Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saketa da ‘yaya rab’e rab’e, Sittin ta ubangiji wasu kan wasu muke kwanciya a daki. Ga ‘yata ta biyu itama ta kamu da cutar shan inna kowa ‘kyamatar ta yake. Ga Hinde itama ta haife shege. Sittin ta ubangiji bamu da cin yau bare na..”

Haj Husna taja tsaki tana karkada mata yatsa,

“Tashi kificemun a gidah. So kike ki aure nawa mijin. Mumugunciya, munasura, Tashi ki fita..”

Cikin kururuwar kuka Bintalo ta yage zani sai ga robar curry ta fado. Hajia Husnah ta kira Inna Rabi ta caje jikin Bintalo. Bintalo sai kyarma jikin ta yake tana raba idanuwa hade da kwaso rantsuwa kala kala ta dire. Rayco da Curry sai cokali aka samu a kullin dan bantan ta. Da gyatuma rad’au din taa kulli d’aya.

“Sittin ta ubangiji tsautsayi ne Hajia.”

Hajja husnah ta kwashe Bintalo da mari. Bintalo ta baje a kasa tana jera rantsuwar sai dai Inna Rabi ce ta saka mata. Hajja Husnah kuwa sai huci take taci ka fam zata fashe,

“Dama ana tamin yan sace sace duk na dauka sabbin almajirai ne ke mana. Ashe kece barauniyar. Shegiya, Ku dai bakuji dadi ba wallahi. Daga mai asircemin ‘da tana nanuka masa yarta. Sai mai min sace-sace da son aure min miji, Fi ce min daga gida kafin nasa a dauke ki da shegen duka. Karyai gulai kawai.”

Bintalo ta tattare zanin ta tana sake dadawa takashin ta duka, Ta dubi Hajia Husnah dake jiran ta fice mata daga gida,

“Kudin aiki na fa Hajia..”

Hajja Husnah ta saki guda tana tafe hannaye,

“Ah lalle! Wane kudi? Ai duk sace sacen da ki kai a kudin ki ne. Miji na kuwa ko a mafarki ba zaki samu me kama da inuwar sa ba. Ficemin daga gida.”

Bintalo ta dire tsallen albarka kan bata yadda ba wallahi sai an biyata kudin aikatau dinta.

“Ke ko kunya bakiji ba? Wallahi tallahi kinji rantsuwar musulmai? Sisin kobo bazan baki ba. Allah kadai yasan abinda kika sassace mana.”

“Sittin ta ubangiji Indomie ce guda biyar wancen satin da madarar ruwa guda uku. Sai sauran kashin miyar Alhaji da kuma ragowar lemon roba, Danyen sa...”

“Rabi futar min da barauniyar figalalliyar matar nan kafin nai kasa kasa da ita anan.”

Bintalo ta shiga kwaso rantsuwa tana direwa kan sai an biya ta kudin aikin ta. Dakyar Inna Rabi ta jata ta fitar da ita daga gidan. Bintalo kuwa ta tsaya a tsakar gidah ta shiga kwararawa Haj Husnah kwandon tsinan taka itada ahalin ta. Tana yi tana gwafe zani tana dukan takashin ta, Haka ta jima tana lailayo ashariya tana durawa sai da tai mai isarta sannan ta fice daga gidan tana tafe tana mita har ta karasa layin su.

*GIDAN MATA TARA*

Tunda shagunan Kawu ila suka kone ya zama mazaunin gidah. Masallaci ma tuni yayi sallama dashi. Kullum yana gida. A tsakar gida akan bokitin sa. Ya lailayo ashar ya durawa wancen ya shararawa wasu mari. Gaba d’aya ya kara zama rigimamme marar mutunci. Fada kuwa kullum sai anyi rabiya dashi. Lamarin dai sai addua kawai. Toh kamar kullum yau ma yana zaune a tsakar gidah ya zabga tagumi yana sakace hakora. Lokaci zuwa lokaci yakan jera tsaki akaro na ba adadi. Yaran sa su takwas cif ba d’aya suna tsakar gidan ana harkijimi dasu kamar kullum da sauran bataliyar yan gidan mu. Cikin haka Mariya yar sa ta shigo kanta dauke da kwanon tallar gyadar da take. Babu sallama bare sallallami haka ta wuce shi ta zauna a kusa da mahaifiyar ta. Sai hararar kudin hannun ta yake da alamun tayi ciniki sosai. Domin tun sanda gobara ta samu kayan sa ya zamto ciyarwa ta gagare shi. Mahaifin Ummitan dake tallafa musu kuma ya rasu tuni an raba gadon ta bashi yaja musu jari ya cinye su tas. Shi yasa yanzu Ummitan ke dorawa su Mariya tallan kayan koli da gyada. Kawu ila sai hararo kud’in hannun Mariya yake yana sauraron yadda take lissafawa Ummitan cinikin da tayi. Hamma yake ta jerawa yana mikar yunwa. Ya sake kaikace kunne yana jiyo su,

“Abbas ne ya siye ta duka yasin. Yace gobe ma akai masa sai siye. Kayan kolin ma kingani rabi ya siya.”

“Ah dakyau! Ya kyauta gaskia. Na gangaren cikin tasha ko?”

“Eh shi.”

“Ai kuwa da yawa za’ai gobe. Ri’ke ungo nan naki ne.”

Ummita tafad’a tana mika mata gudar dari biyar. Sauran kudin kuma ta kukkulle ta d’aure a bakin zanin ta. Kawu ila yaja dogon tsaki yana hararo kudin hannun Mariya. Cike da jin haushi yasa kafa ya hambare butar kusa dashi yana hararar ta tamkar ita tayi masa lefi. Mik’ewa yai daga kan bokitin sa. Ya gogge shi ya shigar dashi d’aki. Gungun yaran dake wajen ne suka tashi suna musu suka nufe shi, Dauke da wani katin biki a hannun Furera yar Hajara ta uku,

“Baba karanto mana ka fassara mana. Musu muke yi.”

Kawu ila ya shiga zare idanu yana gyaran murya. Dauke katin yake da wasu sunayen amarya da ango christians an rubuta:
‘Happy married life Uchenna and Ikke.’

Kawu ila ya sake gyara tsayuwar sa ya tsurawa katin idanu kafin cikin Irin nuna iyawar nan ya fara karantowa,

“Hafafeya maredade li-fe ukeniya anaduwa ikko. wato birnin ikko kenan legas.”

Walidi ya buga tsallen murna yana rawa irin baban nan nasa ya amsa musu. Basmah dake gefe tace,

“Toh baba me hakan ke nufi?”

Kawu ila ya zauna a bakin rijiya ya takarkare yana shiryo bayani,

“Ita wannan matar da kuke gani. Haifaffiyar birnin ikko ce wato legas hada lefe take yi. Shi kuma wannan lefen sa ne ya ‘bata shine suke tallatawa ma’ana, idan ansamu kayan lefen akai lagos. A takaice dai itace ta hada lefen ya ‘bata shine suke cigiya, Hafafeya maredade li-fe ukeniya anaduwa ikko. Wato Idan an samu lefen akai birnin ikko.”

Usaiba dake gefe ta sheke da dariya tana buga zani,

“Kutsin ubancan kayya kai, Allah ya raba mu da sharota.”

“Waye ya sharota Usaiba?.”

Usaiba ta dafe haba tana kwashe kayan wankin ta,

“Da wanda ya tsargu nake..”

Kwafa kawu ila yayi yana girgiza kai. A lokacin Bintalo ta shigo gidan tana tale kafafu. Tana ganin Kawu ila taja ta tsaya tana daure mayafi a kugu.

“Ilyasu bani hamsin dita daka ara satin baya. Sittin ta ubangiji sai ka biya ni domin ba yadda zan ba.”

Baba Usaiba taja guda ta saki tana taka rawa,

“A hayye! Fatara mai tada tsohon bashi.”

Kawu ila ya cire tagumin daya zabga yana baje kofofin hanci,

“Yanzu babu sai dai idan na samu.”

Bintalo ta dire tsallen albarka tana yarfe hannu,

“Sittin ta ubangiji ba yadda zanyi ba. Alo tsiya alo danja, Shege ka fasa dan halak sai yanka..”

Baba Usaiba ta kara sakin gud’a hade da dukawa ta zana layi agaban su da gawayi,

“Ku casu banban ku casu, Ku casu ba mai raba ku.”

Sauran y’an gidan suka bushe da daria. Baba Ummita da Mariya suka shige ‘daka abinsu. Bintalo kuwa ta shiga lailayo ashariya tana durawa kan sai ya biyata kudin ta.

Tun daga farkon layin mu nake jiyo sautin muryoyin yan gidan mu. Ruwan zagi kuwa sai zuba yake. Na dafe kai na da hannu na na hagu ina girgiza shi. Wannan wacce irin rayuwa ce akeyi a gidan mu. Babu abinda ya canza tun ina kankanuwa har girma na. A zaure na jiyo duk fadan nan akan nera hamsin akeyin sa. Ja nayi na tsaya a tsakar gidah bayan nayi sallama. Na zuge zip din jaka ta na ciro nera dari na mikawa Bintalo ganin yadda take huci. Tak’i karb’a tana jijjiga. Hinde ta tunkubar da darin ta fad’i a kasa. Aka bushe da dariya. Bintalo taja tsaki tana tura dauri gaba, A yamutse ta dube ni cike da kumfar baki tace dani,

“Mikomin.”

Na kalli kudin na kalleta na kuma maida kallo na ga Hinde, Ita ko kunya bataji dan ta khaleel na gefe hancin sa yayi dumu-dumu da majina. Ya tsaya a tsaye ya sau fitsarin sa. Daga abin kirki sai abu ya dawo na tsiya? Na fada a zuci ina murmushi. Ko kallon su banyi ba na fara hawa matattakalar bene,

“Zo ki mikomin kyallukazar kaya. Anje yawon ta zubar an ciko jaka da kudi dole a nuna mana.”

Ban kulata ba na cigaba da hawa sama, Sai nanatawa take cike da umarni. Na tsaya daga hawan da nake ina murmushi. Bansan ya akai ba ni dai kawai naga bakina na furta kalmomin,

“Baba kenan. Kyallukazar kaya ai gasunan kin haife su. Sannan yawon ta zubar kinga sakamako a dakin ki. Daga tsatson ki. Domin ga d’aya daga ciki nan a kusa dake. Tamkar uban sa yayi kaki ya tofar. Dari na bayar, Hinde ki rike hamsin din kya siyawa wannan yaron naki pampers ko ze dena sakin fitsari a tsaye.”

Ina gama magana na haye sama, cirko cirko na bar yan gidan mu. Gaba d’aya tamkar anyi ruwa ya cinye su. Tsit kake ji da alamun maganganu na sun dake su. Domin tunda Allah ya halicce mu bantaba maida martani ba irin yau. Ko meyasa oho? Murmushi nayi na shige d’aki. Autar mu dake lab’e tayi tsalle ta rungume ni tana jinjina min. Alhamdulillah na fad’a ina ajiye jakata agefe. Domin Innar mu bacci take yi. Kilan data jiyo ni da kashi na ya bushe yau. Ina jiyo muryar baba usaiba tana sakin gud’a,

‘"Ayyiriririririir! Kutsin ubancan kayya kai! A hayye kayya kai..."


*Unedited*

**
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[7/26, 8:32 PM] +234 904 419 1709: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*27*

*
*
*
*GIDAN MATA TARA*

Bintalo ta zube a ‘kasa tana kururuwa hade da sallallami.

“Ilyasu kana jin bakaken maganganun da yarinyar nan ta gasamin?”

Kawu ila ya buga tsaki yana shigewa d’akin sa, Usaiba ta doka guda tana taka rawa,

“A hayye kayya kai, Mungan su a rana.”

“Du’kurkusar banza.”

Bintalo tace da Baba Usaiba hade da tsirtar da yawu a gefe. Baba Usaiba taja guda ta saki tana buga zani.

“Kutsin ubancan kayya kai, Ai gwara ni, Ke kuwa figalalliyar banza da wofi. Ta gama ‘kare miki da gayyar ‘yaya rab’e-rab’e kowanne da bakin cikin da yake kunsa miki sa...”

Bintalo tayi kukan kura ta cafko wuyan Usaiba suka shiga dambe, Yan gidan mu suka yanyana akan su ana kallon su. Hijabi na zura na tafi gidan su Fadilah domin gaba d’aya karakainan fad’an su ya ishe ni. Can naje muka baje tashar hira da Fadilah, Fadilah taja ajiyar zucia ta sauke tana zabga tagumi,

“Tawan munyi kwantai fa, Ko kinsan Harira y’ar bayan layi aure zatayi kuwa? Kanwar kanwar bayan mu.”

Nayi murmushi kawai ina cigaba da kurbar lemon da ta kawomin, Sai da nasha mai isata tukun,

“Komai lokaci ne Aminiyas, Wallahi da mutuwa da aure da haihuwa duk lokaci ne. Idan Allah yayi toh fa ba makawa sai anyi ko ana muzuru ana shaho sai anyi.”

Fadila ta sake sakin wata bahaguwar zuciar kafin cike da sanyin murya tace,

“Hakane kam! Toh Allah yabamu ikon cin wannan jarabawar. Ai gwara ke ma kin gama karatu kina sana’ar ki ga koyarwa. Ni kuwa rayuwa ta sai cigaba da tabarbarewa take yi.”

Harara na dankara mata ina rufe lemon da murfin sa.

“Karki sabo k’awata. Toh duk abunda nake da shi na kama kafar rufin asirin ki ne? Ai Allah baya hada maka duka, Kada kiyi sab’o. Ki cigaba da godewa Allah a duk halin da kika tsinci rayuwar ki. Allah ya cigaba da dafa mana kede kawai”

“Toh Ameen dai! Ya labarin Haysam kuwa?”

“Yana gidan baban sa.”

Daria Fadilah ta tuntsire da ita tana bubbuga k’afa,

“Meya baki daria? Na raba ki da yaron nan.”

“Tunowa nai mune rabin hamsin din. Yanzu ai shi ya haura haka. Har yanzu kina kan bakan naki ko kuwa?”

“Mu bar zancen nan Aminiyas, Ni tuni mun raba hanya dashi domin wutsiyar rak’umi tayi nesa da k’asa. Allah yabani wanda ya fishi, Shima Allah yabashi wadda ta fini.”

“Ameen tawan..”

Haka dai mukai ta jajantawa junan mu sannan na tashi domin tafiya gidah. Fadila ta yimin rakiya, A tsakar gidah muka ha’du da mahaifiyar su wato Aunty Nanah tana gani na ta dashere hak’ora tana murmushi. Na juya baya na don ganin da wa take? Ganin ni din takewa murmushi yasa nayi yak’e ina sosa kai na,

“Ina wuni Aunty?”

“Lapia qalau Batoul.. Ya mutan gidan?”

Murza idanu na nayi don tantance ko mafarki nake yi.? Ai kuwa dagaske ne, Hakan yasa na amsa ta da sauri cike da farin ciki,

“Sunanan qalau Aunty, Suna gaishe ki.”

“Ina amsawa. Dan Allah ki gayda Innar taku. Uh uhm nace makarantar ku sun fara daukan sabbin dalibai kuwa?”

“Zataji Insha Allahu Aunty! University?”

“Eh nan.”

“Farkon shekara inajin zasu fara IN SHA ALLAH!”

“Masha Allahu! Toh dan Allah yar kanwar ki zaki samawa, Kinsan komai sai da hanya.”

“Toh babu damuwa, ALLAH ya kai mu lokacin.”

“Ameen Ameen.”

Haka dai mukai sallama da Aunty, Fadilah tamin rakiya har farkon layin mu. Ina tafe ina mamakin Auntyn su. Lalle Allah qadirun ne ala Manyasha’u, Ya daga wanda yaso a duk sanda yaso. Wai ni ce yau Aunty ke neman alfarma awaje na?

“Alhamdulillah Ya Allah for the unlimited blessings..”

Na fada a zuciata ina murmushi. Can kofar Ghali mai shago naga dandaxon mutane. Karasawa nai ina jiyo sautin dukan da ake lakadawa galin yana callara kara. Wani yaro na tambaya menene? Nan ya sanar min cewar ai kama galin akai yayiwa wata yarinya fyade. Sai da yaci duka ya lissafo sauran sunan yaran daya lalata. Ciki harda Basma da Farida. Kasa b’oye farin ciki na nayi. Na shige gidah ina hamdalah da karfi hade da kururuwar shelar fadar gali ne yayiwa su Basma fyade. Kankace me? Tuni gidan mu da unguwar mu ya kacame da hayaniyar zancen. Mu kuwa dadi ne fal xukatanmu. Innar mu har hawaye se da tayi. Yayan mu agaban kowa yayi sujjada yana godewa Allah. Ranar dai baccin dadi muka yi ni da su Innar mu. Banda su Bintalo da abun ke ‘bararrakar zukatan su. Domin sam basu ji dad’in hakan ba.

**
Dukawa Bintalo tayi ta gwagwada mursuleta a duburar ta. Ta dadawa takashin duka tana sakin tsaki,

“Yar kundin uba, Yanzu mursuletan zai hallaka ki. Baki da aiki sai cin zalina a duwaiwai..”

Ta karasa fada tana sake ‘dadawa takashin ta duka. Gaba d’aya a hautsine suka a dakin. Kan katifar Alawiyyah ce da Hauwa da Khaleel dan Hinde. Sai daga ‘kasa a gefe kuma Bintalo ce a tsakure itada Hinde, Daga gaban katifar kuma zabbau ce itada yaranta su biyar wasu kan wasu. Bintalo ta dube su duka taja tsaki tana sosa diddigaggen gashin ta. A lokacin daya d’aga cikin yaran zabbau ya tashi yana kuka,

“Mama kahi, Kahi zanyi.”

“Kashi kuma? A daren nan? Dan kundin uba.”

Bintalo ta fada tana dungure masa kai, Zabbau ta mike tana sakin hamma,

“Tahi muje. Shege tsinanne nafara bacci ka tahe ni.”

Kankace me? tuni sauran yaran sun tashi suma, Wasun su suka fara kuka wasu kuma suna neman abinci.

“Ni gaskia shegun yaran nan sun isheni, Zabbau ki samo mafita dan Allah.”

Cewar Hinde tana sake jan hijabin data rufe jikin ta dashi. Zabbau har ta kai bakin k’ofa ta juya tana tafa hannaye,

“A hayye! Ke Hinde har kinada bakin magana? Su da uban su ai, Ke kuwa kece uwar shege. Ga shege nan kin haife batare da hanyar aure ba. A hayye.”

Nan dai fad’a ya kaure tsakanin su. Bintalo taja tsaki ta fita daga dakin tana dura musu ashar. A k’ofar dakin ta shimfida dan buhun ta da matashin kai ta kwanta tana rantsuwar da safe sai taci mutincin su.

“Sittin ta ubangiji Allah ya kai mu safiya duk sai kunbar gidan nan. ‘Yayan iska..”

Haka dai su kaita fada suna doke-doke. Mu kuwa sama sama muke jiyo hargagiyar su. Kwanciya ta na gyara ina lumshe idanu. Sakamakon daddadan baccin daya fara ‘dauka ta....

*BOMO ZARIA*

Tunda suka koma gida ya wuce side d'insa bai fito ba sai dare, daren ma sai da mahaifiyarsa taje ta kamo shi ya d'an sha tea sannan ya koma, bai sake fita koda bakin gate ba har yau da suka yi kwanaki biyu da zaga garin. Muhammad Mubeen kenan, yana kwance sai faman juyi yake akan gado tamkar wani mai ciwon jiki. Wayarsa ya janyo ya kunna ya shiga daddanwa yana hira da abokansa da suke can k'asar.

“Mubeen! Mubeen!!”

Amb Salees dake bakin k'ofar side d'in Mubeen d'in yake ta faman kiransa, da yaji shiru yayi tunanin ko bacci yake yi, ya juya zai tafi sai yaji alamun tafiya ya waiga.

“Ohh Mubeen, kanaji amman amsawa ya gagara, oya zo muje kayi min rakiya wani guri.”

Yatsansa wanda ake d'agawa idan za'ai zaman tahiya ko za'a nuna abu shi Mubeen ya zura a cikin kunnansa na b'angaren hagu yana sosawa. Amb ya kuma binsa da kallo wayarsa rike a hannu ana ta faman kiransa amman bai d'aga ba saboda yana son ya gama tabbatar da abinda d'an nasa yake nufi.

“Karka ce min ba zaka ba, kaje ka shirya kazo ka sameni a wajan mota.”

Amb Salees na gama sanar masa ya juya ya wuce cikin gida, yabar Mubeen a tsaye yana faman had'e rai. Shi yasa baya kaunar zuwa k'asar nan saboda sam ba'a bari su huta, kodai a d'auke su akai su gidan 'yan uwa da abokan arzuk'a, ko kuma 'yan uwa suzo gidan duk su ishi mutane da surutu. Mubeen ya kad'a kai ya juya cikin bedroom tare da zama a bakin gado, sam baya son fitar nan musamman bugun zuciyar da ya dinga yi ranar da suka fita, da ya kwanta da kyar ya iya yin bacci saboda rashin samun nutsuwa da yayi. Ya jima zaune yana tunanin inda zasu je, can kuma ya kalli agogon dake kafe a jikin bango. Karfe hud'u da kwata na yamma (4:15pm), ya tashi ya bud'e wardrobe yana karewa kayan ciki kallo.

A hankali idanunsa suka sauka akan wasu riga da wando na shadda kallar ruwan toka (ash colour), ya d'akko su tare da ajiyewa akan gadon ya nufi inda takalmansa suke a jera sai walwali suke yi. Wani had'add'an covered shoe ya d'akko shima kalar kayan sannan ya dire su a k'asa ya bud'e cikin wani show glass, huluna ne a jere suma kala-kala abin gwanin ban sha'awa, ya d'akko ash wadda mahad'ar kayan ce itama ya ajiye akan gado. Bathroom ya nufa ya sakarwa jikinsa shower, ya gama wankan tsab sannan ya fito sanye da bathrobe fara kal. Wajan mirror ya nufa yana karewa dukan ilahirin jikinsa kallo, kafin ya d'akko d'an karamin towel ya fara goge sumar kanshi, wacce take a kanannad'e. Sai da ya tabbar ya shafa mai da body spray sannan yaje ya sanya vest ya saka kayan.

Watabarakkallahu Ahsanilkalik, ko wanda yafi kowa hassada da kyashi, idan yaga Muhammad Mubeen dole ya yabeshi dan ba karamin kyakyawa bane. ALLAH ne mai yadda yaso a lokacin da yaso kuma yayin da duk yaso sai ya tsara abu. Wannan bawan nasa kam ya had'a komai, ya taso cikin arziki yana rayuwa cikin daula, wajan hallita tamkar shine aka bawa damar ya halicci kansa. Fitowa yayi yana d'aura agogo a wutsiyar hannunsa, ya tsaya a wajan freezer d'in dake parlourn ya bud'e tare da janyo kwalin hollandiyya ya zuba a cup ya sha sannan ya mayar ya rufe ya fita.

Shima Amb Salees fitowarsa kenan shi da su Aeedah, Maman su kuma tana bakin k'ofar zata rufe.

“Yayya Mm muje ko?”

Cewar Amb Salees yana kallon babban d'an nasa dake tsinkar wani pink d'in fure a jikin wata shuka. Ba tare da yayi magana ba yaje yaja hannun kaninsa Mashkur suka nufi wajan mota.

Zaria city suka nufa, can unguwar Kwarbai gidan sarkin zazzau d'in. Kai tsaye gidan suka dosa, ganin irin motar da ta nufo gidan yasa aka fara yi musu kirari, ana mik'a musu gaisuwa. Mubeen dake zaune a gefe kusa da glass ya kawar da kai saboda hayaniyar fadawan da suke ta yiwa Amb Salees kirari domin tuni suka gane shi.

“Mm please ka dinga gaida mutane, kaga nan ba Ethiopia bane, karka ja min surutu kaji big son?”

Amb Salees ya fad'a bayan sunyi parking yana lek'en Mubeen, maganar yake masa cikin tausasa harshe da nuna tsantsar kulawa had'e da lallashi. Kai tsaye cikin fada aka nufa dasu sai gaishe su bayi suke yi, ran Mubeen gaba d'aya a b'ace yake, tunda ya dora kwayar idanunsa a gabas bai sake waigawa ya kalli wani abun ba har suka shiga. 'Yar gaisuwar da Amb ya roki yayi kasawa ya yi saboda rashin sabo, ga tafiyar mota yasa ranshi ya kuma b'aci, har suka shiga fadar sarki bai saki fuska ba. Duk gaida shi suka yi, sarkin ya kirawo Mubeen ganin yayi shiga ta kamala, gashi da kunya kamar ba matashi d'anye sharaf ba.

“Amb wannan ina yiwa little princess d'ina kamu, amman yanzu tana primary 2”

Gabaki d'aya gurin aka yi dariya amman ban da Mubeen wanda yake jin tamkar yayi k'asa. Albarka ya dinga sa masa iyayen suna amsawa.Mamma Ahlaam suka fito ita da yaran zuwa side d'in Fulani Aisha matar sarki ta farko aka bar Amb da Mubeen dake zaune a can gefe yana kallon wasu zanuka da aka yi a gurin. Cikin girmamawa Amb Salees yake mayarwa da maimartaba amsoshin tambayoyin da yake masa.

“Yanzu dai ka dawo da karfinka kenan na tsayawa takarar ko?”

“Eh ranka shi dad'e ALLAH karama lafiya, jiya ma munyi maganar da party leader d'in jam'iyar, ya kuma tabbatar min da cewar ni za'a nad'a d'an takarar gwamna a jam'iyar tamu.”

“Toh Amb sai kun dage sosai, ni dai ina bayanka, amman kasan ba zan fito fili na bayyana ba. Kuma kasan abu ne da kamar wuya a ce jam'iya mai mulki sun bari ta adawarsu ta samu galaba akan su ba. Ka dage sosai wajan janyo talakawa a cikin shekara d'ayan nan da zaka yi kafin zabe, kaji?”

Amb Salees ya dinga jinjina kai alamun zai yi k'ok'ari wajan ganin hakan ya tabbata. Sun dade a gidan domin har wajan 9:00pm suna gidan, maimartaba sai janyo mutane yake yana sake had'a Amb dasu wad'anda zasu dad'a taimaka masa wajan campaign. Mubeen kuwa tun yana jin dad'in gidan har ya fara takura kasan cewar yaki zuwa ya d'an zazzaga gidan, yana zaune ne kawai a cikin wani kayataccen parlour yana kallon kwallo.

Kira ya dinga dannawa Mamansa idan ta d'aga kuma yaki magana kuma yana ji, bud'e baki yace suzo a tafi shine yake masa matuk'ar wahala. Ita kuma Haj Ahlaam ba zata iya kiran Amb ba, dan tasan tunda bai fito ba har lokacin magana suke yi. Sai da taran tayi sannan Amb ya kirawo su suka fito, Mubeen sai kuma had'e rai yake kamar zai fashe dan haushi har suka karasa gida bai yi magana da kowa ba.


*LIMANCIN KONA*

Kwanaki sun shud'e sun koma sattitika, yayin da sattitika suka koma watanni, wasu da dadi wasu sai addu'a, a gurin mu kuwa sai hamdala, domin duk irin yadda 'yan gidan mu suke tozar tamu hakan bai hana ALLAH rayamu ba. Ina ta yin teaching d'ina ana biya na muna cikin rufin asiri sosai. Mazajen aure kuwa sai hamdala domin zuwa suke yi kamar ana kai musu talla ta, sai dai nakan samu matsalar su kawu ila. Gabaki d'aya sun hana samari na zama, wasu da aure na suke zuwa gadan-gadan amman sai 'yan gidan mu suyi yadda sukai wajan wulak'anta ni har sai sun tabbatar na rasa saurayin sannan zasu kyale.

Watanni na bakwai da fara yin teaching, ina zaune a staff room ina marking d'in wasu test da na yiwa yara sai ga massege ya shigo ta cikin waya ta sabuwa dana sake saya, ta wajan Haysam kuwa Inna na barwa ita. Zaro wayar nayi daga cikin jakata na duba.

_''Kizo da takardunki gobe da safe

Please Login or Register in order to submit comment