Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiya, Ta danyi Ajiyar zuciya, a haka har bacci yayi awon gaba da ita.

Washegari yakama Friday, da wuri ta shirya dan ta wuce makaranta, Amma tana fitowa parlour da uwar safiyan nan kawai taga Jalal a parlour, ta tsorata sosai, shigowar dare yayi, dan haka bata san ya dawo ba, ya ďaga kai ya kalleta, ya sunkuyar da kansa ya cigaba da abunda yake, ba tareda ya kalleta ba, Jalal ya rame sosai ta bakin Hanan kaman bashida lafiya, bredi yake ci babu ko tea se lemo me sanyi da yake sha, yana ci yana bata rai, gaba daya tausayinsa ya kamata, Amma yadda yayi kaman be ganta ba yasa itama tai wuce shi a parlour tai ficewarta.

Koda taje makaranta tunanin ne yake damunsa ya hanata sukuni, dukda yau juma'a se karfe biyar ta gama lectures.
Da ta koma gida motarsa tana harabar gidan, da sauri ta shiga cikin gidan amma baya palour kamar yadda tasaba in ta dawo tana tarar da shi a parlour, ko baze kulata ba, kullum yana zaune a palour seta dawo yake barin palourn ya shiga wasu sabgogin, Amma yau baya nan, mazewa tayi taje ta watsa ruwa, ta shiga ayyukanta Amma hankalin ta yana kan rashin ganin gilmawar Jalal, wasa2 har dare yayi amma bata ganshi ba, ta sa kayan bacci ta kwanta taji zuciyarta takasa nutsuwa.
Dan haka Mikewa tayi tasa hijjabinta ta nufi dakinsa, seda ta ďan ja wasu mintuna tana nazari, sannan ta murda kofar ta shiga.

Koda ta shiga dakin warin sigari yake, Can ta hange shi akan gado daga shi se 3 quarter da vest, ya rufe ido se juyi yake akan gadon, da sauri takarasa gaban gadon tace "meyake damunka ne?"
Bece komai ba idonsa a rufe, se juya kai yake, ya dafe kansa da hannunsa kan gadon ta hau tana magana "ka gayamin ko baka da lafiya?"

Hannu tasa ta janye hannunsa daga kan nasa, ji tayi jikinsa ya dau zafi sosai

"Jalal meyake damunka ne?" yanayin yadda ya bude idonsa ya kalleta ya mayar ya rufe tagane a buge yake, juyawa tayi bayan gadonsa taga guntayen sigari da ya shanye, ga dogayen kwalaban giya da ya shanye.

Tuni idonta ya ciko da hawaye tace "giya Again, Jalal why? Meyasa haka? Kacemin zaka dena kuma kawai inga haka why Jalal?"

Da kyar yake iya bude idonsa, sunyi jawur kaman an hura garwashi, cikin maye yake kokarin yi mata magana amma yakasa.








Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣4️⃣107

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724





_MY FIRST NOVEL _

Gaba daya jikinta yayi sanyi ta tsaya tana kallonsa, juyawa tayi ta koma daki ta barshi a parlourn, se bayan ta tafai yaji gaba daya jikinsa yayi sanyi, yake tambayar kansa meyasa yayi mata shouting? Laifin me tayi masa? Gaba daya se yaji ransa ya baci. Ya tashi ya bi bayanta, amma ya tarar ta rufe kofarta sannan ta kashe futile, haka ya hakura ya koma dakinsa.

Washegari bayan tayi salla, ta shiga kitchen ta hada breakfast, kafin ya tashi har ta kammala abunda zatayi tai ficewar ta.

Naja ce ta shigo gidan ko sallama babu sekace korarriya, Yaya mairo ta kalleta tace "ke meye haka ko sallama babu"?
Dan guntun tsaki Naja tayi tace "wallahi matsiya ciyar yarinyar nan ta cuceni, da yanzu ina Abuja ina hutawa, Amma gashi ba Auren, kuma duk samarin nawa sun gudu ga talauci ya isheni"

Yaya mairo tace "kema ke kika cuci kanki, shaye2 Naja, na miki fada har bansan adadi ba, ga wannan abun kunya da kikayi, ba dan Allah ya rufa asiri ya zube ba da shikenan, kinjamin masifa"

"Amma da ya aureni aida zan dena, wannan bakar shegiyar ta zalunceni ita da Allah makira, kuma itama tayi Aure sun barni a titi"

Yaya mairo tace "Aure kuma, wata aura?"

Naja tace "Agurin daurin Auren aka bawa wannan dan shaye2 sadakarta, Jalal suke ce masa ko Jamilu oho dai"

Sa'ada da tun dazu ke kwance na danna waya ba tace uffan ba se yanzu, ta kalli Naja tace "Ke bana son shirme, da gaske Jalal ta aura"

Cikin tsiwa Naja tace "Bansani ba tunda baki yadda ba meye na son se kin tabattar aikin banza kawai, na tsani inyi magana a karyatani"

"Sorry ba karyataki nayi ba, amma waya gaya miki?"

Cikin kosawa Naja tace "Zancen duniya yana buya ne? A anguwarsu naji, har gidan seda aka kwatanta min, shi aka Aura mata, Ai Allah ya kara, Allah yasa yayi mata dukan da seya kashe ta"

Yaya mairo tace "Ameen dai Naja, Ai Allah ne yasaka miki ya hadata da dai dai ita, yayi ta cin kaniyarta"

Kallonsu kawai Sa'ada take da sun san me Jalila ke nufi a rayuwar Jalal da basuyi wannan maganar ba.

Tashi tayi tsam tabar parlourn ta koma dakinsu ta dakko waya ta kira Hannah.
Seda ta kusa katsewa sannan Hannah ta daga Sa'adah tace
"ke Hannah, wai kina inane?"
"kamar ya ina ina? Kefa na Gaya miki Jalal yasa 'yan sanda su nemoni, ina Abuja se ya huce zan dawo, daga nan na kara shirin tinkarar sa, dan koda tsiya sena cika burina"

"ke dalla banza kina can kina garanci to yayi Aure"

"ke saurara, kamarya yayi Aure? Ya Auri wa? Mutumin da ko budurwa bashida?

Sa'adah tace " sadakar mata aka bashi a bati, wannan Jalilan dai ita aka bashi sadaka"

Cikin tsawa Hannah tace "Impossible how? Ta yaya? Ke waya gaya miki? A ina kikaji?"

"Yanzu Naja tazo tana zancen, tace haf gidan da yake ta sani"

Hannah tace "please help me, kije ki tabattar min dagaskene, karki sa jinina ya hau bayan karyane"

Sa'adah tace "ke nikike so inje gidansa in yana nan fa, kinsan ba cukakken hankali ne da shi ba, tijara zemin a bainar nasi"

Hannah ta marairaice tace "please Sa'adah ki temakamin, i dan zancen nan ya tabatta sena kusa hauka wallahi, ke dole ma in zo kano ayita ta kare, dan girman Allah Sa'adah ki samomin sahihancin maganar nan"

"karki damu zan duba miki Insha Allah"

Hannah tace "Yawwa kawata ki temaka, dole in tattaro kayana in dawo, dama tazo min da zan nunawa yarinyar nan ta tari aradu da kai"

Sa'adah tace "a da baki nuna mata ta tari aradu da kai ba se yanzu, da ta baku mamaki keda Kanwarsa, kuna nan kuna wahala ta aureshi ta barku"

"haba Sa'adah kefa kikace sadakarta a ka Bashi, ta yaya kike tunanin ze so matar sadaka, kyaleni da shi kawai"

"Hannah wani tabbaci kike da na cewa shi baya sonta, ke kina tunanin za'ayiwa Jalal auren dole a yadda yake ne"

Hannah tace "ke mu bar maganar naan ji nake zuciya ta kaman ta faso kirjina saboda takaici, duk abunda kika gano kimin bayani"

Sa'adah tace "shikenan zanyi kokarin bincika miki"

Sa'adah takoma parlour tace "Naja nikam inane gidan yarinyar nan, inason inje inga kwakwaf, daga nan inci mata mutunci"

Naja tace "kyaje ta bakanta miki rai, kin san ba mutunci ta cika ba"

Sa'adah ta lallabata ta gaya mata kwatancen gidan Jalal.


Koda Jalal ya tashi ya tarar harta tafi school, se yaji babu dadi dabe ganta ba, sedai tayi girkin breakfast ta ajiye masa, yayi breakfast yayi wanka ya fice.
Jalila na daf da kammala lectures message ya shigo wayarta

"in kin gama ina jiranki a harabar department dinku"
ABDUL JALAL


Ajiye wayar tayi, suka gama lectures sannan ta fito, tana fitowa daga lectures ta hango motarsa, tana zuwa ta bude gaban motar ta shiga ba tareda ta kula shi ba, kallo daya yayi mata yasan ta gaji sosai,
Yace "Sannu" bata amsa ba sema kwanciya da tayi a jikin kujerar ta juyar da kanta daga kallonsa tana sauke numfashi. Dukda daddadan kamshin turaren Jalal da kuma turaren dake ta shi a cikin motar sa, hakan be hanata jin tashin wari sigari kadan2 ba.
Ya kunna motar yafara tafiya can ba tare da kalleshi ba Jalila tace "Jalal ka sha sigari ko?"
Jalal yace mata "Eh na sha"
Tace "Good"

"Amma kadan na sha guda biyu ne kawai fa"

Shiru tayi masa har suka je gida, suna zuwa ma bata bi ta kansa ba tai tafiyarta dakinta tai salla ta huta sannan ta fito ta nemi abunda zata ci, jallof din macaroni tayi, ta zauna tana ci a parlour Jalal ya fito, yana zama ta tashi ta koma daki.

Kasa daurewa Jalal yayi ya tashi ya bita dakin nata, ta harde akan gado tana cin Abincin ta, dan stool dinta na kwalliya ya janyo ya zauna a gabanta ya tsura mata ido.

"kaga ni dan Allah kar kasa in kware, kasani a gaba da kallo, shiyasa na baro maka parlour ni bana son kallo"

"Ai ba wani abun nake kallo ba nima, mezan kalla a jikin kwailar da na dauka a hannuna, na goya a bayana, na dinga jefawa sama ina cafewa, ga Yamin me zan kalla?"

Jalila a ranta tace "Lallai Jalal dan rainin hankali ne ya cini wasa"
Amma ta kara hade rai tace

"to tunda ni kwailace bani da abun kallo meye na zuwa kasani a gaba ka tsiramin ido?"

Ta yunkura zata mike, ya riketa ya zaunar da ita akan gadon yace
"dan kinga ina shiga damuwa in kika dena kulani shiyasa kike ta hademin rai kina wani shareni ko?"

Dagowa tayi ta kalleshi tace "Jiya kayimin shouting dan kawai nace kayi Azkar, kuma kasan bana son shouting, yau kuma ka sha sigari abunda yafi bata min rai, dan me ba zanyi fushi ba? Ko sokake in cigaba da shiga harkar ka kanamin shouting"
Ta karasa maganar tana kara hade rai da dan tura baki.

Hannayenta ya riko yace

"Jalila na sha gaya miki ba lokaci daya na fara shaye2 ba, bazan iya denawa lokaci daya ba, kuma ina kokari sosai in dena, sedai lokuta dayawa inaji kamar zanyi hauka idan ban sha ba, duk da haka ina cigaba ds kokari, ki cigaba da yimin Addu'a, sannan Indai Adhkar ne zamu dinga yi shikenan? "

Zumbura baki tayi tace " ba shikenan ba da saura"

"me yayi saura kuma?" ya tambaya

Tace "ba kabani hakuri ba fa"

Dan tsura mata ido yayi yana kallon ta, yarinyartarta ta kara fitowa sosai musamman idan tana jin rigima


"Nine zan baki hakurin?"

"Eh kawai ka bani hakuri, ai laifi kayi min"

"idan na ki baki hakurin fa? Ke bakiji kunya ba da kikace in baki hakuri?"

"Kunyar me zanji kuma? Laifi fa kayi min, ko kai agurinka ba komai bane?"

"to shikenan I am sorry, bazan kara ba"

Murmushi tayi tace "Yawwa ko kaifa, Jalal duk lokacin da ka batawa mutum rai ko bani ba Dan Allah ka bawa mutum hakuri, Nagode, yi hakuri, dan Allah, kalmomi ne masu sauki se dai suna da wahala a harshen wasu mutanen, duk mutumin da baya gane kuskuren sa ya nemi afuwa hakan alamace ta girman kai, kumma Allah baya son masu girman kai, dan haka ka ko yarone karami ya in dai ka bata masa babu laifi ka bashi hakuri, bazaka ragu da komai ba"

Yadda ta kwantar da kai take sarrafa harshenta gurin yi masa nasihar ne ya burgeshi.

Amma yace
"Waike bazaki dena kirana da Jalal kai tsaye haka ba, kefa baki da kunya"

"to Yaya Jalal"

Hararta yayi yace "niba yayanki bane ba, ni mijinki ne dan haka bana son wani Yaya da can ma inaji haka kike cewa Yaya Jawwad, amma ni saboda kin rainani wai ABDUL JALAL kai Allah ya yafe miki kwailar Ummi"

Dariya tayi tace

"waye mijin, wai kaine mijina, tabdijan, kuma wallahi niba kwaila bace, kuma Allah ya yafe maka dai, yadda ka dinga cin zalina, dan ma ina rufa maka asiri, amma ka ci zalina da yawa wallahi"

Dariya yake sosai, befi ta kirga sau nawa taga yana dariya haka ba

dariyar tayi masa kyau sosai yace
"kin kyauta zakiyi bayani da manyan baki ne, bani Abincin nima inci tun dazu kamshi ya cikamin hamci"

"wannan dan Abincin, me naci me na baka? Jeka dafa naka wannan nawane, meze sa ma kaci Abinci da kwaila?" ta fada tareda dauke plate din Abincin.

Sakkowa yayi ya zauna kusa da ita yace
"dan sanmin mana, ko kadan ne"

Jalila tace "to tsaya yi spoon daya"

Tana miko masa plate din ya mike yace

"Se anjima kin gama cin naki, sannan a kawomin wayata da'aka kwace, dan nasan 'yan mata na sun kirani ba adadi"

"har zawrawanka ma sun kiraka ai, ni kayiwa wayo zan rama ne"

Murmushi yayi ya nufi haanyar fita yace "kawomin wayar daki, zanyi wankane"


A dan shirin da suke kwanan nan ta kara fuskantar he's so simple, yana da wasa da dariya ga shi ya iya tsokana sosai, abunda bata taba zata ba, saboda kusan koda yaushe ransa a hade, babu abokin hira, babu me sauraron matsalolinsa.

Bayan fitarsa taje kitchen ta ajiye kwanon da taci Abinci ta dawo daki ta dakko wayar Jalal domin kai masa wayar a silent take dan haka akwai missed calls dayawa a wayar, ta karo volume din wayar ta shiga dakin nasa da sallama, ya riga ya shiga wanka, tana ajiye wayar, wayar ta fara ringing, Tace Jalal "ana kiranka a waya"

"ki daga mana"

"niba zan daga ba, gata nan dai anmaka miss calls da yawa"

Jalal yace "nina ce ki daga ai, yanzun zan fito, kinsa ina surutu a toilet sekace ke"

Daga wayar tayi tasa a kunnenta tare da fadin "Salamu Alaikum"

Muryar mummy ce ke fadin

"ke ina dana yake? Mara mutunci tun jiya nake kiran sa amma kika hanashi dauka, ki bani zanyi magana da shi mara mutunci"

Jiki a sanyaye Jalila tace "Mummy ina wuni, wayar tasa ce a silent shiya.....

Ke dalla ki rufemin baki, mara mutunci wadda bata san darajar kanta ba, kingama zagun sa da cin mutuncinsa agabana kuma kinkoma kin lallaba kin aureshi kina kokarin rabani da shi, saboda wulakanci tunda ya bar gidan nan koda wasa bezo inda nake ba, to baki isa ba wallahi, kuma ki fara kirga kwanakin barinki gidan nan daf nake da datse auren nan bazan taba kaunarki ba, ki bashi waya zanyi magana da shi"

Tuni hawaye ya jika fuskar Jalila tace "yi hakuri Mummy, wallahi ba laifina bane, nima...

Dayake Mummy a hands free tasa wayar Ilham tana jin maganar dasukeyi, Ilham ta karbe wayar tace" dalla malama tace miki da danta take son tayi magana, ke wace irin dabba ce ne haka? Mara zuciya wadda bata ganewa, uwar mutum tace bata sonki dayake ke jinin maita ce kin like masa, dukiyarsa kike yiwa shiyasa kika hada baki da marikin ki kika aure shi, nasan dai ba wani sonki yake ba dan ba abunda zeyi dake, giyar da yake sha tafiye masa komai mahinmmanci ciki kuwa hadda ke, dan haka ba saurararki zeyi ba"

Jalila ta kawo iya wuya, a ranta tace, idan bataka wa wannan Ilham din briki ba bazata sauraramin ba, so take taji halin da nake ciki a zaman gidan nan dan haka tace

"kinga dan Allah saurara Ilham, ke meye naki a ciki da Mummy muke magana ba dake ba, tunda kin matsu bari in gaya miki yana bandaki yana wanka"

Da sauri Ilham ta kalli Mummy ta Zare ido tace "wanka kuma?"
Jalila tace "Eh mana wanka yake yi"

Karaf a kunnen Mummy, hakan yayi dai2 da fitowar Jalal daga toilet yana goge kansa, karasowa inda Jalila take yayi yasa hannu ya karbi wayar daga hannunta, juyawa tayi zata bar dakin ya riketa, yasa wayar a kunnensa yaji muryar Mummy tana masifa
"kinfadi sako, kuma naji, nasan dani kike, ni kike gayawa yana wanka, aiba se kin gayamin ba, mara mutunci"

"ai ba dake take ba, Ilham ce ta tambaya aka bata amsa"

Mummy najin muryar Jalal tace "Yanzu Jalal kayiwa kanka adalci, dama kana nan kana ji amma kaki amsa min waya, tun jiya nake kiranka a waya amma kaki dagawa"

"Duk lokacin da zaki kirani abunda zaki batamin rai kikeyi, zuwana gida bashi da amfani, Daddy baya Gari, daddy ne kawai yakeson abunda nake so, idan nazo ma Zaki yi maganar da ze batamin raine dan haka ba wani amfani kona zo inda kike tunda..
Rufe bakinsa Jalila tayi tana girgiza masa kai idonta duk hawaye
A hankali tace

"Mummy ce fa, karka fadi abunda ze bata mata rai, Allah zeyi fushi da kai"
Tausayin Jalila ne ma yakama shi, yasan tunda yaga tana kuka yasan Mummy taci mata mutunci ne, ajiye wayar yayi yasa hannu yana share mata hawayen fuskarta.

Jalila Tana tunanin zama da mutumin da mahaifiyarsa ke mata wannan mumunnar tsanar haka, ta tuna yadda mutunci da girmamawane tsakaninta da Mummy Jalal amma gaba daya ta canza mata, ta maida ita makiyyarta.

"kidena kuka mana, ke har yanzu sekace wata jaririya, dukkan tsanani yana tareda sauki, so stop crying" ya karasa maganar yana yatsina fuska kaman zeyi kuka.
Jinjina masa kai kawai tayi, ya cikata ta juya ta bar Dakin.

Jalila a kwana uku tayi saukar qur'ani a cikin zuma da zam2, da safe kafin Jalal yaci komai take fara bashi zumar nan, sam Jalal baya son zumar nan, dan daya sha yakejin kamar zeyi amai, wani lokacin se sunyi fada sosai yake sha. Ga zam2 da take bashi me dauke da saukar qur'ani. Ta dage sosai akan ganin yana Addu'oi. Zaman nasu ba laifi sedai Jalal bashi da niyyar yi mata komai na bangaren Aure shiyasa ta kara sakin jiki da shi sosai.

Jalila ta kai masa zumar da ta saba bashi, ta tarar yana waya da Jalal

Jawwad yace

"Jalal dan Allah ka siyo mana taura da magarya ka kai tasha a kawo mana, Hanan ce ke so, ni kuma ban san inda zan samu ba anan, kuma bazan iya gayawa Maama a siyo mata ba inajin nauyin hakan"

Jalal yace "Tab to ai nima ban san inda ake saida wannan abun ba tunda ba sha nake ba amma zanyi maganar da Jalila se a siyo a aiko muku" sukayi sallama akan haka.

Jalila tace "ga zumar ka ka sha, zanje in kwanta"
Ya yamutse fuska yace " Nifa bana son abun nan ciwon ciki take sani"

"yi hakuri ka sha mana, spoon daya kawai" sekace karamin yaro seda taita lallabashi sannan ya karba yana ya mutsa fuska

Jalal ya kalleta yace "A ina ake saida magarya da taura?"

Jalila tace "a kasuwa mana"

Jalal yace "wai Hanan ce take so, za'a siya a aika musu"

Jalila tace "gaskiya Hanan tana bawa yayana wahala, yau tace wannan gobe tace wancan, zan gamu da itane"

Jalal ya harareta yace "dan me bazeyi wahala ba, da haka takeyi? Tunda shi yayi dole ya kula dashi"
Ya kuma maze kamar bashi ya fada ba, itakuwa Jalila ji tayi kamar kasa ta bude ta shige dan kunyar abunda ya fada, ta mike tsama tace

"Amma seda safe"
Murmushi yayi yace "tun yanzu, yau baza'ayi Azkar din bane?"

Tace "A'a ni nayi a dakina, kayi kai ka dai"

Tana fita ya kwashe da dariya, yace "Jalila kenan, kema ina jiran lokaci ne, Allah ka cikamin burina akan Jalila yasa ta soni kaman yadda nake sonta"

Yauma weekends ne dyk suna gida ta kammala aikace2, tana kallon bollywood, knocking din kofar parlor akayi dan haka ta tashi taje ta bude, ga mamakinta Naja ce da sa'adah amma ta boye mamakinta ta saki fuska "Ahh manyan baki sannunku da zuwa" ta basu hanya suka wuce suna mata wani irin kallon banza.

Sukaje suka zauna a parlor, Sa'adah ta kalli Jalila tace "Ashe Aure kikayi?"
Jalila tace
"Aiba ashe bane, tunda gaki a gidana"
Naja tayi tsaki tace "aka dai bada sadakarki tunda bashi yace yana so ba"

"to ke abada sadakar taki mana, ai ba kowace mace ake bada sadakarta a karba ba se ishashshiyar mace"

Sa'adah tace "Ke karki cimina mutunci dan munzo inda kike, matsiyaciya kawai"

Jalila tace "aibani na gayyato ku ba"

A fusace Naja tace "ke karki ci zarafinmu dan munzo gidanki"

"aibana cin mutuncin kowa, musamman wanda yazo inda nake sedai da abunda kazomin dashi nake karbarka"

Jalal tun farkon zuwansu yana jin duk abunda sukeyi, yasan Sa'adah ba zuwan Allah ne ya kawo su ba, shikam yana kokari ya toshe duk wata kafa da zata kawo masa tashin hankali a gidan sa.

Dan haka ne ya fito daga daki ba tareda yace musu uffan ba ya wuce ya bude kofar parlor, 'yan sanda ne suka shigo, gaba daya suka razana dan basu san Jalal yana gidan ba.

Jalal yanunawa' yan sanda Sa'adah yace "Arrest her" mikewa sukayi gaba daya Jalila tace

"Jalal meyasa? Me sukayi maka?"

Jalal be kulata ba yace "Arrest her har seta fito da inda Kawarta take"

Sa'adah tace "Amma ni meye nawa a ciki, wallahi officer banyi komai ba"

A tsawace Jalal yace "Arrest her, seta fito da Hannah" aikuwa haka ayi suka kama su Naja suka fita dasu.

Jalila tace "Jalal meyasa? Me sukayi maka haka zaka sa akamasu?"

"calm down, count yourself out of this, babu ruwanki"

"Amma Jalal ace daga sunzo inda nake kasa an kamasu why?"

Janyota jikinsa yayi ya kwantar da murya "Jalila duk abunda nakeyi, duk shaye2 na bana yadda in cuci wani, don't mind me"

Jalila ta mariraice Tace "Amma"

"Shhh bana son musu"





Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ

What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 🌹

*ABDUL JALAL*

_Story, writing and edited _

By
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)

*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*🌞

(π•Žπ”Ό 𝔸𝕀ℕ'𝕋 ℙ𝔼ℝ𝔽𝔼ℂ𝕋 π”Ήπ•Œπ•‹ π•Žπ”Ό'ℝ𝔼 π”Έπ•ƒπ•Žπ”Έπ•π•Š, 𝕋ℝ𝕐𝕀ℕ𝔾 π•†π•Œβ„ π”Ήπ”Όπ•Šπ•‹ 𝕋𝕆 𝕄𝕆𝕋𝕀𝕍𝔸𝕋𝔼 𝔸ℕ𝔻 𝔼ℕ𝕋𝔼ℝ𝕋𝔸𝕀ℕ π•†π•Œβ„ β„π”Όπ”Έπ”»π”Όβ„π•ŠπŸ’ͺ)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A*✍️

PART 2
_PAGE 5️⃣5️⃣108

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724





_MY FIRST NOVEL _




Jalila kaman zatayi kuka tace

"please Jalal, kome sukayi maka kayi hakuri kasa a kyalesu, karka karamin bakin jini a gurin mutane.

Jalal yayi kasa da muryarsa sosai ya kai bakinsa kunenta yace

"ko kowa ya ki ki, ni ina tareda ke kuma ina sonki, duk me kinki Bashi da gaskiya, duk wanda yake adawa dake wanda baya son cigaba nane, kinyi yaki da mutane da dama saboda ni, ina sonki Jalila,"

Gaba daya jikinta yayi sanyi taji tsigar jikinta na tashi, a hankali tace" Amma Jalal.....

"karki kuma yimin magana akan su, akwai dalilin da yasani yin hakan, karki damu kinji my wife"




Yaya mairo ta kira wayar su Naja babu adadi amma sunki dagawa, sun saba da gantalinsu bata damuwa amma haka nan taji yau takasa nutsuwa, har maghariba bata gansu, se wajen Isha'i Naja ta dawo a wahalce, ko Abinci bata ci ba ga yunwa da kishirwa.

Yaya mairo tace

"ke lafiya kuwa? Ina sa'adah take?"

Naja tace

"ina fa lafiya, sa'adah ta jamu gidan wannan Yarinyar mijinta yasa aka kamamu, wai ko seta fadi inda wata take, nima da kyar yayi waya aka sakeni"

Yaya mairo

Please Login or Register in order to submit comment