Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaske sannan wanda ya tada kai da naira, sannan tanada burin tazaga duniya, tayi ilimi me zurfi a kasashen waje, yadda zata goga kafada da manyan mata a kasar Nigeria dama nahiyar Africa gaba daya, shiyasa duk wanda yazo indai yanada kudi zata wankeshi son ranta sannan ta sallemeshi, dan har yanzu bataga dai dai da itaba, malam munir yayi iya yinsa dayimata nasiha itada yar uwatta saudat amma abu ya gagara, ana cikin wannan haline Allah yayiwa malam munir rasuwa, mutane sunji mutuwarsa saboda mutumin kirki ne kwarai dagaske, bayan an gama makoki khadija tacigaba da tsiyarta daga inda ta tsaya, ganinda Kabir yayi masu kudi na neman aurenta yasa kara zage damtse, dayasamu kudi ko anmusu albashi dayake yasamu aiki a wani kamfani, seyaje ya kashewa khadija su, har rawar jiki yake wasu kudin sushigo yakuma kaimata, alhalin gidansu wataran se a kwana biyu ba a dora tukunya ba, se ayi term biyu ana korar kannensa saboda kudin PTA, amma baze iya basu ba sedai khadija.
Mahifiyar Kabir ta zubda hawaye ba'adadi amma bayadda ta iya da wannan hali na ko inkula da danta Kabir yake musu itada kannensa, sam takasa gane kansa.
In khadija ta dau wanka ta taho seka dauka wata yar hamshakin Attajiri ce, saboda 'yar kwalisa ce ga karya data dorawa kanta, khadija tayi candy amma taki cigaba da makaranta tace seta auri mekudi zataje abroad tacigaba da karatu, sabida abun kunyane a ce nan gaba intazama wata a Nigeria ace za' ayi interview da ita tace a Nigeria tayi karatu.
Yauma yammace taci uban ado tana taku kamar tana taka kwai, taji anamata horn da babur amma tayi banza taki matsawa, mutumin yadinga horn amma taki ko daga kai balle tabashi hanya ya wuce, parking yayi ya kalleta yace "baiwar Allah kokurma ce ne? Inata horn kibani hanya zan wuce amma kinyi banza" wani mugun kallo tayi masa, "idanni kurma ce kaikuma mara hankali ba" zaro ido mutumin yayi saboda yasan a haife ya haifi wannaan yarinyar
"nine mara hankalin yarinya?"
"kwarai kaine mara hankali, ya za'ayi ina tafiya zaka isheni da horn da wannan rubabben gwangwanin naka, kana nema ka kashemin dodon kunnena, aida seka tsaya in wuce, kokuma ka canza hanya, tunda bakai ka gina hanyar ba ai"
"Amma kina ganin ya dace ki kirani mara hankali da girmana da komai"
Cikin tsiwa tace "to semenene? Ai abun rashin hankalin kayi"
"shikenan in abunda kikayimin dai2 ne za'ayiwa mahaifinki kiji inda dadi"
"to ya mutu wata uku dasuka wuce, inkuma kabarin za'abishi ayi masa se inji, aikin banza mutane suyita abu kaman wasu yan kwaya"
Cikin rawar murya yace "nine kaman dan kwayan"?
"kaimana da dawani nake, wayasanima ko ita kaje kasha, kake nema kayimin akuya nonsense" tayi gaba abunta, mutumin nan seda ya zubda hawaye, ya kunna babur dinsa yazo daidai saitin khadija ya tsaya ya kalleta yace "Insha Allah sekin haifi dan kwaya, sekuma ya miki abunda kikayimin"
"kai kasani, koma kwayar zan haifa, shirmen banza kawai, adai dinga kula, da irin kwayar daza'asha in bahakaba a kare a gidan mahaukata" bataji mezece ba tayi tafiyarta.
A fusace ta shiga gida tana ta mita, saudat na tsakar gida tana danna waya, ta dago ta kalli khadija tace "Ahh kaga manyan mata a gidan Kabir ya akayine, waya taboki kike mita?"
A wulakance khadija ta kalli saudat, "waye kuma kabir, karki kara hadani da wannam matsiyacin, a tunaninki mace mai daraja kamarni zan iya auren wani Kabir, tausayinsa kawai nakeji wanke dan banza zangama, da zarar nasamu my dream hubby inyi dumping sha3 aside inyi aurena, idan na auri wannan fakirin ta ina burina ze cika" murmushi saudat tayi, "angaisheki matar manya, banga laifinkiba, nima ina bayanki wayakeso talauci ai kudi kawai alaji, amma meya bata miki rai haka?"
Nan khadija ta gayamata abunda yahadata da wannan mutumin, saudat tace "ke manta dashi, kinsan irin wannan mutanen, basa raina abun magana"
"aikuwa yajawa kansa dan sedana masa rashin mutunci naji dadi a raina" sukayi shewa gaba daya, uwar gidan malam munir tana jinsu tace
"khadija baki kyauta ba abunda kikayi"
Khadija ta murguda baki "ai dama banyi dan in kyauta ba, kinganni ba ruwana, da kusanci, ko girman mutum ana mun nake ramawa ehee"
"to Allah ya shirya"
"Ameen ya shirya abunda yafi hakama".
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, khadija tana gwara kan samari, yau ta wanke wannan gobe ta wanke wancan, ba wanda yake da ikon yin Magana, gefe dan wahalarta wato kabeer yanata faman wahalta mata, uwarsa da kannensa kuma ko oho.
Yau ake sa ran za'a kawo kudin auren kanwarsu khadija, wato surayya babbar yayarsu maryam tanatayiwa khadija da saudat fada akan su tsaida miji sudena wannan shiriritar, zumbura baki khadija tayi "waike Anty Maryam akanki muke zaune ne? Duk kinbi kin ishi mutane, itakanta surayya guda nawa take za'ayi mata aure, yarinya da kuruciyarta shekara iyanzu ta haihu, ga mijin shiba kudi ba, gaba wani ilimi me zurfi duk tabi ta tsofe da wuri" bude baki Anty Maryam tayi "lallai sannu khadija, surayya ce tayi yarinta da aure, kuma shi arziki na Allah ne ai, sannan ita ya mace darajarta shine dakin mijinta, ba gararamba a layi tana tara samari ba"
"eh ansan arziki na Allah ne amma ba wanda yakeson talauci ai, tara samari yanzu muka fara semun wankesu munci rabonmu mayi auren"
Saudat ta kwabe baki sannan tace "batta ai ita na fuskanci so take kowama yayi rayuwar wahala kaman yadda tayi, kuma babu wannan zancen"
Anty Maryam dataga abun nasu dagaske suke tace "to Allah ya baku hakuri matan masu kudi"
Khadija tace "Ameen Anty Maryam, Allah yabamu mutemakamuku tunda ku baku da rabo" suka kyalkyale da dariya itada saudat. Ana haka sega surayya ta shigo dakin goye da yarinyar Anty Maryam tace "Anty kinga humaira tayi bacci a bayana gaskiya na iya raino" Anty Maryam tace "Aikuwa dai kin iya raino, badi iyanzu in Allah ya kaimu Insha Allah kinkusa haifar naki" rufe ido surayya tai tace "gaskiya inajin kunyarki Anty maryam amma dai Ameen" dan zaro ido khadija tayi "au kekinayin auren zaki zage kiyita barin yara sekace kazar hausa"
Saudat da sauri tace "ganemin hanya dai"
Surayya tace "to meye a ciki yaya khadija, yara rahama ne bakasan wanda zaka huta dashi ba"
"Ai seki zage kibada himma, ga auren talaka ga haihuwa, nan da nan ki ragwabe akasa banbance tsakaninki da mamanki, kinga bari in tashi in je in abunda yake gabana wannan batamin rai zatayi" khadija ta fice daga dakin, Anty maryam ta girgigiza kai "Surayya kyale wadannan sunyi nisa basajin kira, se fatan Allah ya shirya". Haka rayuwa tacigaba har akayi bikin surayya, yayinda su saudat duka dorawa ransu dogon buri musamman khadija, bata saurarawa duk wani saurayi da yashigo hannunta, duk tsiyarka duk arzikinka seta wankeka sannan ta sallemaka, amma duk da haka tana tare da Kabir, sha wuyanta kuma yana cigaba dayimata hidima iyakar yinshi, ya wofantar da mahaifiyarsa da kannensa.
Kawayen saudat sun san khadija sosai, duk da kasancewarta me izza da jin kanta, ko kawayen kirki khadija bata da su se yaran manyan masu kudi, yaran masu kudin ma se yarinyar da akasan ubanta wanda ya tara dukiya sannan tayi kawance dake.
Ranar wata laraba suna zaune, saudat tayi bakuwa, kai daganin yarinyar kasan kudi sun zauna, saboda ba tayi kalar wahala ba, motar da aka kawota ma a ciki ba karamar mota bace, kawar saudat din me suna Salma ABDUL JALAL Tajudden, kawar saudat ce sosai tasanta da dadewa dasuka hadu a gurin wani biki, khadija tanajin sunan salma a gurin Saudat, tana bata labarin kudin da familyn su salma ke dashi, bayan Salma sun gaisa da mutan gidan, taciro iv card a Jakarta ta bawa Saudat tace "ga iv din nan, saudat dan Allah kizo gurin bikina saura three weeks" saudat tace "Insha Allah zanzo, ashe abun yazo yama za'ayi kice bazanzo ba bayan nayi duk ankon bikinki"
Salma tayi murmushi tace "Ainasan halinkine saudat, yanzu in bakiga dama ba sekice bazaki ba"
"zanzo Insha Allah"
"kinga bari inyi sauri, akwai guraren danake son zuwa, se anjima" har Salma ta mike zata tafi, khadija tace "Salma ni baza'a gayyaceni ba, anyway ina miki murna Allah yasanya Alkhairi" murmushi salma tayi "ni na isa, kema ga naki, ina gayyatarki yaya khadija" ta mikawa khadija iv, tasa hannu ta karba, bayan fitar Salma suka duba iv din nan, kwana bakwai cif za'ayi ana bikin nan, khadija tace "Saudat wai ita kam wannan wazata aura haka"
"mhmm yaza'ayi insani khadija? Najidai ance dan uwanta ne, boyeshi take kaman ciwo batason aganshi, iya sanina da ita tana son gayen nan kaman ranta, ko sunansa bata fada, kinga jikin iv dinma sunan tane kawai, Allah ya kaimu bikin dai muje muga wazata aura haka"
"Ainima dole inje bikin nan, dan naga alamar irin bikin da nake sone, dan haka dole a kece raini, muyi wanka kaman yaran senetes, inje inyi sababbin kamu" dariya sukayi gaba daya suka tafa. Kafin lokacin bikin Khadija tasa Kabir a gaba, seda yasamomata kudi kusan dubu arba'in ta sai less din dinner, ta dinga bin samarin ta, tana karbar kudi a gurinsu da haka seda ta sai komai sabo, tayi anko kafin lokacin bikin nan
Ranar da'aka fara biki, khadija da saudat sun dau wanka, kaikace sune dangin amaryar, khadija takira wani saurayinta yazo ya daukesu a tsaleleliyar motarsa, ranar kamu da bridal shower, da mother's evening duk ango bezoba, amma anci an sha, anyi barin kudade, kai dagani kasan wannan family sunci sun tada kai, naira ta koka a wannan bikin, gasu kyawawa kaman su sukayi kansu, daga mazansu har mata, gasu dayawansu ba farare baneba amma sunada matukar kyau, sunada dogayen hanci mazansu da matansu, wanda hakan ze tabattar maka family dayane, saboda suna kama da juna, khadija tayi samari a gurin bikin nan, saboda tayi kwalliya tayi kyau harta gaji, kaman uwa daya uba daya suke da amaryar, bangaren saudat ma hakane tasamu samari a gurin bikin.
Ranar dinner hall ya cika taro yayi taro, manyan mutane maza da mata daga bangarorin Nigeria sun halarci bikin, Mc yabada announcement cewar ango da amarya zasu shigo, nan aka shiga yimusu kirari "Ango Alhaji Habib kamal tajudden, matashin Attajiri me ji da kansa, me gwalagwalai da zinare, Ango kayi dacen amarya hajiya salma ABDUL JALAL Tajudden, me kyautar zinare da dama hagu bata saniba, me ado da sarkar zinare, abu naku maganin a kwabeku" haka aka cigaba da yimusu kirari tareda saka musu kida flower girls ne suka fara shigowa, se wasu kyawawan 'yan mata sannan ango da amarya a tsakiya.
Amarya da ango sun hadu, sunyi kyau harsun gaji, tunda khadija tayi tozali da angon nan tarasa nutsuwarta, ya hadu karshen haduwa bata taba zaton akwai kyakywa a maza irinsa ba, da farine toda tabbas zaka iya rantsewa kace bayajin hausa, wannan shine irin mijin datake tsarawa zuciyarta tana son aure, wanda bata taba zaton ganinsa a gaske ba, Habib ta maimaita sunansa a hankali kaman yadda taji Mc yafada dazu, gumi taji yana tsatstsafo mata a goshi. Shikam ango se fara'a yakeyi cameras kota ina se hotuna akeyimusu, Saudat ta janyo hanun khadija sukaje suka dinga hotuna da ango da amarya, bayan sun dawo gurin zamansu ne saudat tace "khadija kinga wannaan bawan Allah kaman shi yakera kansa, dan Allah ga kyau, wallahi yafita kyau sosai" da kyar khadija tace
"mhmm aikam dai yana da kyau" duk bata cikin hayyacinta, haka aka gama dinner din nan aka watse, a hanya khadija tacewa saudat "Sauda amma Salma ba hausawa baneba ko?"
"eh to rabinsu hausa rabinsu kanuri, yan borno ne, kasuwanci yakawo wasunsu kano"
"lallai kam, gasu da kyau gasu da kudi" haka suka cigaba da hira har sukaje gida,ranar khadija kwana tayi tana tunanin habib, tareda mafarkinsa.
Suncigaba dazuwa gurin bikin nan har akayi akagama. yayinda kullum khadija insukaje suka dawo, soyyaya da tunanin habib ya cigaba da ninkuwa a zuciyarta.
Ranar daza akai amarya, juyin duniya saudat tayiwa khadija akan suje kai amarya tace bazata ba, tun tana lallabata har itama ta hakura tace tafasa zuwa gurin kai amaryar, taje daga baya, in Salma ta tare. Ranar Khadija ta kwana da matsanancin kishin Salma, kasa bacci tayi daren ranar dan tayi mamaki yadda kaunar habib ta mamaye zuciyarta lokaci daya haka, haka ta kwana sake2 da tunani har gari ya waye. Koda gari ya wayema bata fito tsakar gida ba tana tana kan gado tana juyi Saudat ta shigo dakin tazauna gefen gadon ta kalli khadija tace "yar uwa tashi muyi wata magana kibani shawara dan Allah" khadija ta kalli saudat idonta duk yayi ja alamar rashin bacci, ta mike zaune ta dan yatsina fuska ta kalli saudat "fadi inajinki?" Saudat ta gyra zama tareda kallon khadija sannan tace "Khadija nifa tunda mukaje bikin salma, nayi ido hudu da mijinta naji wallahi inasonshi, shiyasa nazo kibani shawara yazanyi, Dan gaskiya bazan iya hakuri ba, bazan iya auren kowa ba seshi, dan Allah sister bani shawara ta ina yakamata in fara?"
Gaban khadija ne yafadi, zuciyarta ta shiga bugawa da karfi, ga wani gumi dayake tsatstsafo mata a iya goshinta, taiwa Saudat wani irin kallo, sekuma tayi murmushi seda hakoranta suka fito, ta kalli saudat" Kin tabatta kinason Habib? " da sauri Saudat tace" Wallahi khadija so bana wasa bama, wallahi ina sonshi, aurensa nakesonyi" khadija ta gyada kai takuma yin wani murmushi



Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 1️⃣7️⃣70_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]


_MY FIRST NOVEL _

Ta dafa kafadar saudat "bakida damuwa zanyi meyuwuwa inga burinmu yacika, amma kisani dole abu daya yafaru, ko kiyi nasara, kokuma akasin haka" "hakane amma ni nafi sa ran nasara dan kome zefaru sedai yafaru"
"gara kidinga sawa ranki nasara da akasin haka, yanzu dai macigaba anjima, inada abunyi yanzu"
"to shikenan bari zan dan fita dama, sena dawo"
Saudat nafita khadija tabi bayan saudat dawani mugun kallo, sannan tayi kwafa "gaskiya Saudat bakida hankali, kekin isa inso abu kema kice kinaso, zakiga tsiya dake zanyi tarkon cikar burina, ita kanta Salma seta barmin Habib" ta sakeyin kwafa ta nemi guri ta kwanta.
Sati daya da kai Salma gidan habib, Saudat ta shirya taje gidan Salma, ba karamin tsinkewa Saudat tayi ba da ganin aljannar duniyar dake gidan Salma, gidane na alfarma kaman ba a Nigeria ba, ga shi an kashe masa kudi da kayan alatu, haka Saudat ta sake taita kallo tana video gidan dan ta nunawa Khadija, bangaren kayan Abinci ba a magana, tasamu kyakyawar tarba daga salma, ta karramata da kayan Abinci sukayita hira Saudat tace "Salma kawo in turamiki hotunan da nadingayi miki lokacin biki" ba musu Salma tabawa Saudat wayarta, tana cikin yimata turi ta faki idonta ta dauki lambar Mijin Salma wato Habib, haka suka dinga hira se la'asar sannan saudat ta tafi, saudat taso taga habib amma bata ganshiba salma tagaya mata baya gari.
Tunda saudat taje gida tana rawar jiki taje tasamu khadija tadinga nuna mata video gidan salma, gaba daya khadija ta rikice da ganin aljannar duniya, tabbas habib shine mijin daya dace da ita,
Daga nan ta nuna mata ta samo lambar Habib "khadija ga lambarsa na samo ta ina yakamata in fara"
Hanzarin me kike ne, ba tace miki baya gari ba, kibari se kaman nan da sati daya mana maybe lokacin ya dawo"
"anya zan iya jira har sati kuwa, nifa banki ace ko a satin nan a daura aure ba dan ba karamim so nakeyiwa gayen ba, kokuma ince nakewa dukiyarsa ba"
Khadija ta jinjina kai tace "to wai yazakiyi da kawarkine, in ta gane zaki aurar mata miji" tsaki saudat tayi "wayake tawani matarsa, ai ranar biyan bukata rai ba a bakin komai yakeba, indai buri zecika, to babu batun kunya da cin amana, inma ta gane ita tasani nidai fatana in ganni a cikin wannan daukar" "hmm Gaskiyar ki yar uwata, Allah ya ida nufi"
"Ameen khadija, ammafa in Salma tagane ba karamin hauka zatayu ba, dan tana masifar son gayen nan, gata da kishi kamar bala'i, amma tasamu dai dai da ita indai nice" murmushi khadija tayi
"gaskiya zata taro match kishi da hajiya Saudat" sukayi shewa gaba daya.
Kwana biyu da zuwan saudat gidan Salma, khadija ta shirya tun safe ta fita ashe wayar saudat ta dauka tun dare ba wanda yasani, ta fita ta cire sim din saudat tasa a wayarta ta dauki lambar Habib, sannan ta kakkarya layikan saudat ta zuba a kwata, sannan ta jefar da wayar tai tafiyarta, bata koma gida ba se bayan magariba yaje ta tarar anata jimamin wai barawo yashigo gida jiya da daddare yasace wayar saudat, ta shiga sahu akaita jajantawa saudat, saudat tabiyo khadija dakinta kaman tai kuka tace "wallahi khadija ba batan wayatane yabani haushi ba, rasa lambar habib itace ta konamin rai"
"don't panic dear, karki damu, inkika canza waya seki kuma samo lambartasa, aibawani abu a ciki"
"haba khadija kinsan da yadda nasamo lambar nan kuwa idan nakoma mezance mata inkuma karbar wayarta, kuma kwata2 yaushe naje gidanta dazan koma" ta karasa maganar kaman zatayi kuka
"haba saudat kefa kikace ranar biyan bukata raiba abakin komai yake ba, amma kibari kaman in akayi sati biyu sekikuma zuwa, kinga ba wanda ze zargin wani abu"
Saudat ta kalleta "haba khadija har sati biyu, anya kuwa zan iya jurewa"
"Saudat idan kikabari matarsa ta gane zaki aurar mata miji to tabbas bazata kyaleki ba, gara kibi komai a sannu in lokaci yayi taji"
Saudat tayi nannauyar ajiyar zuciya tace "kuma kinyi gaskiya khadija, shiyasa nakeson shawarwarinki nagode sosai, bari anjima Mukhtar zezo se in sashi yakawomin wata wayar"
"eh hakan ma yayi kyau"
"hakane nagode bari inje inyi salla" tana fita khadija tai murmushin mugunta.
Khadija tasa kabir yasiyo mata sabon waya, me madannai tayi saving lambar habib a ciki, kullum safiya da dare seta tura masa zazzafan text messages da addu'oi , hakama da daddare zata tura masa bata taba kiransa a waya ba, shima kuma betaba biyowaba balle yaji waye. Amma habib yana mamaki wacece take turomasa wannan messages haka, shidai yasan ba Salma bace bata da wannan lambar, kuma tunda sukayi aure bata yimasa tex kamana yadda take masa kafin suyi aure, amma bari ya tambayeta ko itace take turo masa, salma na gaban mirror tana taje kai, habib yana kan gado a kwance ya kalleta yace
"my sweet lambobinki nawane?" kallonsa tayi "meya farune??"
'No bakomai na tambayeki ne dai"
"fadamin gaskiya ko watace take kiranka ka zata nice" gabansa ne ya fadi ya kalleta, amma yakasa magana a hankali ta tako tazo ta zauna a kusa dashi tace
"yanaga ka tsorata, nafada dai2 kenan"
"A' a kam kinbani mamakine kawai, daga tambaya kin canzamin magana, kaman kina zargina"
Tayi Ajiyar zuciya "Habib kada Allah ya nunamin ranar da wata mace zata dinga kiranka, amatsayin budurwarka, inaga a wannan ranar se zuciyata tayi bindinga, bazan iya jure ranar dazanyi sharing dinka da wata mace, inasonka habibi da'iman" seda cikin habib ya duri ruwa, amma ya dake yace
"I love you too hibbaty, karki damu zuciyata kekadai ce a ciki, zan rayu dake har zuwa karshen rayuwata" yai mata murmushi tareda yin kissing dinta a goshi, ta dora kanta akan kirjinsa tanata ajiyar zuciya, message ne yashigo wayarsa, yasa hannu ya dauka ya bude message ne na nuna tsantsar soyayya da kauna da khadija ke turomasa, sauri yayi yasa lambar a blacklist, ba tareda salma ta dago ba tace "habiby waye ya turomaka message?"
"Alert ne, kayan dana siyar aka turomin kudin" har cikin ranta ta yadda da abunda yace.
Haka khadija takuma canza layi tacigaba da turawa habib messages baji ba gani, abunne yafara damun habib kar by mistake Saudat tagani, gashi layinsa ne dayakeso wanda huldodunsa na kasuwanci duk akai suke da se ya cire layin ya yar, besan mezece ma Salma idan taga wannan messages dinba, dan Yasan halinta da mugun kishi, yanzu se cibi yazama kari, ba dan haka ranar ya yanke shawarar yakira yaji kowacece, da safe wajen karfe goma khadija tana kwance tanata tunanin habib tana kallon hotunansa, karamar wayarta datake kiran habib da itane tafara ringing, ga mamakinta taga Habib ne nannauyar ajiyar zuciya tayi tareda yin murmushi ta rungume wayar a kirjinta tanajin ringing din wayar harcikin zuciyarta, wayar tayita ringin harta katse bata daga ba taitajira koze kuma kiranta amma be kirata ba. Kusan kwana uku bekuma kiranta ba itamuma tacigaba da turamasa, rana ta ukun da daddare yakuma kiran wayar khadija seda ta kusa tsinkewa, sannan khadija ta tattara duk wata nutsuwarta ta daga wayar, tana dagawa kafin tayi magana a fusace yace "wai dan Allah wacece haka, kina nema ki hadani fada da matata meye hakane, karki kara turomin wannan rubbish din nagaya miki" maganganunsa sunyimata zafi, amma ta dake tace "ohhh masha Allah, zanyi bacci irin wanda bantabayiba yau habib, naji muryarka Ina sonka, kayi bacci me dadi kaman yanda zanyi cike da farinciki" tunda tafara magana gaba daya jikinsa ya mutu yakasa cewa komai, itama bata jira meze ce ba ta kashe wayarta, tace "Lallai Habib bakasan wacece khadija ba bazaka taba kufcemin ba tunda kayi gangancin kirana" khadija bata taba gajiyawa ba gurin yi masa aiken zafafan kalaman soyayya.
Yau sati biyu cif tacika da zuwan saudat gidan Salma, tun karfe goma na safe ta shirya, tazo tayiwa khadija sallama cewar zataje gidan Salma, ita khadija ta manta ma cewar sunyi da khadija yau zata koma gidan Salma, khadija ta dake taimata fatan nasara, bayan ta fitane ta dinga mata dariya. Koda saudat taje gidan me gadi yasanar da ita cewa masu gidan basanan sun tafi Abuja karfe 2narana zasu bar Nigeria zasu wuce Dubai, Saudat jitayi kaman ta dora hannu akai tayi ihu, tacewa me gadin "dan Allah yayana kozaka temakamin da lambar me gidan?" zare ido yayi "lallai da alamu kina da tabin hankali yadda tsaro yayi karanci zakice abaki lambar megida, to ni kaina bani da lambarsa, seta PA dinsa, se in abun me mahimmanci ne sannan ya hadaki dashi kuyi magana, inkuma bame mahimmanci bane ba yakamaki yace bakida gaskiya, indai baya gari tokomenene hakura nake"dafe kai saudat tayi takuma cewa" dan Allah kabani lambar P. A dinnasa mana" "waike wace irin mayyace ne, bar kofar gidan nan ko inyi waya azo a tafi dake wallahi" "No yi hakuri zan tafi, insun dawo senazo" daga nan ta juya ta taho gida, tareda tsinewa barawon dayasaci wayarta albarka, tasamo lamba a bagas an sace wayara haka ta dawo gida jiki a sanyaye, kallo daya khadija tamata tagane babu alamun nasara, nan Saudat tabawa khadija labarin abunda yafaru taita rarrashinta tareda bata karfin gwiwa kaman gaske. Khadija takoma daki ta tsarawa Habib text

"Hayateee ashe zakabar kasarnan ba labari, masoyi masoyine ai at least yakamata in sani ai, Allah yakaika lafiya, yatsaremin kai yakareka ya kare dukiyarka, Allah ya albarkaci neman ka, ya doraka akan makiyanka, dukda ni baka damu daniba amma ni kullum soyayyarka ninkuwa take a zuciyata, gangar jikina tana Nigeria, zaka tafi da rayuwata Dubai, kaine rayuwata habib ka kulamin da rayuwata, zanyi

Please Login or Register in order to submit comment