bakin ciki yake nufi ina yi musu. Domin gaba d’aya banga abunda zan musu bakin ciki akai ba. Sau nawa ana kawomin fiye dasu ina mayarwa wanda suka bani. Saboda ni abun hannun samari ba damu na yayi ba. Cikin maganganun da nake a zuci na sake tsinkayo muryar sa yana cemin,

“Ko dan naki samarin hannun su irin na yan dambe ne? Kullum basa miki ungo? ‘Kan’kamin na ‘kamora masu hannu kamar na yan dambe.”

Gaba d’aya yan tsakar gidan suka bushe da dariya. Nayi murmushi kawai ina girgiza kai na, Ina mamakin irin ahalin gidan mu. Domin tabbas yaci kirarin/sunan da yan unguwa ke gaya masa,

‘Gidan Mata Tara: Gidan guntsi fetsi, Ba babba ba yaro, Gidan da rashin daraja ke arha, Barbadaddu, Tsigalallu. Gidan su Ila baban Yusha’u, Su Alawiyya yayan gwal din karyar gulai Bintalo, Gidan Dan Dawooda malalaci mai macacciyar zucia. Mai kwanan daki matar Hafsatu mai neman na kai. Mace mai kamar maza kwari ne babu, Nasu Aminatu kanwar Batoulu mai kyau...’

•••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

_*SHAFI NA: TARA_*

••••

Rankwashi Kawu ila ya sakarmin a ‘kwanyar kai na. Na dafe wajen ina runtse idanu na saboda azabar rad’adin da yake min. Allah ka sakamin. Na fada a zuciata ina sake sadda kai na ‘kasa.

“Je ki. Kyallukazar kaya.!”

Na wuce sama hade da kwasar ‘yan kwanukan da muka wanke. Ina jiyo su suna gulmata hade da shewa. Ina shiga da’ki na ajiye kwanukan a ma’ajiyar su. Sannan na zauna ina zabga tagumi, Innar mu dake gefe tana zazzage abincin gidan su Haysam a filate din abincin mu ta dube ni, fuskar ta dauke da alamun tambaya,

“Ke kuma menene hakan? Ban hanaku tagumi ba?”

Cire tagumin nayi na dan muskata kusa da ita ina matsa mata k’afafuwan ta.

“Babu komai Innar mu. Su Kawu ila ne a kasa ya rankwashe ni akan su Alawiyya.”

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dube ni,

“Ko mai ya miki dan ya isa ne. Kakki manta mahaifin ku ne shima. Sai ki kokari ki dena yin abunda zai rankwashe kin.”

Daman nasan abunda zata ce kenan. Domin sai dana ayyana abunda zata fada a zucia ta. Bata taba fad’an lefin su, kullum Sai dai tace ai iyayen mu ne mu rabu dasu lapia albarkar su ta bi mu. Amman su basa ganin hakan, Rashin mutunci sala-sala suke yanka mana. Murmushi kawai nayi,

“Toh Innar mu zan dena..”

Na fada domin kawo karshen maganar tasu. Mik’ewa nai na shiga duba lungu da sako na dakin mu.

“Yaya Batoul me mike nema ne?!”

Autar mu ta tambaye ni tana bina da kallo Itada Innar mu ganin yadda na hautsina dakin gaba d’aya. Gumin daya zubo min na sharce ina daria,

“Wai ko ALLAH zai sa na gano wayar Innar mu. Wallahi zuwa akai aka dauke ta.”

“Ai kuwa dai na gayawa Innar mu nagan ta a hannun Yusha’u d’axu tace ba ita bace.”

“Wohoho biri yayi kama da mutum, Domin Yusha’u dazu dana hange shi a majalisar su dauke kai yayi yana sosa keya. Innar mu dan Allah ki kyaleni naje na karbo miki wannan wacce irin sata ce. ?“

“Uhm uhm dai! Da kika fada me nace miki Auta?”

“Ca ki kai ba taki bace ai ba kekadai kamfanin wayar su kayiwa ba.”

“Yauwa banason neman rigima. Idan shi ya d’auka ma yaje na bashi. Da nasan zan samu ne?”

Girgiza kai nayi ina kwafa. Na rasa wacce irin zucia ce da Innar mu. Sam bata bari wata ‘baraka ta shiga tsakanin mu da yan gidan mu. Koda kuwa hakan zai janyo mana bacin rai su ya faranta musu. Ita kullun dai burin ta bai wuce taga zumunci ya wanzu a tsakani ba sam batasan husuma ko kadan. Jiki a sanyaye na koma na zauna a gefan randar mu. Har cikin dakin mu ya shigo ya sace wayar Innar mu. Shi yasa nake so ALLAH ya hore min na sai mana kwado muma mu dinga kulle k’ofar mu. Ina cikin zancen zuci na jiyo Innar mu nace min,

“Wanko hannun ki kuci abincin Uwata.”

“Toh Innar mu.”

Na fada ina wanke hannu na a gefan tukunyar kusa da randar mu. Shinkafa da miya ne da kafafun kaza guda biyu da kai d’aya. Sai kamshin tafarnuwa ne tashi a miyar, Kallo d’aya za kai mata kasan miyar gidan yan gayu ce. Bismillah mu kayi sannan muka fara ci. Har wani lumshe idanuwa autar mu keyi tana kada hannayen ta cikin dadi. Rabon mu da irin cimar nan har mun manta. Domin sai sallah ko kuma gidan biki ko idan mun kai ziyara kaduna gidan Gwaggo Aminatu. Kan kace me? Har mun tashi da abincin nan. Innar mu ta bar mana kai da kafafuwan. K’afa d’aya na dauka na taune na barwa autar mu sauran,

“Alhamdulillah!”

Na fada ina shafa ciki na, Innar mu tayi murmushi tana tattare shinkafar data zubar a gaban ta. Harhada kwanukan da suka ba’ci nai na sauka kasa dasu. Wanke su nai tas na koma sama abuna. Lokaci zuwa lokaci mu kan taba hira da Innar mu. Domin kullum cikin lazumi take. Wani littafin hausa mai suna duk kyan takalmi na dauka na fara karantawa, Littafin kwarai yayi dadi. Inason yadda rayuwar Aisha-Farida take itada Dr Shureim. Dake ba sallah nake ba haka na wuni ina karantawa har bayan magrib.

Cikin daga murya na jiyo wasu yara na magana suna ambaton suna na. Ta sama na leka ina kallon yaran. Su uku ne kowanne hannun sa dauke da ledoji shake da kaya a ciki. Daki na koma ina sanarawa Innar mu,

“Innar mu kinji an aiko wasu yara guri na.”

“Toh je ki ji menene? Allah yasa alkhairi ne.”

“Ameen!”

Na fada ina zura hijabi na. K’asan na sauka, dandazon yan gidan mu kowa ya fito ciki harda Bintalo da ta tasa yaran agaba tana tanbayar su,

“Anya kun tabbata wajen ta aka aiko ku? Ko dai ca akace muku Alawiyyah ko Hinde?”

Yaran suka ka’da kai alamun a’a. Na biyun wanda ya fisu dan tasawa yace,

“Aa mu dai ca akai mana mu bawa Batoul din Innar mu.”

Bintalo tasa hannu a kirji tana zare idanuwa. Kawu ila yafuto daga bandaki yana baje idanuwa,

“Kai su waye wannan?”

“Toh ga su dai wani ne ya aiko su, A k’aryar su dai sunce wajen shegiyar yarinyar nan ne.”

“Kai waye ya aiko ku?!”

“Ca yai muce gashi inji Haysam.”

“Waye haysam?”

Kawu ila ya fada yana dora hannayen sa a kugu. Bokitin zaman sa na gefan sa. Bintalo taja k’wafa tana girgiza kai,

“Haysam dan gidan Alhaji Kabeer Wafa, Sittin ta ubangiji akwai wani abu a kasa, Domin acan Kaltume ke aikatau.”

Usaiba matar Kawu Ishaq dake sama ta sakko tana tafa hannaye harda rawa, Domin tasu ba tazo d’aya da Bintalo ba. Ledojin ta karba daga hannun yaran tana taka rawa,

“Kuce masa angode ALLAH yayi albarka.”

Ta karasa fada tana mika musu nera ashirin data ciro a gefan zanin ta. Bintalo taja tsaki tana matsawa gefe, Kawu ila kuma ya shiga daga wuya yana zare idanuwa dan hango abubuwan da aka kawo min. Ni dai na tsakure a gefe na zabga tagumi. Rayuwar gidan mu na bani mamaki wallahi, Na rasa a wane hali nake ciki, shin fari ne ko baki oho?. D’aya daga cikin yaran da aka aiko ne ya dawo da sauri,

“Wai ana sallama da Batoul..”

“Aiyiriririrururuuuuu! A hayye Nanaye! Masu abu da abunsu! Kaga wa’enda su kai gadon abun arziki, Kaga wa’enda kuttin farin jini ya fashewa, Kaga wa’enda ake zuwa har gidah a aiko musu da cimar ‘yayan manya. Kaga masu daraja, Kai Kai Kai shagali! A hayye sama ruwa kasa ruwa.. Kaje kace gatanan zuwa yanzu.”

Cewar Usaiba, Tana fada tana rausaya wa, Duk dan saboda Bintalo. Rai na a turnube na fita ina jan hijabi na ya rufe min hanci. Har ga Allah banso baba Usaiba ta karbi kayan can ba. Domin bana karbar abun hannun saurayi, saurayin ma Haysam wanda rai na yafi tsana aciki. Ciki ciki na gaishe shi ina juyar da fuska ta. Muna tsaye ne a zauren gidan mu. Ina kallon yaran gidan mu na leken mu, Zasu Kai wa iyayen su tsegumi.

Sanye yake cikin shadda kalar sararin samaniya, Ta sha turarren aiki kalar kayan, Yasa takalmi da hula duk kalar aikin jikin rigar sa, Kamshi sai tashi yake a jikin sa. Hasken wutar injin teburin Haladu Mai Shayi ne ya haskaka shi, Mu kai ido biyu dashi, Gaba d’aya ya tattara hankalin sa da nutsuwar sa a kai na yana karemin kallo. Mayen kallon sa ne ya karasawa na tsane shi. Na tsani yawan kallo a rayuwata. Domin babu kyau ko a musulunci. Baki na tabe ganin bai amsa gaisuwar sa ba, Ko bai jiba oho? Na sake cuno baki gaba,

“Ina yini?”

“Alhamdulillah Mine! Kina lapia?”

“Gashi kuwa ka ganni.”

Dan murmushi yai mai sauti yana shafa sajen sa, Na saci kallon sa ta gefan ido, Sai wani bokarewa yake yi kamar wani babba. Cikin wani irin salo ya amsa ni,

“Naji dadin kasancewa ta dake yau dinnan. Batoul! Pls ki jiyo ki saurare ni.”

“Kunne ke ji, Ina jin ka.”

“Ya batun d’axu? Shin kin aminta na fara zuwa zancen?”

Ajiyar zucia na sauke, Na dan ja hijabi na kasa ina wasa da yatsun hannu na. A tsaye muke yana kallon gabas ina kallon yamma, Amman lokaci zuwa lokaci na kan dan juya na saci kallon sa.

“Kayi hak’uri Ya Haysam. Gaskia yanzu dai bazan fara zance ba, Kaga yau ne fa na gama makaranta. Ina bukatar tunanin me zanyi a gaba.”

Shima ajiyar zuciar ya sauke. Duk kuwa da nasan tasa ta damuwa ce. Cikin marairaicewar murya kamar zai yi kuka yace,

“Dan Allah ki sasssauta min Mine! Ki bari manyan ki su san da ni. Kar kiyi *ZATON* da shiririta nazo, Ni wallahi da aure nake neman ki Mine. Dan Allah ki dai duba.”

“Shikenan duk yadda ake ciki dai zaka ji daga bakin Fadilah In Sha Allah.”

“Meyasa sai a bakin Fadilah? Uhm! Mine? Meyasa?”

Murmushi nai, Yaron nan yana bani daria, Sai wani lankwashe murya yake yi. Shi fa ganin sa yake matashi mai jini a jika ko? Kofa rabin hamsin beyi ba (25) Dududu fa shekarun sa 23 kila ma bai cika ba. Amma wai neman aure na yazo yi. Na tabe baki ina sake ‘kurawa bango ido. Domin juyawa nai bangon gaba d’aya saboda nagaji da nacin kallon sa. Dan iska. Na fada ina zura hannu na na daga hijabi na daga saman kirji na dan karya kwanta ya kalle min na ALLAH ya isa. Sake jiyo shi nai yana narkar da murya,

“Mine! Pls kiyi magana ko zucia ta zata samu sassauci.”

“Dankari!”

Na fada a hankali, Dan satar kallon sa nai, Hannun sa rike da mukullin motar sa,

“Ya Haysam kayi hak’uri zakaji daga bakin ta, Sannan dan Allah ka dakata na dakko kayan can daka bayar aka kawo min.”

“Wai meyasa bakya karbar abun hannu na? Tsanar har ta kai haka?”

Saurin girgiza kai nayi,

“Aa wallahi! Ba haka bane. Kawai dai bana amsar abun hannun samari ne”

“Toh ki fara a kai na, Ai ni yayan ki ne. Ki dauka tamkar Najibu ne ya baki. Kyauta ce na murnar kammala karatun ki. Na roke ki da ALLAH kar ki mai do da hannun kyauta baya kinji ko?”

“Shikenan Nagode! Amma kayan sunyi yawa ne bandai duba ba, amman naga ledoji da yawa.”

“Kai haba! Tarkace ne kawai. Amma akwai yar karamar waya wadda nake so mu dinga magana. Nasa layi da komai. Dan Allah dan Allah kar ki ce bakyaso. Dan Allah”

“Shikenan! Ka rigada ka hadani da ALLAH kaga bazan ki ba. Nagode Allah ya kara bud’i. Allah ya saka da alkhairi.”

“Ameen! Allah kuma ya bani ke a matsayin matata. Ameen”

‘Ba Ameen ba In Sha Allah’

Na fada a zuciata ina yak’e a fili. Agogon sa ya kalla kafin ya dube ni.

“Toh zan gudu Mine! Congratulations once again. Allah yabada nasara a rayuwa.”

“Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum! Nagode sosai Ya Haysam.”

Sallama mu kai ya fice ni kuma na shige gidah. ‘Yayan gidan mu dake labe suka shige da sauri nai murmushi kawai ina tuno d’aya daga cikin kirarin gidan mu. Gidan Mata Tara: Gidan guntsu fetsi. Ba babba ba yaro. Gidan da daraja ke arha, Tarbiyya tai karanci.

******
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan, KAFIN A FARA KAFTA WASAN🙌🏻❤️💋


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

_*SHAFI NA GOMA_*

Ina shiga na tarar Usaiba tayi ‘dai-dai da kayan ledojin tana fadar sunayen wa’enda tasani. Himilin yan gidan mu kuwa kowa ya zuro kayuwa yana kalla, Wasu ta d’akunan su, wasu ta sama wasu kuma ‘yayan su suka aiko. Wucewa nai zan hanye sama Usaiba ta janyo ni tadawo dani kusa da ita,

“Tsaya ki kallon kayan ki ‘yarnan. Anci uban nera yasin. Yayi gwarzon kokari wannan saurayi naki. Kutsin uban chan kayya kai. Dubi kaya ahayyye.”

Ni de murmushi nai ina mai da kai na gefe. Usaiba kuwa ta shiga daga kayan nan tana fadan sunan kowanne yadda kukasan kayan lefe. Bintalo na gefe hannunta a baki tana ciza. Su Alawiyya kuwa sai cika suke suna batsewa.

“Ledar farko mayukan shafawa ne da turaruka masu kamshi da tsada. Leda ta biyu kiret din kwai ne guda biyar. Leda ta uku chakulats ne masu tsada gasu nan kuna gani. Leda ta hudu atamfofi ne guda uku da mayafi d’aya. Leda ta biyar kuwa lemukan kwali ne gasunan da biskit masu tsada suma a kwalin su. Ledar karshe kuma kaji ne masu tashin kamshi. Kutsin uban can kayya kai harda wayar tarho ta salula... Ayirrrruruuuuu.’

Usaiba ta karasa fada tana sakin guda. Gaba d’aya gidan mu ya kacame da magana. Harda yayan makota da suka shigo gulma. Usaiba ta shiga sakin guda a karo na ba adadi. Sai da tayi mai isarta tukun sannan ta janyo hannu na tana mikamin ledojin,

“Rike yarinyar arziki, Mai farin jinin samarin gidan manya. An buga dake anbar ki ya zasuyi dake. Dole aganki kuma a bar ki yarnan. Ledoji shida rigis aka kawo miki ‘yar nan. Kowanne yaro hannun sa leda biyu ya dakko, Idan aka hada da ta yar karamar wayar ki ma ta kama bakwai kenan. A hayyyye kayya kai..”

Murmushi nai, Baba Usaiba na bani daria kwarai duk sanda ta fadi kalaman ta na kullum wai kutsin uban can kayya kai. Mik’ewa nayi ni dai na haye sama abuna. Ai kuwa tatas ta tattare ledojin ta hayo min dasu itada ‘yayanta Larai da Talatuwa. Uffan ba wanda yace domin kowa shakkarta yake. Ciki harda Kawu ila bata raga masa. Kayan suka kai gaban Innar mu dake kara rediyo a kunnen ta tanaji, Sakamakon batirin da yai sanyi bata kara, Allah ka horemin na siyawa Innar mu sabbin batiran rediyo da kwadon kulle kofa. Na fada a zucia ta ina sauke ajiyar zuciya.

“Kaltume, Ajiye rediyo ki kallon kayan abun arziki...”

Innar mu ta

Please Login or Register in order to submit comment