Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ballantana dalibi hakan kamar toshiyar baki ce ta abubuwan makaranta. Na kalli Innar mu ta gefen ido ina daria kasa kasa,

“Innar mu bafa saurayi bane, Ina wannan yaron dan gwamnan nan. Shine zai zo ya gayshe ni.”

“Eh duk da hakan dai uwata ai shi dan Adam Allah ya karramta shi, Babu kyau wulakanci. Kuma kinga dalibin ki ne koba komai zaki samu yabo mekyau.”

“Hakane, Nayi kuskure. Bazan sake ba IN SHA ALLAH..’

Tunowa nai da dan kwalin daya bani tun kafin exams nayi. Dakko shi nayi acikin jaka ta don ganin menene. Wani siririn zobo ne mekyau dashi. A gefen kwalin daga saman sa an rubuta ‘english gold.’ Ajiye shi nayi a gefe yana zuwa zan mayar masa da kayan sa. Yaron nan bai zoba sai bayan sallar ishai na fara hamma ma zanyi bacci Bala yashigo kira na wai nayi bako. Hannuwan sa niki niki da ledoji. Zoben na dauka na sauka bayan na burma hijabi. Ko kallon fuska ta banyi ba a mudubi. Yana zaune a saman motar sa yana danna waya, Na dan daga murya ina hararar sa,

“Karaso to..”

Karasowa yayi sanye cikin kananun kaya ya rufe fuskar sa da takunkumi da alamun bayason agane shi. Ashe shiyasa ranar da yafara zuwa na ganshi dashi? Naja gefe na tsaya ina muzurai jira nake ya gayshe ni amman yaron nan ya shiga murmushi yana kallon kasa.

“Ya akai ne? Yauwa ungo zoben ka rike..”

Na karasa fada ina mika masa. Kin karba yayi yana hada hannuwa waje d’aya,

“Ayana.. Barka da dare! Yasu Ummah da baby? Naga kuna kama.”

“Lapian su lou! Yes autar mu ce. Ungo zoben mana.”

Kin karba yayi yana make kafada,

“Kyauta fa na baki Ma! Ba’a mai da hannun kyauta baya. Dan Allah kakki bani.”

“Fine! Nagode. That aside. Meya kawo ka uhm? Kai da mukayi tun d’axu zaka zo. Shine zaka zo yanzu? Ko daga zance ka biyo nan.?”

Yai saurin girgiza kansa yana murmushi, Nima murmushin nai da alamun kunya ta yake. Dan matsowa yai yana haskoni da hasken wayar sa. Na galla masa harara ina kauda fuska ta,

“Meye haka? Matsa.”

“Mah kinada kyau wallahi. TubarkAllah! Kullum kara kyau ki...”

“Ya isa haka! Kaga dare yayi. Sai da safe. Yauwa dakata na dakko maka kayan daka kawo. Wai meyasa kake hakane uhm? Ka denamin haka banso.”

Kasa-kasa yake kallo na yana jan lips sa,

“Ni baby na bawa. Kuma Ma’am dan na kawo miki abu ai ba wani abu bane ko? Nifa student dinki ne. Kuma bakyau kin amsar kyauta..”

“Toh naji.. Angode kwarai. Congrats! Naga dad dinka ya xama governor.”

Rage annurin fuskar sa yayi domin sam bayason mukamin da mahaifin sa ya samu. Shikenan yanxu mutane zasuyi nisa dashi ta k’arfi da yaji? Kad’a kai kawai naga yayi yana murmushi. Na Kalli agogon wayata kafin na kalle shi,

“Amman xaka canxa sch ko?”

Saurin girgixa kai Mubeen yayi,

“A’ah! Meyasa kikace haka Ma? Bakyaso na cigaba da schooling anan?”

“Ba kaduna zaku koma ba? Ai sai yafi maka sauki. Ka fara fresh start.”

“No ina nan IN SHA ALLAH! Bazan je koina ba Ma’am. Ko a hostel ai sai na zauna.”

Kad’a kai nayi ina jaddada karfin hali irin na sa. Yana dan gwamna yana tunanin sake zama a makarantar da ba iyayen sa a kusa.

“Ni zan koma ciki.. Sai da safe.”

Kamar zai yi kuka haka Mubeen yai raurau da idanu.

“Sai da safe Ayana.....U made my nig...”

Daga masa hannu kawai nayi na shige cikin gidah. Mubeen kuwa ya dan jima a tsaye yana dafe da saitin zuciyar sa. Kafin ya lumshe idanu ya fice zuciyar sa fal da farin cikin kasancewa da malamar tasa.. Ina shiga daki naci karo da ledojin fal. Kayan kwalam da makulashe ne shak’e aciki. Na dubi autar mu dake karatu nace,

“Innar mu na dawo.. Autar mu wai ke ya kawowa. Wash! Nagaji wallahi.”

Autar mu ta buga tsallen murna tana dudduba ledojin. Innar mu ta debar mana kafin ta karkasashi autar mu ta mimmikawa kowanne daki nasu kason.


••X••O••X••O••

*Da* wuri na tashi na kintsa, Domin an koma makaranta. Inda Allah ya temake ni ma wannan second semester din banida koyarwa sai dai guidance da kuma shigar da electives/subsidiary courses na yan level one..

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_[8/26, 8:15 PM] Miss Xoxo: 𝓘𝓖𝓘𝓨𝓐𝓡____𝓩𝓐𝓣𝓞


*39*

Kafin naje office tuni an gyara an tsaftace shi. Ina shiga school na je dean’s office dana head of department dama sauran senior lectures dina duk na gayda su. Kafin na wuce office dina. Na gyaggyara yan abubuwan da gyaran bemin ba sannan na zauna baki na dauke da addua. Sauri nake yi na gama abinda zanyi domin yau za’a kai lefen yayan mu kuma sati na gaban ne bikin. Akwatuna uku da kit yayan mu yayi ba laipi komai yayi domin yayi kokari sosae. Sosae students suka rika tururuwar shigowa office dina suna kawomin crfs (course registration form) Na shiga signing da cikewa ina duban agogon hannu na. Mikewa nai bayan na gama na shiga hada kaya na acikin jaka. A lokacin Muhammad Mubeen ya shigo yana karemin kallo. Na girgiza kai kawai na lura baya gajiya da kallo kamar tsohon maye.

“Ma!”

“Yes..”

“Tafiya zaki?”

“Eh sauri nake yi. Ajiye crf din zan duba a gidah.”

K’arasowa yai wajen table din ya ajiye yana rausayar da kai. K’amshin turaren sa ya daki hanci na.

“Barka da rana Ma..!”

“Yauwa..”

Na amsa shi ina murmushi domin inason abani girma na. Harhada komai nawa nayi na zuba a jaka ta ina ratayawa, Biyoni yai a baya yana sunkuyar da kai,

“Zan rufe office din.”

“Ma zan kai ki gidah.”

“A’a nagode.”

“Dan girman Allah kiyi ha’kuri na kai ki kinji?”

Tsaki naja na sauke Ina dankara masa harara,

“Akwai lectures uku da zakuyi nan gaba. Abeg jeka class.”

“Ma elective ne wanda za’ai yanzu kuma banayi. Na anjiman ne 2-4 shine nake yi.”

Yamutsa fuska nayi nai gaba abuna yabi ni a baya yana murmushi. Kafin na karasa motar ya bude ta a key. Nai shigewa ta baya ina hura hanci. Gaba ya shiga ya zauna ya tayar da motar. Fadilah ta kira ni awaya na daga ina murmushi,

“Amaryar mu...”

“Na’am aminis! Ya kindawo kuwa ko kina school?”

“Gani a hanya zan k’araso ISA. An kawo lefen ne?”

“Ke dalla ni wajen dinki ma nakeson muje. Ance K-boy mai dinki ya hadu da hatsari.”

“Subhan’Allah! Allah ya bashi lapia. Bara na dawo sai mu zaga ko xamu samu wanda zai mana ko?”

“Eh sai kin karaso tawan.”

“Ai agidan ku zan sauka ma kawai.”

Ina gamawa na katse. Ta mudubi na hangi mubeen yana kallo na. Harara na dankara masa ina daga wayata sama,

“Ma bikin brother dinki xa’ai ko?”

Baki bude na tsaya ina kallon sa,

“Aina kaji kai kuma?”

“A status dinki nagani.”

Ashe ban rufe shi daga ganin statuses dina ba? Shaf na manta wallahi! Dafe kai na nayi da hannu na cike da takaici. Yayi murmushi yana gyara mirror din. Ina kallon sa yana gyarashi saiti na. Ya rainani wallahi. Cikin haka kafin mu karasa unguwar mu Haysam ya kira ni na rage murya ina waya dashi kasa-kasa. Mubeen ya sake hade rae yana yamutsa fuska. Batoul kuwa hankali kwance ta gama wayar ta bayan sun zuba soyayyar su. Ta katse tana murmushi,

“Har mun karaso ashe?”

Shiru Mubeen yai yana taune kasan leben sa na kasa. Na sake maimatawa ina kallon kan titin layin mu,

“Mota zata iya shiga ta can?”

Na fada ina mai masa nuni da layin su Fadila. Gyada kai yayi kawai ya figi motar, Dai dai k’ofar gidan su Fadilah nace ya sauke ni,

“Yauwa dan albarka.. Godia nake.”

Kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yayi cikin sarqewar murya yace,

“Ba..b. ba fitowa zakuyi ba?”

“Oh wajen dinki? Ai kada ka makara kuma. Ka basshi”

“Ni nayi niyya..”

“Toh bara mu fito. Godia muke.”

Batoul na fita daga motar Mubeen ya kifa kansa a sitiyari yana lumshe idanu. Yasa hannun sa d’aya yana wargaza sumar kansa,

“Ya Rabbi...!!!”

Ba jimawa suka fito daga cikin gidan Itada Fadila da kaya fal leda. Fitowa yai daga motar da sauri ya bude musu booth. Fadilah sai kallon sa take domin bata san shi ba. Gaba batoul ta zauna Mubeen yai murmushi. Ita kuma Fadila ta zauna a baya.

“Sannu...Ina wuni..?”

Cewar mubeen. Fadilah ta amsa fuskar ta dauke da murmushi.

“Aminayas sunan sa Muhammad Mubeen dalibi na ne. Mubeen ga aminiyata Fadilah, Amaryar yayan mu.”

Gaisawa su kai shida Fadilah. Haka su kaita watangaririn neman wajen dinki. Dakyar suka samu wani Senegalese tailoring services. Mubeen ya faka suka fito suka shiga ciki. Shi kuma ya zauna akan mota yana hango su. Yana ganin sanda wani tela ya dakko tape yana gwada Batoul. Rintse idanu yayi yana cije lebe. Gaba d’aya kishi ya kama shi. Sam bayason yadda telan yake faman aune jikin ta. Kasa kasa ya shiga kallon ta yana k’are mata kallo. Ashe yadda yake kiyastata har tafi haka? Kasa jure kallon ta yayi ya koma mota ya zauna yana mita a hankali. Basu jima ba suka fito aka sauke Fadilah a makotan su, Batoul kuma ya kai ta gidah.

“Nagode Muhd Mubeen. Allah ya saka da alkhairi.”

Kad’a kai kawai Mubeen yayi yana lumshe idanu,

“Ma meyasa kika bari namiji yake daukar measurement na kayan ki.?”

Batoul ta shiga ware idanu tana masa wani kallo. Mubeen yai murmushi kawai yana sake cewa,

“Afuwan Ma.”

Ni kuwa na rasa abunda zance masa ma wallahi. Dubada yadda yaita yawo damu shiysa na danne bacin rai na ina kakaro murmushi,

“Babu komai..”

Cikin haka Yayan mu ya fito daga gida yana waya. Yana hango ni ya nufo ni yana murmushi,

“Yayan mu..”

“Na’am aminiyar mu.”

Murmushi nai ina rufe baki,

“Tun yanzu na koma kawar ka kenan. Yauwa an kai kuwa ko yana ciki?”

“A’ah yanzu dai za’a kai su Kawu ila ne ke gani..”

Sai a sannan ya kula da Mubeen dake danna wayar sa. Hannu ya bashi suka gaysa,

“Dalibi na ne.. Muhammad Mubeen. Mubeen ga babban wanmu Yaya Najibullah.”

Gaisawa suka sake yi cikin girmamawa.

“Ina zuwa Mubeen bara na dakko maka ruwa.”

Kad’a kai Mubeen yayi domin bai gaji da ganin ta ba. Shigewa nai cikin gidah da sauri domin dakko masa ruwa da lemon da Yayan mu ya dan siyo don baiwa wanda zasu kai lefen. Ina shiga na ja na tsaya don ganin yadda Kawu ila ke surfa masifa yana kwararo rantsuwa,

“Wato saboda an renani ba aganin girma na shine har za’a kai kayan shegen yaron can bansani ba sai yanzu? Dan jakar uba kuma yana gayamin wai sauri ake mutane sun taru. Uban uban wanda ya hada auren. Na soke ma babu wani aure da zeyi. Dan tsabar tsagwarar munafurci shine har an tambayo auren an gama komai za’a kai lefe amman sai yanzu zan sani? Na hada ku duka na kwashe muku albarka.”

“A hayye kayya kai! Ai kasan kai ka haife mu da zaka kwashe mana albarka ta kwasu. Billahil lazi naci biride na yage leda zan nunaka gaddi a kasa.”

Baba usaiba ta fada tana sakin gud’a. Kawu ila yasa kafa ya shure akwatin kayan yana bambamin bita. Baba Usaiba ta bishi da guda tana buga zanin ta,

“Wooo! An daiji kuma sai anyi. Billahil lazi naci biredi na yage leda.. A hayye kayya kai. Sandar ba’are kawai.”

Girgiza kai kawai nayi na haye sama. Daki na shiga na gaggaysa da yan Shema da suka zo kai lefen. Na dakko lemo da ruwa da sauri na sauka kasa wajen Mubeen. Suna tsaye shida Yayan mu suna hira na karasa,

“Batoul ashe ke harda dan gwamna kike koyarwa. Sai da na kare masa kallo nagane shi wallahi..”

Murmushi nayi kawai ina mik’awa Mubeen ruwa da lemo. Hannu na da nasa suka dauki wani shock na janye da sauri ina kallon gefe. Shi kuwa Mubeen lumshe idanu yai ya bude su a kai na yana murmushi.

“Ka tafi kada ka makara...”

Kallon agogon sa yayi yana girgiza kai,

“No zan tsaya mu kai kayan. lecturer din bada wuri yake shiga ba.”

Kad’a kai kawai nayi na koma cikin gidah abuna. Ba jimawa aka fito da akwatunan lefen Yayan mu. Yan gidan mu rankataf sun hadu za’a kai dasu ciki harda yara. Toh waya isa ya hana? Da kafa wasu su kai gaba suna hira. Akwatinan kuma aka sanya a motar abokin Yayan mu. Bintalo ta tsaya cakoko a kofar gida tana bin kowa da kallo. Saurin shigewa motar Mubeen nayi ina kara waya a kunne na. Cikin sauri Bintalo ta karaso wajen motar tana zuro kanta ta wundon hade da gaftarar goro tana ci tana magana dik ta feshe mu da ruwan goron bakin ta.

“Yar kundin uba gaba zaki yi kenan a mota? Sittin ta ubangiji ba zan dab’a a kasa ba ehe..”

Na kalle ta ina dafe kai na cike da takaicin abunda take gumamin a gaban Mubeen. Bintalo ta mai da kallon ta ga Mubeen dake danna wayar sa,

“A hayye yau ga gaye ba makilis! Aina kika samo dan bature ke kuma? Wannan yarinya da jajibe-jajiben masifa ki ke. Kai ‘dannan ka iya hausa ma kuwa?”

Mubeen da surutun ta ya ishe shi yai murmushi kawai yana mai da kansa gefe da alamun yan basarwar sun motsa kuma.

“Baba shigo muje..”

Bintalo ta sake gaftarar goro tana tattare zani tamkar wadda zata hau mashin, Haka ta shigo ciki tana zubar magana.

“Tab! Sittin ta ubangiji anyi kerarriyar mota. Wohoho anya bata yan damfara bace?”

Ni kuwa nai mata banxa ina rintse idanu na cike da takaicin yadda take ta bada ni agaban dalibi na. Haka muka karasa gidan su Fadilah Bintalo nata kwararo zance kamar ya’yan kanya. Tun Mubeen na sauraron ta har ya dena. Dakyar Bintalo ta sauka daga cikin motar tana mitar bata k’oshi ba. Sai kace abinci. Tana sauka nasa hannu zan bude naji ta rufe. Na kalli Mubeen dake kallo na shima yana sake sunkuyar da kai,

“Budemin xan fita..”

Bai cemin komai ba ya cigaba da kallo na. Ya d’au tsawon lokaci kafin ya bude yana cije kasan leben sa. Na fice da sauri ina lek’o da kai na ta kofar,

“Nagode sosae Mubeen. Allah ya maka albarka.”

Ina gama fada nai shigewa ta gidan su Fadilah. Shi kuwa Mubeen murmushi kawai ya yayi ya tashi motar ahankali ya nufi gidah bai koma makarntar ba. Zuciyar sa fes da farin cikin kasancewar su da malamar tashi...

••
ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
[8/26, 8:15 PM] Miss Xoxo: 𝓘𝓖𝓘𝓨𝓐𝓡____𝓩𝓐𝓣𝓞


*40*


Ranar jumu’ah itace ranar da za’a fara gudanar da bikin su Yayan mu. Mother’s eve shine event din da xa’ai kawai, Kafin washegari a daura aure a mika amarya gidan ta na sunnah. Tun ranar alhamis muka yi kunshin biki da gyaran kai. Na kuma yi dilke da halwa a wajen mai gyaren jikin Fadilah. Wallahi munyi kyau sosae. Tun safe muke shiri na karbo mana dinkin mu awajen tela na kaiwa Fadilah nata. Wata had’addiyar fitted gown akamin daga baya tayi tattara kamar riga da skirt. Sosae shape dina ya fita. Har naji baxan iya sata ba wallahi.

“Yaya bakyaso ne?”

Autar mu ta tambaye ni tana mai nuna rigar hannu na. Na girgiza kai ina sakin ajiyar zuciya,

“Ca fa nai yamin mekyau a saukake. Amman ya min fitted gown duk na takura wallahi.”

“Ai kuwa ya miki kyau da kika gwada Yaya.”

Kad’a kai kawai nayi na juya baya na saka kayan ina jujjuyawa. Na dubi Innar mu dake lazimi a gefe ina murmushi,

“Innar mu komai yayi?!”

Kallo na tayi tana gyada kai alamun ‘Eh.

“Innar mu wai dagaske ba zaki ba dai..?”

“Ai mu a al’adun mu uwa bata zuwa gurin shagalin bikin ‘ya’yanta. Saboda kunya.”

Cewar adda sabira data shigo ciki a lokacin. Murmusawa nai na dauki sauran kayayyaki na na fita. A kofar soro naci karo da Mubeen yana gyara karin hular sa. Na ware idanu ina kallon sa da mamaki,

“Meye haka Mubeen?”

“Biki Yayan mu naxo mana.”

“Toh fah!”

“Muje ko?”

“Ina fa?”

“Ba gidan kwalliya za’a kai ku ba?”

“Inji wa kenan?”

“Ya Najibu ne ya gayamun..”

Na kad’a kai cikin karfin hali kawai na fice abuna. Budemin gaba yai na xauna ina hura hanci,

“Ina zamu fara zuwa Ma!”

“Baka iya gaisuwa bane?”

Dan murmushi yai yana taune kasan lips dinsa,

“Afuwan! Barka da rana.”

Harara na dankara masa muka karasa gidan su Fadilah. Ciki na shiga na kirawo Fadilah itada wasu kawayen mu su biyu. Muka shiga mota Mubeen ya kai mu gidan kwalliya.

“Mungode..”

“Zan jira ai..”

Kallon sa nayi yana wani bobbokarewa tamkar wani babban mutumi. Yasha adon wata shadda kalar toka. Komai na jikin sa kalar aikin shaddar ne. Girgiza kai kawai nayi na shige gidan kwalliyar. Mun jima kafin a gama mana kwalliyar nan. Dan ni hoda da jambaki kawai nasa aka shafamin banda gira. Amman dukda haka nayi masifar kyau. Na cire hijabin dana doro akai ina yafa mayafin kayan a kafad’a. Gaskia baxan iya fita wajen yaron can a haka ba. Na fada ina kallon yadda rigata ta kamani. Waya ta na janyo na kira Haysam na kwatanta masa inda muke. Da niyyar idan yazo ni na bishi su kuma subi Mubeen. Gaba ki d’aya muka futa kofar gidah naja na tsaya abakin kofa. Su Fadilah suka shige mota ni kuma na tsaya jiran Haysam. Mubeen ya fito daga motar ganin shiru ban karaso ba. A lokacin na fito daga zauren ina daukar kai na awaya ta. Tunda Mubeen ya taho yake kallo na baki bude. Wani irin kallo mai dauke da ma’anoni wanda har sai da hakan yasa na ji a jiki na. Hada idanu mukai na shiga tukwikwiye mayafi na.

“Ma kinyi kyau..”

“Y..yauwa.”

“Shall we...?”

“No kuje za..Za’a zo dauka na.”

Hade rai yayi yana sake doso inda nake. Na shiga ja da baya ina raba idanu. Cikin ikon Allah sai ga motar Haysam. Ai kuwa da sauri na goce na tafi wajen Haysam. Yana faka motar na shige ciki ina dagawa Mubeen hannu. Haushi, Takaici, Kishi.. Duk suka takura suka tsayawa Mubeen a wuya. Dakyar ya iya jan k’afafuwan sa ya shige motar yaja suka tafi.. A mota Haysam sai zubamin kalamai yake ni dai gaba d’aya nagaji so kawai nake na sauka daga cikin motar wallahi,

“Mine ki bani dama na turo iyaye na ai maganar auren mu dan Allah... Wallahi ina son ki! Sau da yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyar tawa, Su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya. Inaso mu kasance cikin inuwa d’aya. Ki bani dama na shayar dake zumar soyayyar mu idan mu kai aure. Dan Allah yaushe zan turo? Na matsu wallahi Mine, Idan da gaban matsuwa ma wallahi nayi,

“Banaso wani yazo yamin shigar sauri ne wallahi. Kinga shekaru nawa ina adana soyayyar ki? Uhm? Wallahi Mine naso da aure na akan ki kike koyarwar nan wallahi. Saboda department dinku ya cika maza baga daliban ga baga malaman ba. Kuma duk idanun su akan ki..”

Murmushi kawai nai masa ina cigaba da kallon hanya. Ya kuma numfasawa kafin ya cigaba da cewa,

“Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da soyayyar dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki Mine. Wallahi banason rasaki..”

“Wai duk wadannan zantukan na menene Ya Haysam?”

“Mine kenan! Naga alamun har yanzu ni ke watangaririn wahalar dakon soyayyar ki. Anya kina tausayi na kuwa? Ko suna gashinan kinki canzamin.”

“Kunya nake ji..”

“Kunya? Ni Wallahi ba Yayan ki bane, Zan kuwa yi ko’kari na cire kunyar nan da munyi aure..”

Ganin zai ‘barota yasa nayi murmushi kawai hade da hanzarin taran numfashin sa,

“Ya Haysam meyasa kake cewa kana jin tsoro?”

“Mine gani nake za’ai min shigar sauri wallahi. Pls ki bani dama na turo magabatana..”

“Na baka Ya Haysam....”

“Dagaske Mine!”

Gyada kai nayi. Ya buga sitiyari yana hamdala. Haka yaita zantuka yana kwararo mun godia kamar wanda aka daura mana aure a lokacin. Nide muna karasawa wajen taron na fice daga motar na koma wajen su Fadilah. Tana daga bayan motar Mubeen tana jiran zuwa na. Domin dik kawayen sun hallara. Jira ake na karaso mu shiga da amaryar ciki. Ko cikan ki Mubeen bai cemin ba ya cigaba da danna wayar sa yana kurbar ruwa. Na girgiza kai kawai muka shiga cikin wajen taron bayan mc ya sanar da shigowar mu. Dj ya sakar mana kida. Guri yayi kyau sosai wallahi komaiba tsare. Muka raka amarya wajen zaman ta. Akayi addua na bude taro sannan aka fara gudanar da shirye shirye. Inda aka kira babban abokin ango ya bada tarihin sa. Nima aka kirawoni a matsayi na na babbar kawar amarya na bada tarihin ta. Duk a takure amman nake saboda yanayin dinki na ga idanun mutane a kai na. Duk inda nai bina ake da kallo. Haka aka cigaba da hidimar biki har lokacin da aka gama. Wannan karon abokin ango ne ya tafi da amarya. Ni kuma na shiga lalubo number Haysam zan kirawo shi yazo ya dauke ni. Naji takun mutum a gaba na. Mubeen ne hannun sa dauke da suit babba ya ratayamin a bayana inda ta sakkomin sosai ta rufe min baya,

“Muje ko..?”

Bansan meyasa ba. Kawai na daga kai nabi bayan sa ina kambama girmamawa irin tasa da sanin ya kamata. Can ciki muka baro su Bintalo da Usaiba suna fada akan abincin daya ragu. Yan gidan mu kenan ako’ina sai sun saida halin su. Ko a mota ahankali Mubeen yake tafiya ga sautin kira’ar shureim na tashi. Na lumshe idanu inajin wata nutsuwa na ratsani..

“Mah yaushe ne bikin ki..?”

Na jiyo tambayar a baibaice,

“Biki na?”

Na juya ina kallon sa dauke da mamaki. Kada kai yayi alamun Eh yana cigaba da tukin sa hankali kwance,

“An kusa ISA! Soon.”

Murmushi naji yayi mai sauti,

“Menene? Meyasa ka tambaya?”

“Bakomai..”

Kada kai nayi na cigaba da sauraron karatun dake tashi a hankali har muka karasa gidah. Nayi masa godia na shige cikin gidah da sauri. Domin a yau ba sai gobe ba sai na maidawa tela dinkinnan ya gyara minshi...

*WASHE-GARI*

Da misalin karfe 10:30 na safe dubban mutane suka sheda d’aurin auren Yayan mu Najibullah da amaryar sa Fadilah akan sadaki nera dubu talatin lakadan, Tunda aka daura auren nan suka dawo gida Kawu ila ke zazzaga masifa a tsakar gidah. Daca yai ma ba xashi daurin auren ba sai da Gwaggo Aminatu ta tursasa shi tukunna ya tafi yana zunduma mana xagi. Bokitin sa ya karkad’e ya zauna yana jijjiga kafa shi ko kunyar mutanen dake tsakar gidan bayaji. Gashi sai shige da fice akeyi.

“Mutanen banza da wofi an debi uban kudi an kai na daurin aure. Ga abinci kala-kala anayi. Na hada ku duka na kwashe muku albarka mutanen banza da wofi..”

Murmushi nai alokacin ina ajiyewa wata makociyar mu waina da miya a gaban ta. Domin kallo d’aya zaka masa kasan yana cikin tsantsar ba’kin ciki. Ya dube ni yana kwakwulo cikin

Please Login or Register in order to submit comment