Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyarawa daki, yayi fata2 da komai, kuma in ban gyara masa ba a haka ze barshi, kar inje ya bugu yace ze shiga dakin ya kwanta a haka" Jalila tai murmushi tace "Allah yasadaka da dukkanin wani alkhairi na duniya da lahira hakika ka cancanci yabo, Yaya Aliyu Jawwad sha gwagwarmaya, amma meyasa sekai zaka gyara masa?"
"Kinsan halin dan uwan nawa, bakowa yake so yashigar masa daki ba, baya son sa ido"
"Hakane muje in tayaka"
"Anya kar in takura miki fa"
"Bawani takura gyaran gida aina matane" ta rakashi suka dakko tsintsiya suka fito akan idon Naja suka fita tare aikuwa tasaki Ashar, Da sauri Nana ta kalleta "Lafiya kike mana Ashar haka sekace ba musulma ba"
"Dalla rabu dani yanzu nacewa Jawwad ya rakani unguwa yace bazashi ba yanada abunyi, amma kalli sunfi ta tare da wannan jakar yarinyar, zasu gane kurensu bari Maaman ta dawo" Nana ta tabe baki tace "Wallahi Naja duk inda kikaje sekinja masifa, muna zamanmu lafiya amma kinzo zaki tayar mana da hankali Aikin banza kawai" Nana ta mike ta fice tabar mata dakin.
Jalila ta dinga taya Jawwad suna kwashe kayan daya fasa suna fita dashi a hankali dakin yafara hankali kula tayi kaman Jawwad yagaji sosai tace "Yayan Baby what's wrong" yace "Baby yunwa nakeji sosai, ga Jalal yafice ban san inda ya tafiba koya ci Abinci oho"
"Allah sarki jekaci kadawo ina jiranka, Abincin yana nan a kitchen"
"God bless you my dear, yanzu zan dawo Insha Allah"
Sosai Jalila tacigaba da aikin dakin, bedroom din zuwa palour ta gyara komai, taje tana goge kan fridge kawai ta bude, kwalabene manya da kanana, tanagani tasan giyace ga kwalayen sigari nan duk ya shiryasu a ciki sekuma kwalayen madara da Apple a ciki amma kwalaban giya sunfi yawa, fito dasu ta dingayi daya bayan daya ta taresu agabanta ta girgigiza kai, ta tattaresu guri daya tadinga bude kwalbar tana tsiyaye giyar a cikin dustbin, ta zazzage tabar nan a cikin shara, tacewa megadi yafita da ita. Ta koma dakin ta juya baya tanata mopping taji an rikota ta baya..



Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣7️⃣80

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]






_MY FIRST NOVEL_



Da sauri ta waiwayo don ganin waye ya cukumota haka, tozali tayi da Ilham ido cikin ido, a fusace Jalila tace "Malama lafiya? Meye haka sekace wata mara hankali"
"Nikike cewa mara Hankali? Uban me kikeyi a dakin nan?" wani irin kallon rainin hankali Jalila tayi mata
"Uban da kikeyi shina keyi, Dan Cikani mana" kara rikon Ilham tayi "Bazan sakekiba, munafuka ranar kinje gurinsa kin zauna a Asibiti dan shishshigi, yau kuma uban me yakawoki dakinsa? Makira Annamimiya"
"Ilham ba ina binki a sannu bane dan ina tsoronki, uban dayake kawoki dakinsa shiyake kawoni kicikani"
"Bazan cikaki ba se kin gayamin uban meye hadinki dashi da har zakizo dakinsa wai kina gyarawa, akan me wayasaki, ke nifa ban yadda dake bama wallahi" hankade ta Jalila tayi ta nunata da yatsa, kikakuma gigin tabani wallahi sena baki mamaki, inkin isa in yazo shikije ki titsiye shimana kokuma kema ki dinga shige masa in zaki samu gindin zama, wallahi Ilham ki kiyayi shiga sabgata inbahakaba sekin gane bakida wayo, bar yimin kallon haka, sakarya kawai"
A Fusace Ilham tayi kan Jalila ta riko hannun da Jalila ta fadi akai sanda Jalal ya tureta fadi, "Wallahi sekin gayamin meye hadinki da Jalal, sannan meyasa kike shishshigi a lamuransa, bazaki bar gurin nan ba sekin fadamin uban da kukeyi" "Dalla cikani, ubankine Jalal din ko dan kekadai aka halliceshi, sha3 mutumin dabata taki yake ba, inma wani abun mukeyi kema kizo kuyi"
Jalila ta fizge hannunta aikuwa Ilham ta dauka mopper tayo kan Jalila, tana cewa "Wallahi sekin gayamin yau senaga uban da yatsaya miki koni koke, matsiyaci ya kawai, wallahi sena miki dukan dabazaki sake shigowa gidan nan ba.
Jalila tai sauri ta dauki Ruwan mopping ta shekawa Ilham shi gaba daya a jikinta, sannan ta bita tana kwala mata bokitin. Seda yafara fashewa a jikin Ilham, inda Allah ya temaketa bokitin robane, Jawwad ne yakawo kai yaga ana wrestling, Ilham ta durkusa tanata ihu Jalila tana bugamata bokiti tana huci, da sauri yaje ya riketa yana fadin "Subhanallah lafiya kuwa? Jalila meye haka?" A fusace Ilham tace
"Dole ka tsaya kana tambaya mana kaima munafuki, wallahi tun wuri kajamata kunne inbata kiyayeni ba sena illata ta wallahi, nikika jika da ruwan datti kika dakeni ko? Wallahi sena sa kinyi danasanin zuwanki duniya"
"Karki fasa, nikuma bazan gaji da lakada miki dukaba tunda bakya gane yaren mutane sena jakuna in an dakeki" Jawwad yace "Jalila yimin shiru, Ilham dan Allah kiyi hakuri komene nasan Jalila ce bata da Gaskiya, rigimanmiya ce tun asalinta dan Allah kiyi hakuri"
"wallahi ni inada gaskiya, akanme zatazo tana zagi....... Jawwad yace" yimin shiru ko in zane miki jikinki yanzun nan, bata hakuri sannan ki wuce kitafi gida sarkin fada kawai" Jalila tai murmushi tace "Ilham dan Allah kiyi hakuri, sharrin shedanne, Insha Allah inkika dena shiga harkata bazan kuma tabaki ba, amma kika cigaba da rainamin hankali zaki gane bakida wayo" Jalila ta juya tai ficewarta, Ilham tacigaba da zazzaga bala'i Jawwad yana ta bata hakuri. Seda Ilham tagama zazzagewa Jawwad rashin mutunci sannan ta bar dakin, Jalila tagama gyara dakin fes, sedai ruwan mopping data zubawa Ilham duk ya kwantaa a gurin, Jawwad yasa abu yai mopping din gurin, har kusan goma na dare sannan Jalal ya dawo, koda ya dawo gidansu ya wuce, yaje ya siyo kayan shaye2, yana shiga dakinsa ya ganshi fes kaman ba dakin ba koba a fada ba yasan Jawwad ne ya gyara, ya danyi Murmushi ya karasa inda fridge dinsa yake amma me yaga an kwashe komai na ciki se madara, iya saninsa Jawwad baya taba masa kayan shaye2 tunda suka taba fada akan haka, a fusace ya mike ya fita harabar gidan yana kwalawa Me gadi kira, a sukwane me gadin yazo dan Jalal baya shiga harkarsa indai yaji yamasa wannan kiram to akwai matsala Jalal yace "Bayan Jawwad waya shigarmin daki? Seda gabansa ya fadi take ya rikice yace yace "Ammm Ilham ce yallabai" a fusace Jalal ya juya ya shiga cikin gida, dakin Ilham ya nufa yana zuwa ya tarar ta fito daga wanka tana sanye da rigar wanka, tana duba goshinta inda Jalila ta daketa da bucket cike da tsana yace "Ke ubanwa yabaki izinin zuwarmin daki?"
"Nikuma?" "tambaya ta ma kike zan tattakaki, ina kayana da kika kwashe a fridge?, nakine koke kika ajiyemin, ina kayana"? Yafada cikin shouting
"Ni ban taba maka kaya ba, kaje dai ka duba" fizgota yayi ya dauke ta da mari, "nizaki Rainawa hankali kinsan nawane kudin kayan nan kuwa, ki gayamin ina kayana ko in shakeki, inkuma kinfara shane kema se inji" dafe kunci tayi tana kuka "Ban saniba, niban daukarma komai ba, meyasa kai Azzalumi ne wallahi se Allah yasaka....... Tas! Yakuma wanka mata mari wallahi sekin fitomin da kayana, gobe in ance kikuma shigarmin daki bazaki ba yai kanta, da sauri ta haye gado tana ihu sosai "Nashiga uku, atemakeni wallahi ya haukace ze kasheni, bashida hankali " kalmar hauka data kirashi yakara bata masa rai, kan gadon yabita ya shaketa dama kuma a buge yake,
Da sauri Mummy ta nufo dakin a gigice, tana zuwa ta tarar ya shake Ilham idonsa yayi Jawur, Daddy ma da sauri ya fito ya nufo dakin, a gigice Mummy tace
" Jalal meye haka inka kasheta fa?"
" Na kashe banza, ubanwa ya kaiki dakina kika tabamin kaya"
Da kyar daddy ya kwace Ilham a hannun Jalal, Daddy ya kalli Ilham yace "Ilham meya kaiki dakinsa mekika taba masa?"
"ni wallahi bani bace ba, Jawwad ne ya shiga, kuma nida naje Jalila na tarar tana gyra dakin, ni ban taba masa komai ba" takarasa fada tana kuka
"Jalila tabbas itace" ya fada a ransa juyawa yayi ya fice daga dakin da sauri. Daddy yaita bawa Ilham hakuri, suka fita suka bata guri, Ilham fashewa tayi da kuka "lallai Jalila bata da mutunci, bayan dukan datayi min shine taje ta kitsamin sharri, wannan wce irin Jarabace" haka Ilham taita kuka. Shikuwa Jalal yana komawa dakinsa yarasa mezeyi ya huce, Jalila ba karamin Asara tai masa ba, yasan itace ba wani ba, giyace me matukar tsada da wuyar samu, ga kwalayen sigari duk ta kwashe masa haka ya kwanta yana tunanin mezeyiwa Jalila ya huce ne.
Nana tanata waya da Mahmud, abun nasu ya rikide yakoma Soyayya, Jalila ta kule a cikin bargo tana chatting, Zahra take sanarmata ankuma kama baban Samira, ya zaneta ashe tanada karamin ciki, sannan yaje Club yakama Saurayin Samira ya sossoka masa Kwalba, A sukwane Jalila ta tashi zaune, takira Zahra, Zahra na dagawa tace "Jalila kinga sakona ko?"
"Eh nagani Zahra dan Allah dagaske kike koda wasa?"
"Haba Jalila yazan miki wasa a wannan maganar wallahi gaskene, har wasu sunje dubata tana Asibiti"
"Thank you for the Update dear, nagode sosai Zahra Allah ya biyaki" ta kashe wayarta, ta shiga tunanin mezatyi wanda zata sa A rike Alhaji Kabiru wannan karon kar asakeshi a gurfanar dashi a kotu.
Take Suleiman ya fado mata a rai, wani dan guntun murmushi tayi, tamike ta shige toilet ta rufe kofa sannaan ta kira suleiman, sun dade suna waya, tagaya masa komai, tace dan Allah inda wani taimako daze mata yayi, a karbi case din abawa wanda zasu jajirce a gurfanar dashi a kotu, yamata Alkawarin zeyi iyayinsa, sannam intanada wani sheda ta tura masa, ta turawa suleiman dukkan waya da chat dasukayi da Alhaji Kabiru, ta tiramsa har recording din maganar su Samira da barazanar da suka dingayiwa Zahra, Suleiman yace insha Allah zeyi kokari yaga me ze iyayi, yace zesa amasa bincike, kafin yazo kano tai masa godiya sukayi sallama sannaam ta fito daga toilet din, tana fitowa Nana ta dan tsuramata ido sannan tace "Jalila kekam me kike a bayi haka, kinkusa awa daya fa, murmushi Jalila tayi tace
" Ke Awa nawa kikayi kina waya, kai Nana Allah ya shiryeki da sa'ido wallahi" sukayi murmushi gaaba daya banda Naja, data ketawani hura hanci tana shan kanshi, Jalila ta kalli Inda Naja take sannan tace "Bari inzo inkira Yaya Jawwad inji in yayi bacci, in beba ya tayani hira, Tunda ke Nana naga hankalinki nakan wannan Mahmud din" Nana tai murmushi tace "Jalila bazaki gane ba Mahmud ya hadu, he is so romantic"
"Aifa gashi nan gaba daya kin Afka soyayya ba kyaji ba kya gani" suka kuma dariya, Naja ta tsurwa Jalila ido, jira take taga Jalila ta kira Jawwad tai mata rashin mutunci amma taga Jalila tayi kwanciyar ta. Can cikin bacci Jalila ta farka, take jin surutu kasa2, tai shiri setaji Naja ce take waya da Saurayi kusan karfe ukun dare, ga wayar tasu batsace kawai sukeyi, Jikin Jalila yai sanyi, "Yanzu wannan ake kokarin a hada salihin bawa kaman Jawwad da ita, bazan taba bari hakan ta faruba, ai gara Hanan da wannan" Naja tacigaba da wayarta dan tunanin ta gaba daya bacci sukeyi, haka Jalila takasa komawa Bacci har Asuba.


An samu Jeje ya farko da kyar, ya zubarda jini sosai, dan haka ana bukatar akara masa wani, duk abokan shaye shayensa suka zame sukece bazasu iya ba, suma jinin be wadace su ba, balle su bashi, Jeje yace dan Allah agayawa Jalal yasan ko kowa ya hanashi Jalal ze bashi Jini, sukace dan dai sako zasu gayawa Jalal.

Kusan kwana hudu Jalal be kara ganin Jalila ba, Jalal yarasa yadda zeyi ya ga Jalila, ko gidansu yaje ya dena ganinta, sannan kuma ta dena zuwa gidansu, gaba daya ransa a bace yake, saboda wannan mummunar Asara datayi masa, shiba kudinne damuwarsa ba se wahalar samu da irin wannan giyar take dashi, kuma ita kadaice in yasha yake jin yaji yadda yakeso. Yana zaune yaji karar mota, ya leka ta window palourn sa yaga Daddy ne yafita shida Mummy, jinjina kai yayi, Wayarsa ya dauka ya kira Jawwad, tana fara ringing Jawwad ya dauka, Jalal yace "Kana inane?"
"Maama ta dan aike nine, ya akayi?"
"Kagayawa kanwarka Mummy na nemanta"
Jawwad yace "to bari in kirata zatazo" ya kashe wayar, Jawwad ya kira Jalila a waya yagaya mata, bata kawo komai a ranta ba tace zataje.
Jalila ta dauki gyalen doguwar rigarta ta saka, ta fito ta tafi gidansu Jalal, sam ta manta da tasaka an fita da kayan giyar Jalal.
Koda taje gidan ba kowa, abun yabata mamaki, ta hangi Ilham a kitchen tana hada Abinci, dan haka ta dan Jira Ilham tafito, tana fitowa Jalila tace "Yawwa Ilham, ina Mummy kuwa? Ance tana nemana" A fusace Ilham ta kalleta "Ban saniba matsiyaciya jarababbiya, wallahi senasaki kuka kaman yadda kikemin, saboda kin iya makirci, kikayi min sharri gurin Jalal bayan dukan da kikamin, shima yazo ya shakeni ya kusa kasheni, wallahi in sharri ne gidan kika tarar, sekin gane bakida wayo, ina nan ina shirya miki trape kuma wallahi sekin fada" cikin mamaki Jalila tace "Ke ni ban gane wani makirci na miki ba, shi makircin ba kekika sanshi, dan Allah ina Mummy"?
"Ninake nemanki ba itaba" waigowa tayi ta kalli Inda Jalal ke tun karo ta, tsayawa tayi kaman wata gunki tana kallonsa har ya karaso inda take, A fusace yakamo hannunta yai waje da ita yana janta, Ilham na ganin haka tace "Allah yasa yamata dukan mutuwa" cikin sanďa ta biyo bayansu. Be tsaya da ita ko ina ba se part dinsa a gaban fridge, ya bude fridge din ya kalleta a fusace yace "Ina abubuwan da kika kwashemun a fridge?" kallonsa tayi ido cikin ido, ta dauke kanta tai masa shiru "Magana nake miki ina kayaana?"
"Meye kayan naka?"
"Tambayata ma kike?"
"Eh, ai bansan wani kayan bane gara ka gayamin, idan nina dauka, se ince maka nina dauka inbani bace ba zance bani bace"
"Ke meyasa a rayuwarki, kikeson rainamin hankali ne? Kekika dauka ko kaffara bazanyi ba, ina kayana ko in kakkaryaki yanzun nan" ta kalleshi cike da tsiwa da gadara tace
"Na dauka na zubar a shara, nabayar an fita dashi ansaka a bola" ta kare maganar tana kallonsa up and down, wani mugun takaici ne ya kama Jalal, shi takewa wannan gadarar haka, hannunta ya janyo, sukazo daf suna iya jin numfashin juna sannan yace "Ubanwa yasa ki daukarmin kaya, kekika ajiyemin?"
"ba uban daya sani, nina sa kaina, kaga sakarmin hannu, last week ka hankade ni kakusa karyani yanzu kuma kana kokarin karasamin hannu, cikani" lallai Jalila ta kai makura wajen iya rainin hankali, ta masa laifi kuma tana masa gadara
"Ka cikani nace kobaka jinane, kaikam Allah ya shiryeka, kota lafiyarka bakayi, se tsabar masifa da taurin kai ni cikani....
Wanka mata mari yayi, wanda yasa Jalila dena gani na wani dan lokaci,
"bansan a dadin lokutan dana dauka ba ina miki kashedi akan kifita daga harkata, ke wace irin mara zuciya ce, wace irin uwar shishshigi ce ke? Darajar Ummi da Jawwad kikeci da tuni na kakkaryaki na karya banza, ina ruwanki da mara tarbiya wanda baya ganin darajar iyayensa, ina ruwanki dani? Ke kullum burinki kiyi abunda zaki bata min rai ko?" tuni Hawaye ya wanke mata ido, dan sau daya aka taba marinta shima Hanan ce, kuma seda ta koyawa Hanan din darasi, idonta na kwararar da hawaye, cikin nutsuwa tace
" Hakane na fiye shishshigi, kuma inka karyani ka karya banza, amma da ina cin darajar Ummi da Jawwad koda wasa bazaka mareni ba, dan nasan Jawwad baze taba marin wanda yafito daga ahalinka ba, Nagode sosai da wannan marin da kaimin, bazan taba mantawa ba, Allah yabaka Hakuri, Allah ya huci zuciyarka nadena maka shishshigi Insha Allah, Kacigaba da shan giyarka Jalal da dukkan wani nau'i na shaye2 karka dena, bazan kuma takura rayuwata akanka ba, na tafiyar da lokuta masu tarin yawa akan tunani dan ganin kazama mutum kamar kowa, sannan mutane sudena kyamatarka, nashiga damuwa da gwargwamaya saboda kai, but this is what I deserve from you, dana san abunda naimaka ze bata maka rai ta kai gaka mareni da banyi ba, ina me baka hakuri, Insha Allah dana kammala abunda nake zan dena maka shishshigi, balle incigaba da bata maka rai" gaba daya jikin Jalal yayi sanyi, be gama gane inda magamganun Jalila suka dosaba
"Cikani in tafi" yana kokarin yin magana, cikim Zafin Rai tace "Kacikani Jalal tun kafin in rama marin dakayimin, kaine mutum na biyu daya mareni a rayuwata, wadda taimin na farko seda na tabbatar da na koya mata darasi, kaima wasu dalilaine zasu hanani ramawa ka cikani nace maka" tai maganar tana Hawaye, gaba daya Jalal ya rikirkice, ta fizge hannuta ta fito waje ta tafi gida, seda ta tsaya a waje ta gyra fuskarta ta maze sannan ta shiga gida.
Ilham da take labe kuwa gida ta koma tana murna tareda yiwa Jalila Allah yakara.
Shikam Jalal guri yasamu ya zauna yai shiruu yana tunani, danasanine ya lullube shi, meyasa ya mareta ya akayi har ya mareta, "Jalila ce fa ya akayi na mareta ne? Mtseww yarinyar nan ta fiye shishshigi da taurin kai" magamganun Ilham da mamanta da sukayi a Asibiti ne suka dinga dawo masa. Mikewa yai da sauri yabi bayan Jalila amma kodayaje gidansu ma tariga ta shige cikin gida, dakin Jawwad ya tafi ya zauna yai shiru duk abun duniya ya dameshi musamman inya tuna Hawayen daya gani a fuskarta. Wayarsa ce tafara ringing, lambace ba suna ya daga yasa a kunensa, anan aka sanar da Jalal Jeje yana kwance a Asibiti rai a hannun Allah yana bukatar jini amma an rasa me bashi, bill din Asibitin dana magani ma ba'a biyaba, Jalal yace Insha Allah gobe zezo Asibitin aduba jininsa in yayi daidai asawa Jeje, sannan ze biya bill din Asibiti.
Jalila bata taba zaton Jalal ze iya marinta ba, yau taki kula kowa har dare ba wanda ta kula, duk yadda Naja taso ta tsokane ta suyi rigima Jalila taki yadda.

Washegari karfe sha daya na safe Jalal ya shirya ya tafi Asibitin da Jeje yake, ya tausaya masa ganin halin dayake ciki, bakowa a gurin Jeje se shikadai gashi ba'a wani kula dashi saboda ba'a biya kudin Asibiti ba, Jalal yana zuwa yabiya kudin Asibiti, sannan yasa aka canzawa Jeje daki, Jalal yana zaune agaban gadon Jeje, yana jira likitocin suzo aje lab a duba in jininsa zewa Jeje, 'Yan sanda biyu suka shigo dakin suda wani babban mutum sekuma Jalila mamakine yakama Jalal ya tsaya yana kallonsu, Kokusa Jalila bata nuna tasan Jalal ba sukaje gaban gadon Jeje, y'ansandan suka mikawa Jalal hannu suka gaisa, amma hankalin sa yana kan Jalila, ta kalli babban mutumin ta nuna Jeje tace "Yallabai wannan ne, shine wannan" mutumin ya gyada kai yace "aidaganinsa kaga criminal, ni kaman na taba ganinsa a wani guri, amma wannan fa, dan uwansa ne kokuwa? Shima wannan da gani drunker ne" kalmar drunker da Suleiman yafadawa Jalal, Jalila taji bataji dadi ba, amma ba yadda zatayi tunda Jalal yana shaye2
Jalila tace "Yallabai yanzu zakaji komai daga bakinsa" ta taka a hankali ta tafi gaban gadon Jeje ta tsaya ta kalleshi ya kalleta tace "Yau nacika maka alkawarin dana dade inayi maka, senaga bayanka, inaga kusan sau hudu ina gayamaka wannan kalmar, bari inbaka wani sako kagayawa ubangidan ka Oga KB, kokuma ince Alhaji Kabiru, kagaya masa Ni Jalila Aliyu Imam, ni nasaka aka kamaka da shi da 'yarsa a gidan karuwai" gaba daya suka juyo suna kallon ta.




❀️❀️❀️❀️ ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 🌹 inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku 😍😍😍😍



Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
What's app only 07063065680.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹 🌹

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 2️⃣8⃣81

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]






_MY FIRST NOVEL _


Gaba daya sukayi shiru suna sauraranta, tareda kallon mamaki, tacigaba da cewa "Sannan kuma zan tabattar maka da zarginka Nice kuma nasaka aka dauke Jalal ranar birthday dinsa" ta juya ta kalli Suleiman tace "Yallabai gashi nan, ku tambayeshi"
Suleiman ya janyo kujera gaban gadon Jeje ya zauna, ya kalli Jeje yace "Ya jikin naka dan uwa" da kyar Jeje ya motsa baki yace
"Da sauki"
suleiman ya gyra zama yace "Inbazaka damu ba, zamuyi maka tambayoyine gaskiya muke bukatar ka gayamana in kayi karya, zamu daukeka a haka mutafi da kai office ka warke a can, mecece Alakarka da mutumin daya yi maka wannan raunukan?"
Jeje yace "Ubangida nane, ni yaronsa ne"
"Ubangidanka kamar yaya? Aikin me kake masa, A ina kuka hadu? Yaushe kafara masa Aiki?" Jeje ya juya ya kalli Jalal ya sunkuyar da kai kasa, a fusace Suleiman yace "magana fa nakeyi maka, kabani Amsa kuma in kayimin karya seka gane kuskuren ka" Jeje ya juya ya kalli Jalal yace
"Jalal ina fatan zakamin Afuwa jin abunda ze fito daga bakina, Asalina nidan garin Azare ne, a cikin wani kauye, mahifina ya dakkoni yakawoni Almajiranci lokacin inada kananun shekaru dabasu fi takwas ba, tunda aka kawoni bawanda yakuma zuwa inda nake, balle susan halin danake ciki, sedana shekara goma shahudu sannan naje gida, kodanaje gida mahaifiyata ta rasu, nayi bakin ciki me tarin yawa nadawo kano, Rayuwar Almajiranci Rayuwace me matukar matsi da wahala, ba kula ba Abinci sabulun wanka wanki, balle magani komai kai zakayiwa kanka Rayuwa tayimin Zafi nafara shiga kasuwa domin neman na kaina, na gudu daga makaranta a haka na shiga makarantar boko, a kasuwar nan nasamu aiki a gidan karuwai nake musu aiki, a haka nakoyi shaye2, neman mata tunda kananun shekaruna, Jagaliya da bangar siyasa ba wadda ba'adamawa dani, mun hadu da Alhaji Kabiru a gurin campaign din wani ubangidansa, ninake jagorantar group din jagaliya da 'yan

Please Login or Register in order to submit comment