Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TO DAUTA *BILLY S FARI*💝💖_
_*GRATITUDE GOES TO: YA HAJJAH CE💖💝_*


*NIGERIA*

*KADUNA*

Mun sauka kasar haihuwar mu lafiya, haka kawai na tsinci kaina cikin wani irin farin ciki da nishadi, duk da banajin dadi haka naita aro kwarin gwiwa ina dorama kaina. Sosai tarbar da muka samu daga family' din Mubeen ta bani mamaki, sai kace gwamna dinne da kansa yay tafiya akazo tararsa. Kunyar duniya ta dabaibayeni saboda rikon da Mubeen yaymin, nayi-nayi duk dabarar da zanyi ya sakeni amma ko gezau baiyiba har jannat ta karaso ta rungumemu gaba dayanmu.

Yanzu kam kwace hannuna nai da iyakar karfina daga cikin nasa saboda karasowar Mamma Ahlaam wajen itama fuskarta washe da fara'a tana mana lale.Ta janye Jannat daga jikina tana fadin,

“Ki saketa taji da kanta shugabar rawar kai”..

Murmushi kawai nayi ina risinawa da na gaisheta, dan ban fahimci ma'anar maganar tataba.Itama ta riko hannuna fuskarta na sake fadada murmushi na musamman, ta amsa min da dunbin kulawar da tafi ta da canma.

Sai faman sunkuyar da kai nake nidai, ta kai dubanta ga Mubeen daya tsume waje guda yana kumbura fuska. Karamar dariya ta masa, hakan yasani kallon inda yake, hararata yayi, niko namasa gwalo. Sosai yanzu kam Mammah ke dariya, dan duk taga abinda mukayi. Tace,

“Muhammad ya kamata dai idan an girma asan an girma, kazama Daddy fa yanzu”.

Babu shiri yay dariya, yayinda ni kuma nai mamakin furucinta sosai, tambayar daya jeho matace ta katse tunanina..

“Mammah Daddy kuma? An taba zama Uba babu da?”.

Kallona tai tana sake fadada murmushinta na dattako da cikar kamala, sai kuma ta dauke kanta tare da jan hannuna kawai. Sosai ta sake daure mana kai, sai dai rufuwar da jama'a yan sannu da zuwa da sukai a kanmu ya mantar damu wancan batun.

Mun dunguma zuwa gidan gwamnati baki dayanmu, inda muka tarar da liyafar cin abinci ta musamman da aka shirya mana. Papa dai baya nan, yana Abuja wajen wani taron gwamnoni. Mamma ta bamu umarnin zuwa mu watsa ruwa kafin a kammala shirya sauran abincin, da sauri nai gaba saboda banason Mubeen ya takurani. Harko na shige dakina baima tahoba, dama na bar shi yana magana da wani saurayi dan family din nasu da bai wuce sa'ansa ba, da alama dai abokinsane na kusama kuwa.

Ina wanka najiyo bugun kofa, nasan shine sarai, daya gaji sai ya daina naji Shiru. A tsanake nai shirina bayan na fito, sai dai jikina wani irin daukar zafi yake. Hakan ya sakani saurin kashe ac sannan nai shiri cikin doguwar riga ruwan makuba. Kasancewar haske da fatata ta kara da gogewane ya saka rigar min bala'in kyau, ni kaina sai sake duban kaina nake da karawa a mirror. Nayi mamakin harna kammala kimtsawa na fito banji motsin Mubeen ba, shidin nan dana sani da masifaffen naci akan abu. Zama nayi ban fitaba, ina jiran zuwansa mu koma tare, dan nasan sai ya dawo.

Sosai mamaki ya fara riskata ganin na shanye kusan mintuna talatin babu Mubeen babu dalilinsa, na dai daure wata minti goman ta sake shigewa suka zana arba'in, zuwa yanzunkam na fara tunanin lafiya?. Zaman mintuna uku na kara nanma dai shiru, ina kokarin mikewa da son zuwa na duba sai naji anyi knocking. Ajiyar zuciya na sauke tare dajin wata nutsuwar da bansan daliliba. Mikewa nai naje na bude kofar yana dan daure fuskata, sai dai ina budewa naci karo da abinda bashi nai hasasheba. Jannat ce tana min murmushi, nima na maida mata murtani cikin danne abinda yake son tasomin.

“Aunty Bee Mammah ce tace na kiraki, tun dazun ya MM ya fita amma ke babuke, ta tambaye shi yace kina zuwa kema, kusan mintuna ashirin kenan kuma munji shiru”.

Mamaki ne mai yawa ya ziyarci raina, dan ban fahimci dalilin Mubeen na aikata hakanba kai tsaye, na danne zuciyata ina murmushin yake,

“Eh Jannat Ina dan karasa abune, amma nagama dama tahowa zanyi, kinga muje kawai”.

Batace komaiba sai gyadan kai da tayi tana murmushi, tai gaba nabi bayanta. Koda muka iso falon abin mamaki Mubeen ko inda nake bai kallaba, hasalima ya dauke kansa ya maida ga abokinsa dana gansu tare dazun. Daure raina nai ban kawo komaiba, na zauna inda Mammah ta nunamin ina murmushin yake. Da alama dama nikadai ake jira, dan ina zuwa akai bismilla kowa ya fara dibar abinda yakeso. Har lokacin Mubeen bai kalleniba, zuwa yanzu kuma nasan yasan nazo wajen, tunda a cikin yan uwansa harda masu tsokanata wai nakara kiba da haske, kodai kodai?.

Babu wanda na bama amsa sai murmushi, dan yanayin Mubeen din yaso tsayan a rai, karan farko a rayuwata danaji wani abu mai kama da tsoro tattare da Mubeen, dan wannan ne karan farkon daya nunamin halin ko in kula.Daurewa nai na dauke kaina nima, na zuba dambun cous-cous kawai kadan na fara ci, dan duk yawan abincin wajen babu wanda ya kwantamin arai, wasuma idan na kallesu tashin zuciya suke sakani. Ina lura da Mamma duk motsina idanunta na kaina, sai dai batacewa komai. Ban kuma shiga damuwaba sai da har muka kammala cin abincin nan banga idan Mubeen ako gefen da nakeba, zazzabin danaji yana neman kadani kasa yasani cewa zanje na huta. Mammah tace,

“dama yanzu nakeson cewa kije ki hutan, dan na lura bakyajin dadin jikinki daughter ”.

Bance komaiba sai murmushi kawai, ta lallame nk na tafi, abinda ya kuma daure kaina Mubeen na kusa damune, kuma sarai na fahimci yaji duk abinda muka tattauna amma yayi kunnen uwar shegu damu. Kafa babu kwari na nufi sashenmu, na kwanta tare da shigewa cikin bargo mai nauyi saboda yanda nakejin kasusuwana na kwankwatsar zazzabi .Babu jimawa barci mai nauyi ya daukeni, ban sake sanin hidimar da akeba.

Motsin bubbuga filon da nake kaine ya sakani bude idona da kyar, a mamakina sai naga Mubeen tsaye a kaina tamkar wani soja, fuskarsa daure tamau fiyema da dazun, hakan da bai saba minba ne ya sakani jin wani tsoro da dunbin shakkarsa, na maida idona zan sake lumshewa yayi magana a kausashe.

“Ki tashi kiyi salla lokaci zai kure”.

Sosai zuciyata ta wani tsinke, dan bansan Mubeen da wannan muryarba, sai kawai na tsinci kaina da tashi zaune cikin hanzari. Dauke kansa yayk kamar bai fahimceni ba, na kafeshi da idanu bakina fal tambayoyi, sai dai yanayin fuskarsa ya hanani furtawa.Mikewa nai zuwa bandaki ina tangadi, nayi tunanin zaice zai taimakamin kamar yanda ya saba, amma sai naga yama dauke tamkar baisan inayi ba. Harna fito na gabatar da sallolin yana wajen zaune idonsa a tv yana kallon film, daurewa nai bayan nayi addu'a na maida hankalina gareshi.

“Mubeen lafiya wai?”.

Banza yaymin tamkar bazai tankaba, sai kusan minti biyu yace,

“Lau” daga haka yayi shiru.

Sosai amsar daya bani ta min zafi, sai nima na dauka aniyar share shikawai, dan nikam bazan juri wulakanciba, tunda nasan babu abinda nai masa balle yace.

••X••O••X••O••

*Kamar da wasa* sai karamar magana ta zama babba, dan kwanakinmu hudu da dawowa nigeria kenan, tsakanina da Mubeen kuwa babu wani canji, saima zafi da abin ya kara dauka, dan nima nahau dokin zuciya na watsar da lamarinsa, sai dai a gefe zuciyata na azabtuwa ainun. Dan bansan shakuwar danai da Mubeen har takai haka girmaba, duk yanda nake dokance dason zuwa Zaria naga ahalina sai wannan bacin ran ya shanyesa duk, ga rashin isashshiyar lafiya dana gaza fahimtar ta meye?.

Papa ma tun washe garin dawowarmu ya dawo daga abuja, ya nuna murnarsa da dawowarmu sosai, harma murnar tasa taso bani mamaki. Dukda kulawar dana rasa wajrn Mubeen a tsakanin nan ina samunta Mammah sai hakan baisa zuciyata nutsuwaba, ban taba tunanin Mubeen nada zafi irin hakaba, gashi a gaban iyayensa nunawa yake bamu da wata matsala, amma damun kebe ko kallo ban ishesaba, ya raba mana makwanci, tunda muka dawo kowa dakinsa yake kwana, idan ka ganshi a dakina sai dai yazo tashi na salla, saboda mayen baccin da nake faman yi yanzu, ya raba mana kwanon abinci.

Tun ina bashi laifi da daukar abin wulakanci irin na maza da ake fadamin har dai na fara zaman binciken laifin danai masa, ban gano komaiba, hasalima nidai a sanina ban masa komaiba. Nai kokarin hadiye abinda yazo ya tokare kirjina amma na kasa, sai ma sake tasomin yake yana kuma taruwarmin, Idanu na lumshe wasu zafafan hawaye suka gangaro saman kumatuna, tabbas inason Mubeen, ban kuma tabbatar da hakanba sai yanzu daya nisanta kansa dani, so nake masa maiban mamaki, mai nanewa a zuciya da babu abinda ke girgizashi, ga wata shakkarsa da nakeji a yanzu, duk yanda na shirya fada masa bakaken magana bana iyawa idan ya shigo, daren jiya har dakinsa na nufa da shirin fada masa ya bani takardata na kara gaba, dan bazan dauki wulakanciba, sai dai inazuwa kofar dakin gabana ya shiga faduwa, wani dunbin tsoro da fargaba suka mamayeni, nai tsaye kasake a wajen inaji tamkar kafafuna bazasu iya daukataba.

Kamshin turarensa ne ya sakani dawowa hankalina, na dago idona da sukai min nauyi, sai naci karo dashi kwance a falo yana waya, muka hada ido, amma sai ya dauke tamkar baima ganniba, yama mike daga falon ya nufo inda nake, sai dai ko kallona baiyiba yazo ya shige dakinsa ya rufo kofar harda murza key. Wasu zafafan hawaye naji a lokacin, na nufi daki da gudu ina kuka, da wannan abun na kwana a rai, nakuma tashi dashi, shine har yanzun bai fadaminba yaymin cak a kahon xuciya. Ga zazzabi da ciwon kai da sukaimin rijib..

Jin yawaitar kamshinsa a dakin ya sakani dagowa, tsaye yake jingine da kofa hannayensa harde a kirjinsa, fuskarnan a murtike tamkar ba Mubeen dana saniba, sai naga yamin yar rama ya kuma kara haske. Samun kaina da rissinar da kai nayi, dan haka kawai naji yamin kwarjini da cika idanu. Mun dauki kusan mintuna biyar a haka kafin najiyo sautin takunsa zuwa gareni, gabana ya sake zuwa ya tsaya, muryarsa a daje yace,

“Fateemah kinfi karfin kiwa mutum laifi ki fahimci kuskurenki ko? Ni har yanzu zuciyata ta gaza daukar irin girman da kikeji kina dashi, koda shekaruna goma a duniya kinada saba’in nidinne dai mijinki, lokaci yayi da zamu ajiye batun shiririta da shirme mu dauki gaskiya mu yafa a dukkanin zukatanmu, tabbas ni mutumne da idan naso abu bana masa daukar wasa, hakama idan na kishi, sai dai na gaza fahimtar aibuna a gareki sam, wane sharuddane na cikakken namiji ni Muhammad Mubeen ban cikaba da har yanzu zuciyarki ta kasa darattani matsayin miji? Dan kawai kina malamata a makaranta sai akace miki karki bani darajata? Bance dole ki so niba, dan soyayyar da nake miki kawai ta isheni jagorantar rayuwar aurenmu har karshen numfashina, bakuma zance miki bana bukatar soyayyarki, dan duk wanda yaso yana bukatar shima a soshi, ki zauna kiyi tunani da iliminki da tarbiyyarki, idan kinga dukkan mizanin dakika dorani dai-daine saimu cigaba da tafiya a haka, idan kuna kin fahimci da kuskure zaki iya bama kanki zabi, abu na karshe dazan fada miki kawai shine na tsani raini!”.

Yanda ya karasa maganar a kausashene ya kuma tsinka zuciyata, kirjina yay wani irin zallo nai firgigit alamun tsorata da lamarinsa, baiko kalleniba ya juya ya fita yanajan tsaki mai karfin da bantaba cin karo daga gare shi ba. Samun kaina kawai nai da fashewa da kuka mai cin rai da bansan dalilinsaba, nasan tabbas dukkan abinda ya fada gaskiyane a gareni, kuma na amsa laifina, saidai na kasa fahimtar tushen laifin nawa har yanzu, tunda nasan lafiya lau muka sauka har zuwa gida, siraran hawaye suka kara ziraromin, na zame na kwanta a gadon ina yin wani kuka mai cin rai. Tabbas ina bukatar shawara, to amma wazan budema cikina da wataran bazai ci amanata ba? Wazan bama kofar sanin matsalar da ni nasan nice na kirkirarma kaina ita, Innar mu takance ciki ba'a yi shi dan cin abinciba kawai ai, hawayen da suka sake silalomin na goge, sai kuma nasihar Gwaggo da Innar mu ta shiga dawomin cikin zuciya daki-daki.

Lallai Mubeen bai cancanci hakan daga gareniba, koda kaunar da yake nunamin yakamata na amshe shi matsayin miji mai daraja da kima a gareni, yakamata na karbi wannan kyautar da UBANGIJI yayimun , bai kamata na bijireba na butulce, tunran ginifa tun ran zane, kaddarata da auren Mubeen rubutaccene tunkan zuwana duniya, why nake kokarin nunama ubangiji tamkar ya kuskuremin? Lallai akwai sharrin shaidan ma'abocin sakama zuciyoyi munanan abubuwa a cikin ayyukana, akwai rashin godiyar ALLAH da runtse idanu daga gaskiya tattare dani, musamman idan na tuna a gidan dana fito da rayuwar dana taso a ciki, amma sai ubangiji ya sakankamin da Mubeen matsayin mijin aurena, Meyasa na gaza koyi da Nana Khadijatu mace mafi daraja a cikin mata, ta kasance matar MANZON ALLAH SAW dukda ta girme shi, sannan a karkashin ta yake a harkar kasuwanci, amma daya kasance mijinta sai tazama mai biyayya a gareshi, ta sake girmama girman darajarsa fiye da komanta, hakan yana nuna ba shekaru bane aure, shekaru basu da wani muhimmanci ko dalili ga mace wajen daraja mijinta, lallai nayi kuskure, na kasance mai kuskure da bazan iya yafema kainaba harsai na gyarasu..

Tamkar an tsikareni na mike, jikina har rawa yake wajen kokarin cimma dakin Mubeen, na tura kofarsa cikin sassarfa na shiga babu ko sallama, baya a dakin, sai dai motsin ruwa da naji ya tabbatarmin wanka yake. Kasa zama nayi, nai tsaye daga bakin kofa ina rarraba idanu tamkar dan akuya a gaban sarkin fawa. Ya dau dogon lokacin da har ya kamata ace nagaji da tsaiwa bai fitoba, sai dai dunbin damuwar da na tsinci kaina da farkawa a mummunan barcin daya danne fahimtata yasa banji gajiya ko damuwa da tsaiwar, na sake mannewa da kofa saboda jin hajijiyar dake neman yaddani saboda rashin jin kwarin jiki, a haka na riski karar bude kofar toilet,

Mubeen daya fito daure da karamin towel a kugu ya sauke idanunsa akan Batoul, dauke kansa yay tamkar bai gantaba, dukda kuwa ganin nata ya saukar masa da wani yanayi, amma saiya danne kamar yanda yake kokarin yi a tsakanin nan. Yanda yaymin din ne ya sake karya zuciyata, na durkushe kasa saboda rawar da kafafuna kemin, cikin dasasshiyar muryata na fara magana,

“Nasan ni mai laifice a wajen ALLAH ma bakai kadaiba, sannan mai laifice ga iyayena kansu, na kasa amsar kaddarata da hannu biyu, na kasa fahimtar baiwar samunka da ALLAH ya bani matsayin shugaba, na watsar da tarbbiyar da mahaifana suka bani saboda wani banzan tunanina mara tushe, dan ALLAH mijina ka gafarceni, hakan ne kawai zai bani kwarin gwiwar gyara kurakuraina har a wajen ubangiji na, idan har baka yafeminba nima bazan yafewa kainaba, aure bautar ALLAH ne, sannan ya sanya mazaje su zama shugabanni ga mata komai yawan shekarunsu ko girman mulkinsu ko dukiya, badan ya kaskantar damu yayi hakanba, domin shi mai hikimar masu hikimane, sannan mai rahamane da jinkai, nayi alkawarin gyara kuskurena, nayi alkawarin yin koyi da Nana Khadijah, nayi alkawarin yin koyi da mahaifiyata, zan cigaba da neman tsarin ALLAH daga shaidan mai sanya wasiwasi a zuciyata akan dabi'un daba nawaba, dan ALLAH kace ka yafemin mijina koda bazaka cigaba da sona kamar da ba, a yanzu ba soyayya nafi bukataba, cika ka'idojin bautar ALLAH nakesonyi Mube.....”

Sai kuma ta kasa karasawa ta fashe da kuka mai cin rai ga ma'abocin saurarenta. Cikin sassarfa Mubeen dake tsaye tamkar gunki yana kallonta tunda ta fara magana ya karaso, shima durkushewa yayk a gabanta yay azamar jawota jikinsa ganin tana shirin kaiwa kasa, tsam ya rungumeta tamkar zai maidata cikin tsokarsa ta gauraye da jininsa ya maida ya dinke.

Cikin wata murya mai sanyi da rauni yace,

“I love you so much Fateemah na! dan ALLAH kibar kuka, ina sonki ina kaunarki, ina miki son da bantaba yiwa wata halitta kwatankwacinsaba, kece mace ta farko datafi kowacce mace kima a idona bayan mahaifiyata, nagodema Allah da kika fahimci kuskurenki da wuri, na gidema Allah dayasa na zama ma hakuri akan komanki, Fateemah na dan Allah ki soni, kice kina sona koda kashi dayane a cikin dari nason da nake miki a zuciyata, zuciyata takanyi tamkar zata bude saboda kaunarki Fateemah, ban tabama abu so mai azabar zafiba kamar yanda nake miki, har mamakin kaina nake Fateemah, dan Allah ki tallafi lamarina, ki rungume zuciyata taji dumin yar uwarta, kimin kallon miji mai daraja tamkar yanda naga Mammah nawa papa na tunda na taso na mallaki hankalina....”

Kankame shi tai sosai itama har kirjinta na zafi saboda matsesun da tayi a faffadan kirjinsa, taso dan sassautawa amma saiya sake matseta shima, sai da yaji numfashinta na fita da nishi sannan ya sassauta mata.Tace,

“Ina sonka sosai hubby na, so irin na har karshen rayuw......”

Wata zabura yayi mai ban mamaki da tu'ajjibi, ya dagota babu shiri jikinsa na wani irin rawa, a mamakin Batoul da itama ta dago tana kallonsa sai taga kawai yana hawaye, tadan zaro idanu dakai hannu saman fuskarsa ta dangwali hawayen, duk da itama nata basubar zubaba kuwa. Cikin rawar murya tace,

“kuka fa Mub....”

Kasa karasa sunan tayi, dan bala'in jin nauyinsa take akan harshenta. Hakan da Mubeen ya fahimtane ya sakashi yin murmushi yana jawota jikinsa ya hade bakinsu waje guda. Karon farko a tarihin aurensu da Batoul tazoma Mubeen da sabon salon hadinkai, tuni ya gigice ya dauketa sukai kan gado, dan baiyi zatoba sam.....

Dolene Mubeen ya saka wannan ranar cikin jerin ranakun tarihinsa a duniya, rana ta musamman da ko daren farkonsu bai isa nuna mata yatsaba, a yau gaba daya dan kallo ya zama a filin yakin, Batoul ce ta hada rundunar da makaman kuma ta yaki arnan. Sai faman boye fuskarta take a jikinsa, dan ita kanta kunyar kanta takeji a yau dinnan, ya saki murmushi tare da shafa lallausar suman kanta kafin yakai baki ya sumbata yana furta,

“I love you fikre”.

Cikin cusa kanta a kirjinsa itama tace,

“ Nima I love you so much! Stud muffin dina”.

Jiyake tamkar ba Batoul dinsaba, tamkar an canja masa ita baki daya, ashe wannan ranar zatazo? Ashe dai shima namijine? Ashe dai shima karansa yakai tsaiko?. Haka yayta kullawa da kwancewa har yafara jiyo saukar fitar numfashin Batoul a kirjinsa a hankali, mamaki ya kara kama shi, sam barcu baya mata wahala yanzu, data rufe idone kotaji dumin jikinsa zakaji tafara shi, sai tausayinta ya kamashi, a kwanaki takwas dinnan ko yaya tayi da rashinsa? lallai sai ya hukunta kansa dan ya azabarta dasu baki daya, shi kansa fadar halin daya shigama bata lokacine a tsakaninan, daurewa kawai yake domin son gyara gidansa, dan masu iya magana kance icce tun yana danye ake tankwarashi, idan ya bushe kuwa akace za'ai karyewa zaiyi, shiyyasa yayi wuff ya tankwara nasa kar wankin hula ya kai shi dare, Gashi kuwa ya samo nasara mai ban mamaki da ajiye tarihi.

Dakyar ya iya zare jikinsa yaje yayi wanka, a toilet dinma haka ya kasance cikin sambatu, ya fito a gurguje yayi shiri dan abokinsa kuma dan uwansa ke jiransa zasuje wani waje mai muhimmanci, badan yayi alkawariba da babu abinda zai sakashi fita a wannan lokacin. Bayan ya fito yayi shiri ya rankwafa yaiwa Batoul sunba kusan biyar a fuska, kafin ya dauki takarda da biro yai rubutu ya ajiye mata saman mirror, harya fice yana waiwayenta, jiyake kamar yadawo yace ya fasa, sai dai bayason zama cikin mutane masu raunin cika alkawari.

•X•O•X•O

Kusan baccin awa hudu Batoul tayi, sai gab da magriba ta tashi dakyar, tayi mamakin rashin ganin Mubeen, cikin tangadi dana zafin zazzafi ta nufi toilet, wanka tayi da ruwan dumi ta tsarkake jikinta, ta fito dakyar zuwa dakinta ta canja kaya, sallar magriba tayi, ta sake mikewa dakyar zuwa wajen kayan shayin dake jere a dakin cikin wata kyakykyawar kantar gilashi, yunwa takeji bata wasaba, ta hada shayin da masifar kauri, jikinta har bari yake tahau sha. Tana gamawa tamkar jira ta shiga kwara amai a wajen, tun tanayi da dan karfin ta harta gaza, jitake kamar zata amayo harshenta da kayan cikinta. A wannan halin Jannat ta shigo ta sameta, ba karamin firgita tayiba, dama Mammah ce tace taje ta duba mata Batoul din, dan duk yau bataje can sashenba, ita kuma Jannat Mubeen ya kafa mata dokar zuwa dan bayason ta fahimci tsakaninsa da matarsa akwai matsala.

Cikin matukar firgici taje ta sanarma Mammah, itama a firgicen sukayo nan harda Papa da dawowarsa kenan ko dakinsa bai kai ga shigaba. Suma hankalinsu ya tashi da ganin Batoul, Papa yace su fita da ita zuwa clinic din cikin gidan gwamnatin, Mammah tai saurin cemasa kodai a kira Dr Affan, dan jikin Batoul din yayi laushi da yawa. Bai musaba ya mikama Jannat wayarsa yace ta kira Dr affan, shikuma ya fita dan Mammah ta samu damar gyara Batoul din.

Kusan a tare Dr Affan da Mubeen suka shigo, sosai Mubeen ya rikice, har sai da Mammah ta fara lallabashi, shi kuma Dr Affan ya shiga aikinsa cikin kwarewa, bayan ya diba jininta ya fita da neman afuwan su jirashi. Suna zaune jigum-jigum sun saka Batoul dake baccin wahala da karin ruwa agaba suna kallo. Dr Affan ya dawo kusan awa daya da rabi bayan fitarsa, yanda ya shigo fuska a washere ya bama kowa mamaki, ya mikama Mubeen takardar hannunsa da fadin

“Congratulations yallabai”.

Baice dashi komaiba, sai takardar daya bude kawai, wani tsalle da ihu ya saki yana rungume papa, Papaya shiga jero masa tambayoyi shima yana dariya, Mommah da dama dai tana zargin cikinne itama murmushin kawai tai tana girgiza kai da halin Mubeen da kullum sam baya fahimtar ya girma. Papa ya dauka takardar shima ya duba, ai kasa fahimtar wayafi wani murna tsakanin da da uban akai, kafin aja wani dogon lokaci naganar ciki tafara zagaya dangi daga bakin Jannat parrot, sai ga sakon taya murna ya fara rige-rigen shigowa wayar Mubeen.

A wannan rana dai cike da dunbin farin ciki wannan ahali sukayi shi, da safe Batoul tai masifar tashi da mamakin tattalin da ake mata, ga yan dubiya sai zuwa suke wai gaisheta, ita saima ta fara tsorata kodai wani ciwone da ita, gashi Mubeen yaki mata bayanin komai akai, sai faman sake sabunta tattalinsa a kanta yakeyi, daga karshe dai sai a bakin Jannat taji komai. Nayi murna sosai wanda har sai da Mubeen ya shiga tsokana ta. Su Gwaggo Aminatu suka zo dubani suda su Zabbau da autar mu. Banda Innar mu tace dai ayimin sannu tana dubani. Daman nasan bazata zoba yanzun saboda akwai kunya a tsakanin mu...

•••X••O•••X••O

Ranar wata monday na shirya na tafi makaranta submitting resignation letter. Kamar yadda Papa ya zabar min na hak’ura zan yi business zan kuma zama personal assistant din Mamma. Sannan yacemin nan da yan wani lokaci zai samamin lecturing na online. Ni kuwa mai zance da wa’innan bayin Allah da suka sanya haske acikin rayuwata?.

*ABU*

A hankali nake kallon bishiyoyin makarantar ina karewa daliban dake wucewa kallo. Murmushi nayi sanda na tuno rayuwa ta ta baya da Mubeen dalibi na daya zamto miji na a yanzu. Ahankali driver din yake tafiya saboda yadda ciki na ya tsufa. Daman shi Mubeen tuni ya taho zarian ganin kwangilar da papa ya dora shi akai. Message ne ya shigo waya ta na dauka ina kallon screen din wayar ganin sakon na stud muffin💕 ne kamar yadda na rubuta.

“Dear Whole world😘😍Zuciya ta na cike da kewar ki, Mata ta soon to be maman babyn baby. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune a site cikin tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina son ki...

“Bani da kamar ki Wholeworld😘Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe

Please Login or Register in order to submit comment