Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hancin sa,

“Zo nan dan uban uban ki..”

Karasawa nai nesa da shi na tsaya, Ya dubi abincin gaban mutane kafin ya kalle ni a sheqeqe,

“Zubomin malmalar tuwo goma, Waina goma, Alala goma da funkaso goma, Sinasir goma da kunu goma. Da nama ishasshshe.. Kawomin yanzu”

Gyada kai nayi na haye sama. Baba usaiba da innani matar baffa ardo ne akan abincin. Su na samu na gaya musu yadda yace a zuba masa. Baba Usaiba ta zuzzuba masa ta saukar masa dashi,

“Sannu Ilyasu mai cikin zani. Dan bakin hali da mugunta ya za kai da uban abinci haka? Ina xaka kai shi? An daiji kunya billahil lazi.”

Kawu ila ya dankara mata harara,

“Wai ina ruwan ki ne usaiba? Ni fa banason shisshigi wallahi.”

“Toh mu daku mana Ilyasu. Billahil lazi naci biredi na yage leda. Zan nanuka gardi a kasa wallahi.”

Yan biki suka taru akansu suna kallon yadda suke cacar baki. Dakyar Gwaggo Aminatu dake sama hayaniyar su ta ishe ta ta sakko,

“Haba ya isa dan Allah! Ke usaiba haye sama ku cigaba da raba abincin ku. Kai kuma uban neman magana tashi ka fita cikin yan uwan ka maxa. Cikin gida ai na mata ne.. Gashi kuma hayaniyar biki ta kara kacamewa.”

Kawu ila ya zumburo baki yana sakin mik’a, Ya fice daga gidan yana mita. Ni kuwa wanka na sake yi na sauya kaya cikin wani leshi maroon color da yasha stones royal blue. Na saka komai royal blue na fice dan zuwa gidan su Fadilah. Aka danyi wani wunin kafin wajen karfe daya aka dunguma kano kai amarya gidan ta. Can unguwar shagari quarters anan gidan yayan namu yake. Komai yayi wallahi dai dai karfin mu. Iyayen Fadilah sun zuba mata kaya masu kyau gaskia. Da zamu taho naci kuka wallahi. Kuka biyu nake yi na rabuwa da Yayan mu mahaifin mu na biyu. Da aminiyata wadda ta zamto yar uwata ta jini. Haka muka kamo hanya muka dawo zaria kowa yana santin gidan amarya. Alhamdulillah sannu ahnkali rayuwar mu nata gyaruwa abun ba’a cewa komai sai sam barka..

*GOVERNMENT HOUSE: KADUNA*


**
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_𝓜𝓐𝓓𝓐𝓜𝓔_𝓨𝓔𝓡𝓦𝓐🧕🏼


*41*


Gaba d’aya farfajiyar gidan dankam take da mutane kowa yanata hada hadar halattar liyafar da za’ai a d’aya daga cikin hall din dake gidan gwamnati na taya his excellency Dr/Amb salees muhammad lashe zaben zama gwamnan jihar ta kaduna. Yan uwa fal da abokanan arziki sun cika gidan kowanne bakin sa har kunne ciki harda yan bakin ciki dake murmusawar yak’e.

Mubeen dake baje akan gadon sa yana karewa hotan Batoul kallo a waya data sa a status ya sau nannauyar ajiyar zuciya yana dafe saitin zuciyar sa. Lokaci zuwa lokaci yakan lumshe idanun sa yana sakin murmushi. Cikin haka mahaifiyar sa ta shigo dakin nasa shirye cikin wani datsattssen lace purple tasha ruwan gold. Tayi kyau babu karya. Kallo ta kare masa ganin yadda take ta doka sallama amman bai amsa ba yana can duniyar tunanin malamar tasu..

“Muhammad Mubeen..”

Sai data kira shi sau uku kafin ya farfado daga duniyar tunanin daya tafi. Ya mike daga kwancen da yake yana sosa keya,

“Wa alaykm salam Mamma..”

“Tab! Tun daxu na gama doka sallamata ai. Inata kiran ka kuma kamar wanda baya dakin. Meke damunka ne Mubeen?”

‘Batoul...’

Ya fada a zuciar sa, A zahiri kuma yamutsa sumar kansa yayi kawai ya mike yana gyara kayan jikin sa,

“Bakomai Mamma!”

“You sure?”

“Yesss Mamma..”

“Toh shirya ka fito kai ake jira za kubi tawagar shigar da baban ku cikin wajen taron.”

“Mamma kai na ci...”

“No excuses Mubeen. Ka shirya ka fito yanxun pls.”

Kada kai kawai yayi ba don yanaso ba, Ita kuma ta fice da sauri tana amsa kiran da akayo mata a wayar ta. Cikin wata dandatsetsiyar shadda kirar getzner ya sanya hade da agogon azurfa da takalmin batozzi. Kai komai nasa yayi kyau. Ya taje kwantacciyar sumar kansa yana dora hula akai. Ya feshe jikin sa da turaruka masu kamshi da tsada. Cikin takama ya fice daga dakin nasa kai tsaye ya wuce babban parlorn mahaifin nasa shake da mutane. Mahaifin nasa na hangoshi ya kirawoshi yana mai nunawa mutanen wajen shi da matsayin sa. Daga nan suka jera su kai wajen liyafar da aka shirya. Tab tsayawa fada muku tsarin wajen bata lokaci ne wallahi. Ya hadu fiye da tunanin mai tunani. Nera tayi kuka domin komai yaji citta. Yammata sai kallon Mubeen suke. Shi kuwa gaba d’aya jinsa yake a takure saboda bayason hayaniya da yawan mutane sosai. (Social phobia). Anci ansha an kuma gyatse. Sai dai muce gwamna Allah ya tayaka riko ya baka ikon sauke alqawarurrrukan da kayiwa jama’a.


*WASHE-GARI*

Da wuri Muhammad Mubeen ya tashi ya kintsa komai. Ya debi kayayyaki da yawa ya zuba a akwatunan sa. Ya jima a parlor yana jiran mahaifin sa bayan yaci abinci. Gaba d’aya ya lura yanzu mahaifin nasu kulawar da yake basu ta dan ja baya akan da. Saboda yanzun bashi da lokacin zama a jikin suyi hira kamar da. Shiysa ya tsani harkar siyasar da mahaifin nasu ya tsunduma rayuwar su. Lokaci zuwa lokaci yakan saki tsaki yana kallon agogon sa. Sai can daga baya mahaifin nasa ya shigo ciki yana gyara rigar jikin sa.

“Papa...”

“Yes MM ya kake?”

“Alhamdulillah Papa! Barka da safiya!”

“Barkan mu dai...”

Yana fadar haka yai gaba Mubeen ya bishi a baya yana sosa keya,

“Papa zan koma school..”

“School? Oh ai ina ganin zaka iya barin school dinnan Mubeen sai ka zaba wata yanzu bazan hana ka ba..”

“No papa inaso. Nafuson can..”

“Amma Mubeen yanzu fa ba’a zaria muke ba. Kuma bazan iya nisa da kai ba Mubeen.”

“Papa plsss..”

“Meyasa ka canza ra’ayin ka ne Mubeen? Kai fa ka nuna bacin ranka sosai akan makarantar. Meyasa yanzu kake so? Yanzu mun kara nisa da ita Mubeen. Da wahala ace kullum kana tafe akan titi..”

Cewar Haj Ahlaam dake tsaye a matattakar bene tana jiyo su tin sanda suka fara maganar. Mubeen ya dafe kansa yana girgiza shi. Shi kam a rabashi da komai amman banda abinda zai nisanta zuciar sa da idanun sa da malamar tasu. Muryar sa na rawa saboda baya iya doguwar magana yace,

“Mamma, Papa pls kuyi hakuri zan zauna a hostel ko a kamamin apartment pls..”

Haj Ahlaam tai saurin girgiza kai tana sakkowa daga benen,

“A’ah gaskia Mubeen. Kasan ba ishasshiyar lapia ce da kai ba so bazeyiwu kai nisa daga gidah ba gaskia.”

“Fada masa dai. Ai taurin kai ya masa yawa.”

“Ok fine! Zan zauna agidan Aunty Rahila (kanwar Amb Salees) kaji Papa?”

“Shikenan..”

Cewar Amb Salees. Yana gama fad’a ya fice cikin sauri. Haj Ahlaam ta zabga tagumi tana kallon yadda Mubeen ya rikice musu ta rasa meya canza zuciyar sa haka dayake son makarantar yanzu. Bayan ada kullum cikin korafin bayaso yake.

“Meyasa kakeso ka cigaba da zuwa? Ka zabi kayi nisa da gidah. Ya akai haka Mubeen? Shin menene a makarntar yanzu da kake sonta?”

‘Batoul..’

Ya fada a zuciar sa yana taune lebe. A Zahiri kuma ya yamutsa sumar kansa yana zama a gefen kujerar da take,

“Bakomai Mamma! Kawai dai ina enjoying courses dinne. And nayi making lots of friends..”

Haj Ahlam ta ware idanu tana jaddada kai,

“Kai ne kayi making lots of friends Mubeen? Kai taya ma kake bada fuskar da zakai abokai? Karya kake.”

“Allah Mamma.”

“Fine! Allah ya bada sa’a da narara. But duk sanda bakuda lectures ka dawo gidah kaji ko?”

“In Sha Allah mamma.”

Haka dai taita bashi shawarwari hardasu hawaye saboda so da shakuwa. Kannen sama suka tasa shi agaba suna koke koke. Amma saboda tsabar soyayyar malamar tasu ta gama zaga jinin jikin sa ko kadan baiji son zama a gida ba. Sai ma hak’uri daya babbasu ya harhada kayan sa ya shiga mota direba yaja shi sai zaria. Ba abinda yakeson tozali da shi sai malamar tasu. Ya kuma ci alwashin sanar mata da zuciar sa a koda yaushe.

*GIDAN MATA TARA*

Na gama kintsawa cikin doguwar rigar atamfa mai zanen jaka baka. Na yafa bakin mayafi ina tafe a kafar bene ina daure agogon dake wutsiyar hannu na. Sauri nake ta zabgawa zan tafi makaranta naci karo da Mari yar gidan Kawu ila da Hinde a soro suna magana kasa kasa. Na musu kallon Allah ya shirya domin yanzu basa kwana a gidah kullum suna gidan magajiya (gidan karuwai) A can suke kwana da kwanaki. Sai lokaci zuwa lokaci suke dawowa gidah. Gaba d’aya sun fita hayyacin su. Sun lalace sun fige saboda masifar neman maza da shaye shaye jikin su duk ya saki. Gaba d’aya tsami suke yi. Bana jiyo mai suke cewa na dai ji kalmar ‘lagos’ aciki. Na rab’a ta gefen su zan wuce hinde ta janyo mayafi na tana tangarin buguwa,

“Y... Yar kanwata bamu nera hamsin mana.”

“Hamsin kawai batoul. Lalubo mana ita.”

Na zabga musu harara ina kwace mayafi na. Kunsan dan shaye shaye da rokon balai. Haka suka baje akasa suna rok’ona. Naja tsakin takaici ina binsu da fatan shiriya kafin na zaro nera dari na mika musu. Na fice daga gidan gaba d’aya zucia ta babu dadi.


*GIDAN ALHAJI KABEER MAI WAFA*

Shi kuwa Haysam tunkarar mahaifin nasa yayi da maganar batoul. Babu bata lokaci kuwa Alh Kabeer yace ya amince zai kuma tasa aminan sa su biyu agaba suje su nemar masa auren batoul din. Murna awajen Haysam ba’a magana. Haka ya dinga kwararowa mahaifin nasa godia cike da farin ciki. Haj Husnah dake labe ta sa hannu a baki ta gatsa tana k’wafa. Tana kallon sanda Haysam ya fito daga wajen mahaifin nasa ya shiga dakin sa ya dakko mukullin mota ya fita. A baya ta bishi tana hango sanda yake bin batoul da mota harya dauke ta suka tafi. Tamkar tai hauka haka taji. Dakyar ta koma gida tana ‘kissima yadda zata warware shirin Haysam din.


*A•B•U*


A hankali Haysam ke tafiya da mota yana zubamin kalaman soyayyah. Agogon hannu na na kalla ina murmushi,

“Ya Haysam dan kara gudun motar mu karasa ciki zan makara.”

“Wato ni bana gaban ki kenan ko Mine?”

“Nina isa?”

“Har kinyi yawa ma mine! Nagaya miki dai Abba yace zasu zo gidan ku da abokan sa a cikin satin nan..”

“Uhum..”

“Kiyi magana kinji...?”

“Allah ya kawo su.”

“Ba zaki mana addua ba?”

“Ni kunya nake ji. Nayi a zuciata.”

“Ni kam gaskia kunyar nan na cutata.. Ki rubuta ki ajiye muna aure zan yage kunyar wallahi.”

Ban bashi amsa ba sai dai murmushi kawai dana yi masa. Muka karasa har office dina. Dakyar ya barni na fita daga motar. Muhammad Mubeen dake kallon su tun tahowar su a mota yaja tsaki yana fusgar da iskar bakin sa. Cike da bacin rai ya shige theatre yana rintse idanun b’acin ran ganin yadda take ta faman dasharewa gayen can baki. Amma dole ya fasalta mata zuciar sa shima. Har suka kare lectures dinnan ba fuskanta yake ba. Ayyana yadda zai tunkari malamar tasu kawai yake yi. Kansa sai ciwo yake masa dubada shidin ba lapia ce ta isheshi ba. A daddafe ya sha magani ya nufi ofishinta. Tana zaune akan kujera tana danna waya sai murmushi take yi ya shiga bakin sa dauke da sallama,

“Wa’alaykm Salam!”

Kujera Mubeen ya janyo ya zauna yana kifa kansa akan desk. Dagowa nayi na kalle shi ko lapia?

“Meke damun ka Mubeen? Ka tafi gidah mana..”

Bai amsa ni ba ya cigaba da sauke numfarfashi yana ajiyar zuciya. Na ajiye wayar hannu na ina kallon ikon Allah. Haysam ne ya kirawo ni na daga zan dauka kenan Mubeen yai taku biyu ya karbi wayar yana sanyata cikin aljihun sa na gaba. Nai masa mugun kallo ina mamakin renanin da yayi.

“Meye haka? Bani waya ta..”

“Pls....! Ki bani lokaci.”

“Lokacin me? Bani wayata kafin na mugun sab’a maka. Yaushe rai ni ya shiga tsakani na da kai haka? Tashi ka fitar min a office. Get out! This instant..”

Meyakwan ya fita zubewa yayi a kasa yana zubar da hawaye. Na dafe goshi na ina kallon sa. Da naga abun nasa babba ne yasa na shiga harhada kaya na a jaka ina jan tsaki. A hankali na jiyo shi yana magana cikin yaren su na jiyo sautin saukar numfashin shi akan fuska ta yana cewa,

“irisiwo be’ā‘imiroyē ina belibē wisit’i ānidi bicha newoti። be’inē layi mini tets’i‘ino inidasaderu yawik’alu? bech’inik’eti gīzē wisit’i inikwani ፣ kewetirowi yebelet’e irasēni āregagalehu ፡፡ benegerochi ina behunētawochi hulēmi k’eleli yale goni yagenyehu yimesilenyali። yihi inē kek’edimowi betek’aranī inē inidek’edimowi yalenyi gelelitenya newi ፡፡ begeneti libē wisit’i ānite bicha ānidi meli’āki nehi”

Bangaje shi nai zan fita ya rikomin yatsu yana hawaye sosai. Cikin harshen turanci yake cewa,

“You are only one in my mind and in my heart. Do you know the effect you have on me? Even in times of stress, I find myself calmer than usual. I always seem to find the lighter side in things and situations. This is so unlike me, Kin canza ni Ma,

“The pessimist I used to be. You are the only angel in my heart of heaven. Ma. Ina ‘kaunar ki ma z...”

Hannuwa na nasa da sauri ina dafe kunnuwana. Sam banason na cigaba da mafarkin da nake yi. Domin kuwa amafarki na dau hakan. Ko’karin k’wace hannu na yake ya damke hannun sosai yana ko’karin sanya idanun sa cikin nawa, Na samu na fincike zan fuce ya rufe kofar da sauri da dukkanin sauran karfin sa. Hannuwan sa yasa ya sanya ni a tsakiya ya tokare kofar yadda bazan fita ba, Na rasa meyasa kawai ji nayi na fashe da kuka. Na tabbata kukan bakin cikin yanayin da nasamu kai na ne da dalibi na,

“While I might not have the most tantalizing words at my disposal to express my love to you, I will manage these three words (I love you) to let you know that my world revolves around you all year round. You know how I feel about you, I want you to also know that there is no mistaking in it. My love for you is real and I will love you forever because you are the only one that deserved to be loved this tenderly. Fikre....! Ina miki son kauna Ma! Ina sonki so mai tsanani Ma..”

“Baka da hankali ko kana hauka ne?”

Na fada muryata na rawa. Mubeen yai murmushi yana taune kasan lips dinsa,

“Yes! Inde akan son ki ne ni mahaukaci ne. Soyayyar ki tamin lahani. Bazan iya rayuwa babu ke ba...”

Wani k’arfi ne yazo min na bangaje shi na fuce ko takan jakata da wayata banbi ba. Na fice nai hanyar gate ina salati. Gaba d’aya a hautsine nake. Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun raji’un. Dakyar na samu babur na haye nai gidah. Ni kam inaga zan ajiye koyarwar da nake gaskia. Wannan wacce irin musibace? Dalibi na? Wancen yaron? Ko rabin hamshin yayi ne ma? Amman tsabar baida kunya ya kalli tsabar idanu na yace ni yake so? Ina matsayin malamar sa? Shi kuwa Mubeen murmushi kawai yayi ya harhada duk abinda ta bari yasa a jakar sa. Ya kulle mata ofishin. Domin jin sa yake wasai ya sauke abinda ke zuciar sa. Kuma yaci alwashin sai ya cusa mata son sa a zuciar ta.

Batoul kuwa sai data dawo gidah ta dau kudin da take ajiyewa ta bayar aka kaiwa mai mashin din daya kawo ta. Wunin ranar ko abinci kasa ci tayi. Sai data ji dama-dama ne ta sauka kasa zata yi wanka ta jiyo muryar wata mata tana kwarara ruwan bala’i tamkar zata babbaka gidan...

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_[8/28, 9:32 PM] Miss Xoxo: I⃠G⃠I⃠Y⃠A⃠R⃠____Z⃠A⃠T⃠O⃠


*42*


Haj Husnah ce ta shiga mayafinta a gefen kafada ta kumbura zata fashe saboda bala’i. Idanuwan ta sun sake shigewa ciki saboda masifa. Cire mayafin tayi ta daura a kugu tana buga hannuwa a bango,

“Kaltume! Kaltume! Kaltume! Fito nan dake zanyi billahil lazi.”

Kasa shiga bandakin nayi na fito daga lungu ina binta da kallon mamaki. Innar mu dake sama a daki bata tanka taba na tabbata kuma ta jiyo. Amman rankataf din yan gidan mu kowa ya firfito. Kawu ila ya dakko bokitin zaman sa ya zauna yana zabga tagumi,

“Baiwar Allah meya faru ne? Wacce shegiyar ce ta miki abu?”

Haj Husnah ta kalle shi a wulaqance tana yatsina,

“Ance kudin duk yan uwa ne anan ko?”

“Eh toh kusan hakanne, Wasu daga cikin namu dai ana dai zama dasu ne saboda babu yadda za’ai dasu. Kamar ita matar da kike kira itada iyalin ta..”

Haj husnah taja majina tana girgiza,

“Dakyau! Shegu ne yaran ko kuma yan uwa ne na nesa?”

“Ai Hajia sai dai abar kaza cikin gashin ta kawai..”

Haj Husnah ta sake kwafa tana bubbuga hannu a bango,

“Toh ku saurare ni. Yauwa bawan Allah ina kaltume mahaifiyar figalalliyar yarinyar can?”

Ta karasa fada tana nuno ni. Kawu ila ya kada kai kafin ya haye saman mu ina jiyo shi yana saukewa Innar mu ruwan masifa da bala’i. Ba jimawa sai ga Innar mu ta leko ta saman bene tana jan carbi,

“Okay kinfi karfin ki sakko kenan? Toh keda ‘yarki ku bude kunnuwan ku saurare ni dakyau. Kuma yan cikin gidan nan inason ku zama shedu.”

Banda rawa babu abunda jiki na keyi. Wannan wane irin cin mutunci ne har gidah fisabilillahi? Daman gashi rai na abace yake tazo tana kara min wani. Wai shinma meya kawo ta? Kenan Haysam karya yamin yace ta amince? Wallahi daman sai da Innar mu taita tambaya ta nace ta amince. Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun! Naita maimaitawa ina dafe da goshi na.

“Kada kiji komai Hajia. Tamkar agaban alqali kike kuwa. Zan tsaya miki akan komai daya hada ku. Dan basuda mutinci gaba dayan su dakika gansu. Shi yasa na hada na kwashe musu albarka..”

Cewar Kawu ila dake murmushin mugunta. Bintalo taja tsaki tana dankara masa harara,

“A hayye yau ga gaye ba makilis, sittin ta ubangiji sai dai kaga kwashewar albarka akan ka da yayan ka.”

Haj Husnah ta mata banzan kallo tana tsurtar da yawu a gefe hade da toshe hanci,

“Au ashe kema d’aya barauniyar kina nan. Ice ko andai na dan halin? Ku kuwa dai bakuji dadin rayuwar ku ba wallahi.”

“A hayye nanaye! Hajia kenan, Nifa yadda kika ganni nan sittin ta ubangiji sai na zugewa mutum ta zuge duk girman sa wallahi. Hakki na da aka hanani kwa biyani a lahira.”

“Sai ki zuge ai banza kazama, Bakida aiki sai sosa takashi kina tsamin wari. Banza barauniya wadda ke neman mijin wata..”

“Ahayye yau ga gaye ba makilis! Neman mijin wata fa kikace hajjaju? Yo ai kema mijin watan kika aure ai ba kece matar sa ta farko fa. Munsan shafe shafe, Munsan mai. Munsan jagira da hoda..”

Haj Husnah taja tsaki tana yamutsa fuska,

“Karamar yar iska. Miji na ya miki nisa wallahi. Ko a mafarki mai kama da inuwar sama ba samu zaki ba..”

“A hayye nanaye... Oho dai! Nide nagaya miki kema mijin watan kika aure. Kuma mata hudu rigis gis sai alhajin ku yayi.”

Gaba d’aya sai muka zama yan kallo mu kalli waccen mu kalli wannan. Sai bankada maganganu suke yi. Ni wallahi banmasan abinda ya faru kenan ba. Ai gashi nan tasu taxo ta hada su. Sai da su kaiwa juna wankin babban bargo tukun sannan kowannen su yai shiru. Haj Husnah taja fasali kafin ta shiga karkadawa Innar mu hannuwa,

“Kaltume ina figalalliyar ‘yarki ina ‘dana? Tun shekarun baya na miki kashedin ku rabu da ‘dana. Kun mai dashi saniyar tatse yana dauke mu wahalhalun rayuwar ku. Cin ku, Shan ku, Suturu duk shine, Hakan bai ishe ku ba sai da kuka asirce shi yaso wannan jemammiyar yar taki?

“Ai ruwa ba sa’an kwando bane. Toh ku saurare ni wallahi baku isa ku hada aure da dana ba billahil lazi. Kalle ku mana, Kuna fama a gidah duk sai hayaki da warin talauci. Ina tunanin daki dai dai ne daku ma. Kina matsayin yar aikin mu kice zaki bawa yar ki dana? A garin wani gab’a gaban mahaukatan ake haka?

“Ai wutsiyar rakumi tayi nesa da ‘kasa, Dai dai ruwa daidai tsaki. Kwarya tabi kwarya akeyi. Badan ma aikatan da kike mana ba ada ke kin isa ma ki doshi kofar parlor na? Bankadaddu, Matsiyata, Mugaye kawai. Dan tsabar ba Allah a ranku shine kuke tunanin hada zuri’a ta daku? Da wannan shegiyar yar taki? Da ake yawo da ita a gari. Jami’a kala nawa tayi yanzu tana koyarwa ga gawan tazubar. Yar iskar ya.....”

Zubewa nai a kasa ina kuka, Wannan wane irin cin mutinci ne haka? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Haysam yamin adalci kenan? Ya nuna min ta amince yanzu gashinan tazo har gida ta dankara mana rashin mutinci. Innar mu ce ta sakko ta tari numfashin ta.

“Ya isa hajia dakata! Inaso ki koma ko ki kira dan naki ya zama sheda. Wallahi summa tallahi tun Batoul batasan menene so ba Haysam yake sonta. Yarinyar nan Allah ne shahidi wallahi tallahi bata son ‘danki. Shi kanshi ya sani. Shekaru nawa yana bibiyarta akan ta amince ya turo manya? Idan baki sani ba ki sani har ca yai mata kin amince suyi aure. Kamar yadda kika fada Hajia ba karya kikai ba,

“Tabbas wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Batoul ba tsarar auren Haysam bace. Kamar yadda shima ba tsaran auren ta bane. Adduar kowacce uwa akan yarta shine ta samu miji nagari, Adali mai ilimin addini wanda zai ci da ita ya tufatar da ita ya kuma biya mata bukatun ta idan sun taso. Kuma kowacce uwa zata so yarta tasamu dangin miji wanda suke sonta sukeson iyayen ta. Wanda zasu sota tsakani da Allah su dauke ta tamkar ‘yar da suka haifa. Saboda suma za’a kai nasu yaya matan wani dangin mijin,

“Shi fa komai na duniya idan kai dakyau zaka ga dakyau wallahi. Duk abunda ka shuka zaka girbe shi Hajia. Ita bintalon data fara rura miki wutar ai ga irinta nan tagani akan nata ‘yayan. Saboda shi sharri dan aike ne duk inda yaje sai ya dawo maka ko wanin ka. Saboda haka karki kara zagemin yarinya wallahi. ‘Yata ba yar iska bace, Tayi karatun ta boko da arabi cikin aminci. Tsayuwar datai akan turbar gaskia shiysa gashinan rayuwar tata kullum kyau take. Kuma ina tabbata miki cewar dan ki ma abunda yagani kenan ya nace mata. Kuma inason ki cire ki cire *ZATON* ‘danki zai auri Batoul. IN SHA ALLAHU! Yadda bakyason ta Allah bazai sanya ta shigo ahalin ku ba. Allah ya mana tsari daga gare ku Hajia. Batoul tayiwa Haysam nisa na har gaban abadan IN SHA ALLAHU! Allah zai azurta ta da miji wanda ku kanku sai kun amfana dashi. Wanda zaki ciji yatsa da yardar Allah.

“Sama tayiwa yaro nisa sai dai yata da kai ya kallo. Toh haka Batoul zatai wa Haysam ni sa. Nisa wanda kudi ko mulki bazai taba sa ya same taba. Akan haka dama kiketa kumfar baki? Gaba dayan mu Allah ne yayi mu daga ‘kasa Hajia. Talaka da mai kudi duk rami d’aya za’a zuramu wallahi. Kuma sai kiga talakan da aka rena shine mafi soyuwa agurin Allah. Kuma kisani badan baya sonsa bane ya yi shi a talaka. Kada ki manta gidan biyu ne akwai na lahira wanda shine na gasken

Please Login or Register in order to submit comment