Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda Allah yayi ta ka cigaba da yi mata Addu'a wataran se labari, kai ka ɗai ne ɗan da ta mallaka, be kamata a ce kana mata irin wannan halayen ba"

Kaman ze kuka cike da zuciya da ɓacin rai yace "nika ɗai take dani, kuma nika ɗai take azabtarwa"

"Jalal ya za'ayi mahaifiyar ka ta haife ka sannan kace tana azabtar da kai, baka fahimce ta bane....

" Enough Jalila kidena pretending kaman baki san komai ba mana, Jalila bana jin daɗin Alaƙata da mahaifiya ta, ina kulle kaina inyi kuka da hawaye na saboda rashin soyayya da kulawar mahaifiya, ban san jin ƙai na tsakanin ɗa da uwa ba, kullum tunanin Mummy burin ta kowa ni abu da take hange ya cika, bata tunani makoma ta, duk lokacin da nayi niyyar in shiga jikin mahaifiya ta in bata kulawar da zan iya, se ta bijiromin da wani abu da yake saɓanin tunani, me yasa yaushe Mummy za ta gane inda rayuwa ta dosa,? shi kansa Daddy yanzu bata gaban sa, shekaru talatin da uku yana haƙuri, Jalila har yanzu ina ganin lokacin da mahaifiyar Daddy ke zubar da hawaye saboda halayen mahaifiya ta yaushe Mummy zata canza tunanin ta se yaushe? Yaushe zata gane mutunci da soyayya gaba suke da dukiya? "

Jalal ya ɗau zafi sosai dan har jijiyoyin kansa sun fara miƙewa ya zuciya da yawa.
Ƙara matsowa kusa da shi Jalila tayi tace
"Jalal a duk lokacin da mutane zasu zauna da junansu ba dan Allah bato tabbas wannan zama ba shi da wani amfani, wanda suka zauna da Mummy a baya ba masu ƙaunarta bane, masu son abun hannunta ne, Baka tunanin in kayi haƙuri da ita kai mata biyayya a hankali ta shiryu? Rayuwarmu da mukayi a baya da wadda muke da kai a yanzu misali ce a gareka, Jalal baka da uzuri a gurin ubangiji idan ka mutu kana ɓatawa mahaifiyar ka rai, abubuwan da tayi tsakanin ta da Allah ne, Amma kai zaka yi aikin gyara halayen Mummy idan kaso"

"ta yaya?"

"ta hanyar bata matsayin ta na uwa, ka girmama ta, duk lokacin da tazo da abunda ba dai dai ba ka gyara mata cikin sigar rarrashi, kuma kaga yanzu bata da cikakkiyar lafiya tana buƙatar kulawa Amma kai baka shiga sabgarta Daddy ma ya ƙyaleta dama bata wani jituwa da 'yan uwan ta me kake tunani ze faru da ita?".

Haka Jalila ta cigaba da lallaɓa Jalal da yi masa nasiha har ya amince zasu tafi Kano dan yaje yaji neman da Mummy ke masa.

Koda yaje kiran da take masa ba akan komai bane face wasu daga cikin
ma' aikatansa za suyi ritaya, ya ware wasu maƙudan kuɗi domin ya sallame su, tun yana ƙaramin yaro suke juya masa dukiyarsa sunyi wa kasuwancin sa bauta, dan haka ya ware kuɗi masu yawa akan cewar ze basu, sannan ya bawa kowannen su vacancy na mutum biyu ze ɗauke su aiki, shine Mummy take faɗa akan danme ze bayar da wannan kuɗaɗe masu yawa haka?
Ƙarshe dai haka ya taho ya bar gidan ransa a ɓace tare da dana sanin zuwa gidan da yayi, yana mamakin wannaan hali da zuciya na mahaifiyarsa be san meze sa zuciyar ta tayi laushi ba.

A kwana a tashi tunda cikin Jalila ya shiga wata takwas zuwa tara aka yiwa Jalal ƙarin matsayi akai masa transfer ya dawo kano gaba ɗaya, Jalila tafi kowa farinciki da wannan transfer.
Jalila bata da aiki se ɗora yaran su Nana a status ɗin ta, Jaririyar Hanan kamarta ɗaya da Jawwad Jalila taita tsokanar su da "gidan Jajaye, uwa Ja uba Ja 'yarsu ma Ja"

Jalal na shan wahala tunda cikin Jalila ya shiga wata tara yau tace nan ciwo gobe tace can, ba ƙaramin tausayin ta yake ji ba, wataran se dare zata tashe shi tace "ita ta kasa bacci" haka zeta faman rarrashi.

Ummi ta gayawa Jalila kayan da zata shirya na haihuwa da alamomin da za taji wanda zata gane naƙuda ne. Gaba ɗaya jikin Jalila yayi sanyi dan tana matuƙar jin tsoron haihuwa sam ta kasa bacci, ga shi a satin nan tana ta fama da ciwon baya da ƙafafuwa, ga ciwon mara da yasa ta gaba ya hana ta bacci sam.
Juyawa tayi ta kalli Jalal yana ta baccin sa ita kam bacci ya ƙauracewa idon ta, tashin Jalal tayi ya kalle ta yace "Baby lafiya kuwa?" kamar zata yi kuka tace
"na kasa bacci fa"

"to kiyi haƙuri zakiyi baccin Insha Allah, ba abunda yake miki ciwo dai ko?"

"Jalal ina jin tsoron haihuwa, Hanan tace min akwai wahala fa"

"haba Jarumar mata, ita Hanan ɗin da suka haihu ba gashi ya wuce kamar ba'ayi ba, kiyi ta ambaton Allah komai zezo da sauƙi Insha Allah, da kinji ciwo kimin magana"

Jinjina masa kai tayi tace "to ɗan kwanta, se in kwanta a bayan ka"

Ya juya ya kwanta ta tada kai da bayan sa, ta ɗora ƙafafuwan ta akan pillow, A hankali yaji tana sauke numfashi alamar tayi bacci.
Ɗan girgiza kai Jalal yayi, lallai mata sun cancanci a girmama su kodan Albarkacin wannan ɗawainiyar da suke yi Allah ka ɗai yasan me suke ji, ko iya tashi da ƙyar da juyi ya ishi abnun tausayi, dan wani lokacin idan tana bacci ya kalli cikin yana ganin yadda cikin yake motsi, Yana wannan tunanin shima baccin ya ɗauke shi.

Juyi Jalal yayi akan gado yaga bata kan gadon ya kunna fitilar ɗakin can ya hango ta durƙushe a gaban gado tana ta haɗa gumi dukda fankar da take ta juyawa a ɗakin amma Jalila gumi take, da sauri ya sakko yana kiran sunan ta.

Kasa magana tayi sedai juya kai a hankali tace "Jalal bayana ze ɓalle"

Riƙota yayi yace "Sannu bari in saka riga mu tafi Asibiti"

A daren ya ɗauki Jalila suka tafi Asibiti, amma koda suka je aka sanar da su labor take yi amma da sauran lokaci.

Ba Jalila ba shi kansa Jalal seda ya ɗan karaya duk wannan wahalar ace da sauran lokaci.

Haka suka kwana a Asibiti, yana ta nafila da Adduoin Allah ya sauke ta lafiya.

Da safe yaje gida ya dafa Abinci da kansa ya kawo mata, tana zaune kaman ba me labor ba.

Zama yayi suna hira ya haɗa tea ya bata tana sha suna hira, wata nurse tace "gaskiya ba haihuwa zakiyi yanzu ba soyayya ma kike yi zaki ci ƙaniyar ki ne"

Jalila dai ba tace komai ba ta cigaba da shan tea ɗinta, Ba yadda Nurses ɗin basu yiba Jalal ya fita ba yaƙi, tana cikin shan tea ɗin tayi jifa da kofin hannun ta, ta riƙe rigar Jalal tana ambaton Allah gaba ɗaya Jalal ya ruɗe da ƙyar ya ƙwace rigarsa duk ta yamutsa ta, tun daga nan Jalila take fama kasancewar haihuwar fari ce.

Jalal ya kira Maama a waya ya sanar mata suna Asibiti, ya kira Hajiya Salma ya gaya mata suyi wa Jalila Addu'a suna Asibiti.

Befi minti Arba'in da wayar da Jalal yayi wa Maama ba tazo Asibitin.

Jalal ya fito harabar Asibitin yana ta kaiwa yana komawa, kallo ɗaya zakayi masa kasan hankalin sa ba'a kwance yake ba.

Suka gaisa da Maama ya rakata ƙofar ɗakin da Jalila take, suna iya juyo Jalila tana ambaton Allah daga inda suke.

Maama taita kwantarwa da Jalal hankali, suka ci gaba dayi mata Addu'a.

Jalila tun karfe biyun dare suke Asibiti se karfe sha ɗayan daren Washegari ta haihu, ta haifi ƙaton jariri namiji su kansu ma'aikatan seda sukayi mamakin girman jaririn.
Seda suka kintsa Jaririn da Jalila tsaf sannan suka sanar da Maama Jalila ta sauka lafiya.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi tare da fadin "Alhamdilillah"

Jalal ta kira a waya tace yazo tana son ganinsa, sam Jalal ko Abinci be iya ci ba, gaba daya tausayin mata ne ya mamaye zuciyar sa be taba zaton mata na shan wahala iirn haka idan zasu haihu ba, ya dauka abun ba wuya.

Yana zuwa Mama ta sanar da shi Jalila ta haihu kasa magana yayi se murnar tareda sauke ajiyar zuciya kafin daga baya yace "Alhamdilillah"

Suka shiga dakin da Jalila take, tana zaune an hada mata tea tana sha, kaman ba itace ta ke ta shan wahala ba.

Jalal ya kalli Jalila yace "Sannu Jalila ya jiki? Ina ne kuma yake miki ciwo?"
Tai murmushi tace "Alhamdilillah ina haihuwa na dena jin ciwon komai"

Maama tace "Sannu Jalila"

Jalal ya karasa gadon Baby ya dakko shi, jaririn kato dashi kaman Jalal yayi kaki ya tofar saboda kamar da suke yi.

Jalal yace "Maama yanzu wannan nawa ne? Ni Allah ya bawa?"

Maama tace "naka ne Jalal, Allah ne yaba ka"

Ya ƙanƙame yaron a kirjinsa ya tafi gadon Jalila ya zauna a gefen ta yace "Masoyiyya kalli waini ni ne da ɗa yau"

Maama ta fita ta basu guri.

Jalila tace "Zaujee ya zama Daddy"

Ya haɗa da jaririn da Jalila ya rungume su yace "Jalila ban taba zaton zan samu wannan Ni'imar ba, Allah ya shiryeni ya bani mace ta gari, yanzu kuma ya bani ɗa, Alhamdilillah"

Jalila ma rungume shi tayi tace "Zaujee kaga wahalar nan dana sha? Watakila Mummy ta sha wahala fiye da wadda na sha a gurin haihuwar ka, shiyasa Annabi salallahu alaihi wassalam yace "abi uwa sau uku sannan yace uba" dan haka zaujee dan Allah ka gyara tsakanin ka da Mummy "

"Jalila ina ƙaunar mahaifiya ta kamar yadda kowace halitta ta keyi, halayen mahaifiya tane bana son zuwa inda take"

Maama ta dawo ɗakin tace "Jalal ya kamata ka tafi gida dare yayi, gobe in Allah ya kaimu in an sallame mu se kazo ka dauke mu"

Da ƙyar Jalal ya yadda ya tafi gida.

Washegari da safe aka sallami su Jalila suka wuce gidan Maama, aka dinga sanar da 'yan uwa da abokan arziki Jalila ta haihu.

Nan da nan gidan Jalila yafara ciki da mutane, kowa ya ɗauki Yaron nan seya yaba kyansa.

Jalal bewa yaron nan huduba seda Jawwad yazo, yai masa huduba da sunan Jawwad Aliyu Haidar.

' yan garin su Mummy sunzo, mutanen Bauchi da Maiduguri ma duk sunzo, Hajiya Salma ma kwana uku da haihuwar tazo, dan taya su Jalila murna, kowa se yaba girma da kyawun jaririn yake, babu wanda yayi zaton Jalal ze samu canjin rayuwa daga tsohuwar Rayuwar da yake a baya.

Ranar suna ƙaton hall Jalal ya kama saboda taron suna, taron Sunan ya tara jama'a masu tarin yawan gaske, akaci aka sha jariri yaci sunan mahaifin Jalila kuma sunan babban Amin Jalal, Jawwad.
Kamar yadda kuka sani dama dangin Jalal Akwai bajinta haka suka dainga yiwa jaririn nan da mahifiyarsa kyautuka, kowane bangare yayi bajinta daidai gwargwado.

Akwatuna Jalal yayiwa Haidar da kuma Jalila ya bata kujera me girma a kamfanin sa, tare da rantsatsiyar motar hawa, (mhmmm Abun manya dai na manya ne) "

Jawwad yaji dadin karar da Jalal yayi masa, nasakawa dansa na fari sunan mahaifin Jalila kuma sunan Jawwad.
Kullum se Jalal yazo gidan Maama dan ganin Jalila da Haidar, Daddy ma ya zazzo ganin Jariri yayi masa Adduoi tare da bashi kyautu ka.

Tunda akayi haihuwar nan Mummy bata taba zuwa taga me aka haifa ba, musamman da taji abunda Jalal yayi, Abun ya damu Jalila matuƙa.

Dan haka da daddare da Jalal yazo ganin Jalila ta saka masa kuka
"Zaujee kwana goma da haihuwa ta, Koba danni ba yakamata Mummy tazo taga jikan ta, Jalal ina cikin matukar damuwa akan lamarin nan"

Jalal yace "Jalila zaki tausayamin idan kika san kuncin da nake ciki na halin ko in kula da mahaifiya ta ke nunawa akan al'amura na, ko baki fada ba dama nayi niyyar insha Allah da kaina zan kaiwa Mummy Haidar, da safe zanzo muje"

Jalal yaita rarrashin ta yana kwantar mata da hankali, Sam Jalal baya kara akan dansa, ji yake kaman ransa yaita kallon Haidar yana cewa "yanzu ni Allah ya bawa ɗa, dukda tarin laifukana a gare shi Alhamdilillah"

Tun daren Jalila take Addu'a tana fargabar me zata tarar in suka je gurin Mummy.

Kamar yadda suka shirya da safe, Jalal yazo ya dauki Haidar Jalila tace Hanan ta raka ta da yake bata koma ba, sukabi bayan Jalal zuwa gidan su.

Suka tarar da Hajiya Salma a gidan da Daddy, Mummy kana kallon ta zaka san ta rame saboda rashin lafiya, Amma har yanzu tana nan da gayun ta, hannun ta yasha lalle Ja, kanta ba ɗan kwali tai parking din gashin ta, wani abu take sha a cup kamar bata san da zaman Daddy da Hajiya Salma a gurin ba se kaɗa ƙafa take abun ta.

Su Jalila suka yi Sallama, Su Daddy ne suka amsa banda Mummy, Hajiya Salma tace "Jalila me yasa kika fito kina ɗanyen jego"

Tuni Jalila ta fara kuka tace "Anty Salma, Daddy dan Allah ku saka baki Mummy ta yafe min abunda nayi mata, dan Allah kar laifina ya shafi Haidar, kwana na goma da haihuwa bata ga abunda na haifa ba"

Har ƙasa Jalila ta zube tana cewa
"Mummy dan Allah kiyi hakuri kidena fushi dani, ki yafemin abunda nai miki kar laifina ya shafi jikan ki dan Allah"

Gaba daya tausayin Jalila ya kama su, ita kanta Mummy jikin ta seda yayi sanyi, ta ajiye kofin hannun ta ta dauke kai taƙi kallon Jalila, A hankali Jalal ya tako yazo gaban Mummy shima ya durƙusa akan gwiwowin sa ya ɗora Haidar akan cinyar Mummy yace "Mummy na, ga Abunda aka haifa min ba danni ba ba dan halina ba ki sawa jikan ki Albarka, koba komai ke kika haifi ABDUL JALAL ɗanki ɗaya tilo, kuma wannan jininsa ne, sannan zanyi Amfani da wannaan dama gurin neman Afuwar ki akan Abubuwan da nayi miki a baya, Mummy na, tabbas Jalila ta fini gaskiya duk abubuwan da kikayi min a baya, be kamata in saɓa miki ba duba da irin wahala da ɗawainiyar ciki da haihuwa ta da kikayi, ban taɓa ƙinki ba ke mahaifiya ta ce, halayen kine bana so, Mummy na kuɗi da ɗaukaka ba komai bane abubuwa ne da suke fararru ƙararru lokaci daya se Allah ya ƙwace abunsa, Amma soyayya da mutunci basa taɓa gushewa indai anyi sune dan Allah, Ki yafemin sannan dan Allah ki dena ƙin Jalila saboda haakan yafi komai cutar da zuciya ta, Mummy Jalila bata da wani laifi da ta aikata miki da ta cancanci ƙiyayyarki, kin manta alkhaiaran ta a gare ki? Kidinga hukunta mutum da alkhairin sa ba sharri ba"

Ƙurawa Haidar dake hannun ta Ido Mummy tayi, sak Jalal lokacin yana Jariri, ta tuna yadda Daddy yake bin ta Jalal yana kuka, Daddy yana haɗa ta da Allah ta shayar da Jalal, kamar Mummy na da Jalal yayi Amfani da ita ya tuna mata yadda In tazo hutu Jalal yake bin ta yana Mummy na dan Allah karki tafi ki barni, dan Allah ki zauna a gida ki dinga bani Abinci. Ta tuna yadda ya taso me biyayya daga baya rayuwarsa ta tarwatse sanadiyar sakaci da kuma kwaɗayin ta, dama Jalal ze shiryu har ya iya durƙusawa ya nemi Afuwar ta? tabbas ita ya cancanci ta nemi Afuwar sa dan tun bashi da wayo ya sha wahalar kadaicin rashin kulawar uwa.

Take taji ƙaunar Jaririn ya mamaye ta, inama da zata dawo, inama Jalal taiwa wannan kulawar lokacin yana kamar Haidar Rungume Haidar tayi ta fashe da kuka.

Daddy yace "ba kuka zakiyi ba, yara na durƙushe a gaban ki, rashin kyautawa dai kinyi ta tunda har seda suka zo suka kawo miki jariri da kansu"

Mummy tace "Jalal ɗina ni namaka laifi tabbas, ba inda yaron nan ya barka a kamanni irinsa sak na haife ka, sedai na gaza cika haƙƙina na uwa akanka, nabi son zuciya, ruɗin duniya da kuma ƙawaye na ajiye ka na tafi neman duniya, ƙarshe ga duniyar ta samu amma Alhakin Mutanen da na ɗauka ya dinga bibiyar ka yanzu kowa ni yake jin haushi kowa laifi na yake gani, Haihuwar yaron nan ya tunamin abubuwa da dama da suka gabata"

Kuma fashewa tayi da kuka tana shafa gashin kan yaron tace "Jalal am sorry forgive your Mum please"

Jalal ya zauna kusa da Mummy yace "Mummy na babu buƙatar ki nemi yafiya ta, wahalar da kika shiga kafin inzo duniya ya isa in duba ta in miki biyayya amma idona ya rufe, Alfarma ɗaya nake nema a gurin ki yanzu"

Ta kalleshi alamar ina jinka

"Mummy so nake ki ɗauki soyayyar da nakewa Jalila a matsayin tawa ƙaddarar kuma sakayya akan abunda kikayi a baya, Mummy ni kaina ban san wane irin so nake mata ba, Amma Mummy Jalila ta cancanci in so ta ne, Mummy kin san waye ni a baya, kin san irin ƙazamar Rayuwar da nayi, amma kalleni yanzu, jajircewar tace ta saka na gane ni me laifine nazo na durƙusa ina neman afuwar ki, baki nasha faɗar Jalila itace silar haske a rayuwa ta amma baki ɗau hakan da mahimmanci ba, Amma zan gaya miki dalilin da yasa bazan iya cutar da ita ba nake matuƙar son ta, Mummy idan duniya da gaskiya be kamata in wulaƙanta 'yar da Ummi ta haifa ba, dukda ba kya garin nan Daddy yasan komai yasan ita ta maye min gurbin uwa a lokacin da kikayi nesa da ni"

Nan ne ya zauna ya dinga warwarewa Mummy zare da abawa, Daddy yana tuna masa abubuwa da dama, har kawo lokacin da Jalila tazo kano suka haɗu, hatta ɗuren hayaƙin sigari da yayi wa Jalila seda ya faɗe shi, ya bata labarin gwagwarmaya da fama da Jalila ta dinga yi da Ilham akansa da wahalhalun da ta sha da abokan da suke sashi shaye2, Hanan ma seda ta faɗin abubuwan da shi kansa Jalal ɗin besan anyi su ba.

Shiru Mummy tayi ta sunkuyar da kai, ta kasa ɗaga kai ta kalli kowa a falon.

Jalal yace "dan Allah Mummy ki tayani son abunda nake so, idan kikayi yunƙurin rabamu banyi mata adalci ba, ban kyauta wa Ummi ba kuma naci amanar Abee, Mummy Jalila ta sha wahala ta, in dake ta, in zage ta in ranƙwasheta har hayaƙin sigari na bata saboda tana takura min, Amma bata karaya ba, ta cigaba da bani kariya da kulawa, itama in hakane ya kamata ta ƙini saboda abunda nayi mata, please Mum kiyi hakuri ki kyaleni da matata wallahi ina sonta "

Hawaye Mummy ta cigaba da gogewa amma ba tace komai ba.

Daddy yace
"Deejah kiyi magana mana"

"Daddy mezan ce, inajin kunyar abunda na aikata, nayi kuskure masu yawan gaske tabbas sakayya ce tasa Allah ya jarabci Jalal da son matarsa, da a tunani zan iya kaucewa ayimin abunda nayi shiyasa naso in zaɓo masa mace da kaina, Amma ba'ayi wa Allah wayo, Alhamdilillah Jalal ka samu sauyin Rayuwa, ina matuƙar jin kunyar ka da matarka, tabbas matar ka ba ta dukiyar ka take ba, kaine a gaban ta da rayuwar ka, tabbas itada Jawwad sun taka mahimmiyar rawa a rayuwar ka, wanda ni ban sani ba, dan Allah kuyi hakuri ku yafe min"

Murmushi Jalila tayi ta sunkuyar da kai tana share hawaye tace "Nidai Mummy in dai kin yafe wa Jalal shikenan"
Haidar ne yafara motsi zeyi kuka, Jalal yace "Mummy kawo shi"

"A'a Jalal ka ƙyalemin shi mana, zan iya rarrashin sa ai Gani nake kaman kaine lokacin kana jariri"

Jalal yace "A'a Mummy ke ɗanki ya girma, wannaan ɗana ne idan kina so to kimin ƙani"

Hannu tasa ta talle ƙeyar Jalal tace "sannu mara kunya"

Hajiya Salma tace "Masha Allah, naji daɗin faruwar hakan, ina fatan zaki dena zarginmu akan mun aurawa ɗanki yarinya bada izininki ba, ba muyi hakan dan cutar da shi ba, wanda be guje ka ba lokacin mutane suna gudun ka ba, to tabbas shine masoyin gaskiya"

Mummy tace "Hakane kema Salma kiyi Hakuri dan Allah ki yafe min, tawa tayi kyau da Allah be jarabce ni kamar yadda ya jarabci 'yar uwa ta Saudat ba, Daddy dan Allah ka tayani neman Afuwar family ɗinka, tabbas na aikata kurakurai masu yawa a rayuwa ta"

Jalila tace "Mummy aishi Allah me Rahama ne da jin ƙai babu ruwansa da girma da yawan laifukan ka, indai harka roƙe shi afuwa ze yafe maka"

Mummy tace "Jalila ban san haka al'amuran suka faru ba, na miki wulakanci na ci mutuncinki dan Allah ki yafe min"

"bakomai Mummy abunda yafi komai yimin daɗi be wuce ganin dai daita warki da Abban Haidar ba"

Sosai Mummy tayi nadamar abunda tayi, sega Mummy da kanta take neman yafiyar wanda taiwa laifuka, Sosai take nunawa Jikan ta ƙauna ta ɗauki son duniya da tattali take wa Haidar.

Ummi tayi Aure, ta Auri wani ɗan uwan ta a can garin su.

Ilham kuwa seda aka kaita Asibitin masu tabin hankali saboda zabure zaburen da take yi, Umman ta kuma se gidan gajiyayyu aka kaita a can ta rasu.

Yaya mairo ma komai ya kwaɓe mata, Naja ta zama tantiriyar 'yar ƙwaya kuma karuwa, Sa' adah kuwa tana can gidan yari.

Farinciki ya shiga tsakanin iyalan, duk wata hayaniya da abubuwan da Mummy tayi ta sauke su a gefe ta rungumi carbi tana tuba ga Allah ga kuma jinyar larurarta na hawan jini da ciwon zuciya ga ciwon sugar.
Dukiya gata a jibge amma babu lafiyar morarta yadda ya kamata, ga shekaru sunyi nisa.

Daddy ya dawo Nigeria domin ya huta girma ya kama shi, ya ɗora Jalal akan al'amuran ya cigaba da kula da komai, ya canza gida ya haɗe Mummy da Hajiya Salma a gida ɗaya.

Seda Jalila ta haifawa Jalal yara shida, Haidar kam gurin Mummy ya koma da zama saboda ƙaunar da take nuna masa.
Haka Nana da Hanan suma sun hayayyafa suka Cika gida da
'ya'ya ga soyayya da ƙaunar juna da ya wanzu a tsakanin iyalan





TAMMAT BIHAMDILLAH
ALHAMDILILLAH ALA KULLI HALIN
DUKA DUKA ANAN NA ƘARƘARE WANNAN LITTAFI ME SUNA ABDUL JALAL ALHAMDILILLAH ƘWARIN GWIWARKU DA ƘAUNAR KU CE' YAN UWA DA MASOYA TA KAINI GA KAMMALA WANNAN LITTAFI.

JINJINA DA GODIYA TA MUSAMMAN GA IYAYENA DA ABOKAN ARZIKI
NAGODE DA KULAWA DA ƘAUNAR KU

ABDUL JALAL NOVEL FANS GODIYA TA MUSAMMAN BAZAN MANTA DA GUDUNMUWAR KU BA INA ƘAUNAR KU, KUN ZAMA WANI ƁANGAREN FARIN CIKI NA RAYUWA TA.

PERFECT WRITER'S ASSOCIATION ƘUNGIYA DAYA TAMKAR DA DUBU, GODIYA TA MUSAMMAN A GAREKU 'YAN UWANA, ALLAH YAKARA MANA KAUNAR JUNA YA KAIFAFA ALƘALAMINKU.

INA FATAN AN AMFANA DA SAƘONIN DA DARUSSAN DAKE CIKIN WANNAN LABARI, KURA KURAN CIKI DAGA GARENI NE INA FATAN ALLAH YA YAFEMIN

INA FATAN DUK WANDA NA ƁATAWA RAI, KO WANI LAIFI DAN ALLAH YAYI HAƘURI YA YAFEMIN.

INSHA ALLAH ZUWA BAYAN SALLA IN ALLAH YA KAIMU ZAN SANAR DA KU LOKACIN DA ZAN CIGABA DA KAWO MUKU SABABBIN LITTATTAFAI NA

ƘOFATA A BUƊE TAKE DOMIN KARƁAR GYARA SHARHI, ƘWARIN GWIWA KOKUMA ƘORAFI.

TAKU HAR KULLUM
AISHA HUMAIRA DADDY'S GIRL WACCE KUKAFI SANI DA AYSHERCOOL

WHAT'S APP 07063065680
WATPAD @ AYSHERCOOL7724 [email protected]


Nafara wannan littafin July 2020
Na kammala a April 2021
Alhamdilillah






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet

Please Login or Register in order to submit comment