Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gand’ama-gandama daku? A hayye yau ga gaye ba makilis! Bayan ku ga gayyar yara? Sullutuwar wofi idan baki sani ba barbade ki suke yi a abincin da suke baki suna kalallameki da zance cikin tsohon munafurci. Sahorama, Ki tashi ki zaga gari idan da rabon ki kya samo.”

Girgiza kai kawai nayi nayi hanyar shiga bandaki Bintalo tasha gabana tana nuna ni da yatsa, Dayan hannun ta kuma tana sosa takashi. Nayi murmushi ina gumtse dariyar data tahomin.

“Wa kike wa dariya iyye?”

“Ah bazan yi daria ba baba? Toh bada kowa nake ba.”

“Da kaltume kike sittin ta ubangiji.”

Wani kallo na watsa mata wanda yasa tasha jinin jikin ta,

“Uhm uhm dai baba, Ki tsaya akai na banda tab’o uwata wallahi.”

Usaiba dake gefe ta saki guda tana buga zani,

“Jar ubancan kayya kai! A hayye kayya kai..”

Bintalo ta dora hannaye a kirji tana min wani kallo,

“Ni kike zagi Batoul?”

“Wa? Kinji na zage ki? Ai banma iya ba domin ban tashi naji anai ba.”

“A hayye yau ga gaye ba makilis. Toh waye me zagin iyye? Sittin ta ubangiji zan zugewa mutum tazuge duk girman sa kuwa.”

Daria na kyal’kyale da ita. Don wallahi gani nake tamkar wasan kwaikwayo, Guga na dauka na shiga janyo ruwa na Ina wak’a ta ahankali.

“Ga yar iska tana magana ko?”

“Hajia Baba Bintalo kenan. Ni fa wanka zanyi, Allah ya huci zuciyar babar mu.”

Dogon tsaki taja tana watsa hannu baya sai bambamin mita take ita kadai. Ni kuwa bandaki na shige nayo wanka na na haye sama. Sallah nayi na dan kishingida tuni bacci ya dauke ni. Ban farka ba sai gab da magriba, Alwala na dauro nayi sallah. Ina zaune ina lazumi Basmah ta shigo daki kira na,

“Wai kizo inji baba.”

Kada kai nayi kawai na cigaba da lazimi na domin banason a katse min shi. Sai da Innar mu ta min magana tukun sannan na sauka k’asan. Dakin sa na shiga ummita tacemin yana waje. Soro na leka. Tumbin wani mutumi na fara cin karo dashi, Gefen sa kuma Kawu ila ne sai dashare hakora yake. Yana gani na ya gyara tsayuwar sa yana nuno ni da hannu,

“Yauwa Alhaji ga.. Ga yarinyar da nake gaya maka nan ta fito.”

Alhajin ya mike yana shafa tumbi hade da sake matsowa yadda zai gano ni sosai. Ni kuwa kallo na shiga binsu dashi tamkar wata mutum mutumi...

**
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_



MX🧕🏼*32*

NANA HAFSAT

•••

Alhajin ya shiga shafa tumbin sa yana dagemin gira duba da yadda wutar lantarki ta haskaka zauren. Kawu ila ya shiga gyaran murya yana yafito ni ciki. Hade rai nayi na karasa bakin kofa na tsaya ina bin Kawu ila da kallon karin bayani,

“Ina wuni..”

Na ja a hankali ina k’arewa mutumin kallo ‘kasa-kasa. A haife ya haife ni, Sanye yake cikin wasu kaya farare kirar yadi. Kasan wandon ya tattare. Ya bulala babbar riga tana sharar kasa. Hular da ya sanya a kansa tayi wa kansa kadan. Sai ta tsaya a tsakiyar kan. Kallo na ya tsaya akan silifas din daya saka kafafuwan sa yayi masa kadan ainun. Shin meke tafe dashi? Na fada a zuciata ina sakin gwauron numfashi. Kawu ila dake gefen sa yana dashare hakora ya dube ni yana min kallon na saki jiki na. Ai kuwa na kara kudundunewa acikin hijabi ina kallon gefe, Na gaishe shi bai amsa ba mezan yi kuma?

“Alhaji itace wadda nake baka labari. Tayi?”

Na tab’e baki, Sai kace kayan sawa. Alhajin ya murmusa yana sosa gemun sa wanda ke dauke da furfura taso taso a cuccure. Ahankali yake bina da kallo kafin ya maida duban sa ga Kawu ila

“Tayi Ilyasu. Shi yasa ma na kasa magana. Tab carkwai mazwai. Komai yaji acan-acan ragad’au-dau abun ba acewa komai. Allah yayi halitta.”

Na kalle shi a kaikai ce ina maimata kalaman sa a hankali hade da nanata TubarkAllah! Shakka babu akwai alamun tambaya a tattare dashi. Kawu ila yai murmushi yana kokarin shigewa cikin gidah Alhajin ya dakatar dashi ta hanyar cewa,

“Zan ciko maka sauran alqawarin anjima ilyasu.”

“Toh Allah godia nake. Ke idan kun gama tad’in kya kirawo ni.”

Cewar Kawu ila yana kallo na. Naki hada idanu dashi ina bin gansamemen da yake cewa zamuyi tad’i da kallo.

“Amshi nan yar budurwa ya sunan ki?”

Alhajin ya tambaye ni yana sake dage girar sa dukka biyun. Ko me zan amsa oho?

“Sunana Zara’u.”

“Madallah malama zarau. Amshi nan diba, Toh ni dai sunana Alhaji Usman Usman Jibiya. Kuma anan zaria nike da zama, Amma a kankiya aka haihe ni. Nace ina neman matashiyar budurwar da zan aura ta haifamin yara dagwai-dagwai Ilyasu yace akwai yammata anan kala-kala. Banyi ‘kasa a gwiwa ba kuwa nace ya rako ni. Sai gashi ina tozali da ke wani abu yazo ya soke ni a zucia ta,

“Na da’de inason kara aure, Domin matana uku biyu sundena haihuwa, Dayar kuma data samu ciki sai ya bare. Ni ba wani babba bane da kike gani na haka, Furfurar kudi ce ta yanyane min kai...”

Kallon sa nayi na kalli kan nasa. Mutum ya tsufa amma ya ki amincewa. Wai furfurar kudi? Na maimaita a zuciata ina murmushi. Daga masa kai nayi ya cigaba da cewa,

“Yayana talatin ba biyu. Biyun kai mahaifiyar su mun rabu tuni. Yan biyu ne su. Aure nake son ‘k’arawa saboda inason yara. Ilyasu yace min bakida tsayayye na aure. Nace toh ni nasan ba zaki kini ba. Akwai abinci agidah na sosai yammata. Domin ni dan kasuwa ne ina da tafkeken shago a layin mu, Sannan ina kiwo. Zaki sha shayi da burodi a gidah na da bota, Akwai shinkafa yar gwamnati da cous-cous. Kinsan cous-cous? Kin tab’aci?”

Daria ya bani wallahi, Yadda ya zage yana zayyano irin cimar gidan sa. Ko ta hakan aganin sa shine cinyewa oho?Wai cous-cous zai tambaye ni. Girgixa masa kayi na alamun bansani ba. Ai kuwa ya shiga zayyono bayanin cous cous yana fadar yadda akeyin sa da dafa shi, Sai sharara karya yake yi. Gaba d’aya nagaji da surutan sa. Na rufe hammar data tahomin ina kade hijabi na saboda guggun saurayen dake cinye mun naman kafafu na.

“Toh Zahra’u amshi nan kiji. zaki dinga cin cimar yan gayu, Ciki harda bombita da madarar ruwa. Da komfules.”

“Allah sarki...”

Na bashi amsa ina sakin wata hammar. Wallahi nagaji.

“Yauwa amshi nan nayi karatu naje har matakin sakandire. Anan na hab’aka a harkar kasuwanci. Kin ‘kare sakandire kuwa?”

Tari na shiga yi da alamun tambayoyin nasa sun ishi mak’ogoro na.

“Alhaji nayi karatu sosai.”

“Amshi nan. Diba! Sakandire ko iya karamin aji?”

“Jami’a n...”

Gwalalo idanuwa yai yana sarqafe hannuwa a kirjin sa,

“Jami’a fa kika ce? Ke zahrau amshi nan. Fadamin gaskia.”

“Alhaji dagaske nayi har matakin digiri na bi..”

“Digiri?”

Ya sake maimatawa cike da mamaki. Yasa hannu ya naushi bango yana cizan yatsa. Lokaci zuwa lokaci yakan nanata,

“Ilyasu ya cuce ni.”

Na karkad’e saurayen dake bina ina sakin wata hammar a karo na ba adadi.

“Amshi nan zaharau, Diba. Kirawo min ilyasu yanzu.”

Kada Kai nayi cike da murna na shige gidah ina murmushin Allah ya raba ni da alaqa-qai cikin sauki. Kofar parlorn Kawu ila na tsaya. Yana zaune a tsakiya yaran sa sun zagaye shi yana karkasa kullin tsire. Yana gani na ya tukwikwiye takardar naman ya dora hular sa akai.

“Ya akai? Kin taho fankan-fankan kin tsaya min akai?”

“Ca yai kaje.”

“Ayyo to! Kun gama kenan?”

Daga kai nayi shi kuma ya zura yar sharar rigar sa yana lashe hannu. Zauren ya nufa,

“Alhaji ashe har kun gama?”

Ina jiyo muryar Alhajin yana rufe Kawu ila da bambamin masifa. Kawu ila sai kwararo rantsuwa yake yana wallacewa,

“Akwai su kala kala agidan nan. Sai a samo maka wata ai..”

“Ai ba haka mu kai da kai ba. Yanzu dai dakkomin kudade na dana babbaka. Da rabin gonar da na yanka ma duk dawomin da su.”

Kawu ila ya zube a kasa yana hada hannu alamun ban hak’uri,

“Alhaji kayi hak’uri dan Allah. Ka yafemin, Wallahi gonar nan tuni na sayar. Kudaden kuma na sissiyo ka..”

“Karya kake yi mutumin banza da wofi. Diba nan! Na baka kwana ki uku rak ka tattaro min duk abunda na baka ka dawomin dashi.”

Alhaji na gama magana ya fice yana kade wa Kawu ila riga a fuska. Kawu ila ya shiga tambotsewa yana rigingine kamar bal a zaure. Yaran gidan mu suka taru akan sa. Bintalo da shigowar ta kenan Itada Ruma taja ta tsaya tana kallon Kawu ila,

“Meye haka ilyasu?”

Kawu ila bai ce mata kanzil ba sai ma bige-bigen kansa da yake gwarawa a bango duk ya fara fashewa yana jini.

“Wayyo Allah na! Wallahi sai na biya shi. Ina zan gan su?”

“Ilyasu su wa zaka gani? Ko aljanu ka samu ne? Oh ni Bintalo.”

Kawu ila ya cigaba da birgima yana ife-ife. Meya tuna oho? Yai parlorn sa da gudu yana leken yaran sa,

“Kada wanda ya dauki naman nan. Zan raunata mutum idan naga ba d’aya. Domin na irge su kafin na fita.”

Baba usaiba ta kyalkyale da dariya tana tafa hannaye,

“A hayye kayya kai? Kaji da abunda ya dame ka amman hankalin ka na kan nama?”

Ya wurga mata harara. Sannan ya kara runtumawa zaure yana kururuwa. Bintalo ta ja tsaki tana janye da hannun Ruma,

“Zo mu tafi Ruma. Sittin ta ubangiji dadi ne yai masa yawa..”

Sama sukai hayewar su. Hannun Ruma dauke da leda. Da alamun kudin adashen ne Bintalo zata ajiye. Girgiza kai nayi zan haye sama Kawu ila ya kirawo ni yana sharce gumi,

“Uban uban me kika fadawa Alhaji Usman ya janye neman auren ki? Wato bakin ciki kike min ko? Zan samu alkhairi a wajen sa shine kikasan makircin da kika kitsa yace ya fasa?”

“Kawu bance masa komai ba wallahi. Lapia muka rabu.”

Dogon tsaki yaja yana kwak’ular hanci,

“Rantamin kudi.”

“Ba ni dasu.”

“Karya kike yi.”

“Babu Kawu. Bani dasu.”

Tsaki yaja ya gyara zaman rigar sa hade da zura takalmin sa ya fice yana banbamin mita. Ni kuwa sama na haye ina mai kaiwa Innar mu korafin Kawu ila,

“Wallahi nagaji Innar mu. Wai shin mena tsarewa Kawu ila? Nima dan babu yadda zanyi ne. Mutum baya janyo lokacin sa. Babu wani nagari dake zuwa fyace Kawu ila ya kore su. Allah Innar mu mutumin yau ma baki ganshi ba. Allah ya rufa asiri ma bayason me zurfin karatu. Don tinda ya tambaye ni gurbin karatu na na fada naga ya canza fuska.”

Innar mu taja ajiyar zucia ta sauke tana murmushi,

“Toh adai yi hak’uri me sunan uwa. Duk ma abinda ya miki ai dan ya isa ne ko?Ilyasu uba ne awajen ku. Ballantana yanzu da babu ran mahaifin ku. Duk inda zakije ki zaga ki dawo su dinnan dai su ne iyayen ki. Saboda haka ki cigaba da addua. IN SHA ALLAH ke da duk masu nema Allah zai baku mazajen kwarai. Tabbas mutum baya janyo lokacin sa. Komi lokaci ne da mutuwa da haihuwa da aure duk tare suke. Fata dai Allah ya zaba muku abunda yafi alkhairi kawai. Kina jina?”

Daga kai nayi ina goge hawayen dake zirara a idanu na. Fisabilillahi banda Haysam ba wani wanda yake sona tsakani da Allah. Shi kuma Haysam mahaifiyar sa bata so na. Bama wannan ba wutsiyar rakumi tayi nesa da ‘kasa. Dai-dai ruwa dai-dai tsaki. Cikin haka Yayan mu ya shigo inda yake tambayar abunda ya sani kuka, Innar mu ta gaya masa. Suka hadu su kai tabani baki. Gaskia daren ranar naci kuka sosai. Anan Yayan mu yake shaida mana cewar baban su Fadila ya bashi damar ya turo manyan sa ayi magana. Sosai na yiwa Fadila farin ciki. Nima ina fatan Allah ya kawo wanda zai zo neman aure na. Muradin zucia ta. Daren ranar kuwa nayi sallar nafilfili inda nai kuka sosai a sujood ina gayawa ALLAH bukatu na. Hade da neman mafificin alkhairin sa.

*ABU*

Da wuri ya shirya ranar saboda suna da lecture d'in ta. Ya riga kowa zuwa hall d'in ya zauna ya dan tab'a karatu kafin daga bisani ya mike ya nufi inda zai dinga hangenta idan ta shigo makarantar. Ko minti talatin beyi ba sai gata tana fitowa daga napep domin har ciki ya kai ta kusa da office d'inta. Kudi ta zaro ta bawa mai napep din ita kuma ta bude office ta shiga dan ajiye wasu takardu dake hannunta. Mubeen da tun sanda ya dora idanunsa akan ta ya dan ja tsaki, saboda sam ba tayi kala da wadda za'a ce an ajiye a napep ba, kasan cewarta kalar wayayyu. Ya mike tsaye tare da gyara rigar dake jikinsa, kamshin turaren jikinsa sai bugun hancinan 'yan mata da samarin dake kusa da yake.

Sai da yaga ta fito sannan ya nufi hall d'in yana murmushi dan ba karamin kyau ta sake yi mishi ba a lokacin. Sanye take cikin wata atamfa kalar coffee da ratsin fulawoyi ruwan madara, hakan ne yasa tayi amfani da milk d'in mayafi, sai dai jakarta baka wacce ita ce dai take kare yawa da duk kalar kayan da tasa, sai takalmi baki shima. Cikin nutsuwa take tafiya har ta karasa inda zata yi lecture, students suka gaida ita, Mubeen ya gyara zama yana kuma karewa hallitar ta kallo.

Gyaran murya nayi sannan nayi musu kallo d'aya gabaki d'ayan su, naga lallai sunzo da yawa. Sai nayi murmushi ba tare da na kallesu ba idanuna ma yana kan handout d'in da nake bud'ewa nace dasu.

“Kowa ya yago paper ya rubuta reg number d'insa kar wanda yasa suna, zamu yi test.”

Nan da nan d'aliban suka hautsena hall din da surutu, wasu na cewa basu shirya ba yayin da wasu suke cewa amman dai open test ce, wasu kuma suna cewa ayi sun shirya. Idanuna ne suka fara zagaye d'aliban fuskata cike da fara'a, can suka sauka akan Mubeen wanda ya yi tagumi ya zuba min na mujiya kamar wanda aka dankwafar a gurin. Marker na dauka nasa kasanta ina bubbuga desk d'in dake gabana alamun suyi shiru. Da kyar suka yi saboda kowa da abinda yake cewa, na kuma tabbatar musu da cewa test zanyi koda sun shirya koda basu shirya ba, domin kullum idan muka gama darasi na yi tambaya cewa suke min sun fahimta.

Questions na karanto musu sannan na koma gefe ina kallansu one by one. Sai da na basu lokaci isashe suka kammala sannan na kalli Mubeen dake zaune a gaba yana cizon kasan biron shi, idanuwansa a kaina, dan na tsaida hakan sai nace dashi.

“You..!”

Amman takaicin yasan dashi nake amman sai yaki koda motsawa, kuma idanunsa suna kaina amman d'an rainin hankalin baiko kifta ido ba bare na tabbatar yaga sanda nake nuna shi.

“Heyyy you..! What's your name?”

Yaron nan yayi shiru har sai da ta gefensa ta tab'a kafad'arsa da biron ta, sannan ya d'an kalleta. Murmushi ta sakar mishi dan tun zamanta a wajan taga yaki koda kallon ta, sannan ta yi masa nuni dani tace.

“Ana maka magana.”

Mubeen kenan, maimakon ya kalle ni, sai kawai ya fara waige-waige shi adole bai san daga ina ake kiransa saba. Karaf kuwa muka sake had'a ido na watsa masa hararar ka rainawa kanka hankali, sai kuma naga wannan ta kusa dashi d'in tana kuma yi masa magana tana nuna masa ni, sannan ne ya taso yazo gurina.

“Kaje ka tattaro min papers d'in ka kawo min.”

Nayi maganar ina bude wani littafi dake hannuna ba tare da na ko kallesa ba, ya sunkuyar da kai k'asa alamar to ya juya yana murmushi. Ashe hakan da nayi ba karamin dad'i yasa shi ba, ni kuma nayi masa hakan ne dan na takura masa nasan irin wannan yaran basu fiye son ana shiga harkar su a irin wannan abubuwan ba. Sai da yaje ya karb'o su tas sannan ya kawo min, ban karba ba na fara kwashe kayana ina sawa cikin jaka, na juya zan tafi nace dashi.

“Biyo ni dasu office.”

Wani shegen murmushi ya saki wanda har sai da fararan hakoransa suka bayyana a waje, sauran students da suke kallansa aka fara mamakin sa ganin wa yake yiwa wannan murmushi da basu tab'a gani ba a fuskarsa. Bayan ta yabi da ta cire kafarta zai dora tashi akan sahun takalminta, tana tafiya tana waya da Yaya Najeeb inda yake ce mata zasu tafi kaduna yanzu shida Inna duba gwaggo Aminatu wacce aka yo musu waya d'azu aka sanar musu ruwan zafi ya kwarar mata a k'afa duk ta sale suna ma asibiti. Yana jin yadda take wayar cike da damuwa, har suka karasa cikin office d'in.

Sai da na zauna akan kujera ta sannan na mik'a masa hannu alamun ya mik'o min takardun sai naga ya kawar da kansa gefe.

“Bani mana.”

Daman so yake ya kuma jin murya ta kuma yaji, hakan yasa ya miko min, na karba sai naga yana shirin jan kujera ya zauna. Na had'e rai fuskata babu alamun fara'a nace dashi.

“Tashi ka tafi na gode”

Kamar ba zai mik'e ba sai kuma ya tashi ya fara tafiya, yau ma sai da yaje har ya bude k'ofar ya waigo, nima kamar an d'ago da tawa fuskar dan ba'a san raina hakan ya faru ba, sai muka had'a ido ya sakar min murmushi wanda ya kara kona min rai dan naga alamun yaron ya yi bala'in rai na ni. Fita ya yi ni kuma na mai da kwayar idona kan papers d'in ina karanta ta farko wacce ke daga sama, ashe tashi ce ya dora ni kam ban sani ba kasan cewar ba sunayen su bane. Ina karantawa ina jin dad'in ganin yadda mai ita ya tsarge duk tambayoyin da nayi, musu. Haka na fara dubasu tun a office babu laifi sunci da yawa, na ware mutane goma da suka cinye duka da nufin idan zan mai da musu zan yabe su sosai.

Koda lokacin tafiya ta yayi na fito na tafi dan nasa a raina ba zan koma shiga lift ba ganin yadda yaron nan ya yi min kwanaki.

Bayan sati d'aya da na koma yi musu lecture, kafin mu fara sai na ki dawo registration numbers d'in d'in mutane goman dana ware, abin mamaki kiran farko da nayi sai naga Mubeen ya fito. Na kallesa na kalli paper d'insa ganin ashe shine mai wannan had'add'an rubutun, na mik'a masa yasa hannu zai karb'a yatsunsa da nawa suka hadu sai naga yayi saurin lumshe idanunsa. Sakar masa nayi ganin yaki rikewa sosai, aikuwa ta fad'i kasa amman yaki ya bud'e idon bare ya d'auka. A raina na fara zargin anya yaron nan ba d'an iska bane? Kafin na kuma kallonsa lokacin ya bud'e idon shi wanda ya soma canza kala, kwayar idansa sun tara ruwa kamar wanda yake shirin yin kuka.

“Why Ma'am?!”

“Pardon?”

Nima na mayar masa da tambayar domin ban gane abinda yake cewa why ba. Takardar yabi da kallo kafin ya sunkuya ya d'auka yana bin good d'in da nayi masa a jikin paper da kallo. A kirji naga ya dora takardar sannan ya juya ya koma gurin zamansa. Babu laifi yaron akwai nutsuwa, komai nashi a hankali yake yinsa tamkar wani mace. Ni kuma naci gaba da kiran sauran ina basu har na gama, ragowar kuma na kira monitor na bashi nace ya tabbatar ya bawa kowa kar wani yazo yace min baiga tashi ba. Nayi musu lecture na tafi abu na, domin yanzu ni kaina ina jin dad'in yadda nake koyar dasu kuma suke fahimta harma basa son lokacin tafiya ta yayi.

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*33*

*NANA HAFSAT*

Ranar lahadi wajan karfe goma na gama shiryawa zanje saloon, su Innar mu kuma suna ta shiri zasu je kuma duba gwaggo Aminatu kasan cewar ranar da tayi kunar da suka je basu samu ganinta ba asibitin basa bari a shiga a lokacin. Yau duk suke saka ran suwa duba ta, na yiwa Inna adawo lafiya nace tayi mata sannu sai nazo, na kama hannun Autar mu da zata min rakiya muka tafi. Ashe bayan fitar mu Yaya Najeebu ya taro musu mota bus zasu yi shata su tafi, sai duk aka taru a tsakar gidan mu. Kawu Ila ya karka ce kai yana cewa.

“Ke Kaltume ai banda ke aka lissafa za'aje, dan haka sai kiyi hakuri ki koma tunda an dauki Najeebu a d'akin ki.”

Maganar ta bawa Innar mu haushi ganin ai ba a bayansa zata je ba, kuma kudin mota bashi zai biya mata ba bare ya hanata yin abinda ranta yake so. Ranta a bace itama ta kawar da kai tace masa.

“Zuwa kuwa ko a taya sai naje, idan Najeebu yaje wannan ra'ayinsa ne. Yanzu kuma ni nake son zuwa dan haka babu mai hanani tunda nima ban hana wani ba”

“Iyeeeeh! Lallai ma Kaltume ni kike gyarawa cewa babu wanda ya isa ya hanaki? Ni zaki nunawa cewar komai kike yi gaban kanki ne baki da mashawarci? Yayi kyau, duk laifin mu ne da har muka barki a cikin gidan nan duk kika raina mu. Toh kuwa babu inda zakije kinji na gaya miki”

Innar mu ta yi murmushi mai kona zuciyar wanda yasan dashi ake, sannan ta girgiza kai tace.

“Toh naji ba zanje ba sai kun dawo. Kai Yayan su ka biyo ni d'aki zan aike ka wani guri.”

Innar mu na kaiwa nan ta koma sama sam bata bari maganar kawu ila ta zauna a cikin zuciyarta ba, tana barin wajan Yayan muzo zai bi bayanta kawu ila ya yi saurin janyo masa riga. Kallo ya watsa masa ba ina zaka? Cikin kumfar baki yace dashi.

“Ka dai gama biyan mai motar kud'in ko?”

“Kawu wane kud'in?”

“Kai kaji min yaro da wata tambaya. Kudin mota mana da zai kai mu gidan gwaggon taku, mu nan duk kai muke jira ka biya mana mu tafi.”

Zaro ido Yaya Najeebu yayi yana kallan jama'ar gurin da suke jiransa ya biya musu kud'in mota shi kadai sai kace wani don. Girgiza kai ya shiga yi domin duka kudin dake aljihunsa naira dubu uku ne, idan ya kwashe ya basu ya zai yi? Gashi bai san kiran da Inna take masa ba, dan haka yace.

“Kawu bani da isassun kud'in da zan iya biyawa kowa, sai dai kai da kawu khamis na biya muku.”

“Toh shikenan su sauran kowa ya biya idan yana son zuwa.”

“Ahayye nanaye kai, yau kuji min Ilayasu da wani batu. Wato kai tunda an biya maka shine harda saurin cewa mu kar a biya mana ko? Toh bani da kudi na fasa zuwa ai daman kara zanyi muku naje dubata.”

Cewar Bintalo tana buga tsakiyar zaninta tare da juyawa ta koma d'aki tana jefar da mayafi. Nan da nan duk wad'an da ba'a biya musu ba suka ce sun fasa zuwa duba gwaggo Aminatu. Yayan mu ya tab'e baki ya haye sama bayan ya bawa kawu ila dari biyar ya bawa kawu khamis dari biyar. Kawu Dawood daman ba dashi za'a je ba saboda tun asali da aka ce za'a yi tafiyar cewa yayi bashi da lafiya, yana zaune a k'ofar d'aki yana hangen bidirin da ake yi.

“Karda Allah yasa kuje d'an matsiya ta, idan itace ai bata duba alak'a zuwa take yi kowa yaci darajar masu daraja wato iyayen mu. Khamisu zo mu tafi bar shegu mu zamuje.”

Kawu ila ya fad'a yana jan numfashi tare da yin hanyar k'ofar gida.

“Zan biyawa Babar

Please Login or Register in order to submit comment