Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na sakko k'asa inda na tsaya ina sanar da Innar mu ana kirana a k'ofar gida. Amsa min tayi da kai hakan yasa na fita ba tare da na sake cewa komai ba. Abin yayi matuk'ar bani mamaki ganin Mubeen a tsaye ya zare glasses d'in yasa a gaban aljihunsa, face mask d'in ma ya sanya a aljihu yana facing k'ofar gidan da alama baya son mutane su gane shi.

“Mubeen..!”

“Mah.”

Ya amsa yana mai karasowa cikin zauren gidan mu. Daman ina son ganinsa kuwa domin nayi masa wasu tambayoyi game da exam din sa.

“Ya akai kazo gidan nan wani abun ne?”

“No Mah, zuwa nayi kawai mu gaisa.”

“Okay na gode, but Mubeen ya akai haka? Ya akai naga duk test's d'in da nayi muku kaine me highest scores a ajinku. Sannan ko questions nayi kafi kowa bani amsa, but exams kayi failing baka rubuta komai ba sai wani irin language why Mubeen?”

Wani irin azababben dad'i yake ji idan har yaji ta kirashi da Mubeen. Lumshe idanunsa yayi tsawan mintuna ya bud'e su akan fuskata wacce nima kallonsa nake yi ina mamakin yadda naga yana dafe kirjinsa.

“Mah banyi k'ok'ari ba ne?”

“K'ok'ari kuma? Bama kayi exam din ba domin baka rubuta min abinda na tambaye ku ba.”

“Sorry ma'am

“Sorry for your self Mubeen, domin babu ta yadda za'a yi na taimaka maka. Dole kaga sai ka kuma maimaita courses d'in.”

K'asa yayi da kanshi yana jin wani irin farin ciki, yana sane yaki bari yayi passing exams din na saboda baya kaunar duk wani abinda zai sanya nisantaka a tsakaninmu. Kafin yayi magana muka jiyo hayani a cikin gidan, Zabbau da Alawiyya suna fad'a, tun suna yi a cikin d'aki har sai da suka fito tsakar gida. Had'a ido muka yi da Mubeen na dankara masa harara kafin na yatsina fuska dan bana son ayi abinda zai rage min kima a gaban duk wani mai ganin darajata nace dashi.

“Shikenan kaje na gode da ziyara.”

“Wallahi sai kin biya ni fate ne dan abu takazar ki. Kin san da k'ak'a naje na samo shi da zaki zo kisa sharb'eb'iyar kafarki ki kifar min?”

Haushi kunya takaici bakin ciki duk suka taru sukai min yawa a cikin zuciya ta. Na juya zan koma ciki na ji ya kira ni.

“Mah.”

Kamar karna juya domin a kunyace nake saboda harga Allah banji dad'in yadda yaron yaji ana fad'a a gidan mu ba. Kura min ido ya yi yana cewa.

“Ki bani numbern wayanki please Mah karki hanani dan Allah.”

Ya zanyi dashi? Ya riga ya had'a ni da Allah hakan yasa na karanto masa ya juye su a cikin wata 'yar karamar waya sannan na shige gida dan gabaki d'aya kunyar kai na nake ji akan hayaniyar da Mubeen yaji ana yi kuma akan faten tsaki da Alawiyya ta samo a yawan ta. Kota kansu banbi ba haka na haye sama takaicinsu na damuna.

*GIDAN ALH KABEER MAI WAFA*

Zaune Haj Husnah da Alh Kabeer mai wafa suke suke suna karin kumallo a center carpet din dake tsakiyar parlorn. Haj Husnah ta nannada wainar kwai ta cusa a bakin ta tana kurbar ruwan tea,

“Alhaji maganar yaron nan shiru fa har yanzu..”

“Maganar wa fa?”

“Autan ka mana. Har yanzu ba aikin yi alhaji? Ga karatu fal yayo.”

“Toh ni me zance hajjaju? Yaron nan he’s very selective. Yanzu aiki ko wanne ka samu ai yi kake yi yanzu. Allah na tuba yanzu hustling kawai mutum yake like a dropout. Amman Haysam ya dakkota da zafi shi sai babban aiki saboda yayi karatu me zafi. Yace ba zeyi b’angaren bureau de change ba. Yace sai nnpc ko firs da cnn. Gaba d’aya fa harkar waka sani waya sanka ne?,

“Guraren da yake daukarwa kansa ni wallahi banida wanda na sani. Shi a komai albarkar ubangiji ake so ba son zucia ba. Nima abun kwatance ne awajen sa. Yasan matsayin da na ke a karatu amman tun ina matashi na da naga tsayawa neman aiki sai kanada hanya yasa na fara bin abokai kano. Tun muna zama muna kallon yadda yan canji ke yin kasuwancin su sannu a hankali har muka zama yaran su. Dake Allah yasa arzikin mu anan yake sai gashi kowannen mu ya zama babba. Duk mun kawo yadda muke yau, Su sauran abokan nawa da yawan su sun sanya ‘yayan su a harkar ana damawa dasu. Nima kinga ai sauran yaran sun shigo ciki amman na wajen ki ya’ki. Ya kike so nayi dashi? Allah ya bashi aikin da yake so...”

Ya karasa fada yana kafa kofin shayi a bakin sa. Hajia Husnah taja numfashi ta sauke tana sake narkar da muryarta,

“Toh Alhaji ai yanzu komai yazo karshe ko?”

“Saboda me yasa kikace haka?”

“Wai Amb Salees abokin ka da naga yaci takarar gwamna.”

Alhaji Kabeer ya dire kofin shayi yana mata wani kallo baki bude,

“Lalle hajjaju ni asuwa na zama abokin Amb? Ki rufamin asiri. Tsakanin mu dashi harkar canji kawai, Sai Y’ar kwangila idan ya bamu.”

Hajia Husnah ta yamutsa fuska tana cizan yatsa,

“Toh Alhaji Yaushe zaka kai mu gidan nasu ne? Inata damun ka tun kwanaki.”

“Haba hajjaju. Ni wallahi matar sa ma ko gaisawa sau d’aya muka tab’a yi. Lokacin na kai masa ya zabi yanayin yadda yakeson tsarin gidan nasa da ake ginawa...”

“Ance wai balarabiya ce ko?”

“Y’ar Ethiopia ce dai..”

“Alhaji kuma yaran ta nawa?”

“Nakejin kamar hudu ne fa. Amma meyasa kikemin wannan tambayoyin?”

Hajia Husnah tai murmushi tana lankwasa yatsun ta,

“Babu komai kawai dai inaso mu d’aura zumunci ne. Yaran nata manya ne kuma?”

Murmushi yai irin nasu na manya ne yana tattare burbushin kwan daya zube akan carpet,

“Hajjaju kenan. Kamar biyu ne manyan mace da namiji. Biyu kuma yara ne kanana...”

“Toh dan Allah ni dai Alhaji ka kai mu gidan nida Haysam. Ai ta haka ake sabo.”

Mik’ewa Alhaji Kabeer yai yana gyara zaman kayan sa. Yasa toothpick yana sakacen hakoran sa,

“Hajjaju mutan makka. Dai dai ruwa dai-dai tsaki dai. A tsaya daga nesa nesan dai. Wutsiyar rakumi tayi nesa da ‘kasa...”

Yana gama maganar sa ya haye sama yana girgiza kai cike da takaici. Gaba d’aya halin ta ya fara gundurar sa. Sai taita kai kanta inde Allah be kai ta ba. Sarai ya gano so take ta hada Haysam da y’ar Amb Salees bayan ko a mafarki hakan ba zata taba faruwa ba. Gaba d’aya ita da dan nata suna dorawa kansu abinda sam ba zai taba faruwa ba. Shi sai yanzu ya gano ma awajen Haysam din ya dauki halin sai abinda yakeso lalle zai samu. Yana hayewa sama taja tsaki tana zumburar baki.

“Yo ai gaskia ne. Ga inda zamu dandali arziki kana zizzillewa. Ni xan samo yadda zanyi naje gidan wallahi. Mu daura zumunci. Na zama sirikar yar gwamna...”

Tana fada tana tafa hannaye cike da farin ciki.Haysam dake lab’e tun sanda suka fara maganar gidan Amb Salees. Sai asannan ya shiga parlorn cike da takaicin halin mahaifiyar tasa. Ga wadda yakeso amman tak’i yadda sam, Wadda itace dai-dai auren sa. Ina shi ina yar dadadden ambassador wanda ya rik’e matakai da dama. Gashi yanzun kuma ya zama gwamna. Kansa a kasa ya karasa nesa da ita ya zauna,

“Ina kwana Umma?”

“Lapia lou.. Yanzu Ka tashi ne?”

Girgiza kai yayi yana yamutsa fuska. Ahankali yace,

“Duk najiyo maganganun ku. Umma dan girman Allah ki dena ma dakko zancen gidan Amb Salees. Gwamna ne fa mai ci a yanzu Umma. Bama haka ba kamar yadda Abba ya fada kwarya tabi kwarya ake fa. Ina ni ina neman auren yar sa? Ni wallahi bana son ta ma..”

Harara ta wurga masa tana bantarar goro a leda,

“Sallamammen banza da wofi, Ana ga gabas kana yamma. Shashasha, Sullutu sakarai. Ai duk dan kai nake yi, Saboda ka samu aikin yi kuma ka zama sirikin gwamna riba biyu kenan. Da xakace baka sonta ita dinma ai ba son naka take ba. Kuma ko da yaya sai na qulla zumuncin nan...”

Murmushi Haysam yayi yana mai cigaba da hada shayin sa,

“Ummah kenan. Ni fa ba mace bane da za’aimin auren dole.”

“Magana dai nagama ta. Aure ne tamkar anyi an gama ne.”

Mikewa yai ya fice ya bar mata parlorn hannun sa dauke da kofin shayi.. Taja tsaki tana hararar bayan sa.


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_[8/24, 5:26 PM] Miss Xoxo: _I˟˚G˟˚I˟˚Y˟˚A˟˚R˟˚ Z˟˚A˟˚T˟˚O˟˚_

N˟˚A˟˚

れ丹れ丹 卄丹下ち丹匕💞

37

•••. •••. •••

Bayan sallar magrib na idar da lazimin da nake yi sak’una har biyu suka shigo waya ta, Daya Haysam ne d’ayar number kuma bansanta ba. Sakon Haysam na fara dubawa inda yake shedamin zai zo zance bayan sallar ishai. Dayan number kuma sakon fatan alkhairi ne kawai. Daga kasa an rubata: ‘Mms’. Mubeen ne domin nagane sunan sa. Saving number tasa nayi saboda idan ya kira bazan dauka ba domin nagano wanene.

“Allah ya taya shi ri’ko. Allah yasa ya sauke alkawarurrukan daya dauka Ameen..”

Cewar Innar mu dake sake karo sautin rediyon ta.

“Innar mu wanene?..”

“Sabon gwamna mai ci.. Bani sunan sa. Yauwa! Ambasada ne ada. Wai Alhaji Salees Muhammad.”

“Allah sarki Allah yatashi riko..”

“Ameen! Ance dai gaskia adalin mutum ne. Domin wai ya ri’ke mukamai masu yawa a gwamnati.”

“Allah ya bashi ikon cika wa’ennan ma. Alh salees...”

Na maimata narasa ina nakejin sunan. Youtube na latsa na shiga domin inason naga hotan sabon gwamnan namu mai ci. Naci sa’a kuwa shine na farko a newsfeeds. Danna kan video din nayi na matsa kusa da Innar mu. Autar mu ma ta zuro kai tana kalla. Goge idanu na nayi da kasan mayafi don ganin wani tamkar Mubeen an haskalo shi a matsayin dan gwamnan mai ci.. Shine wallahi na nanata sunan nasa sai yanzu ma nagano ‘Muhammad Mubeen Salees.’ Zamewa nayi nayi zaman dabaro. Innar mu ta dube ni tana mikomin wayata,

“Ungo nan! Allah yasanya alkhairi..”

“Innar mu yaron sa dinnan da aka nuna a ajina yake fa..”

“Allah sarki..”

Innar mu tafad’a tana jinjina kai. Naja majina ina sake duba videon wallahi shine,

“Autar mu ina wanda yazo rannan dinnan? Wanda yasa takunkumi a fuska?”

Autar mu ta gyad’a kai tana tsalle,

“Har yace min baby..”

“Oh haba? Toh shi dai. Innar mu wanda nace miki ina zuwa dinnan? Toh ashe wannan yaron ne.”

“Kai Masha Allahu! Allah ya tayasu riko.”

“Hmm Ameen! Innar mu ya fadi duka jarabawoyi na wallahi..”

Suka zaro idanu suna kallo na.

“Toh fa garin yaya haka? Ko da yake tasa kaddarar kenan.”

“Wallahi kuma bakiga ba Idan akai tambayoyi yafi kowa amsawa. Kuma sauran gwaja-gwajen zangon karatu wallahi duk yafi kowa ci. Amman ya fadi exams din. Kuma jarabawar itace mai makin da yawa.”

Na karasa fada jiki na a sanyaye. Innar mu ta jinjina kai cike da tausayi. Ta numfasa kafin tace,

“Toh Allah yasa hakane yafi alkhairi. Ai kila kuma zai bar makarantar yanzu. Kinga kaduna zasu koma ba dad’ewa.”

“Gwara ma wallahi. Ko su futar dashi waje ya karasa. Ko da yake daga can suka dawo fa. Mahaifiyar tasa ma yar wajen ce k’asar Ethiopia.”

“Au haba? Shi yake fada miki?”

“Eh wallahi wai baban nasu ne hausa/fulani.”

“Toh Allah ya hada kowa da rabon sa. Kede hakan ba zai janyo miki matsala ba ko? Kin kada dan gwamna a jarabawa?”

Na numfasa ina girgiza kai,

“A’a banaji gaskia. Saboda babu ta yadda za’ai a wutar da shi. Sai dai fa idan manyan makaranta ne suka sa baki. Tunda kinga gaba d’aya kasar ma akan tafarkin da take kenan.”

“Zahiri! Toh Allah yabamu sa’a dai....”

“Ameen Ya ALLAH...”

Cikin haka aka kirawo sallar ishai. Muka muke muka yiyyi. Bayan na idar da addua. Ina ninke sallayar mu na dubi Innar mu,

“Innar mu wai Haysam zai zo yanzu. Haka yace min ya turo sako.”

“Toh kardai ki jima. Sannan mahaifiyar tasa ta sakko ne ta yadda? Kinga uwata banason abunda zai je ya dawo.”

“Wallahi Innar mu nima banaso. Amman yace wai ta bashi zab’i. Abinda yasa ma har nake kulashin saboda babu tsayayye ne. Kamar sharar fili ne kafin Allah ya kawo wani. Wai kar ace bame zuwa wajen ka..”

“Toh Allah ya kawo muku mazan kwarai.. Masu dimbin albarka.”

“Ameen Innar mu. Ah wai duk yau ina Yayan mu?”

“Kina bandaki ya shigo dazu. Yace zai je kano wajen uban dakin sa. Akwai yan kudaden sa da zai karbo a fara siyan kaya ana ajiyewa. Daman tuni kinsan Yaya Amina tace zata biya kudin nagani inaso. Toh daga nan ma kuma yace zai je gurin wani uban gidan nasa ma ya masa alqawari kafin tahowar sa.”

“Ah Masha Allahu! Yayan mu dai aure nata matsowa. Gwara ayi dai muma mu samu guda d’aya mai auren. Allah yasanya alkhairi..”

“Ameen ya Allah..”

Gyara kai na nayi na yafa wadataccen mayafi akan rigar material dina orange color. Sallama naiwa Innar mu na sauke kasa bakina dauke da addua. A zaure na hango shi sanye cikin shadda kalar toka. Bai sa hula ba ya taje kan sa. Nayi murmushi ina kallon yadda yake bubbudawa.

“Ina wuni..?”

“Alhamdulillah Mine! Meye kike murmushi na miki kyau ne ko? Kada ki damu ni fa mallakin ki ne..”

Wani murmushin nayi, Shi da yasan murmushin me nake da beyi magana ba. Sai kace wani babban mutum yadda yake abubuwa. Ya cika son girma. Tamkar kuwa ya karanci yanayin me nake fada a zucia ta yai wani murmushin mai sauti yana zuba hannuwan sa a aljihun sa,

“Nifa yanzu ba rabin hamsin bane. Na dora talatin fa..”

Ya karasa fada yana kannemin ido d’aya,

“Ah menace Ya Haysam?”

“Ai nasan kina fadan ne a shekarun baya..”

“Banda sharri dai Yaya Haysam.”

“Ba sharri bane, Aminayar ki ce tace na muku yarinta..”

Rufe baki na nayi ina dariya kasa-kasa.

“Ya maganar auren mu?”

Shiru nayi masa ina lankwasa hannaye na. Toh me zance masa fisabilillahi? Ya sake tambayata a karo na biyu,

“Allah ya zaba mana abunda yafi alkhairi Ya Haysam..”

“Ameen. Ni dai gaskia acanzan suna. Ni ba yayan ki bane wallahi, Haka kawai kin fake da wani Yaya kin ki fitowa mu gwangwaje soyayyar mu. Adai canzan suna Mine..”

“Toh Ya H..”

“Gaskia kidena cemin Ya Haysam. Banaso wallahi.”

Ya karasa fada yana marairacewa hade da turo baki gaba alamar shagwaba. Maza na sha’anin su. Na fada a zuci ina kakaro murmushi.

“Bara na fado miki sai ki zabi wanda zaki dinga gayamin. Kinji...?”

“Naji.”

“Yauwa zabi d’aya cikin su, Good-looking, Handsome, Prince Charming, Boo, Casanova, Knight In Shining Armor, Bugs Beau, Lover boy, Sai Honey bun..”

Na gwalalo idanu ina jaddada kai, Sake maimata su yayi yana narkar da muryarsa.

“Mine...Wanne kika dauka?”

“Ai..”

“Babu wani ai wallahi. Nide.. Ni ..Ni de kawai acanza min suna..”

Yana faman bubbuga k’afa kamar dan k’aramin yaro. Wallahi yadda kukasan na sharara masa mari haka nake ji. Na danne bacin rai na ina kallon gefe,

“Boo! Na dau shi..”

“Yauwa Mine.. Nima bara na canza miki wani.”

“A’a Ya Hay.. Au aa ka bashshi Mine din issokay.”

Haka dai muka cigaba da hirar mu. Ina yi ina mantawa ina kiran Ya Haysam din. Dan wallahi bazan wani iya jurar kiran sa da boo ba kamar waata yarinya. Haka dai mukayi fada. Kunsan fadan masoya. Akan naki kiran sa da boo shine yai fushi ya tafi fuu ba ko sallama. Na karkade mayafi na nai sama dama nima cizon sauro ya ishe ni. Nifa gaba d’aya ma na tsani zance wallahi. Azauna aita magana tun ana fad’ar gaskiya har akoma sharo karairaki.


••X••O••X••O••


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[8/24, 5:26 PM] Miss Xoxo: I⃠G⃠I⃠Y⃠A⃠R⃠ Z⃠A⃠T⃠O⃠


*38*


𝓜𝓐𝓓𝓐𝓜𝓔_𝓨𝓔𝓡𝓦𝓐🧕🏼

•••. •••. •••.


Bayan zagayowar sati su Kawu Khamis da Baffa Ardo suka kai kudin nagani inaso na Yayan mu da kawata Fadilah. Nayi murnar da na kasa b’oye ta. Abun mamaki mahaifiyar Fadilah Aunty Nanah tuni ta zubar da makaman yakin ta. Har zuwa gidan mu take yanzu wajen Innar mu suna tattauna yadda za’ai komai. Yayan mu uban gidan sa ya bashi kyautar gidah karami madaidaici amma agarin kano. Dan haka acan zasu zauna. Nima yan kudaden da nake taru na fiddo su na bawa Innar mu taki karba ta dai dauki wani sashe an fara gudanar da harkar biki dasu. Tace na ajiye abuna. Saboda inda rabo nima gidan wani za’a kai ni. Anko kala d’aya na atamfar ghana muka fitar itace ta futar biki ni da Fadilah. Munata shirye-shiryen mu kowanne sashe zukatan mu fal da farin ciki, Domin mu a dakin mu akan Yayan mu za’a fara aurarwa, Fadilah kuwa kaf gidan su akanta za’a fara aurar wa. Lamarin sai sam barka da fatan alkhairi kawai.

Zagayowar satin da zamu koma makaranta kuma aka fiddo da Kawu Ilyasu daga police station. Ya kod’e ya jeme ya zama abun tausayi. Amman abin mamaki daya shigo gidan mu ni yafara harara yana baje hanci. Gaba d’aya kayan sa sun daddare wajen mazaunan ma a bele yake. Sauran yara suka sa daria. Ni kuwa na cigaba da jan ruwan da nake a rijiya. Zama yai akan bokitin sa yana sauke ajiyar zucia kafin ya daga murya yana kwararo ruwan zagi da rantsuwa. Ya kar’kare da,

“Mutanen banza da wofi, Mahassada, Masharranta, Masu ba’kin ciki da bakar zuciya, Annamimai wanda ba komai a zukatan su sai sharri. Masu son ganin baya na. Na hada ku duka na dauke muku albarka.”

Baba usaiba dake tatar koko taja guda ta saki tana matse katon hancin ta,

“A hayye kayya kai! Sannu ilyasu! Yanzu kai a haka har kana da bakin magana? Koma me za’ai sai ayi idanma babbaka gidan za kai sai kayi. Amman fa bayan kaje ka tsaftace jikin ka. Domin banda hamamin wari da tsami wallahi ba abunda yake tashi daga jikin ka. Yo wannan idan masifa ce ke cinka sai ka amayar ka bari kayi gwabi-gwabi dai ko? Dube ka fa tamkar a hure ka ka fadi. Amma sai kwashe mana albarka ka ke. Nikam naci biride nayaga leda wallahi a shirye nake na nanuka gaddi a kasa wallahi. Naci biredi na yage lede ehe, A hayye kayya kai..”

Kawu ila yaja tsaki yana girgiza kai kawai. Bintalo dake karya kashin wuyan tayi murmushi tana sude hannu bayan ta kafa kwalbar lemo a baki, Sai data shanye tas tukun sannan tai jifa da kwalbar ji kake ‘taratsitss’ ta fashe. Kawu ila ya jaddada kai yana k’wafa,

“Hmm! Wai harda ke Bintalo, Aka juyan baya..”

Bintalo tai shewa tana sosa takashi,

“A hayye yau ga gaye ba makilis, Ilyasu! Dan bakin annamimanci irin naka ina kasan da yara a gidan nan yammata zagada zagada amman ka tsallake kai sai batoul zaka hada shi da ita? Ai gashinan ta watsa maka kasa a idanu kuma a banza ka jibgu a folisitehen. Da da ‘yayan mu ka hada shi ai da hankali kwance zaka tatsi kudin ka muma mu dandali namu arzikin...”

“Amman ko kowa zai juyan baya ke be kamata kiyi min haka ba Bintalo..”

Baba Ummita ta sha gaban sa tana watsa hannu a fuskar Bintalo,

“Nace ku auri juna mana ku huta, Ai ba kanku farau ba. Tun ba yanzu ba nake hankalce da ku. Shakuwar dake tsakanin ku ko mu matan sa bamuyi dashi ba. Kin taho fankan fankan kina turo kirji nace ki aure shi mana k..”

Bata karasa ba Kawu ila ya dakatar da ita yana daga mata hannu, Ta dalla masa harara tana maida kallon ta gare shi,

“Kai ma ahake nake da kai bakin munafiki. Kanata nanata ko kowa zai yi maka haka bai kamata ta juya maka baya ba. Matar ka ce? Ko ita ta tsugunna ta haife ka? Ko ‘yar kace ta cikin ka? Ni fa nagaji da bi ta bayan fage. Ku aure juna ku huta kawai. Aikin banza mamalam..”

Baba usaiba tai shewa tana buga zani,

“Kut-sin ubancan kayya kai. Yau ana yinta. A hayye naci biredi na yage leda.”

Bintalo taja tsaki tana buga zanin ta a fuskar Baba Ummita.

“Na auri Ilyasu fa kikace? Allah ya sawake ko maza sun k’are wallahi, Me zanyi da sauran wasu, Nawa yake dashi nawa ya tara? Nafi karfin kaf mazajen ku wallahi, Banda abun ki da inason Ilyasu zan tsaya jin shawarar ki ne? Sanda zan aureshin zama ki sani ne? Sittin ta ubangiji a shirye nake na zugewa mutum tazuge duk girman sa wallahi.. Kina maganar na taho fankan fankan ina turo kirji ko? Toh ai nagodewa Allah inada kirjin turowar ma, Ke kuwa naki a sheme, Sekace silifas. Sittin ta ubangiji bashi da maraba da k’irjin maza. Sad’od’o dake ba gaba ba baya..”

Baba Ummita ta shatalo k’afar Bintalo suka fara dambe. Nai murmushi kawai ina daukar ruwan wanka na. Nayi matattakar karshe Kawu ila ya dokamin kira wai dan ya cusan haushi,

“Zo ki kawo min ruwan nayi wanka, Figalalliyar banza da wofi..”

Juyawa nai na koma kasan na janyo bokiti na juye masa shi,

“Sawu uku zaki min..”

Ya maimata yana dankara min harara, Janyo masa nayi har bokiti hudu ma na zuba masa a babban bokitin su. Na juya na kuma dibar nawa nai hayewa ta sama, Shiru ma ai magana ce ga mai hankali, Ai kuwa ya sandare a zaune da alamun bai tsammaci hakan ba. Ina shiga da’ki Innar mu ta nunamin wayata,

“Sai kira ake tayi wallahi.. Allah yasa dai lapia.”

Ganin me kiran yasa na yamutsa fuska na dire ta akan katifa, Ai kuwa ya sake kira,

“Wai waye yake ta faman kira kina kin dauka? Iyye?”

“Innar mu wata number ce..”

“Toh ba sai ki dauka kiji menene ba? Amman ai babu dadi ana kiran ka kana kin dagawa. Yanzu idan kira ne me muhimmanci fa.? Duba da yadda tun d’axu ake kira.”

15 missed calls. Na dubi yawan kiran ina mai dagawa na kara a kunne na. Ajiyar zuciya ya sauke ina jiyo sautin ta,

“Assalamu Alaikum..”

Na fada ina hararar wayar. Shi kuwa Mubeen dake kishingid’e a cikin motar sa ya kara yin baya da kujerar yana lumshe idanu. Ba kadan ba muryar malamar tasu na tafiya dashi. Kai komai nata ma.

“Waye ne?..”

Ahankali yai murmushi yana sanyata a handsfree hade da dora wayar a kirjin sa,

“Mahhhh! Ya gidah?”

“Alhmldh da..Da wa nake magana?”

“Habba ma bakiyi saving number na ba? Muhammad Mubeen ne.”

“Ohh ya kake?”

“Alhamdulillah Ma! Ya gidah da komi?”

“Lapia lou! Ya.. Ya akai? Wani abun ne?”

“Kina gidah? Anjima?”

“Bana nan..”

Innar mu ta gallara min harara tana karo sautin rediyon ta, Nayi murmushi kawai domin da alamun batasan waye ba. Kilan ta dauka wani saurayin ne. Allah sarki Innar mu. Marairacemin yayi tamkar zaiyi kuka. Na tuno haka Haysam yake min. Ni kam na ha’du da gamo na.

“Shikenan.. Kazo. Amman wait...Me zakai ne?”

“Mah lefi ne dalibi yazo wajen malamar shi?”

Na girgiza kai tamkar yana gani na,

“A’a.”

“Toh sai nazo.. Kinason na taho miki da wani abun?”

“No..”

“Pls anything? Haka dan chocolates”

“No nagode..”

Kit na katse kiran ina jifa da wayar. Dan kuturin munafurci sai kace wani saurayi ne zai zo. Ni ko saurayi bana son kar’bar abun hannun sa

Please Login or Register in order to submit comment