Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taburmin dake daki suka yasar dasu,

“Kai na dauka zanji ni garau wallahi ashe fanko ce?”

Mu’azzam yace da Alhaji yana gyara tazugen wandon sa, Alhaji ya bushe da dariya yana kallon tarin cikon dasu Alawiyyah su kai,

“Ciko ne ashe, Gwarama tawa tafi gwab’i gwabi.”

Suka sake bushewa da dariya suna tafawa. Su Alawiyyah basu farfado ba sai washe gari. Da kuka kowacce ta tashi, Alhaji labaran ya shiga basu hak’uri yana kalallame murya,

“Wallahi al’adun yaren mu kenan, Kuma ba wai me gaba d’aya akai ba. A’a! Gwaji ne wannan na ganin ku din yammata ne ko kuwa? Amma hakan shine ya nuna mana kudin yan halak ne. Har shedar haka muka dauka mu ka kai gidah wajen su Hajian mu. Sun amince, Mun gama shawarar a wannan shekarar za’ai au..”

Bai karasa ba Alawiyyah ta rungume shi tana hawayen farin ciki,

“Wayyo dadi! Alhaji wannan daddadan labari naka kwarai ya kauda duk wani bakin ciki dake zucia ta. Na amince da kai domin da yaudara ce ta kawo ku da tuni kun gudu kun bar mu anan.”

Alhaji ya girgixa kai yana murmushi, Hinde ma ta kwanta a kirjin Mu’azzam tana jan majina. Abinci suka basu suka ci suka k’oshi, Sannan suka yawata dasu a garin na kaduna, Sai gab da magriba suka mai dasu zaria cike da kayan k’walam da makulashe. Bintalo sai shewa take tana kururuwar kayan dadin da suka zo dasu, Babu mai tambayar a’inda suka kwana. Tun daga wannan rana Alhaji Labaran da Mu’azzam suka mai dasu Alawiyyah tamkar matayen su. Bidirin su kawai suke dasu acewar al’adar yaren su ce ta kawo hakan......

___
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼

__
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*_IGIYAR ZATO_..........💕_*


_*NA_*


_*NANA HAFSAT_*
_*(MISS XOXO🧕🏼)_*


_®️ZAFAFA2020_*
_(TAKU NA BIYU)_


ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE, ME SO DAN GIRMAN ALLAH YA BIYA YA KARANTA HANKALI KWANCE😘❤️

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*2️⃣1️⃣*


*BATOUL*

Hutuna na farko da nazo gida naga tashin hankali wanda yasani yin nadamar dawowa gidan mu, gashi Innar mu ta shiga halin ciwo domin jininta ne yake yin k'asa, daga sakkowa kasa zuwa hawa sama sai tayi fad'uwa biyar, amman babu mahaluk'in da zai taimaka mata, daman Usaiba ce, to itama tunda taga kwana biyu bana gari kayan dad'i sun dena shigowa Innar mu dai ta dena kulata. Kowa a gidan mu bashi da mutunci yaransu da manyan su, na kalli Innar mu dake kwance akan tabarma nace.

“Yanzu Inna kina da katon saurayi mai jini a jiki amman ki bari a yi miki nisa dashi? Haba Inna, ya kamata kema ki dinga kwato hakkinki a cikin gidan nan, su waye ya korar mosu d'a ko 'ya daga gidan nan? Dubi yadda kike fama da ciwo duk kin kuma ramewa babu mai kulaki bare ya taimaka miki. Inna kisa Yaya Najib ya dawo gabanki kodan kula da lafiyar ki, idan kuma ba haka ba ni na tattaro na dawo gida, domin lafiyar ki tafi komai a tare damu.”

Na karasa maganar ina zumb'ura baki, dan har cikin raina abun da ake mana ya isheni. Gabaki d'aya sun tarwatsa farin cikin mu bayan babu abinda muka tare musu.

“Uhmm! Mai sunan uwa ba zaki gane duk wani abun da nake son ki fahimta ba, gani kike yi kamar rashin wayo ko rashin fitowa nayi rashin mutunci shine ya jaza mana shiga cikin wannan matsatsin rayuwar. Ba haka bane, kinga na farko gidan nan ina zauna ne albarkacin haihuwar ku da nayi a cikinsa. Sannan ke da Auta mata ne, dole nan gaba wajan su za'a zo neman auranku, toh idan nace zanyi cece ku ce dasu ki gaya min waye zai zama dangin ku koda bayan babu nawa ran? Kina gani yanzu a hakan ba wa bai gama yadda sukai cewar mahaifinku shine ya haifeku ba saboda tsabar kiyayyar da suke yi min.”

“Toh Innar mu a haka zamu barki cikin wannan larurar bayan su basa kulaki?”

Nayi saurin tambayarta domin naga alamar ba zata gane irin zafin da nake ji ba da na ganta a haka.

“Eh kubar ni a haka ina tare da Allah, kedai ki dage kiyi karatunki nan gaba zakiji dad'i koda babu ni a raye nasan zaki kula da kanwarki. Bana son ki kuma cewa zaki dakatar da karatunki, kiyi shi koda babu dad'i saboda watan wata rana.”

Kwallar da ta taru a cikin idona suka fara zubar da hawaye, nasa hannu na share ina kuma jin tausayin Innar mu. Kud'in da na dawo dasu sune naje na saro kayan siyarwa saboda na tara wanda zan koma dasu da kuma abubuwan da zan tafi dasu, cikin hukuncin ALLAH Awarar da na fara yi kuma a cikin gida sai ALLAH ya sanya min albarka a cikin ta, duk da cewar 'yan gidan mu bashi suke karb'a kuma basa biya. Amman Alhamdulillahi! domin ina samun riba duk da suna kin biya na. Kafin na koma makaranta Innar mu da Autar mu har sun maida jikin su saboda a kalla zamuci sau uku, gashi Yayan mu ya turo da kudi dan haka kafin na tafi sai da na tabbatar suna da d'an abun da zasu yi amfani dashi.

Ina tafiya babu dadewa aka yi biki a gidan mu, wato bikin Fareedah yar gidan kawu Dawood, wadda bikin ya haddasa hatsaniya inda akai ta yiwa su Alawiyya gorin cewa sunki auruwa sai yawo da suke faman yi babu mai kwab'ar su. Da kyar aka gama bikin nan, lokacin da na kuma komawa hutu ne Innar mu take gaya min, cikin zuciyata ina addu'ar ALLAH yasa ni dai kar lokacin biki na 'yan gidan mu su wulak'anta ni domin ba mutunci gare su ba.

Haka nayi karatu na cikin zan gama ko kuwa ajiyewa zanyi, saboda kud'in registration yana matuk'ar bamu wahala. Haysam kuwa tunda ya lula k'asar waje ban sake jin duriyarsa ba har lokacin da na kammala Degree d'ina.

*2013*

Cikon ikon Allah na dawo gidah da dimbin alheri, Domin na samu yabo sosai daga wajen malamai na kasancewar Allah yayo ni da kaifin daukan darasi komai yawan sa. A shekarar dubu biyu da goma sha uku na kammala karatu na a jami’ar Ahmadu bello dake nan Zaria, Na karanta ‘bangaren zallar turanci wato B. A English! Shekaruna a yanzu haka ashirin da uku.

Bayan wasu yan watanni sakamakon kammala karatun mu ya fito. Masha Allahu! Domin na samu sakamako mekyau inda na fito da upper second class! Hakika nayi farin ciki fiye da tunanin mai tunani, Wai ni batoul ni ce na kammala digiri har ana shirye shiryen tafiya bautar kasa. Hakika na sake gogewa da kyau domin akwai cima me kyau a makarnta da muke ci muke dafa abinmu da yan dakin mu na hostel, Sannan ruwan famfo ne acan wanda ya kara gyaramin jikina, Fata ta kara kyalli da laushi.

Tsangwama da kyara kuwa sai abunda yai gaba a gidan mu. Musanman yadda yanzun muke samun ci da sha abinci sau uku babu fashi. Allah ya sanya albarka a awarar da nake yi. Layi layi ake zuwa siyan ta domin inayin mai inganci a kuma tsaftace, Bayan watanni biyu sunan mu ya fito a wanda zasu tafi bautar ‘kasa. Alhamdulillah domin kaduna aka tura ni. Yar ribar awara ta bayan na bawa Innar mu nasu kason na hada sauran nayi yar siyayyar shiga camp. Wohoho zo kuga bakin ciki awajen yan gidan mu, ‘karara suka fito kowannen su bai ji dadin yadda nake samun cigaba ba, kan kace me? Tuni sun yanyana maganar na zama me yawan tazubar gari gari. Toshe kunnuwa na nayi a daddafe na tafi kaduna a gidan Gwaggo Aminatu na sauka washegari suka kai ni can camp. Sati uku na yo acan aka turani kaduna state affairs office, acan na fara service dina, duk ranar jumu’ah nake zuwa zaria nayi kwana biyu na koma can gidan Gwaggo Aminatu. A haka har na kammala shekara d’aya.

*2014*

Alhamdulillah ba abunda zance da ALLAH sai godia da kuma fatan karawa annabi daraja hade da yalwar farin ciki a tattare damu, Lalle Allah qadirun ne mamallakin kowa da komai. Yayan mu ya sanar mana cewar ya kammala karatun sa a sa’adatu rimi collage of education, Yanzu haka mai gidan sa dake kasuwar singa ya fara koya masa harkar sarrafa shinkafa da fulawa, Ya na aiko mana da sakon kudi lokaci zuwa lokaci, Gwaggo Aminatu tayi ciku-cikun samamin aiki amman hakan yaci tura, Daga karshe ta samamin tallafin karatun digiri na biyu a jami’ar Abu dake nan zaria. M.A English! (Master of Art in English). Alhamdulillah ya ALLAH lalle Allah mai daga wanda yaso ne a duk sanda yaso. A kuma shekarar ne Haysam ya dawo daga k’asar waje ya kammala karatun sa har zuwa matakin PhD!!

Ina shirin tafiya fara karatun masters d'ina ne kawu ila yace ALLAH ya kashe shi ba zan tafi makarantar ba, a lokacin ne ya kawo min wani abokin Yusha'u wai sai na aure sa. Rigima ta b'alle a tsakanin Gwaggo Aminatu da kawu ila domin ita tace sai naje nayi, kuma babu mai yi min auran dole. Shi kuma ya dage cewar idan har banyi aure ba daga can master's d'in na kara gaba, shi duk a tunaninsa karatun da zanyi shima boarding ne, bai sai zuwa zan dinga yi ina dawowa gida ba.

Lokacin da na fara zuwa lectures a lokacin ne Haysam dan yaga ya kara girma da wayewa domin d'an gayu ne sosai. Sai dai yana zuwa da batun aure na gurin Haj Husnah wato mahaifiyarsa, ta nuna masa cewar sam bata yadda ya aure ni ba.

-
Ignore all typos👏🏻Afuwan ido ya matsa, Ma hadu a next page 👏🏻
-
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


_*SITTIN TA UBANGIJI..._*
_(Labarin sarqaqiyar rayuwa cunkushe da kauna)_😘❤️❤️


_NA_


_HANSAI ME GLASS_


2️⃣2️⃣


•<>•<>•<>•


Gyara zama Haysam yayi tare da ajiye remote d'in dake hannunsa yana fuskantar mahaifiyar sa, cikin yatsina fuska yake cewa.

“Ummah ni ya zaki ce ba zan auri Batoul ba? yarinyar nan tana da nutsuwa da hankali, uwa uba biyayya, shin menene aibunta na cewa ba zan aure ta ba ummah?”

“Kai tafi can sakarai kawai, toh tsaya ma, duka-duka nawa kake da har zaka ce min zaka yi aure banda neman rigima? Toh ba zaka auri Batoul ba indai da gaske kake yi na cewar ka matsu kayi auren, toh kaje ka samo ko wace yarinya ce zan amince maka, amman banda Batoul, sam yarinyar bata kwanta a raina ba.”

Haysam ya rintsa ido yana jin tamkar kansa zai tsage saboda bai yi zaton hakan zata kasance ba na k'in amince masa.

“Ummab me yasa?”

“Kaga Haysam karka takura min da maganar wannan yarinyar, nace maka ba zaka aure ta ba, idan kai mai biyayya ne a gare ni toh karka kuma yi min maganarta na gaya maka.”

Jikinsa yana rawa haka ya mike ya nufi sashen sa hankali a matuk'ar tashe ko ganin gabansa baya yi saboda tsabar tashin hankali.

*GIDAN MATA TARA*

Dawowa ta daga kaduna kenan na shiga gidah ina sallama, Gaba na kuwa banda fad’uwa babu abinda yake yi. Runtse idanuna nayi ina addu’oi a hankali. Gaba d’aya tsakar gidan namu a hautsine yake da hayaniyar 'yan gidan mu. Kowanne kara-kainan sa kawai yake, Yan layin bandaki nayi, Yan wanke-wanke nayi, Masu wanki nata dirjewa, Masu tsegumi kuwa kowanne kusufa kwa ga curin su. Innatuwa dake gugar kaushin kafar ta ta dago ta dube ni Ina k’ok’arin dorawa autar mu ledar kayana a kanta don hayemin dashi daki. Ta sake barbajewa a kafar benen taki ta matsa na wuce, Na dubi wawan zaman da tai na dauke kai na ina girgiza kai cike da takaici, Innatuwa ta kaikace tana sakin murya, Wanda kai daka ji abinda take cewa kasan gugar zana ce dani take,

“A hayye tayi kwantai, Godiyallare babu mashinshi ni, Yawan ta zubar shine agaban su, Gandar-dar, Rasausau, A hayye babu mashinshi ni. Sai nanaye kwararo kwararo da sunan karo karatu..”

Dafe kai na nayi, Jin shirmen zantukan dake fita daga bakin ta godai-go’dai da ita. Cikin kosawa da maganar ta na muskuta zan wuce ta gefe,

“Maman Yusha’u zan wuce.”

“Toh kai! to kai! to kai! Taka ni mana ki wuce sai nasan ke ‘kwankwararriyar yar bariki ce.”

Saurin shigewa nai ina jan hannun autar mu domin nagaji da masifar yan gidan mu ta gaira babu dalili. Ina hayewa na jiyo sautin muryoyin su suna zuga Innatuwa wai na mata rashin kunya karta yadda, Bintalo dake tsaye tun sanda aka fara caftar ta callara kara tana buga zanin ta,

“Sittin ta ubangiji innatuwa karki ragawa shegiya, Ki daka ta ki gurji bakin yar bariki, Wai dan ta zama karamar yar tasha fa shine take irin wannan zantukan. A hayye nanaye!”

Murmushin takaici nayi ina jiyo su daga dakin Innar mu, Na cire hijabin jiki na na ajiye a gefe ina firfita da murfin bokiti. Gaba d’aya ni yanzu hayaniyar su ciwon kai take sani, Saboda na kara hankali. Kuma Innar mu kullum cikin yi mana nasihar zaman duniya take. Hira muka dan taba da Innar mu dake sakace kunnanta da tsinken kaza. Bayan sallar magriba na jiyo sautin wasu yara suna ambatar sunana,

“Wai ana kiran batoul awaje.”

Kawu ila dake zaune yana gyara bokitin sa yaja tsaki yana watsa hannu baya had'e da zare musu idanu yace,

“Kai kunci bantan uban ku! Wai tazo inji uban wa?”

Cike da rawar jiki suka fice aguje ganin yadda ya razana su. Ba jimawa wani almajiri ya sake shigowa a karo na biyu da karfi ya shiga dankarawa sunana kira,

“Wai ana sallama da Batoul a waje.”

Kawu ila ya sake jan dogon tsaki a karo na ba adadi, bokitin nasa ya dauka ya shige dakin sa ransa a matukar b’ace, Da alamun wani abun ne ya samu rabin ran nasa.

Hijabi na na zura na sauka kasan bayan na cewa Innar mu ana sallama dani, Daman da niyyar duk wanda yazo zance masa anbada ni gudun kada Kawu ila ya kara ‘kagamin wani sharrin, A soro nai kicib’is da Haysam sanye cikin kananun kaya samfarin jins sa riga mai dogon hannu, Ya sanya hular sanyi kasancewar ranar sanyi na dan busawa, Hannuwan sa zube cikin aljihun wandon sa.

Murmushi na dan yi masa ina lankwasa yatsun hannaye na, Ganin yadda yake wani shasshafe saje yana kobarewa irin ta samarin nan sai abun yaban daria, Lalle mai hali baya fasa halin sa,

“Ya Haysam! Barka da dawowa.”

Na karasa fada ina lekawa cikin gida gudun kar Kawu ila ya taho ya sauke mana kwandon rashin mutuncin sa. Idanuwan sa ya narkar a kai na yana wani langab’ar da kai,

“Mine! Nayi kewar ki da yawa wallahi har rama nayi.”

“Lalle yaron nan!”

Na fada a zuciata ina mamakin kalaman sa. Gaskia yana da tsaurin ido ba ka’dan ba. Ajiyar zucia na ja na sauke kafin cikin kallon kasa nace dashi,

“Ya Haysam an dawo lapia?”

“Alhamdulillah mine! Anya kinyi kewata kuwa?”

Murmushi nayi kawai,

“Ai dole nayi kewar Yaya na! Da fatan an kammala karatu lapia? Allah yabada nasara mai dorewa Ameen!”

“Mine ko sau d’aya baki taba kira na ba da ina cyprus meyasa?”

“Bani da number ka ne shi yasa”

Karkada kai yayi yana cizan leben sa na kasa,

“Shikenan mine, Har yanxu dai alamu sun nuna bakya ra’ayi na ko? Shin har yanzu ban isa ba ne ko kuwa ban kai ba. Ya kamata ki cire *ZATON* da kike a kai na. Dan ALLAH ki sassauta min Batoulll..”

Cikin son kauda maganar da yake yi na sake gyara tsaiwa ta ina girgiza kai,

“Ya Haysam na kammala digiri dina fa, Yanzu haka na dora da master. Kai ne kai tushen komai, Nagode ALLAH ya saka maka da alkhairi.”

“Toh ya batun fara zuwa zance?”

Dan satar kallon sa nayi yana sake tura hannun sa a aljihu alamun sanyi yake ji sosai ganin yadda yake karkada k’afafuwan sa. Na rasa amsar da zan bashi ma, Gashi ba naso Kawu ila ya fito ya ganshi.

“Kayi hak’uri Ya Haysam zanyi tunani Allah ya zabi abunda yafi alkhairi..”

“Ameen Mine! Haka kika kara girma?”

Murmushi nai kawai ina juyar da kai na gefe,

“Lalle kaga makwanci na.”

Na fada a zuciata ina mamakin tsaurin idon sa. Keya ya sosa yana murmushi. Sallama yai min zai fita Bintalo ta shigo zauren da gudun ta. Ganin sa yasa ta kunduma uban ihu tana kururuwa,

“Ilyasu! Ilyasu Ilyasu..”

Komawa ciki tai da sauri tana kiran Kawu Ilyasu, Nayi saurin sallamar Haysam na koma ciki ina raba idanuwa sanin sharrin da Bintalo zata gaya masa. A tsakar gida nagan su tsaye tana kwaso rantsuwa tana direwa hade da watsa hannu baya tana buga zani,

“Sittin ta ubangiji ta bada maka kasa a idanu, Toh ga tanan ma makira algunguma.”

Bintalo tafada tana nuna ni da shigowata kenan, Kawu ila ya kumbura tamkar zai fashe don takaici. Hannu yasa yana karkada shi a kai na,

“Ai dole ki fandare kin rigada kinfi karfi na, Tacacciyar yar iska! Wato ke ishasshiya ko? Shine zaki watsa min kasa a idanu ki sake tsayawa da yaron nan? Shin iskancin naku bai isa acan ba har gidah yake biyo ki?”

Shiru nayi ina girgiza kai na yayin da ambaliyar hawaye ke tsiyaya a idanu na. Shin wannan wacce irin rayuwa ce? Ya Allah ka kawo karshen wannan sarqaqiyar rayuwar! Subhan’Allah.

“Ba magana nake miki ba? Kinci bantan uban ki. Ai dole kiyi shiru tantiriya.”

“Kayi hak’uri Kawu”

“Hak’urin uban uban ki? Bance karya sake zuwa ba?”

Shiru nayi kukan da nake yaci karfi na, Naja majina ina goge hawayen fuska ta. Muryata na rawa na shiga girgiza kai ina hada hannuwa na alamun ban ha’kuri,

“Kayi hak’uri Kawu! Nayi kuskure ba...”

Ban karasa ba Bintalo tasha gabana tana buga zani hade da watsa hannu baya,

“Sittin ta ubangiji karya kike yi, kina sane. Ilyasu ku aurar da yarinyar nan ko da ga d’aya daga cikin almajiran gidannan ne. Kar taje ta ebo mana abun kunya, Kaga dayan shegen da yasan abunda ya aikata tun da ya gudu ba mu kara ganin keyar sa ba.”

“Abunda za’ai kenan, Tunda ta watsa min kasa a idanu. Gwara a d’aura da wuri tun kafin Yaya Aminatu taji ta hana, Bara na sami gwani shu’aibu yana wajen d’axu.”

Kawu ila ya fada yana zura takalman sa hade da gyara yar sharar rigar jikin sa. Ficewa yayi kamar walqiya yana mita shi kadai. Bintalo ta callara gud’a hade da tafe hannaye tana buga zanin ta.

“A hayye nanaye! Sittin ta ubangiji mun kusa rabuwa da ‘kaya.”

Girgiza kai na nayi na fara hawa mattattakalar bene ina sharce hawaye ganin auren sadaqa za’ai da ni akan abunda bai taka rawa ya karya ba. Ina hawa kafar bene ta biyar kenan muka jiyo ihu, An shigo gidan da gudu da yara rab’e rab’e su biyar suna binta a baya. Juyawa nai ina don ganin waye? Zabbau ce yar Bintalo ta farko ta shigo itada yayanta su biyar. Ta baje a kasa tana birgima hade da kurma ihu. Tuni makota da ahalin gidan mu suka bayyana. Cikin muryar kuka hade da shure-shure da zuban ruwan majina zabbau ta callara kara tana surutai,

“Ya sau ni Baba, Walle talle ya sau ni. Shika uku yayi min, Y’aya kuma yace walle bana shi bane”

Cewar zabbau cikin hausar ta ta yan karkarar kod’e. Tana gama fada ta shiga bubbuga kanta a jikin rijiya tana kuka, Bintalo ta yage zani tana ihu,

“Na shiga uku ni Bintalo. Sittin ta ubangiji yaron nan ya cucen. Ke ‘yarnan gayamin gaskiyar lamari.”

Dede da shigowar Kawu ila kenan shi da badamasi mai kwasar kwata kuma almajiri a makarantar almajiran gwani shu’aibu dake kofar gidan mu. Da alamun shine mijin da zai aura min, Domin badamasin sai dashare yalayen hakoran sa yake yana susar duwawu.

“Na shiga uku! ALLAH ka tsare ni.”

Na fada ina runtse idanu na. Gaba d’aya a hargitse yake, Sanye cikin kananun kaya duk sun daddare sun kode sai hamamin wari ne ke tashi a jikin sa. Kawu ila ya janyo bokitin sa ya zauna yana kallon yadda zabbau ke birgima tana nana ta,

“Ya sau ni Baba, Walle talle ya sau ni. Shika uku yayi min, Y’aya kuma yace walle bana shi bane.”

Baba usaiba dake gefe taja guda tana watsa hannu,

“Kutsin ubancan kayya kai!”

Salati kowa ya hau yi ana tafa hannaye, shidai gidan mu kullum ta Allah sai an samu wasu abubuwan na rashin jin dad'i da zai faru, gashi aka rasa wanda zai ce Zabbau tayi shiru tana ta b'are baki kamar wata jaririyar akuya, yaranta na tsaitsaye sun zuba mata ido suma.

“Rabu dashi Zabbau, dole ki koma gidan mijinki. Shi dan bashi da mutunci tuntuni bai san yaran ba nashi bane ba sai yanzu? Naji ance aure yake nema ina jin shine dalilin da yasa ke ya sakeki dan ya samu dakin da zai sanya sabuwar.”

Cewar kawu Ishaq wanda ke tsaye yana asuwaki da ican darbejiya, nan fa Bintalo ta sake bud'e murya tana kutuntumo zagi ta dorawa surukin nata, da kyar dai aka lallaba Zabbau ta shiga d'aki, yaran na biye da ita kamar bindi, Alawiyya na ta faman yatsina fuska dan tasan d'akin nasu kuma cunkushewa zai yi. Wannan sakin na Zabbau shine ya shafe maganar auren da aka ce za'a min, na dinga godewa Allah saboda shine ya rufa min asiri na kin yiyuwar auran da almajiri.

••••••; •••••••; •••••••

Tsab na shirya saboda a ranar karfe goma muke da lecture, amman saboda na isa da wuri sai na shirya da wuri. Jakata na d'auka na yiwa Innar mu sallama, ita kuma Autar mu tana shan kunu da Awara gefenta uniform d'inta ne tana so idan ta kammala itama ta shirya ta tafi makaranta. Ina fitowa tun daga saman bene na hango 'yan gidan sun zage wata a tsakiyar gidan, na sauka a hankali ina satar kallan wajan dan na hango ko wace aka kewaye ana ta faman caccakar ta, naji muryar Hafsatu matar kawu Dawood tana cewa.

“Daman duk kayan da suke shigowa dashi tukwici ne na bada jikinsu da suke yi, gashi dai yau ALLAH ya bankado asirin ku su Hinde. Wai cikin shege Hinde, su Bintalo ana min gorin nayi saurin yiwa Fareedah aure, wai dan naga bani da budurwar da za'a dinga yiwa hidima. Ahayyeee nanayeee yau ga jika mun samu na shegu.”

Da gudu Bintalo ta fito daga cikin d'akin ta ta diro kan bayan Hafsatu jikake dim..tim..ragajaf..jaf, tana dukanta. Nan da nan fad'a ya tashi, ni dai dana lek'a naga yadda Hinde take jibga uban amai, nayi sif..sif na bar gidan. Yau ALLAH ya nunawa 'yan gidan mu kalar wad'anda zasu kwaso abin kunya, ni da suke tunanin zanyi gashi nan ko tsayayyen saurayi bani dashi saboda duk maso son nawa wad'an da nake so na aura yawancinsu suna da mataye, wasu kuma su kawo min

Please Login or Register in order to submit comment