Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kije gida kisameni ina son ganinki" seda Nana ta yamutsa fuska, sekuma tayi shiru takoma daki tana kunkuni tana mita, seda tafara gyara gurin sannan ta shiga wanka, dan Jalila tace wallahi kartin banza bazasu bata daki ta gyara ba. Koda Nana ta wuce daki Yaya Mairo tace "kingani ko zainab yaranki na neman sufi karfinki ace har kina fada tana mayarwa saboda waccan yar karuwar, kinsansu arna ba ruwansu yayansune suke juyasu shiyasa take so ta mayar miki dasu irinta ki tashi tsayefa wallahi aikine babba agabanki"
Koda su Yaya mairo suka tashi tafiya seda aka bude store aka jido musu kayan abinci, banda wanda Abba yakesawa a diba a basu, banda kudi da take bawa yaya mairo, se anbi kayan abincinsa na gida bada saninsa ba anbasu banda sitira da sauran kayan more rayuwa, dayake Yaya mairo akwai mugun sonn abun duniya, duk an kwashi kaya an kai boot Manu direba ze maidasu gida. Nana ta fito daga wanka zata shafa turare, amma ta lura babu wasu abubuwan akan mirror dinnasu, tsaki tayi "Allah ya kyauta wannan masifar, Jalila kallifa hada kayan mu suka sata, wallahi senaje se sun bamu" da sauri Jalila ta dakatar da ita "bari Nana ai yan uwankune inkikayi haka kaman kin tozartasune, ai arzikine sekinada abun sata za a sata, bakomai semu sayi wasu" haka Jalila ta lallabata ta hakura badan tasoba. Jin alamun fitarsu daga palourn yasa Jalila ta fito palour, hakan yai dai2 da dawowar
sa ada zata dauki wasu kaya data bari a palour wanda na Nana ne da Jalila ta dauka bada izininsuba, hada kayan man shafe2 da turaruka da Nana take mita, Jalila ta kalleta tai murmushi "Allah sarki bariki batayi rana ba, ace duk iskancin da ake a bariki ba a tara abunda za a rike tsofaffi ba se an hada da maula a dangi, bayan haka kuma se an hada dana sata to Allah ya kyauta" a fusace ta kalli Jalila ta nunata da yatsa "Karki kara dangantani da bariki" "Ke sauke yatsanki karki kuma nunani karki rainamin hankali mana nasan komai kallonku kawai nake daga ke har mahaifiyarku, kuma wallahi kigayamata ta kiyayeni inasane da abunda takemin da cin mutuncin uwata datakeyi, idan na tashi yimata rashin mutunci se tagane bata da wayo, har yanzu ban taba gwada muku wace Jalila ba, ta kiyayi haduwata da ita" Jalila tai gaba tabar sa ada da bude bakin mamaki. Bayan tafiyar su Naja da daddare Nana se mita take "nikome yaya mairo zata gayamin wani wai senaje gidanta, Allah yasa wani abun Arzikin nanba rainamin hankali zatayiba, nibana son zuwa gidanta saboda wannan Jarabar tata"
"To ai hakuri zakiyi, maybe abunda take son gayamikin yanada mahimmanci ne"
"Anya Jalila bana tunanin hakan amma bansaniba"
"Yawwa Nana dan Allah in tambayeki mana?"
"to Allah yasa nasani" "dama Jalal suna da wani yarene naji sunayi shida Yaya Jawwad" murmushi Nana tayi tace "Eh sunadashi, ta bangaren daddynsa, kakanin Jalal kanuri ne" Jalila ta gyada kai tace "Amma ya akayi Yaya Jawwad ya iya"
"Lallai Jalila har yanzu kina daukar amintarsu da wasa, tare suke kwana su tashifa, yanzune suka dena kwana guri daya, saboda Yaya Jalal yana fita yawonsa, da har maiduguri suke zuwa suyi kwanaki" jinjina kai Jalila tayi tace "lallai kam dole ya iya yaren" daga nan suka bar wannan zancen, Jalila ta kwanta bacci Nana kuma tafara waya da saurayinta.
Yau lecturer su Jalila ya kudiri aniyar yimusu test, unexpected saboda ya hukunta Jalila sir Hafiz kenan, matashin mutum me matukar izza da jin kansa, bashi da mutnci kokadan, kayadda dalibai a course dinsa shiyafi komai sauki a gurinsa, ga kwauron maki shiyafara korar Jalila daga class, sau biyu yana korarta daga class, na farko yana lectures tana tunani na biyu kuma kullum ya shigo class yamata tambaya bata sani ba, gashi ya lura seta gadama take attending class ya fuskanci dakikiya ce amma tana da izza da jin kanta dan haka, bayan anfito daga lectures karfe biyu, unexpected ya kira captain dinsu yace, ze musu test bayan sallar azahar, students din sun shiga damuwa saboda basu shirya ba, kowa yakama littafin sa, zahra ma ba abarta abayaba ta dage tanata dudduba littafinta, yayinda hajiya Jalila bayan ta idar da salla, ta janyo abincinta tanaci tana chatting da yaya Jawwad yana dariya , zahra ta kalleta "Jalila ke bazakiyi karatun ba? Test fa zeyi kuma ance yanada kwauran maki" "don't mind me, yi karatunki kawai, ni yunwa ce ta dameni" "to amma ai gara...." "shhh ya shiru kicigaba da karatunki kar haddarki ta zube" zahra ba karamin mamaki Jalila take bataba, ga dukkan alamu dai ba wani ja take ba saboda ba ataba tambaya ta bada amsaba amma za ayi test ko a jikinta, se tsabar iya tsiwa fal cikinta,
Karfe biyu da rabi suka shiga test din nan, wadda duration din test din 30minutes ne kawai, ga tsaro a hall din dan duk ya rarrabasu, bame iya ko kyakykyawan motsi, sannan Jalila ita kadai aka ajiye agaba bakowa a kusa da ita bayanta ko gefenta, gashi ya dakko wasu malaman department din su tayashi invigilation, Jalila ta lura yasamata ido sosai, ya dinga safa da marwa yana kallonta, kowa ya dukufa amma ita tana zaune tana kalle kallenta karewa ma ta tafi tunanin abunda yake gabanta na rayuwar Jalal, sir hafiz yazo kanta ya duba paper dinta ammma empty, ya kalleta yai kasa da muryarsa ya dan sunkuyo da fuskarsa yace "dakikiya kawai ba abunda kika rubuta, dama ba kyaja se tsabar iya shege ko? Rashin mutunci kawai shine a kwakwalwarki, bakomai se shirme, sokuwa kawai barikiji in gayamiki wannan shine last chance dinki idankika fadi test din nan kin fadi exams dina" wani irin kasaitaccen murmushi Jalila tayi masa alamar sam bataji zafin maganganunsa ba ta dauke kanta, seda yayi gaba ta bude paper dinta ta amsa tambayoyin, nanma itace karshen bayarwa, yauma batajira manu ba ta tafi gida.
Tana tsaye tana jiran mota, amma bata samuba dan haka ta yanke shawarar fara trecking, tana cikin tafiya taga wata katuwar mota range rover baka wuluk se sheki take, ga wasu mota biyu gaba da bayan motar, range rover tazo ta tsaya agabanta, kokari take ta wuce motar, amma se kokarin rufemata hanya me motar yake, "wai wani tsabar wulakanci ne haka? Bana son wulakanci fa. Wasu yan sanda ne biyu, suka fito daga motar " Yan mata kinsan waye a cikin motar nan kuwa, ki iya bakinki fa, kinsan matsayinsa kuwa? yanzu dai yace yana son magana dake kishiga motar semu ajiyeki" cewar daya daga cikin yansandan, wani mugun kallon banza Jalila tayiwa yan sandan, "ai mutum ne a motar ba aljan bako, to duk matsayinsa ace masa bazanzoba, malam bani hanya zan wuce" kuma shan gabanta sukayi "Ke waime kike takama dashi haka kike mana wulakanci kinsan suwaye mu, kinsan dawa muke tare?" "matsalarkuce koku suwaye kodawa kuke tare ba damuwata bace, kuban hanya kawai in wuce tunkafin in taramana jama'a" motar aka bude, wani hamshakin mutum ne yafito daganinsa yaci ya koshi, sanye yake da kakin yan sanda, nan suka dinga sara masa, babban mutum ne ba yaro bane, dan ze haifi Jalila, gabanta yazo ya tsaya "Am sorry mun tsareki a hanya, kizo mu saukeki a gida kinga da rana sosai" Jalila da rashin kunya taso tayi masa amma ganin babban mutum yasa tafasa "A a bakomai nagode, inada kudin mota, amma kace subani hanya in tafi" "zasu baki hanyane, amma kitemakeni da lambarki inaso zamuyi magana" dan zare ido Jalila tayi "laifin menayi maka?"
'laifine babba kam tsakaninki da hukuma , amma tsakaninki da hukumar zuciyata"a ranta tace "ji tsohon kawai, tab wallahi wrong number zanbashi"
"yakikayi shiru, kitemakamin mana"
"kawo abu inrubuta maka" ya mikomata galleliyar wayarsa, dazata samasa wrong number kawai wata zuciyar tahanata "ze iya zama garkuwa gareki daga sharrin su Jeje" ajiyar zuciya tayi tasaka masa lambarta
"Nagode sosai beauty, muryarki kawai ta isa sani bacci cikin nishadi, bankiba muyita tsayuwa anan kinamin magana, gayamin sunanki"
"Kaga ni nagaji, tafiya zanyi rana ta dameni" "hmm se anjamin aji kenan, to shikenan tunda bazaki bari inkaiki gidaba i will call you Insha Allah" bata kuma cewa komai ba ta wuce.
Tana zuwa gida tai wanka tai salla taci Abinci, Mummy takira Maama awaya tace dan Allah ta turamata Jalila ko Nana,su karbi sakon Ilham tana bacci, Dayake Nana bata dawo ba seta tura Jalila, wani tea flask ne me kyau a kwali Mummy tabawa Jalila tace ta kaiwa Maama, wata coustomer zata siya, ta karba ta fito, Jalila na fitowa harabar gidan motarsu Jawwad ta shigo sun dakko Daddy daga airport, tsayawa Jalila tayi daddy ya fito daga motar dauke da brief case dinsa, kana kallonsa kaga mahaifin Jalal, amma yafi Jalal kyau, sedai wannan dogon hancin Jalal ya dakkoshi, shaye2 ne yabata Jalal amma yana da kyau irinnasa, har kasa Jalila ta zube tana gaisheshi, da fara'a ya amsamata
"Takwarar Jalal, ashe kina kanon har yanzu ya kike ya karatu" cikin tsantsan ladabi Jalila tace "Karatu Alhamdilillah daddy" "Masha Allah, Allah ya temaka yayiwa rayuwarku albarka" "Ameen daddy" Jawwad ya dakko trolley da traveling bag na daddy sukayi gaba yayinda Jalal ya tsaya rufe mota, ta taka ta karasa gurin Jalal yana juyowa yaci karo da ita hade fuska yayi kaaman yaga kashi, dan da yaganta yake tuno cin mutuncin datayi masa, seyaji kaman yaimata shakar da seta kusa zuwa lahira
"Kalleka a haka sewani zumudi kake wai kai kafi son mahaifinka, sekace gaske, abunda inka ga dama shima daga masa murya kake, kokagaya masa maganar daka gadama, kana nuna kana sonsa amma baka hakan a aikace, ka girmamashi, tausasa lafazi a gareshi, in gari ya waye kaje ka gaisheshi, in yana maka fada ka nutsu ka danne zuciyarka, kayi hakuri dashi a duk lokacin daya bukaci taimakonka ko alfarmarka zama taredashi da gudun bacin ransa wanda hakan zesa yaji dadi yayi alfahari dayana da ฤa me kaunarsa, duk fa bazaka iya wannan ba, ta yaya zaka nunawa duniya cewa kana son mahaifinka, hmmm bazaka iyaba banda zafin zuciya da raina iyaye baka iya komai ba kodayake ba abun mamaki bane no need to expect anything good from you, giya ba karya bace, a canza hali abokin Yaya.
Ta danyi murmushi tai gaba, tana addu'ar Allah yasa abunda tafada yai tasiri a zuciyar Jalal, Jalal karasa rufe motar yai ya nufi cikin gida jikinsa a sanyaye, Jalila tazame masa karfen kafa ta uzzuramasa dayawa, gashi har yanzu yakasa samun mafita akanta. Cikin gida yanufa jikinsa a sanyaye yana zuwa ya tarar dasu a palour a zazzaune, daddy ya kalli Jalal yace "Ya dai naganka a haka? Meya faru" dan girgigiza kai yayi "bakomai daddy" haka dai akayi hira sama2 aka watse domin bawa daddy damar ya huta.
Hannah ta na kwance juyi kawai takeyi, zuciyarta fal tunani da damuwa, dagaske son Jalal ne yake damunta, gashi har yanzu takasa samawa kanta wata mafita sam Babu alamar Jalal ze amince ya aureta, a da aikin datakewa Jeje na son Jalal ya amince da ita, sudinga shedanci hakan ya gagara, amma ita yanzu babban burinta ya aureta in har ya aureta tagama karuwanci har abada, to amma tayaya? Yazata samo kan Jalal ya yadda da ita ya karbeta ya aureta, abaya tasan ta taka rawa gurin kara ingiza shi akan shaye2 amma yanzu tayi nadama, son gaskiya takewa Jalal yanzu ita meye abunyi meyakamata tayi, shiru tayi daga can kuma tayi wani guntun murmushi.
Koda dare yayi, Jalal rasa abunda yake masa daฤi yayi, tunani ya dameshi, ransa yagama baci Jalila ta dameshi, to amma dagaske take baya son daddy? Shidai yasan yana son daddynsa to amma fa wataran shima yanamasa masifa kaman yanda yakewa Mummy, to hakan yana nufin hakan danakeyi daddy bayajin dadinsa? , to meyasa nake hakane? Gaskiya ina son daddy na, dan bani da takamarsa, jiyayi kirjinsa yafarayi masa nauyi dan haka yatashi yakunna sigari, yana gamawa ya dora da giyarsa seda yafita hayyacinsa sannan ya kwanta bacci


Share please
More Comments............

๐Ÿ–Š๏ธ ๐Ÿ–Š๏ธ ๐Ÿ–Š๏ธ ๐Ÿ–Š๏ธ ๐Ÿ–Š๏ธ ๐Ÿ–Š๏ธ

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 6๏ธโƒฃ/59_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]



_MY FIRST NOVEL _


Abun takaicin, ya kwanta da bacin ran Jalila, zuciyarsa har wani tafasa take dan bacin rai, amma abun takaicin yauma kwana yayi yana mafarkin Jalila, cike da shaukin soyayya da kauna, a yanayi irin na ma'aurata, mafarkinsa na karshene me ban tsoro, ya firgita kwarai ganinshi yayi wasu mutane sun daureshi akan dutse, maza da mata suna saransa da wasu dogayen wukake, Jalila ta bullo daga wani guri ta taho da sauri ta rungumeshi, tana tare masa saran, yayinda sukuma mutanen suka dinga saranta jikinta yana zubar da jini, ta rungumeshi gam itakuma jini na zuba a jikinta a hankali take kiran sunansa a cikin kunnensa ABDUL JALAL. Juyi ya dingayi yana kokarin ya tashi, A firgice ya tashi daga baccin dayakeyi, yana haki, a hankali ya daga kai ya kalli agogo karfe takwas da rabi na safe, tashi yayi zaune yai shiruu yana nazarin mafarkin dayayi na karshe, jujjuya abun ya dingayi a ransa yana tuno yadda take furta sunansa, tunani yake meye alakarsa da wannan mutanen haka suke saransa, dan gutun tsaki yayi, "komeyema na bata lokacina akan wannan shirmen mafarkin" mikewa yayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet don yayi brush yai alwala kawai ya tuna se yayi wanka, sannan zeyi salla wani dogon tsaki yayi "Jarababbiyar yarinya ta addabawa rayuwata, tazomin a farke ta dameni, dan jaraba har cikin baccina ma seta biyoni, ji yanzu ga rana tayi amma senayi wanka zan salla komeye hakan oho" haka yaita mita yai wanka yafito yai sallar asuba.
Bayan ya idar da sallar ya tafi cikin gida, kai tsaye part din daddy ya nufa, ya tarar daddy ya tashi har yana breakfast Shida Mummy suna hira, sallama Jalal yayi, daddy yadago yana kallonsa yafara murmushi, Jalal yaje kusa dashi ya zauna, cikin girmamawa yace " good morning daddy" ba Mummy ba har Daddy seda ya kalli Jalal, rabon da ya gaida daddy haka da safe cikin girmamawa tun kafin ya lalace dan sedai daddy ya gaida Jalal amma badai ya gaisheshi ba, dama Mummy ba a maganarta itadama baya ta tata, amma abun mamaki yau hada sallama, daddy ya fadada murmushinsa yana shafa kan Jalal yace "Morning yarona katashi lafiya?" "Lafiya kalau daddy, ya gajiyar ka?" "Ba gajiya Jalal, kayi breakfast ne? Ko Jawwad din kake jira?" "No daddy Jawwad nasan ya tafi makaranta" "taho muci nawa to" girgigiza kai Jalal yayi, "kaci Abincin ka daddy, ni zanci nawa daga baya, dama zuwa nayi in gaisheka, sannan in kalleka inajin dadi, kasan na dade ban ganka ba nayi kewarka daddy"
Mummy tace "Hmm wannan soyayya haka, lallai Jalal" daddy yai murmushi yace "to ya ranki, nima kllonka yana sani farinciki yarona, idan na kalleka ina jin daฤi, wannan gudan jini nane, babbar kyauta daga Allah, ina alfahari da godewa Allah dayabani kai" dan shiru Jalal yayi cike da damuwa yace "daddy yanzu har farinciki kake da kasancewata danka, kalleni fa daddy kalli rayuwar danake yi, mutane dayawa na kyamar halayena, yayinda wasu suke gudun a dangantani dasu a matsayin danginsu saboda munin halayyata, mutane kalilan ke kaunata suke son farincikina daddy kai da Jawwad bansan wani irin so kukeminba, kai mahaifina ne amma Jawwad da rana ฤaya be taba kyamata ba"
"Jalal ko a yaya kake kai Allah yabani, kaine nawa ko halinka yafi haka muni inamaka fatan shiriya, amma ni a haka nake sonka, sannan lamarinka da Jawwad soyayyace daga Allah wanda samunta a wannan zamanin abune me wahala, shiyasa nake maka fatan samun mace tagari, Jalal ba abunda yafi zama da wanda yake kaunarka daฤi"
"hakane daddy, Jawwad na musamman ne, naso a ce ciki daya muka fito dashi, amma daddy dagaske bana sauke nauyin dayake kaina a matsayin danka ko? Yadda nake treating dinka bahaka ya dace ฤa nagari yayiwa mahaifinsa bako? Kayi hakuri daddy zan dena Insha Allah"
"waya gaya maka haka kai yaron kirkine, kana kokarin farantamin karka damu lokacine wataran se Labari, Allah ya shirya min kai" "Ameen daddy"
"Jalal ta mahifinka kawai kake, a tunaninka shikadai yake da hakki akanka, ni ko oho ko, da inyi farinciki dakar inyi baka damu bako?" hade rai Jalal yayi, yaiwa Mummy wani kallo me cike da ma'anoni, ya tashi ya fita ya bar dakin gaba daya, daddy ya dan dubeta " Hadiza sam bahaka yakamata ki dinga treating Jalal ba, ko kina manta kece me laifi a gurinsa, yakamata kiyi tunanin hakan. "haba daddy Jalal, shikenan shi abu baze wuceba a gurinsa, kullum da laifina zetamin hukunci" "hadiza ke kike ganin laifinki karamine, banga laifin Jalal ba lokacin danake jan hankalinki, baki saurareniba se yanzu data kwabe miki, seki nemi daidaito da ฤanki".
Jalila tana tafe akan varander na class dinsu ta ga captain dinsu da takaddu a hannunsa, yanata sauri da alama class zeje, wanda tayi Imanin takaddun hannunsa tests dinsu ne, sauri takara ta hada da dan gudu ta tana kiran sa, tsayawa yayi ya waigo, mamakine ya kamashi yaukumashi wannan yar kwalisar takewa magana ya tsaya suka gaisa da ita "Captain wannan tests dinmune ko?" "Eh sune, me yafaru" "yawwa dan Allah alfarma nake nema, sonake kabani tawa anan" "amma meyasa?" "bakomai kawai inason kabani tawa anan ne, banaso sekaje aji" yadda ta kafeshi da ido yaga tayi masa kwarjini matuka dan haka yace "to shikenan ya sunan naki, se in duba miki" "A a bani in duba tawa da kaina, karka damu ba ta wanda zan duba tawa kawai zan dauka" ba musu ya mika mata takaddun an faฤi test din nan sosai, kuma gashi over 40 ce duk an faฤi tunda test din be fadi zeyita ba, Jalila tana ganin tata ta zare, tana kokarin mika masa takaddun taga wani suna Samira Kabir Idris, Tunawa tayi Kabir Idris shine sunan dake dauke ajikin katin da baban faruk yabata a banki, mika masa takaddun tayi tace" Thank you very much "
" You are welcome " tunani ta dingayi waye me irin wannan sunan a ajinsu, maybe ma kawai sunane yazo ฤaya, da sauri ta tafi class taje gurinta ta zauna, Captain yana raba takaddu tanajin ya ambaci sunan Samira Kabir Idris, ta juya dan ganin kowace, wadda tai tsammanice Samira kawar saleema, se yanzu taga tsananin kamaninta da Alhaji Kabiru, kenan 'yarsa ce, ajiyar zuciya Jalila tayi, barewa bata gudu danta yayi rarrafe, ba a banza ba Allah yabashi irin wannan yar, Alhamdilillah bincikena zezo da sauki, sena gane alakarsa da Jeje, tana cikin tunanine taji captain yana cewa
"Yan class kunga munyi test, ga a yadda tazo dan haka se mudage a exams, sannan muyita addu'a dan banga wanda ya ci talatin bama, amma yace yanason ganin Jalila Aliyu Imam, in taji tasan kanta taje yana neman ta, danni ban santaba" zahra ta kalli Jalila," bake ake nema ba? "
"nice"
"Naga ba abaki naki test dinba, ni dai kinga wai 19 na samu" "kigode Allah ai kinyi kokari, yawwa zahra dan Allah samira sunawane yan gidansu" "Su biyune kawai yayanta faruk, sekuma ita sukenan" "Kuma a gidansu ansan me takeyi? "
"Gaskiya bansaniba babansu dai yana da zafi, wataran yana kawota makaranta, mamansuce dai ance ba ruwanta da tsanani akan tarbiyya"
"Mene sana'ar babansu?" "Kai Jalila sekace wata lawyer wannan tambayoyi haka" "yi hakuri akwai abunda nakeson ganewa ne" "gaskiya ban saniba, amma naji kaman ance dan kasuwa ne" "shikenan nagode sosai".
Bayan antashi daga school Jalila tai tafiyarta gida bataje kiran sir hafiz ba, tanata tunanin yazata bullowa lamarin Alhaji Kabiru, dan tana zargin mutumin nan sam bata yadda dashiba, wayarta ta dakko ta duba what's app dinta, taga lambarsa tayi appearing a contact dinta na wats app, dan bayan dawowarta gida ranar tasaka lambarsa a wayarta hotonsa ne akan dp dinsa tayi sa'a yana online, dan haka tayi masa sallama, seconds kadan ya amsamata, suka gaisa yace mata be gane me maganaba, rasa me zatace tayi, kawai ta kashe datarta ta ajiye wayar tai shiru tana tunanin anya haka yakamata tayi, ko kawance zata kulla da samira, amma in tayi haka itama za adingayimata kallon 'yar iska, lambar hanan ta kira amma taki shiga dan haka ta hakura.
Hanan kam tana kwance, tana trying lambar Jawwad amma a kashe, ta ajiye wayar ta dafe kanta, turo kofar dakinta, dan dago kai tayi da mamakinta setaga Siyama, zumbur Hanan ta mike tana murmushi "oyoyo Siyama matar Yaya yauke kika kawomin ziyara" murmushi Siyama tayi "yau nina kawomiki tunda kin mance dani nace bari inyi surprising dinki" "amma naji dadi" Siyama ta zauna, Hanan taje ta kawomata ruwa da lemo da snacks suka zauna sunata hira, Hanan ta kalleta "ta Yaya Abdallah gaskiya Siyama, kin rike wuyan yayana over, komai ke ni ya manta dani gayamin meye sirrine" "haba Hanan waceni rike wuyan Yaya, shiya rike nawa wuyan, wallahi Hanan Abdallah ya iya soyayya shiyake tabarani, bana tunanin akwai namijin daya kai yaya Abdallah iya soyayya da kula da mace" dariya sukayi gaba daya "Siyama ya bakyacin snacks dinne?" "A a ni snacks be dameniba dama chocolate ne" "Ahh sekace queen J, kinsan inkinaso ki birgeta kibata chocolate, gaskiya ina missing Jalila ina kaunarta har cikin raina, amma alakarmu na shirin samun matsala wanda hakan bazemin daฤi ba, amma nakasa samun mafita, dama kobakizoba ina son zuwa siyama" hanan ta karasa maganar cikin damuwa,
"Amma Hanan bangane mekike nufiba, kamarya alakarku na shirin samun matsala kamar yaya?"
"Siyama Jawwad nakeso, da farko na dau abun wasa, inayine domin Jalila ta maida hankali akan Jalal, saboda sunfi dacewa amma yanzu nagane wallahi son gaskiya nake masa kota ina yaya Jawwad ya hadu" zare ido Siyama tayi "Hanan kin san irin soyayyar datakewa Jawwad kuwa?" "Siyama soyayyar dake tsakanin Jawwad da Jalila na yan uwantaka ne, amma da Jalal ta dace shike bukatar taimakonta, ina kaunar Jalila amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba" Hanan ta riko hannun Siyama, idonta taf hawaye tace "Siyama babu wasa a zancena, wallahi dagaske nake inason Aliyu Jawwad, so na gaskiya, sannan ina kaunar Jalila ina jinta kaman wani tsagi na rayuwata, amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba" Ajiyar zuciya Siyama tayi, ta gogewa Hanan hawaye "For now kiyi hakuri ki dan bani lokaci, zanyi tunanin mene mafita, amma kidena kuka" gyada kai Hanan tayi kaman karamar yarinya, daga nan suka shiga wata hirar

Seda aka kwana biyu, Jalila bataje kiran sir hafiz ba, captain ne yazo yana kuma shela a aji, danshi besan wace me sunan ba, tashi tayi ta fita tatafi offers dinsa, tana zuwa ta shiga da sallama ta tarar da shi da wasu lecturers a office din ammasu dattawane ba kamanshi matashiba, amsamata sallamar sukayi, kaman yadda yake ฤabi'ar Jalila har kasa ta zube cikin girmamawa ta gaishesu, suka amsamata cikin mutunci, shi sir hafiz mamaki ma ta bashi, ya kalleta a fusace "uban mekikazo yimin office, kin fadiko? Ba abunda zanyi miki aidama seda nagaya miki fita kibani guri, dakikiya kawai kisawa ranki kin gama faduwa exams dina"

Please Login or Register in order to submit comment