Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bare a kaiga bani kudi. Na kalli kawu ila dake can gefe yana cin dumamen tuwo, kai da kaganshi kasan ci kawai yake amman nutsuwarshi da sauraronshi suna kan duk wani wanda yake magana a tsakar gidan. Na had'iye wani bakin yawu saboda tsabar fargabar abinda zance.

“Kai na ne yake sara min tun kafin na gama wanki, ko zaki bari anjima kafin ki tafi din sai na lallab'e miki?”

“Iyeeee! Batoul ni zaki yiwa kiwa? Nace miki anjima zanje bikin shine zaki ce dani sai anjimar zaki lallab'e min? Toh yanzu nake so wallahi, kodan mu kin raina mu, shine bakya son yi mana kitso? amman ai kan gaytumarki ai kullum cikin yi mata kike yi, idan kuma ba zaki yi ba sanar min.”

“Zan yi miki mana Babah, a kawo kibiyar da kum d'in.”

Dariya ta saki tare da sakin gud'a Ayirrrrrrr tana bugun cinyarta, cikin wata irin shewa taja hannuna muka nufi k'ofar d'akin na zauna akan kujera 'yar tsuguno. Alawiyya ce ta fito tare da cillo min kum din tana cewa.

“Kiyi mata da wannan banga kibiyar ba.”

D'auka nayi bance komai ba, har Bintalo ta zauna a gabana, tana cire dankwalin naga gashin kan nan a harhad'e kamar gashin biri, gashi jawur babu ko d'igon baki a jiki. Yi mata na farayi duk kuwa da irin gajiyar nayi ga bakar yunwar da take sake ciwo ni. Muna farawa naga Innar mu ta dawo jikinta ya kuma saki, tana yin sallama ta haye sama na bita da idanuwa.

“Babah bari naje gurin Innar mu na dawo.”

Na fada ina saurin karasa mata wanda na kusa kaiwa dan naje na gano Innar mu, ta kuwa buka kasa da tafin hannunta tana yatsina fuska tace.

“Bafa zaki bar kujerar nan ba Batoul, har sai kin gama min kitson nan, eh salon ki tashi ku shiga d'aki kuyi kuskus d'insu har lokacin tafiya ta yayi ki barni da rabin kai ko?”

Naji hawaye na shirin zubowa daga cikin idanuna, nayi ta kifta idanu har kwallar ta koma, na d'aga kai sama na hangi Autar mu tana kallo na, da alama ni take son kira amman tana tsoran jarabar Babah Bintalo. Ban tashi ba sai da na kammala mata, tun kafin ma na mike tsaye ita ta riga ni, na tabe baki nima naja kafafuwa na nayi sama, ALLAH ya temake ni har na bar wajan kawu ila bai kulani ba. A kwance na tarar da ita ta lullub'e jikinta da hijabi fuskarta a ciki sai sauke ajiyar zuciya take. Nayi azamar karasawa inda take ina k'ok'arin bud'e fuskarta amman ta hanani.

“Innar mu har kin dawo?''”

Kai kawai ta iya d'aga min.

“Kinyi aikin ne?''

Ta girgiza min kai alamun a'a

“Sannu Innar mu, hajiyar su Haysam d'in ce tace ki dawo?”

Nan fa Innar mu tayi shiru, kafin daga bisani naji sautin kukanta yana fitowa. Hankali na ya sake tashi, na kuma kai hannu zan bud'e fuskarta ta sake hanawa.

“Kyale ni uwata, kuyi hakuri nasan dai kuna jin yunwa zuwa yanzu. Amman yau kam ban iya samo komai ba, kuyi hakuri.. Kuyi hakuri.”

Bansan menene yasa Innar mu kuka ba, amman zuciyata na raya min cewar anyi mata abinda ya tab'a ranta ba wai rashin abinda zamuci ne kadai yasa ta wannan kukan ba. Tsam na mike Na zari hijabi na ba tare da na sanar da ita ba Na fice, Autar mu na kallo na sai dai itama yau duk iya tambayarta bata tambayi inda zanje ba. Kasa na sauka da sauri nayi waje ina ta bankama sauri kai kace bashi aka ce naje na karbo.

Gidan Alhaji Kabeer Wafa na nufa, wato gidan su Haysam inda Innar mu take aiki. A harabar adana motoci na tsaya ina karewa gidan kallo wanda yaji shuke-shuke kamshi sai tashi yake yi. Ba wannan ne ya kawo ni ba, hakan yasa na nufi hanyar da zata sadani da ainahin cikin gida, naci karo da Rabi matar da take yi musu girki. Gaida ita nayi kasan cewar ta sanni sanadin zuwan da muke yi da Innar mu kafin matar gidan ta hana zuwa damu nace da ita.

“Inna Rabi mai ya faru naga Innar mu ta koma gida da wuri? Ko Hajiya ta yafe mata aikin ne ganin bata da lafiya?”

Sai naga Inna Rabi ta fara waige-waige kafin daga bisani taja hannuna muka shige wani d'an korido, tana kallo na tace.

“Ahirr d'inki Batoul da zuwa jin abinda ya faru da mahaifiyar ki gidan nan, abinda nake son kiyi kawai shine, kije kice da Hajiyar kinzo kiyi aikin a madadin mahaifiyarki.”

Baki na a bud'e nake kallon ta, bata ce komai ba sai jinjina min kai da take yi alamun naje nayi abinda ta ce, ban kawo komai cikin zuciya ta ba, hakan yasa na shiga gidan baki na d'auke da sallama. A hakimce a parlour na tarar da mahaifiyar Haysam dashi kanshi a gefenta yana breakfast, kwanuka ne birjik a gaban shi da cup d'in tea a hannunsa alamun sha yake yi suna hira. Na had'iyi wani kakkauran yawu kafin na durkusa kasa ina gaida Hajiyar. Ta amsa min tana had'e rai bayan kuma lokacin da na shigo tararwa nayi tana ta dariya, shi kuwa ko bi takansa banyi ba na fara jeru bayani.

“Hajiya daman zuwa nayi amadadin Innar mu, zanyi mata aikin.”

Baki da hanci Haysam ya bud'e jin abinda yake tafe dani, ina kallansa ta gefen idanuna, najiyo muryar Hajiya tana cewa........

••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

_*SHAFI NA SHA UKU_*

•••

“Daga ina kenan? Wacece Innar ku?.”

Mamaki ne ya mamaye fuska ta, Jin tambayar da take min. Tana nufin batasan Innar mu ba kenan ko kuwa wulakanci ne nasu na masu kudi? Gaba d’aya baki na sai yayi nauyi, Na kasa furta mata kalma d’aya. Haysam dake kusa da ita duk ya dubibi ce da alamun shima ya rasa yadda zai yi. Cigaba da cin abincin ta tayi, Kallo na na mayar kan abincin da suke ci. Sai hadiyar yawu na dinga yi. Rai na ya biya ba kadan ba gashi yunwa sai addabar ciki na take yi. Cikina sai kukan yunwa yake. Nasa hannu na na dafe shamilallen ciki na da babu komai cikin sa tun abincin daren jia. Dagowa tayi ta dube ni tana karkada kafafu, Hannun ta rike da fok dauke da dankalin turawa da kwai, ‘Mak’ot’ na hadiye yawun daya tsayamin a makogaro. Da cokalin ta shiga nuna ni tana yamutsa fuska,

“Ko kece wadda ku kazo da mai wankin mu kwanaki?”

Jiki a sanyaye, Idanuwa na kawo ruwan hawaye na dube ta,

“Eh ni ce!”

“Ni fa gaskia nagaji da halin uwar ki. Yo tazo fa duk tayi yaushi a jeme kamar zata fa’di. Nace mata mu munsamu mai yi mana wanki da guga tun daga kauye aka dakko shi. Nace taje na sallame ta, Kudin aikin ta kuma zan bayar akawo mata, Amman shine ta turo ki?”

Ajiyar zucia naja na sauke, Ina mamakin yadda masu shi suke daukar kansu. Bayan duk takai ta kare dai a rami Iri d’aya za’a sa mu. Shin meye na takamar dan Allah ya azurta ta ka dinga wulak’anta na kasa da kai.? Na duba na hango yanxu idan nai fushi na tafi ba inda zan samo mana abincin da zamu ci. K’asa nai da kai na ganin yadda Haysam ya zubamin na mujiya,

“Kiyi hak’uri Hajja! Yau Innar mu tatashi ne babu lapia shi yasa. Idan da akwai abunda za’a miki yanzun sai nayi.”

“Masu aikin yanzu sai da tsaro, Yanzu mutum zai yi shekararriyar ajiya, Amman rana d’aya yan aiki sai su sace shi.”

Shiru nayi kai na a kasa ina mamakin maganar ta. Sai data dau lokaci kafin ta dube ni,

“Akwai kayan ciki na(undies ) dina a daki ki wanke mun su, Sannan kar dai kiyi min ‘dan hali (sata) Domin ba zan lamunta ba. Biyo ni”

Mikewa tai ta fara hawa benen sama na bita a baya, Haysam sai ya zama tamkar mutum-mutumi domin tun sanda nazo ya tsaya da cin abinci yana kallo na. Wani tankamemen daki muka shiga, Tsayawa na fada muku tsaruwar sama bata lokaci ne. Komai yaji babu k’arya. Durowar dake shake da kaya ta bude, Sai da idanuwa na suka kusa fad’owa saboda ganin yadda take a hargitse. Kayan ta duk a dukunkune wasu akan wasu. Kasan durowar ta janyo, Kayan ciki ne kawai a ciki fal. Wando panties, Siket gajere, bireziyoyi fal sun nadi datti. Wandunan har da wanda jinin al’ada ya ‘bata duk akwai su. Da ‘kafa ta turo min su gabana tana nuna min bandakin dake cikin dakin da hannu,

“Ga bandakin nan, Akwai ruwa da komai aciki, Ki wanke su sosai su wanku yanzu.”

“Toh hajia”

Na fada ina durkusawa hade da dibar kayan a kasa, Ita kuma ta sauka tana wake-wake. Ciki na sai ‘karar yunwa yake yi. K’irjina kuwa har wani zafi yake yi min. Da alamun olsa tace zata tashi domin dukkanin mu muna da ita sakamakon rashin samun ishasshen abinci da bama yi.

Bandakin na shiga, Dankari makari! Babu ce kawai babu. Gaba d’aya kai na sai ya juye, Domin ko na gwaggo Aminatu da nake ganin ya hadu bai kai rabin kwatan wannan ba. Kwamin wankan da wajen wanke hannun ma kadai abun kallo ne. Na dubi wajen kunna famfon na rasa. Na shiga kokarin bude shi na kasa. Gudun kar na lalata musu yasa na juya na sauka domin tambayar ta yadda ake yi, Haysam na kan kujera mai kallon matattakalar bene ya zuba ido, Hajian su kuma tana zaune akan kujera mai kallon tasa, Sake sunkuyar da kansa yai yana kallo na ‘kasa-k’asa. Kayan takaici! Na fada a zuciata ina ‘k’arasawa daga nesa na tsaya, Wani banzan kallo ta watsamin na ya haka? Cikin inda-inda na shiga nuna benen,

“Uhm wannan”

“Wannan me? Ya haka? Me kika aikatamin a daki?”

“Ba-ba komai! Dama famfon ne ban iya kunnawa ba.”

Dogon tsaki taja ta sauke tana yamutsa fuska. Da sauri Haysam ya mike yana sosa k’eya, kallon sa hajian tayi tana murmushi,

“Ina kuma zaka auta na?!”

“Umma sama zani na dan kwanta.”

“Toh dan kunnawa bagidajiyar nan famfon bata iya ba. Ko meye abun wahala oho?”

Kamar zai yi kuka haka yai rau-rau da idanu, Da alamun beji dad’in yadda ta kira ni ba. Haye saman benen yai cikin sauri, Nabi bayan sa a hankali ina nanata kalmar data kirani da ita. Ina shiga dakin na ganshi a tsaye ya harde hannuwa, Ya narkar da idanuwansa a kaina yana min wani shegen kallo. ‘Dan iska! na fada ina zura hannuwa na na dago hijabi na don karya kallemin na ALLAH ya isa. Cikin band’akin na shige bakina d’auke da addu’a’. Shigowa yayi yana murmushi.

“Ya zan kunna?”

Na tambaye shi, Domin so nake ya fice na karasa aikin gaba na. Matsowa yai kusa dani na ja baya.

“Matsoraciya!”

Ya fa’da yana kunnamin famfon. So nake ya fita amma yaki fita yaja baya yana harde hannuwan sa,

“Ba gaisuwa?”

Ya tambaye ni yana murmushi, Wani kallo na watsa masa na cigaba da tara ruwan wankin da zanyi a bokiti.

“Na zo na taya ki?”

Ya sake fada a karo na biyu yana matsowa wajen da zanyi wankin, cikin sauri na girgiza kai na.

“A’a Ya Haysam! Nagode.”

“Saura gaisuwa. Tunda sai da na roka.”

“Ina kwana?!”

“Alhamdulillah Mine! Lokaci yana ta tafiya fa baki gayamin matsayina ba. Ko kawai na fara zuwa.?”

“A’a Ya Haysam! Kawu nama yace na dakatar da kai tukun.”

Ware idanu yai yana kallo na cike da tsantsar mamaki,

“Meyasa? Shin nayi wani laifin?”

“A’ah!”

Na fada a sanyaye ina saka bireziyoyin a ruwa dan fara wanke su saboda yawanci farare ne kuma sunyi dauda. Kamar yayi kuka haka yayi rau-rau da idanu cikin rawar murya ya dube ni,

“Meyasa? Uhm? Mine? Kiyi magana dan Allah?”

Bansan meyasa ba kawai sai naji ya bani tausayi, Ina ya me son ka? Ajiyar zucia naja na sauke,

“Babu komai, Kawai dai yace sai nan gaba kadan.”

Na fadi hakan ina sharce gumin da nake yi. Jiki a sanyaye ya fice yana rufomin k’ofar. Sai da nayi wa kayan wankin nan wanki biyar biyar dauraya biyar biyar. Domin sun nad’i datti ga tsami dake tashi daga cikin su. Yar wayata dake mak’ale a zanina na zaro ina duba lokaci sha biyu saura kwata. Har yanzu bamu ci abincin safe ba. Lokaci d’aya innar mu da autar mu suka fadomin a rai. Ko awane yanayi suke.? Innar mu ba lapia ga autar mu zata tashi taga babu abinci. Duk da ba yau farau ba amman kwanakin nan muna samu mu ci mu sha babu laifi.

A bokiti na zuba su, Sun yi ‘kal dasu suna sheki. Fita nayi ina neman inda zan shanya su. Zaune Haysam yake hannun sa na dama yasa ya dafe kansa. Wata k’ofa na hango da alamun baranda ce dauke da abun shanya da dan abunda ake sawa yake rik’e su kada su fado. Shanya su nai bayan na karkade su. Kamar wadda kwai ya fashewa aciki haka na sauka kasan banbi takan mayen kallon da Haysam ke bina dashi ba. Hajia Husna na hakimce a doguwar kujera tana danna waya, durk’usa wa nayi daga nesa,

“Na gama Hajia.”

“Kin tabbata sun wanku?!”

“Eh na wanke sosai..”

“Toh shikenan zaki iya tafiya.”

Kasa mikewa nai. Domin idan na tafi na koma hannu biyu gidah me zamu ci? Ga Innar mu ba lapia zazzabi ya rufe ta. Kallo na tayi tana tabe baki,

“Akwai wani abunne?”

“Eh.. Abinci!”

“Ni zan baki abincin?”

Ta fada tana watsamin wani wulakantaccen kallo. Kada kai na nayi alamun a’a,

“Zan kai wa Innar mune na baro ta ba lapia.”

Siririn tsaki taja. Cikin dan daga murya ta shiga kwararo sunan Inna Rabi. Da azama inna rabin ta shigo ta dur’kusa cikin azama.

“Gani hajia.”

“Bawa yarinyar nan abincin nan.”

“Toh Hajia.”

“Mungode Allah ya kara bud’i.”

Bata ce uffan ba sai ma nuni da tayi min da hannu alamar naje kawai. Ina jiyo takun Haysam daga kafar bene yana sakkowa,

“Sai ina kuma auta?”

“Zan rage gashin kai na ne.”

“Adawo lapia. An gama maka soup din fa. Ba yanzun zaka ci ba?”

“Eh Ummah sai na dawo.”

Ficewa nayi nabi bayan Inna Rabi shi kuma ya fita daga gidan. Kitchen muka shiga. Sai kamshin tafashen nama yake, Ina rakube ni dai a gefen kofa. Ina kallon Inna Rabi tana kalle kalle, Kafin ta juye wani abinci acikin leda baka ta mikomin, Hannu biyu nasa na karba ina rissinawa,

“Kiyi hak’uri ‘yar nan. Abincin da tace abaki kenan. Kinsan nama da hakki, Gashi yanzu idan na dauka na baki zata gane domin ta gama irgasu kafin a dafa. Kiyi hak’uri kinsan shi nama hakk’i ne dashi..”

“La babu komai Inna Rabi. Ni abincin yafiye min, Domin zamu ci mu koshi. Allah ya saka da alkhairi.”

“Ameen ALLAH ya azurta mu ‘yar nan. Ki gayar da Innar taku. Kiyi mata ya jiki.”

“Ameen. Zata ji In Sha ALLAH!”

Ficewa nayi da sauri daga gidan. Fatana na karasa gidah kawai Innar mu da autar mu suci abinci ganin rana ta hudo. Ta shagon Chibuzor me kyamis na tsaya ina tunanin na bashi wayar hannu na ya bani maganin zazza’bi na kai wa Innar mu. Kyamis din na shiga na jira har layi yazo kai na.

“Chibuzor ya gidah?”

“Laffia batoulu! Kene ba laffia?”

“Lapia lou! Dan Allah temako na zaka yi.”

“Ina jin ki”

“Dan Allah maganin zazzabi na manya zaka hada min dana mura. Amma...”

“Ehen ya akai?”

“Amma zan bada jinginar waya ta. Idan na samu kudin sai na kawo ka bani wayar.”

Dan jim yayi kafin ya mik’o hannun sa alamun na bashi wayar, Domin yasan halin kuncin rayuwar da muke yi agidan mu. Mika masa nayi ya karb’a yana jujjuya ta. Zura ta yai a aljihun sa. Ya daddakko min magungunan ya mikomin, Bayan ya rubuta kowanne adadin da za’a sha. Cike da murna na karba nayi hanyar gidah. Fatana Innar mu tasha ta warke, Cikin sauri na isa layin mu. Ina zuwa kofar gidah zan shige naji yo ana kiran sunana cikin muryar da ko a mafarki aka kira ni zan gane ta waye. Juyawa nai, Tabbas shine! Kamar sa da zatin k’irar sa kai har ma da sautin muryar sa ba zasu taba gushewa a kwakwalwata ba.....
__
Ba yawa ma hade gobe IN SHA ALLAH👏🏻😍❤️


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8

*BATOUL WA HAYSAM*

*NA*

*HANSAI MAI AWARA*

_*1️⃣4️⃣*

•••

Jiki na har rawa yake, Da sauri na koma inda yake a tsaye yana sallamar mai mashin daya sauke shi. Bansan sanda na kai masa runguma ba.

“Yayan mu...”

“Batoul din mu.”

Ya amsa ni yana murmushi. Gaba d’aya ya canza yayi haske. Jikin sa ya murmure yayi kalau dashi, Gaba d’aya tamkar an ‘kara masa cikar halitta. Bacco din jaka ce a hannun sa shudiya, Dayan hannun kuma ledojin viva ne shake da kaya.

“Yayan mu barka da dawowa.”

Na karasa fada ina daukar ledojin gefan sa, Ya riko bacco din a hannun hagun sa, Kafadar hannun daman sa kuma jaka ce yar goyo, Ya goya ta ta gefe. Muna tafe muna yar hira haka muka shiga zauren gidan mu bakunan mu dauke da sallama.

*GIDAN MATA TARA*

Da Bintalo muka fara cin karo taci kwaliyya kamar bazawar akuya. Bakin nan yasha jambaki wanda ake cewa ‘gyatuma rad’au.’ Tana ganin mu mun taho muna murmushi muna magana ta hau buga salati. Yadda kukasan ance wani ya rasu haka ta rafka ihu tana sallallami. Tuni yan gidan mu suka firfito yadda kuka san ana kada ‘kararrawar sanarwa haka manya da yara suka fito, Kowa ya hangi yayan mu sai kaga sun koma gefe suna magana ‘kasa ‘kasa. Usaiba na ganin mu ta taho a guje tana taka rawa,

“Kutsin uban can kayya kai, Yau wacce rana ce? Laraba ce tabawa ranar samu. Ranar albarka mai kawo alheri. Najibu ashe kai ne zaka iso? Shi yasa naji yanayin gaba ki d’aya ya can za. A hayye kayya kai..”

Ta karasa fada tana sakin gud’a: ayyiririririririrrururueurue. Bintalo ta ja tsaki ta sauke tana susar diddigaggen kanta. Ni da Yayan mu kawai sai muka zubawa sarautar Allah idanu. Musanman ni da ke da ayyana tarin tambayoyi kala kala a zucia ta. Shin sun bashi damar ya dawo ne ko kuwa gamon kansa yabi ya dawo? Ina cikin tunani naji an bugo kofar bandaki. Kawu ila ne ya fito yana baje hannuwa yana mammatse idanu. Da alamun kashi yayi. Domin sai baje kofofin hancin sa yake yana wani bubbuda wa irin ‘kauran nan. Bintalo ta sake sakin salati tana yiwa Kawu ila signa na ya jiyo fa ga Yayan mu. Shi kuwa ila shigewa yayi dakin sa yana dafe ciki da alamun katsa masa yake yi. Kilan ko ganin mu beyi ba. Da sauri kuma ya sa kai ya fice a hargitse. Gaggayshe su Yayan mu yayi, Wasun su suka amsa wasu suka share shi. Muka haura sama abin mu, Domin inda sabo mun saba da rayuwar gidan mu. Wadda ake yinta tamkar gidan haya mai dauke da yaruka kala-kala. Dakin mu muka shiga dauke da sallama. Innar mu ta cukwikwiye cikin hijabin ta, Autar mu kuma ta tasa tukunyar jia agaba tana cin ‘kanzon ciki domin tun jia bamu saka komai a bakin mu ba. Tana ganin Yayan mu ta ‘dane jikin sa tana murna,

“Yayan mu...”

Shima rungumeta yayi yana daria.

“Autar mu! Haka kika kara girma? Iyye yanzu ajin ki nawa?”

“Firamare fayib.”

“Masha Allah! Allah yasanya albarka a karatun ki.”

Innar mu ta dan daga hijabin ta tana duban mu. Idanun ta sun sake rinewa sunyi jajir. Jijiyoyin kanta sunyi rad’au rad’au dasu. Dak’yar ta mike tana dafe kanta. Da sauri Yayan mu ya durk’usa daga gefan ta,

“Sannu Innar mu! Baki da lapia dama?!”

“Eh wallahi zazzabi ya rufe ta. Innar mu sannu! Ga abincin na samo, Aminatu wanko tiren can ki kawo a juye”

Na karasa fada ina sunce kullin ledar abincin da Hajian Haysam tace Inna Rabi ta bani. Da gudu autar mu ta dauki tiren tayi kasa ta wanko shi.

“Sannu Innar mu! Allah ubangiji ya baki lapia yasa kaffara ne. Allah ya tashi kafadun ki Innar mu.”

“Amin wannan yaron.”

Tafada tana jingina da bango hade da rintse idanu cikin ciwo. Magungunan dana karb’o mata awajen chibuzor na dakko. Hade da ebo ruwa a kofin kan randar mu.

“Inna ga magungunan. Kici abinci sai ki sha.”

Karbar ledar magungunan tayi tana bina da kallon karin bayani.

“Aina kika samo su Uwata?”

“Innar mu awajen chibuzor me kyamis na karba. Na bashi jinginar wayata. Duk sanda Allah yasa muka samu sai na kai masa.”

Murmushi tayi cikin ciwo tana dafe kanta,

“Toh Allah ya kawo yadda za’ai. Amman da kinsani baki karbo ba. Na fa warke.”

Murmushi kawai nayi. Innar mu kenan. Kullum Idan tana rashin Lapia haka take cewa ta warke don kada ta daga mana hankali mu shiga cikin damuwa.

“Nawa ne magungunan? Ga chanji ki kai masa ki karb’o wayar taki”

Yayan mu ya fada yana ciro dari biyar a aljihun gaban rigar sa. Karba nayi hannu biyu cike da murna,

“Angode Yayan mu! Allah ya kara bud’i.”

“Ameeen.”

“Tab Yaya kaga yadda ka dawo kuwa, ALLAH ka zama dan gayu Yaya. Kano ta karb’e ka.”

Murmushi yayi yana shafa ‘k’eyar sa. Innar mu sai kallon sa take a sace. Domin bata iya hada idanu dashi saboda kunyar ‘dan fari da take yi.

“Haba? Ni kuwa ku nagani kun kara girma TubarkAllah! Innar mu cema naga ta dan rame kodan saboda bata da lapia ne.”

“Allah dai ya bata lapia.”

“Ameen Ya Rabbi.”

Autar mu ta kawo tiren sai rawa jikin ta yake saboda tsabar yunwa. Juye abincin nayi gaba dayan sa. Kwananniyar jalof ce sai tashin tsami take yi. Gaban Innar mu na kai ta. Yayan mu sai kallon mu yake cikin so da k’auna ta yan uwantaka. Caccakuna Innar mu tayi ta bar mana. Mu kuwa nida autar mu handamar abar mu muka shiga yi muna korawa da ruwa. Saboda yunwar da take addabar cikin mu, Cikin kankanin lokaci muka lakume taliyar nan tatas. Muka lallashe hannayen mu. Babbalowa Innar mu magungunan Yayan mu yayi ta hahhadiya da ruwa. Cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ta. Ganin haka yasanya na kwashi tukunyar da autar mu ta kankare kanzo da tiren da muka ci abinci yanzu nayi kasa dashi dan wankewa. Ina sauka kasa nai kichibus da Bintalo da Kawu ila sun shigo daga waje. Da alamun nemo shi taje tayi ta kira shi. Ba zancen zuwa biki tuni ta ajiye shi agefe. Tayi wuri-wuri da ita gaba d’aya alamun rashin gaskia sun bayyana a tattare da ita. Wanke kayan na shiga yi ina kara sunkuyar da idanu na. Domin muddin idanuna ya hadu da nasu yanzu zasu fara aibata min shi suna tanka halitta

Please Login or Register in order to submit comment