Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gasu. Ke Bintalo baki da wata kadarar a kasa?”

Bintalo ta barke da kuka tana jan majina,

“Ba ni dasu Yaya..”

“Toh fa! Ni dai nacewa Zabbau yanzu tazo tatafi kod’e ta sanarwa yan uwanki suma su dan tallafa a harhada a bada wani sashen dan wallahi bansan ya za’ai ba..”

Shiru tamkar ruwa ya cinye gidan mu haka akai dif na yan wasu mintina, Da alamun kowannen mu ya tafi tunani. Cikin haka zabbau ta shirya ta tafi kano kauyen lahadin makole can cikin rugar kod’e. An dau tsawon lokaci kafin ta dawo tun wajajen 11 saura kwata na safe ba ita ta dawo ba sai shida saura na yamma. Ta dawo hajaran majaran tana haki,

“Walle talle Gwaggo sunce babu ruwan su, Wai ai bata neman su duk tsawon hekarun nan sai yanzu? Dak’yar ma wallahi suka bani ruwa na hya. Dantakibiruwa ne kawai ya bani wannan..”

Zabbau ta karasa fada tana mikawa Gwaggo wasu kudi sun cuccure da juna, Yan ishirin da yan hamsin. Gwaggo ta kada kai ,

“Dantakabiruwa da suke uba d’aya dai?”

“Hi dai..”

“Sana’ar meya ke ma?”

“Rake ike siyarwa..”

“Allah sarki gashi ya bayar dari biyar cif. Angode Allah ya saka masa da alkhairi. Bintalo kinga irin ta, Yan uwan ki da kuke uwa d’aya uba d’aya ma sunki temakar ki saboda kin yanke zumunci dasu, Sai wanda kuke baba d’aya ne yaba ki. Bayan irin bak’ar muguntar da kika yiyyi masa, Har kaduna yaje yake gayamin. Allah dai ya kyauta kawai.”

Gwaggo ta fada tana d’aga kudin yan ashirin guda goma da yan hamsin guda shida. Direban ta ta kira awaya tabashi atm card dinta ya ciro mata kudi, Ta harhada dana wajen Innar mu da na kayan dakin Bintalo da aka siye, Sannan ta kira Ruma ta bata,

“Iya abunda Allah yasa muka hada kenan, Sauran abunda bai samu ba sai kuyi hakuri sai nan gaba idan Allah yabata lapia?”

Ruma taja tsaki tana watsa hannu baya,

“Sai na jira ta samu lapia? Wannan ai ba zata tab’a tashi ba. Ta rigada ta gama tashin aiki kuma. Kinga hajia ku biya ni kudade na kawai.. Babu wani xancen sai nan gaba. Babu wannan harkar a dishinari na ehe..”

Gwaggo Aminatu ta mike tsaye tana gyara zaman mayafin ta,

“Duk abunda kika ga zakiyi sai kiyi, Da kinsan ta yadda aka harhada wannan kudin na hannun ki da kin sha mamaki. Naga alamar jirgi d’aya ne ya debo ku keda ita. Toh mu dai munyi iya yin mu..”

“Toh billahil lazi na bada kwana ki uku rak dole abiya ni saurin kudade na.”

“Duk yadda zakiyi kiyi baiwar Allah!”

Gwaggo Aminatu tace da Ruma haka. Ruma taja tsaki ta figi mayafin ta ta fice tana masifa. Gwaggo ta tab’e baki tana jinjina kai,

“Allah yasa hakan ya zamto muku iznah agare ku. Sai ku gyara ku nemi yafiyar wanda kuka zalun ta. Ku kuma tuna zumunci ba abin yarwa bane. Allah ya kyauta ni zan koma. Bintalo Allah ya baki lapia..”

Gwaggo Aminatu na gama magana tai kasa tana rataya jakarta. Har waje muka rakata muka mata sallama ta tafi. Mata mai mutinci da karamci kenan. Duk duniya idan na cire iyaye na banida na biyu fyace ita. Bayan magriba yan gwangwan suka zo suka kwashe kayan dakin Bintalo duka ko tsinke babu abunda suka rage. Ina jiyo sautin kukan ta dana yaran ta, Cikin kuka take rokon su su temaka mata tai fitsari,

“Zabbau fitsari! Kinji Zabbau! Alawiyyah zanyi fitsari.”

“Walle nagaji bazan iya tahi ba. Sau hi kawai a haka.”

Zabbau ta bata amsa tana karkada kafafuwan ta. Alawiyyah kuwa cikan ki bata ce mata ba. Wohoho rayuwa, duniya kenan! Duk wanda ya d’aura da ita yai gaggawar kunce ta. Domin duniya tamkar rawar yammata ce na gaba ya koma baya duniya makaranta. Allah kasa mu dace.. Ni kuwa daren ranar gaba d’aya raya shi nai da sallolin nafilfili ina rokon Allah ya kara karemu daga sharrin masu sharri. Ya kuma biya mana bukatun mu na alkhairi..!


•••X•••O•••X••••O••••


“Mubeen! Mubeen! Mubeen!”

Haka Aunty Rahila kanwar Amb Salees ta shiga kwalawa Mubeen kira ganin yadda abincin da yace a zuba masa yake sandarewa, Shi kuwa Muhammad Mubeen alokacin yana dakin sa ya takure waje d’aya yana dafe da kirjin sa dake barazanar fadowa kasa. Sai wani wahalallen tari yake yi ahankali. Ganin bai fito ba yasa ta mike ta shiga dakin da yake. Tana shiga taja tayi turus tana dafe kirjin hade da callara karar neman kawo dauki,

“Wayyo Allah!! Gwaggo nashiga uku.”


ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_𝓘𝓖𝓘𝓨𝓐𝓡_____𝓩𝓐𝓣𝓞💞



*46*


Mahaifiyar su Malama Adama Modu wacce suke kira da ‘’Ya” Itace ta shiga dakin hankalin ta a matuk’ar tashe.

“Meya faru dashi?”

“Ya wallahi bansani ba. Dazun nan fa na gama magana dashi akan abinci nace sai yaci dole. Yace a zuba mishi shine kuma shiru-shiru bai fito ba. Na shigo na ganshi haka..”

Aunty rahila na magana jikin ta na rawa, Yayyah Adama ta karasa wajen Mubeen tana tana taba goshin sa,

“Muhammadu! Kana jina?..”

Shiru Mubeen bai amsa ba. Gaba d’aya ya tukwikwiye jikin sa yayi zafi rad’au. Tashin duniyar nan anmasa ya’ki motsa jikin sa. Ganin haka yasa hankali tashe babban ‘dan aunty rahila ya sungume shi yasa a mota suka tafi asibiti. Temakon gaggawa aka fara bashi amman lamarin yaci tura. Likitan ya shiga office dinsa su Aunty Rahila na biye dashi. Ya shafe gumin goshin sa hade da bubbuga biro a teburin sa yana duban su Yayya Adama,

“Wacece mahaifiyar sa acikin ku?”

“Dr ni kanwar mahaifin sa ce, Wannan kuma mahaifiyar mu ce..”

“Toh Masha Allahu, Dama yana da dadaddiyar rashin lapia ne? Tun yaushe kuka same shi a wannan yanayin?”

“Gaskia Dr iya sani na dashi bayason abinci, Sannan da a Ethiopia suke, Toh akwai wata shekara da muka je kasar, Anan muka same shi bashida lapia Dr din yace a dena bata masa rai..”

“Okay... Shekarar sa nawa kenan yanzu? Yayi talatin?”

“A’a gaskia bai yi ba..”

“Toh a zahirin gaskia yaron ku yana fama da matsananciyar rashin lapia data yiwa gangar jikin sa da zuciyar sa mugun kamu. Gashi chronic ulcer taci karfin sa. Ya akai kuka bari matashin saurayi haka ya samu wa’innan mugayen cututtukan?”

Yayyah Adama da Aunty Rahila suka kalli juna kowannen su cike da mamakin kalaman likitan. Likitan ya kara numfasawa kafin ya cigaba,

“Inde har baku yi gaggawar bashi abinda zuciyar sa da gangar jikin sa ke muradi ba to akwai matsala gaskia..”

“Toh zan gayawa mahaifin sa yadda ake ciki..”

Likitan ya sake kallon su Yayya Adama yana kafa robar ruwa a bakin sa. Sai da yasha mai isar sa kafin ya cigaba da ce musu,

“Mahaifiyar sa da mahaifin sa sun rabu ne?..”

Aunty Rahila tai hanzarin kada kanta,

“Aa suna tare.. Shi karatu yake yi anan dinne a gidah na.”

Meyakwan yai shiru sai ya sake jeho waata tambayar. Kilan a tunanin sa riko a kewa Mubeen wanda ake takura masa dinnan da har hakan ke cin sa a ransa.

“Ya akai baya karatun awajen su..?”

Yayyah Adama ta cire tagumin data zabga,

“Kaga dakta! Mahaifin yaron nan shine gwamna mai ci na kaduna a yanzu, K...”

Bata karasa ba likitan yamik’e tsaye yana dafe da kirjin sa idanuwan sa duk sun furfuto,

“Gwa me?”

“Gwamnan kaduna..”

Rigar sa ya shiga kadawa yana jijjiga kai,

“Dankari! Billahil lazi sai da kika fada naga kamar sa da gwamnan mu tamkar an tsaga kara an karya. Allah ya bashi lapia, Ba.. Ba naje na kara dudduba shi.”

Sumsum ya fice yana sauri, Shegiya naira. Kankace me tuni ya fesawa sauran likitoci sun taru akan Mubeen suna sake dudduba shi. Aunty Rahila kuwa waya ta janyo ta kira Amb Salees da Haj Ahlaam inda ta sheda musu yadda ake ciki. Ba’a dau lokaci ba sai gasu sunyi ‘badda kama sunzo. Babu wanda zai dauka gwamna ne, A matuk’ar hargitse suke. Gwaggon ta kwakkwantar musu da hankali. Hankalin Amb ya kasa kwanciya da asibitin suka tattara suka koma kaduna.

*KADUNA*

*GOVT HOUSE*

Amb Sales ya kira private family doctors din su suka dauki Mubeen suka rankaya kaduna gaba d’aya. Manyan physicians ne suka taru akan Mubeen dake kwance bai san inda kansa yake ba. Gwaje gwaje suka yi tayi masa suna ganin results din. Haj Ahlam takasa zama sai zubar da hawaye take yi..

Tuni aka kira malamai suka shiga addu’oi suna ro’kon Allah. Cikin ikon sa da qudurar sa kuwa sai gashi Muhammad Mubeen ya farfado daga doguwar sumar da yayi. Amman bai motsa jikin sa ba. Numfashin sa dai na fita a hankali, Ya rame lokaci d’aya ya zabge. Karan hancin sa tamkar an sake jansa, Rubdugu suka shiga yi akan sa suyi wancen suyi wannan. Wani dogon numfashi yaja yana girgiza dan yatsan kafafun sa na kafar hagu,

“Muhammad Mubeen! Mubeen! Mubeen... Kana jina?”

Dr Affan (cardiologist) ya shiga tattaba kafafun Mubeen yana kokarin bud’e idanun sa. Amb Salees ya shiga zagaye dakin cikin tsantsar damuwa, Fita dr Affan yayi daga cikin dakin ya koma parlor wajen su Aunty Rahila. Suna ganin sa suka mimmike daga xaunen da suke,

“Hajia shin akwai wani abu daya faru dashi ne kafin zuwan ku wancen asibitin?”

“A’a likita, Kasan shi da ‘kin cin abinci. Na sashi a gaba kan ya temaka yaci ko kadanne. Sai ya tashi ya shiga dakin sa yace bari ya watsa ruwa ya fito yaci. Wallahi har na zuba masa abincin ma, Shiru shiru ganin bai fito ba abincin nasa na sanyi. Sai na tashi naje dakin nasa domin kiran sa. Shine fa na same shi cikin wannan yanayin. Ko Yayyah..?”

Ya Adama ta kada kai alamun Eh. Tana mai cigaba da jan carbin ta. Gaba d’aya itama hankalin ta a tashe yake. Dr Affan ya sauke gwauron numfashi yana kallon Amb Salees,

“Your excellency gaskia Muhammad Mubeen na cikin wani yanayi, Kasan daman shi ba ishasshiyar lapia ce dashi ba, Ga chronic ulcer data sake rarake jikin sa. Jinin sama yayi low wallahi. Meya taso da wannan ciwukan nasa lokaci d’aya haka?”

“Wallahi dr ni bansani ba. Iya bakin k’ok’ari dai muna yi masa. Akan abinci dama sai an ta fama dashi wallahi.”

Amb Salees ya bashi amsa yana dafe da goshin sa, Dr Affan ya sosa kunnen sa yana cije kasan leben sa,

“Wallahi kuwa taci karfin sa, Shiysa kullun zamu yi masa saline na tsawon sati uku da kuma alluran histidine monohydrochloride (Larostidin, Roche) Matsalan Muhammad Congenital heart disease dinsa yayi karfi da yawa, Abu ne da zamu kira shi da tun yana zanin haihuwa yake fuskan ta, Gashi bugun zuciyar sa ma ya canza (Arrhythmia). Kuma kaga it needs to be taken more seriously and treated. Ga Mitral regurgitation shi yasa yawanci yake jinsa a gajiye.

“Allah ya temaka ma bai shiga Myocardial infarction ba irin na shekarun baya. So dan ALLAH your excellency acigaba da kokarin tarairayar mUhammad wallahi yana shan wahala. Tun yana zanin goyo yake experiencing pains.“

“IN SHA ALLAHU! Allah dai ya tashi kafad’un sa.”

“Dr Affan ya tashi..”

Cewar Dr Uchenna daya le’ko da kansa ta k’ofa yana kiran sa. Da sauri Dr Affan ya koma ciki shida Amb Salees,

“Muhammad.. Mubeen ! Kana jina?”

“Son! Son son! Kana ji?”

Dr Affan da Amb Salees suka shiga kiran sunan Mubeen ganin yana kokarin bud’e idanun sa.

“Batoul...Ayana... Batoul!!!”

Sune sunayen da bakin Mubeen ya shiga nanatawa yana dafe da saitin zuciar sa. Likitocin suka shiga bashi temako. Shi kuwa Amb Salees sandarewa yayi a tsaye yana maimata sunan Batoul da Mubeen yake nema. Kowacece oho??

“Mubeen kana jina..? Dr Affan ne! Kana gani na?”

“Batoul..”

“Ba inda yake maka ciwo?kan ka, Cikin ka, kirjin ka inane yake maka ciwo?”

“Batoul.. Dan Allah ki saurare ni.. Ma plss!!”

Dr Affan yana kada kai yana kallon Amb Salees,

“Your excellency wacece Batoul? Tana ina Pls? Idan tana kusa sai komai yafi zuwa da sauki..”

“Wa..Wa..Wallahi bansan wacece Batoul ba.”

“Subahanallahi!..”

“Akwai matsala ne Dr?”

“Eh toh gaskia da son samu ne dai ace Batoul din na nan wajen.. Komai zai fi zuwa da sauki!”

Ficewa yai ya koma parlor wajen su Aunty Rahila,

“Ko kinsan wacece Batoul a zaman da ku kai da Mubeen?”

Amb Salees ya tambayi Aunty Rahila yana kallon agogon hannun sa,

“Gaskia a’a Yaya! Wallahi bansan ta ba..”

“Ko cikin yaran kuma?”

“Anya banaji gaskia, Amman bara na tambayi su Jawad.”

Daukar wayar ta tayi ta shiga kiran yaran ta maza ko sun san da masaniyar hakan? Duk cikin su babu wanda yasan komai. Ta katse kiran a sanyaye tana sanar dasu yadda akai. Amb Salees ya koma wajen Haj Ahlaam dake shararar hawaye,

“Ko kinsan wacece Batoul din Mubeen ke kira?”

Girgiza kai tayi tana fyace hancin ta,

“Bansan ta ba wallahi.. Pls a nemo masa ita.”

Mikewa yai bayan ya k’ada mata kai ya koma ciki wajen su Dr Affan,

“Dr bamusan wacece ita ba gaskia.”

“Toh Alhamdulillah mun masa allura ya koma bacci ma zuwa anjima zai tashi, Dan Allah adai cigito masa Batoul dinnan your excellency!”

“IN SHA ALLAHU! Mun gode sosai, Ga abinci can a site dina an ajiye muku.”

Ya karasa fada yana gaggaysawa da likitocin. Cike da girmamawa suka a’amsa kafin su fice don cin abinci, Amb Salees ma fita yayi ya koma wajen meeting da suke gabatarwa shi da sauran muqarraban sa akan matakin kwamishinas da zai nannad’a..

Muhammad Mubeen bai farka ba sai gab da sallar la’asar. A hankali yake bubbude idanuwan sa da su kayi masa nauyi saboda tsabar ciwo. Ya Adama da Aunty Rahila, Haj Ahlaam, Jannat da sauran yan uwa da aka taru akan sa. Wani likitan ya shiga dudduba shi yana tambayar sa,

“Mubeen kana gani na? Yatsu nawa ne na daga yanzu?”

Ya karasa fada yana hada hannayen sa guda shida. Mubeen ya kikkifta idanu yana taune leben sa na kasa ahankali cikin ciwo yace,

“Guda... 12 ne.”

“12????”

Likitan ya maimata yana dafe kansa, Mubeen ya kada kai alamun Eh. Amb Salees dake gefe ya shiga jujjuya kai cike da damuwa.

“Double vision... Ina Doctor Lyna??”

Cewar surgeon Isah! neuro-ophthalmologist Lyna ta matsa kusa da Mubeen tana dudduba idanun sa. Ta duba shi sosai sannan ta juya tana wa sauran doctors din bayani.. Haka dai su kayi ta gwagwarmaya akan sa. Amb Salees ya koma parlor ya zauna yana dafe kai. Daman Haj Ahlaam tana zaune tana kuka. Gaba d’aya sauran yan cikin dakin suka firfito ciki harda doctors din,

“Doctor ya..?”

“Ah bakomi! Mun mishi allura ne yana bukatar bed rest! Kakka dama your honor. “

“Ya batin double vision din?”

“Zai dawo normal nan da some hours daman transient ischemic attack ne...”

“Ya Subhan’Allah!!!”

“Kakka damu your honor! ISA zai wartsake dama ace ita Batoul din na kusa da tuni ma ya tashi..”

Fita Amb Salees yai ya kira direban dake kai Mubeen makarnta. Yan tambayoyi ya yiyyi masa anan ya gano cewar Mubeen din na kula wata malamar su dake zaria unguwar ‘limancin kona’. Mai suna ‘Batoul’ Waya ya zaro ya kira mijin Aunty Rahila inda yace ya gudanar masa da binciken Batoul din. Sannan ya sake kiran Alhaji Kabeer mai wafa a waya yace masa yayi bincike shima. Cike da karfin gwiwa ya koma parlorn da ahalin nasa suke. Yayi sa’a kuwa sai Ya Adama ta idar da sallar ta babu kowa sai Jannat a gefe tana danna waya. Yace ta basu wuri, Sannan ya shiga zayyane mata komai ya k’ark’are da,

“Toh kinji dai yadda ake ciki Yayya. Nama kira Alhaji Salim mijin rahila a
waya da wani yaro na Alh Kabeer mazaunin zarian ne. Ya kike gani Yayya? A nemo yarinyar tayi jinyar sa ko?”

“Toh agaskiya ‘dannan (Saboda shine dan fari) bazan bada goyon a dakko yarinyar mutane ta rika jinyar sa ba..”

“Toh Yayya ai shawarar ki nake nema.. Ya kika gani? Banda ma Mubeen da fitnar sa yarinyar ma fa malamar su ce wai..”

“Toh ai ba haramin bane ‘dannan. Ba kansa farau ba. Sai kaga idan Allah yasanya alkhairi a lamarin zaka sha mamaki. Wani hanzari ma ba gudu ba, Ita yarinyar babu maganar auren wani akanta ko? Saboda kaga babu kyau neman aure akan aure..”

“Hakane amman Yayyah hakan ba zai janyo surutai ba ganin ta fishi shekaru? Duk da dai shi din bai karatu da wuri ba ba kuma tabbatarwa mukayi da ta girmeshin ba...”

“Babu komai ‘dannan ni ina ganin zai samu ladan sunnoni biyu, Koda ta girmeshin. Wato sunnar aure da kuma ta koyi da fiyayyen halitta annabin mu (SAW)Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi. Kuma kowanne dan adam yanada yadda Allah ya qaddarar masa rayuwa, Idan kayi hak’uri sai kaci ribar hakan agaba. Allah dai ya zabi abinda yafi alkhairi Ameen.”

“Ameen Ya... Duk yadda mu kayi dasu zan sanar miki”

“Allah yasa muji alkhairi..”

••X••O••X••O••

Alhaji Salim da Alhaji Kabeer duk sunyi bincike akan Batoul kuma Alhamdulillah babu wata suka da samu daga gare ta, Kuma babu neman auren wani akan ta. Uwa uba shekarun da ake kawo mata ba hakan bane. Nan da nan Amb Salees ya kira kanin sa awaya wato senator Bilalu da Alhaji Salim da Alhaji Kabeer kan suje su tambayo auren Batoul a gidan su...

Alhaji Kabeer daya gama kammala wayar da yake da Amb Salees ya dashare hak’ora yana murmushi. Haj Husnah ta kalle shi tana neman karin bayani,

“Alhaji samuwa ce ne?”

“Na’am Hajjaju.. Eh toh kusan hakane. Kinga neman aure aka samu ne, Munyi bincike akan wata yarinya dake nan kasan unguwar mu. Kinga har ana zancen nemo auren ta ma..”

“Wa kenan?? Alhaji har kai za’a sa binciken aure?”

“Eh gaba da gabanta ne hajjaju! Amb Salees ne ya samu.”

Hajia Husnah ta zaro idanu tana dafe kirji,

“Gwamna da kansa? Ya rasa inda Za’a nemo aure sai nan unguwar?Shine zai yi auren ko kuwa?”

“Toh menene aciki? Shi aure ai albarka ake nema ba kyale-kyalen duniya ba hajjaju.. A’a bashi zai yi ba”

“Wa..Yarinyar sa”

“A’a yaron sa ne..”

“Kuma Alhaji a kasan layin nan yake nema? Kaf unguwar nan akwai wanda ya kai gidan nan arziki?”

Dafe kansa Alhaji Kabeer yai yana sakin tsaki,

“Kina da matsala wallahi. Allah ya kyauta miki hajjaju, Sai yar me kudi zai aura? Ki canza dan Allah! Toh yarinyar ma marainiya ce mahaifin ta ya rasu. Inda Allah ya temaka ma tana aiki akace.. Ni kuwa yasunan gidan da muka jema?”

Alhaji Kabeer ya daga kansa yana tunani. Haj Husnah duk ta birki ce tana sosa kai. Alhaji Kabeer yai murmushi,

“Yauwa gidan mata tara.. Sunan ta Batoul! Ance yarinyar akwai nutsuwa da sanin yakamata.”

Wani gundumemen zagi Haj husnah ta saki tana zare idanu, Banzan kallo Alhaji Kabeer yayi mata yana girgiza kai.

“Alhaji da..Dan girman Allah dagaske?”

“Ga gaskiya ga rantsuwa..”

“Batoul dince zata auri dan gidan gwamna??? When! How? Why?”

Dai dai nan Haysam dake tahowa ya jiyosu. Dafe kansa yai da lokaci d’aya ya shiga juya masa. Hannu yasa ya rike bango yana rintse idanun sa. Alhaji Kabeer ya mike tsaye yana tattare rigar jikin sa,

“HasbunAllahu wa ni’imal wakil! Hajia kin fara bani tsoro gaskia. Ina ruwan ki da shiga harkar wanda ‘yayan su zasu aura? Taya akai ma kikasan yarinyar?”

Cikin rawar jiki da baki tamkar susucacciya Haj Husna ta sosa kanta tana yarfe hannuwa,

“Alhaji ina matar nan da tazo ta mana aikatau..? Shegiyar matar nan na tsane su itada ‘yarta.. Nan fa suka yiwa Haysam sihiri ya sururuce akan yarinyar. Batoul din ita ce dai wacce ka gama magana yanzu.”

Alhaji Kabeer yaja tsaki yana girgiza kai,

“Toh idanma kin tsane su ai Allah yana son su ko? Gashi yanzu cikin hikimar sa da zatin sa zai sanya yarinyar ta shiga gidan gwamnati.”

“Ba za’ai haka ba. Dan girman Allah kayi meyiwuwar hana auren nan.. Yarinyar nan fa itace wadda suka gama sihirce Haysam wai shi lallai sai ya aure ta.”

“Itace kwanaki yamin maganar ta ya dawo yace an bada ita ko? Kiji tsoron Allah husnah ki dena hada husuma. Sai yanzu na gano kece kika hanashi auren ta saboda ba masu kudi bane ko? Toh ai gashi nan ta xarce tunanin ki..”

Haysam ya shiga parlorn yana tangadi, Alhaji Kabeer ya kalle shi yana yamutsa fuska,

“Kai Haysam kasan Batoul?”

D’aga kai Haysam yayi jikin sa a matuk’ar sanyaye yana kallon idon mahaifiyar sa,

“Abba itace wadda nace ku nemar mun auren ta..”

“Kacemin aure za’a mata kuma? Meyasa?”

Saurin girgiza kai Haysam yayi yana mai da kallon sa ga Abban nasu, Saboda yadda Haj husnah ta tsare shi da idanu alamun karya kwafsa mata.

“Abba umma ce ta hanani neman ta.. Tace bata yafe min ba idan har na aure ta.”

Kada kai Alhaji Kabeer yai cike da takaici. Yana kallon Haj husnah dake raba idanu,

“Tsaya kaji Alhaji.. wa..”

“Inji me? Dakata tsaya Hajia. Kinsan na dade ina taraki daman ko? Toh a zahirin gaskia nagaji da ire-iren abubuwan da kike aikatawa a gidan nan. Kowa ya budi baki sai dai ya yabi abokiyar zaman ki? Sam baki da hali, Kowa yaita kawo korafi akan ki. ‘Yayan ki ma kin bata tarbiyyar su? Nagaji wallahi Asmau! Nagaji da halin ki..”

“Alhaji tsaya kaji”

“Kai Haysam kaga yanzu an riga da an fara nemawa yaron Amb Salees auren ta, Saboda shidin ba mai cikakkiyar lapia bane. Saboda haka kayi hak’uri, Allah yayi ba matar ka bace. Kaje ka nemo auren yar kanwata sahura d..”

Haj Husnah ta zunduma kara tana bubbuga k’afa,

“Alhaji auren yar sahura fa? Su da suke a can kauyen kura dake kano? Haba Alhaji”

Alhaji Kabeer ya jijjiga kai yana hade hannuwan sa,

“Yaje ya auri wadda kika zabar masa amman ba anan gidan ba. Kina jina? Ki tattara komai naki ki tafi gidah na sake ki saki d’aya, Idan naga kinyi hankali kya dawo, Idan kuma zaman mu ya kare ma shikenan..”

Haj Husna ta zube ak’asa tana kuka harda jefar da d’ankwalin kanta,

“Saki fa Alhaji? Alhaji me zanyi a kauye yanzu? Fisabilillahi na saba da miyar ja tasha nama anan na koma k’auye? Kuka ce fa akeyi shar da ita kullum, Ga ruwan kogi ne ake wanka. Ba wuta fa Alhaji.”

“Kinsan da hakan mahaifar ki take kike wulakanta mutane? Wallahi Allah sai kin tafi a yau ba sai gobe ba. Idan na dawo gidan nan na ganki ko naji labarin kina garin nan sai na mugun sab’a miki.. “

“Wayyo Alhaji ka temake ni..”

“Babu abinda zan iya miki. Ki tattara kayan ki ki koma inda kika fito. Alhamdulillah sahura jini na ce bazan taba iya rabuwa da ita ba ko na canza wata. Amman ke zan iya sauya ki na nemo wata. Tamkar hular sawa kike a wuri na kina ji? Ki koma can karkakar da kika fito. Allah ya kyauta.”

Yana gama magana yai hanyar kofa har yaje ya dawo yana duban Haysam dake tsiyayar da hawaye,

“Kai kuma ka tafi gidan Idris ka huta(kanin sa dake abuja) Ga habule direba can ya kai ka yanzu ba sai an dau lokaci ba. Allah ya kiyaye hanya kaji?”

D’aga kai Haysam yayi yabi bayan mahaifin sa. Ita kuma Haj husnah ta shiga birgima tana koke koke. Inna mai aiki na jin haka ta tattara komatsanta tayi gaba. Haysam ma mota ya shige direba yaja shi sai Abuja. Gaba d’aya ji yake komai na duniyar ya tsaya masa sak. Cikin addu’oin da yake kamowa yaji wani sanyi a ransa. Lambar Batoul ya lalubo ya goge yana tsiyayyar da hawaye hade da yi mata fatan alkhairi acikin rayuwar auren ta. Lokaci kankani bacci yai gaba dashi. Direban kuwa sai sharara gudu yake.

Please Login or Register in order to submit comment