Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitowa Jalal ma ya fito, ya sanya shadda coffee color, kansa ba hula, ya taje sumarsa ta sha mai, se kyalli take, ga kamshin turarensa ya cika gurin yana kokarin daura wrist watch, Jalila ta kare masa kallo tace


"wow looking so masha Allah" dagowa yayi ya kalleta yana murmushi, karasowa tayi ta karbi agogon ta saka masa, ta shiga daki ta dakko masa hula, tasaka masa sannan tace

"kafi kyau da hula, bari inyi maka hoto"

Jalal yace

"gaskiya sekin biya zakimin hoton"

Jalila tace

"danma zan saka a wayata shine sena biya? To an fasa"

Dariya yayi yace

"hmm ni hotonki a wayata sunkusa dubu, nikuma ko daya nasan baki da shi, bakomai nidai ina sonki my wife"

Jalila ta dan harareshi tace

"ina ka samu hotona har kusan dubun?"

"kina mamaki ne? In mun dawo zan nuna miki"

"to shikenan Allah ya kaimu mu da wo din"

Ta dinga daukarsa hoto, seda sukaci lokaci suna wannan hotunan, sannan sukayi nufin fita, Jalila ta kuma kare masa kallo daga sama har kasa, ta tuna lokacin da yake kan ganiyar shaye2, irin shigar daya keyi, yadda yake magana ga rashin fara'a, ta kalleshi yanzu a hankali ta furata "Alhamdilillah '

Jalal yace

"lafiya kuwa kike min kallon kurilla, kinsan fa bana son kallo?"

Dan murguda masa baki tayi tace

"Sena kalla din in yaso a dau mataki"

"haka kikace ko? Zan dau mataki kuwa"

Ta dan laankwasar da kai tace

"kayi kyau sosai, kaman karmu fita a ganka"

Da sauri ya kalleta yace

"do you really mean what you said? kina kishina kenan?"

Dan tabe baki tayi tace "hmm to maybe, Amma kaman ba yau nafara kishinka ba, To ban saniba ko kishin ne koba shi bane"

Wata ajiyar zuciya ya sauke yai murmushi yace

"shikenan muje karki makara, dan 10 minutes kawai zamuyi kuma zamu dan tsaya a wani guri"

Haka suka jera gwanin sha'awa, ya bude mata gaban mota ta shiga sannan ya kunna motar suka fice.

Befi mintuna shabiyar da tafiyarsu ba Ilham tazo gidan, amma me gadi ya sheda mata cewar

"masu gidan yanzun nan suka fita"


Ilham Tace

"megidan shi dawa suka fita"?

Megadi yace

"shida matarsa mana, da alama wani gurin zasu je"

Ilham tace "basu gaya maka ina suka tafi ba?"

A fusace yace

"ke ko dai 'yar leken asiri ce ke? Nace miki sunfita ubansu ne ni da se sun gayamin ina zasu"

Haka Ilham ta koma gida gwiwa ba kwari.

Koda sukaje gurin biki kallo yakoma kansu, sunyi kyau sosai, a table daya suka zauna itads Jalal,' yan makarantarsu sukazo suka gaisa, dayake a cikin kawayen Jalila Jalal yafi sanin Zahra ya dan fi sakin jiki da ita, tunda yanzuma kokari yake yana gaisawa da kawayen nata dan kar yayiwa Jalila laifi, bayason taro kuma befiye sakewa da mutane ba, Zahra tace

"Jalila gaskiya ya kamata ayi muku hotuna kaman a saceku a gudu" zahra taita zolayarsu, nan ma hotunan suka sha, maman amaryar tazo wucewa ta tsaya suka gaisa, Jalal yai mata alheri, Jalal kenan zuma ga zaki ga harbi. Seda sukayi kusan awa biyu a gurin, ya bar Jalila ta sake a cikin kawayenta, dan kanta tace ya tashi su tafi gida.

Seda Jalal yafara biyawa ta police station tukuna, suna zuwa suka tarar da Yaya mairo a gurin tana magiyar a barta taga Sa'adah, Jalal kota kanta bebi ba, yayinda Jalila ta gaisheta

Yaya mairo cikin kuka tace

"na gamaki da girman rabbil izzati ki cewa mijinki ko ganin Sa'adah a barni inyi, ina cikin damuwa wallahi"

Jalila ta dafa Yaya mairo tace

"kiyi hakuri Yaya mairo, insha Allah za'a saketa yau din nan ki dena kuka, zesa a saketa"

Jalal daya ga yadda Jalila ke rarrashin Yaya mairo ji yayi kaman ya maketa, wani lokacin halinta daya da Jawwad, komai girman laifin da kayi musu basa riko, ya tuna cin mutuncin da Yaya mairo tai mata a baya, Amma yanzu se lallabata take yi.

Jalal ya gaisa da 'yan sanda cikin girmamawa sannnan D. P. O yai umarnin a kawo masa su Sa'adah,
Sa' adah tayi baki kirin ga waga muguwar rama da tayi se uban hakora, Ga Hannah itama har dan gwara Hannah akan sa'adah, seda Jalila ta tsorata da ganin ta.

Hannah seda ta sandare dan mamaki, Jalal ne a cikin wannan shigar manyan kaya na alfarma, yazama wannan kamilin haka? Gefensa ga matarsa Jalila, yarinyar da tafi tsana, lallai Jalila kwararriya ce gurin makirci, tai musu makirci itada Ilham ta aure Jalal

Jalal yace

"Yallabai wannan itace Hannah, ina son a auna ta a tabattar da tanada ciki? Idan tana da shi seta haifeshi ta shayar da shi ta raineshi inya shekara biyar ta bani shi, idan kuma ba ta dashi zanyi kararta a kotu ta nemomin cikina da ta zubar"

Kallonsa Jalila tayi tasan rainin hankali na Jalal zatayi magana ya daga mata hannu, kuka Hannah ta farayi tace

"wallahi Jalal karya nakeyi, bani da komai nayi hakane danka aureni, dan Allah karka yi min haka, zaka tozartani inkamin haka"

Jalal yace "kina gudun tozarci ni kika tozartani a gurin iyayena, idan har karya kike alfarma daya zanmiki, kije dubai gurin mahaifina ki bashi hakuri ki karyata kanki"

Cikin kuka tace

"na shiga uku Jalal, ina naga kudin zuwa Dubai, kayi min rai dan girman Allah"

Jalila ta kalli wani dan sanda tace

"yallabai Sa'adah bata da lafiya ne naga ta rame sosai? Dan Allah Jalal a saki sa'adah tunda ta nuna inda Hannah take kaman bata da lafiya"

Wani dan sanda yace

"to kusan hakan, tana nan a tsare bata samun shan magungunan ta, ankira likita ya dubata maganinta na kanajamau da bata shane yasa yafara nunawa, amma an bata wani, sannan bazamu saketa ba saboda ta hada kai da wannan kawar tata Hannah sun damfari wani Alhaji makudan kudade, dan haka zamu gurfanar da su a kotu"

Ba Jalila ba hatta Jalal da Yaya mairo seda suka sandare a gurin, Yaya mairo ta dora hannu aka tace


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, sa'adah maganin da kike sha tsawon shekaru kikecemin na gyaran jikine dama na wannan cutar ne, Allah ya wadaranki Sa'adah ni Allah yasa baki gogamin ba bansaniba, abun naki hada damfara kai Allah ya wadaranku wallahi banyu dace ba nikam, daga ke har kanwarki da dan uwanku bana zabe, dan uwanku na prison saboda sata, ke karuwanci da damfara, kanwarki shaye2 da karuwanci nashiga uku ni mairo, Allah ya tsinemuku gaba dayanku 'ya' yan jaraba"

Jalila tuni fuskarata ta jike da hawaye tace

"kidena wannan maganar Yaya mairo, sannan kai kuma officer, this is confidential you don't need to expose her like this baka kyauta ba"

Jalal ba kunya ya rungumo matarsa a gaban mutane yana goge mata hawaye yace

"Haba Jalila kidena kuka mana, Allah ne ya saka miki, ke da'akewa gori Ana cewa tubabbiya ce mahaifiyarki ke gashi Allah yayi ki shiryayiya, SU da suke ikrarin an haifesu a musulinci, kalli yadda suka kare, musulincin nasu a bakine, mu tafi gida kidena kuka "

Jalal yace" Yallabai zan dawo Insha Allah "

Sa'adah ta sunkuyar da kanta tana zubda hawaye, aka tasa keyarsu aka mayar dasu ceil

Sukayi sallama yasa Jalila a mota se gida.

Da sukaje gidan ma taki walwalwala, duk abun duniya ya dameta, wayarta ta dauka ta hau online aikuwa tai sa'a Nana ma tana online suka dinga chatting Jalila ta Gaya mata abunda ya faru
Nana tace "Alhamdilillah ai dama sharri dan aikene, tayi ya kuma koma kanta"

Jalila tace

"A'a Nana, a duk lokacin da musiba ta fada kan wani be kamata muyi murna ba musamman mata, duk abunda yasamu mace raguwar muce"

Nana tace

"rayuwar su dai dan bandani, Allah ne yakamasu wallahi naji dadi kuma, dan sun dade suna zige Maama, yanzu naga ta bakin zagin 'ya' yan wasu"

Jalal na zuwa ya karbe wayarta yaga da Nana take chatting voice message ya turawa Nana yace

"Nana ki kyaleta ta zauna ta damu kanta akan wannan mutanen, ki mata fada kema, ki gaida su Mahmud da Anty Salma"
Ita dai Jalila kallonsa kawai takeyi


Ya ajiye wayar ya zauna kusa da ita ya bude system dinshi, ya shiga wata folder ya mika mata system din, dan zare ido tayi, dan kuwa hotunan tane kawai a folder sun kusa dubu kaman yadda ya fada tun daga na jariran taka har iyanzu, mamakine ya kamata, dan wasu hotunan nata bata taba tunanin sunfita daga wayarta ba tace



"Jalal ya'akayi ka tara wannan hotunan nawa haka?"

Dan hade rai yayi yace "Jalal ko?"

"ohh sorry Zaujeee" ta fada tana murmushi

Ya dan gyara zama yace

"wasu hotunan naki tun kina gurin Ummi, wanda na nunamiki ne a gadon kaya, wasu hotunan kuma Hanan ce take turomin, Hanan ta dade tana supporting dina akanki, wasu a wayar Jawwad nake turawa be sani ba, ta saki ta turamata hotuna nikuma tana turomin"

Bude baki Jalila tayi tace

"Amma gaskiya Hanan bata da kunya, ashe an dade ana yaudara ta, inta antaya mata hotuna na tana tura maka, wayace ka kalleni ba mayafi a lokacin?"
Tai maganar tana yamutse masa fuska kaman yarinya karama.

Jalal yace

"Abunda yasa nake kallonki yanzu ba mayafi shine yasani ake turomin hotunanki ba mayafi nake kalla"

"mekenan?" ta tambayeshi

"So mana" ya bata amsa, ya dora da cewa

"Jalila kaman kina tantama akan son da nake mikine, tun a wancan lokacin da nayi kokarin in cire sonki daga raina ganin hankalinki yana kan Jawwad, Amma duk sanda nayi yunkurin yin hakan se inji ina kara azabtar da zuciya tane, Jalila so mugun ciwone, haduwar da mukayi sanda kikazo kano, nasaka miki wasika a cikin cover Al'qur"ani, amma bana tunanin kin gani, Jalila lokacin dana ganki da Ahmad seda naji kaman in kashe kaina saboda kishi, ko yan kwanaki nayi ban ganki ba sena shiga damuwa, dukda in muka hadu bawani abun arziki da ke hadamu"

Ya kalleta ya dan murmusa yace

"kinsan wataran Jawwad ya sha kamani ina kallon hotunan ki? Na maze na hade rai sedai ya kalleni ya kyaleni kawai, kwana biyu na hanashi taba wayata, abunda banayi a baya, ya dau wayar yaga na saka password yana saka sunaki ta bude, wallpaper na hotonki ne da mukayi a gurin birthday dina, aikuwa ya ritsani da tambayoyi, seda na tabattar masa dani har yanzu wannan soyayya da nake miki a baya tana nan, Amma kar ya gayawa kowa, shine yace ze shigemin gaba Indai Aurenki ze sani farinciki, Jalila na dade ina azabtuwa da soyayyarki "

Ya kwanta a jikinta yace

" please Jalila karki rabu dani, ko da ba kyasona ki cigaba da jin tausayi na dan Allah, ko iya tausayinne, nasan watakila watarn tausayin yakoma soyayya, nikam Soyayyar da Umminki tayimin da sadaukarwa da kikayimin, bazata taba bari in cutar dake ba Jalila, Ina sonki my wife ko baki soni ba dan Allah kiyi hakuri zama dani, kinfi kowa sanin halina da fuskantar abunda nake so ciki harda mahaifiyata, ina sonki"

Hannu tasa tana shafa gashin kansa, tausayinsa duk ya mamaye jinkinta, ta kasa magana, shi kuma yayi lamo a jikinta kaman maraya

Jalal Yace

"Gobe in Allah ya kaimu zaki tafi da kayanki, Munyi magana da Abba yace zakuje bauchi da Maama tunda kunyi hutun makaranta, nima zan koma lagos zan cigaba da aikina Insha Allah, amma sati biyu zanyi kawai in dawo, sannan in kun tafi bauchi karki kirani a waya, sedai in nina kiraki"

"But why?"

"haka nan kawai, zakiji dalilin hakan amma, zanyi missing dinki sosai Baby gaskiya transfer zan nema, in ba hakaba damuwa zata min yawa"

Jalila tace

"kanemi zabin Allah kafin ka nemi transfer din nan Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi"

"zamana a kusa dake shine mafi Alkhairin ai"

Tacigaba da shafa kansa a hankali tana tunani daban daban a ranta.









Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣7️⃣110

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _

Washegari tun safe Jalila take shiri tana murnar zata je gida, gefe guda tana tunanin in taje dole ne taje ta gaida iyayen Jalal, ko wane tarba Mummy zatayi mata oho? Ga abunda ya faru da su Sa'adah har yanzu abun yana damun ta sosai, karfe goma na safe ta kammala shiryawa tsaf, ta hada kayanta, tun dare ta hadawa Jalal nasa kayan shima wanda zeyi tafiya dasu Lagos.

Jalal ma ya fito tsaf da shi, Jalila ta kulle ko ina, Jalal kuma yafita da akwatunan su, a mota taje ta tarar da shi ita kawai yake jira, ta bude ta shiga ta zauna, ya kalleta yace

"Baby ya dai naga duk jikinki a sanyaye?"

"bakomai fa" ta bashi amsa

"shikenan tunda bazaki gayamin ba"

Ya kunna motar suka tafi, koda yaje unguwar su yayi parking kin fitowa tayi daga motar, ya kalleta yace

"Fito mana, ni nakasa gane meyake damunki ne?"

Jiki ba kwari ta fito daga motar, Jalal yace

"muje in gaida su Abba, daga baya sekije ki gaida Daddy"

jinjina masa kai kawai tayi tabi shi, suna shiga cikin gidan kofar parloun a rufe take, Jalila ta dakko wayarta ta kira Maama, bugu daya Maama ta dauka Jalila tace

"Maama ina kika tafine, ina gida amma kofan parlor a rufe"

Maama tace

"ya salam, ai ban dauka da wuri zakuzo ba, kinga mun dan fita da Abba ne, yanzun nan zamu dawo insha Allah"

"shikenan se kun dawo" ta kashe wayar ta kalli Jalal tace

"basa nan wai yanzu zasu dawo"

Jalal yace "shikenan zomuje gida seki jira su"

Dan shiru Jalila tayi tana kallon Jalal.

"kina tsoron Mummy ne? Karki damu ba abunda ze faru muna tare, muje"

Jiki a sanyaye tabi bayansa danji take kaman tace bazata ba, tasan bazeji dadi ba idan tayi hakan, gabanta nata faduwa tana karanta addu'oi daban2, tun daga harabar gidan har cikin parlor ba kowa part din daddy ya nufa tana biye da shi, suna shiga suka tarar da Daddy na zaune na kallon labarai su Jalal sukayi sallama, ya amsa tare da waigowa, yana ganin su ya fadada murmushinsa tare da dan bude baki, ganin Yadda Jalal yazama wani babban mutum.

Jalal yana zuwa ya zauna kusa da Daddy, yayin da Jalila ta zube a gurin tana gaida Daddy, Daddy yace

"Haba Jalila zauna mana semu gaisa, yazaki zauna a kasa"

Cike da kunya da girmamawa Jalila ta dan zauna tana kuma gaida Daddy, ya amsa mata yana tambayarta ya gida. bayan sun gama gaisawa da Daddy ne Jalal ya dan risina yace

"barka da warhaka father, ya hanya?"

Daddy yace "lafiya kalau, ya gidan naka kuma? Ya 'yartawa take? "

"lafiya kalau, ba gata nan kana gani tana lafiya ba"
Daddy yai murmushi dan tabbas inka kallesu zaka gane suna cikin farinciki

Suka zauna sukayi ta hira da Daddy, Jalila se kunya takeji tana sunkuyar da kai, yayinda Jalal kam se zuba yake yana hira, daddy yaji dadin ganin Jalal, yadda yake magana yanzu ya sha banban da yadda yake yi da babu respect a maganganunsa a baya cikin gadara yake yinsu, amma yanzu gashi yasaki jiki yana hira babu hade rai da masifa.

Daddy yace

"gaskiya Son naji dadin ganinka, kaga yadda kayi kiba kuwa, ka wani zama babban mutum"

Jalal ya kalli kansa yace

"Allah Daddy thank God, and thank my wife efforts, she's behind the changes you saw on me, behind any successful man their must be a woman, da baku aura min ita ba ban san ya zanyi ba"

Jalila ji tayi kaman kasa ta tsage ta shige dan kunya, daddy yace

"tabbas Jalal matarka ta cancanci yabo da godiya, ubangiji Allah ya kara hada kanku, ya wanzar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakaninku, Allah yasaka miki da alkhairi Jalila"

Jalila ba tace komai ba, Jalal yace "Ameen ya Allah Daddy"

Jalila tace "Daddy ina Mummy ne?"

"bata jin dadi ne, ta sha magani ta kwanta bacci"

Jalila tace "Daddy meyasa meta?"

"kawai dai jikin nata ne bata jin dadi, gashi bata son zuwa Asibiti, likita yazo ya duba ta yabata magani"

"Allah ya bata lafiya"

Daddy yace "Ameen" yayin da Jalal ya basar kaman besan zancen da suke ba.

Daddy yace

"to nima zan dan fita ne, inada meeting dazan shiga karfe daya"

Jalal yace "shikenan Daddy seka dawo, nima daga nan karfe hudu Insha Allah zanbi jirgi zan koma Lagos"

Daddy yace "to Allah ya kaika lafiya, kafin in koma zan biyo ta Lagos din in ganka"

Sukayi Sallama da Daddy ya shirya ya fita.

Babban parlor suka dawo suka zauna suka cigaba da hirarsu kaman a gidansu dayake babu kowa a parlor.

Jalal ya kalli Jalila yace

"nifa yunwa nakeji"
Dan zare ido tayi tana kallonsa

"yunwa kuma? A yanzun"?

"Eh ni yunwa nakeji"

Jalila tace

"to yanzu meye abunyi ga mutan gidan basa nan? Gashi ban fito da komai naci ba tunda ka zama jariri"

Murmushi yayi yace

"tashi muje kitchen mu duba seki dafa mana wani abun"

Jalila tace

"kana ganin babu matsala idan mukayi hakan?"

Jalal yace "matsala kuma? Tashi muje ba wata matsala"

Ta mike suka tafi kitchen.

Ilham juyi take kawai akan gado, tarasa me zatayi taji dadi a ranta, tunda Jalal yayu aure ko bisa kuskure basu hadu da Jalal ba, gashi kaman masifa haka wutar son Jalal ke ruruwa a zuciyar ta ba dare ba rana, gaba daya ta rame tayi baki, idan ta tuna artabun da suka dingayi da Jalila a baya akan Jalal ta tuna yanzu ita ya aura, kuma har yake gaya mata wai yana son matarsa, setaji duniyar ta kara mata zafi taji kaman ta samu wuka taje gidan ta kashe Jalila, gashi yanzu fafutukar Ummanta akan ta dauki fansa ne kawai, gashi ta gaji da zigar da takeyiwa Mummy, ga ciwon so na neman halaka ta, ko Abincin kirki bata iya ci, bata taba zaton radadin ciwon so ya kai haka ba, ko da wasa batayi tunanin son Jalal ze juye ya koma mata gaske ba, ta yanke shawarar zuwa gidansu yaseera taji wace shawara zata bata, yunwa ta isheta dan haka ta sakko daga kan gadon dan neman abunda zata zubawa cikin ta.

Kunun gyada Jalal yasa ta dama masa, ta soya masa irish potatoes, ta zuba sugar da madara ta na juya masa, yasa hannu ya karba, Jalila tace

"kai zaujee se'a zata bana baka Abinci ai kabari ya huce in ka sha zaka kona baki ne"

A dan shagwabe Jalal yace

"ai ba kya bani in koshi duk na rame"

"A hakan ne ka rame, kalli ka fara tumbi fa kalli kumatunka ma"

Dariya yayi ya shafa cikinsa yace

"bafa wata yunwa nake ji ba, kawai zanyi missing delicious food dinki, shiyasa nake so inci kafin in tafi"

Murmushi tayi ta juya tana gyara gurin da ta bata tana tattarw kwanukan.

Ilham da kusan mintunan ta biyar a tsaye a kofar kitchen din ba tareda sun san tana gurin ba, taka sa daga Koda karamin yatsanta, sedai ji da tayi kaman an kunna gobara a kirjinta. Abun mamaki Jalal se dariya yake shida matarsa, cike da kulawa, yasha kayansa na mutunci sabanin a baya,wanda ganin dariyar Jalal seka shafe wata baka ga yayi dariya ko sau daya ba.

Jalal ya dau cup din kunun ya kai bakinsa, aiko yana sha ya kona harshe saboda akwai zafi sosai, aje kofin yayi yana rintse ido, tareda zukar iska cikin bakinsa. da sauri Jalila ta juyo

Tace

"subhanallah sannu wai sha kayi?, dama na Gaya maka da zafi fa amma ka sha a haka"

Janyota yayi da sauri ya hade bakinsu ya fara kissing dinta, Jalila ta tsorata sosai gaba daya jikinta yake rawa, sunyi kusan three minutes a haka sannan ya cikata ta ja da baya tana zare ido kaman mara gaskiya, ya dan kashe mata ido ya juya ya nufi fridge ze bude ya hangi Ilham ta gefen idonsa, a kofar kitchen tana hawaye basarwa yayi ya dau ruwa a fridge ya sha, ya janyo kujera dake dining din kitchen din ya zauna.

Kallon Jalila yayi ya ga yadda take rarraba ido kaman wadda aka kama tana aikata wani zunibi, ya dan kashe mata ido yace

"inkin gama zare idon kizo ki bani Abinci, lokaci yana kurewa, zanje inyi salla inyi haramar tafiya"

Kan table din dake gabansa ta aje Abincin, tana debo kuna tana hurawa tana bashi a baki.

Ilham da tayi kaman ta juya ta fasa shiga kitchen din, amma ta dake ta shiga, ko kallon inda suke batayi ba, suma basu kulata ba, Jalila ce tace

"Ilham ya kike ya gida, ranar me gadi yace kinje bama nan"

Wata uwar harara Ilham ta jefawa Jalila tare da jan uban tsaki, ita kuma Jalila tayi kaman bata gani ba, ta cigaba da bawa Jalal Abinci.

Jalal yace

"Baby badan nayi sauri nai kissing dinki ba, da tuni harshena ya kone gaba daya"

Dan murguda baki Jalila tayi tace

"seda na gaya maka da zafi ai amma ka sha da zafin"

"na matsu in sha ne shiyasa"

"ai gashi nan ka kone, kayi shiru kuma karka kware dai"

Shiru yayi yaci gaba da karbar Abinci kaman wani karamin yaro, yayinda Ilham keta kokawa da tukunya tana kokarin dora tukunya amma tarasa ta ina zata fara dora tukunyar saboda bakin ciki, kafarta se rawa take, saboda wani azababben kishi da taji yana taso mata.

Jalal kaman ba kowa a gurin haka ya cigaba dayiwa Jalila shagwaba tana bashi Abinci har ya gama ci.

Jalila ta kalleshi tace

"dan Allah meyasa kace in ka tafi kar in kira ka for two weeks"?

Dan murmushi yayi yace

"inda zanje aiki babu network ko kin kira baze shiga ba"

A shagwabe tace "Amma meyasa?"

Kafin yayi magana Ilham ta jefowa Jalila tukunyar dake hannun ta, da sauri Jalila ta rike Jalal tana fadin

"subhanallah"

huci Ilham takeyi tana kuka tare da fadin

"Allah ya isa ban yafe miki ba, wallahi sekinga abunda zanyi miki, sena hanaki sukuni da jin dadin rayuwa makira Azzaluma, kika dinga nuna ba wanda kika tsana sama da Jalal dan mugunta kin aure shi, wallahi ciwon son Jalal baze kasheni ba sekin dandani abunda nakeji"

Ta kuma rarumo food flask ta jefowa Jalila, da sauri Jalila ta shige bayan Jalal ta rirrike shi.

A fusace Jalal yace

"ke wace irin mahaukaciya ce haka? Wallahi kika illatamin mata se na daureki"

Daga bayan Jalal, Jalila tayiwa Ilham wani irn gwalo passionately tareda kashe ido cike da neman tsokana tace

"ni nace miki na tsaneshi? in ma na fada a da yanzu na janye"

Wani farinciki ne ya ratsa zuciyar Jalal tundaga sama har kasa da jin abunda Jalila ta fada akansa.

Hannun ta ya rike suka fice suka bar mata kitchen din.
Jalal yace

"kidena biye mata dan Allah, lokaci nake jira itama seta girbi abunda ta shuka, samunki a rayuwata yafi komai dadi a rayuwa ta"

Murmushi Jalila tayi tace

"nikam muje in duba in Maama ta dawo, dan bazan zauna ta nakasta ni a banza ba"

Jin hayaniya ne yasa Mummy ta Farka daga baccin da take ta fito dan ganin meke faruwa, tana fitowa parlor taga Jalal da Jalila yana gyara mata mayafinta, Ilham ta fito daga kitchen ido duk hawaye da katon muciya a hannun ta tana ihu tana

"wallahi sena ga bayanki muguwa makira, yadda kika kunsa min bakin ciki sekin kunshi wanda yafi nawa, saboda makircin ki burin mahaifiyata be cika ba, nikuma ciwon so ya kamani ina ta azabtuwa, wallahi sena tozarta ki"

"wallahi ba'a haifi 'yar da zata tozarta ni ba, ko ta wulakantani ba, kuma ni makirci ai uwarsa ce ni, nina

Please Login or Register in order to submit comment