Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din yake. Matsawa na cigaba dayi muka kai har karshen karshen karfen tower din,

“Kin kalla titanic??”

Na daga kai na ahnkali ina hadiye wani yawu. Yai murmushi yana yamutsa fuska,

“Toh haka zaki yi..”

Hannuwan sa yasa ya d’aga nata sama, Shima ahankali cikin tafiyar tsutsa daga cikin ta zuwa can saman kirjin ta ya daga nasa saman. Su kai tamkar fuka-fukai,

“Ki saki jikin ki kiji iskar masoya mai kad’awa Fateemah na! Kina ji?”

Ya fada a kunne na yana cizan sa hankali..Juyowa yai dani ya bani wata kyakkyawar runguma, Daga nan ya hade bakin mu waje d’aya yana gaya min wasu kalamai,

“A yayin bayyana miki adadin yadda nake jin son ki a zuciyata Fateemah na! zan iya yin amfani da kalmomi irin su…….hmm ko dan ina ganin cewa babu wata kalma da za ta iya wakiltar matsayinki a gare ni. Sai dai a yau a kuma yanzu ina mai ƙara sanar da ke cewa, ina son ki Fateemah na.. you’ve slipped under my skin, invaded my blood and seized my heart...”

Kokarin kwace kai na nake Mubeen ya sakamin karfi ta hanyar hade hannuwa na biyu ta bayan karfen. Dayan hannun sa kuma ya shjga gyaramin gashin kai na daya zubo gefe. Wasu Shegun kisses ya shiga bata a ko’ina wanda yasa Batoul hawaye. Abun mamaki sai ga Mubeen yasa harshen sa yana lashe hawayen cikin wata irin siga ta soyayyah,

“I love you babe, and every time I see you I just want to hold you in my arms and never let go because you’re the girl that fills all the little dark places in my heart, Fateemah na! Darasin mu na yanzu zamu yi shine akan french kiss’ dama gamu a french country ko? Wato Paris! Ga kuma Eiffel Tower!...”

Kafin nayi magana ya rankwafo dani yana kallon fuska ta. Wata irin sumba ya shiga yi min wanda duk ilahirin jiki na sai da ya amsa sakon sa cikin girmamawa.

“I am addicted to your love! I am crazy about you Fateemah na! Komai nake is just! Ya salam! Fateemah na! I get lost in ecstasy when you make love to me. Allah ya biya miki bukatun ki na alkhairi.”

‘Gaba d’aya na rai na ajina, Tunani na, Shekaru na kai dama karatu na. Gaba d’aya muhammad Mubeen ya gama birkitamin lissafi. Wallahi tamkar a film haka nake ji. Danshin hawayen sa ne ya shiga diga a fuska ta, Ko na meye oho!

“I will travel a thousand miles to be with you. If I could I would make love to you a thousand times..”

“Dan Allah ka sakarmin baki na! Wallahi ciwo yake! Baka ji baya na ba...”




_Could this actually turned into something real? Shin ya zata kaya ne da zukatan masoya biyu wanda suke da banbance-banbance a tsakanin su? The class of the have and the have not??? Suraidah 'yar gidan wani babban oil tycoon ce. Muhammad Mahboub kuma d'an gidan talakawan talak ne. Shin ya zata kaya ne da qulluwar zuciyoyin wanda ba tsaran rayuwa bane ballanatana aure😮? Tab Shin ya kuke ganin wannan ruguntsumin zai kaya? Dr Falal Rabiu mai Mai wani sanannen billionaire ne wanda keda rijiyoyin mai a fad'in Najeriya, yana taimakon talakawa amma shi kam baya son talaka ya rab’e shi. Taya za’ai Muhammad Mahboub ya zamto siriki agare shi? Kai abin da kamar wuya. Mahboub *ANNURIN ZUCIYAR* Suraidah ne. Da sonshi ta rayu ya rene ta ya girmama a zuciar ta. Shin ko Suraidah zata iya bijerewa mahaifin nata? Tab! dankari Makari. Akwai cakwakiya fa, kun ta6a ganin talaka mai tsattsauran ra'ayi? Ku biyoni muje dan kuji me za'a kulla a tafiyar. Wannan labarin yasha banban da sauran rabarai na, zai ta6a zuciyoyin masu karatu, sannan zai fad'akar daku masu karatu, insha Allahu zai sanyaku nishad'i. Akwai zazzafar soyayya da kuma zazzafar kiyayya, akwai jarumtaka, sadaukarwa ta fannoni da dama, *ANNURIN ZUCIYA* daban yake a cikin sauran labarai. Domin mallakar ANNURIN ZUCIYA na marubuciyar MUSAYAR ZUCIYA (HAJJAH CE) ku tuntubi lamba kamar haka akan nera dari biyu kacal: +234 706 528 3730_[9/15, 10:34 PM] Miss Xoxo: _Could this actually turned into something real? Shin ya zata kaya ne da zukatan masoya biyu wanda suke da banbance-banbance a tsakanin su? The class of the have and the have not??? Suraidah 'yar gidan wani babban oil tycoon ce. Muhammad Mahboub kuma d'an gidan talakawan talak ne. Shin ya zata kaya ne da qulluwar zuciyoyin wanda ba tsaran rayuwa bane ballanatana aure😮? Tab Shin ya kuke ganin wannan ruguntsumin zai kaya? Dr Falal Rabiu mai Mai wani sanannen billionaire ne wanda keda rijiyoyin mai a fad'in Najeriya, yana taimakon talakawa amma shi kam baya son talaka ya rab’e shi. Taya za’ai Muhammad Mahboub ya zamto siriki agare shi? Kai abin da kamar wuya. Mahboub *ANNURIN ZUCIYAR* Suraidah ne. Da sonshi ta rayu ya rene ta ya girmama a zuciar ta. Shin ko Suraidah zata iya bijerewa mahaifin nata? Tab! dankari Makari. Akwai cakwakiya fa, kun ta6a ganin talaka mai tsattsauran ra'ayi? Ku biyoni muje dan kuji me za'a kulla a tafiyar. Wannan labarin yasha banban da sauran rabarai na, zai ta6a zuciyoyin masu karatu, sannan zai fad'akar daku masu karatu, insha Allahu zai sanyaku nishad'i. Akwai zazzafar soyayya da kuma zazzafar kiyayya, akwai jarumtaka, sadaukarwa ta fannoni da dama, *ANNURIN ZUCIYA* daban yake a cikin sauran labarai. Domin mallakar ANNURIN ZUCIYA na marubuciyar MUSAYAR ZUCIYA (HAJJAH CE) ku tuntubi lamba kamar haka akan nera dari biyu kacal: +234 706 528 3730_


_*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER_

_07067124863_

*_Ko kuma*_

_09032345899_


_*IGIYAR ZATO.......💖_*


_Wattpad: missxoxo00_


_Gaba d’aya shafin nan sadaukarwa ne agare ku: TAWAN🥰❤️ (Billyn Abdul) Kina ran nana hansatu akoda yaushe.. Tare da Hansatu Rano (Opay)Madame fried rice 😂💖❤️_


_54_


Kallo na ya yi tamkar zai min kuka, cikin ransa tunani yake yi me yasa bana yi masa kwatankwacin son da yake min? Me yasa yake jin soyayya ta a ranshi tamkar ya mutu? Ya fara tunanin anya ba wani babban laifi ya aikatawa ubangiji ba har yake hukuntasa ta wannan hanyar? Sai kawai ya sakar min hannu da jiki ma gabaki d'aya, hakan da naga ya yi ne yasa jikina yin sanyi, meye laifin me sonka mai share maka duk wani kuka naka? Ya juyo ya kalleni muka hada ido bawan Allah ya sakar min murmushi tare da cewa.

“Mu wuce ko?”

Kallansa kawai nake sai kuma daga baya nabi bayan sa muna tafiya yana dan gogar kafada ta, nasan so yake ya rungume ni amman gudun bacin raina yasa ya jure. Sai da ya fara kai mu muka yo siyaya sannan muka koma masaukin mu. Kayan jikina na rage shi kuma ya kunna mana room heater cikin sauri na haye kan gado bayan na dauki chocolate d'aya na rufe duk ilahirin jikina da blanket saboda sanyin ruwa da naje na kwaso. Jiyo shi nayi shima ya shigo blanket d'in a raina nace 'bashi da zuciya' amman a zahiri sai cewa nayi.

“Waye haka?”

“Kina da wani bayan ni ne?”

Banza nayi masa ya shigo ya rungume ni, na lumshe ido tare da gutsirar chocolate d'ina ina lumshe ido. Lalube ya fara yi a jiki na nayi masa banza dan naga shi sam baya gajiya da hakan, yasa harshensa a wuya na yana lasa, ai kuwa na goga masa chocolate d'in a gurin da yake sid'ar, yana kai harshensa yaja tsaki sai kawai naji ya wuntsuloni jikin sa gaba d'aya ya hau sumbatata ta ko'ina.

“Please Mub.....”

Ya yi saurin rufe min bakin da nashi, murya na rawa jikin sa na Kyarma yake min magana.

“My Fikre ina son ki gaya min abinda kike bukata nayi miki shi a doran duniyar nan, ki gaya min ko menene I promise you zan miki shi saboda farin cikin ki. Sanar dani abinda kike so zan aiwatar da shi da ikon Allah indai abin baifi karfina ba.”

Nayi shiru ina sauraransa, hakika ina da burika da yawa, sai dai su ina son na cimmusu ne a hankali, amman yanzu zan iya bashi guda biyu tunda ya tambaye ni.

“Dan Allah ki tambaye ni karki ki, ko menene zan miki shi.”

Na gyara kwanciyar da ya yi min a jikinsa nace.

“Bani da abinda nake nema a gurin ka domin baka rage ni ba ta ko'ina.”

“No please ko ba a kanki ba dan Allah ki tambaye ni my Fikre.”

Ganin ya dage da son sai ya faranta min yasa ni sauke ajiyar zuciya, murya ta a sanyaye nace dashi.

“To na gode Mubeen, bani da bakin yi maka godiya saboda kayi min komai. Alfarma guda biyu nake rokan ka da kai min, sannan kamar yadda ya zama alfarma ina son idan na gaya maka ko menene karka yi min mummunan *ZATO*, kayi min kyakkyawar fahimta.”

Sai ya da dakatar dani da kwanakwanar da nake yi yace.

“Sanar dani kawai zan fahimce ki my Fikre.”

Wannan karon da kai na na kuma narkewa a kirjinsa sannan nace.

“Ina son kabi hanyar Papa ka samawa Haysam aiki, ya kammala karatunsa amman aiki ya gagare shi, Mubeen Haysam ya yi min abinda ba zan iya mantawa dashi ba, shine ya tsamoni daga fadawa gurbatacciyar rayuwa. Kuma kasan ance Zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri. Lokacin da na kammala secondary school Ina zaune babu abin yi sai bi gida-gida neman aikin yi mu samu na abinci, Allah ya kawo min Haysam ya biya min kudin tafiya jami'a n....”

“Sshh ya isa, na fahimceki na gane irin d'in bin alkairin da yayi miki a rayuwarki. Oya wace ko waye ko su waye next.?”

Cike da jin dadi ban san lokacin da nake shafar kirjinsa ba nace.

“Sai d'an gidan kawu na kawu khamis sunansa Yusha'u, shima yana nan yana gararanba a gari dan Allah ko shi ka taimakawa ya samu aiki nasan zai taimaki 'yan uwa mu, wadannan sune kawai abinda zaka taimaka min akan su.”

“Amman my Fikre ban ji kin fadi Yayan mu Najib da kanwar mu Auta ba why?”

Yadda yake sake manna ni a jikin shi ne yasa na kuma narkewa, samun kaina nayi da sanya hannu ina yamustsa gashin kansa kafin na girgiza kai nace.

“Babu komai, gani nayi suna da kai kaga ai basu da matsala.”

Sai kawai naji ya wulkitani na koma kan gadon shi kuma ya dawo sama na, wasu lafiyayyun sumbata ya dinga sakar min wad'anda suka sake warware notikan dake jiki na. Gabaki d'aya ya rude sai sambatu yake yi yana kuma matseni a jikin shi, baki na rawa yace dani.

“Nayi miki alkawarin cika miki duk wani buri naki, zan sanya ki farin ciki a cikin duniyar da Allah ya ara mana. Yanzu ya za ai na samu details d’insu?”

Tabbas na yadda Mubeen yana so na, na kuma tabbatarwa da zuciya ta kaunar da yake min ta zarce baki ko alkalami su rubuta, daga gaya masa muradi na har ya fara shirin aiwatar min dasu? Shin wane irin so na Allah ya dora masa? Tausayinsa ya kama ni karo na farko a zaman mu da naji zuciya ta ta amince da karbar soyayyarsa, na amince da ya zama cikakken miji a gare ni sai dai naki na nuna masa game da yadda nake jinsa, sai lumshe ido nake yi kafin nace dashi.

“Mahaifin Haysam yana karkashin Papa, Nasan idan ka sanarwa papa sunan zai gane.”

“Uhmm, wane sunan kenan?”

“Sunan shi Alhaji Kabeer Wafa, dan canji ne domin lokacin da aka je nemar maka aure na harda shi a ciki.”

“Wow gaskiya kinsa naji kwarin gwiwar yi wa Papa maganar, bari gobe insha Allahu zan masa text zan kuma yi masa waya sannan zan yiwa SSG d'in sa yadda abin zai fi saurin yi.”

Cikin sassanyar murya nace masa.

“Na gode Mubeen, Allah ya saka da alkairi ya kare ka da iyayen ka a duk inda kuke.”

Fuskata ya dago tare da kallo na ta cikin light green d'in hasken daya haskaka dakin sannan yace.

“Friends dina suna kira na Mubeen, kawayen Mammah Mubeen, abokan Papa Mubeen su Jannat ya MM but ke matata kema kice min Mubeen why?”

“Sorry uhmm.. Uhmm.. Uhmm.”

“Ina jinki uhmm! what?”

“Mr. Right.”

“No bana son shi ki sake min.”

“To ai kaji ka, fadi wanda kake so sai na dinga kiran ka”

“No no ke zaki zabo da bakin ki.”

“OK tom Wonder boy.”

Na fada cike da shagwaba wacce sam ban san ma ina da ita ba. Dariya naji ya saki yana sake matsi ni cikin jikin shi, na hade rai sai ji nayi yace.

“Wato ni ne wonder ko? Gaskiya ki canza bana son wannan ma.”

“Oh my God Mub....”

“Shhhh karki karasa ki kwashi zunubi, oya samin wani sunan irin romantic nick name d'in nan.”

Sai da na turo baki sannan cikin sauri na fara fadowa.

"Loverboy.. Stud muffin, my king, my heart, bae, Butternuttt, heart beat, ki..."

Ban karasa ba ya zura bakin sa cikin nawa ya kama sarrafa shi yadda yaga dama, cikin rad'a-rad'a yake cewa.

“Stud muffin or heart beat is enough, fadi naji.”

Na kuma turo bakin tare da cewa.

“Stud muffin 🥰shi kenan ko kaji dadi.?”

“Yeaaaaa zo kiji ma irin godiyar da zanyi.”

Yana kaiwa nan ya rufe mu sai wasan ya canza muka tafi wajan neman lada ta ko wace siga, sannu a hankali soyayya da kaunar Mubeen suka fara karyar da zuciya ta, ni kai na idan ya fita siyo mana wani abun wanda ba sai munje tare ba kafin ya dawo duk na kosa, sai naga tamkar ba zai dawo gare ni ba..

*HAYSAM*

Tunda ya tafi garin Abuja gidan uncle Idris yake ta faman rashin lafiya, gabaki d'aya ya rame ya yi baki, abubuwa uku ne suka taru a zuciyar shi suke kuma neman zame mishi matsala a rayuwarsa wato, rashin abar kaunarsa ga rabuwar auran mahaifiyarsa da mahaifinsa sannan rashin samun tsayayyen aikin yi. Haysam ya yi kuka kamar zai karar da ruwan idanunsa, gashi ya kasa mantawa da komai saboda ya dade tare dasu a cikin rayuwarshi. Uncle Idris yana kula dashi sosai yana kuma kwantar masa da hankali, tare da yi masa alkawari cewar mahaifiyarshi zata dawo gidan mijin ta yasan cewar ran Abban nashi ne ya bace har yasa hakan ta faru ba tare da ya yi nazari ko ya nemi shawara ba.

Gyara kwanciya ya yi tare da bude idanuwansa wadanda suke a rufe. Kofa yaji yan bude an shigo, ya kalli mai shigowar ganin uncle d'in nashi yasa shi tashi ya zauna yana faman sunkuyar da kansa tamkar wanda yake gaban suruki. Kafadunsa uncle Idris ya dafa yana kallonsa yace.

“Haysam kunyi waya da Abbanku yau?”

“A'a uncle na dai kira shi dazu wayar a kashe, to kuma ban sake gwada kiran ba.”

“To daman magana muka yi akan aikin da za'a samar maka. Wane iri kake son yi.”

Haysam ya yi shiru yana tunani, shi kam ga abinda ya karanta me yasa ba za'a nemar mishi aiki akai ba? Koda yake kullum addu'a yake yi Allah ya bashi abin yi mai albarka, dan haka komai ya gani shine mafi alkairi a wajan sa.

“Uncle duk wanda na samu zanyi, ni dai fatana kawai na samu aikin da zanyi.”

“To shi kenan Haysam mun yi magana dashi Abban naku yace idan har zaka iya irin aikinsa na canji to ga hanya ya samar maka daga gurin surukar mai girma gwamna, wannan matar dan sa da aka yi biki kwanaki, zaka dinga akin amman a can kasar saudiyya a garin jidda can za'ai maka komai ka koma idan da hali ma sai kayi aure ka tafi da matarka.”

Haysam yaji dadin samun aiki musamman ma da yaji cewar Batoul ce ta yi masa hanya ya samu, gashi a can kasa mai tsarki ne, sai dai maganar auren da aka yi masa shi a yanzu kam bashi da wacce zuciyar sa take so, kai gaba daya ma shi bashi da wacce zai iya kawowa yace a aura masa ita. Muryarsa a raunane yake magana yana faman kifta idanuwa.

“Uncle ba ni da wacce zan iya cewa ina so a yanzu, sai dai kayi min alfarma uncle ka samo min wata zan aure ta zan kuma zauna da ita.”

Uncle Idris ya yi shiru yana kallon Haysam cike da tausayinsa, hannunsa ya rike cikin nashi yace.

“Ka kara hakuri Haysam nasan abinda kake ji a cikin zuciyar ka, sannan zaka zabo matarka da kankin kanka kaji ko?”

“Toh uncle babu damu zanyi yadda kace d'in na gode Allah ya kara girma.”

Daga haka uncle Idris ya mike ya fita, shi kuma Haysam yaci gaba da yan tunane tunanensa yana shiwa Batoul albarka.

Cikin yan kwanaki kuwa aka gama shirya masa komai shi kuma a wannan lokacin yaje zaria ya tambayo auran yar aminiyar Ummansa saboda yana son ko babu komai ya faranta wa umman nasa duk da cewar baya jin soyayyar yarinyar. Haka kuwa aika yi Abbansa bai tauye masa ba wajan hanashi auran yarinyar dan yasan tuncan ita Haj Husnah ke son ya aura.

Haj Husnah kuwa duk da tana can gidan su da Haysam yaje ya sanar da ita wacce zai aura yasha albarka da fatan alkairi sannan ya yi mata alkawarin zai san yadda za a yi ta koma gidan Abbansa. Tayi murmushi kawai dan gani take yi abu ne mai wahala mahaifinsa ya mai da ita.

*KURA*

*GIDAN MALLAM SHEHU SANI*

Sanye take cikin wasu kodaddin kaya samfarin riga da zani, Kowanne daban daban. Rigar ta wata atamfa ce shudiya me ratsin baki ta fattattake, Zanin kuma na wani material ne shima ya huhhuje yaji jiki. D’ankwalin kanta kuma na wani kayan ne daban. Daddagaggen gashin kanta ya lek’o ya hada uban datti.

Tulin wanki ne agabanta , Tana yi tana fyace majina tana jan kukan ta ahankali mai tsuma zuciya. Alokacin mahaifin su ya shigo hannun sa dauke da takarda da kosai guda shida aciki. Dayar ledar kuma kullin koko ne shima, Mika mata yayi,

“Rike nan Asmau! Au dan bakin munafurci har yanzu kukan kike yi? Kaga yar abu ta kazar ubancan. Matsa kafin na gaggabza miki mari....”

Hajia husnah ta sanya kasan zanin ta tana fyace majina, Cikin kuka ta tsugunna a kasa tana ko’karin kamo kasan rigar mahaifin nata ya matsa da sauri yana dalla mata harara,

“Baba dan Allah kasa Alhaji ya maida ni daki na. Wallahi na shiryu.”

“Ni ba mutumin banza bane Asma’u, A kaf karkarar nan ke ake kwaikwayo, A gidannan ma ke nake kalla naji dadi Asmau, ki kai fatali da maraicin ki kika rungumi wawiyar ‘dabi’a. Yanzu wa gari ya waya uhm? Ki zauna kiyi karatun ta nutsu. Sannan ki debo ruwa a rafi ki cika randunan can.”

Ya karasa fada yana mai nuni da randunan ruwa guda uku sannan ya fice yana kada rigar sa a fuskar ta hade da dire mata koko da kosan a gefen inda take a tsugunne. Kuka ta barke dashi tana jan majina, Ta dubi koko da kosan tai wulli dasu, Can kuma ta mike ta dakko su tana daddannawa a bakin ta. Tana ci tana hawaye tunawa da tayi da irin karin kumallon cimar da’din da suke ci a gidan ta. Bokiti ta dauka ta tafi rafi tana hawaye, Gaba d’aya nadamar rayuwar ta take yi ta baya, Haka ta shiga debo ruwan tana juye wa a randunan.

*WASHE—GARI*

Da la’asar tana zaune ta hada kai da gwiwa ta zurmama duniyar tunani ta jiyo muryoyin yaran ta akanta su uku, Ga akwatunan lefe guda bakwai suna shiga dashi. Hannuwan su shake da ledoji. Mik’ewa tayi zumbur tana sosa kai,

“Ah sannun ku da zuwa...”

“Umma...!”

Cewar Haysam, Ya rungumeta yana sakin ajiyar zucia, Tabarma ta shimfida musu suka zazzzauna suna gaishe ta d’aya bayan d’aya,

‘Fadima itace yarta ta farko me aure, Sai Hibbatu dake aure a Misau, Sai shi auta Haysam..’ Duk amsa musu tayi kanta a kasa cike da nadama, Mahaifin ta ne ya shigo shi da matar sa ta biyu kasancewar mahaifiyar Hajia Husnah ta dade da rasuwa.. Inna lantai da dawowar ta kenan daga k’auyen su na ‘kacako’ ta ajiye shamilallen mayafinta a gefe tana watsa burbudin goro a bakin ta, hakoran ta gaba d’aya sun rine sunyi jajir dasu, Su Haysam suka shiga gayda su cike da ladabi, Kayan suka matsar dashi gaban Hajia husnah,

“Umma ga kayan lefen Haysam za’a kai jibi ki sa musu albarka..”

“Allah yasanya albarka”

Ta fada a sanyaye, sam ta kasa ma sakin jiki da yaran nata. Suma kallon ta suke cike da tausayin yadda ta sauya gaba d’aya.. Basu wani jima ba suka mata sallama suka tafi bayan sun ajiye mata tarin alkhairi mai yawa. Haysam kuwa harda hawayen sa.

“Asamau karki manta da kai markadan geron can, So nake gobe muyi aikin sa ayi mekyau, Nasan da wuri za’a siye shi. Kinji?”

Inna lantai tace da Hajia husnah. Gyada kai kawai Hajia husnah tayi tana maida hawayen ta.

Cikin kankanin lokaci akai komai na bikin Haysam, kasan cewar ba anan zasu zauna ba yasa babu abinda aka siya sai anje can zasu siya abun su. Shi yasa koda taje bikin Haysam d'in ba can taje ba gidan wata k’awarta ta zauna har aka kammala komai ta koma kauyen kura.

Sati d'aya da yin biki Haysam suka daga shida amaryarsa Azeema zuwa kasa mai tsarki, tare da rakiyar uncle Idris kasan cewar shine zai nuna musu gidan da zasu zauna.

•••X••O•••X••O•••

Ciwo sosai Hajia husnah tayi bayan an gama bikin Haysam abun tausayi ta sake ramewa ta kanjame, Duk ta fita hayyacin ta, Daren ranar ta sake komawa wajen mahaifin ta ta roke shi kan yasa Alhaji Kabeer ya maida ita dakin ta wallahi tayi nadama. Ganin dagaske ta horu tayi nadamar yasa mahaifin nata nuna mata zai kira shin hade da doriyar,

“Asmau ki bude kunne kiji: Hak’ik’a musulunci yana umarni da kyakkyawan ZATO. Addinin musulunci ya umarci Musulmi da su yi wa junansu kyakkyawan zato kuma su yi wa ayyukan mumini kyakkyawar fassara wadda ta dace da shari’, Bai halatta ba wani ya dauka cewa wane fasiqi ne matuqar bai tabbatar da qaqqarfar hujja ba. Kinji d’aya?,

“Imam Ali (AS) yace: Ka dauki al\'amarin dan uwanka a matsayi mafi kyau har sai wani abu da zai sa ka janye ya bayyana a gare ka, ka da ka yi mummunan zato ga kalmar da ta fito daga bakin dan uwanka alhali za ka iya yi mata kyakkyawan zato, Littafin Jami\'us Sa\'adat, Juz\'i na 2, shafi na 28: Yi wa juna kyakkyawan zato yana qulla qauna a tsakanin jama\'a kuma ya samar da hadin kai a tsakanin su. Shugabannin musulunci sun yi bayanai iri-iri dangane da sakamakon kyakkyawan zato. Imam Ali (AS) yana cewa:Duk wanda ya yi kyakkyawan zato wa mutane to za su so shi.”

“Musulunci ya himmantu da karfafa damkon soyayya tsakanin musulmai, da karfafa IGIYAR yan-uwantaka tsakanin muminai, don haka ne yayi kira zuwa ga duk abinda zai kara damkon wannan zumuntar, Kaman yada sallama, da musafaha yayin haduwa, da dai sauransu. Hakanan musulunci ya tsoratar game da duk abinda zai raunana wannan soyayya, kamar mummunan zato tsakanin musulmai, da gulma da annamimanci , da dai sauran su. Lallai mummunan zato wata babbar hanya ce ta yada gaba da kiyayya tsakanin musulmai, da yanke alaqoqi, da wargaza iyalai, da bata yan-uwantakar musulunci,

“A ZATON ki gani kike kinfi kowa ko? Kin kere kowa, Kina wulak’anta mutane, Ki sani duk abubuwan da kika yiyyi sun kokkoma kunnuwan mijin ki, Bayan wallahi mu bamu rene ki da haka ba, Ba tarbiyyar gidan nan bace. Zan gaya miki halayen da ya kamata kiyi koyi dasu,

“Shin menene kyawun hali? Kuma ta wacce hanya mutum zai bi ya kyautata halayensa?. Kyawun HalayE adunkule yana nufin kyakkyawar Mu’amalah tsakaninki da Jama’a. Ita kuwa kyakkyawar mu’amala da Jama’a zata iya gudanuwa ta hanyoyi da dama. Wadannan hanyoyin sun hada da: Sakin Fuska ga Mutane : Sakin fuska abu ne mai muhimmanci a Musulunci. Annabi (saw) ya Qirga abubuwan da mutum zai yi Allah ya bashi ladan yin sadaka. Acikinsu har da sakin fuska ga mutane, Sakin fuska yakan kiyaye mummunan ZATO, yakan gyara Mu’amala, yakan kawo alkhairai da dama.

“YIN KYAUTA DA IHSANI : Yawan kyauta da kuma kyautatawa yana daga cikin halayen Manzon Allah (SAW). Ya kasance yana yin kyauta ga masoyansa har Makiyansa. Wannan ya janyo zukatan mutane da yawa suka shiga Musulunci. Shi yasa ma Manzon Allah (saww) yake cewa: MAI YAWAN KYAUTA, YANA KUSA DA ALLAH KUMA YANA KUSA

Please Login or Register in order to submit comment