Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai, da kuma shekaru goma sha hudu sakamakon lalata da kanan yara mata.
Sekuma su Jeje da'aka yankewa hukuncin shekaru ashirin2 a gidan prison.
Daddy ne yasa hannu ya karbi Jaridar shima ya duba, Jalal yace
"Mummy Allah yakawo karshen mutumin da dasa hannunsa a lalacewata, shiyabada kwangilar koyamin shaye2 saboda ya huce takaicin abunda kikayi masa akaina, kalli keda laifi nida karbar hukunci"
Daddy yace
"Jalal kai waya gayamaka shiya bada kwangilar hakan?"
"ba gayamin akai ba, Jeje abokina yaronsa ne, idan nagaya muku wanda yayi sanadiyar kama Jeje da uban gidansa har nasan wannan lamarin kila karyatani zakuyi, sanin hakan bashida Amfani, Mummy yakamata ki zubar da makamanki kikoma ga Allah tun kafin kema ya dankeki, Kabir makiyinane na boye bansan dashiba sedaga baya, nasan makiyana na fili, suma ina nan nasasu a Addu'a very soon Allah ze yimin maganinsu"
Yasa hannu ya dauke Jaridar ya fice.
Daddy yaja ajiyar zuciya yace "Khadija lokuta da dama bana ganin laifin yaron nan, ba wai ina goya nasa bayane ba, amma kinmasa laifuka masu tarin yawa, ba kya duba haka se wanda yakemiki, anyway Ansamosa aikinyi na gwamnati wanda muke saka ran ze dauke masa hankali daga kan shaye2"
Kallon Daddy tayi tace "bangane ansamosa aiki ba, wani irin Aiki? Me Jalal yanema yarasa da zeyi wani aiki, ina kamfaninsa na sarrafa robobi meyasa bazaka bashi abunsa ya rike ba?"
"ba an samomasa aiki ne dan wani abuba, ansamo masa ne dan hakan zesa yayi kokarin dena shaye2, kuma bazan iya cewa wanda yasamo masa din A'a ba, kuma nima naga dacewar hakan"
"wai waye ya samo masa?" ta tambaya cikin kosawa
"General Abdurasheed ne"
Dan zare ido tayi tace "Ina yasanshi daze bashi aiki, sannan wani irin aikine haka? Dan dana baze aikin soja ba"
"Eh ya gayamin Jalila ce tace tanason yasama masa aiki a NDLEA, hakan ze temaka masa wajen dena shaye2"
Hade rai tayi sosai tace
"Baze yuwu ba, baza'a mayar minda ďa bawa ba,
Akan mene? Meye hadinta dashi dazata sa a samo masa aiki, banda cin mutunci tasan yana shaye2 shine zatace yayi aiki a hukumar yaki da shaye2 salon tasaka akama shi, kokuma taji dadin juya shi yadda takeso ko? Dama yanzu na fuskanci maganarta yakeji akanta ba irin wulakancin daba yawa Ilham, to bata isaba da raina babu yarinyar dazata juyamin ďa, baze yuwu in haifi ďa wata ta juyamin shiba"
Mikewa daddy yayi tareda yin murmushi yace "Eyya kin makara khadija, duk abunda kayi se an maka, ki gode Allah da yarinyar ba cutar dashi take ba, dan ta damu da halin dayake cikine hartasa a sama masa aiki, nayi farinciki da hakan, kuma batun kice baza'a juya miki ďa ba daga baya kenan aikin gama ya gama" be jira yaji martanin da zatayi ba ya shige bedroom ya kulle kofarsa.


Jawwad ko sallama basuyi da Jalal ba suka tafi bauchi shida Abba.
Maama kam a sukwane take tambayar Jalila "me Abba ke nufi, me kika gaya masa haka? Sannan wa zeje nemawa Aure?
"niba abunda nagaya masa, yaushe rabon da in zauna dashi balle ince masa wani abu, nibansan waze nemawa aure ba be gayamin ba"
A fusace Maama takoma dakinta tana tunanin yazata bullowa lamuran.

Jalila takoma daki suka dinga murna itada Nana, Jalila tace "Nana ban taba zaton Abba ze yadda da abunda nagaya masa ba"
Dan bata rai Nana tayi tace "Jalila nayi mamakin abunda ya fusata Abba haka, har yayi fushi yake ikrarin abar masa gida, nayi mamaki sosai be taba hakaba fa"
"to yanayi na rayuwane Nana, tunda kikaga haka akwai abunda ya bata masa raine, sannan akwai dalilin dayasa yayi haka"
Nana ta dan numfasa tace "Jalila nifa damuwata naji Abba yana batun akawo kudin Aurena, Allah yasa ba dana Yaya Jawwad za'a hadamin ba, nan da wata hudu da 'yan kaifa kenan"
Nana takarasa maganar kaman zatayi kuka
Jalila tace "to meye aciki? Keda rabin rankine fa Mahmud zaku kasance inuwa daya"
"To Jalila karatun fa? Kinsan Mahmud a kasar waje yake nasa karatun tayaya abun ze yuwu?"
"ze yuwu mana, kicigaba da naki karatun a can riba biyu, Allah sarki Rayuwa hajiya Nana za'a zama matan Aure, bari in lissafa yaushe zaki haihu"
Hade rai Nana tayi "Ke Jalila komai sekin sako wasa a cikine? Inamiki maganar serious kinamin wasa, ke yanzu akace za'ayi aurenki nan da watanni hudu kin shiryane? Ni yanzu ma meyasa Abba bece a hada dake ba"
Dariya Jalila tayi tace "gidan Ahmad yana bauchi, shi yana aiki a maiduguri, ni ina karatu a kano tayaya kike zaton inyi Aure yanzu, se nagama tukuna"
Wayar Jalila tafara ringing, ta kalli Nana tace "Excuse me, let me pick the call"
Nana ta daga mata kai, Jalila ta amsa wayar tareda yin sallama
Amsamata yayi sannan ya dora da "Babyna kwana biyu kin gujeni you are not picking my calls, ina fatan ba laifi nayi miki ba?"
Cikin siriyar muryarta na shagwaba tace
"Ohh no ni bakamin laifi ba, bana dan jin dadine kawai, amma yanzu Alhamdilillah naji sauki"
"Ya salam amma baki gayamin ba, yau zan shigo kano dama shiyasa na kiraki, in kin amince zanzo in ganki"
"Babu damuwa my one, ina fatan in ganka nima am missing you"
"Like serious, karkisa inyi Ihu attention din mutane ya dawo kaina"
Murmushi tayi tace "ba sekayi ihuba, aini yakamata inyi, kwana nawa zakayi a kano?"
"zanyi sati daya Insha Allah, zanyi wani assignment ne"
"Shikenan Allah yakawo ka lafiya"
"Ameen my queen, bazaki tambayi Antynki ba?"
Dan yamutsa fuska Jalila tayi tace "Ainasan tana lafiya tunda najika haka"
Murmushi yayi yace "Queen da alama kinada kishi sosai, anyway sena shigo, idan nazo da wuri zaki ganni yau, in ban shigo da wuri ba se Allah ya kaimu gobe"
"to shikenan Allah ya kaimu, take a good care of your self"
"Ok Baby i will Insha Allah" ta katse wayar, Nana ta zuba mata ido tana kallonta, Jalila tace "Madam lafiya kuwa?"
"Lafiya mana, nina kasa gane inda kika dosane, gane lamarinki se Allah mutum baya taba ganeki, gaba daya rayuwarki zigza ce"
Sosai Nana tabawa Jalila dariya tace "rayuwartawa ce zigza, lallai ma Nana bakida dama, Rayuwata normal ce kaman ta kowa"
"A'a ban yadda ba, Allah yasa ayi miki aure kafin ayiwa Yaya Jawwad"
"Ba Ameen ba, back to sender muguwa kawai"
"eh amma ni kikayimin fata saboda son kai"
Wayar Jalila ce takuma daukar ruri, ta kai hannu ta dauka tana dubawa taga Hanan ce dan haka ta kashe wayarta.



Tunda suka fara tafiya Abba beyiwa Jawwad wani gamshashen bayani akan wannan tafiyar ta bazata ba, yanason yayiwa Abba magana amma yakasa duk sunyi shiri Jawwad na driving,
"Dama Aliyu akwai wadda kakeso kaki ka gayamin kabari ake kokarin auramaka wannan yarinyar?"
Tambayar tazowa Jawwad a bazata, kuma idan yaji Abba ya ambaci sunansa na gaskiya kai tsaye haka, alama ce ta he is so much serious.
Jawwad ya dan sosa keya yayi shiru
"yaka sosa kai kayi shiru? Kamin bayani mana"
Cikin kame2 Jawwad yace"Amm.. Dama Abba, ai..."
Abba yacce " Jawwad da farko sister dinka Jalila tagayamin inyi bincike akan yarinyar nan Naja, tacigaba da gayamin hakan, sannan taki gayamin komai game da Naja, sedai cewa inyi bincike, tacigaba da nunamin cewa kunyarka da kawaicinka baze bari ka nuna abunda ke ranka ba, na dauki maganarta serious nafara kokarin bincike, ina kan binciken ne, Mahaifin Hanan ya kirani yamin magana akan in dai dagaske kana son 'yarsa yabaka dama ka fito, wanda ni bansan da zancen ba, nayi kokarin in zauna da kai muyi maganar kafin ta kai ga haka Jalal yazo ya sameni har gurin aiki yamin bayani akan alakarka da' yar gidan general Abdurrasheed, sannan ya daukeni ya kaini inda aka gayamin komai akan Naja, bantaba tunanin Mamanka zata zaba maka mace irin wannan mara kamun kai a matsayin mata ba, Jawwad meyasa baka gayamin abunda ke ranka ba, kabari nakusa gangancin saka rayuwar ka a hatsari? "
"Abba nasam bazaka zabamin abunda ze cutar dani bane, banason bijirewa umarninka dana Maama, shiyasa na amince"
"Nasan da wannan Jawwad, amma dukda haka a matsayin mu na iyaye yanada kyau mudinga baku zabi, ba wai bin son zuciyarmu da tirsasamuku akan abunda bakwa ra'ayiba, yana da kyau kadinga faďan ra'ayinka ba laifi bane naji dadin kokarin yimana biyayya dakayi, Allah yayi maka Albarka yakara haďamin kanku, Allah ya shirya mana ABDUL JALAL dukda kasancewar halinsa amma yadamu da lamuranka sosai, yadda yazo ya sameni kaman zeyi kuka, Alhamdilillah nayi mamaki naga abubuwan sa sun fara raguwa, yafara dawowa hanya, ya rage rashin ji"

"hakane ya rage sosai makuwa, abokiyar fadansa keta kokarin sashi a hanya ai"
"Wa kenan?" Abba ya tambaya
"Jalila mana, tanata kokari akansa, kuma naga inga masa nasiha koba duka ba yana ďan dauka"
Abba yace "masha Allah, at least kaga an samu improvement, itama General Abdurrashed yamin magana, yace akwai abokin ďansa dayake sonta, wai Ahmad sunansa kowaye?, yabiyo ta hannunsa a nema masa Aurenta, amma nace na bashi wuka da nama shima babanta ne, duk abunda yaga dace yayi"
Jawwad yai murmushi yace "hakane Abba, lokacin da mukaje kaduna yamin zancen nima, yace shima mutumin sojane yana da kirki sosai"
"Hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi yamuku zabi da abokan zama nagari" Jawwad a zuciyarsa yace Ameen.



Hanan taita kiran wayar Jalila amma Jalila taki dagawa, saboda bataji dadin abunda Hanan tayi mata ba, sako Hanan ta turimata kamar haka

"Assalamu Alaikum, Am very sorry my twiny, nasan na miki laifi kiyi hakuri dan Allah, Yaya Jawwad yazo kano shida Jalal, yamin bayanin komai abunda ke faruwa, kiyi hakuri so dakuma kishinsane yasa namiki haka, sannan naji Yaya Abdallah yana maganar Ansamawa Jalal aiki za'a gama interview ranar laraba amma har yanzu bejeba, you have to take action"

Jalila nagama karantawa ta kira Hanan, seda Jalila ta kira sau biyu sannan Hanan ta dauka tace
"'yar rainin hankali inata kiranki kinki ďagawa, amma da kikaji batun ABDUL JALAL harkin kirani"
Jalila ta hade rai kaman Hanan na ganinta tace "ke banason wulakanci, ai banji dadin abunda kikayimim ba sam wallahi"
"Nasani amma ai nace kiyi hakuri, you won't understand how far my loves go on your brother, inasonshi ina kishinsa shiyasa na shiga damuwa, inata addu'a dai amma ina cikin damuwa Queen"
Tausayin Hanan yakama Jalila tace "ki kwantar da hankalinki kinji my twiny, komai ze wuce kece zaki zama matar Yaya, ina nan ina tayaku da Addu'a"
"Masha Allah, Allah yabiya ki da mafificin Alkhairi Jalila, bazan iya biyan kaunar da kike nunamin ba"
"bakomai Sister na, nace are you serious Jalal beje interview din nan ba?"
"Wallahi dagaske nake miki, hala aikinma kekisa aka samo masa?"
"to meye naki aciki nason kisani, nice nagayawa Daddy ya samo masa, kuma be isa ya watsamin kasa a ido ba zan sameshi, seyaje interview din nan"
Dariya Hanan tayi tace "wai zaki sameshi irin Mum din nan tasa, kai lamarinku din nan yana birgeni wallahi, kowa da guntun taurin kansa dan Allah duk yadda kukayi ki gayamin dan wallahi....
Katse wayarta Jalila tayi jin Hanan zata fara mata bare2.



Ilham shiryawa tayi takanas ta tafi gidansu, domin taji abunda yakamata suyi, dan ita ta riga ta karaya da lamarin nan bata tunanin akwai nasara dan kullum Jalal kara bauďewa yake, babu alamar ze sakko.
Tayi sa'a ummannata tana gida, suka kule a daki kaman yadda suka saba in Ilham ďin tazo.
"Umma nifa najiki shiru ya'ake cikine? Na ďora mata sata amma Jalal bakiga rashin mutuncin dayayi min ba, wallahi son yarinyar nan yake, kincemin zakije Nijar gurin wani malamin amma shiru kullum abubuwan kara tabarbarewa sukeyi"
Umma tace "ke nayi maganar zuwa nijar, munyi waya da mutumin na masa bayanin komai, amma budar bakinsa wai yayi bincike akan yarinyar indai inason a yimin aiki akanta zan bashi dubu ďari biyar, nikuma ina naganta? Banida ita bani da wata kadara da zan sayar in bashi wannan uban kuďin, dan haka nakoma gurin wanda muke zuwa tun farko, shikuma yacemin baze iya aiki akanta ba sedai a kara watsa rayuwar Jalal"
"to Umma batun Auren namu fa?"
"shima za'ayi ne amma yace muďan kara hakuri"
"umma kenan, mu kara hakuri fa kikace? By mistake idan Asirin ya karye gaba ďaya kuma yaya zamuyi?"
"bazeyiba, malamin yabani wannan tabbacin ki kwantar da hankalinki burinmu seya cika, sena wulakanta shi shida uwarsa hada uban nasa, bana yafiya ga wanda yamin laifi"
"to shikenan Umma, Allah yasa, ni bari in tafi, zan ďan tsaya inyi siyayya".



Dogon wandone a jikin Jalila da riga, dan haka ta ďakko katon hijjabinta me hannu tasaka ta fito part ďin Jawwad taje tana tsammanin ganin Jalal a can amma baya nan, rabonta da shiga gidansu Jalal kuwa harta manta, direct ta nufi gidansu Jalal, amma tarasa ina zatayi tasan dai be dace ta tafi part dinsa nemansa ba, fasawa tayi ta juyo tanufo gate zata fita itakuma Ilham ta shigo.
Tsayawa sukayi suna kallon kallo itada Ilham, haďe rai sosai Ilham tayi tareda yin tsaki tazo zata gifta gefen Jalila ta wuce, caraf Jalila tasa hannu ta riketa ta janyota gabanta suna fuskantar juna, a fusace Ilham tace "ke dalla malama meye haka? Meyasa bakida tunani ne?"
Jalila taja wasu seconds tana karewa kwayar idon Ilham kallo sannan tace
"banida tunani kam, dole ki fadi haka, kinsan ba'a tabani a zauna lafiya, dan haka sekinyi hakuri da duk abunda zaki gani har se kin biya abunda kikayimin"
Hararta Ilham tayi takuma kokarin rabawa ta wuce ta barta, amma Jalila takuma shan gabanta tace
"Ilham nasani tsawon shekaru ina bata miki rai, kinyi alwashi daban2 akan ganin bayana, baki taba nasara ba se wannan karon da kika ďora min sata, to bari kiji in gayamiki wani abu dabaki saniba, babu abunda zakiyi a rayuwa ki rama abunda nayi miki, na riga nagama dake Ilham, kuma Wallahi Jalal baze taba aurenki ba, nagaya miki dama muddin kudirina yayi karo da naki sena watsa naki, kudirinki akansa yaci karo da nawa na watsa shirinki watsawa ta har gaban abada zanso ingaya miki wani abu daya kamata ki sani amma ban saniba ko kinason ji"
Kallonta kawai Ilham take batareda tayi magana ba, Jalila ta ďora tace
"Ranar da Jalal ya kwanta a Asibiti, kukazo duba shi keda Mahaifiyarki kisani idonsa biyu yaji duk abunda kuke faďa, dan haka ki cirewa ranki cewar burinki ze cika, Na riga naganoki Ilham tuntuni shiyasa nayi miki illa inda ba wanda ze gani, na illata shirinki bakida wata dama data miki saura, damarki ďaya shine ki jajirce kicigaba da jarraba sa'arki kozaku daidaita"
Jalila takarasa maganar tana mata wani mugun kallo sannan ta juya tayi ficewarta, gaban Ilham ne ya shiga dukan hamsin2, kaddai Jalila dagaske take, amma to in hakane da yaji aida yaďauki mataki, "kai karyane bejiba, koma yaji wallahi seya Aureni, se burin mahaifiyata yacika"
Ta shige cikin gida da sauri hada tuntube.

Maama takasa zaune takasa tsaye, Naja batasan budurin da'akeba dan lokacin da Abba yayi wannan maganar bata nan tafita yawonta, harta dawo Maama tarasa ta inda zata fara mata bayani.

Jalila na fitowa taga Jalal ya dawo a mota, yana kokarin shiga gida, ganin da yayi ta tsaya ta ki tafiya ta kura masa ido yasan akwai magana a bakinta, tsayawa yayi agaban ta yayi parking, yana tsayawa ta zagaya inda yake, ďan ďage mata gira yayi alamar meke faruwa?
Ďan kallonsa tayi tace
"daga ina?"
"kin aikenine?" ya tambayeta
"Ohh No Allah yabaka hakuri"
Yace "Ina Jawwad ne? Na duba baya nan ban san inda ya tafiba?" hade rai tayi itama tace
"ka duba shi mana, kokabani ajiyarsa ne?"
Kallonta yayi, wato ta rama kenan
Yace "A'a ban baki ajiyarsa ba"
"dama.." sekuma tayi shiru
"Dama me?"
"inada magana ne"
"fadi ina jinki"
"toka fito daga motar mana"
"In fito kuma? Gaskiya ni yunwa nakeji, zuwa zanyi in kwanta, naje neman Abinci narasa me zanci, dama in kin bawa Jawwad nake ci nima amma yanzu baya nan nasan bazan samuba"
"Hmm to kace Ilham tabaka mana"
Hade rai yayi sosai yana Kallonta, sunkuyar da kai tayi tana dariya kasa2
"Yi hakuri, ai yanzu mundena faďa ka jirani a part din Yaya Jawwad zan kankaro maka kanzo in za kaci" tayi maganar tana dariya, tana matukar kyau idan tayi dariya, gyaďa kai yayi ta juya ta tafi, yabi bayanta da kallo harta shige gida, sannan yaja motar ya shiga da ita gida.
Gida takoma taje ta ďakko masa breakfast ďin Jawwad da yatafi beci ba, dayake da zafinsa a cikin flask, tana zuwa ta tarar dashi a zaune a palourn Jawwad yana jiranta, ta shiga tayi sallama amma be amsaba, seda tazo kansa ta tsaya takuma yimasa sallama ya ďago ya kalleta ya amsa a hankali, ta ajiye tray din tace
"Yana daga hakkin musulmi akan musulmi in yayi sallama ka amsa masa, kadinga amsa sallama please"
Shiru yayi yaki kulata, Jalila tarasa wane irin miskilin mutum ne Jalal, koma tace ďan rainin hankali kana masa magana yana jinka amma yayi maka banza dan tsabar wulakanci,
ta aje masa Abincin ta zauna a kujerar dake kallonsa. Ta danne fushinta
Ya hada Abincinsa yafara ci, can yace "Me ya kai Alqur'ani dana baki hannun Ilham?" yai tambayar kamar bashi yayi ba
"ďauka tayi" tabashi amsa a takaice
"Ya'akayi ta ďauka baki hanata ba?"
"Ina bauchi aka aikota taganshi shine ta ďauka"
Bekuma cewa komai ba yacigaba ds auna loma, can Jalila tace
"Ya akai kasan yana gurin ta?"
Kallonta yayi ya danyi murmushi
"in kinaso in dawo miki dashi, yana gurina, amma bakiga abunda na ajiye a cikiba ko?" ďan yatsina fuska tayi sannan tace
"Nifa tsawon lokacin da yayi a gurina banga komai a ciki ba"
"zan dawo miki dashi kikuma dubawa"
"to naji zan duba"
Ya cigaba da cin Abincin sa, can ta ďan nisa tace
"An baka aiki ance kaje interview kaki why?"
Ďagowa yayi ya kalleta, "dama nayi tunanin kece kikasa aka nemamin wannan aikin, tayaya ina shaye2 zakice asamomin aiki a hukumar dake yaki da shaye2, amfanin me zanyi ko nima so kike a kamani?"
"calm down let me explain, mezesa in so akamaka? da hakane naso akamaka da nasa an ka maka kaida abokinnaka jeje ai"
ďagowa yayi ya haďe rai kaman be taba dariya ba
"Am sorry banyi hakan da wata manufa ba, sedai inkana aikin na farko ze rage maka yawan damuwa, sannan ze sa ka kara kokarin kadena shaye2 kaima, at least in kana da gurin zuwa ze kara dauke hankalin ka daga kan Shaye2"
Zuba mata ido yayi yana tunani daban2 akanta, ta damu dashi dayawa, she's so simple and calm, matsalarta kawai taurin kai da rashin kunya, Amma tanada zuciya me kyau.
Tsarguwa tafara yi da kallon dayake mata tace
"Ya dai?"
"meyasa kika damu dani haka?"
Shiru tayi dan bata san mezatace masa ba, basarwa tayi tace
"dan Allah kaje interview din nan karka watsamin kasa a ido"
"Senayi shawara" yabata amsa
"shawara kuma, dan Allah mene kuma na wani shawara dan Allah Yaya Jalal kaje please karkasa inji kunya" da shagwaba takarasa maganar
Bude baki yayi tareda yin murmushi kaman karta dena magana
"Nine Yaya kuma yau, yarinyar bakida kunya fa"
"Aida ďinma dan muna fada ne amma yanzu mundena faďa, dan Allah kaje ba dan halina ba, kaji Yayana ďan gidan daddy abokin Yaya Jawwad, badan halina ba" murmushi yayi ya ďan girgiza kai yace
"Aikuwa kinsan indan halinkine bazaniba, innayi tunani zan gaya miki"
"to Allah yasa inji alkhairi"
Be amsaba ya kai hannu ya dauki cup ya kai bakinsa amma jikinsa yafara rawa yakasa kaiwa
"lafiya menene kuma?"
Ajiye cup din yayi, yai shiru yana rintse ido"
Da sauri ta mike ta nufi inda yake tana faďin "Subhanallah meyafaru?"
Dagowa yayi idonsa yayi jawur yace
"Gi.. Giy..... Giya,.... Giya zansha, ita nakeson sha"
"giya kuma? Meyasa zaka sha giya?"
Numfashi yake ja ya mike tsaye ya nufi hanyar fita, idonsa yayi jawur jikinsa se rawa yakeyi da sauri ta sha gabansa
"dan Allah Jalal karka sha giya, meyasa idan kuma kasha ka bugu daga nan ka mutu mezaka cewa Allah? Dan Allah karka sha kayi hakuri zaka ji bakason sha"
Tureta yayi ze fita, takuma tare kofa tana masa magiya, yasa hannu ya hankadata jikin kofa ta bige kafaďa ta faďi a gurin shikuma ya fice kaman wani horrorn dayake bukatar jini.



Godiya mara iyaka ga members na kungiyar mu me tarin Albarka Perfect writers association, Allah yakara haďa kanmu.
Abdul Jalal Novel Fans❤️🌹 kaunarku a ruhina take, inajin dadin comments dinku hada wakokin da'ake reramin😂😂😂
Masu bina private suna min comment kokuma bani karfin gwiwa, da masu biyoni suna neman littafina da masu karantawa wanda bansansu ba ina godiya Allah yasaka da alkhairi Allah yabar kauna.

Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️

What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*ABDUL JALAL*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹


*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(𝕎𝔼 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 𝔹𝕌𝕋 𝕎𝔼'ℝ𝔼 𝔸𝕃𝕎𝔸𝕐𝕊, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 𝕆𝕌ℝ 𝔹𝔼𝕊𝕋 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ 𝕆𝕌ℝ ℝ𝔼𝔸𝔻𝔼ℝ𝕊💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/





_*Story, &writing*_


_and edited_

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)


*P.W.A*✍️



PART 2️⃣
_PAGE 4️⃣1️⃣94


Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724



_MY FIRST NOVEL _


Jalila ta bugu sosai, ta rike hannunta tana rintse ido saboda azabar zafi, shikam yasa kai ya fice yabar dakin.
Ta dade a gurin a zaune, sannan ta mike ta koma cikin gida tana yamutsa fuska.

Su Jawwad kam har la'asar sannan suka isa Bauchi, Abba yakira daddyn Hanan a waya yagaya masa sun karaso, aka turo wasu sojoji sukazo suka tafi dasu har estate din, Ba Jawwad ba har Abba seda yayi mamaki irin tsaruwar da estate din yayi sekace barrack duk inda ka juya sojoji ke shawagi a ciki, akai musu Jagora zuwa gidan daya kasance nan ne center.
A dankareren dakin Daddy akayi musu iso, da murna daddyn Hanan ya tarbi su Abba, suka gaisa yai musu barka da zuwa, seda suka fara gabatar da salla sannan daddy yai umarnin akawo musu Abinci.
Wasu matasan 'yan matane dabasu wuce sa' anin su Hanan ba su uku suka kawo Abincin suka ajiye, tareda gaida Abba da Jawwad, ďaya daga cikinsu wadda da gani kasan hutu da jin dadi ya ratsata tace
"daddy wannan yana matukar kama da Yaya Yusuf, ko shine sirikin naka?" Jawwad ya sunkuyar da kai saboda kunya
Daddy yace
"kaniyarki yusra, sarkin surutu, tunda kunkawo Abincin kukoma, ki gayawa Inna bakin sun iso zasu shigo anjima su gaisheta"
Murmushi Yusra tayi tace

"Yadda kace haka za'ayi daddy"
Abba yace "General wannan ma 'yar wajenka ce?, tana kama da Hanan"

"' yar wana ce, gaba dayansu yaran 'yan uwanane, Aini Hanan da Abdallah kadai Allah yabani, sekuma diyata Autar mata Jalila, Zuma kenan ga zaki ga harbi"

Gaba daya sukayi dariya, daddy yace su ci Abinci, Amma gaba daya Jawwad yakasa sakewa yaci Abincin nan saboda kunya "Sekace wani mace🙄, (ya kuke gani in goga Jalal ne? 😂 yaseen

Please Login or Register in order to submit comment