Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

office d'ina.''_

Nayi murmushi bayan na karanta, cikin rai na nace Mrs Suleiman bata san na samu aiki ba, ina ji a jikina cewar kila aiki take son samar min itama, saboda tun ina degree take cewa insha Allahu zata samar min aiki, bayan na kammala masters na sanar mata nan ma ta min fatan alkairi tare da cewa zata tuntub'eni wani lokacin. Ni kuma dana samu aikin teaching d'in nan sam ban sanar da ita ba, amman a raina na kudiri aniyar zuwa goben wato ABU d'in na kai mata takardun sai na gaya mata ina aiki.

Da muka tashi daga school na nufi gida, yau kam gidan mu babu hayaniya na shiga cike da kasaita har wata iska nake ji tana shiga jikina. Nayi mana sha'awar ina ma mu kadai ne a gidan mu, nasan da tuni nafi haka kyau da kiba, amman su Bintalo ba zasu barni ba kodan shegunan bakunan su. Na shiga cikin d'aki Innar mu ta gama abinci sai kamshi yake na kifi, na zauna ina cewa.

“Washh Inna yau kam na gaji.”

“Toh sannunki sai ki huta ai kiyi sallah.”

“Tom Inna. Gashi gobe ma zanje can makaranta ana nema na nakai takardu.”

Inna ta tsaya da abinda take yi tana kallo na tace.

“Wacce makarantar kuma?”

“Inna can ABU Mrs Suleiman na nema na.”

“Allahu akubar, kedai taku tazo d'aya da wannan matar, toh ALLAH yasa alkairi ne yasa take nemanki.”

“Amin Inna, a ci gaba dayi mana addu'a insha Allahu alkairi ne.”

Daga haka muka danyi hira kafin na tashi naje nayi alwala, ina cikin yin sallah Yayan mu suka dawo shida Autar mu itama sun had'u ne tana dawowa daga makaranta. Shima na sanar dashi zuwa na can makaranta yayi min fatan alkairi har yace shine zai rakani. Da safe kuwa da wuri muka shirya nida Yayan mu muka tafi, bayan munje na shiga office d'inta shi kuma Yayan mu ya jira ni daga waje. Na shiga na gaida ita ta bani lemo da ruwa na jarka sannan ta karb'i takardun tace na tafi duk yadda ake ciki zanji. Haka nayi mata godiya bayan na sanar da ita ina koyarwa a primary tace dani ba komai naje zata nemeni, muka tafi ina bawa Yayan labari.

Bayan wata daya ina zaune ina shirya result d'in yara da suka yi exam sai ga kiran Mrs Suleiman, na gaida ita cike da girmamawa, kawai naji tace min na samu lecturing a nan cikin ABU samaru campus.......


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*28*


*SARQAQIYAR RAYUWA*
1🤩

Ina daga zaune ban san lokacin dana mik'e tsaye ba saboda tsabar farin ciki, nayi zaton ma kunnuwa nane basuji ba sosai, sai da na kuma tambayar Mrs Suleiman ta tabbatar min. Kamar a gabanta haka na durkusa tsakiyar d'akin mu ina ta zuba mata godiya da addu'o'i, har sai da ta katse dan kankin kanta. Innar mu ta tambaye ni abinda yake faruwa na sanar mata, itama ta dinga zambad'a addu'a. Yayan mu kuwa ban bari sai da ya dawo ba, a take na buga masa waya na fara sanar masa, Babu network inda yake sam bai ji me nake ce masa ba. Mi’kewa nai na zura hijabi,

“Innar mu bari na fadawa Yayan mu wannan daddadan labari.”

“Toh Allah ya temaka, Yasa a fara a sa’a.”

“Ameen Innar mu..”

Ina sauka matattakalar bene na jiyo muryar yayan mu daga zaure yana magana da kassim almajiri. Sai da ya shigo ciki a tsakar gidah na sanar dashi ina murna, Ban damu da ahalin dake tsakar gidan mu ba. Ai kuwa Yayan mu ya tayani murna sosai, Yan bakin ciki kuwa sai zund’e suke yi suna tsegumi a hankali.

Kawu Ishaq dake gefe yana alwala a bakin rijiya ya daga kai yana duban mu,

“Menene ne kuke ta murna kuna dashare hak’ora kamar gonar auduga?”

Yaya Najibu cikin fad’ad’a murmushin sa cike da girmamawa yace da Kawu Ishaq,

“Kawu ta samu babban aiki ne..”

“Ai me..?”

Cewar Kawu ila dake fitowa daga dakin sa yana sakin hamma. Sai da yai mika mai isar sa tukun sannan ya zura takalmi wari da wari hade da d’akko bokitin zaman sa ya zauna yana goge kunnen sa da dan yatsan sa karami,

“Ai me kace?”

Ya sake tambayar Yayan mu dake tsaye yana jiran sa. Ni kuwa jingina nayi ajikin bango ina dudduba waya ta,

“Nace ta samu babban aiki ne.”

Yayan mu ya sake fa’da masa. Kawu ila yaja dogon tsaki ya sauke yana karkada hannuwa,

“Kiramin kawunnin ku. Shikenan gandar-dar da ita sai ta zauna tana aiki babu batin aure a gaban ta? Yasin ba zata sab’uba..”

Yayan mu yayi murmushi yana gyara tsayuwar sa,

“Kawu ai komai lokaci ne.”

“Lokacin uban uban ka? Aina ake haka? Gandamemiyar budurwa ta zauna banda karatu babu abinda tasa a gaba? Ba za tai aure ba kenan. Ke Mari hau sama ki kirawomin sauran kawunnin ku.”

“Sittin ta ubangiji dai abin yayi yawa, Kuma duk Kaltume ce ta dora su a hanya..”

Bintalo ta fada tana watsa hannu baya cike da zuga. A sanyaye nace,

“Kema fa baba ga su Hinde nan agaban ki...”

“A hayye nanaye! Ni kike duba tsabar idanuna na kike gayawa haka? Ah lalle kin zama cikakkiya.”

Ba a dau lokaci ba Kawunnin mu dik suka hallara a tsakar gidah. Lalle ba karamar tijara za’ai ba. Fuska na murtuke ina cigaba da addua a zuciata domin a shirye nake da mai da martani ga duk kanin su wallahi. Kawu ila ya gyara murya yana nuna ni da yatsa,

“Ga tanan wai aiki ta samu. Dan tsohon munafunci ma ba gaya mana akai ba ji mukai a gari.”

Na murmusa kawai ina kallon sa da mamakin kalaman da yayi. Kawu Ishaq dake shimfida buhu zai yi sallah ya dube ni,

“Aina ne wajen aikin?”

“Koyarwa ce fa Kawu..”

“Ba koyarwar kike ba ko wata ce daban?”

“Eh Kawu... Ta jami’a ce wannan.”

“Jami’ah! A hayye nanaye. Sittin ta ubangiji yau ga gaye ba makilis. Kece zaki fara koyarwa a jami’a? Shin ta yaya ma kika samu aiki a jami’a?”

Banza nayi mata na cigaba da salatin da nake a zucia ta. Bintalo sai maganganu take yi ni kuwa nayi biris da ita, Su Kawu khamis sun biye mata suna tayata,

“Gaskia dai wannan zance babu shi a soke shi...”

Cewar Kawu Khamis, Kawu Dawood shi dai sakacen hakorin sa kawai yake yana daga kai. Kawu ila ya cika yayi fam. Ya dube ni shakeke yana yamutsa fuska,

“Kinsan kuwa shekarun ki nawa? Waton ba zaki aure ba sai neman duniya?..”

Kai na a kasa bance dashi komai ba na cigaba da wasa da kasan hijabi na. Shi ko kunya bayayi, Bayan dukkanin samari na shiya koremin su da sharri.

“Tab sittin ta ubangiji ta rena ka, Har kai kana magana tana yi maka shiru?”

Bintalo ta ceda Kawu ila haka cikin kururuwa, Kawu ila ya dankara min harara kafin yace,

“Ai wuyan ta ya isa yanka, Taga yanzu zata fimu arziki, Dama ta kere mu. Shiysa rainin ya ‘karu.”

“Kuyi hak’uri Kawu. Wallahi babu wanda na raina acikin ku.”

“Raini kuma ai kingama raina mu, Kinsan shekarun ki kuwa? Ke nan ba zaki aure bane ko kuwa kwantai kikai ba samari?”

Girgiza kai na nayi. Cike da murmushin yak’e nace,

“Kawu shekaruna ashirin da shida (26) kuma su Alawiyyah agaba dani suke..”

Bintalo ta saki guda tana buga zani hade da watsa hannu baya,

“Bashakka! Kwarai, Lalle yanzu kika fito da abunda ke zuciar ki. Dama sittin ta ubangiji tun ba yau ba nake da masaniyar da sa hannun ku a dagula lissafin rayuwar ‘yayana. Guda d’ayan dake gidan aure ma kun fiddo ta saboda ta tsone muku idanu.”

Murmushi nayi kawai ina wasa da wayar hannu na,

“Baba *ZATO* zunubi ne ko da ya zamto gaskia, Akan wane dalilin zamuje mu gurbata rayuwar yayan ki.? Yan uwanane fa na jini. Sannan ni wallahi tallahi hanyar malamai ma bamu sani ba ballantana mukai sunan ‘yayan ki.”

“Rufemin baki, Makira. Malam mai gobe da nisa sittin ta ubangiji yace dasa hannun kaltume da Ummita a tabarbarewar rayuwa ta da yarana.”

Bance komai ba, Saboda ba nida amsar jahilar maganar da take yi, Domin mu da ALLAH muka dogara, Shine zai yaye mana dukkanin lamurran mu. Haka dai Bintalo tai ta maganganun ta yan amshin shatan ta na taya ta. Kawu ila ya sake gyaran murya yana sakace da zaren taburma,

“Babu wani jami’a da zakije koyarwa, Idan kuwa kin tilasta toh zaki dinga bada wani sashe na kudi a albashin ki.”

Murmushi Yayan mu yayi yana kallo na kafin cike da girmamawa yace da Kawu ila,

“Babu damuwa Kawu, In Sha Allah hakan ba zai gagara ba. Allah ya dai ya kai mu lokacin da za’a fara biyan nasu.”

Bintalo ta buga tsaki hade da sab’ar mayafi tafi ce waje. Ni kuwa Yayan mu na cewa haka na haye sama abuna. Ina shiga da’ki na sanarwa Innar mu yadda akai, Har Yayan mu ya shigo shima muka cigaba da maganar,

“Wallahi Innar mu bakin cikine kawai sunga na fisu ilimi kuma Allah yana bani nasara a karatun nawa.”

Na fada ina girgiza kai na cike da takaici , Yayan mu yai murmushi

“Babu komai wanda ya isa yai yawa shi akeyiwa hassada. Zallar hassada ce gani sukai idan su kai wasa zaki fisu arziki. Kuma da yardar Allah sauran daukaka ma na gaba.”

“In Sha Allah kuwa! Allah ya daukaka mu baki d’aya Yayan mu.”

“Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum.”

Haka dai muka shiga hirar mu cike da so da kaunar juna. Na dafa mana taliya da kifin gwangwani muka ci a tare da Yayan mu da autar mu. Innar mu kuma taci nata ita kad’ai. Fankar da Yayan mu ya siyo sai wulwulawa take yi tana bamu iska. Domin tuni aka gyara mana wutar dakin mu. Munci sa’a kuma ana kawo wuta sosai babu lefi.

*WASHE-GARI*

*1st January, 2017.*

Bintalo taja majina hade da cigaba da yanka tuwon da take yi a faranti. Tana yi tana sakin tsaki a karo na ba adadi. ‘Kandas tuwon yake ba mai bare magi. ‘Yayan zabbau kuwa sun jeru su biyar suna binta da kallon tagama ta basu. Tsaki ta sake ja tana mai dankara musu harara,

“Sittin ta ubangiji yaran nan ko mayu sai haka. Sai kace masu cikin randa sam bakwa ‘koshi? Sittin ta ubangiji ko su’din kwano ba zan baku ba. Daga yau kowa ici da kansa a dakin nan.”

Hinde ta wangame baki tana hamma cike da yunwa. Dukawa tayi ta sab’i danta a baya ta zura hijabi. Alawiyyah dake numfarfashin ciwo ta dube ta dakyar tace,

“Ina zaki?”

“Bara zani! Zanci babu ne ni da ‘dana?”

Alawiyyah ta girgiza kai tana mai komawa kishingidar da tayi cikin ciwo. Bintalo ta mike da sauri ta fice da kwanon tuwon nata. Ranar dai kowannen su shi ya samawa kansa abincin safe. Da rana Bintalo ta zauna a kafar bene tana neman magana. Baba usaiba ta shiga yan wakokin ta tana yagawa Bintalo magana,

“Idan ta ‘karewa mutum shikenan kuma. Kusufa-kusufa zaka ganshi ya zauna yana neman magana. A hayye kayya kai.•

Bintalo taja tsaki tana mai da kanta gefe.

“Aikin banza.”

Baba Usaiba tai ta kyalkyalawa Bintalo daria, Irin dariyar nan mai sanya mutum kuka, Ta ‘kularwa sosai. Daga karshe Bintalo ta figi mayafi ta fice bayan ta kwararo rantsuwa ta direwa Usaiba kan zata sab’a mata. Ita kuwa usaiba dariya taita kyalkyala mata tana sake ‘kular da ita. A can gangare ta ha’du da Ruma, Suka tsaya suna gaisawa.

“Dama wajen ki zani fa.”

Bintalo tace da Ruma dake sake gyara zaman mayafin ta.

“Haba? Ai kuwa Allah yayi zamu hadu da munyi sab’ani..”

Bintalo taja gwauruwar ajiyar zucia ta sauke,

“Ruma ina cikin gararin rayuwa. Kinga in takaice miki zance dai na bar aiki a gidan Alhaji Kabeeru.”

Ruma ta gwale baki hade da jan Bintalo su koma inuwa. Cike da mamaki take duban Bintalo,

“Dagaske?”

“Sittin ta ubangiji kuwa..”

Bintalo ta shiga ha’da karya da rantsuwa tana gayawa Ruma. Ruma ta jajanta mata sosai,

“Toh yanzu ya za’ai Bintalo?”

“Sittin ta ubangiji Ruma bansani ba, Ba nida mafita. Ta ‘karemin, Abinci ma gagarar mu yake.”

Ruma ta kad’a kai tana tunani can ta nisa kafin tace,

“Zan cigito miki ko zaki samu wani gidan aikin. Yanzu dai idan zaki iya muje bakin kasuwa kya samo yan chanji ko ki zama uwar dashi.”

“Yauwa Ruma. Nagode.”

A tare suka taka har yar kasuwa. Ba ita ta dawo ba sai bayan isha’i. Hannun ta rike da biredi dan yanka-yanka da asusu ta karb’o na adashi. Ruma ta bata tace ta zama uwar ajiyar su. Idan karshen wata yayi anzo d’auka sai ta dauki zubin karshe itama, wato ladan ajiya kenan. ta haye bayan ta tsaya a band’aki ta kwarara fitsari. Tana shiga d’aki yaran zabbau suka yanyane ta. Kowanne yana jiran ta bashi. Harara ta daddankara musu tana mai basu uku uku,

“Dik wanda na bawa ya tashi yabar nan wajen. Shegun yara da kayuwa runtuma-runtuma.”

Kankace me tuni har sun lankwame suna sake zubawa Bintalo ido don ta kara musu. Karamin cikin su ya tafi wajen ta tinkis-tinkis yana kwakwalwar tasono, Domin kullum cikin kazanta suke, dikin-dikin dasu ba wanka bare wanki.

“Ban kohi ba. Ki k’aramin”

Bintalo taja tsaki tana hararar sa.

“Bazan kara ba. Marasa godiyar Allah. Kunsan yadda akai na samo shi ne? Zaka zo da wani runtumemen kanka wai baka koshi ba.”

Bintalo ta k’arasa fada hade da sakar masa rankwashi a kwanyar kansa, ji kake ‘kwas. Yaran ya hau kuka yana kururuwar yunwa. Sai da Bintalo taci tai nak sannan ta jifesu da sauran tana binsu da kwandon tsinantaka.

Cikin dare kunnuwana suka fara jiyomin tamkar ana sand’a, An wuce ta gaban dakin mu. Na rintse idanuna ina mai kwararo addu’ar tsari saboda dare mahutar bawa ne, Yayin da wanda bama gani kuma ke karakainan su. Gilmawar mutum naga ni da koriyar riga. Cike da fargaba na rintse idanu ina cigaba da adduar kariya. Ashe Yusha’u ne dan innatuwa ya shiga dakin Bintalo da sand’a. Suna kwance wasu kan wasu a dakin. Bintalo tayi bacci da Asusun a hannunta tana jan munshari tamkar bijimin sa. Ai kuwa Yusha’u ya zare asusun ya gudu. Da asubar fari Bintalo ta cika gidan mu da kururuwa da hargagi, Kai harda kumfar baki take tana watsa hannu baya hade da kwaso rantsuwa da zallar zagi marar surke.

“Sittin ta ubangiji duk barawo ko barauniyar data dau asusun nan sai ta bani shi, Wallahi tallahi ba yadda zanyi ba, Wato har fakar idona akai, Sai da aka bari dare yayi nayi nisa a bacci aka sad’ado aka dauke min shi, Sittin ta ubangiji ba yadda zanyi ba. A hayye yau ga gaye ba makilis, Munsan shafe shafe munsan mai. Sittin ta ubangiji ko gidan nan sai an sayar an biyani kudin mutane..”

Yan gidan mu su kai tsit, Kowa kallon ta yake. Ta zama kamar sabuwar tabi. Sai maimatawa take tana had’awa da zagi kala kala.

“Wai me aka dauke miki ne Bintalo?!”

Hansatu matar Kawu Dawood ta tambayeta tana zabga tagumi. Bintalo ta buga zani tana kwaso rantsuwa,

“Sittin ta ubangiji asusu ne na zubin adashen su Ruma kawata. Shine aka biyo dare aka sace shi. Kuma sittin ta ubangiji yan gidannan ne. Kuma sai an biya ni a yau. Tab yau ga gaye ba makilis. Sittin ta ubangiji ba zata sab’uba. A’hayye...”

Idar da sallata kenan na futo ina mamakin abunda take fada, Tabbs da cikin dare naga wulgawar mutum da koren kaya. Na tsaya ina bin yan gidan mu da kallo. Ai kuwa na hango Yusha’u da koriyar rigar shadda sai sunne kai yake abinka da maras gaskiya.

“Kuna ina ahalin gidan mata tara? Sittin ta ubangiji sai an biyani kudi na.”

Baba usaiba dake alwala a kasa taja tsaki tana buga zani,

“Wanda ya sace dai shi zai biya ki. Amman billahil lazi banci nanin ba nanin ba zata ci ni ba. A hayye kayya kai..”

Bintalo ta shatalo kafar usaiba suka fara dambe, Ni kuwa na shiga daki na d’akko bokitin wankan mu na sauka k’asa nayo wanka na. Domin da wuri nake son zuwa makaranta saboda sanin gurbin da aka bani. Wanka na na fallo na koma daki. Ina jiyo hargagiyar su sai yi akeyi. Fata na dai Yusha’u yace shine ya bata kawai ba sai anyi tone-tone ba. Innar mu na gaydar na fara kintsawa ina azkhar. Har wajen bakwai saura suna fada banajin akwai wanda yai sallah acikin yan kallon nan ma. Na karya kumallo na. Inata sauri na fara shafe jiki na da tururuka na dana sissiyo masu sanyin kamshi. Sanye nake cikin royal blue din doguwar rigar material dinkin A shape. Na yane kaina da mayafi silver, Takalmi na ma da jakata duk silver ne. Banyi wata kwalliya ba kawai dai na dan shafa hoda da man lebe na taje girata. Nayi kyau sosai, Tamkar ka dauke ni ka gudu. Saboda yanzu Alhamdulillah akwai ishasshen abinci ga wuta muna kunna fanka, Dan mai na da sabulu suma suna karawa fatata sheki. Light brown color dina ta kara turuwa sosai. Hakama kirar jiki na komai dai dai, Domin tamkar ni na kera abuna. I look younger than my age. Domin idan ka kalle ni zaka bani shekaru ‘kasa da nawa. Murmushi nai bayan na kalli kai na ta mudubi na dubi Innar mu dake lazumi,

“Innar mu komai yayi?”

“Komai yayi uwa ta. Tamkar zaki gasar zaben kyau. Masha Allahu! Allah ya bada nasara akan abunda akaje yi. Yasa ki fara a sa’a.”

Nan danan gaba na ya fadi tunowa da nai da dimbin daliban da zan koyar. Dubada yadda muma aka koyar damu. Na hadiye yawun daya tsayamin na tsoro kafin nayi karfin halin cewar,

“Ameen dai Innar mu. Ki tayani da addua. Har gabana ya fara fa’duwa wallahi.”

“In Sha Allah alkhairi ne. Allah ya shiga lamurran ki. Kede ki kara tsare mutuncin ki kawai. Allah yabada sa’a.”

“Ameen Innar mu. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Allah ya jikan baba da sauran magabatan mu.”

“Ameen Ya ALLAH..”

Kasa na fara sauka ina kallon Yusha’u dake dibar ruwa a rijiya. Zan fice kenan Bintalo ta janyo ni tana kwaso rantsuwa tana direwa,

“Wa? Ina zaki? Ai baki ga ta tafiya ba ‘yar nan. Sittin ta ubangiji ko dai kuyi karo karo ku biya kudin mutane ko kuma a sayar da gidan nan a biyani kudin mutane.”

Agogo na na kalla dake daure a hannu na ina girgiza kai,

“Baba ni ban daukar miki kudi ba wallahi, Sauri nake zan tafi dan Allah ki sake ni kada na makara.”

Bintalo ta callara kara tana buga zani,

“Sittin ta ubangiji babu inda zaki ko hansatu dake fita yawon bara yau na hana ta saboda sai an biyani kudin mutane sannan kowa keda kwanciyar hankali..”

Baba usaiba ta taka rawa tana gud’a,

“Ayyiririririr! A hayye kayya kai! Nifa banyadda ba sai dai idan acikin yayan ki ne wata ta d’auka.”

“Sittin ta ubangiji babu wadda ta dauka acikin su. Asusu dauke shi aka yi. Cikin dare aka sad’ad’o aka dauke min shi., Barayin banza, Barayin wofi.”

Haka su kaita ja’inja, Ta fada, Baba usaiba ta maida martani. Sauran yan gidan na kallon su kamar wasan kwaikwayo. Ganin zata sa na makara yasa naja tsaki ina kallon Yusha’u.

“Kai Yusha’u kune bakwa baccin wuri. Bakuga wanda ya dauka ba.”

Saurin girgiza kai yayi yana dora bokitin ruwa a kansa. Na sake jan wani tsakin a karo na biyu ina kallon agogo na.

“Baba ni dai cikin dare naga wulgawar mutun da koren kaya..”

Bintalo ta buga zani tana sallallami, Ta kara matsowa kusa da ni jin karin bayani, Nayi baya ina dan rufe hanci na jin tashin warin da take yi.

“Wane barawon ne kikaga wulgawar sa? Mace ko namiji? Fad’amin yanzun nan na zugewa mutum ta zuge. Sittin ta ubangiji duk girman sa kuwa.”

Ni kuwa nayi murmushi kawai ina kallon Yusha’u. Har ga Allah banason na tonashi nafuso ya dakko ya bata abinta. Amma yak’i magana. Kuma yanzu duk yadda zata kai ta kawo kan yan dakin mu za’a ‘kakaba mana sata bamuji ba bamu gani ba.

“Ni dai koren kaya nagani. Kuma dik wurin nan babu mai koren kaya fyace Yusha’u.”

Innatuwa tai kukan kura ta tsaya a gaba na tana huci,

“Mak’aryaciyar banza da wofi. Kun sace mata shine zaki kakaba masa sharri? Wallahi karya take Bintalo. Duk yadda akai sai dai idan Najibu ne ya dauka.”

Bintalo ta callara guda tana watsa hannu baya,

“Nide babu ruwana, Sittin ta ubangiji a biyani kawai. Amma dai tunda taga koren kaya, Wajibi ne ai yar caje anma takan kayan Yusha’u za’a fara..”

Innatuwa tai kukan kura hade da buga tsalle ta dire kan ai ba Yusha’u ne yai sata ba sharri nake masa. Ai kuwa dai Bintalo ta bangaje Yusha’u daya runtuma da gudu ya rungume buhun kayan sa. Wafcewa tai ta zazzage a kasa sai ga asusun ta ya fado. Ta buga tsalle tana kururuwa tare da faffallawa Yusha’u maruka kala biyar ya zube yana kuka a kasa. Innatuwa tayo kai na tana haki naja gefe ina murmushi,

“Sai dai idan kece kika sace kika saka masa acikin k...”

Yusha’u ya mike yana kuka ya dakatar da innatuwa.

“Yasin yazeedu ne ya koya min shi dasu Fareed kancewar idan na dakko za’a raba dai dai. Hakama su kai da wayar Innar su Batoul shekarun baya. Kuma harna makota suke dauka dana shaguna..”

Nayi murmushi kawai jin kalaman sa na karshe. Innatuwa sai dankara min harara take yi. Ni kuwa hamdalah nayi domin taga sakayya akan bakaken maganganun da take gasamin hade da sharrin da take binmu dashi, Sai gashi dan ta na cikin ta ‘barawo ne. Ai kuwa Bintalo tayi wata uwar kara ta shiga bubbugawa Kawu ila kofa,

“A hayye yau ga gaye ba makilis. Toh Fitonan ilyasu, Kai ma Dawood ka sakko.Munafukan banza da wofi. Ashe kunsan ‘yayan kune suke sace sace shiysa tunda na fara maganganuna babu wanda ya fito acikin ku.? Toh sittin ta ubangiji anyi na farko anyi na karshe. Ku jawa barayin ‘yayan ku kunne kada su kuskura su kara maimaita rana irin ta yau. Domin idan aka kara karo na biyu sittin ta ubangiji duka sai na makaku a kotu.”

Kawu ila ya fito daga dakin sa hannun sa na hagu dauke da bokitin zaman sa. Ya wangale bakin sa ya saki hamma yana sosa ciki. Ni kuwa sauri nayi nai ficewa ta na barsu suna ta ruguntsumi. Har titin yar kasuwa ana jiyo hayaniyar su. Ni dai mashin na hau ya kai ni inda ake lodin samaru campus. Bakina dauke da adduar samun nasara a rayuwar mu, da karatuna dama sabuwar shekarar 2017 da muka shiga....


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*29*


*IGIYAR ZATO....❤️💫*


*UNGUWAR BOMO*

Da d'an gudu-gudu ya sakko daga d'an steps d'in da zai shigar da kai sashen Haj Ahlaam, hannunsa rik'e da jota da biro ya nufi wajan da ake ajiye motoci. Cikin sauri sabon driver d'in da aka kawo musu gidan

Please Login or Register in order to submit comment