Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bameyiwu bane sai kaga akan sa abin yake. Dan Allah ka gyara halin ka. Idan an girma asan an girma.”

Kawu ila ya tab’e baki yana harara ta,

“Ni dai na yi rantsuwa babu inda zata je, Ba zata shiga wata jami’a ba.”

Gwaggo Aminatu tayi daria mai sauti tana kallon Kawu ila,

“Toh sai kayi azumi uku, Domin da yardar ALLAH jamia kuwa tamkar ta yi tane, Kaga akwatin nan ita nazo kawowa shi, Mun je ganin gonar Baban su Faysal nace mu biyo na kawo mata, Domin nasan da tafiyar ta jami’a. Kuma dai ni ce gaba da kai. Kaga kuwa babu zancen hanata zuwa jamia karma ka fara.”

“Amma Yaya..”

“Mubar maganar nan haka ilyasu, In de na isa da kai a matsayi na na babbar yarka sai kayi hak’uri. Duk banga abun tashin hankula anan ba. Abu kadan a gidan nan sai kuyi ta kicincina shi kuna mai da shi babba. Wallahi tun daga bakin titin layin ku ake jiyo hayaniyar yan gidan nan. Ace kullum dai magana d’aya za’ai tayi, Kun janyo kaf gari babu wanda baisan halin ku ba? Dan Allah ku canza ko dan na ‘kasa su taso cikin bin nagaba dasu.”

Fuuu Bintalo ta haye sama tana cuno baki tamkar bazawarar akuya, Kawu ila ma ya dauki bokitin sa ya shige da’ki. A haka aka fara watsewa daga tsakar gidan. Gwaggo Aminatu ta girgiza kai kawai cikin takaici tace,

“Allah ya kyauta!”

Kafin wani dan lokaci tuni su Kawu Ishaq dake majalisa suka daddawo dan gaisawa da Gwaggo Aminatu. Sama na haye baki na dauke da azkhar na yamma. Sai da Gwaggo Aminatu ta shisshiga ko’ina a dakunan kasa sannan ta hayo sama, Dakin Usaiba ta shiga suka gaisa sannan ta shigo dakin mu. Gayshe ta muka sake yi ni da autar mu da ta tashi a lokacin, Amsawa tayi suka cigaba da gaysawa da Innar mu,

“Yasu Meenal duk sunanan qalau?”

Innar mu ta tambayi Gwaggo Aminatu,

“Kowa lapia lou Karimatu. Ya Najibu har yanzu bai dawon ba?”

Kamar na fad’awa Gwaggo Aminatu sharrin da akai masa sai dai nayi shiru kawai? Don gudin abinda zai je ya dawo, Kar ta tafi tabar baya da ‘kura. Innar mu tayi murmushi kawai, Domin duk abinda ya danganci Yayan mu bata sa baki saboda kunya ta ‘dan fari.

“Kai! Mikomin akwatin nan”

Gwaggo Aminatu tace dasu Ya Faysal dake bakin kofa a zaune domin dakin ba zai dauki dukkanin mu ba, Kawo akwatin yai ya koma ya tsaya,

“Faysal ma ya taddo Naseer a tsaye TubarkAllah!”

Cewar Innar mu data bi Ya Faysal da kallo lokacin daya kawo akwati, Gwaggo Aminatu tayi murmushi kafin tace,

“Ya fishi ma, Ai shi Naseer tsawon dangin baban sa yayo.”

“TubarkAllah ba lefi kam.”

“Ungo Batoul rike zai isheki ki zuba kayan ki ko? Sanda mu kai waya dake shekaran jia na manta na tambaye ki yadda zai ci.”

“Nagode Gwaggo! Wallahi harna zuba suma a leda.”

Gwaggo Aminatu ta ri’ke haba tana daria,

“Kayan jami’ar acikin leda? ki rufamana asiri kar ayi damu.”

“Nagode k’warai ALLAH ya saka da alkhairi ya kara bud’i Ameen!”

“Ameen Ya Rabbi! Ga dan tarkace nan inji su Meenal, Sunce ace miki suna miki murna, Allah yasa ki fara a sa’a.”

“Ameen ya Allah! Nagode sosai Gwaggo! Allah yabar zumunci. Allah ya yalwata muku arziki ya saka muku da alkhairi Ameen..”

“Ameen Batoul! Me sunana baki da lapia ne?”

Gwaggo Aminatu ta dubi autar mu tana fadin haka. Murmushi nayi ina gyarawa autar mu d’aurin d’ankwalin kanta,

“Daga bacci ta tashi ne yanzu.”

Na fa’dawa gwaggon haka. Hira aka dan yi sama-sama , Gwaggo dasu Ya Naseer suna ta dorani kan yadda zanbi jamia sannu a hankali. Na kuwa ji dadin hakan domin na kad’an ba na karu sosai. Sai bayan anyi magriba su Gwaggo Aminatu suka tafi bayan ta biya ta dakin Bintalo sun gaysa. Naira dubu biyar tabawa Innar mu kan ta sissiyi kayan abinci wadatacce wanda zai da’de mana. Har mota muka rakasu ta babbamu dari bibiyu ni da sauran yaran gidan baki d’aya. Har suka ja mota bandena d’aga musu hannu ba, Zuciya ta kal da ita na shige dakin mu. Ina mai jin da’din samun Gwaggo Aminatu a matsayin yayar mahaifina wadda ke mana son ‘kauna marar gauraye. Allah dai ya dore mana zumuncin mu har gaban abadan..

Bintalo kuwa na daki itada su Alawiyya, Motsi kadan taja tsaki tana rafka tagumi. Wayar Alawiyya ce tai ‘kara ta dauka tana kada idanu tamkar wanda ya bugu mata wayar yana ganin ta,

“Hello sweet! Okay kana waje? Toh gani nan..”

Katse wayar tayi tana yafa yalolon mayafin ta, Fuskar nan tata ta kwailaye taci uban bilicin.

“Baba bara naje na dawo.”

“Toh sai kin dawo, Kada ki manta dai kya ce yasiya mana yar kaza da biredin nan mai laushi.”

“Kai Baba uwar kwadayi, Bara dai naje.”

Ficewa tayi tana rausaya, Ta wuce ta gaban usaiba dake tsaye tana jiran layin ban’daki yazo kanta, Usaiba ta kece da daria tana buga zanin ta,

“An tafi yawon ta zubar, Dan ALLAH a dinga tunani in an girma asan an girma. A hayye kayya kai..”

Alawiyyah taja tsaki ta sauke, Can gaban teburin haladu mai shayi saurayin nata ya tsaya a motar sa, Wajen babu haske kullum anan suke zance, Bayan mota ya bu’de musu suka shjga shi da ita, Babban mutum ne a haife ya haife ta, Sai wani rausayar da murya yake yana kashe mata idanu,

“Alawiyyah ta Alewar zucia ta. Son ki kullum kara luntsuma yake a kogin zucia ta.”

Alawiyyah tayi murmushi tana bankaro masa kirjin ta,

“Alhaji na banki na, Wai yaushe zaka turo ai zancen auren mu ne kai da Mu’azzam ‘kanin ka (saurayin Hinde)?”

“An kusa Alewar zucia ta, Kinsan ginin da ake muku ne maginan dake ginin daga kasar waje muka dakko su, Sati na gaba ma zamu je daku kuga gidajen naku, An kammala ginin kasa sauran na saman.”

Alawiyyah ta dashe baki tana kwantar da murya,

“Sama da ‘kasa ne Alhaji?”

“Tab hawa uku ne ai, Akwai ‘kasa munace masa ondagurawun (underground) da falon ki, Sai na kuma sashin tsakiya me tankama tankaman dakuna uku da falo biyar, Sai saman karshe me dakuna takwas da falo takwas.”

Alawiyyah ta rungume Alhaji tana murna, Ya lakuce kumatun ta yana tande harshe kamar maye. Kasa kasa ya ke mata magana yana sake nanukata ajikin sa,

“Na nawa zan tab’a?”

“Haba Alhaji wannan albishir din da ka gayamin ai yafi kowanne dadi, Taba na nuna godia ta agare ka. Kawai dai Idan zaka tafi ka biya musiyo kaza da biredi.”

Alhaji ya kece da daria yana zura hannun sa a rigar ta, Hade da janyo kofar motar ya rufe su ruf, Dama gilasan duk a rufe suke....................


___
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_*


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(TAKU NA BIYU)_


ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE, ME SO DAN GIRMAN ALLAH YA BIYA YA KARANTA HANKALI KWANCE😘❤️

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*1️⃣8️⃣*

Sai da Alhaji ya jagwalgwala Alawiyyah son ransa sannan ya matsa gefe yana gyara botiran rigar sa. Ya sanya hular sa ya gyaggyara ko’ina sannan ya bude ya koma kujerar tuki yana sai ta mudubi sai tin Alawiyyah.

“Muje ko?”

“Eh Alhaji na..”

Cewar Alawiyya dake zuge zip din rigar ta, Can wajen tukubar nama suka je. Alhaji ya futa ya siyo dakwalan kaji guda biyar, uku daban biyu daban. Ya karb’i biredi guda biyar shima uku daban biyu daban. Mika mata guda bi biyun yai ya ajiye sauran a gaban mota, Lekawa tayi tana hararar ledar.

“Alhaji waccen fa?”

Yamutsa fuska yayi yana baya da motar,

“Ta yarana ce.”

Tsaki ta saki tana zundumawa yaran ashar a zuciar ta. Har kofar gidah ya kai ta,

“Toh Alewar zucia ta, Sai munzo daukar ku ganin gidajen ku ko?”

“Okay Alhaji na, Yadda kace ai hakan za’ai.”

“Haka yake, Toh a gayda min da Hinde taki fitowa mu gaysa saboda bada mutumin ta akazo ba.”

“Ai kuwa dai! To zataji.”

Sumba ta kai masa ya dashe Hakora yana murmushi,

“Godia nake Alawar zucia ta.”

Daga masa hannu tayi ta shige gida tana karkada jiki, Ya ja mota ya tafi kaduna.

*GIDAN MATA TARA*

Kayan da su Ya Meenal suka bawa Gwaggo Aminatu ta kawomin na shiga dubawa ni da Innar mu da auta. Kayane kala goma cif, Kunce suka bani kuma masu kyawun gani, Wasun su daga ciki ma sababbi ne basu sassasu da yawa ba. Ga takalma shima dede ni dama kusan kanmu d’aya TubarkAllah, Suma kala biyar da jaka ta gayu guda uku sai ta ratayawa a baya ta yan jamia guda biyu. Sai mayafai guda uku da hijabai guda biyu sabbi fil fil. Kayan basu tsaya anan kadai ba. Harda su kayan kwaliya da zanin gado na kwanciya da jakar filo. Da yan kwanuka masu kyau madedeta. Dayar ledar kuma risho ne dan karami dashi sabo acikin kwalin sa, Da fulas na shayi da kular abinci. Sai Indomie zatai guda ashirin da kwamfulas da madara da bonbita. Sai ledar maganin sauro na kunnawa. Saboda tsabar farin ciki mik’ewa nayi na shiga taka rawa ina murna, Innar mu da autar mu sai dariya suke kyalkyala min suma cike da farin ciki. Dan dadi wallahi sai dana zubar da hawayen farin ciki,

“Alhamdulillah! Allah kai ne abun godia. Allah ga bayin ka yadda suka faranta mana ya ALLAH ka faranta musu ninkin ba ninkin namu, Ya ALLAH ka kara musu yalwar arziki da wadatar zuci. Allah ka kare su daga sharrin mutum dana aljan. Ya ALLAH ka biya musu bukatun su dunia da lahira.”

Na fada ina goge hawayen farin ciki,

“Innar mu kalli yadda su ya Meenah suka futo dani, Da me zan saka musu? Wallahi Inna har cikin magudanar jini na nake jin su. Allah ya azurta mu nima na yi musu wani abun.”

“Ameen! Allah ya saka musu da alkhairi. Ki tsaya ki karatu sosai ta yadda zasu ji dadi suma.”

“In Sha Allahu Innar mu.”

Da temakon Innar mu da autar mu na karasa shirya kaya na a akwatin Da Gwaggo Aminatu taba ni, Sai ga Fadila tazo hannunta rike da wata leda cike da kaya itama. Zama tayi a gefe na bayan ta gayda Innar mu. Nunnuna mata kayan da Gwaggo ta kawo min tayi nai. Sosai ta taya ni murna hade da adduar Allah yasa na fara karatun a sa’a. Mun ‘dan taba hira kafin tayi min sallama tatafi bayan na rakata har kofar gidah tana hawaye ina yi. Ledar data kawomin na bude ina nunawa Innar mu.

“La Innar mu kinga itama ta kawomin kayan shayin, Wannan soyayyiyar miya ce. Kai ALLAH sarki Fadilah, Nagode k’warai ALLAH ya dorar mana da zumuncin mu har abada..”

“Ameen ya Allah! Yarinyar kirki. Allah ya shi mata albarka. Maza ki hada karki manta wani abun.”

“Tab Innar mu kenan wallahi kayan sunyi yawa, Ku rike na wajen Fadilan wancen sun isheni ni kadai ce fa. Miyar ma ku diba kwa barmun yar kadan.”

Sam Innar mu taki yadda ta karba, Sai da nai ta mata naci ina had’ata da ALLAH sannan ta dauki kayan shayin. Ta kuma tsakuri miyar yar kadan. A daren dai na shirya kayan tafiya ta tsaf. Safiya kawai nake jira idan ALLAH ya kai mu sai tafiya. Tuni bacci daddad’a ya dauke mu bayan munci biredi da miyar da Fadilah ta kawomin.

***Alawiyya na shiga daki kuwa tsalle ta dire tana dukan Hinde a takashi, Hinde ta sosa tana mikewa tsaye haka ma Bintalo da Hauwa ganin yadda Alawiyyan ke farin ciki sun san ta samu ne.

“Lasamin naji mana.”

Hinde tafada tana murna, Alawiyya ta lelleka ko’ina kar ajiyo su sannan ta rufe kofar dakin tana jan hannun su suka dawo tsakiyar dakin. Ledojin ta janyo ta kai gaban Bintalo tana murmushi,

“Mu fara da taune ‘kashi kafin kuji kanun labaran.”

“A hayye nanaye..”

Bintalo tafada tana bawa Hinde hannu suka tafa ji kake ‘cassss. Gwaggwafe wa Bintalo tayi ta raba musu naman da biredin, Ba zancen bismilla haka suka tattaune suka cinye suka gyatse. Bintalo ta tsotse diddigaggen kashin tana jujjuya tukar a hannun ta,

“Sittin ta ubangiji bai isheni ba.”

Alawiyya ta yamutsa fuska tana sake karyo biredi kamar jaka. Ta cusa a baki tana cewa,

“Shegun ‘yayan nan nasa zai kai wa wai. Ina jiyo shi yana cewa da Falalu mai kaji wai kashi biyu zeyi, Leda d’aya kaji uku d’ayar kuma kaji biyu. Su zai kai wa ukun ni kuma biyu. Ai da sake wallahi, Ina shiga gidan nan zan fitar da shegiyar matar nan tasa.”

“Haba Alawiyya, ai bama sai kin fad'a ba. Yo irin wannan matayen ai da sun ganki ma zasu bar gidan da kafafuwansu, saboda itama matar tashi tasan kuna da tazara sosai. Kedai Alawiyya kice gaba da faranta masa rai, duk abinda yace kiyi kawai kiyi, dan yasan ma tun yanzu zaki masa biyayya.”

“Ai dama Baba ina masa, shifa baik'i ba, ace yau ya turo magabatansa ayi magana. Abu d'aya ne yake hanashi turowa, yace min so yake sai an gama gini kinsan hawa uku yake yi, kuma nice zan fara shiga, sannan ni zan fara zab'a na darje.”

“Aiyirrrrrr..yirrrrrr..riiiiii, a hayye nanayee. ALLAH na gode maka da ka azurtani da 'ya'ya mata, masu farin jini a kaf gidan *MATA TARA*, Iya gani iya kyalewa wallahi, sunsha tabara sunsha suratul yasin, kuma kurwarsu d'aci gareta. Idan kashi banza ne kaza tayi itama.”

Bintalo ta fito tsakiyar gidan mu tana wannan hayaniyar, wacce tasa baccin da muke yi mai dad'i ya kaurace mana nida wasu mutanan gidan harma da Innar mu. Cikin ikon ALLAH babu wanda ya fito bare ya tanka mata, haka tayi ta habaice-habaicenta ta koma d'aki tana cewa su Alawiyya wai bakin ciki ake musu, shi yasa babu wanda ya fito yi mata ALLAH ya sanya alkairi na murnar da ta fita tana yi.

*WASHE GARI*

Tunda asubahi na tashi nayi wanka na sake kimtsa kayana, Innar mu kuma ta dora min taliya da manja wacce taji daddawa da albasa. Bayan ta kammala ne ta zuba mana nida Autar mu, muka yi bisimillah muka faraci cikin raina ina tunanin daga yau shikenan bazamu sake cin komai tare da 'yar k'anwata ba sai idan ta dawo gida hutu. Bayan mun kammala ne na tashi na wanko hannuna, na koma d'aki na dauki hijabi nasa sannan nace da Innar mu.

“Bari naje na yiwa su Kawu Khamis sallama, sai nazo na tafi, Suraj yace mu had'u a tashar mota zai sani a wata wadda zai karb'i lambar direban.”

“Toh mai sunan uwa jeki dawo d'in, duk abinda suka gaya miki na 6acin rai karki bari ya zauna a zuciyarki saboda kinga doguwar tafiya zaki yi, kinji ko.?”

“Toh Innar mu.”

Na fad'a sannan na fita, kai tsaye d'akin Kawu Khamis na nufa, nayi sallama daga bakin k'ofar ya amsa min tare da cewa na shiga. Da sallama a bakina tare da dorkusawa kasa na gaida shi, ya amsa min yana ya faman sakace da tsinken tsintsiya, kai kace yaci wata lafiyayyar suyar ne da sassafen nan.

“Kawu Khamis ayi mana addu'a zamu tafi makaranta.”

Sai da ya zare tsinken daga cikin bakin shi, sannan ya kalleni tsab kafin ya maida tsinke yace dani.

“ALLAH yasa da gaske karatun zakije Batoul, nidai babu ruwa na idan kikaje kika lalato rayuwarki. Bazan hanaki tafiya ba, domin 'ya'yana ma ba hanasu abinda suke sonyi nake ba, kije ALLAH ya bada sa'a shikenan abinda zance miki.”

“Na gode Kawu Khamis, ni daman addu'a nake buk'ata daga bakunanku.”

Daga haka na mike ina jin dad'in yadda ya yi min addu'a, sannan nabi sauran dakunan kafin na karasa majalisar Kawu ila wato bakin k'ofar shigowa gidan akan bokitinsa na gado. Tunda ya hangoni ina nufowa gurinsa naga ya had'e rai kai kace zuwa zanyi na rokeshi kudi, na karasa dai zuciyata na lallashi na akan jure duk wani cin kashi da zai min. Har k'asa na durkusa na fara gaishe dashi amman fur yaki amsawa, ganin haka yasa na dora da abinda ya kaini gurinsa.

“Kawu ila zan tafi makaranta ina bukatar addu'arka.”

Kamar daman jirana yake na furta hakan, cikin fad'a da masifa tare da hargagi ya fara magana.

“Karya kike yi munafukar yarinya, ba bu wata addu'a ta da kika zo nema. Ni zaki rainawa hankali? Da kinso addu'ar tawa mai ya hanaki tunda aka fara zancen zakije baki zo kin same ni ba na baki shawara da kuma addu'ar a matsayina na d'an uwan mahaifinki, shine sai yanzu zaki tafi yawan ki na shaid'anci daman ga d'an uwanki can yaje ya dad'a koyowa yazo ya fara bata mana yara, shine ke ma kika zo salon na tofa wata maganar, kije ki dawo da cikkunan shege ace nine na miki addu'a. Toh ba zanyi ba, tashi ki bani waje, ALLAH ya raka taki gona.”

Duk iya k'ok'ari na wajan danne zuciya ta sai da na kasa, wani irin kuka yazo min nayi saurin sannya tafukan hannayena na toshe tare da rugawa da gudu na haye sama. Ina shiga na soma k'ok'arin had'iye kukan amman sai da ya bayyana.

“Sai da nace ki daure da duk abinda zasu gaya miki, musamman ma shi Ilyasu da ba kaunarmu yake yi ba. Tashi ki wanke fuskarki kizo ki tafi kar yaron can yayi ta jiranki”

Jikina a sanyaye na mike na gyara fuskata. Karfe takwas da mintuna hud'u agogon wayata ya nuna, a kuma lokacin ne Suraj ya bugo min, na dauka bayan nayi masa sallama yace na fito ni yake jira, na amsa masa tare da maida wayar cikin jakata da gwaggo Aminatu ta kawo min. Kayan na dauka na yiwa Inna sallama, sai naga ta sanyo hijabi tana cewa ai zata rakani har tasha sai ta dawo. Naji dad'i kuwa, daga nan muka fito harda Autar mu. Muna cikin sakkowa sai ga 'yan gidan mu sun firfito suna ta kallon mu kamar wasu bakin fuska, sai da muka gama sakkowa zuwa kasa mukaji muryar Bintalo tana cewa.

“Ohh la'ilaha'illallahu, wannan duniyar tamu tazo karshen d'anewa. Ku duba min ku gani, yau Kaltume da kanta zata kai 'yar cikinta tashar 'yan iska, to dai idan an kunso abin kunya kar a sake a dawo mana gidan nan ahe!.”

“Ahaiyeee nanaye babu mijin aure za'a tafi rakashewa.”

Cewar Ummita matar Kawu ila ta farko. Shi kuwa yana bakin k'ofar ya babbake yasa k'afarsa alamun bazamu fita ba, sai da Innar mu ta sanyayya tace masa.

“Zamu wuce.”

“Toh Kaltume ku wuce”

Ya fada yana sake tare hanyar. Inna ta kalleshi sosai taga ya murtuke fuskarsa tamkar ba'a sanya mishi dariya ba a cikin tsarin halittar sa.

“Ke yanzu Kaltume da kanki zaki kai yarinyarki jami'a? Kuma bama zuwa zata yi tana dawowa ba, a'a kwana zata dinga yi a can ke babu abinda ya dameki ko?”

Kawu ila ya fad'a yana kallan Innar mu wacce itama shi take yiwa kallon kaji dashi.

“Indai nice toh na amince mata taje duk inda zata neman ilimi ba zan hanata ba, karka manta ko barinta nayi anan kafi kowa aibata min ita, to yanzu zata yi nisa daku, yadda bakunanku zasu huta akan ta, kuma indai bakin ku ba zai furta mata kalmar alkairi ba, toh ku barshi amman tafi kam kamar tayi ne”

Innar mu na kaiwa nan ta nufi hanyar da nufin idan bai dauke kafarsa ba zata hamb'are shi mu wuce. Cikin tsananin mamaki dajin irin kalaman da Inna ta gayawa Kawu ila, yana zaro ido yaga ta nufoshi, da sauri yaja baya, yadda yayin yaso bani dariya saboda naga alamun tsoro a tare dashi. Amman dan karna janyo wata matsala sai na had'iye dariyar muka bi bayan Inna mu wacce tuni ta fice ranta a b'ace.

Muna tafiya Innar mu na sake jamin kunne akan kula da kaina, nayi mata alkawarin insha Allahu zan yi yadda take so, a haka har mukaje tasha inda muka tarar da Suraj yana ta kalle-kalle da alama ni yake nema. Karasawa wajan shi muka yi, ya gaida Innar mu sannan ya nuna min motar da zan shiga. Kayan ya karba ya sanya a booth, sannan aka ce na shiga, a lokacin ne naji wasu zafafan hawaye sun biyo saman kumatuna, na rungume Innar mu wacce itama kukan yake shirin kwacewa.

“Sai hakuri mai sunan uwa, ayi ta hakuri aje a dawo. ALLAH ya bada sa'a yasa a samu abinda akaje nema.”

Daga haka Innar mu ta b'anb'aroni daga jikinta, taso taga tafiyar mu, amman yadda taga ina kuka yasa ba zata iya jura ba, taja hannun Autar mu suka tafi babu ko waiwaye daga ita har Autar tamu. Na san kuma Inna ce zata hanata waigowa saboda kar suga yanayi na. Na kalli Suraj cikin share hawaye nayi masa godiya da addu'a ta gamawa da duniya lafiya.

“Babu komai Batoul, ALLAH dai ya baku nasara gabaki d'aya keda mutumin.”

Murmushi nayi masa bance komai ba, mota na shiga na zauna. Har muka tafi Suraj na gurin, na dinga jinjina irin amincin sa domin banyi tsammanin zai rik'e alkawarin da Haysam ya bashi akai na ba.

*BATOUL TABAR BAYA DA K'URA*

Tunda wannan abun ya faru muka bar gidan, shikenan Kawu ila ya dinga surfa masifa yana tsine musu albarka. Kowa na gidan yayi tsit ko Bintalo da ta take d'an taya shi, itama yanzun shiru tayi saboda babu wanda yayi tsammanin Inna zata iya shafawa idanunta toka ta zazzaga bayanan nan. Bokitinsa na gado ya jawo ya zauna yana huci kamar wani kumurci, ya karewa mutanan wajan kallo tsab kafin ya mike yana yafufo Bintalo da hannu alamun tazo. Tana karasawa ya matsala gab da ita a saitin kunnanta yana cewa.

“Ni babu wanda zai kawo min wulak'anci a cikin gidan nan wallahi, kinga Bintalo yau dole a tona asirin da ake rufewa nasu Kaltume.”

“Babu shakka, ai daman kaine kaki yadda tuntuni ayi komai a gaba. Yanzu mai kake so ayi?”

Kawu ila yaja Numfashi ya sauke, ya kuma komawa kan bokitinsa ya zauna yana hura iskar cikin bakin shi tana fitowa waje yace.

“Gidan Alhaji Kabeer Wafa zakije, ina nufin gidan da Kaltume take aikatau, idan baki fahimce ni ba, ina nufin gidan su wannan d'an iskan yaron ya biya kud'in d'akin da zasu zauna idan taje jami'ar suyi masha'arsu. Can zaki ki warwarewa asararrun iyayensa abinda yake faruwa. Bintalo karkije kiyi min ba dai-dai ba a gidan can, sittin ta alkur'ani zamu raba k'afa dake. Duk wani iskanci da kika san ana yi, da irin kayan da yake kawo musu duk ki fad'a, kafin Kaltumen ta dawo ta same ni anan wajan.”

“An gama Kawu na kowa, ALLAH yaja da ranka yayi k'asa-k'asa da idanun makiyanka, bari naje na dawo.”

Bintalo tayi maganar tana mai juyawa ta koma sama cikin d'aki ta dakko mayafi.

“Ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, kuma duk sharrin mai sharri kansa yake komawa, kowa yasan masu bin maza a gidan nan. A hayye kayya kai... Ana yi muna jin dad'i, ana bari muna jin haushi billahillazi.”

Usaiba ta fad'a tana daga matakalar bene na uku. Bintalo da ta kusa kaiwa fita daga kofa ta juyo tana shirin cire mayafi, da sauri kawu ila ya dakatar da ita ta hanyar cewa.

“Yi tafiyar ki Bintalon mu, kinsan ai idan d'an tasha yana baka kayan tashancin da yayo, toh komai za'a ce d'an tashar yayi shi wanda ake bawa ba zai yadda ba har sai lokacin da aka yi masa abinda ranshi baya so. Wuce kije, ALLAH ya baki nasara.”

Bintalo kuwa ta juya ta fita, yayin da Ummita ta harareshi tana hura masa hanci kamar zata rufe shi da duka. Cikin d'akin ta ta koma tana la'antar su, saboda mijin nata ko ita baya bawa umarni kamar yadda komai ya jajibo sai ya fara yiwa Bintalo. Nan fa guri ya kaure da gutsiri tsoma, kowa ya fara fadar albarkacin bakinsa.

__
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI

Please Login or Register in order to submit comment