Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daba, Alhaji Kabiru ya gayyaceni gidansa da zummar yanaso inmasa wani Aiki zena biyana, na yadda na Amince, ya nunamin hoton Jalal yace akansa yakeso inmasa Aiki, nace kamar yaya, yace soyake Jalal yazama mugun dan shaye2 dan Jagaliya kamar ni, nace masa amma tayaya hakan ze faru yacemin inyi duk yadda zanyi zena biyana duk wata dubu Ashirin, idan har burinsa yacika Jalal ya lalace ze bani wasu kudi masu yawa, Na amince na karbi Adress din Jalal nafara zuwa unguwar su, na lura yanada saukin Kai dayawan kyauta, dukda na girmeshi haka na dinga kokari ina shiga jikinsa, ina turamasa Akidar shaye2, dabe amince ba har sabani muka samu, amma daga baya bansan ya akayi ba ya Amince da kansa, Abokinsa Jawwad yayi kokari yaga ya rabamu amma abu yaki, haka nakoya masa zuwa clubs daban2 kasancewar yanada kudi kayan maye se wanda mukeso zamu sha, Nayi kokarin in koyamasa bin mata amma yaki, sam hankalinsa baya kan wannan shidai kawai yayi shaye2 Alhaji Kabiru yacigaba da biyana makudan kudade kafin daga baya ya nunamin sana'ar dayakeyi ta saida miyagun kwayoyi da makamai ta barauniyar Hanya, idan Jarinsa yai kasa senazo nasan yadda nayi na karbo masa kudi masu yawa a gurin Jalal seyaraba yabani kasona, nazama babban Aminin Jalal, Alhaji Kabiru yasa nadinga Jan ra'ayin Jalal akan mutafi Dubai semunfi holewa acan bame samana ido, mussaman shi da mahaifiyarsa take takuramasa aikuwa ya yadda, shikuma Alhaji Kabiru yahada baki da wasu ma'aikata za'asaka kwayoyi a kayan Jalal, yadda semunje dubai za'a kamashi, idan mukaje dubai aka kamashi da wannan kayan hukuncin kisa ne, Amma abun mamaki se a Airport Jalal yace yafasa tafiyar nan, Saboda Jawwad. Ba karamin fushi Alhaji Kabiru yayi dani ba, yana ganin sakacina ne, da wannnan ya wuce se muka shigo da Hanna wata karuwa cikin tafiyar tamu, Saboda tasirin mace ga da namiji, Amma duk yadda taso ta janyo hankalinsa kanta yaki, Idan yayi shaye2nsa yayi bacci A gurin wataran Jawwad ne yake zuwa ya dauke shi, muka hada baki aka shirya masa birthday party, da nufin cewa za'ayi party ne imu imu abokan shaye2nsa, Amma abun mamaki muka ganshi shida yan uwansa dasu Jawwad, muka shirya idan aka bashi kayan maye a gurin zamu faki idon mutane mu daukeshi, za'a kaishi wani gida da aka kama Hayarsa na wasu yan awanni, Zamu kai Jalal can, a gidan Akwai manyan makamai, Akwai yara kanana da aka hayo aka saka a gidan, Alhaji Kabiru ya saye wasu manyan "yan sanda da kudi, cewar za'azo akama Jalal a wannan gidan, da wannan kayan za'ace an kamashi da miyagun kwayoyi, da Makamai sannam yana safarar yara mata, Amma shima se akasa aka Sace Jalal a gurin party muka nemeshi muka rasa, shima Alhaji Kabiru yai fushi dani da kyar ya hakura, Sekuma karon karshe da Alhaji Kabiru yakamani da 'yarsa a gidan Karuwai, da muka dau tsawon lokaci tareda ita, Yallabai wannan shine Abunda ke tsakanina Da Alhaji Kabiru " gaba daya dakin yayi shiru, Jalal cikin Rawar murya da sanyin jiki yace
" Jeje waye Alhaji Kabiru, Menayi masa haka A rayuwa? Laifin menayi masa yazabi ganina a wannan Kazamar Rayuwar?" Jeje yace" Alhaji Kabiru shine mahaifin wannan Abokin naka Faruk, da mahaifinsa ke yawan yimasa kashedi akanka, sannan kuma shine tsohon Saurayin mahaifiyarka data Yaudara, Yasha alwashin daukar fansa"
"Shine ya zabi Ramawa akaina? Ina ina lokacin dahaka tafaru tsakaninsu? Meye Nawa a ciki? Meyasa kowa akaina yakeson daukar fansa? Meyasa? Jeje nikayiwa haka ko? Kashiga Rayuwata ka lalatamin komai, harda kokarin Rabani da Aminina Jawwad na yadda da kai amma aka hada kai da kai ana hadamin wannan miyagun tarkunan, Yanzu badan Allah ya kiyayeni ba.... Kasa karasa maganar yayi, Hawaye yafara fita a idonsa ya mike yanufi hanyar fita da Sauri, bayansa Jalila itama tabi da Sauri, tana kiran Sunansa amma kafin ta cinmmasa tuni ya hau motarsa ya kunna, ya tasheta da gudu yabar Asibitin.
Haka ta dawo dakin data bar Suleiman, suleiman ya kammala tambayoyinsa.
Jeje ya kalli Jalila yace "Kin shammaceni fiye da tunanninki, ban taba zaton karamar yarinya kamarki zata iya aikata wannan abunba, kin kassaramin Rayuwa, kisani Babu wanda ze iya daukar mataki akan Oga KB, saboda za'a sakeshi ki Saurari abunda ze biyo baya idan aka sake shi" wani mugun kallo tayiwa Jeje "Duk wani zalunci da kassara Rayuwa yabiyo bayan wanda kukayiwa Jalal, Azzalumi daga kai har uban gidan naka, Kaike min kallon karamar yarinya, duk abunda nasa gaba sena ga bayansa, zamu gani nagama da babinku har gaban Abada, kuma ka saurara kagani ko ansakeku zalincin dakukayi baze barku ba" Ganin Jalila ta dau zafi sosai yasa suleiman yace "Kwantar da hankalinki, ki share hawayenki wanda zan dankawa case din shima wanine, za'adau matakin daya dace, kaikuma ina gurin kake wannan maganganun ko? Ka kara daure kanka zaka gane bakada wayo" sannan ya kalli Jalila yace "Shi waye wannan din? (JALAL) Jalila tace" Yaya nane"
"Gaskiya an cutar dashi Sosai, and he needs counseling, kusa ido sosai akansa sannan ku kuladashi, ajashi a Jiki a dage da Addu'a har Allah yasa a raba shi da shaye shayen nan"
"Hakane Insha Allah za'ayi kokarin hakan,
" Yawwa yanzu dai muje in ajiyeki a gida ko? "
" A'a ka ajiyeni a hanya dai" Yai murmushi yace to muje.

Jalila ta koma gida cike da farinciki jin kamshin Nasara tana saka ran tunda aka kama Jeje to ko Jalal be dena shaye2 ba ze rage sosai, tunowa tayi a halin da yabar Asibitin
"ko yana ina yanzu?, Allah yasa yazo gida lafiya" ta shige cikin gida abunta, tana shiga Nana tace "Jalila ina kika tafine?"
"Hmm kedai bari kawai, gidansu Zahra naje, amma ai gani na dawo"
"Kinci sa'a Abba baya nan, shiyasa kika samu sake" Murmushi Jalila tayi tace "Aiko yana nan ma baze ce komai ba"
"kyaji dashi dai, anjima ze dawo yayo waya ya tambayeni kina ina? Nace masa kindan fita"
"Dagaske anjima ze dawo? Bari inzo inshiga kitchen dole in kintsa cikin Abbana, wannan karon ya dade a lagos" Nana tai murmushi "'Yar gidan Abba, dama yafi sonki akanmu" Jalila dariya tayi ta wuce cikin daki, ta shiga da Sallama amma Naja bata amsaba sema wani dogon tsaki data ja, Jalila ko a jikinta bata damu ba, dan ita nasarar data samu ta fiye mata duk wani neman magana da Naja takeyi, Jalila tanemi guri ta ajiye jakarta da hijjabinta, Wayar Jalila ce tafara ringing ta duba taga Hanan ce, Murmushi Jalila tayi ta daga wayar, tace "Hanan wai yaushe zaku zone?"
"ke ba gaisuwa ba tambayar ya nake se yaushe zamuzo, idan munzo mezaki bani?"
"Ba'abunda bazan baki ba, yau ina cikin farinciki, nasamu Nasarar daban taba zaton samunta ba"
"Wannan wace irin Nasarace kekuwa kike ta murna haka?"
"Bazaki gane ba, bakina akwai magana sosai, kedai kawai sekunzo"
"Gaskiya kifara gayamin yanzu dan zaki barni da tunani"
"Gaskiya bazan gayamiki yanzu ba, innafara bazan iya gamamiki ba, kuma zakiso kiji komai, kawai se kinzo dai"
"Amma naso kifara gayamin yau, daddy ya kira Abba, amma yace yana Lagos kifara hada kayanki zebamu ke, tare zamu tafi Bauchi"
"Eh dama yau ze dawo Abban, Wayaga Jalila a Bauchi, zanga gari inci waina inture"
"Ji kwadayayyiya, ke burinki kici waina, to bazakici wainar ba" sukayi dariya gaba daya, Hanan tace "Baby, ina Abun kaunata" dan jimm Jalila tayi sannan tace "kinada lambarsa ai, meya hana ki kirashi"
"Ban niyya ba, ke nakeso ki amsamin"
"Yana lafiya" Jalila tafada a takaice
"Kimikamin sakon soyayya, kigaya masa kullum yana kawwame a cikin wani bigire me girma a zuciyata, I Love Him, Kaunar Jawwad a jinina take, kigaya masa ina nan zuwa sati me zuwa, in ganshi"
"Kan bala'i wane Jawwad din, ke banason karamin karauwanci, kobaki San anmasa mata bane?" NaJa ce take masifa daga gefe jin an ambaci Jawwad, dayake duk wayar da suke tana ji, Hanan tace "Jalila se anjima ki isarmin da sakona gurin abun kaunata, ba ruwana da kowace mace ko mata hudu aka masa Wallahi seya saki daya ya Aureni, sannan kigayawa me maganar nan Hanan tafi karfin tayi karamin Karuwanci se babban Karuwanci me lasisi, sati me zuwa Insha Allah zan shigo kano, zan gwada mata nawa salon karauwancin, ki gaida mutan gidan" Hanan ta kashe wayarta. Naja ta hau bala'i ta inda ta shiga bata nan take fita ba, yayinda Jalila ta samu guri ta zauna ta dinga kyalkyala dariya, tace "Allah ya kaimu my Hanan tazo, za'a sha drama, zanga yadda zata kaya, agama mu fece Bauchi in garin dadi in zamana se ankuma ganina" Hakan yakara bakantawa Naja rai, ta tashi fuuuu tabar dakin, Seda Jalila tagama dariyarta sannan ta mike lokaci2 Jalal yana fado mata a rai. Kitchen ta tashi ta tafi, ta tarar an Aiki Nana, ta shiga tafara Kokarin dora sanwa musamman dataji batun Abba ze dawo, tana tsaka da Aiki Jawwad ya shigo ya sameta
"Sannu kukunmu, kullum cikin adanamana cikinmu kike, weldone baby" ta juyo ta kalleshi tana murmushi
"Allah yatemaki babban Yaya, da girman kujerarka, Nace Yaushe za'a dakkomin Abban, na dade ban ganshi ba fa" takarasa cikin shagwaba, karasowa yayi gabanta yace "Autar Abba saekin rikici anjima kadan zanje dakko shi ai"
"Yawwa naji dadi sosai, Ina dan uwanka ne?"
"daga gurinsa nake, bayajin dadi ya kwanta bacci"
"Meyasameshi haka?"
"Jalal ba a rabashi da damuwa, be gayamin ba, yace yana bukatar hutu ne kawai" dan jinjina kai, har cikin ranta takejin tausayin Jalal, hawayen dataga yanayi dazu a Asibiti ya tsaye mata a rai, basarwa tayi tace "Yaya Su Hanan zasuzo a cikin next week Insha Allah, zamuje Bauchi in Abba ya yadda"
"Bauchi kuma? Zasu daukemin ke?"
"Ai bazan dade ba ai, nima zanga gari sosai"
"Bawani nan nidai bansoba gaskiya, banason kiyi nisa dani" tai murmushi tace "Hanan tace inmiko mata gaisuwa, tace in gaisheka"
"nifa nayiwa Hanan laifi Jalila, da tana kirana mu gaisa amma yanzu ta dena"
"Karka damu Yaya Jawwad, nasan halin kayaya don't mind her"
"Kinsan banason in batawa kowa rai ni"
"Ni zanbada wannan shedar akanka, kai abun sone ga kowa Yaya Jawwad, Irinka basu dayawa ko a cikin mutane shiyasa........
" To maye bita zaizai" gaba daya suka juyo, Maama ce itada Naja a kofar kitchen din, suka karasa shigowa
"Jawwad ban isa in gayamaka magana kaji ba saboda wannan shegiyar yarinyar ko? Sam kaki saurarar Naja kaki kulata, ka tare a gindin wannan 'yar macen, to wallahi baka isaba Jawwad, Akan yarinyar nan idan na juya maka Baya sedai kanemi wata uwar baniba" da Sauri Jalila ta kalli Maama, Naja se kara zigata takeyi, Maama tace
"Eh kalleni da kyau, munafuka Mayya za' a mallakemin da kaman yadda uwarki ta mallake ubanki aka dinga wulakanta ni a lokacin, wallahi baki isaba kinyi kadan, kuma dan uwarka dan ubanka Naja zaka Aura, kekuma kije kinemi mara mutunci mara Asali irinki, ba dana ba dan dangi gaba da baya"
Jawwad yace "Maama dan Allah kiyi hakuri, kidenai gaya mata haka"
"Wato bakason bacin Ranta, gara batamin Rai akanta ko? Nikae gayawa abunda zanyi, ka kiyayi bakina Jawwad" A hankali Jalila ta tako ta rabe gefen Maama zata wuce, Naja ta kamayi mata Gwalo, bata kulata ba ta wuce daki.
Tana zuwa daki tasamu gado ta Haye, ta sunkuyar da kanta se Hawaye wani nabin wani, Jalila ba karamin dagawa Maama kafa take ba amma sam ita bata gani, amma lokaci yana zuwa da zata gane kuskuren abunda take mata, amma tayiwa kanta Alkawarin seta koyawa Naja hankali. Koda Nama ta dawo tayi mamakin ganin Ran Jalila a bace, tabarta da fara'arta amma ta dawo ta tarar da ita rantaa a bace, Nana tace "Jalila nasan wasu lokutan zaman gidan nan baya miki dsdi, mussaman da Naja ta dawo gidan nan, amma kiyi hakuri komai me wuce ne, dukkan tsanani yana tareda sauki"
Murmushi Jalila tayi tace "Ni nace miki ammin wani abunne? Bana jin dadine kawai"
"Amma ai idonki ya nuna kuka kikayi"
"Baki yadda dame ma fada ba kenan"
Nana tace "shikenan Tashi muje, tunda kin kafe, amma idonki ya nuna akwai damuwa, muje mukarasa girkin" Jalila tai kokarin ta danne damuwarta sucigaba da aiki amma abun yaki yuwuwa, ko yaya Nana ta kauce se Jalila zubda Hawaye, ita kanta tasan tana Hakuri da kauda kai akan wasu abubuwan.
Da la'asar sun kammala komai Jalila tayi wanka ta canza kaya, amma duk ranta ba dadi, tasan Jawwad ma yana nan ransa babu dadi, da sunci karoda Naja seta dinga yar mata da miyagun maganganu, ga Maama agurin babu damar ta rama,
"Ai wallahi Maama mungode Allah, danginmu a tsarkake muke, ai karshen masifa a hada maka zuri'a da Arna" Maama tace
"Godewa Allah kam yarinya, dukkanmu musulmi ne, babu shegu babu Arna" Naja tace
"Maama 'ya' yan halak dinma im aka bincika wasunsu shegune, dan Arna da Auren suma bin maza suke"
A fusace Nana tace "Naja waike dabbar dajin inace? Wani irin hauka... Maama ta katseta ta hanyar cewa
"Rufemin baki ko make miki baki, aiba karya tayi ba kudinma babu tabbas kun hada jini da ita"
ficewa Jalila tayi gaba daya daga cikin gidan tafito harabar gidan. Nanna ta yunkura zata bi bayan Jalila Maama tace "wallahi kika bita sena baki mamaki, wuce ki zauna daga nan inta tafi karta dawo, haka Nana ta koma ta zauna"
Koda Jalila tafito harabar gidan, taga Manu driver da abokansa, a harabar gidan suna gyran flowers, ta duba taga bataga motar Jawwad ba, dan haka ta wuce part din Jawwad, ko ganin gabanta batayi, ta samu gefen kujera ta zauna ta toshe bakinta tafara kuka, bata son kowa yaganta balle a rarrasheta ta zauna tana kukanta, tanajin yadda ranta yake mata zafi. Tana tunanin meyakamata tayi ta huce yadda Maama ke wulakanta ta, bata son gayawa Abba halin da'ake ciki, tasan hakan ba karamin matsala ze jawowa Maaman ba, tana bukatar wanda zata gayawa damuwarta koba komai ta rage damuwa, tasan Hanan zigata zatayi tayi rashin mutunci, gashi ita bada kowa ta yadda ba, balle tagayawa wani abunda ke damunta,, tana cikin tunani tareda kuka taji magana
"Meyasaki kuka haka?" bata san da mutum a dakin ba, dan haka ta juya da sauri da doguwar sumarsa ta ganeshi, sam bataga kowa a dakin ba, shiru tayi tacigaba da kukanta, karasowa yayi gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ji tayi duk ya takurata a hankali yace
"Meyasaki kuka haka?"
"dan Allah nika kyaleni, ina ruwanka da kuka na"
"Inada ruwa da kukanki, kamar yadda kike da ruwa da Rayuwata, now talle me what happens?"






❤️❤️❤️❤️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku 😍😍😍😍

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
What's app only 07063065680.
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣9️⃣82

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]






_MY FIRST NOVEL _


Banza tai masa ta dauke kanta, yakuma kallonta yace
"Gayamin mana"
A fusace tace "bazan fada ba, meye hadinka da damuwa ta?"
"Nasan kinajin haushina saboda kuskuren da'aka samu, amma...
" kace kuskure? Ba wannan ne karo na farko daka mareni ba, kace na fiye maka shishshigi, nakuma yi Alkawarin na dena yimaka kaikuma meye naka nayi min shishshigi, dalla matsa kabani guri in wuce"
"zan baki guri ki wuce, amma meyasa kika damu dani haka, kike bani wannan kariyar bansaniba, dukda irin halayena? Kinyi kokarin kareni a lokuta daban2 bansaniba meyasa? Gashi kinsan abubuwa dayawa dani ban saniba, at least kin haska wani bangare a Rayuwata da yakasance me tsananin duhu, nesanta Jeje dani hakika haskene me yawa a rayuwata, bansan ya akayi na yadda da Jeje nafara wannan muguwar rayuwar ba, kawai na tsinci kaina a wani yanayi dani ka dai nasan menakeji, amma meyasa kika temakeni, kike kokarin ganin kin canza akalar Rayuwata?" yai tambayar yana kara tsareta da ido, itama kallonsa takeyi dan bata san mezatace masa ba, wani uban tsaki taja ta wuce ta gefensa ta fice daga dakin.
A hankali ya koma ya zauna yana tunanin abubuwa da dama, abubuwa dayawa ya dinga tunawa, Jalila tayi Rawar gani a Rayuwarsa, yanzu ya gane abubuwa dayawa da a da sam besan dasu ba.
Itakam guri tasamu tai zamanta taki komawa cikin gidan tanata zancen zuci, karar motar Jawwad ne ya dawo da ita hayyacinta, shida Abba ne ya dakko shi a Airport, da fara'a Jalila ta tashi ta nufi inda suke, Abba yace "Jalila bakida lafiya ne? Naga kin rame haka" murmushi tayi "Haba Abba duk wannan kibar danayi kayana sunmin kadan fa"
"Anya kuwa in yadda? Idonki kaman kinyi kuka fa"
"Abba nikam meze sani kuka yau zanganka? Bacci nayi kawai, kawo jakan in rike maka" tasa hannu ta karbi jakarsa, Jawwad yana ganin dakiyar Jalila daka ganta kasan tana cikin damuwa, amma ta maze tanata kokarin boye damuwar.
Ba karamin murna sukayi ba dawowar Abban nasu, Jalila tasan koba komai zata samu saukin wani Abun,
bayan sallar magariba suka gabatar masa da Abinci yaci, nan suka sake aka shiga hira da Abba, Maama tanata dan dari2 kar Jalila tagaya masa wani abu, dan ta lura tun dazu Abba yake tambayar Jalila koda matsala amma tace ita ba komai. Sekusan goma na dare suka watse suka tafi dakunansu.

Ilham tagaji da azabtarwar da Jalal yake mata, yakamata sunemi wata mafitar, tsawon shekarun datayi a gidansu Jalal bataga alamar zasu cinma burinsu ba, Jalal mugun baudadden mutum ne, ga tsabar jaraba da masifa, gashi da rashin yadda, kwanan nan ta lura kaman yakara tsanarta batasan metayi masa ba, ta lura yanzu har uwassa ma yakara fita harkarta, ko cikin gidan baya shigowa, mikewa tayi ta tafi palourn mummy, ta tura kofa bako sallama ta shiga ta samu guri ta zauna
Mummy ta kalleta tace "Ke lafiya kika shigomin bako sallama meye haka?"
"Mummy yaushe zaki cikamin alkawari na ne?"
"Wanne kenan?"
"Mummy har yanzu banga alamar Yaya Jalal ze yadda ya Aureni ba, lokaci fa kuremin yake ni macece yakamata zuwa yanzu kiyi wani abu akai, ina sonshi, banajin zan iya Auren wani bashiba, kitemaka Mummy dan Allah kiyi wani abu" Ajiyar zuciya Mummy tayi "Ilham yakikeso inyine? Yaron naan kullum wutar kiyayyata ruruwa take a ransa, kiduba rashin lafiya nayi amma da naje kansa ga yadda ya rikice gana sambatu infita baya son ganina, ya zanyi Ilham? Kaina ya kulle al'amarin Jalal sunfara bani tsoro"
"Kina nufin in hakura dashi kenan?"
"Bahaka nake nufi ba, amma kidan karamin lokaci, nina miki alkawari ai, bakuma zan saba ba"
"Shikenan Mummy seda safe" Ilham ta tashi ta fita ranta a bace, ji take kaman ta shake Mummy, takoma dakinta ta kulle kofa, ta dau waya takira ummanta tagaya mata abunda ke faruwa, tace mata ta kwantar da hankalinta, in tasamu lokaci taje gida, zasu san yadda zasu bullowa lamarin Jalal da Mummy.

Da sassafe Jalila suka shiga kitchen hada Abinci, bayan sun kammala kowa ya hallara a palour don karyawa, bayan an gama breakfast suka shiga hira, anan Maama ta sanarda Abba ai Naja tazomusu hutune, sannan akwai maganar datakaeso zasuyi da Abba amma ba yanzuba, ba karamin faduwar gaba Jalila taji ba dan tasan be wuce zancem Auren Jawwad da Naja ba.
Abba nan yashiga rarraba musu tsaraba kamar yadda ya saba in yayi tafiya, Abba yabada zuma a gwangwani yace akai gidansu Jalal, A ajiyewa daddyn Jalal, ya daga waya ya kira Jawwad yace yana son ganinsa, bayan yagama waya da Jawwad ya kalli Jalila yace
"Baby Babanki yayo waya daga Kaduna (baban Hanan) yace nan da kwana uku zasuzo, yanaso zasuje dake Bauchi yana neman Izinina, nace masa inkin amince ba damuwa amma bana so ki dade a can" Jalila tai murmushi tace "Na yadda Abba, zanje" Nana kam ta hade rai tace "Ni gaskiya ban yadda ba" Abba yace "Jalila nayi mamakin saurin Amincewarki da batun tafiyar nan, iya sanina dake ba kyason barin gida, amma ya'akayi haka, ko akwai wani abu bakyason gayamin ne?"
"Haba dai Abba, ba wani abu ni kawai inason inzaga inje garuruwan dabantaba zuwa ba"
"Eh hakan yana da kyau, amma bazan bari ki dade ba kinga ga komawa makaranta"
Jawwad yai Sallama ya shigo palourn, ya durkusa ya gaida Abba sannan ya gaida Maama, aciki ta amsa masa dan tanajin haushinsa, yakoma gefen Abba ya zauna yace
"Abbana gani, Allah yasa ba laifi nayi ba"
"Aini baka laifi a gurina, da dai wannan ce tafi kowa iya laifi" Abba ya fada yana nuna Nana, dariya sukayi, yayinda Nana ta dan hade fuska da sigar shagwaba tace "Abba niko? Aikam bana wani laifi ni" Abba yace "Anya kuwa a tambayi Jalila?" haka Abba yasake ya dinga wasa da dariya dasu, banda Maama da take ta cika tana batsewa, Naja kam dama tuni tabar gurin, Abba ya kalli Jawwad yace "Babban mutum, daddynka yamin magana yace yasamo maka aiki a NNPC amma kace kai A'a, yace in rarrasheka ka karba, meyasa bakason Aikin"
"Abba ba banaso bane ba, banason tafiyane saboda Jalal, bansan wani hali ze shiga ba, dukda Alhamdilillah ana samun cigaba a daidaituwar lamuransa, amma banason in tafi yacigaba da mummunar Rayuwa tunda......... Ai kafin yakarasa a fusace Maama tace" Jalal din ubanka ne? Kai meyasa bakada tunani ne? Ana nema amaka gata amma kana maganar wani, baka isaba seka karba ka tafi, tunda kagama karatun zaman jiranwa zakayi? Shiru Jawwad yai bece komai ba, a hankali Nana da Jalila suka zame suka bar palourn ya rage saura Maama, Jawwad da Abba, Abba yace "Jawwad tashi kaje zamu karasa maganar" Jawwad ya tashi ya tafi, Abba yace

"Waime yasa mata wasunku bakuda halaccine? Haba Maman yara, Abunda Jawwad yayi, yai dai2 shine halacci irin kaunar da yaron nan yake masa bekamata kice hakaba, ki kyale shi zuwa wani lokaci tukuna mugani, kinsan kowane dan adam baya wuce rabonsa"

"Naji, Amma Jawwad ya kai munzalin da a yanzu yadace ya fuskanci Rayuwarsa, ya nemi Aikinyi sannan ya mallaki iyali"
"Eh gaskiyane, samun Aiki ba wani babban Abu baneba, kuma bacewa yayi bazeyi Aikin daza'a samomasa ba sedai yace abashi lokacine saboda Jalal, Amma kuma aini har yanzu becemin ga wata wadda yakeso ba tukuna, kinsan mutumin nawa da kunya Akwai fulatancin sosai a tareda shi, Allah yasa ko budurwa ma yanada ita" Abba ya karasa zancen cikin murmushi, Maama tace "inma bashida ita se asmomasa, bazan cigaba da zura masa ido se ya tsofe ba Aure ba, dama maganar danakeson yimaka kenan, ga Naja nan 'yar gidan Yaya mairo da ita nakeso in hadashi, tunda yarinyar itama ba laifi akwai hankali" Abba ya danyi shiru sannan yace
"To banki ta takiba, Amma banason ayi abunda ze zamana an cutar da dayansu, yakamata muji ta bakinsu tukuna"
"Kamarya semunji ta bakinsu, muba iyayensu bane ba dole subi abunda mukeso, hakan ze kara karfin zumuncin dake tsakaninmu"
"To Allah ya tabattar mana da alkhairi, ni bari in wuce daki zan dan kwanta, kar amanta akaiwa Baban Jalal wannan zumar"
"Za'akai" Abba ya wuce daki.
Jalila tanata tunanin yazata bullowa wannan lamarin, dan in aka hada

Please Login or Register in order to submit comment