Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d’aya exams din tazo musu cikin sauki da kuma annushuwa......

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[8/21, 7:30 PM] Nadady: *35*

*IGZ*

•. •. •

*NAKORE POLICE STATION*

Wani basamuden murdadden mutumi ne ya shiga laftawa Kawu ila wayar inji a jikin sa. Ji kake ‘rigijib-jib, Fas,Tas. Jikin sa yayi rud’u-rud’u da shatin duka ya faffashe. Gaba d’aya ya rame ya jeme idanuwan sa tamkar na mujiya sun ‘kara shigewa ciki, Sai yawun wahala ne ke dalala daga bakin sa. Mutumin ya sake zuba masa wani dukan yana huci,

“Kaga kafaffen tsoho. Nace ina ku’dade da takardar filin Alhaji Usman suke?”

Kawu ila ya sau fitsari a zaune ji kake ‘Tsiiii. Cikin wata irin wahalalliyar murya ya dafe kansa yana sakin hawaye,

“Babu wallahi. Ai ca yai ya bani. Kuma na baka ta rabaka da kayan ka...”

Wani dukan ya sake zuba masa yana zare idanu,

“Aiyi kukai abisa alqawari. Kuma baka cika masa alqawarin sa ba ka sab’a. Wato daka fito dasu ka gwammace zaman nan ana narkarka ko?”

‘Jib, Rigijib, Ragas, Tas, Was.’
Wannan sune sautukan na jakin da ake lakadawa Kawu ila.

“Wayyo! Wayyo! Babu na auno abinci dasu.”

“Ya maganar filin.”

“Babu...”

“Amsar dai kenan?”

Haka yaita dukan Kawu ila yana tambayar sa. Amma Kawu ila sai wallacewa yake yana kwararo rantsuwar babu su ya auno abinci. Cikin kuka yaja majina yana sosa bayan sa,

“Allah ya saka min..”

“Kace me?”

“Ca.. Ca nai Allah ya saka maka da alkhairi.”

Tsaki ofisan yaja ya fice. Kawu ila ya gyara zaman sa dakyar. Gaba d’aya yayi jina jina da jini. Ya muskuta yana kukan radadi,

“Billahil lazi sai nayiwa ahalin gidan mata tara rashin mutinci. Ni za’a yiwa kaskanci? Babu wanda ya fito dani?”

Ya sake kwafa yana sakin wani fitsarin a zaune. ‘Kulululu’ Cikin sa ya shiga kukan yunwa yana neman agajin abinci.

*GIDAN MATA TARA*

Gaba d’aya na sake yin fresh, Jiki na ya murmure. Zaune nake akan taburmar dakin mu ina yanka salatip (seal-tape) din da zanyi lalle dashi. A hankali nake bin wakar dana sanya a waya ta,

‘Ka iya tsaro labari wanda yake sa annuri idan da cuta kai ne magani. Zuciya garwashi ruri dan kuwa tayo tasiri soyayyah ta tuna dani.. Ina ta guje guje. Na rasa shin ina zanaje? Kira ni kacemin inzo muje soyayyah tayiwa zuciya ah’ah’ah...🎶’

Ni kadai ce a dakin babu kowa. Domin Innar mu da autar mu da Yayan mu sun tafi wajen Gwaggo Aminatu. Don kai mata xiyara da kuma shaida mata halin da Kawu ila yake ciki, Domin kaf yan gidan mu an rasa wanda zai gaya mata. Sai yanzu nake mamakin anya ma suna son Kawu ilan kuwa? Domin sunfi damawa dashi Lokacin da yake cikin halin samu. Yanzu kuwa da halin rashi ya riskeshi sai suka guje shi. Lalle duniya budurwar wawa ce. Mu din da bayaso mune ke neman hanyar da zamu fito dashi.

Ina gama yayyankawa na ajiye plate din a gefe domin so nake nayi cikin dare na kwana dashi. Kakkabe rigata nayi na tattare wajen dana ‘bata. Har na dakko takardun students xan cigaba da marking sai wayata ta yi kara alamun sak’o ya shigo. Duaka nayi ina murmushi ganin Haysam ne. Shi dai sam baya gajiya da kira da turo sakonni.

“Assalamu Alaiki Ya Habibaty! Mine! SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata...”

Murmushi nai kawai bayan na kammala karantawa, Ajiye wayar nai na sabi kayan undies dina da zan wanke. K’asa na sauka ina kallon sauran yan gidan mu dake hidindimin su kamar ko yaushe. Zancen sungumar Kawu ila da akayi kuwa babu shi. Domin babu wanda ya nuna alamun damuwa acikin su. Ruwa na debo a rijiya na fara wanke su ina dauraye wa. Bintalo ta sakko da sauri tana saka hijabi,

“Yauwa yama sunan dan shafaffen abunnan mai kamar marar kwashe tuwo da yake da ‘bula a tsakiyar sa?”

Na duddubi gabas da yamma ganin ko da wani take? Ashe dani take. Mikewa nai daga durkushen da nake ina wanki. Na d’aga kai na sama alamun tunano ko me take nufi. Dan wallahi na manta menene abu mai kamar marar kwashe tuwo mai bula a tsakiyar sa. Na girgiza kai ina kallon ta,

“Bangane ba Baba..”

“Abun nan da naga kina sayowa naci dinnan. Na shagon Nata’ala. Murmushi nayi tunowa da ko menene,

“Yadda kika fasalta ne kamar wani abun daban..”

“Yasunan sa. Fad’amin da sauri ci zanyi na kora da abu mai sanyi.”

“Doughnut sunan sa..”

Bintalo ta shiga xare idanu tana sake muskutowa kusa dani. Hannun ta na dama tana aikin sosa takashi. Kasa kasa tace dani,

“Maimata min du.. me?”

“dow-nuht ake cewa..”

Na karasa fada ina gaya mata yadda zata ce. Bintalo ta watsa hannu baya tana gasamin harara daga abun arziki,

“Fadamin sunan sa da hausa”

“Bansani ba gaskia..”

Tsaki taja tana sakin gud’a. Ta watsa hannu baya tana shewa,

“A hayye yauga gaye ba makilis. Wato saboda zan siya naci shine zakimin bakin ciki ko? Wani bakisan sunan sa da hausa ba. Toh baturen ma na hadasu na zage tas. A hayye nanaye! Sittin ta ubangiji ci ya zamto dole. Mtscew.”

Ta karasa tana sakin tsaki hade da kademin zani a fuska. Nayi murmushi kawai na juya na cigaba da wanki na. Bata jimaba kuwa ta dawo hannun ta d’auke da leda shak’e dashi. Neman magana ta fara yi. Ta bararraje a matattakar bene tana ci tana jifan maganganu,

““Allah sarki dad’i. Allah gwanin hikima inji barawon zuma. Jakar ubancan kai! Sittin ta ubangiji wanga abu akwai da’di, Ga laushi ga dadi. A hayye! Yau ga gaye ba makilis. Sittin ta ubangiji duk mai bakin ciki sai dai ya mutu..”

Nayi murmushi ina karkade shanyar kaya na. Yayan gidan mu suka zuba mata na mujiya suna jiran ta babbasu. Amma haka ta takarkare ta cinye tana nishi. Wasu daga ciki suka sa kuka ta bisu da rankwashi a kwanyar kai. Dakin shanyar mu na shiga wato dakin da aka tashi Rabi’atu matar kawun mu. Na shanya kayan nawa na haye sama. Ina hankalce da Bintalo dake rike da ciki tana ziyarar band’aki cikin ta sai kara yake,

‘Kulululu...Tutututuwiyyy.... Ta sau iska tana baje hanci. Yaran suka hau dariya suna tsalle,

“Bintalo ta sau tusa.. Bintalo ta sau tusa..”

Ta kofar ban’daki Bintalo ta zuro kai tana karkada musu hannaye,

“Sittin ta ubangiji zan raunata na jijjiga yaro. Shegu da runtuma runtuman kai. Tusa ce uban kowa yana yi. Bara na fito na same ku..”

Ai kuwa suka fice suna cigaba da fadar tayi tusa. Baba usaiba ta kece da dariya tana buga zani,

“Waiii. Gumaama, Kutsin ubancan kayya kai. Sai kashe shekararren mushe. Maganin marowaci kenan. Idan baki basu ba kya bawa bandaki ai. A hayye kayya kai..”

Nayi daria kawai na koma d’aki. Kullum ne ya zama jazaman Bintalo da Usaiba su haurawa. Ina jiyo karakainan su a kasa suna tayi. Ni kuwa marking exams din dalibai na na cigaba da yi hankali kwance..

*Da* misalin karfe hudu da yamma su Gwaggo Aminatu da Innar mu suka dira a police station wajen Kawu ila. Gwaggo Aminatu tayi kukan ganin Kawu ilan cikin mawuyacin hali. Bata bata lokaci ba kuwa ta nemi a kira mutumin da ya shigar da karar. Mintina kalilan Alh Usman Usman ya garzayo caji ofis din. Bayn sun gaysa ne Gwaggo Aminatu ta nemi sanin kanun labarin. Inda Alh Usman ya sheda mata tundaga farko zuwa karshe ya kar’kare da,

“Amshi nan Gwaggo diba, Wallahi alkawari mukai dashi ya sab’a. Ya za’ai ace cikin yan kwanaki kalilan ya cinye makuden kudaden ya kuma sayar da gidan gonar? “

Gwaggo Aminatu ta girgiza kai tana kallon Kawu ila cike da takaici,

“Kayi hak’uri Alhaji.. Dan Allah”

“Amshi nan Hajia, Diba. Wallahi sai ya biyani tunda bashi da amana ba kuma shi da mutinci.”

Gwaggo Aminatu taja ajiyar xuciya ta sauke tana zabga tagumi,

“Toh ka kara bamu lokaci dan Allah! Zamu san yadda zamuyi da sauran yan uwan sa mu samu mu biya ka. Kada ka kai karar kotu na roke ka Alhaji..”

“Amshi nan Hajia. Diba. Idan ba za’a dau lokaci ba babu damuwa zan jira, Amman da sharadin sai dai ya cigaba da zaman sa anan har sai anbiya ni hakk’i na duka..”

“Allah ya bamu ikon biyan ka Alhaji. Mun...”

“Haba Yaya na cigaba da zama anan fa kikace? Meyakwan ku fitar dani kwa biya daga baya.”

Cewar Kawu ila hade da hararar Innar mu. Gwaggo Aminatu tayi murmushin yake tana sallama da Alhaji. Yana fita ta hau Kawu ila da fada ta inda take shiga batanan take fita ba.

“‘Yayan dan uwan ka. Kake watangariri da rayuwar su tin bayan ran mahaifin su? Tir da hali irin naka Ilyasu. Ace wai rayuwar batoul kake siyarwa kana cinikin auren ta kamar kayan sawa? Kasan hakkin zumunci kuwa? Tsaya kaji...

“FALALAR SADA ZUMUNCI DA ILLAR YANKESHI,

ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﺃَﻳُّﻮﺏَ ﺍﻟْﺄَﻧْﺼَﺎﺭِﻱِّ، ﺃَﻥَّ ﺃﻋﺮﺍﺑﻴﺎ ﻋﺮﺽ ﻟِﻠﻨَّﺒِﻲِّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻓِﻲ ﻣَﺴِﻴﺮِﻩِ، ﻓَﻘَﺎﻝَ : ﺃَﺧْﺒِﺮْﻧِﻲ ﻣَﺎ ﻳُﻘَﺮِّﺑُﻨِﻲ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠَﻨَّﺔِ، ﻭَﻳُﺒَﺎﻋِﺪُﻧِﻲ ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺭِ؟ ﻗَﺎﻝَ : " ﺗَﻌْﺒُﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻟَﺎ ﺗُﺸْﺮِﻙْ ﺑِﻪِ ﺷَﻴْﺌًﺎ، ﻭَﺗُﻘِﻴﻢُ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ، ﻭﺗﺆﺗﻲ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ، ﻭﺗﺼﻞ ﺍﻟﺮﺣﻢ ." ﺁﺩﺍﺏ ﺍﻟﻤﻔﺮﺩ
Ankarbo daga Abu Ayyubal ansary (R.A) wani mutumin kauye ya bijirowa manzon Allah (S.A.W) acikin tafiyarsa sai yace: Kabani labarin abunda zai kusantar dani Aljannah kuma ya nesantar dani daga Wuta ? sai Manzon Allah (S.A.W) yace: "Kabautawa Allah kar kahada shi da komai , kuma katsaida Sallah , kabada Zakkah , kuma kasadar da Zumunci "
ﻋَﻦْ ﺃَﻧَﺲِ ﺑْﻦِ ﻣَﺎﻟِﻚٍ؛ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ " : ﻣَﻦْ ﺃَﺣَﺐَّ ﺃَﻥْ ﻳُﺒْﺴَﻂَ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺭِﺯْﻗِﻪِ، ﻭَﺃَﻥْ ﻳُﻨْﺴَﺄَ ﻟَﻪُ ﻓِﻲ ﺃَﺛَﺮِﻩِ ، ﻓَﻠْﻴَﺼِﻞْ ﺭﺣﻤﻪ ".
Daga Anas dan Malik Manzon Allah (S.A.W) yace: "Duk wanda yakeso a yalwata masa Arziqinsa , kuma a jinkirta masa ajalinsa to yasadar da Zumunci.
ﻋَﻦْ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺑْﻦِ ﻋَﻮْﻑٍ؛ ﺃَﻧَّﻪُ ﺳَﻤِﻊَ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻳَﻘُﻮﻝُ : " ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﺰَّ ﻭَﺟَﻞَّ : ﺃَﻧَﺎ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦُ، ﻭَﺃَﻧَﺎ ﺧَﻠَﻘْﺖُ ﺍﻟﺮَّﺣِﻢَ، ﻭَﺍﺷْﺘَﻘَﻘْﺖُ ﻟَﻬَﺎ ﻣِﻦَ ﺍﺳْﻤِﻲ، ﻓَﻤَﻦْ ﻭَﺻَﻠَﻬَﺎ ﻭَﺻَﻠْﺘُﻪُ، ﻭﻣﻦ ﻗﻄﻌﻬﺎ ﺑﺘَﺘّﻪ ".
Daga Abdurrahman dan Auf, yaji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Allah mai girma da buwaya yace : " Nine mai Rahama , kuma ni na halicci Zumunci , kuma na ciroshi daga suna na, duk wanda yasadar da shi zan sadar dashi (zuwa ga Rahamata) wanda kuma yayankeshi zan yanke shi (daga Rahamata) ".

Sadar da zuminci,shine ziyarar yan uwa da dangi da abokai na alkhairi da taimakonsu da agaza masu”.

Annabi s.a.w ya bayyana mana sadar da zuminci hanyace ta samun arziki da rayuwa mai dadi anan duniya da Lahira.

Sai yace:
(ﻣَﻦْ ﺳَﺮَّﻩُ ﺃَﻥْ ﻳُﺒْﺴَﻂَ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﺭِﺯْﻗُﻪُ، ﺃَﻭْ ﻳُﻨْﺴَﺄَ ﻓِﻲ ﺃَﺛَﺮِﻩِ ، ﻓَﻠْﻴَﺼِﻞْ ﺭَﺣِﻤَﻪُ)

Duk wanda yake son Allah ya yalwata arzikinsa kuma ya tsawaita rayuwar sa, to ya sadar da zumincinsa).
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏) 2067 ‏( ،ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏) 2557 ‏( ،ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏) 1693 )

Awani Hadisin yana cewa:
(ﺍﻟﺮَّﺣِﻢُ ﻣُﻌَﻠَّﻘَﺔٌ ﺑِﺎﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺗَﻘُﻮﻝُ ﻣَﻦْ ﻭَﺻَﻠَﻨِﻲ ﻭَﺻَﻠَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﻣَﻦْ ﻗَﻄَﻌَﻨِﻲ ﻗَﻄَﻌَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪ)

(Zuminci yana rakaye ajikin al’arshi yana cewa ya Allah ka sadar da wanda ya sadar dani ka yanke wanda ya yanke ni).
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏) 5989 ‏( ﻣﺴﻠﻢ ‏)

ILLA DA HATSARIN YANKE ZUMUNCI

ﻋﻦ ﺟﺒﻴﺮ ﺑﻦ ﻣﻄﻌﻢ؛ ﺃَﻧَّﻪُ ﺳَﻤِﻊَ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻳَﻘُﻮﻝُ " : ﻟَﺎ ﻳﺪﺧﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻗﺎﻃﻊ
ﺭﺣﻢ ".
Daga Jubairu dan Mud'im, yaji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: " Mai yanke Zumunci bazai shiga Aljannah ba".
ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﺑَﻜْﺮَﺓَ ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ " :
ﻣَﺎ ﻣِﻦْ ﺫَﻧْﺐٍ ﺃَﺣْﺮ.

“Ilyasu shin ba mummunan abu kake aikatawa ba? Marayu ne fa ‘yayan dan uwanka na jini? Subhan’Allah!”

Kawu ila ya yamutsa fuska yana sosa kunne alamun maganganun ta sun shiga sun fita. Gwaggo Aminatu tayi murmushi tana kallon Innar mu,

“Kaltume mu tafi ko? Zan taho yanzu.”

Kad’a kai Innar mu tayi ta fita dama tuni Yayan mu ya futo shi. Gwaggo Aminatu ta muskuta kusa dashi tana karkada hannuwa,

“Ka cigaba da abinda kake yi Ilyasu, Ai gashi nan kana girbar su ahankali. Su wanda kake uzzurawan rayuwar su na gyaruwa kai taka na shiga cikin matsatsi. Yanzu wa gari ya waya?”

Kawu ila ya shiga kunkuni tamkar karamin yaro. Gwaggo Aminatu ta mike tana gyara mayafi,

“Kasan da sanin munsan kudaden daka cinye na marayu..”

“Kudin su wa?”

“Kudaden da marigayi salisu ke bibbinka ai hakkin yayan sa da matan sa ne yanzu. Nabi diddigi ance baka bayar ba. Na tsaya na auna hankalin ka ko zakayi tunani ka basu abinsu kaki. Kai baka tunanin meyasa masifu ke addabar ka? Komai naka ya kare? Shagunan ka sun kone, Iyalanka ma wasu sun guje ka? Kar kayi *ZATON* kaci bulus,Domin duk wanda yaci dukiyar marayu ka sani Allah yace,

“Lalle dukkanin wadanda suke cin dukiyoyin marayu da zalunci, abin sani kawai suna cin wutane a cikinsu, kuma da sannu za'a kona su a wuta wacce ake rurata''Suratun Nisa'I, aya ta:10. “

Tana gama fa’da masa tayi fucewar ta fuuu cike da takaicin bakin hali da tsantsar mugun ta ta dan uwan nata da yake watangariri da rayuwar ‘yayan yan uwan sa na jini....

••
Assalamu Alaikum dearies🥰😻 Nagode kwarai da addu’oin ku gare ni. Alhamdulillah jikina da sauki. Kunsan makarfafa a jikin mutum. Banida lapia sai kuma nazo na fadi na bugu sosai na dan zauna a asibiti. wallahi har ta kaiga nasa neck collar👏🏻Alhamdulillah da sauki. Shiysa kwana biyu kuka jini shiru. IN SHA ALLAHU zan cigaba da typing amma kilan I will be Lil slow and off somedays saboda ina kokartawa nayi typing dinne kawai saboda haqqin ku akaina🥰❤️Nagode da kirana da kuka yiyyi, Messages da kuma addu’oi na comments groups. Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci. ya kuma bamu lapia mai dorewa❤️❤️ Masu ganin laipi na kuyi hakuri bada niyya bane kunsan lapia uwar jiki ce. Thank you all. Jazakum Allah bil jannah❤️❤️

••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*36*

*NANA HAFSAT*

• • •

*Wajajen* biyar na yamma su Innar mu suka dawo da gwaggo Aminatu. Dama tuni Yayan mu ya kira ni awaya ya sheda min suna nan tafe. Don haka da sauri na dora spaghetti datasha kayan lambu da bushasshen kifi. Na kuma karb’o zobon matar soja sanyayye.

Sosai Gwaggo Aminatu da su Innar mu sun narki taliyar nan. Gwaggo sai yaba dadin da tayi take yi. Murmushi kawai nayi na cigaba da marking booklets din exams na students dina. Ba laifi naci rabin marking din na dakata domin yana bukatar hutu da kuma kulawa. Acikin wa’enda na maka wasun su sun cinye, Wasu sun fad’i wasu ba lefi. Shigar da wanda na maka nayi na na janyo 40Rabbana ina karanta addu’oin da suka zamto min lazim sai nayi.

Gwaggo kuwa suna ta hirar su da Innar mu kafin ta mike ta shisshiga sauran dakunan. Dakin Bintalo ta shiga ina jiyo ta suna maganar kudin adashin da take ajiyewa, Domin yau kusan mutane goma ne suka kawo nasu. Ruma ma ta kawo wasu cikin leda.

“Bintalo babu matsala haka? Ba zaku kai banki ba?l

Cewar Gwaggo Aminatu, Ta karasa fada tana rafka tagumi ganin himilin kudin dake gaban Bintalo tana cusashi a asusu. Domin yanzu asusun harda mai mukulli ta karo. Bintalo tai shewa tana sosa hanci,

“da ido d’aya nake bacci saboda masu dan hali..”

Gwaggo Aminatu ta tari Bintalo tana murmushi,

“Ba abinda nake nufi ba kenan. Ina nufin ku dinga ajiyewa a banki mana kamar zai fi sauki..”

“A hayye! Tabdijan. Ai Yaya sittin ta ubangiji zaman sa awaje na shine zaman lapiar sa kuma ‘karuwa tace. Domin idan aka kammala inada nawa kason mai tsoka...”

Gwaggo Aminatu ta jinjina kai tana gyara zaman mayafin ta hade da yin hanyar fita daga dakin,

“Eh zahiri! Toh Allah ya bada sa’a. Ni zan tafi idan muka gama magana dasu Dawood.”

“Toh Yaya. Agayda yaran..”

“Zasuji..”

Dakin Kawu khamis ta shiga. Nan sauran kawunin mu suka shisshiga suma. Mai suka tattauna akai oho? Bayan wani lokaci kuma na jiyo sallamar Gwaggo Aminatu zata tafi. Kasan na sauka na rakata har wajen motar ta. Sallama na mata direban ta yajata su ka koma kaduna...

Bayan sallar isha’i na dakko sauran booklets din da banyi marking ba na shiga duddubawa ina maka su. Akwai wuta ga fanka nata bamu iska. Autar mu tuni tayi bacci. Innar mu kuma tana kishingid’e tana lazimi. A hankali nazo kan wata takarda. Da farko shafin ta an fara introductory part aka soke. Daga kasan kuma yare ne kawai aka rubuta shima kad’an. Gaba d’aya sauran shafukan ba abunda aka rubuta. Na ware idanu ina cigaba da dudduba ta. Lamarin ba ka’dan ba ya dagamin hankali. Ganin koma waye dole yana d’aukar dayan course din nawa. Hakan yasanya na dakko booklets din dayan course din nawa na zakulo booklet din. Abin mamaki itama hakan akai. Har gwara ta farkon ma gaba d’aya wannan ko paragraph d’aya ba’a rubuta ba sai wasu watsattsulallun kalamai na wani yaren.

Hankali na yai mutukar tashi ganin koma wanene babu yadda za’ai na iya temakon sa na wutar dashi. Gaba d’aya gumi sai ya shiga kwaranyo min. Domin harga Allah banason bada carryover. Nafiso kowa ya wuce. Ganin daga wannan semester na rabu dasu. Son samu ne kowa ya wuce ba matsala. Domin ni da su munyi hannun riga inde a lecturing ne. Kawai dai ni ce level coordinator dinsu ta’iya level one din.

Jiki na na rawa na xakulo wani littafi mai dauke da sunayen yan ajin baki d’aya. A hankali na shiga duba sunayen ta reg number da ke kan booklet din. ‘MUhammad Mubeen Salees’ shine sunan dake rubuce baro baro. Na rufe baki na da tafin hannu na gano ko waye. Shi kuwa meyasa yai haka? Dama kenan bai iya written abu ba sai oral ko kuwa dai bashida man kai ne?

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un..”

Na shiga maimatawa gumi na kwaranyo min ga fanka na bada iska. Amma tsabar tsantsar tashin hankakij da nake ciki bana ji,

“Mubeen, Why?”

“Kika ce me?”

Innar mu ta fada tana rage sautin rediyon ta. Na girgiza kai ina harhada takardun waje daya. Gaba d’aya bani da lakar cigaba da maka takardun a lokacin..

“Babu komai Innar mu..”

Raina ba dadi haka na kwanta a katifar mu bayan nayi addu’a. Daren ranar dai baccin mintina nayi.

•X••O••X••O••

A yau ne ta kama za'a gudanar da zabubbukan gwamnoni da senators din jahohin dake duk fad'in Nigeria, gabaki d'aya iyalan Amb Salees sun hallara a polling unit d'in su. Amb Salees shine a farkon layin sannan matarsa hajja Ahlaam sannan Muhammad Mubeen wanda ke ta faman yatsina fuska kai da ka gani kasan ba'a son ransa ya fito gurin ba, kawai dan an tilasta masa ne. Gabaki d'aya mutanan wajan ihu suke suna murna ana cewa sai Amb Salees Kaduna tashi ce sai sun canza, bakin Amb a washe yana ta fara'a har yaje ya dangwala jam'iyarsa sannan matarsa ma ta dangwala sai Mubeen sannan aka bar mutanan gari suma suka cigaba da dangwalawa. Daga nan gurin gida aka maida hajja Ahlaam da Mubeen, shi kuma Amb Salees ya shiga cikin mutane akaci gaba da janyo ra'ayoyin jama'a har aka kammala aka kirga, Alhamdulillah sune da nasara domin mutane suna son shi sosai.

Tunda suka koma gida mutane ke shiga da fita a wajan hajja Ahlaam wacce keta rarraba musu kudade da sabulai da omo da dai sauran su. Mubeen ya fito cikin shirinsa na son zuwa unguwar su Batoul saboda ya dade bai ganta ba tun da suka gama jarabawa koya koma makarantar baya tarar da ita. Mukullin mota ya d'akko kai tsaye ya nufi inda ake ajiyewa ya bud'e zai shiga yaji an rike kofar motar. A hankali cikin mamaki ya kalli wanda keyi masa hakan yaga wani soja ransa a b'ace tamkar Mubeen din yayi masa laifi, murya a kaushe yace dashi.

“Daga yau babu wanda zai kuma fita daga gidan nan har sai bayan an fad'i sakamakon zab'e.”

Baki bud'e Mubeen yabi sojan da kallo, shi sam be ma san da zaman su ba sai yanzu ya hangesu barbaje a harabar gidan. Wani gududun haushi ne ya tukare masa a wuya kawai ya juya yabar gurin cike da haushin siyasar gabaki d'ayan ta. Dan ba dan mahaifinsa ya tsaya wannan takarar ba da tuni yana nan yana fita duk inda yaga damar zuwa.

•X••O••X••O••

Cikin hukuncin Allah washe gari da yamma wajan karfe biyar aka yi announcing cewar Amb Salees yaci zab'en governor d'in jihar kaduna. Murna a wajan zuri'ar nan da magoya bayansa ba'a cewa komai. Gidan yayi dank'am da al'umma maza da mata yara da manya anata celebration. Hajja Ahlaam bakinta har kunne dan ko Amb Salees d'in ba zai nuna mata jin dad'in wannan lamarin ba. A dai-dai lokacin ne kuma Mubeen ya samu damar ficewa daga gidan ba tare da sojojin da aka barbaza a gidan sun lura ba. Duk inda ya tsoma kafa mutane ne majalisa majalisa suna ta murna ya sanya face mask ya dora bakin glasses a idanunsa hakan yasa ba'a gane shi gashi yasa hula, ya tari napep yace ya kai shi unguwar limancin kona.

Mai napep d'in har yaki d'aukar sa saboda unguwar da nisa gashi shi kuma rally zasu tafi da sauran abokansa masu sana'ar, ganin irin uban kudin da Mubeen ya bashi ne yasa shi cewa to zaije koma ina ne indai mai hawan zai jurewa iskar da zasu kwasa a hanya. Dubu biyar ya bashi suka d'auki titi, gabaki d'aya hankalin Mubeen yana kan malamarsa da ya jima bai sanya a cikin kwayar idanunsa ba. Suna zuwa unguwar su Batoul nan din ma a cike take da mutane anata maganar zab'en, wasu na murna wasu suna zage-zage. Shi dai Mubeen babu abinda ya damesa irin yaga malama Batoul. Yana ta neman wanda zai tura da kuma yadda zai furta wajan kiranta sai ga Autar su tazo zata shiga cikin gidan, yayi saurin tare ta yana kare mata kallo.

“Baby ciki zaki shiga?”

Ta kallesa itama sannan ta d'aga masa kai ba tare da tayi magana ba.

“Tom kice ana sallama da Malama Batoul.”

Kuma binsa da kallo Auta tayi, sai kuma ta shiga gidan ba tare da ta bashi amsar zata kira ko ba zata kira ba. Tana shiga ta sameni a kwance ina chatting a wayata, sai da ta zauna kusa dani ta janyo hannun damana sannan tace.

“Yayyah!”

“Na'am.”

Na amsa ina k'ok'arin kwace hannuna da ta rik'o amman yarinyar nan taki saki na.

“Ana kiranki a k'ofar gida.”

“Kirana kuma?”

Na tambaya cike da mamaki.

“Waye kuma a cikin irin wannan lokacin?”

“Ban sanshi ba Yayyah, amman dai dogo ne ya rufe bakinsa da takunkumi.”

D'an karamin tsaki naja sannan na mik'e zaune tare da zare hannuna daga nata. Innar mu na k'asa tana alwala kasan cewar wacce take jikinta ta warware shine take sakewa. Hijabi na na d'auka nasa tare da d'aukar sosan shafa powder na d'an goge fuskata dashi sannan

Please Login or Register in order to submit comment