Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai lapia ya bada sa’ar karatu.”

“Ameen Papa.”

Sauri yai ya fice domin idan mahifiyar su ta fito ta ganshi dayan biyu ne ko dai ya hakura da zuwa makarantar ko kuma ya tsaya ya ci abinci. Mota ya shige driver yaja shi sai school...
Suna tafe yana duba agogo, Sam bayason yayi missing lectures dinta. Lokaci zuwa lokaci yakan furta,

“My Ayana...! irisiwoni isikīyayu diresi yit’ebik’u.”

(My beautiful flower can’t wait to see you...)

*TWIN THEATER*

Ruwa ake tsugawa tamkar da bakin ‘kwarya, Gashi ban taho da lema ba. Tagumi na zabga ina kallon yadda dalibai ke gudu suna shigewa cikin lecture hall din. Gani ni malamar a waje ina tsoron kada ruwa ya doke ni, Domin inada saurin yin mura. Agogo na na kalla saura minti goma lokacin fara lecture din yayi. Wata k’atuwar mota mai numfashi ce tazo ta tsaya agaba na. Wa zan gani? Miskilin yaron nan na jiya shine ya fito daga ciki yana gyara zaman P-cap dinsa. Direban sa da sauri ya fito ya zuge lema ya rike masa. Karbar lemar yayi hade da da yiwa direban alamun ya tafi. A hankali ya shiga takowa inda nake. Hannun sa d’aya ya rike lemar da notepad d’ayar kuma ya saka shi a aljihu. Tsayawa nayi ina kallon ikon Allah.

Har inda nake ya tako tamkar zai shiga jiki na, Na ja baya ina dalla masa harara. Handkerchief ya zaro a aljihun sa ya sunkuya kasa yana gogemin takalmina da cakwalin ‘kasa ya batamin. Shiru nayi ina kallon ikon Allah! Yana gama gogewa ya mike tsaye yana murmushi. Yau ma ba zai gaishe ni ba? Na fada a zucia ta ina kallon sa a dakile. Lemar hannun sa ya sanya a saitin kai na. Cikin maganar sa a hankali tamkar rad’a na jiyo shi yana nunamin hanya hade da cewar,

“Ayana...Shall we?!”

Ka’da kai nayi kawai nayi muka fara tafiya, Ya sakalo lemar guri na. Ruwa sai dukan sa yake. Dan matsa masa nayi ya shigo ciki. Tamkar wasu wanda suke a tare muka karasa bakin kofar ajin. Zan fita daga ciki yai saurin riko jakata yana girgiza min kai. Tamkar wanda ake koyawa magana haka ya shiga girgiza kai yana wani marairacemin,

“Ayana...Please don’t....”

Gaba d’aya sai kai na ya kulle da al’amarin renin hankalin balaraben yaron nan. Menene kuma Ayana? Bai gaishe ni ba yana matsayin dalibi na sai nunamin iko sai kace shine malamin? Muka shiga kallon kallo dashi. Sai shine ya sunkuyar da kansa kasa yana sake rike jakata da karfi,

“Please ki bari na raka ki...”

Fuzge jakata nayi na shige cikin theatre din. Ina kallon sa ta gefen ido yana min kallon kin kyauta. Ciki ya shigo ya zauna yana kallona ‘kasa-kasa. Na sake daure fuska ta na shiga basu hak’urin rashin shigowa ta da wuri. Duk wani movements dina a idanun sa yake. Ya kasa ya tsare ni da kallo har da wani kishingid’ewa yana lumshe idanu. Lalle zanyi maganin ka ko wanene kai. Na fada a zucia ta ina rubuta kalmomin ‘Concept Of Literature’ a board. Juyawa nai na tambaye su cikin harshen turanci shin kowanene zai iya fadamin ma’anar literature? Dan renin hankalin ku shi ya fara daga hannu yana murmushi. Daga kai nayi alamun ina jinsa. Cike da k’asaita murya ‘kasa kasa ya fara fadar,

“Literature is an imaginative work of art, That uses languages, Plots etc to express the beauty of life..”

“Excellent...”

Nai saurin fada to avoid his gaze hade da nuna wani dalibin. A daddafe na karasa musu lectures din ranar. Domin na tsani mayen kallo. Wani irin kallo yake bina dashi mai dauke da tarin ma’anoni....

——-
Assalamu Alaikoum dearest fans😘❤️Toh masu comments suna maganar na bawa Batoul dan shekaru arba’in da biyar ko kuma wanda ya girmeta sosai ku RUNGUMI sorry 🥺👏🏻wannan LITTAFI yana dauke da wasu rassa na cikin sa wanda suka faru a gaske. Kunga kuwa babu damar canza akalar littafi. A zahirin gaskia ma duk wanda ke bibiyar books Dina yasan bana canza yadda na dakko littafi na. Fatana dai yan darussan dake ciki kawai mu amfana dasu. Kurakuren ciki Allah ya yafemu duka👏🏻 So IGIYAR ZATO is 'Almost Based on a true story' And almost based on a true story refers to the recreation of a story with changes to the storyline to suit the audience's understanding and expectations. Often done to entertain the audience and dramatises certain events for that purpose. 👏🏻👏🏻👏🏻 Get that puh lease dearest fans😘😘 Na son zaku so littafin nan fiye da rubuta na baya, Saboda yana dauke da salo na daban.
Da fatan munsha ruwa lapia? Toh Allah ya biya mana bukatin mu na alkhairi AMEEN SUMMA AMEEN. Gobe sallah💃🏿HAPPY EID AL ADHA MUBARAK in advance 😘May Allah accepts it form mine and yours❤️❤️ALLAH YA MAIMAITA MANA... ASHA HUTUN SALLAH LAPIA💃🏿💃🏿ZAFAFA NA MUKU SON KAUNA MARAR GAURAYE...🥰😍😻❤️✅✅✅

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


MX🧕🏼*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/LxY42ErBf_8


*31*


Har ina tuntub’e haka na fice daga theatre din ina zabga sauri. Office dina na shiga dauke da sallama na bararraje ina jujjuyawa a kujera. Gaba d’aya I’m worn out. So nake kawai na jini a katifar Innar mu. Sallama na jiyo a saman kai na. Miskilin yaron nan ne ya shigo. Amsawa nayi a dakile ina cigaba da duba takarddun gaba na.

“Yes.”

Na fada don jin shirun yayi yawa. Zama yayi a kujera mai kallon wadda nake zaune. Ya harde kafafu yana kallo na. Ajiyar zuciya na sauke na dube shi ina hade rai.

“Ya akai?”

Murmushi yayi yana shafar hard'add'iyar sumar kansa wacce take ta faman kyalli tamkar anyi b'arin mai a kanta. Ya sake gyara kujerar da yake kai yadda zai dinga kallo na sosai, na kallesa cike da b'acin rai nace masa.

“Kai! Wai menene haka ne? Ni sa'arka ce da zaka dinga min abu kamar mate d'inka?”

“Sorry ma'am, wata tambaya ce nake son yi miki.”

Yayi maganar cikin sigar da nake so, wato girmamawa. Hakan kuma ba karamin dad'i ya yi min ba, domin ji nayi lallai ni malama ce a gurinsa, amman duk da haka sai na kara d'aure fuska ta tare da janyo wani littafi ina budewa ina masa magana.

“Okay yi tambayarka dan sauri nake yi ina da aikin yi. Kuma karka min tambaya wadda ba ta shafi darasin da muka yi daku ba. Idan kuma bai shafi karatu ba to karka saka ran zan baka amsar tambayarka.”

Tunda na fara magana idanunsa suna kaina baya ko kiftawa, ni kuma sai bud'e Page's nake yi babu abinda ya shafeni da irin kallonsa a kaina. Mubeen ya saki wani sihirtaccen murmushi wanda ina da yakinin cewar dad'i yake ji gani gashi harma yana min magana ina bashi amsa. Shiru ya kuma ratsawa hakan yasa na rufe littafin na d'ago ina kallonsa, sai naga ni ya kurawa ido, na d'auki biro tare da nuna masa hanyar fita naji yace.

“Sorry ma'am, daman akan darasin mu ne na yau.”

“Ina jinka, mai ya faru?”

“Ma'am, duk ban gane ba shine nazo ki sake min karin bayani badan hali na ba.”

Wani irin kululun takaici ne yazo min wuya ya tokare, haushi da bakin ciki suka taru suka zauna a cikin zuciyata, rai na a cunkushe na kallesa.

“Idan kace duk baka gane darasin mu na yau ba, shin daga ina kake d'akko duk wasu amsoshin tambayar da kake bani? Idan ban manta ba, bana jin kabar wani ya bani amsa a cikin hall d'in, duk kai ka amsa shine yanzu zaka ce baka fahimta ba?”

Mubeen ya shafa keyarsa yana yin kasa da idanuwa, ni kuma na hararesa tare da kuma tsuke fuska nace.

“Okay naji abinda kace, yanzu dai kaje ka samu wasu wadanda suka fahimta sai su yi maka bayani ni yanzu akwai abinda zanyi, idan na dawo next lecture sai na d'an sake yi muku bayani ku duka ajin.”

Ina gama yin magana na sake nuna masa hanyar fita, kamar zai yi gardama sai kuma ya rausayar da kai ya mike yana dora p.cap d'insa a kansa, kasan cewar da ya shigo office d'in nawa cirewa yayi ya dora akan desk. Har ya kai bakin k'ofa zai fita kamar wanda aka tsikara ya sake dawowa baya yana kallona, na yi masa kallon karka kuskura ka kuma tambaya ta, sai kuma naji yace.

“Thank you Ma'am.”

Na yatsina fuska bance komai ba naci gaba da rubutu cikin wani file, shi kuma ya fita yana sakin murmushi yasan cewar sarai ya takura min duba da yadda nake bashi amsa. Wasu lectures d'in ya shiga sai kusan karfe hud'u sannan ya gama. A dai-dai lokacin kuma na fito zan tafi gida, jakata rataye a kafad'a kaina a kasa kamar yadda na saba idan zanyi tafiya saboda bana son yawan kallo ji nake kamar zan fad'i. Dan yayyafin da ake yi shine yasa ni tafiya da d'an sauri ina tsoran kar wani ruwan ya kuma ke cewa na rasa yadda zanyi. Mota naji tana bina a baya a hankali, can kuma sai naji ta tsaya a gabana hakan yasa ni tsayawa. Driver d'in ne ya fito ya karaso kusa dani yana gaisheni tamkar wata shugabar shi, naji ya fara magana.

“Hajiya ki shigo a kaiki saboda wannan yayyafin zai iya haddasa miki zazzabi”

Na kalli mutumin sosai, ban san shi ba na kuma manta da kalar motar su Mubeen. Nayi murmushi domin naji dad'in yadda yaso taimaka min, sai dai ba zan iya hawa ba saboda ban tab'a ganinsa ba, hakan yasa nace dashi.

“Babu komai zan karasa bakin gate na samu abun hawa, na gode da taimakon ka gare ni.”

Ina kaiwa nan na juya zan tafi bawan Allahn nan ya kuma biyo ni, har kasa ya tsugunna yana rokona yana had'ani da girman Allah harda cewa.

“Wallahi hajiya ni ba barawon mutane bane, kuma ba macuci bane ni bazan cuceki ba taimaka miki kawai zanyi.”

Naja numfashi tare da gyara jakata sannan nace masa toh, muka nufi motar abin mamaki ya bud'e min gaban motar na kallesa shima ya kalleni kafin nayi addu'a cikin zuciyata sannan na shiga. Abinda ya daure min kai shine ganin Mubeen yazo ya bud'e wajan driving ya zauna tare da rufe motar, shi kuma wancan na lek'a ta window na hango shi yana tafiya hanyar gate. 'Had'in baki ne kenan?' Na ayyana a cikin zuciyata sannan na kama kofar zan fita naji ta gam sai na kalle shi ina masa kallon ka raina ni tare da cewa.

“Kai kuma lafiya ka sake biyo ni nan?”

Bai yi min magana ba ya fara k'ok'arin yiwa motar key, na kuma juyawa ina kallansa cike da takaici nace.

“Naga alamar akwai rashin girmamani a tattare da kai, kasan matsayina a wajanka kuwa? Bud'e min na fita tun kafin na sab'a maka.”

“Kiyi hakuri ma'am ruwa ake yi, zanje na kaiki gida ba wani abun. Ban raina ki ba, hasalima wani irin girma da daraja gareki a cikin idanuwa na. Kiyi hakuri na kai ki wallahi ba zan iya jin dad'i ba naga ruwa yana dukan malamata ba, bayan ni d'alibinki ne akwai taimakekeniya a tsakani. Nasan kema wata rana zaki iya taimako na ta hanyar ba banyi tsammani ba. Ina respecting din ki har cikin zuciyata, kiyi hakuri.”

Jikina ne yayi sanyi jin tabbas haka ne abinda ya fad'a, toh amman mai yasa duk ga mutane nan da suka cancanci ya taimaka musu bai yi ba sai ni? Ga makafi nan da guragu duk ya tsallake su ya taho gareta? Wannan akwai ayar tambaya a tare dashi dole akwai dalilin da yasa yake shishige min. Na d'auke kai daga kallansa ina cewa.

“Toh amman mai yasa baka je kace na shigo ba kasa wani?”

“Mah nasan idan ni naje ba zaki hau motar ba, shi yasa nace da driver d'in yaje kuma gashi anci sa'a.”

“Ya akai ya tafi bai tsaya ya hau ba.?”

“Ma'am, na bashi kudi ya hau abin hawa mu had'u dashi a gida. Kinga idan nace ya hau baya ai ba tsari tunda shine fa yake tukani.”

Kallansa nayi naga yana lumshe idanunsa haushi ya kuma kamani, cikin rai na ina ayyana cewa kila d'an gidan mai kudi ne saboda gashi nan komai nasa neat, gashi har wani driver gareshi motar kuwa ta koshi sai wani kamshi take mai matuk'ar sanyaya zuciya. Jan motar Mubeen ya fara yi a hankali, hakan da na gani shine yasa ni yin magana nace.

“Kodai baka iya motar ba? Karka jefa ka watsar damu a banza.”

Ya saki murmushi tare da lasar lips d'insa na sama sannan ya kalleni tamkar wani babba. Tafiya yaci gaba da yi ba tare da ya sake ce min komai ba, hakan ya bani haushi matuk'a duk da cewar na fi bawa zuciyata laifi domin nice na yarda na shiga motar dole duk abinda zan gani na kawar da kai tunda yaron naga akwai jin kai. Sai da muka fita daga gate ya tsaya saboda zamu hau titi ya tambaya wane hannu zamu bi hagu ko dama, sai nima nayi shiru tamkar banji ba. Kamar daman haka yake so sai naga ya koma damu gefe ya yi parking tare da dora kansa jikin glass din window yana lumshe idanunsa.

“Ya haka? Baka da lafiya ne?”

“No ma'am, na tambaya ina zamu nufa baki yi magana ba, ni kuma bana son takurawa malamata da surutu na, shine na tsaya.”

Haushi ya sarke zuciya ta yaro karami ya tsaya yana rai na min hankali kamar wata sa'ar shi. Sai na d'auki jakata dake kan cinya na rataya ina k'ok'arin bud'e murfin motar na fita.

“Bud'e min na gode da taimakon ka, zan iya karasawa da kai na.”

Mubeen yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, na kai ido na kan mukullin motar zuciya ta na raya min na murd'a idan na murd'a ta kunnu sai kawai na bud'e na fita dan yaron akwai rainin hankali. Sai dai ina kai hannu tamkar shima an sanar dashi abinda zan aikata sai naga ya kunna motar ya fara tafiya, ganin mun hau titi yasa nace dashi.

“Limancin kona nan zamu tafi.”

Sai ya kalle ni yana zaro ido, na kauda kai ina had'e rai, kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace dani.

“Wane hannu zanbi kenan? Bansan hanyar ba, sai dai nasan mun tab'a zuwa unguwar har naji mahaifina ya fad'i sunan limancin kona.”

Tsaki na saki a cikin zuciya ta kafin na nuna masa da hannu, shima bai kuma magana ba ya karya motar muka tafi. Gabaki d'aya nice na dinga nuna masa hanyar da zai bi har muka kusa zuwa gida sannan nace dashi.

“Yauwa nan ya isa na gode sosai.”

Na karasa maganar ina shirin bud'e motar amman gam yaki, na sake kallonsa fuskata babu yabo ba fallasa nace.

“Bud'e min na fita, idan kuma baka son gobe na sake yadda da taimakon ka karka bud'e min har sai na kuma yin magana.”

Babu musu Mubeen ya bud'e motar yana bin ta da kallo, haka kawai yaji wani irin nishad'i a cikin ransa. Ni kuma na bud'e nayi ficewa ta ko godiya banyi masa ba saboda ya b'atamin rai kwarai. Shi kuwa Mubeen ina tafiya ashe ya biyo ni ba tare da na sani ba, kuma banyi zaton zai biyo bayana ba hakan yasa koda ina tafiya ban waigo ba har sai da na sha kwana na shiga gidan mu. Shi kuma ya tsaya ya tambaya shin nan ne gidan mu? Aka tabbatar masa da nan ne sannan ya kad'a kai ya koma mota, sai da ya zauna sannan hankalinsa ya tashi domin bai san ina zai bi ya koma gida ba, ya bud'e murfin motar yana faman kalle-kalle tamkar mai neman wani abun.

“Ranka ya dad'e mu wuce ne?”

Mubeen yaji muryar driver d'insa, abin ya bashi mamaki ganin yace masa fa ya tafi gida amman ya akai ya ganshi anan? Cike da rashin son magana yace.

“Ya akai ka biyo ni?”

“Kayi hakuri ba zan iya barin ka tafiya kai kadai ba saboda amana ce kai a gare ni, shi yasa na tari napep na dinga binka a baya.”

Baice komai ba sai komawa baya yayi ya zauna shi kuma driver din ya shiga yaja suka tafi. Mubeen na zaune yana ta murmushi saboda d'an zaman nan da suka yi da malamar tashi ya gama gano cewar tana da son girma, duba da komai yayi zata ce ya manta matsayinta a gareshi. Da wannan ya shiga gida bayan yayi wanka yayi sallah kwanciya ya yi kota kan abinci bai bi ba har sai da mahaifiyar sa tazo masa dashi ya d'an ci kad'an sannan ta fitar da sauran bayan ta yi masa gargad'i akan ya tabbatar yasha maganinsa.

Yatsina fuska yayi sannan ya juya ya kalli kan bedside locker d'in dake d'akin, magungunan ya harara saboda ya gaji da shan su. Juyawa yayi ba tare da ya dauka ba ya janyo remote ya kunna tv wacce ke kafe jikin bango, yana kwance yana kallo hankalinsa a kwance, cikin ransa yana tuno malamarsa wacce salonta yake neman kai shi inda bai cancanta ba. Labarai ya kunno, cikin sa'a kuwa yaga an hasko inda mahaifinsa yake gudanar da campaign d'insa, yaji matar tana cewa.

“Amb Salees kenan wanda yake shugabantar mazauna kasar Najeriya a can kasar Ethiopia, yana kaddamar da campaign neman zabe ta kujerar gwamnan jihar kaduna, a unguwar rigasa, tare da amininsa Alhaji Kabeer wafa, sai mataimakin sa Dr Hafiz M Baba, wanda ke gefe yana d'agawa jama'a hannu kafin kaddamar da kamfen din. Amb Salees ya kaddamar da kamfen d'in tsayawa takara a zaben gwamna da za'a gudanar cikin watan janairu na sabuwar shekara da zata zo. Amb ya sanar da haka ne a jiya Asabar a gaban dubban magoya bayan shi da suka hallara a unguwar rigasa. Amb ya shaidawa magoya bayansa cewa jahar Kaduna tana cikin wani irin yana yi na son canji. Bisa ga cewar shi, zai tsaya takara ne sabida ya hakikanta cewa, zai iya jagorantar jahar zuwa samun sabon canjin. Ko mai sauraro da kuma kallon mu zai iya amincewa ya bawa Amb kuri'arsa?”

Mubeen ya kurawa tv d'in idanuwa yana kallon yadda ake nuna mahaifinsa yana ta yiwa al'ummar annabi alkawarurruka da dama. Tsaki yaja dan shi bai sai abinda mahaifinsa zai yi da siyasa ba, suna da komai yana da kud'in sa wanda duk Nigeria babu wanda ya isa ya takashi bai rama ba, amman meye na shiga harkar siyasa salon suna tafiya a hanya ana zagin su idan ba'a cika alkawarin da aka d'auka ba. Sumar kansa ya shafa yana sauke numfashi, can kuma ya d'akko jota d'insa yana duba darasin da tayi musu, sannan yana shiga google ya duba wasu abubuwan saboda ya samu na bata amsa idan tayi tambaya.

*GIDAN MATA TARA*

Cike tsakar gidan mu yake da ahalin mu. Kowanne yana kara-kainan gaban sa. Zabbau dake kankare ‘kanzo a tukunya gayyar ‘yayan ta na gaban ta suna lashe lebe. Ta mike hade da gantsarewa ta sakarwa d’aya daga cikin ‘yayanta ran’kwashi ji kake ‘kwas.

“Hegun yara, ‘kanzon ma don mayata sai kun cinye bayan abincin da nasamo muku.? Tahi kubar nan kafin na muku lahani..”

Ta ‘karasa fada tana binsu da murfin tukunya. Ficewa su kai suna kuka Ita kuma ta cigaba da kankaro ‘kanzon tana afawa a baka. Shigowa ta kenan na fara cin karo da karakainan su. Sama na haye ina mai yiwa Allah godia a zuciata bisa ga yadda ahankali yake canza mana rayuwar mu. Na sake duban zabbau dake cin kanzo ka’indana’in tamkar zata ‘kware. Na tuno muma a shekarun baya muke cikin halin rashi suna na samu. Amman yanzu duniya ta fara canza musu sun fita daga cikin halin samu suna na rashi. Daki na shiga da sallama. Innar mu da autar mu ne kawai. Suka amsa kowanne fuskar sa dauke da fara’a. Autar mu ta rungume ni tana murna. Lumshe idanu nai don jiyo ‘kamshin man kuli dake tashi. Ina wa man kuli son so wallahi. Musanman a shinkafa da wake. Ai kuwa ban gama maganar da nake a zuci ba autar mu ta mikomin kwanon abinci na. Shinkafa da wake ne da yajin tafarnuwa a gefe. Sai dan karamin filet dauke da salak da tumatir da cucumber ga magi shima a gefe. Sai kamshi ne ke tashi. Saurin sakkowa nai daga kan yar katifar mu. Na wanke hannu na a robar da autar mu ta kawomin. Bismillah nayi na shiga cin abincin nan ina daga kai cikin jin dadin abincin.

“Innar mu mungode Allah ya saka da alkhairi, Wallahi tun satin baya nake son cin wake da shinkafa. Wayyo Allah dadi.”

Autar mu ta kyalkyale da daria, Innar mu kuma tayi murmushi kawai ganin yadda suka ga ina santi harda ka’da hannuwa na. Robar zob’o autar mu ta sake matsomin da ita. Tayi sanyi kau da alamun ba’a dad’e da siyo shi ba. Had’adden zo’bo ne da matar soja keyi. Ga dadi ga tsafta naira talatin kuma me sanyi.

“Kai yau dai na zama yar gata. Harda zob’on matar soja? Alhamdulillah Allah ya kara budi.”

“Ameen..”

Haka dai na karasa cinye abincin nan ina santi. Bayan na gama na gyatse da hamdalah. Na rage kayan jiki na hade da daukar kayan wanka na don sauka kasa yin wanka. Har na kai kofa na juya,

“Innar mu a dan zubamin abinci na bawa zabbau naga tana cin ‘kanzo.”

Innar mu ta mike daga kishingiden data ke tana kokarin janyo kular abincin gaban ta,

“Kai haba dai? D’axu ma na bata nace ta bawa yaran wallahi..”

“Wlh Yayya Batoul Bintalo tazo nan tai ta zagin...”

Autar mu bata karasa fada ba Innar mu ta mata dakuwa tana zuba abincin,

“Tashi ki fara shiri ma kada ki makara.”

Mikewa autar mu tayi tana mika. Murmushi nai don tuni na gano Bintalo ce tayiwa Innar mu tijara akan ta bawa zabbau abinci. Gashi ita ta dena yi dasu. Girgiza kai nayi kawai na karb’i abincin da Innar mu ke mikomin. Sauka nayi kasa. Usaiba na wanki, talatuwa na sab’e mata. Zabbau kuma ta zubawa rijiya idanu da alamun tunani take. Kofar band’akin na hango an karo ta. Da alamun wani ne aciki. Ajiye kayan wankan nawa nayi agefe kafin na karasa kusa da zabbau ina mai mika mata kwanon abincin,

“Zabbau gashi ki bawa su ‘dan abbasi..”

Zabbau tasa hannu zata k’arba Bintalo ta fito daga bandaki tana kururuwa hade da buga zani ta watsa hannu baya, Usaiba dake gefe taja guda ta saki,

“A hayye kayya kai.”

Bintalo ta wafce abincin ta kifar dashi a kasa, Hade da sa kasan kodadden jemammen takalmin ta ta take abincin,

“A hayye yau ga gaye ba makilis! Sittin ta ubangiji naki jinin makirci a rayuwata. Makirai, Algungumai, Shin wai ana dole ne? Sittin ta ubangiji sai yanzu na gano. Wato ku kunfara dandalar arziki shine zaku fara yiwa mutane annamimanci? Dan bakin munafunci ina ku ina bawa tsatso na abincin ku? Bama dake zanyi ba matsa.”

Bangaje ni Bintalo tayi tana huci. Ta buga zani tana yarfa hannaye,

“Kaltume fito nan babbar munasura. Duk ke kike kitsawa ‘yayan ki komai. Kaltume, Kaltume ba zaki fito ba sai na hawo?”

Shiru nayi na ja gefe ina zabga tagumi daga abun arziki sai ya koma na tsiya? Bintalo sai lailayo ashariya take tana durawa ita kadai. Kanzil Innar mu bata ce ba. Domin ko fitowa ba tai ba. Zabbau ta saki hamma tamkar bakinta zai zazzago tana rufe baki,

“Baba gaskia ni yunwa nake ji, Ke kin ki bamu, Sannan kin hana a bamu. Ni gaskia na gaji tun d’axu ruwa nake dankwarawa ciki na . Bayan naga burodi kin hyafehi da buta keda Hinde kuna ci...”

Bintalo ta dankarawa zabbau harara tana watsa hannu baya,

“Itama mashinshinnin ta ne ya aikonta yaron kirki mai hannu a sake. Zan zauna ina ciyar daku ne

Please Login or Register in order to submit comment