Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alhaki ne ke binsa Batoul! Nayi nayi nayi da Ilyasu ya dena abubuwan da yake yaki ji, Bansan meyasa yake haka ba. Wallahi shi kadai ya fita zakka acikin mu. Allah ya bashi lapia ya kuma ganar dashi gaskia Ameen.”

“Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum!”

“Yauwa bude kunnuwon ki na miki nasiha Batoul... Ina fatan zaki amfani dasu”

“IN SHA ALLAHU Gwaggo!”

Kai na a k’asa. Ina jina tamkar mafarkai wai ni ce yau za’aiwa jan kunne na raruwar aure? Wainan daura aure na? Wallahi tamkar mafarki haka nake ji. Gwaggo ta fyace hancin ta fara magana cikin hankali da nutsuwa....

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻__*ETERNAL LOVE💕_*


_*EPI: 4/8*_

••
“Toh!..Zan d'anja hankalin ki akan yadda ya kamata ki dinga tarairayar mijin ki ta siga daban-daban kamar; kissa, jan hankali da kuma ladabi da biyayya kowanne xan daukeshi d’aya bayan d’aya na miki bayani akansa, ki sani dukkan xamantakewar rayuwar aure ba xata yiwu ba saida kissa, idan akace kissa ta kunshi abubuwa da yawa, kissa ta kasu kashi biyu akwai kissa marar kyau akwai kuma kissa me kyau, Mara kyau itace ta shirye tuggu da makirci da sihiri, Za ki ga kishiya ta kullawa kishiyarta sharri ko idan ta daidaici ta gama girki taje ta tsuga mata gishiri ko yaji ko kananzir ko kuma tai k’ok’arin fitar da ita daga gidan ma gaba d’aya, zaki ga mace ta shiga tsakanin d’an mijinta da mijin,

“Ta cikin dabara ko mace tashiga tsakanin mijinta da iyayensa da makamantansu wannan kissa mara kyau sede muce tur da ita. Allah ka ganar da masu irin wannan kissa, Amma kissa mai kyau itace kulawa da mai gidah da tarairayarsa kamar kwai wanda daga ciki akwai, Kissar magana, kissar tafiya, kissar kwalliya, kissar abinci, kissar tsafta, kissar kallo mind you ba kallon film ba to kallon miji nake nupi, yawwa se kissar shagwaba da kissar kwanciya se kissar kula da jikin mai gidah suma xan d’auki kowanne nai miki bayani akansa Ina fatan kina ganewa?!''

Cikin k’asa da kai da murya na amsa ma ta da,

“Eh Gwaggo..”

“Kissar magana: Cikin nutsuwa da tauna magana xaki gaya masa kafin ki fadeta don gudun gaya masa maganar da baxai ji dadinta ba ko bata masa rai, Ki dinga magana cikin sigar hankali karki dinga bud’e masa muryarki kala-kala wani lokacin ki maketa wani lokacin ki dan budeta wani lokacin ki dinga yi a hankali kamar bakyason magana, wataran kuma idan kinason gaya masa magana mai dadi ko ta soyayya kice saiya baki kunnensa xaki rada masa. Sai kissar mu ta gaba,

“Kissar tafiya; idan xakiyi tafiya kuma kin tabbatar yana gurin ko yana kallonki daga inda yake ki dinga tafiyar da xata dauke masa hankalinki xuwa gareki misali ki dinga tafiya a hankali kamar bakyason taka k’asa wani lokacin ki dinga tafiya kina karairaya kina dan jujjuya jikinki wani lokacin kuma sauri-sauri xaki dingayi kina juya maxaunanki idan ta gaba yake kallon ki kisan yadda xaki dan dinga girgiza kirjinki cikin hikima bata sigar da xai gane ba, amma fa Batoul mijinki kad’ai xaki dinga yiwa wannan kala kalar tafiyar cux kikaiwa wani xaki dau zunubi ne,”

Cigaba da koya mata kissoshi tadingayi kama daga kissar kwalliya, da kissar abinci kissar tsafta, da kuma kissar kallo ciki harda kissar shagwab'a data kwanciya, wanda sosai Gwaggo taja kunnen taakan kissar kwanciya ta k'ar-k'are mata da yadda zatai kissar kula da jikin mijin ta,

“Kin gane?!”

“Nagane Gwaggo”

Cewar Batoul datai wiki-wiki da idanuwa wai yau Gwaggo ce take mata irin wannan zancen, Maganar ma ta manya duk kunya ta dabaibaye ta.

“Yawwa to sai dan karin jan hankali daxan miki wanda idan kika durfafi yinsa tabbas Zaki xamo shalele awurin mijin ki. yaxamto ba wacce yake so da gani sai ke. hanyoyin jan hankalin sune,

“Kula da duk wani abu da mijin ki yafi so, kula sosai da duk wani abun da baya so, ki lura da abinda yake damun shi da hanyar da zaki kula da iyayen shi da dangin su da yadda zaki xauna lafiya da kowa babu ruwan ki da wani kishi na banxa da wofi wanda zai kaiki ga samun hypertension, kishi dole ne ba ace karki yi ba amma akwai irin kishin da akeyi bana yanxu da yaxama na hauka ba, Kede babu ruwanki, domin kin taso Kinga yadda ake zaman chakewa a gidan nan ko?”

Kad’a kai Batoul tai tana wasa da yatsun hannunta d’aya , Dayan kuma tana goge hawaye, cike da nutsuwa.Gwaggo ta cigaba da yi mata jan hankali akan rayuwar gidan miji ta k’ark’are da,

“Abu na k’arshe shine ladabi da biyayya, babbar magana kenan domin duk abubuwan dana fada abaya idan ba ladabi da biyayya yaxama na banxa don duk iya tafiyar ki ko iya farinki idan bakya yiwa miji biyayya meye amfaninsa?! Misali kinyi kwalliyar jan hankali kinyi masa kalar girkin dayake so jira kike ya dawo yaga kwalliya, Yaci abincin da kika tanadar masa amma yashigo ba sannu da xuwa ba karb'ar kayan hannunsa sai dai ki bishi ki dire masa abincin da kika yi masa tana iya yiwuwa ma alokacin ki fara masa k’arar ko kudi da makamantansu toh tell me tayaya zaiga kyan kwalliyar sannan kuma yaji dadin abincin?!,

“Ko kiga wasu matan miji na magana suna yi suna fada sosai fad’i in fada bai dace ba sam, kamata yai idan mai gidah yana fadansa ki masa shiru idan yagama sai ki bashi hak’uri idan kuma ke aka batawa baxaki iya bada hak’urin ba tunda ranki yakai kololuwa a baci to kiyi shiru kawai kuma ko menene yace kiyi masa koda kuwa ran naki a bace yake don kansa shima xe sakko ku shrya, Wasu kuma matan xaki ga suna yawan korafi akan maxajen su don abinda ba abin fada ba sai su rufe su da fada wasu ma kawai xakiga sun fice daga harkar matan kwata kwata inkinga sun kusancesu to sede idan rabo ya tsinke yawanci kuma xakiga akan maganar da mukai d’axu ne akan rashin gamsuwa damu da maxajen mu ba sayi xakiga mace har mace, Kamar ita tai kanta don kyau sai kiga sun had’a kishi da wadda bata kaitan ba harma xata xamto itace mai fada aji gurin mijin xakiga yana Allah Allah girki ya xagayo kanta don yafi gamsuwa da ita xakiga wasu matan suna yawan tambaya to meyasa wata macen ake gamsuwa da ita wata ba’ayi?!,

“Ba komai bane yake kawo haka kisani sai kowa da irin ni’imar da Allah yai masa misali kowanne jinsin halitta akwai maza akwai mata kuma both ana samun farare da bak’ake dogaye da gajeru mai kib’a da siriri ke kowanne abu dake jinsin bil adama xaki ga nawani yafi nawani to haka ma ni’ima take ajikin mata da maxan wata macen tanada ni’ima sosai bata buk’atar kari wata kuma tsaka tsaki ce wata ma bata da ita se d’an abunda ba’a rasa ba,

“Don haka Batoul, ki sani kamar masu bukatar karin jini da ake cewa ga abubuwan daya kamata suci haka ma matan masu neman k’arin ni’ima ajikin su akwai abinda yakamata suci domin ance idan kanada kyau to kadad’a da wanka,sai dai wasu matan suna amfani da magunguna barkatai wanda wasu ma basusan komeye ba sudai suci susha buk’atar su ta biya kawai shikenan, Wanda zaki ga yin hakan yana haifar da cututtuka barkatai ga mata,shawara ta dake karki xamto cikin irin wa’innan matan masu bankawa cikinsu kowane magani suka ji ance yanayi aa sam karki soma kowaye yakawo ko yaxo maki dashi karki soma amfani dashi kinji dai na gargadeki domin hakan yana haifar da toshewar mahaifa, hana haihuwa ko canxawa yaro kamanni kamar wata k’awata sumayya matar ma’aruf wallahi abinda yafaru da ita kenan, Tahaifo yaro marar cikar halitta abun tausayi saboda ita komai cusawa take ta bankashi a baki duk bamu sani ba se bayan da xata haihu a asibiti dr tace har cancer magungunan suke sawa dakyar aka mata cs don kasa haihuwan tayi abu nabiyu ga kaikayin gaba wato infection,Da kurajen gaba plus ciwon ciki ke da abubuwa da dama de, ki lazimci shan fruits kamar yadda kikaga ana saki sha a kaduna,

“Kankana, gwanda, ayaba, guava, lemo, tumatir, rake, aya, kwakwa, dafaffiyar gyada, xuma, nono, madara, madaran shanu, gurji, cukwi, zogale da ruman da inibi sai tuffa da kuma xaitun kina ganewa kuwa?!”

Nodding kai kawai nayi, gaba d’aya jiki na yayi sanyi sai yanzu nasan tabbas aure aka min, batare da Gwaggo ta damu da damuwar da na shiga ba tacigaba da maganar ta,

“Se abu na k’arshe naga lokaci na ja, Addu'a wato ki rik’e addu'a, wallahi addu'a makarin mumini ce ke duk wanda ya lazimci addu'a wallahi baxai tab'a tab'ewa ba azkhr dinnan ki dinga yawaita yinsu nataho miki ma da wasu littafin du’as din suma ki rik’esu gidanku kullum yaxamto cikin karatun qur’ani musanman suratul baqra domin duk gidan da ba’ayinta ance kamar kango yake, Ki yawaita yin addu’oi na neman tsari ga korar shaid’an ya kuntata masu ya karyasu dama mutane ma sharranta masu nufarku da sharri, addu’a tana jawo yardar allah ta’ala, suna gusar da bakin ciki da bacin rai a zuciya,suna janyowa zuciya farin ciki da nishadi,suna karfafa zuciya da jiki,suna jawo arziki suna kara imani da tawakkul da sabr, kai sunasa komai na mutum ya daidata ya samu peace of mind! Ki kama Allah ,ki rik’e addua da qur’ani Insha Allah rabbi zaki bani labari,anan xan tsaya seki fad’i tambayoyin ki karkiji kunya ta ko tsoro, ki saki jikin ki, ki fad’amun abinda baki gane ba.,”

Shiru Batoul tayi, tana k’as k’as da yatsun hannunta, kanta a ‘kasa kunya dukta isheta jin shirun yayi yawa ne yasa Gwaggo sake tambayar ta,

“Uhum ina jin ki”

Nanma tayi shiru! Gwaggo ta cigaba da cewa,

“Yawwa sai magana ko ince jan hankali da zan miki akan WAYAR MIJI! Kinga wayar miji wallahi tallahi daukar ta masifa ce, Kai idan ba dole bama Karki bari kisan kalar yanayin wayar mijin ki! Domin saninta hypertension ne, daukar ta kuma tamkar shigar ciwo ce, lalubar cikin ta kuma Wlh ciwon zucia ne. Domin ganowa kan ka abinda yafi karfin ranka zakai, tamkar albasa ce idan baki bareta ba babu ruwan ki da yajin ta ko zubar hawaye, kina fara barewa kuwa idanuwan ki zasu fara rena kansu, Daga nan sai ambaliyar hawaye. So dan ALLAH Batoul babu ruwan ki da wayar sa, Kiyi harkar ki da taki yayi harkar sa da tasa. Shikenan a zauna Lapia. Kina koyarwar ki, Idan ya barki fine ki cigaba ki had’a da business non stop, keep ur self busy, engage in activities by one way or the other. Ki karfafa fara business dinki, income ya dinga shigo miki, wani abun ba sai kin tambayi miji ba kiyi da kan ki, Bani bani idan tai yawa sai miji ya fara kosawa. Akwai wata friend dita *Haj Hafsat Rano* Matar nan tana karatu kuma tana business daban-daban, wallahi baki gaba yadda take maida biyar goma ba, hustler ce. So haka rayuwar ta canza yanzu, keep doing you, find a job ko business of your own, ki kare martabar ki data iyayen ki, stand on your own feet... Ba sai da namiji ake neman kudi ba, kowacce irin sana'a indai ba haramiya bace ki yita ki samarwa kanki sauki dama mijin ki baki d'aya.. lastly inaso kiyi hak'uri , ki kuma yiwa iyayen ki halacci! Ki rike rayuwar auren ki cikin lumana da 'kaunar juna! Haka ALLAH yayi wannan mutumi da yazo d’aga baya shine mijin ki, Saboda haka ruguntsumin rayuwar baya ta wuce Pls! Yanzu kin shiga sahun matan aure, sabon foundation ne zaki gina na zaman gidan miji, wata sabuwar rayuwa ce ta daban, wanda Alhamdulillah kece first wife din mijin ki, turbar da kika dora shi akai haka zai tashi wallahi, Dan kuwa mijin 'kazama, 'kazami ne..hhhh! Toh anan zan dira aya, May your matrimonial home be forever blessed❤️”

(Wannan shawarwari kowanne book dina sai kun gansu😂Nasha wahalar hadata shiysa zatai ta circulating🧜🏼‍♀️ Allah ya samu mu amfana da dan abunda ta kunsa Allahumma Ameen!!🥰)

Kuka na barke dashi wanda har sai da kai na ya fara ciwo, Cikin dashasshiyar murya na cewa Gwaggo Aminatu,

“Gwaggo nagode. Allah ya saka da alkhairi.. Ameen!”

“Ameen Batoul din mu, Share hawayen ki kinji? Allah ya baku zaman lapia ya kauda fitna Ameen.”

Tana gama fada ta fice tana nanatawa su Zabbau dasu tsaftace wajen da Bintalo ke kwance, Ni kuwa kifa kai na nayi akan katifa na shiga rera kuka ahankali, Gaba ki d’aya daren ranar ni de bacci kadan nayi domin kuka yafi yawa..

*WASHE-GARI*

Da sassafe Gwaggo ta tashe ni, Sai kara gyaran jiki ake min, Na tsugunno ne, na wanka na sha da naci, Gaba d’aya nagaji wallahi, Kamshin dake tashi a fatar jiki na ma ta ishe ni. Wani dandatsetsiyar laffaya lace wanda Gwaggo Aminatu ta hado a gudunmawar ta aka nad’amin. Maroon color ne da dishi-d’ishin black. Kai na yasha gyara da sheki, Sosai aka nad’a min ita ta zauna daram. Wani dogon takalmi mai tsini da tsada na sanya shima baki, wallahi nayi kyau domin ni kai na na sheda hakan.

Wajajen sha biyu da rabi motar daukar amarya suka zo guda biyu rak, Domin Gwaggo ta hana kai amarya saboda halin da Kawu ila ya shiga na rai a hannun Allah.. Batoul kuwa tunda aka fa’di sanarwar zuwan su take kuka. Kawunnin ta sun sata a tsakiya da Gwaggo Aminatu sun mata nasiha mai ratsa jiki sosai, Wadda ta sanya Batoul yin hawaye. Daga nan kuma aka hau da ita wajen Innar mu inda Batoul tun ta rungume ta tana kuka,

“Innar mu zan tafi.. Zan tafi.. Innar mu zan tafi..”

Batoul ta shiga maimatawa tana kuka shab’e shabe. Duk dakiyar Innar mu sai da tayi hawayen itama. Tai saurin goge wa tana kallon gefe,

“Allah yasanya alkhairi agidan auren naki, Allah ya kade fitnah. Allah ya azurta ku da yara masu albarka. Allah ya bashi lapia ya baku zaman lapia. Tashi ku tafi.”

Innar mu ta karasa fada tana janye ni daga jikin ta. Kuka na fashe dashi sosai ina goge majinar hanci na. Lokaci d’aya mura ta kama ni, Kai na ya shiga sarawa sosai. Dak’yar aka bambare ni daga jikin Innar mu,

“Wayyo Allah na Innar mu! Wayyo Allah na!”

Autar mu ta rirrike ni itama tana hawaye, Muka kankame juna muna sakin ajiyar zucia, Gwaggo Aminatu ta janye ni suka shigar dani wata zungureriyar mota itada wasu mata biyu dangin mijin dana aura, Sai hak’uri suke bani suna kwantar min da hankali. Tunda muka shiga motar na kifa kai na ina rera kuka a hankali....

*KADUNA*

Tunda muka shiga kaduna gaba na yake fad’uwa, Banmasan mun isa ba sai da na jiyo hirar su gwaggon kancewar mun isa. Gaba na sosai ya shiga fa’duwa tamkar zai fadi. Na rintse idanu ina lumshe jikakkun idanu na da suka jike saboda hawaye, Bamuyi wata tafiya mai nisa ba naji alamun tsayuwar motar mu, Ahankali matan suka kamo ni suna maimata,

“Yauwa futo amaryar mu munzo...”

Ahankali na fito suna rike dani kai na a kasa, Wani sashe aka shiga dani mai dauke da mutane, amman ba masu yawa ba, Muna shiga suka yo kai na suka rungume ni, Tamkar zasu cinye ni don murna, Lalle sunason dan uwannan nasu domin da alamun soyayyar da suke masa ce ta shafeni.

“Mamma Ahlaam gata..”

Aka kaini gaban wata farar mata kamar ita tayi kanta dan kyau, Rungume ni naga tayi tana sumbatar goshi na. Na sunkuyar da kai na kasa ina sake jan laffayar ta rufemin fuska, Ina jiyo wasu agefe suna zuzuta kyau na. Haka dai akaita adduoi sosai. Aka kai mu wani babban parlor ni dasu Gwaggo Aminatu. Abinci ne kala kala a bubbude wanda kowa zai je ya diba da kansa, Ahankali sauti ke tashi acikin babban parlorn. Sanyin na’urar ac dik ta ishe ni abunka da basabun ba, Na kudundune jiki na ina karkarwa, Sunci abinci sosai ni kuwa na kasacin komai su Innar mu kawai nake tunawa, Dak’yar fadila ta tursasamin na tsakuri wanda take ci naci na kora da ruwa, Bayan sallar la’asar suka dau hanyar komawa Zaria, Naci kuka da zasu tafi harda majina wallahi, Na rungume Fadilah da Gwaggo suna hawaye ina yi, Haka aka janye ni su kuma suka tafi cike da abubuwan arziki da aka babbasu. Bayan sallar ishai wata yar budurwa ta shigo kira na tana murmushi,

“Aunty wai ga kaya kisa zan raka ki wajen Ya MM..”

D’aga kai na nayi ina bin kayan hannun ta da kallo,

“Tohm. Nagode”

Kada kai tayi tana nuna min takalma a gefe kalar rigar,

“Ga shoes din. Ina jiran ki a parlor.”

Murmushi kawai na mata ta fice tana janyomin kofar. Mikewa nai dak’yar na cire laffayar jiki na. Wani band’aki na hango acikin dakin na shige ciki na rage fitsarin da nake ji. Kayan na cire na wanko fuska ta. Rigar na daga ina binta da kallo, Irin arabian dogayen rigunannanne masu duwatsu ajikin su. Tasha ado orange and black. Na yane kai na da mayafin ina zura covered shoe din da ta nunamin. Na kalli kai na ta mudubi ina cije lebe, Ya Mm na maimaita, it sounds familiar ko a film ne oho? Na fice ina lek’a parlorn. A karshen parlorn na ganota tana danna waya, Tana gani na ta mike ta rungume ni tana murmushi,

“Kinyi kyau Aunty Batoul..”

“Nagode sis...?”

“Jannat!”

Ta maimata tana murmushi, Nima nayi murmushin ina riko hannunta yadda ta rike nawa. Inata maimata sunan nata na yan gayu a zucia ta. Ta corridors muka shiga wani babban sashe, Daga kofar da zata sadaka da shiga sashen ta tsaya tana murmushi, Tanada fara’a gaskia,

“Anan zan tsaya Aunty! Ki shiga yana ciki..”

Kada kai nayi gaba na na matukar faduwa. Adduoi na shiga kamowa ina maimatawa har na shiga ciki, Na wuce wani babban parlor na kutsa cikin wani daki, Can na hango mutumi a lullube acikin bargo ga ‘karin ruwa anayi masa a hannu d’aya,

“Assalamu Alaikum!”

Na fada gabana na matukar faduwa kamar zai fad’o. Tamkar a mafarki muryar Batoul ta shiga yin karakaina a kunnuwan Mubeen, Mikewa yai daga kwanciyar da yake yana kokarin bu’de idanun sa, A hankali ya shiga bude su ya sauke su akanta. Tana Juyawa suka hada idanu, Su kayi wani kallon kallo marar fasaltuwa. Mubeen ya mike zumbur yana goge idanun sa,

“Ma..!”

Ya furta a hankali yana kokarin takowa inda nake, Bansan sanda na saki waya ta a ‘kasa ta fadi ba ji kake ‘tartsisss’, Duk na dubibice na shiga dudduba lungu da sako ko zan hango wani daban bashi ba,

“Me...Me kakeyi anan Mubeen?”

Kansa ya dafe yana cije lebe saboda jirin dake dibar sa, Shi duk a zaton sa ma mafarki yake. Tangadi ya shiga yi zai fadi dakyar ya koma baya ya zube akan gado, Dai-dai lokacin su dr Affan suka shiga suna bashi temakon gaggawa, Ni kuwa sandarewa nayi a tsaye domin mamaki, Al’ajabi da tsoro sun gama cika ni. Likitoci ne suka taru akan sa suna bashi temakon gaggawa, Kenan shine marar lapian da aka auramin zanyi jinyar sa? Kenan boyemin akai kowa ya sani? Ina tsaye ina zancen zuci jannat ta shigo ciki ta kirawo ni kan mahaifin su na kira na. Lalle man kai na ya malale da daxu bangane Ya Mm na nufin Muhammadu Mubeen da Jannat ta fadaba. Wurin mahaifin su ta kai ni yana zaune shida wa’enda na gaisar a kofar gidan mu rannan. Duk sai yanzu abubuwa suke ta dawomin da can bangane ba. Kasa jure kallon su nayi na sunkuyar da kai na ina gaishe su. Kowanne ya amsa fuskar sa a sake wasun su nata tsokana ta. Amb Salees wanda shine mahaifin mubeen kuma gwamna na kaduna yai gyaran murya ya shiga yi min nasiha mai ratsa jiki ya kar’kare da,

“Kiyi hak’uri ‘yata. Nasan an tauye miki hakki na aura miki wanda bakyaso kuma dalibi a karkashin ki. Kiyi hak’uri dan Allah! Ga amanar Mubeen nan mun danka mki, Mubeen miskilin matashi ne da baya iya boye abunda zuciar sa ke so ba kuma zai bayyana a tallafa masa ba, Yana dauke da ciwo a zuciar sa wanda kusan haihuwar sa akai dashi, Ciwon nasa shi ya hanashi karatu. Kullum ba lapia dakyar ya fara samun sauki inda muka dawo nan nayi masa sha’awar fara karatu anan jami’ar da kike koyarwa, Ashe Allah zai sa ya hadu dake har ta kaiga aure duk kuwa da ba lallai idan kinsan yana kaunar ki ba.. Munyi mamakin mai ya mayarda Mubeen ya zamto kullum fuskar sa a sake yana wasa da dariya ba kamar shekarun baya ba? Changes de kala kala aka samu daga gare shi, Sai da muka yi zuzzurfan bincike muka gano kece sila.. Batoul! Kiyi hak’uri ki karbi Mubeen a matsayin mijin ki kinji? Dan Allah na roke ki, Ko dan rashin lapiar da yake ciki ahalin yanzu dai kece zaki zamto silar wartsakewar sa ganin ki kawai a tare dashi ya wadatar.

“Da sunan ki ya farfado a bakin sa daga doguwar sumar da yayi, Ta haka muka gano ki muka fara bincike akan ki, Ni da anawa shirmen rokon ki zanyi kizo ki jinyar sa, Sai mahaifiya ta tace a’a ba za’ai haka ba, Gwara ya aure ki tinda dama akwai k’auna a tsakani. Hakan kuwa akayi gashi har an daura, inaso ki dau hakan ki ajiye a matsayin taki kaddarar kenan, Kuma babu wanda ya isa ya wuce kaddarar sa.Kinji ko ‘yata..?”

Tunda ya fara magana kai na a kasa yake, hawaye sai zirara suke. Tabbas na gama hawa *IGIYAR ZATON* ba zan mallakawa Mubeen soyayyata ba da gangar jiki na, Sai gashi Allah ya sanya hakan a matsayin tawa qaddarar. Duk tarun shekarun nan daman shine mijin da zan aura? Hawaye na na sharce ina kara sunkuyar da kai na kasa,

“Babu komai Insha Allahu ranka ya dade..”

Amb Salees yai murmushi yana kada kansa,

“Masha Allah daughter! Ki kira ni da papa kamar yadda mijin ki yake fada kinji? Kinason wani abun?”

Na girgiza kai na,

“A’a Papa..”

“Toh Allah ya miki albarka.. Inde kinason wani abun ki gayamin ko ki aiko a fad’amin kinji?”

Kada kai nayi ina yaba kambawa da dattako irin na ahalin gidan. Mikewa nayi Jannat taja hannu na muka koma sashen da Mubeen yake. Har yanzu likitoci na kansa suna gwagwarmaya. Wani daga cikin likitocin ya leko yana dagomin hannu,

“Yauwa Mrs Mubeen.. Zo Pls”

“Mrs Mubeen?”

Na maimaita ina yamutsa fuska. Dakin na shiga ina sunne kai,

“Zo ki dan kira mana sunan sa kinji..”

Likitan ya sake fada yana nunamin saitin Mubeen.. ‘dankari mak’ari’ ‘Na furta Ina k’arasawa wajen jiki na sai rawar tsoro yake.

“Mu..be en...”

Na fada a rarrabe kamar maijin tsoro, sannan kuma a ahankali ina dafe kirji na dake barazanar fad’owa, wallahi a tsorace nake. Likitan ya sake cemin na nanata sau uku ko zai farfado,

Shiru na d'anyi kamar bazance komaiba, Doctor yace,

“Sau uku pls, Saboda ke kadai ce muke da hope akai. Ko mu baku waje?”.


Kai na d'aga a hankali, alamar "eh", dan hakan kamar zaifin sauk'i.

Babu musu duk suka fice aka barmu mu biyu kawai.

Hakan yasa naji d'an sakewa, na juya idanu tamkar mai hararsa, Mai kuma na tuna sai na sauke ajiyar zuya kad'an ina ciza leb'ena tare da sake matsawa jikin gadon sosai yanda zai iya jina, mayataccen k'amshin turarensa na sake shigemin k'ofofin hanci.......

“Mrs Mubeen! An dace ne?”.

Muryar Doctor ta katseni daga waje. Da sauri nace, “Gashi dai inayi”.

Likitan baice komaiba. dan haka nima na maida hankalina ga Mubeen dake kwance tamkar wani gawa, cikin wani irin yanayi nace,

“Mubeen, Mubeen ka tashi gani nazo, ga Batoul d'in...”

Na kare maganar da wani irin karsashi.

Gani nai hannunsa yad'an motsa, na waro idanuna waje da fad'in “Doctor gashi ya motsa.....”

Da sauri su Doctor suka shigo cikin sassarfa, dai-dai Mubeen na

Please Login or Register in order to submit comment