Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Yallabai yau akwai ruwa da kankara kaine a kamfani yau, rabonka da nan shekara nawa?"
Murmushi Jalal yayi yace "Ya aikin?"
"Lafiya kalau anata fama"
Jalal yace "Masha Allah hakan yayi kyau"
Daga nan yai gaba Jalila tacigaba da binsa, wata katafariyar kofa sukazo Jalal yasa hannu a aljihunsa ya dakko key yabude kofar ya kalli Jalila yace "Bismillah" tareda yi mata nuni da cikin gurin, jiki a sanyaye kuma a matukar tsorace ta shiga ta tsaya a bakin kofar tana rarraba ido, Office ne dankarere, sekace na hamshakin sarki ko gwamna, babu abunda babu a ciki, idonta ne ya sauka akan hotunan dake cikin Office din, akwai hoton shugaban kasa, gwamna da na sarki, sekuma hoton Daddyn Jalal, ta juya daya bangaren tangamemen hoton Jalal ne da Jawwad sanye da kaya iri daya sunyi murmushi an rubuta J&J global concept, sekuma hoton Jalal shikadai, ba karamin kyau yayi a hoton ba Ganin da Jalal yayi a tsorace take ta takure a tsaye, ya maida kofar ya rufe yasa mata key, kallonsa Jalila ta tsaya ta nayi a matukar tsorace hankali yace "muje ko?"
"ni ba inda zani, ka maidani makaranta zan tafi fa"

Baya kaunar wannan gaddamar ta Jalila dan haka be tsaya bata lokaci ba ya danko hannunta da karfi, hakan yasa ta saki wani uban ihu saboda zafi, hannun dayake mata ciwo ya rike, a tsorace ya cikata yana kallon yada tuni ta rike hannu tana Hawaye
"Meye haka? Sekace wadda nayiwa wani abu" ya fada adan gigice

"eh dole kace haka mana, jiya ba kai ka hankadeni na fadi akan hannun ba, yana min ciwo shine ka famamin" Jalila gaba dayanta shagwababbiya ce

Dan shiru yayi yana kokarin tuna abunda ya faru shi gaba daya ya dauka a mafarki abun ya faru ba gaske ba yace "Ok naji amma yanzu zauna"
Guri ta samu akan kujera daya ta zauna, yace "zan iya ganin hannun?"
"Bazaka gani ba" ta fada tareda janye hannunta
"Shikenan tunda kimce bazan ganiba, am sorry, ban san nayi miki ba, a tunanina mafarki ne, idan kinga na shiga wannnan yanayin kidena zuwa inda nake, kome zanyi karkiyi kokarin hanani, in bahakaba wataran zan iyayi miki illa"
Dan kallonsa tayi tace
"to meyasa kake hakan?"
"Nima ban saniba, haka kurum nake tsintar kaina a wannan yanayin, Jawwad ne kawai ya damu da halin da nake shiga, Mummy da ba damuwa tayi daniba, tana ganin kawai shaye2 danake ne ya janyo min hakan, dayawa idan nayi kokarin dena shaye2, kokuma raina ya baci, se in shiga wannan yanayin "
yayi maganar cike da damuwa, cikin tausayawa tace
" Ka dinga yawaita Azkar, kuma ka kulada ibada zaka dena jin abun insha Allah"
"bazan iya ba" ya fada kai tsaye
"Meyasa bazaka iyaba?"
"Har yanzu baki gama sanin waye ABDUL JALAL ba dukda yanzu kinsan abubuwa da yawa akaina fiye da iyayena, just keep praying for ABDUL JALAL, and I really appreciate your efforts on me, Thank you, Allah ya jikan Abee"
Jinjina kai tayi amma takasa magana,
Can tace "dan Allah me nayiwa Mummy? Na gaisheta dazu da kyar ta amsamim tace inje tana son ganina, Allah yasa ba laifi nayi mata ba?"
"meyasa kike tunanin laifi kikayi mata?"
Hawayene ya zubo daga idonta, shi Jalal har mamaki take bashi, kaman shan ruwa haka take kwararar da Hawaye, basa mata wuya sam tace

"Yanzu duk lokacin dana motsa ko nayi wani abu se ansamu wanda zasuce na musu laifi, kowa ya tsaneni komai nayi laifine, mutane kalilan ne suke sona A duniyar nan, daga masu kirana munafuka, se makira, barauniya, karuwa, Arniya se masu cewa uwata ta gudu ta banni, ba ataba barina inyi awa24 cikin farinciki se an samu me batamin rai"
Takarasa maganar cikin kuka muryarta na sarkewa, tasa hannunta biyu ta rufe fuskarta tana kuka me tsuma zuciya, Jalal jin kukan nata yake a kahon zuciyarsa, yaji gaba daya komai ya kwance masa, yace

" Kidena kuka mana, kin manta ke kikemin nasiha amma yanzu kike kuka, Allah baya mantawa da bawansa, Allah yasan halinda kike ciki, ni da nake gabanki a yanzu na isheki misali na isheki darasi, ba'a nasara ba tareda an sha wahala ba, kisawa ranki matakin nasarar kine kike takawa, duk wanda yayi miki gori a rayuwa ko ya cutar dake kisa a ranki kinfi shine, Allah yana son bayinsa masu hakuri, semene dan duniya batayi dake in har ubangijin da yayiki yanayi dake shikenan, kiran da Mummy tayi miki karki sake kije, bashida wani amfani na gaya miki"

Ya mike ya nufi wata katuwar drower ya bude, ya duba ya debo wasu takaddu yazo gabanta ya zube su yace "dauki wannan takaddun, ki dubamin abunda za'a iya nema a gurin, zanyi breakfast yanzu"
Yakoma kan kujera daya yazauna ya fara cin Abincin sa daya siya dazu, Jalila tasa Hannu tana duba takaddun, duk na makarantun da Jalal yayine, abun mamaki results dinsa sunnuna shi din kwarone, kuma duk an masa kyakykyawan yabo a jikin results din, daga ido tayi tana kallonsa yana cin Abincin sa hankali kwance, ba ita yake kalloba amma taji yace
"Ya dai kike kallona? Ko zakici ne?" girgiza masa kai tayi alamar A'a, tareda maida hankalinta kan Takaddun gabanta
Yace "Au Ashefa bazaki iya cin Abincin hannun dan iska ba, karkije na zuba kwaya a ciki ko?"
Shiru tayi masa yagama ciye ciyensa, ya mike yana kuma duba wasu takaddun, yaji muryar Jalila tace
"wai Inane nan?"
"Kamfanina ne?" ya bata amsa
Zare ido tayi, ya kalleta yace
"kina mamakine? Nawane mallakina, akan wannan dukiyar ne aka halakar da rayuwata, dukiya mugun abu me halakar da mutane, me haddasa gaba da kiyayya, me tafiya da Imanin ma'abota kwadayinta, Akan dukiya Mummy tayi cin amana tayi yaudara ta auri daddy,
Akan dukiya Mummy ta ajiyeni tayi tafiyarta lokacin da nake bukatar taimakon ta,
Akan dukiyar akabada kwangilar ruguza rayuwata, Akan dukiya Mummy ta rabu da mutane dayawa, Akan dukiya da daukar fansa aka halakar da rayuwata,
Ilham da mahifiyarta suna son su dauki fansa akaina ne su gaje dukiyar dana mallaka, itakuma Mummy takasa fahimta, tunda suka kyalla ido sukaga Daddy yasayi kamfanin nan yabani, suka kasa nutsuwa, ke sheda ce, Kinsha kama Ilham na kokarin samin magani a Abinci, kuma ta dade tanayi min hakan saboda dukiya, Akan dukiya.......

Sekuma yayi shiru ya dafe teburin gabansa yayi shiru, gaba daya Jalila ta zuba masa ido, jin yadda yake sarrafa magana daki daki ta sigar rarrashi da wa'azi, ko a mafarki in wani ya gaya mata Jalal ze haka karyatawa zatayi.

Yacigaba da cewa "Ban taba kukan babu a rayuwata ba, babu innemi abu in rasa ban taba ba, bansan talauci ba, Amma nidai wannan dukiyar da taza memin bala'i, gara ace talaka futik Mummy ta aura in tsira da mutuncina, A rayuwa bazan manta da mutanen dasuka soni dan Allah ba, family dinku mutane ne masu mahimmanci a rayuwata, kinga Jawwad na yadda in rasa duk abunda na mallaka saboda shi, Yana sona badan dukiya ta ba, duk abunda zamuyi baya sako lissafin dukiya ta, bayan Umminki da Jawwad ban taba zaton zan samu wanda ze tsaya akan lamarina ya damu dani kamar ki ba, bana manta Alkhairi, kinmin abunda banida abun biyanki, dukda bakida kunya, ga taurin kai da tsaurin ido, ga rashin kunya da iyayi, bazan manta yadda kike putting rayuwarki a risk saboda dan iska mara tarbiyya me kama da 'yan daba, dan daba yana godiya" ya karashe maganar yana kashe mata ido,
Murguda masa baki tayi ta dauke kai, ya danyi murmushi yace "Ai bazaki taba canza hali ba"
Ya kwashi takaddunsa ya mayar da sauran yace mata "Tashi mu tafi" ta mike tayi gaba yazo ya bude kofar suka tafi, sosai Jalal ya dingayiwa ma'aikatan nan barin kudi kaman besan ciwonsu ba.
Suna cikin tafiya Jalila tace "Amma meyasa baka zama a kamfanin, at least you will keep yourself busy zaka manta da wasu abubuwan" dan shiru yayi sannan yace
"Ta yaya ina cikin wannan halin zanzo inyi aiki, Akwai manager kamfanin nan dan abokin daddy ne shike kulada komai, duk lokacin danazo na zauna da sunan zanyi Aiki se wannan abun yasa meni, idan na birkice senayi barna sosai kafin in bar gurin, wani lokacin har illa nake wa wasu, shiyasa wasu ke kallon ko inada tabun hankali, kokuma illar shaye2 ne, rabona da gurin nan nafi shekaru goma, yanzun ma saboda takaddun nan nazo, kuma abun mamaki naga nashiga na fita lafiya yau saboda muna tare da ke"
"To Allah ya baka lafiya, Amma yakamata kanemi magani sannan ka dinga Addu'a"
Tasa hannu ta cire farin carbin counter dake hannunta ta ajiye masa tace "ka dinga Amfani dashi, ze temaka maka" Be iya cewa komai ba se kallon ta da yakeyi, har Jalila manta data bashi sekuma taji yace
"Thank you" itama banza tayi dashi taki kulashi.
Haka suka cigaba da dan taba hira har sukazo makarantar, zata bude tafita yace "tsaya, wai ke wannan ce jakar makarantar?"
"Eh mana" ta bashi amsa
"wannan ba jaka bace sekace Jakar tara kudin bara, ina litattafan karatun?"
"Jakar tara kudin maulace bata bara ba" Ji yayi kaman ya tuntsire da dariya amma ya fasa, yasa hannu ya dau Jakar ya bude jotter ce se biro da kudinta dari biyar se waya, yasa hannu a Aljihunsa ya dakko kudi yasamata ya mika mata, ta kalleshi "Ni inada kudi cire abunka"
"Fitarmin daga Mota ko insa lock inyi gaba dake wallahi" Hannu tasa tana kokarin cire kudin ta ajiye masa yace
"Bana kyauta amayarmin, karki bari raina ya baci fita ki barmin mota, mara kunya"
Ikon Allah yanzu suka taho girma girma cikin mutunci amma se wani korarta yake kaman rokarsa tayi, ta hade rai ta bude motar sannan tace masa "Allah yabada sa'a"
"Ameen" ta rufe masa motarsa tayi gaba.


Maama fa hankalin ta ya kai makurar tashi, idan tace zata tsananta maganar nan zata iya rasa Aurenta, dan haka ta nufi part din Abba dan ganin ta inda Zata bullowa Al'amarin, Amma ta tarar yayi ficewarsa, takoma daki tanata nazari, daga baya ta yanke shawarar gayawa Naja halin da'ake ciki, takira Naja dakinta ta sanarda ita abunda ake ciki, Amma bata gaya mata batun Abba yace tabar masa gidansa ba Aikuwa take Naja tafara ruwan bala'i "Harni za'a ciwa mutunci dan tsabar wulakanci da cin fuska, Akaimin kudin Aure in fara shiri sannan ace anfasa saboda tsabar rashin ilimi, wannan ai halin banzane da Jahilci" Maama na kokarin yiwa Naja bayani amma taki saurararta tayi ficewarta, taje ta kira Yaya mairo a waya tana kuka gaya mata, ai tun daga wayar Yaya mairo tafara surfa zagi ta inda ta shiga bata nan take fita ba ta cewa Naja gata nan zuwa gidan.


Jalila test kawai tayi ta dawo gida, dan har yanzu bata jin karfin jikinta sosai tanata nazari akan Jalal, mutumin daya mallaki wannan dukiyar mezeyi da wannan Aikin? Amma akwai ayar tambaya game da Al'amuran nasa, wani lokacin har mamaki yake bata in yana abun Arziki kaman bashi ba, kuma babban abun mamakin dukda yadda Jalal yake wasa da ibasa, yake shaye2 hakan besa dukiyarsa rashin habaka ba, haka taketa tunani harta koma gida,
Amma abun takaicin tana zuwa gida ta tarar da wannan rigimar da akeyi, Hakan ya tabattar mata dasu Jawwad sun dawo, muryar Yaya mairo data jiyone yasa gabanta faduwa, dan sam bata kaunar matar nan, Jalila tana ta Addu'a ta shiga palourn, ta tarar Naja tanata kuka, yayarta sa'ada tana rarrashin ta, Maama tayi zugum Yaya mairo tana sirfa mata bala'i, Jalila tayi sallama ta maze zata wuce, Gaba daya suka dawo kanta da zagi da cin mutunci da tsinuwa, ai kawai tayi kamar kujeru ne kawai a palourn ba mutane ba, ta shige daki ta canza kaya abunta, tayi tunani a ranta muddin tacigaba da zama a yanzu, zasu cigaba da zaginta ne itakuma bazata hakura ba, dan ba shiru zatayi musu ba mussaman in aka hada da cin mutuncin iyayenta, dan data san abunda zatazo ta tarar kenan da bata dawo gidan yanzu ba, ta mike tasa hijjabinta, takuma zuwa ta ratsasu a palour tayi ficewarta tana jinsu suna ita ta haddasa komai ita tayi munafunci batabi takansu ba takara gaba. Tana fita motar Abba ta shigo layin dan haka tayi murmushi aranta tace "yau gidanmu akwai drama" ta tsaya tana jiran karasowar Abba, ya karaso kofar gidan yayi parking cikin fara'a tace
"Abba saukar yaushe?"
Shima cikin fara'a yace "Ai tun karfe goma muka dawo, na dan fitane nayi wani uzuri"
"Masha Allah, sannunku da Hanya, amma tunda na dawo ko Yaya Jawwad ban ganiba"
"Ina zaki ganshi dama? Yana can farinciki ne ya hanashi fitowa Jeki aiken da'akayi miki ki dawo Akwai albishir masu yawa, babyn Ummi"
Cikin murmushi tace "to shikenan bari inyi sauri in dawo" tafada cike da zakuwa, Abba ya shiga gida, se yanzu tafara tunanin ina zata? Kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Mummy taji laifin da tayi mata, dukda Jalal ya gargadeta akan yin hakan.
Tana shiga gidansu Jalal ta tarar da motarsa, abun ba karamin mamaki yabata ba, Anya kuwa yaje interview din? Ta tambayi kanta, taga moyar Mummy dasuka fita dazu alamar sun dawo, haka tayita wasi2 harta shiga cikin gidan, palourn ba kowa tayi sallama amma shiru tasamu guri ta zauna akan kujera, wata yarinya da take musu aiki tacewa dan Allah tayiwa Mummy magana, seda Jalila tayi kusan mintuna goma shabiyar sannan taga Mummy ta fito, da fara'a Jalila tace
"Mummy ina wuni?" Mummy tace
"rike ina wuninki, na baya da kikayi ma sun isa, Allah ya amfana" nan take Jalila ta sha jinin jikinta, Mummy tasamu guri ta zauna ta dubi Jalila a wulakance tace
"Dama na kiraki naki dan inyi miki kashedi akan ďana, sannan in soke haramtacciyar alakar da take tsakanin ku" cikin rashin fahimta Jalila tace "Mummy haramtacciyar Alaka kuma?"
"Eh haramtacciya mana, ko ta halatta ne? Tunda yake jin maganar ki fiye da tawa ai dole akwai abunda ke tsakanin ku, da kike masa Ilham ma sheda ce"
Nan Mummy ta ware ta kwalawa Ilham kira, Ilham ta fito tana ganin Jalila ta ya mutsa fuska kaman me shirin yin amai dan taga kashi, Ilham tazo ta zauna tace "Mummy gani"
Mummy ta nuna Jalila tace "gata nan nace Akwai haramtacciyar alaka tsakanin ta da Jalal amma ta karyatani"
"Mummy ai kinsan ba mutunci ne da ita ba tunda bata san darajar manya ba, tarbiyya ta mata karanci"
Mummy ta gyara zama tace "Ina bukatar duk wata alaka dake tsakanin ki Da Jalal tazo karshe a yau, kiyi nisa da dana, ba ruwanki dashi kome ze aikata, ai ba fina sonshi kikayi ba, a palourn nan agabana kinsha kiransa mara tarbiyya, lattace, kuma dan rashin kunya seki lallaba kina kokarin kara lalata min shi bayan abaya duk fitinarsa ba Ruwansa da mata, Amma kina kokarin kizama se abunda kikeso shi zeyi ni uwarsa ban isa dashi ba seke?" Jalila shiru tayi ta sunkuyar da kai ko tari kasa yi tayi
Ilham tace
" Wallahi Mummy na sha ganinsu suna rungume juna, kuma har part dinsa take zuwa dakin sa, in karya nayi ki karyatani mana munafuka, Kuma...... Setayi shiru takasa karasawa, sakamakon saka idonta da tayi a na Jalal dayake tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa, ba Ilham ba hatta Mummy seda ta tsorata, cikin is da Izza yace "Kuma me? Karasa mana"
Zazzaro ido Ilham tafara yi, jin muryar sa yasa Jalila daga idonta sukayi ido hudu takuma sunkuyar da kai.
Yakara so cikin palourn ya kalli Mummy sannan ya maida idonsa kan Ilham yace
"ki karasa maganar ki ina jinki, ke dan baki da kunya har kin manta ke abunda kika dinga yimin abaya ko danni bana zuwa ina fada, wato kin manta lokacin da kike kawomin kanki har part dina in dare yayi ko?" zare ido Ilham tayi tafara kokawa da numfashi, bata taba tsammanin ze iya fadar hakan ya tona mata asiri ba
Ya kakkafe Ilham da, ido yace
"koba ayi bane?" kasa magana tayi se wani gumi data dinga jinsa yana ratsa cinyoyinta, ya maida idonsa ga Mummy yace
"Kinji kunya, 'yar cikinki cefa, yarinyar data dingayi miki biyayyar dani da kika haifa ban miki ba, ita kikewa wannan bakaken maganganun, meye da ďannaki da za' a dinga, binsa, niba hankali ba niba tarbiyya ba, sedai abini ko asoni dan dukiya ta amma bani da abunda mace kamar Jalila zata bini sedai irinsu Ilham dabasu san ciwon kansu ba" gaba daya suka zubo masa ido, da sauri Jalila ta mike tayi hanyar fita, jin yana kokarin janyo mata bakin jini tana fita ya rufa mata baya,
Ilham tace "Wallahi Mummy Jalal karya yakemin, ni ban taba kai masa kaina ba, Mummy dan Allah kisa baki ya Aureni, wallahi Asiri tayi masa"
"ke dalla rabu dani niba wannan ne ya dameni ba, kina gani yake gaya min magana akanta, ashe har an samu uwar data haifi wadda zata mallakemin da, ya gayamin magana akanta? Baze yuwu ba wallahi, se na dau mataki akansa da ita kanta"

Ilham ma mikewa tayi tabi bayan Su Jalal dan ganewa idonta meze faru, ayita ta kare a yau.
Har suka fito harabar gidan yana kiranta taki tsayawa, seda yasa hannu ya fizgota sannan ta tsaya
"Jalila meye haka? Ina miki magana kina jina kinki tsayawa, uban me yakawo ki bance karki zoba dama?"
Cikin kuka tace "Dan Allah malam kadena min shouting, meye Amfanin abunda kayi? Zaka sa mahaifiyarka da kanwarka su kara tsanata, Mahaifiyarka tace batason ganina tareda kai, ko a hanya karka kara nuna ka sanni, bani ba kai, kayiwa mahaifiyarka biyayya kanemi Aljannarka, dama ba wani abune tsakaninmu ba mutunci ne da girmamawa tunda bata so shikenan "
Gaba daya idon Jalal yayi Ja, a hankali yace
"kince kowa yaje yayi rayuwarsa ko? Kinfison in kara komawa cikin harkar shaye2 kenan kaman yadda nake abaya? Ke Garkuwa ce a taredani me kike tunani idan kika barni, sanadiyar kasancewar ki tare dani yasa ina kara kokarin yaki da shaye2 da nake abaya, kina tunanin inkika min haka kin min adalci? "
" Kayi Rayuwarka inyi tawa, yafi adinga min kallon mazinaciya, zancigaba dayi maka Addu'a a duk inda kake, Amma bani ba kai ko a hanya balle a cigaba da zargina"

Tofa!


Masoya kaunar da nake kumu tasa nai muku dogon page gashi nan, senaji Comments dinku love you all
😍😍😍🌹❀️❀️❀️🌹🌹🌹🌹

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 4️⃣3️⃣96

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724




_MY FIRST NOVEL _




Juyawa tayi ta fice da sauri tana goge hawaye, Ilham dataga duk abunda yafaru tayi wani tsallen farinciki, amma da tuna irin tonon sililin da Jalal yayi mata dazu se taji jikinta yayi sanyi ta juya da sauri ta koma gida.

Jalal bashida zabi da ya wuce ya bar gurin shima kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yakoma part dinsa, zuciyarsa kaman an kunna masa wuta saboda bacin rai, side bed dinsa ya kalla yaga Alqur'anin nan da kuma teddyn Jalila a gurin, a hankali yace

"do she really mean what she said, zata barni gaba daya, bani ba ita? Jalila why? karkimin haka mana, nasan ba'a kyauta miki ba, Amma kar laifin Mummy ya shafeni"
ya zauna a gefen gadon sa ya rintse ido, ya dinga tuno moments dinsu tare, da fitar da sukayi dazu, ji yayi kansa yana juyawa zuciyarsa ta masa nauyi, ya kunna sigari yafara sha, ya sha takai kara biyar amma beji yadda yakeso ba seda ya dakko merlot red wine ya sha ya fita daga hayyacinsa sannan ya yada kwalbar a gurin shima ya zube.

Ita kuwa Jalila seda ta samu guri a cikin flowers tayi kukanta ta gode Allah sannan ta nufi palourn gidan, tunda ta shiga ita dai taji Abba yana bayani yayinda Yaya mairo keta haya gaga, sam Jalila bata gane me suke fada danji take kaman zata fadi ta wucesu ta shige daki ba tareda ta kula kowa ba, tana zuwa ta haye gado ta ja blanket ta cigaba da kuka da kuma tunani, shikenan yanzu kuma kallon mazinaciya mahaifiyar Jalal take mata? Gaskiya tsakanin ta da Ilham se Allah yasaka mata, amma ba komai zata rama ne, zatayi wa Ilham daurin da bata isa ta kwance ba"


Jawwad ya farka daga baccin dayake cike da farinciki ya tashi yayi salla, sannan ya nufi cikin gida dan ganin Maama dakuma 'yan kannensa dan yasan zuwa yanzu sun dawo daga school. Yana fitowa manu direba ya shigo harabar gidan da mota, ya jira manu yayi parking Nana ta fito daga motar kallo daya zakayi mata kasan a gajiye take, se jefa kafa take kawai tana ganin Yaya Jawwad ta yalwata murmushinta tareda fadin "Oyoyo mutan Bauchi, Ashe kun dawo?"
"Mun dawo Nana, ya school din? Naganki ke kadai ina Jalila?"
"Yaya Jawwad kasan Jalila manyan kwarine, yau bataje school ba, amma ancemin angan ta dazu ta shiga zasuyi test"
"Shikenan mukarasa ciki, yau Akwai Albishir masu dadin gaske, muje in gaida Maama tukuna" suka jero tare zuwa cikin gida.

Abba yace "Hajiya mairo ban yanke wannan hukuncin dan cin mutuncin ki kona zuriyarki ba, sedai dan hakan shine masalaha ga yarona, idan baki saniba yaka mata kikara sa ido da bincike akan yaranki, Amma dana san haka abun yake, da tunda fari ban yadda da batun hada Auren nan ba, nasamawa Jawwad wata yarinyar itama Naja, taje Allah ya hadata da rabonta dan binciken danayi akanta gaskiya bazan iya bari Jawwad ya aureta ba"
Yaya mairo tace "dama dai can ka shirya cin mutuncina nida yarinya ta, amma inda arziki da mutuci ita daudar gora ai a ciki ake shanyeta, koma me take aikatawa silar Auren ai sekaga ta shiryu"
"Hajiya Mairo, da abunda ze yuwu ne da na hakura anyi auren nan amma baze yuwu ba, kuyi hakuri, sannan Naja ta koma gidan mahaifinta ta zauna"
Maama da tun dazu batayi magana ba tace
"Dan girman Allah kayi hakuri mun yadda ya auresu su biyu ma bakomai, amma idan akayi haka kaman amci mutuncin gidanmune"
Abba yace
"Ni ban Janye batun Auren nan dan cin mutuncin wani ba, amma da abunda ze yuwu ne dana hakura anyi, zanje in samu mahaifinta muyi maganar, dan ba dake ma yakamata muyi wannan zancen ba"
Naja kam se rusa uban kuka takeyi
"Dan Allah ku kyale masa dansu, sekace shi kadaine namiji, kokuma mijin gold ne? Banda kaddara me zatayi da wani Jawwad mutum sam be waye ba waishi Ustaz, dalla kidena kuka kiyi rayuwar ki kamar

Please Login or Register in order to submit comment