Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Juyawa nayi da nufin karasawa na dakko takalmin da zan sa kawai sai na ganshi a tsaye ya hard'e hannayensa a kirji yana bina da kallo. Murmushi nayi a cikin zuciya ta ba tare da na kuma mai da idona gareshi ba duk kuwa da zuciya ta tana son kuma kallon shi saboda ya yi kyau ba karya. Dukawa nayi ina shirin janyo takalmin kawai naga ya tako har kusa dani ya dago ni yana kare min kallo.

"Proposing u was my desire, having u is my jackpot, loving u is my attitude, pleasing u is my duty, missing u is my habit, kissing u is my wish 2gether 4eva my Fikre."

Yana gama fada ya sumbaci saman lips dina da na gogawa lipstick mai dank'o.

"Kai dai baka gajiya wallahi."

"Akanki ne bana gajiya my Fikre."

"Thank you, mu wuce ko?"

Nayi maganar cikin basarwa dan naga yana wani kifkif da idanuwansa. Murmushi ya yi ganin ina saurin fita daga ɗakin sai ya yi saurin zuwa ya riko min hannu.

"Oya muje mu yiwa Papa sallama naga yana sauri zai je wajan wani taro."

Kai tsaye sashen mahaifinsa muka nufa, ganin yana shirin shigar dani hannun mu saƙale da juna yasa ni tirjewa, ya kada ya raya mu shiga a haka naki sai dai ya yi gaba. Murmushi ya kuma yi tare da cizon lips ya shiga nabi bayan sa bakin mu dauke da sallama.

"Papa zamu wuce."

"To MM yau sai kasar Faransa kenan?"

"Yeah Papa jirgin eight zamu bi gashi yanzu seven thirty karmu makara."

"Toh Allah ya kaimun ku lafiya ya dawo daku lafiya. Fatima sai kin dad'a hakuri da mai gidan naki saboda akwai raki, Allah ya kiyaye muku hanya kun ji?"

"Amin Papa mun gode Allah ya kara girma."

Nayi maganar kai na a duke kafin daga bisani yace mu tashi muje. Ina mikewa Mubeen ya kamo min hannu Papa yana kallan mu ya yi dariya yana kada kai da alama farin ciki ne tsanka a cikin ransa. Muna fito zamu wuce gurin Mammah Ahlaam na fizge hannuna ina turo baki fuskata a haɗe nace.

"Kai ko kunyar su Papa baka ji, a gaban su kake riko mace." Sai da ya matso kusa dani sosai yace.

"Toh wace macen? Ina cewa mata ta ce ba? Karki ja idan muka shiga gurin Mammah na tsotse miki lipstick d'in lips naki Kinga sai ki ji kunyar da hujja."

Nayi masa banza ban tanka ba dan nasan tsab Mubeen zai yi wannan katobarar. A parlour muka tarar dasu Jannat duk sun shirya zasu yi mana rakiya zuwa airport. Na durkusa na gaida Mammah sannan ta yi mana fatan alkairi, har muka fito ta raka mu har parking lot muka shiga mota drive yaja muka tafi. Su jannat sai labarai suke yi daman ba wani bamu lokaci yake yi ba, kullum shi dai na zauna tare dashi kamar kamar wasu mararsa 'yan uwa.

Muna isa airport muka firfito, driver da wasu escorts da his excellency ya bamu suka yo mana rakiya, sune suka fito da trolley d'in kayan mu gabaki d'aya muka rankaya wajan screening. Bayan mun gama komai kasan cewar jirgi ne na gwamnati akawai wasu manyan kusoshe da zamu tafi da su wadanda gwamna ya tura zasu yi wani aiki a can, muka nufi filin jirgin su Jannat suna makale dani.

“Ku ya kamata kuzo ku koma gida, ko bin mu zaku yi ne?”

Dariya duk suka saki ganin yadda yake bude idanuwa.

“Ya MM iyakar mu nan ko da baka yi magana ba, Aunty Bee Allah ya tsare hanya ya dawo daku lafiya Allah yasa daga can ku samo mana b...”

“Jannat ya isa haka sarkin magana.”

Mubeen ya katse ta yana yatsina fuska.

Hannu na yaja muka nufi matakalar jirgin, duk da cewar wannan shine karo na farko da na taba zuwa zan hau jirgi hakan be sanya nayi kauyanci ba, idan kuka ganni sai kuyi zaton daman can na saba shiga. Guri na musamman aka bamu daga ni sai shi, na yatsina fuskata saboda nasan wannan lokacin ma Mubeen ba saurara min zai yi ba.

Zama muka yi ina kusa da shi ya janyo ni jikinsa na kuwa lafe saboda nasan ko ban yarda da yi ba dole ya samu abin da zai sanya mu rungume junan mu. Wayarsa ya janyo ya dinga daukar mu hotuna, lokacin da jirgin zai tashi sama ne luuuu d'in da naji yasa ni makalkale shi ina sake riko shi kamar wacce za'a gudu a bari. Murmushi naji ya yi hakan ne ya ankarar dani kwafsin da nayi, sai na sassauta rikon na gyara zama na.

Drink ya zuba mana ni dai ban wani sha da yawa ba dan bana son naji fitsari, shi kuwa ya dinga kurba ina jikinsa yana rungume dani hannunsa d'aya yana danna waya dayan kuma yana shan lemo. Bacci ne ya dauke ni a jikin nashi, bai motsa ba saboda kada na tashi, ai kuwa har muka kusa isa sannan na bude ido, jikinsa duk ya yi tsami saboda rashin motsi amman bai nuna min ba sai tambaya ta da ya yi me nake so, na kada kai alamar babu komai sannan naga yana faman cije baki. Ganowa nayi ganin baya iya motsi da hannunsa, sai na zare jikina na fara jajja masa yana faman raki.

“Ahh! Wayyo my Fikre da zafi fa! Ahhhh Mammah!”

“Wai menene haka dan Allah, sai abokan Papa sun yi tunanin wani abu ake a nan?”

“And so? Ke ba matata bace”

“Mubeen...!”

“Na'am my Fikre.”

Ganin ni kawai nake jin kunyar ihun nashi yasa na kyale shi dan shi ko a jikinsa. A hankali naji ya dagoni tare da gyara min zama ya janyo ni yana nuna min tagar jirgin. Ya Subahanallahi idanuwa na suka fara dishi-dishi lokacin da suka fara cin karo manya manyan tsaunikan gidaje, tabbas daga kauye muka zo domin Najeriya irin kauyen kyayayau d'in nan ne a kasar France. (Batoul ta saki murmushi tare da kallo na ni Miss xoxo dana dukufa ina ta rubuta labarin, sannan ta maida idanunta kan tawan wato Billyn Abdul wacce ta zabga tagumi tana kallon Mrs Mubeen da take cikin shiga ta kece rai ni, sai Ya Hajja ce da ta saki baki da alama labarin da takeji jin ta take tamkar itace Batoul d'in 😂Sai madam rano dake afkin lodawa cikin ta rice tana lumshe idanu. Kasan cewar su na dauka rakiya muka je government house dakko labarin). Mikewa tsaye tayi tana kallon mu tace.

“Bari a kawo muku abinci sannan kuyi sallah ku huta sai na dawo naci gaba da baku tarihin rayuwata, da abubuwan da suka faru a can kasar Faransa.”

Tana gama magana ta juya ta shige cikin wani ɗaki. Tawan (Billyn Abdul) ta sauke wata katuwar ajiyar zuciya ta kalle ni tace.

“Wai dan Allah matar nan da gaske take ba zata nuna mana koda hoton mijin nata mu gani ba?”

Yaya Hajja ce ta saki dariya tana daukar kwalin lemo ba tare da tace komai ba. Ni ce na ajiye biron tare da rungume littafin da nake daukar story d'in ina lumshe ido nace.

“Tawan barta ta boye abin ta, dan wallahi tunda ta fara bamu labarin nan naji gayen ya min, hmmm idan har na ganshi mukai ido da ido dashi yau ba zan iya bacci ba.”

Suka yi dariya dai dai sannan hadimai suka dinga shigo mana da abinci dana sha dama na kwalam da makulashe, muka baje muka ci daga nan sallah mukai sannan duk muka baje akan carpet sai gata ta shigo cikin wata sabuwar shigar. Gaskiya dole ne ma Mubeen ya dinga mannewa matar nan saboda akwai daukar wanka da kamshi. Zama tayi tare da kallo na tace.

“Kin shirya muci gaba miss xoxolious, madam ceo yerwa. Kinga wannan turaren wutar da na siya a wajanki? Hmmm duk lokacin da na turara kaya na tun daga kofar parlor yake fara zame takalminsa da safa, da ya karaso inda nake...hmmm.”

Nidai nai dariya kawai ban ma so tace hmmm d'in ba naso ta yi min dallah dallah amman matar nan ta gumtse.

“Ai Mrs Mubeen duk turaren yerwa babu mai kauri, wallahi koni ina san su har ma bana son su kare min. Wai kuwa hajjaju kin taba karbar turaran wanka dana wanke pants? Au harda na mopping , wallahi haj...”

“Ya isa Hajja ce kike ko wa? Ina amfani da kayan yerwa gabaki d'ayan su hafsat rano tasani, kuma ko yanzu haka turaran khumran da kika ji a jiki na, miss xoxolious ai na ki ne ko?" Ni dai nayi murmushi kawai nayi na kagu ma taci gaba da bamu labari, aikuwa sai ji nayi tace.

*Paris....The city of love*
(16th arrondissement)

Tun a cikin jirgin na hango symbol d'in Eiffel tower, sai kawai naji bakinsa a cikin kunne na yana cewa.

“Wannan symbol d'in da kike gani na soyayya ne, dan haka na zabar mana d'aya daga cikin hotel din da yake kusa dashi wato Global blue, dan haka ki shirya shayar da babyn ki madarar zallar kauna, idan ba haka ba kuma..”

Ya yi shiru tare da sanya hakoransa ya ciji fatar kunnena.

“Ashhh.!”

Na furta alamun naji zafi kuma babu abinda naji kawai so nake na firgita shi. Ai kuwa ya rude ya janyo ni jikin sa ya shiga hura min wajan yana bani hakuri, ni kuma sai faman rintsa ido nake yi. Fuskata ya juyo tare da kallo na nayi saurin dauke idona akan nasa, bakin sa ya zura cikin nawa ya shiga murza harshensa a ciki, tuni na yafe masa na manta ma da cewar lallashi na fa ake yi, sai da mukaji saukar jirgin a ƙasa sannan ya ciro bakin sa yana kokarin sai mun hada ido naki yadda.

“Kina bani kunya Fikre, wallahi sai ayi abu yanzu-yanzu amman kiyi fuska tamkar ba dake akai ba.”

“To ni kuma me nayi yanzun?”

“Gashi nan kuwa, da kika kama baki na kin saki kikai, please me kika ji da kina kissing d'in?”

“Kaga ni ban san abinda kake nufi ba, ka tashi ka gyara gashi nan ana cewa mu shirya.”

“Uhmm ke dai akwai maziya.”

Na tabe baki ba tare da nace masa komai ba, can kuma shima ya fara gyara nutsuwarsa ya riko hannuna kamar wanda aka ce masa zan gudu. Bayan jirgin ya gama tsayawa akai announcing cewar passengers zasu fito. Hannuna cikin nashi haka muka fito daga cikin vvip suite d'in da aka ware mana a jirgin, ana gama sauke mana talattakalar muka sauka daya sauke kafarsa d'aya zan dora tawa a haka muka diro.

“The city of love.”

Na fada a hankali lokacin da idanuna suka shiga karakaina akan mutanen dake shawagi a wajan, duk mutanan indai mace da namiji ne to tabbas rungume zaka gansu da juna, baka taba gane yaya da kanwa ko saurayi da budurwa bare kuma ace maka mata da miji saboda yadda ake makalewa da juna.

“Me kika ce my Fikre?”

Mubeen ya tambaye ni ashe a fili nayi maganar, amman sai na yi fuska nace.

“Ba magana nayi ba.”

“Okay tsaya a nan bari naje muyi sallama da MD sai nazo muje masaukin mu ko?”

Kai kawai na daga masa sannan ya sakar min hannu ya tafi yana waiwaye na, ni kam sai kalle-kalle nake ina kuma karewa Eiffel tower kallo ganin yadda gadar take da tsawo sosai ga mutane nan sai daukar hotuna suke abin sai wanda ya gani.

Babu jimawa sai gashi ya dawo ya riko ni daya hannun kuma trolley d'in kayan mune yana janta, ga mamaki na ina jiran mu tari taxi sai naga mun isa wajan ruwa yaje yana magana da wani mai jirgin ruwa (yacht) irin me fukafukan nan. Naga mai jirgin ya gyada kai tare da tayarwa, Mubeen ya kamo hannuna, da sauri na cuke a wajan ina zaro ido.

“Ina zamu?” Na tambaya a razane.

“Hotel mana ko anan zamu zauna?”

“Amman a jirgin ruwa?”

“Yes menene? Kinga hotel d'in can fa gashi can a tsakiya babu abinda zai faru dake my Fikre insha Allahu, karfa ki manta daga sama kika sakko meye na tsoran ruwa?”

Ganin duk na tsorata yasa shi janyo ni jikinsa tare da sanya tafin hannunsa ya rufe min ido, bakin sa a saitin kunne na yake fadin.

“Karki ji tsoro ki dauka cewa daki zaki shiga. Yauwa baby na nasan zaki iya jaruma ta, kinsan akan ce, Behind every successful man is a woman–whoever said this is 100 percent right. You're the secret behind my success, my dear wife. I love you...”

Kunsan Allah tsabar jin dad'ad'an kalamansa yasa ban san mun shiga cikin jirgin ba sai kawai gani nayi ya bude min ido muna cikin jirgin ruwan d'are-da’re. Ai kuwa ana fara tafiya nayi saurin fadawa jikinsa tare da kankame shi, ko minti goma bamuyi ba sai gamu a bakin hotel d'in.

Muka sauka mai jirgin ya fito da trolley d'in kayan mu ya ajiye mana bayan mun fito daga ciki muka nufi cikin hotel d'in kai tsaye. Lift muka shiga yana ta faman kallo na wanda na rasa kona menene har muka karasa cikin dakin da zamu zauna.

“Wai banga ka tsaya a reception ka karbi daki ba ya haka?”

“Yeah komai ta online akai aka gama shi yasa kika ga ina zuwa mun taho dakin mu.”

“Uhmm ya yi kyau hakan ma ana ta ci gaba a duniya..”

Bayan mun shiga mun zauna ya kwanta a jikina kamar wani wanda ya yi tafiyar kafa sai faman mika yake yi.

“Mu fara yin wanka ko?”

“Eh amman ka fara yi kafin sannan na gama shirya mana kayan mu..”

Yayi dariya yana kallon fuska ta yasan cewar wayo nake son yi masa, har lokacin na kasa sabawa dashi ina jin nauyin yin wasu abubuwan a gabanshi. Ya tashi ya bude bathroom d'in da kanshi ya hada ruwan wankan sannan ya dawo inda nake fito da kayan mu ina ware nashi ina sakawa a wardrobe. Jan hannuna kawai ya yi muka shiga tare babu yadda na iya dole muka yi tare muka fito lokacin har an kawo mana abinci an zuro mana shi ta cikin wani guri mai kama da window.

“Zo mu fara cin abinci sannan sai mu shirya.” Na daga kafada alamar ban yadda ba ina cewa.

“Wai kai yanzu acici ka zama ne?”

Ya janyo ni muka je muka dakko abincin ya dire a kan wani table dake ajiye a bakin gado ya zaunar dani kusa dashi yana cewa.

“Nima na gani wallahi my Fikre, but kin san menene sirrin?” Na girgiza kai alamar a'a.

“Saboda ke kike bani shi yasa.”

“Yayi kyau acici bismillahi to.”

Nayi maganar ina saka cokali a cikin abincin wanda sam beyi min ba, hasalima amai naji yana niyar taso min. Da kyar na samu na bashi yaci, yana ta cewa naci amman nace so nake sai ya gama sai naci nawa. Bayan na gama bashi sai na tashi zan bar gurin yasa hannu ya janyo ni na koma jikin sa. Kallo na yayi saboda towel d'in jikina da ya dan zame kasa nayi saurin taro shi, sai ya yi tamkar be ganni ba yace.

“Ina kuma zaki je?”

“Zan sa kaya ne wallahi banjin dadin zama a haka.”

“Zo ki fara cin abinci tukunna.”

Naji tamkar ma yasa min shi a baki na nayi saurin kawar da kai na ina kada kai.

“Na koshi wallahi” Ya zaro idanunsa.

“Mekika ci.?”

“Na dai koshi ba zan iya ci ba.”

“Ba zai yiwu ba Fikre ko kalar abin cin ne beyi miki ba?”

Kafin na bashi amsa ya kuma magana.

“A kawo miki shawarma ko pizza or kina da abinda kike so a ranki.?”

Na dinga girgiza kai dan bana bukatar komai, ya kuma jana jikinsa bayan ya gyara zamansa, ya dakko ya fara bani abincin cikin lallashi, ganin ya dage yasa na fara ci ina yatsina fuska. Bai fi spoon uku ba da nayi wani yunkurin amai ya taso min, kafin na kwaci jikina tuni na fara yi na kwaraye tray d'in abincin da amai.

“Meke damunki ne? Me kike ji?”

“Zuciya ta ke tashi, ban san wannan kamshin abincin.”

“Okay.. Okay bari na dauke miki shi sorry please.”

Yana magana yana tayar dani, muka shiga bathroom ya hada ruwa ya wanke mu tas sannan ya nado mu a towel guda d'aya saboda na bata na jikina dana shi da amai. Sai da ya fara ciro min riga nasa ya kwantar dani akan sofa tare da lullube ni da blanket sannan yace ya gyara wajan tas sannan ya dawo kusa dani ya zauna. A ranar dai ya shiga damuwa saboda yanayin da na shiga. Babu inda ya fita a haka muka kwana tare dashi a jikina kamar wani yaron goye.

Sai da na dauki kusan kwanaki uku bana jin dadi har yana tunanin ko dan ban saba da yanayin kasar bane. Sai a kwanaki na hudu ne naji na koma dai dai sannan shi ma yakan fita ya dan siyasa mana wasu abubuwan bukatar a cewar shi idan na warke zamu fita yin abin da ya kawo mu kasar wato shakatawa..

****
A hankali nake jiyo tafiyar harshen sa acikin kunne na. Sake kudundinewa nai ina jan bargo kai na domin baccin be sake ni ba.

“Bacci nake ji...”

Na bashi amsa ina matsar da hannun sa daga kan baya na. Shigewa yai cikin bargon ya janyo ta jikin sa sosai tamkar za’a kwace masa ita,

“Baccin ki yayi yawa yanzu fateemah! Ko dai baki da lapia ne?.”

Bacci na nacigaba da yi harda munshari, A hankali Mubeen ya cigaba da shafa sumar kanta yana sumbatar saman goshin ta. Sai da tai bacci ishasshe kafin ta farka dakyar tana adduar tashi daga bacci.

Mikewa nai na janye hannayen Mubeen daga kai na, Ban’daki na shige na yo wanka hade da alwala. Ina fitowa naga ya mike daga kan gadon sanye cikin kananun kaya har ya tashi tun d’axu kome?

“Ina kwana..?”

Agogo Mubeen ya duba yana murmushi, kusa da ita ya matsa yana kamo kafadunta yana hura mata iska a idanu, a hankali ya rankwafo da fuskar sa dai dai fuskar ta yana bin idanun ta da kallo,

“Kwana fa kika ce Fikre? Sha biyu da kwata yanzu..”

“Dan Allah?”

“Allah kuwa! Tun d’axu na shirya nake ta tashin ki kika ki.. Daman inaso muje wani wuri ne. Bara nayo wanka.”

“Baka yi ba?”

“Ai kin warware shi tas.”

Ya karasa fada yana kanne idanu. Na cuno baki gaba ina tsane kai na da tawul,

“Ni da nake bacci? Wlh babu ruwana..”

“Dande bakisan me nayi miki bane da kina baccin..”

Na shiga dudduba jiki na ina ware idanu, Na bude baki kenan zanyi magana Mubeen yai daria,

“Wasa fa nake! Kawai wanka zanyi da ruwan zafi. An fara snow..”

Gyada kai nayi ina maimata ‘snow’ din daya fada. Nide inde ba a film ba ko a kalmance bantaba ganin ta a Zahiri fa sai yau. Ta balcony na leka. Sharr sai zuba kankarar take yi gwanin sha’awa. Lalle Allah gwanin hikima ne! Shigar wata baturiya na kalla tamin kyau. Daki na koma na ciro riga da wando nima da jacket. Harda sabon booth da Mubeen ya siyo mana jia a blue water mall. Kafin ya fito tuni na gama shiryawa cikin kayan. Na yane kai na da mayafi. Yana fitowa ya tsaya yana bina da kallo kamar wacce ya fara sani a lokacin,

“Ina zaki a haka?”

“Ba kace fita zamu yi ba..?”

Yamutsa fuska yai yana shafa kwantaccen gemun sa.

“Anga zamu fita dinnan kuwa.”

Kasa amsa masa nayi. Haka kawai na tsinci kai na da binsa da kallo. Dogo ne sosai, Yanayin mazantakar kirar jikin sa ta dace dashi, Bashida kiba, Amma ba za’a sashi a jerin masu rama ba. Six packs dinsa sun dace da faffadan kirjin sa TubarkAllah! Yana da kanannadden gashin kai baki wuluk dashi a kwance. kallo d’aya zaka masa kasan ruwa biyu ne shi. Fuskar sa doguwa ce mai dauke da siririn hanci tamkar shiya zana kayan sa. Idanuwan sa dara dara ne mai dauke da kwayar ciki coffee brown! Ga gashin ido dana gira daya kusa hadewa. Labban sa jajaye ne kamar wanda ya shafa Jambaki. Ga sajen daya zagaye fuskar sa ya sake kayata shi. Hakoran sa farare tas a jere suke dauke da hushirya a tsakiya. Ga side dimples dake lobawa a gefen kumatun sa. Cikin shagalar dana tafi a kallon sa na jiyo takun tafiyar sa ya tsaya a gaba na. Ba zato ya sakar min kiss a gefen kumatu na,

“Day dreaming?!!”

“Kind of. Ina tunanin su Innar mu.”

Kada kai yayi yana murmushi, Ya janyo hannu na muka koma bakin gado. Sanye yake cikin wasu kananun kaya samfarin Italy yayi kyau ba karya. Nail cutter naga ya dakko a gefen gado yana mikomin hannu,

“Mu yanke farcen mu ko?”

Na kalli farce na tas dashi ko dan yaji jia ina zan rage? Girgiza kai nayi ina murmushi,

“Aa zanyi da kai na..”

“No! Ai nagaya miki wanke kai, kafa da cire nails duk zan dinga yi miki..”

“Ai kakka zaftare min farata na ni dai..”

“Worry not sweethrt!”

‘Sweetheart?’ Na maimata a zuci ina lumshe idanu. Ba musu na mika masa hannu na ya shiga cirewa a hankali cikin nutsuwa.

“Nagode Mubeen..”

“Anytime my love.. I love you soo much Fateemah na. Ki adding nails dnki acikin abubuwan da nake so a tattare dake. Ina sonki da yawa fateemah na!.”

“Nagode Mubeen!”

“Nifa gaskia sai kindena cemin wani Mubeen. Haba! Babu kyau fadar sunan miji gatsal..”

Murmushi kawai nayi ni dai namike ina gyara mayafi na. Kafadata ya kamo cikin tasa muka sauka ta lift. Wannan karon ma yacht muka hau muka karasa wani tower da ake kira da,

‘Eiffel tower’
(Symbol of love)

“My love welcome to Paris the city of love.. Ga Eiffel Tower symbol of love! Ga mu masoya! Duk wanda kika gani awajen nan masoya ne. Fikre dan Allah ki karbi soyayyah ta! Yaushe zuciar ki zata amince dani a matsayin masoyi! Uhm?..”

Gaba d’aya na shagala da kallon tower din! Banda a movies ko a bayan littafin A’b’c’d bantab’a sheda ta ba sai yau. Idanuwa na na sake mitssikewa ko mafarki nake? Masoya sai wargajamin su suke. Mubeen ya sake janyo ni jikin sa yana nunnuna min ko’ina. Wurin cin abinci muka je agefen wajen muka ci, Sannan muka futo! Photographer Mubeen ya kirawo ya shiga daukar mu a hotuna, Sai matse ni yake a jikin sa mai hoton na bamu styles din yadda zamuyi.

“Ki saki jikin ki.. Nan fa Paris ne! Kowa harkar sa yake Fikre! Basu papa a kusa.”

Yana min maganar mai hotan na dauka a haka, Sai muka bada wani style lokacin yana magana na daga kai na kalle shi. Gurin wani mai sai da kwado (padlocks) yaje ya siyo mana guda biyu, yafuto ni da hannu yayi, Na karasa kusa dashi. Ya mikomin yana nunamin yadda zanyi,

“Yauwa ki zana zanen zuciya anan sai kisa sunana da naki daga kasa ki rubuta forever ko dai wani abun..”

“Saboda me?”

“Saboda haka akeyi anan! Tradition ne. Idan mun gama sai mu sakale su anan, mu jefa keys din acikin seine din”

Banason yi Amman gudun kar na gwale shi yaji ba dadi yasa na karba kwadon na shiga zana karamar zuciya na rubuta sunayen mu ni dashi aciki,

_Mubeen & Batoul..( Forever)❤️_

Murmushi yai lokacin daya karanta, Ya gyara zama sosai yana tsantsara nasa,

_Fateemah na (Batoul) & Muhammad Mubeen 2019! Paris #Eternal love! Two hearts, locked in love. Love is all we need. Happiness is not perfect, until it is shared. You make my heart happy Fateemah.. Love you eternally💚💚_


Murmushi nai lokacin dana karanta abinda ya rubuta,

“Ina keys din naki...?”

Nuna masa nayi, Ya Kada kai hade da jan hannu na muka koma koma inda ake jefa keys din a seine! Nan muka wuwwula muda sauran masoya da suka zazzo wajen. Mubeen ya rungume ni yana murmushi,

“Fateemah na! Wannan tradition ne na Paris daya samo asali a 20th centuries, Saboda Paris birnin masoya ne. Haka ma Eiffel Tower dinnan wurin zuwan masoya ne.Abunda mu kayi yanzu shi yan faransa suke cewa Padlock marked with the railings and throwing the keys in to the river seine . Wai shine Locking thier love forever in the Most romantic city of the world... Abun ya burge ki???”

D’aga kai nayi a hankali ina kokarin zare jiki na daga nasa,

“Ssssh! je t'aime tellement Fateemah na!”

“Na’am?”

Murmushi Mubeen yayi wanda kyakkyawar hushiryar sa ta bayyana,

“Nace I love you soo much! Wai Yaushe xakice kina sona uhm?”

Shiru nayi ina bin mutanen wajen da kallo. Mubeen ya gyara hular kansa yana sake kamo hannun ta cikin nasa,

“Bara na kuma nuna miki yadda dayan tradition

Please Login or Register in order to submit comment