Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina son ki Fateemah na! So mai tsanani..”

Messages din na karanta guda biyu a jere da suka shigo d’aya bayan d’aya. Murmushi nai lokacin dana kammala karantawa. A office din dean nace driver ya faka. Na shiga ciki! Muka gaggaysa sannan na bashi letar kamar yadda su kayi da papa ta waya. Theatre na shiga wajen dalibai na nada. Ina shiga suka hau ihu suna gaida ni. Tsayawa nai akan podium ina a’amsa gaisuwar su. Na shiga basu shawarwari akan yadda zasu kare jamia lapia, Su kuma tsaya su fuskanci karatun su don su cinma burikan su na rayuwa.

Ina tsaye ina kwarara bayani sai ga Mubeen ya shigo sanye cikin bakin gilashi. Cikin takama ya shiga hawa kan stage din da nake hannuwan sa zube cikin aljihun sa. Dama dagaske zuwan zai yi kamar yadda ya fad’a a sako. Dai daita nutsuwar sa yai yana kallon daliban,

“Afuwan daliban mu! Ku danyi hak’uri zan tafi da wholeworld dina yanzu ba sai anjima...”

Tamkar kasa ta tsaye haka na ji wallahi. Na tsuke fuska Ina nonnokewa hakan be hanashi zuwa waje na ba ya rikemin hannu, Bakin sa akan kunne na ya shiga radamin,

“Zo mu tafi... Kafin nayi abunda bakyaso. Allah zaki k’arba hukunci.”

Hannun sa yasa yana janyo nawa na shiiga tirjewa. Mubeen yaja ni da karfin gaske mu ka fara tafiya zamu sauka daga matattakalar, Daliban suka zuba mana idanu suna kallon ikon Allah. Ganin yadda nake bata masa lokaci ya tattare hannu ya dauke ni gaba d’aya, daliban suka sa ihu suna murna. Ni kuwa kunya ce ta gama yagalgala ni. Danma Allah ya temaka ni na dena koyar dasu. Office dina ya kai ni ya dire ni yana gumi nai murmushi Ina yamutsa fuska,

“Meye haka stud muffin? A makarantar ma?”

“A ko’ina ma! Meyasa kika ki replying messages dina. Kinsan yadda na damu kuwa?”

“Afuwan..”

Riga ta ya daga yana saka kunnen sa aciki na,

“Hello little munchkin! Itzz dadda! Ina fatan kina lapia? Daddy loves you more than just to the moon round and back....”

“Wai bawan Allah waya ce maka mace zan haifa?”

“Love kenan! Ni mace nakeso me kama dake.. you and mini you ba. Ina sonku Fateemah na.. zan so ku har karshen numfashi na.”

Yana gama magana ya hade bakunan mu.. Na zare nawa ina kallon idanun sa da suka sauya launi... A hankali na kamo kumatun sa ina bashi sumba ta gefen kumatu, Hade dasa hannu na d’aya na lotsa dimple dinsa. Na sake sakar masa wani kiss din akan bakin sa. Hannu na d’aya nasa ina shafa kwantaccen sajen sa,

“Hasken idanu na! annurin rai na. Miji na, uban ‘ya’ya na. Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a a duniya.miji na abun alfahari na! Kayi fatali da shirme na na baya, Domin tuni na sakko daga *IGIYAR ZATON* duk wasu abubuwa dana aikata maka a baya. Na kanji kunya a duk sanda na tuno. A yanzu na gama hawa *IGIYAR* kaunar ka, kabar *ZATON* bana kaunar ka stud muffin! Wallahi kai ne nake gani na ji sanyi a zuciya ta miji na,

“Kasan Ina fatan kana nan lafiya yanzu haka miji na? Gani nan zaune a tare da kai amman zuciya ta tana tare da kai acikin bargon jikin ka. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina son ka kuma har gaban abadan bazan dena ba. Ina son ka. Ka kula min da kanka a koda yaushe..Please let me know what I did to deserve you… ?A kullum ina...Mai godewa Allah daya azurta ni da samun ka a matsayin miji na. Kafini a komai, kyau, kudi, asali, addini, dattako, mu’amalat.. on and on and on! Na gama hawa *IGIYAR* kaunar ka! Bansan wane irin kauna nake maka ba stud muffin! Kaci nickname dinka you are sexually attractive. Tabbas shekaru shirme ne ada nayi haukan sai wanda ya girme mini sosai, Bansan ba anan take ba. Sai gashi na samu gurbin da ya maye min fiye da tunani na. Ina kaunar ka stud muffin. Ni kam na gama sa’a a rayuwa da samun dalibi na. Tsaran haihuwa na, Wanda ya zamto malami na a yanzu.. Me koyamin ehh! I just can’t love you less baby!,

“I look at you and the world disappears. Nothing matters when I'm with you. Your heart beats in mine and mine in yours. Ours is an unending circle of love. A chord that cannot be broken. I love you so much my darling hubba bubba, Stud muffin, Babyn baby.”

Ina gamawa na tashi na koma cinyar sa ina hade bakin mu. Wannan karon ni ce na shiga tsumar da mutumin ku, Har ta kaiga an raya sunnah a ofishina. Muna gamawa muka kwashe yan kayayyakin da zan diba muka tafi bayan na bawa masinja mukullin su...

*NOVEMBER 30*

Tunda asuba na tashi na gyara daki na sannan na gyara na Mubeen, na yi duk abinda zanyi. Sam naji bana son zama ina son nayi aiki mai kazar-kazar hakan yasa na kwaso kayan baccin mu da underwears na shiga wankewa a bathroom saboda karma a hanani yi. Ina gamawa na shanya su sannan na koma kitchen, ma'aikatan gidan suna ta min sannu tare da tambayar me nake so nace musu danwake zanyi kuma bana so su taya ni. Haka aka yi suka bar ni nayi abuna na zuba na koma daki naci, ina gamawa na shiga wanka nayo tare da zura doguwar riga nabi lafiyar gado.

Kamar ance na rufe ido ina rufewa nayi saurin budewa saboda jin da nayi bayana ya rike sosai, na cije lips tare da mikewa zaune. Yadda naji babyn cikin ya dungule guri guda kamar zai fasa cikin ya fito shine ya daga min hankali, na rintsa ido ina salati kafin na sakko daga kan gadon na fito. Dakin Mubeen na shiga na tarar dashi yana duba wasu files da Papa ya bashi na wata kwangila, yana ganina ya tashi yana tambayar.

“Lafiya kuwa?”

“Ban sani ba nima kawai naji na kasa kwanciya kuma bayana ya rike.”

“Subahanallahi bari na kira Mammah.”

“A'a gaskiya ka zauna kayi min tofi a ruwa nasha.”

Kafin ya yi magana na saki wata kara kawai sai muka ga wani ruwa yana fitowa ta kasa na, gaba daya hankalin mu ya tashi. Karaurawar dakin ya danna kafin kace mene sai ga su Mammah dasu Jannat sun shigo.

“Mammah please ki taimaka karta mutu, wannan abun menene yake zubowa na shiga uku! my Fikre.”

LKai yi mana shiru haihuwa ce tazo, oya muje a kaita asibiti”

Kafin kuce mene tuni an kai ni asibiti nan kusa ne a cikin gidan gwamnatin. Muna shiga ina kwanciya akan gado Allah ya fito min da kyakkyawar baby girl fara tas da ita kamar balarabiya. Kamar su d’aya da Mubeen tamkar yayi kaki ya tofar.

Mubeen kuwa tunda yaga ruwan faya din nan ya fara sambatu yana ririko mutane, da kyar Mammah tasa ya nutsu tace ya zauna ya yi min addu'a, kukan jaririyar da yaji ne yasa shi mekewa da sauri ya nufu cikin dakin yana kalle-kalle. Daidai lokacin da aka yanke cibiya. Yana zuwa kaina ya nufa yana tambaya ta me nake ji na kada masa kai alamun babu komai sannan ya rungume ni lokacin ne nurse take cewa.

“An samu baby girl.”

“Da gaske?”

Ya tambaya cikin zumudi.

“Ranka ya dade ai kayi saurin shigowa shi yasa baka gane me aka haifa ba, daka jira an kawo maka ita cikin shawul”

Cewar nurse Hajara tana faman goge babyn da zaitun.

“Alhamdulillahi my Fikre kin gama min komai a duniya, tukwicinki shine motar da aka kawo gidan nan shekaran jiya.”

Da sauri nurse Hajara tace.

“Ahhhh yallabai nifa mai karbar haihuwar mene nawa tukwicin?”

Mubeen ya zara wayarsa ya mika mata tare da cewa.

“Ki ciro min sims din sai ki rike phone d'in.”

Tasa hannu ta karbe tana rawa tana ci gaba da goge yarinyar.

“Mubeen ba zaka fito bane?”

cewar Mammah tana daga reception.
Mubeen yaki fita har sai da aka gama gyara mu tsab sannan aka cewa su Mamma su shigo. Hararar sa tayi tare da cewa.

“Ko kunya.”

Yayi murmushi kawai yana rike da jaririyar.

“Kayi mata huduba?”

“A'a Mammah ai yanzu suka bani bab

“Toh oya yi mata.”

Ya kara bakin sa kusa da kunnan ta ya yi tare da to feta da addu'a, su Jannat suka fara tambayar sa ya sunan babyn yace ba zasu ji ba sai ranar suna.
Aka yi ta dariya ni kam na kagu naga an kira Innar mu an gaya mata, kamar Mubeen ya sani sai ya dakko wayata dake aljihunsa ya kira Innar mu ya sanar da ita tana ta mana fatan alkairi. Bamu dade ba muka koma sashen mu nayi masa zancen komawa gida wanka bawan Allahn nan ya hana kamar zanyi kuka sai dai na daure. Murna a gurin family d'in shi da nawa ba'a magana, papa kuwa dankareren gida ya bamu a Abuja yace idan na gama wanka zamu tafi can nida mijina.

Zo ku ga ƴan gidan mu a gidan gwamnati, gabaki d'aya sune yan kauye inda Allah ya temakeni basu yi musu kyara ba sai ma dariya da suka dinga sanya su. Nayi murmushi tare da lankwasa kai ganin babu Kawu Ila da Bintalo wanda zan so ace sunga irin gidan da nake ciki da irin mijin da nake aure da irin rayuwar da nake ciki. Sai dai shi Allah baya barin wani dan wani, gashi duk ya hana su ganin irin rayuwar da zanyi wacce basu so ba.

Ranar suna baby taci sunanta Nana Hafsatu muna kiranta da Liya da Ethiopian. anci ansha anyi almubazzaranci yan gidan mata tara sun kwashi banza su Zabbau kuwa abin ba'a magana, Innar mu sai da muka yi arba’in muka je gidan sannan taga baby.

ABUJA
(2020)

“Ashe da rai nake sonki jaruma bada zuciya ta ba! Komai ruwa da iska akanki baza na dai na kewa ba!
Idan na samu zarar samun ki baza na tanka kowa ba! Ni banga mai harara ba bare na wai ya ah🎶🎵

“Indai akanki ne zana jure wahalar zuwa garin nisa, Da an tabaki a jirani dan kuwa tilas nazo na dau fansa, Jumurin jiranki nai dan kizo na kalleki gimbiyar Hausa! Sirri na rayuwata kece kawai da kin kira dana amsa, Zuma a baki dadi gare ta kin bani taki na lasa!
Indai a kanki ne nayi nisa dan ba kiran da zan amsa! Tilas ganin mu tilas barin mu! kaunar ki tunda nayi nisa!
Sam ba batun na fasa ko za'a ce mun in bada rai fansa, 🎶🎶

“Tsarin zubinki dai dai ne....
Ya kama zuciya ta ne.....
Ina jin kamar mafarki ne...........
Ena sonki so mataki ne. Fateemah na! Zawjati! Fikre.. Ayana! My wholeworld🎶🎵

Murmushi nai ina kallon sa, Bansan wane irin so nake masa ba wallahi, Ya zage sai wakar yake min yana lumshe idanu hade damin blowing kiss daga tsayen da yake. Zip din gaban rigata na zuge dana gama bawa baby Liya mama. Na dube shi ina tallabe habar sa,

“Ina sonka Stud-muffin! Ina kaunar ka.. Kaunar ka tagama bin ilahirin jini na da tsoka!..”

“Sssh ina kaunar ki fiye da komai! Zawjati! Bansan wane irin so nake miki na. Domin ahar kullum bana kaunar ranar da zata rabamu idan ba mutuwa ba, So kiyi hak’uri da rashin hanaki fita da nake yi. Wallahi bazan iya jure rashin ki a kusa dani ba..”

Yana gama fad’a ya rufe bakin mu. Hade dasa hannun sa d’aya ya shiga shafa kitson kai na,

“I don’t think you understand, exactly, how much I want your lips. Fateemah na! Lips dinki har wani taste suke kaman ice cream!”

“Uhm naki wayon ni dai....”

“La baki sani ba? Ai Kissing burns 6.4 calories a minute. Wanna workout?”

“A’a daddy.. Yanzu time din Liyaa time ne.”

“Ahhh smooching time ne!”

“Dan Allah kayi hakuri! Ka tashi na bata..”

“Wai ke bazaki dena kunyar nan ba uhm?! Naga jia da dare a tare kika bamu da ita.. Kuma fa nace na daman shi ne na...”

Rufe kunnuwa na nayi ina rintse idanu, Domin gaba d’aya Mubeen baida ta ido a irin maganganun yin su kawai yake a ko’ina! Murmushi yai yana tallafo kafadata ya jingina ni a jikin sa,

“Dear wife, You fill all my emptiness with your endless love. I’m so thankful to have you as my wife. I love you very much!The perfect decision of my life was marrying you. I am lucky to have you as my life partner ..”

“Ana uhibbuka zawj! I love you more than life itself! The more time goes by, the more I learn new things to love about you. You are the most amazing hubby to me. I love you and I always will...”

“Kiji dani.... Ki tausayamin..”

“Daddy ba..”

“Ni wallahi kidena cemin daddy! Stud-muffin din dai...”

Ya yi murmushi tare da matsoni a jikinsa yana shafa kan baby Liyaa💝!

••
“Ban samu na fara business d'in ba sai maganar Corona ta shigo hakan yasa Papa yace na dakata komai ya lafa sannan sai na fara, shima Mubeen sai zaman gida ya kamashi mai makon soyayya ta ragu kamar yadda mata suke kukan cewar suna samun matsala da mazajen su a gare mu kam sai masha Allah kauna taci gaba da wanzuwa tsakanin mu da Mubeen.,

“ *IGIYAR ZATO* tasa na dauki abubuwa ba yadda suke ba, ZATO ko wane iri ne bashi da kyau dan haka ni Batoul na sakko daga IGIYAR ZATON cewar ba zan iya auran wanda bai min ba, ko wanda bai girmemin ba tunda gashi a wannan shekarar 2020 zamu yi 30years nida mijina Muhammad Mubeen abin alfahari na, zabin iyaye na ya zame min alkairi a cikin rayuwa ta. Xoxolious ko na nuna muku shi?"

Na sunkuyar da kai tare da cewa.

“Eh ranki ya dade.”

Tayi murmushi tare da cewa.

"LNo ki bari sai randa kika dawo ke kadai zan nuna miki shi.”

Duk muka yi dariya tare da yi mata godiya da bata lokaci da tayi wajan bamu tarihin rayuwarta....

_*TAMMAT BI HAMDULILLAH_*


_Love is patient love is kind it does not envy it does not boast its not proud it does not dishonor others,it is not self seeking,it is not easily angered it keeps no record of wrongs,Love does not delight in evil but rejoice with the truth,it always protects,always trusts,always hopes,always perseveres#IGIYAR ZATO (ETERNAL LOVE 2020)_


_Godia ta tabbata ga ALLAH ubangijin talikai, mamallakin kowa da komai, Ahadun samadun. Domin shi din mubuwayi ne gagara misali. Toh komai yai farko zai yi k’arshe, duka-duka anan ni Nana Hafsatu nakawo k’arashen littafina me suna a sama😊kun san shi d’an Adam ajizi ne tara yake be cika goma ba, duk wanda nabatawa rai farawar littafinnan zuwa k’arshensa ina neman yafiyarsa..Ina fatan dan fadakarwar dake ciki Allah yasa mu amfana da ita, kurakuren ciki rabbi yafe mana baki d’aya.._


_First of all I wanted to thank each and everyone of you reading this, thank you for reading my story, thanks for the calls,messages and comments I wholeheartedly appreciate it..kusani har kullum kuna ran Nana Hafsaatu,da baxakar ku nake rawa my fans..Fatana Allah yabar mu tare.MISS XOXO na yinku beyond words😊Rabbi yabar zumunci.._

_Afuwan da akasin da aka samu na rashin kammala wannan littafi (IGIYAR ZATO) da wuri! Kunsan nayi rashin lapia kwana biyu. Lapia uwar jiki shiysa updates din ya dinga zuwar muku a hankali.. Amman Alhamdulillahi yanzu da sauki sosai! Nagode k’warai da jirana da kuka yiyyi💖💖Love you all fisabilillahi!!!_

_NAGODE KWARAI ZAFAFA 2020 FAMILY❤️ZAFAFA 5 TEAM MEMBERS😘😘_

_DA MA DAUKACIN MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR2020😍JAZAKUM ALLAHU BIL JANNAH❤️, HAKIKA KUNYI MANA *HALLACI*! NA SIYAN LITTATTAFAN MU DA KUKAI.. HAR GABAN ABADAN KALMOMI SUNYI KADAN WAJEN KWARARO GODIARMU GARE KU.. ALLAH YA SA KA MUKU DA ALKHAIRI 🤲🏻. _

_SANNAN DUK WANDA YA KARANTA BOOK DINNAN BAI BIYA BA YAI GAGGAWAR KOKARIN BIYA GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA🤝NERA DARI BIYU NE TA 08095215215🙏🏾SANNAN IDAN ZAFAFA BIYAR DIN DUKA KAKE SO SO NERA DARI BIYAR NE KACAL. SHIMA ZAKU NEME MU TA LAMBOBIN NAN DAKE SAMAN TALLAR MU +234 903 234 5899, KA SIYA KA KARANTA HAKKIN KA, YAFI KA KARANTA NA SHIGA HAKKIN MUTANE🤝_

_GA MASU TAMBAYAR BOOKS DIN DA NAI.. GASU KAMAR HAKA; AMMA WASU SUN BATA TUN WHATSAPP BA KALA, IDAN KUNYI KICIBUS DA WASU TO KU ANTAYO MUN SU😹._


_1-NAZNEEN_

_2-KE TAWA CE (NABEELAH)_

_3-RAYUWAR MARYAM_

_4-SO KO SHAK’UWA?_

_5-AUREN BASHI_

_6_MATSALAR RAYUWA_

_7-DR SAMEER AMEEER_

_8-DANNAR ‘KIRJI_

_9-NAUFAAL(The Charming)_

_10-UMMI A’ISHA(The Magnificent)__

_11-RANO MAI WAINAR FULAWA_

_12-WUCE MUJE(TAKU NA DAYA BIYU DA NA 3)_

_13-SON RAI KO ZAB’IN IYAYE?_

_14-SAIFUL_ISLAM._

_15-KAI MIN HALACCI._

_16-IGIYAR ZATO_

_zaku samu wasu daga cikin books dina a wattpad: missxoxo00_

_*TAKU NANA HAFSAT BINT MOMMODU HADEEE, BIL LAQNIN: MISS XOXO🧕🏼_*

_INA MASOYA MAKARANTA LITTAFIN LOBAYYAR SOYAYYAH? TO KU MATSO DOMIN NESA TAZO KUSA. TSAYA KUJI_

__Could this actually turned into something real? Shin ya zata kaya ne da zukatan masoya biyu wanda suke da banbance-banbance a tsakanin su? The class of the have and the have not??? Suraidah 'yar gidan wani babban oil tycoon ce. Muhammad Mahboub kuma d'an gidan talakawan talak ne. Shin ya zata kaya ne da qulluwar zuciyoyin wanda ba tsaran rayuwa bane ballanatana aure😮? Tab Shin ya kuke ganin wannan ruguntsumin zai kaya? Dr Falal Rabiu mai Mai wani sanannen billionaire ne wanda keda rijiyoyin mai a fad'in Najeriya, yana taimakon talakawa amma shi kam baya son talaka ya rab’e shi. Taya za’ai Muhammad Mahboub ya zamto siriki agare shi? Kai abin da kamar wuya. Mahboub *ANNURIN ZUCIYAR* Suraidah ne. Da sonshi ta rayu ya rene ta ya girmama a zuciar ta. Shin ko Suraidah zata iya bijerewa mahaifin nata? Tab! dankari Makari. Akwai cakwakiya fa, kun ta6a ganin talaka mai tsattsauran ra'ayi? Ku biyoni muje dan kuji me za'a kulla a tafiyar. Wannan labarin yasha banban da sauran rabarai na, zai ta6a zuciyoyin masu karatu, sannan zai fad'akar daku masu karatu, insha Allahu zai sanyaku nishad'i. Akwai zazzafar soyayya da kuma zazzafar kiyayya, akwai jarumtaka, sadaukarwa ta fannoni da dama, *ANNURIN ZUCIYA* daban yake a cikin sauran labarai. Domin mallakar ANNURIN ZUCIYA na marubuciyar MUSAYAR ZUCIYA (HAJJAH CE) ku tuntubi lamba kamar haka akan nera dari biyu kacal: +234 706 528 3730_

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment