Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakko kudin tabawa manu tace gashi nan, aiwa maman sannu, kuma ita kyauta ta bashi ba rance ba" manu kaman ya yi kuka dan murna se godiya yake mata.
Jalila na zuwa gida, ta tarar gidan ba kowa dan haka ta tafi dakinsu ta haye gado ta sha baccinta, alhalin school ana can ana lectures, se bayan azahar ta tashi, tana tashi da baban faruk ta tashi a ranta, ras take kuma ganin katin daya bata a idonta, kabiru Idris, shine sunan dayake jikin katin, wayarta ta dakko tayi saving sunansa da lambar sa, da adress din dayabata a jiki, duk tayi saving a wayarta, sannan ta aje wayar a hankali, sannan tace kaima ban yadda da kai ba. Ta tashi ta tafi kitchen ta hado cornflakes dan tana jin yunwa, maimakon ta koma daki seta fito harabar gidan tai zamanta a kujerun harabar gidan, ta gefen Jawwad dayake gurin akwai bishiya, ta zauna tana shan cornflakes dinta, tanayi tana karanta qura'ani a hankali, tana dan kaฤa kafarta, Jalal ne ya shigo yazo ya wuce ta gabanta bata kulashi ba be kulata ba, ya wuce part din Jawwad, yana zuwa ya dau laptop dinsa da yabari a dakin ya samu guri ya zauna ya fara video call da daddynsa
"My Man ka girma, naga hotuna na birthday kunyi kyau Allah yakaro tsawon rai da lafiya me inganci" "to Ameen amma ni fushi nake da kai"
Daddy yai dariya "to menayi?" "Kaje ka makale a England kaki dawowa, bakayi attending birthday na ba" daddy yai murmushi "to ai nace ka daga birthday din indawo kaki, kuma abubuwa sunyimin yawa anan gakuma aikin daka sani, koka manta ne?" "ban manta ba daddy, ina fatan ana samun cigaba" "eh anasamu Alhamdilillah" "to hakan yayi kyau, yaushe zaka dawo?"
"ina nan tafe next week Insha Allah"
"To dan Allah ka dawo haka, inaso indinga ganinka" daddy ya dan girgiza kai "Allah sarki yarona, karka damu, nace kazo nan mu zauna tare kaki" Jalal cikin damuwa yace "Haba daddy, in taho nan in bar aminina dan uwana, kasan bazan iyaba" "Hakane Jalal, ina Dan nawane, ko yau bakwa tare?" "Yana makaranta" "that's good, Allah ya nunamin ranar da zaka koma makaranta, yanzu ka zama mutum Jalal ina fatan Allah ya shiryamin kai inmaka aure" ya mutsa fuska yayi ya kalli system din "Aure kuma? Habaa daddy yaushe aka haifeni, ni banason gayyatowa kaina matsala, mata matsalane daddy kaima kasani" ya karashe maganar kaman zeyu kuka,
"ABDUL JALAL, bakowace mace ce matsala ba, in har kayi dace da samun mace ta gari, kaga hotunan birthday dinka danagani, dana ganka tareda Takwararka abun yamin daฤi, senaji dama matarka ce, yarinyar tanada nutsuwa ga tarbiyya " wani mugun hade rai Jalal yayi "What matata kuma, Allah ya kiyaye, wannan kwailar, mara kunyar, na auri wannaan sedai kuzo ku tarar na kakkaryata"
A gigice Ilham ta tashi zaune, ganin hotunan da aka turomata ta what's app, ba tareda tasan waye ya turoba, hotunan dasu Jalila sukayine, a kasa aka rubutamata "Yakika gansu, perfect match, ina musu fatan Alkhairi, da fatan kasancewa tare har abada, wannan itace matar data dace da Jalal bake ba" mikewa tsaye tayi akan gadon, "What ni za ayiwa wannan rashin hankalin, lallai Jalila tayi bal'in rainamin hankali. Ba tunanin komai, taja gyalenta tai waje, Mummy tana yimata magana amma taimata banza, ta fita se gidansu Jawwad, tana zuwa taga mutuniyar tata a hakimce a farfajiyar gidan, kusada part din Jawwad, a inuwa se kada kafa take, tana ciye2 hankali kwance, bazar2 Ilham ta tunkari Jalila taje kanta ta tsaya tana huci, Jalila kam kaman ba kowa a gurin, tacigaba da abunda take. Cikin masifa Ilham tace
"Wato gargadin danayi miki bakiji ba ko? Saboda kin rainamin hankali, abunda kukayi keda JALAL a gurin birthday dinsa be isheki ba ko? Hakan be miki ba seda kika hadani da wannan tsinanniyar yarinyar Hannah a gurin nan, Shine duk be miki ba sekin hada da turomin hotunanku, sau nawa ina gaya miki kifita harkata, ina tausayawa rayuwarki idan na tashi hukunta ki" Ita Jalila abun mamaki yake bata wai wace jarabar hotuna na ake damunta haka akai, ba tareda ta kalli Ilham ba tace
" tunda kekika halicceni dole ki tausayawa hukuncin dazaki yimin mana, ki kasheni ki huta mana, seki tabattarmin dake kanwar Jalal ce, hakan se ya tabbatar da cewar bashi kadai yake shan giya ba"
Takarasa maganar cikin ko in kula, tacigaba da watsa cornflakes dinta a baki, Ilham ta kawo iya wuya, wato Jalila takai karshe gurin raina mata hankali, idonta taf hawaye tace "Wallahi Jalila in baki fita hanyata data Jalal ba, kina daf da fadawa rijiyar sharrina, idan nasakoki gaba ruwa seya gagareki sha, Inakuma yimiki kashedi kinfara kaini bango, idan turn dina yazo bazaki ji dadi ba, ki kiyaye.
Jalal ne yake tajin hayaniya, har ya basar ze kwanta seyaji hayaniyar yana kara yawa, dan haka ya yanke shawarar fitowa dan ganin meke faruwa, yana fitowa ya tsaya a kofar part din Jawwad yana kallon dramar da ake.
Ilham tacigaba da cewa
"waike wace irin mayyace? Mara zuciya, meye hadinki da mune, baki da alaka ta kusa ta nesa damu why do you involve yourself in our family matters, nagaya miki nakuma gaya miki Jalal nawane, wace irin mara zuciya ce ke, kishiga hankalinki harni zaki turawa hotuna, kina kece kika dace da Jalal, zakiga wacece Ilham, na daga miki kafa amma baki ganeba, zakiga me zanyi" Kamshin turaren JALAL Jalila taji, hakan ya tabbatar mata da fitowa yayi, dan haka bata kula Ilham ba ta mike tsaye, ta taka a hankali, cikin takunta na isa, kunsan fa Ummi jinin sarauta ce dan haka akwai abun a jinin Jalila, taje gaban Jalal ta tsaya, ta kalli Jalal sannan ta kalli Ilham, ta nuna Jalal sannan tace "Wannan shine mara zuciya, mara tarbiyya shiyakamata, kigayawa bakaken maganganu bani Jalila ba, shi duk abunda yake meyasa baki ja kunnensa ba dan kina tsoronsa, kokuwa dan abunda yake ranki wanda kike boyewa, to ni bana tsoron kowa se mahalicci na, aike karamar mara kunya ce, ni idan zanyi sedai aga na aikata, bana fada, idan akabari nafadi abunda zanyi komaj muninsa sena aikata, ke alwashi nawa kika dauka kika kasa cika ko daya, Tunda ABDUL JALAL yashiga rayuwar Yaya Jawwad to a cikin rayuwata yake, shi zaki Jawa kunne ya rabu da Jawwad, in har ya rabu da Jawwad, ba ruwana da shi, bari kiji in gaya miki za ayi dayan biyune ko Jalal ya fita daga rayuwar Jawwad kokuma kudirina.... Sekuma tai murmushi ta kalli Jalal
"Kagayawa wannan sokuwar yarinyar, niba abunda zanyi da kai, baka da abunda ze birgeni insoka bana cikin jerin banzayen matan da zasu zubar kimarsu da ajinsu akan namiji mara daraja irinka, wanda besan ciwon kansa ba balle yasan na wani, namijin da besan darajar iyayensa ba, namijin dabaya girmama alaka, dan da kanayi da zuwa yanzu ka tausayawa Jawwad kadena abunda kake, namijin dabe maida sabon Allah komai ba, baya kunyar sabawa mahaliccinsa agaban kowa, shikike tunanin ya cika siffa da kamalar dazan soshi a matsayin uban y'ay'a na, shi kike tunanin zan zubar da kimata ina hayagaga dake akansa "ta nuna Jalal sama da kasa da hannunta
" Ilham ki canza tunani, Jalila ba irin sauran matan da kike tunani bane, duk abunda kikaga inayi i have a mission, kawai ina kokarin rama Alkhairi ne da Alkhairi, karki manta da maganar dana yimiki abaya muddin kudirina yaci karo da na wani zan rusa kudirin ko uban waye dan cikar burina" ta waiga ta kalli Jalal, da idonsa tuni yayi ja, gashi ya kasa matsawa daga inda yake kaman an dasa shi, Ilham rasa bakin magana tayi, Jalila ta kalleshi a wulakance, kaikuma ka gayamata ta kiyayeni dan muddin takuma cin mutuncina saboda kai akanka zan rama, har sena gamsar da ita cewa bawata alaka me ma'ana tsakanina da kai" tana gama fadin haka takoma ta dau Cup dinta tai cikin gida ta barsu nan a tsaye.
A hankali ya lumshe ido, ya tako a hankali ya nufi hanyar fita, Ilham tai sauri tace "Yaya Jalal dan Allah... Daga mata hannu yayi alamar baya son jin mezata ce, yai gaba abunsa, maganganun Jalila na cigaba da tafarfasa zuciyar sa. Yana shiga gida ya nufi part dinsa ya samu guri ya zauna ya dafe kai yai shiru, Ilham ta biyo shi tazo ta zauna a kusa dashi, "Dan Allah yay Jalal kayi hakuri, nibani da laifi anan, kawai ina kokarin kare alakar dake tsakanina da kaine, meyasa bazaka yadda dani a in zama wani bangare na rayuwarka ba"? Tashi tsaye yayi ya tafi bedroom dinsa ya kulle kofa ya barta a palour.
Jalila koda ta koma dakinsu, kwanciyarta tayi ta dakko wayarta, tafara chatting, ta bude pages da take advertising kayan da Maama dakuma Mummy Jalal suke siyarwa, tana kawo musu customers sosai, daga gurare daban2, wasu suzo da kansu, wasu kuma a aika musu har garin da suke, gashi Jalila ma tana harkar catering ta iya girke2, wani lokacin ta kanyi snacks ta siyar, gashi duk karshen wata Abba yana basu kudi, wani lokacin dubu Ashirin zuwa talatin, inda me bukata tayi amfani dasu, Jalila bata da wata matsala se na kewar Ummi da har yanzu yake damunta, dan har yanzu takan kulle kanta tayi kuka me isarta, tana naan tanawa Ummi Addu"ar Inda rabo Allah ya kuma hadasu.
Chats dinsu da siyama ta bude taga ta turomata hotuna tana dubawa taga hotunanta ne da Jalal, wani dogon tsaki taja yanzu watakila saboda wannan hotunan Ilham tazo kanta tanamata hauka, har zata rufe data dinta taga wani sako ya shigo, tana budewa taga an mata sallama, ta duba profile din taga basuda group in Common dame maganar, amma an rubuta unique zarah, batayi reply ba ta rufe data. Da Nana ta dawo tayi mamakin ganin Jalila a gida, Manu yagaya mata ai tun goma da rabi ya dawo da Jalila gida, Nana ta kalli Jalila
"Jalila ya akayi naganki a gida, manu yacemin tun safe kika dawo, kobaki da lafiya ne?" "lafiyata kalau zaman makarantar ne ya isheni, na dawo gida" dan zare ido Nana tayi to lectures dinfa? "
" Kinga ki manta kawai"
"Bangane in manta ba kefa al amuranki se a hankali" "A a nagaya miki gaskiya to meye na tuhumata" Nana tace "tabdijan, A haka zakiyi karatun sekin gadama zakiyi attending class in kika fadi fa" "Nana kidenamin fatan faduwa, ba abunda zekadani Insha Allah" "to Allah ya yadda amma dai banga ta yadda za aci jarrabawa a haka ba" Jalila ta dan tabe baki tace "ke kika ga haka"
Tunda Ilham takoma gida takewa Mummy kuka, "Mummy dan Allah ki gaggauta auramin Jalal, wallahi zuciyata daf take datayi bindiga in har ban mallakeshi ba, Mummy nagaji da wulakancin Yaya" Mummy ta dafata
"Kiyi hakuri mana Ilham kefa macece yakamata kija ajinki, kuma ni namiki alkawarin auren Jalal" "Mummy babu wani batun aji a fagen soyayya, Mummy dan Allah kiyi wani abu"
"Haba Ilham wai meye hakane, kibari daddynsa ze dawo next week Insha Allah, in ya dawo semu san yadda za'yi, tashi ki tafi dakinki ki dena wannan kukan" mikewa Ilham tayi ta tafi dakinta, tana zuwa ta rufo kofa, sannan tai kwafa "Mummy kicigaba da jamin rai akan auren danki, koki sabaki ya aureni ko karkiyi sena aureshi, sena cika burin mahaifiya ta, sekin wulakanta kin dandani bakin cikin da uwata tayi, ko zan tafi tsirara bazan bari A banza Jalal ya auri wataba bayan ni, wasan ze fara nakusa kawo karshen wannan dramar, indai na haifu se nasa bakin cikin ABDUL JALAL ya kusa kasheki, sekuma ya aureni dan zan iya halaka duk wadda tai nufin aurensa ko wacece!!!!!

Share please
More Comments More typing..............................

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

_ABDUL JALAL (2020)_

_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)

PART 2
_PAGE 3๏ธโƒฃ/ 56_

Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki, da suka bibiyeni a littafi na farko, Alhamdilillah yanzuma gani na dawo domin kawo muku kashi na biyu, nagode da kulawarku, ku biyoni domin jin yadda zata kaya a cikin wannan littafi naku me farin jini.
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Gmail @ [email protected]
Facebook real humaira


_MY FIRST NOVEL _


Daga nan Ilham tai kwafa, ta nufi kan gadonta, tai shiru tana sake2 a ranta.

Jalal kwata2 yarasa abunda yake masa dadi, meyasa Jalila tai masa wannan muguwar tsanar haka, bata da burin da yawuce taci mutuncin sa, tabbas maganganun da take gaya masa sun fara isarsa, dole ya hukunta ta hukuncin da suka hadu seta canza hanya, hukuncin da zata dandani abunda yakeji idan taci zarafinsa, gata kanwar kanwarsa, amma ko Ilham dasuke gida ฤaya bata isa tayi masa haka ba, jiyayi zuciyarsa na wani irin zafi mussaman idan ya tuna yadda Jalila take kiransa da namiji mara daraja. Dole ya hukunta ta dai2 da abunda tayi masa, Ilham ma ze gamu da ita, duk yadda yaso ya manta abunda tayi masa kasawa yayi, karshe ma yaji zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi haka yaita juyi akan gado.
Jawwad kam be dawoba se bayan la'asar ya gaji matuka, dan haka benemi Jalal ba se bayan, sallar magariba, yaje gidansu ya duba dakinsa yaga baya nan ya duba bedroom dinsa se yaji shi a rufe, be kawo komai a ransa ba yakoma gida, yai trying lambar Jalal amma shiru baya dagawa, haka ya hakura ya nemi abunda zesawa cikinsa, dan yasan maybe Jalal ya tafi nasa yawon, amma ya damu da rashin daga wayarsa da Jalal beyiba.
Nana tana kwance tana waya da saurayinta, Maama ta shigo dakinsu tace dan Allah in tayi salla taje ta karbo mata laces a wajen Mummy dan in anjima hajiya Jamila zata turo yaranta su karba, dan bata fuska Nana tayi "Maama dan Allah ki aiki Jalila baby ne zezo fa, Maama ta dan bude baki" Lallai Nana, wato saurayinki yafi aikena ko? "" murmushi Jalila tayi tace "Allah ya shiryeki Nana, bari inyi sallar magariba ni se in karbo miki Maama" dan gyada kai Maama tayi ta fice

Jalal kam yanajin wayarsa na ringing yai banza dan tunda ya kulle kansa a daki be fito ba, banda jujjuya kalaman Jalila ba abunda yake, ga yunwa yakeji yanzu yana fita Jawwad ya ganshi a haka ze dameshi da tambayoyin me yake damunsa danhaka ya yanke shawarar ya shiga cikin gida yasamu abinda zeci base yaje gurin Jawwad ba. Ya mike daga kan gadon ya fara yin alwala dan sallar asuba kawai yai, gashi yanzu magariba akeyi, yayo alwala yazo yai sallar azahar da isha'i, seyaji ya gaji dan haka ya mike yace yayi magariba da isha'i anjima kokuma gobe da safe, ya bude dakinsa ya fito, cikin gida ya nufa yana shiga palour Mummy suna kallo itada Ilham bebi takansu ba ya nufi kitchen ya zubo Abinci, ya dakko madara ya fito, abun mamaki yabawa Mummy dan kwanan nan yadena cin Abincin su, Mummy ta kalleshi tace "Jalal zo mana" waigowa yai ya kalleta kaman kar yaje kome ya tuna, kawai se yadawo yasamu guri ya zauna a palourn, yafara cin Abincin sa ba tareda yace komai ba, Mummy takuma tattara hankalinta ta kalleshi "yanaga kana cin Abincin mu yau?" Jalal be dago ya kalleta ba yace
"Dame gidan yakawo Abincin yace banda nine? Yabata amsa ba tareda ya kalleta ba ajiyar zuciya Mummy tayi
" A a ni banceba kokunyi faฤa da Jawwad ne? "
" No, yau abincin gidan mahaifina nakeson ci" "Hmm hakan yayi kyau dan nima bana jin dadin kauracewa abincin mu dakayi dukda tarin dukiyar mahaifinka amma ace sedai kaci Abinci a wani guri. shi Jalal mamakin yadda taketa lallabashi yakeyi, ya sha madarar sa sannan yace "Serious ashe bakya san hakan, hmm amma kinsan wani lokacin abun hannun Jawwad ya fiyemin abun cikin gidan mahaifina" Mummy tace "kaga ba wannan ba, daddynka ze dawo next week" "munyi waya, yagayamin" yabata amsa a takaice "Yawwa dama sonake in yadawo ayi maganar aurenka, tunda lokaci yayi dayakamata ace daga kai har Jawwad din kunyi aure, aure shine cikar mutum"
Bayan Jalila ta idar da sallar magariba ta fito karbowa Maama aikenta, kaitsaye gidansu Jalal ta nufa ta tsaya suka gaisa dame gadinsu sannan ta wuce, tana zuwa ta tura kofar palourn ta jiyo hargagin Jalal yana masifa
" wakike tunanin ze auri mutum irina, wakike tunanin yabani 'yarsa, ko sokike in auri wadda zata soni dan dukiyata? Ta aureni dan ta kasheni ta mallaki abunda nake dashi, Wace yar mutuncin ce zata auri ฤan da kikayi sanadiyar lalacewarsa da kanki, lalatacce dan giya kamarni Mummy kozanyi aure a rayuwata se wadda zata soni dan Allah badan wani abu nawaba, wadda bazata kyamaci rayuwar da nake ba, meye damuwarki da dole senayi aure, ai aure ba dole bane"
Da sauri Mummy ta katseshi ta hanyar cewa "A a Jalal abun duk be kai haka ba, baga Ilham nan ba, itace me sonka tsakani da Allah meze hana ka aureta ai kanwarka ce" wani mugun kallo yayiwa Mummy "Au Ashe kinada wani ฤan da kika haifa bayanni ai ban saniba se yanzu" Mummy ta kalleshi cikin rashin fahimta tace "kamar yaya?" "inba wani ฤan ne dake bayanni ba ai kinsan ba amin dole ko? Ya kalli Ilham" Ke! A tsorace Ilham ta waigo ta kalleshi "tunda muke na tabacewa ina sonki" shiru tayi ba tace komaiba, ya kalli Mummy cikin masifa da tsawa yafara mata magana
"wai dan Allah yaushe zaki fara playing role dinki na uwa, kimin adalci a matsayinki na mahaifiyata, ba kya tunanin in shiryu, se kokarin kuma rusa rayuwata domin wanke laifinki a idon wanda kikayiwa, yakamata ki tausayamin ko sau dayane yakamata ki barni na huta haka, please Mummy ki tausayawa rayuwata haka, a matsayina na tilon danki" karo na farko da Jalila taji ya kira mahaifiyarsa da Mummy, itakam tana son sanin tarihin Jalal da mahaifiyarsa, amma waze gaya mata. Jalal kam yana gama fadin haka ya tashi ya bar palourn ya fito fuuuu kaman guguwa, yana fitowa be kula da Jalila ba a gurin ya wuceta, a hankali tabi bayansa, yana zuwa motarsa ya nufa, yana zuwa ya shiga motarsa yana kokarin kunnata, seya fasa kunna motar ya jingina da kujera yayi shiruu, gefen motarsa taje ta tsaya tai knocking glass din, a hankali ya sauke glass din motar kawai yai tozali da fuskar Jalila. Kokarin kunna motar yake, saboda yasan in har ya tsaya ze iya illata yarinyar nan, dan yasan yanzunma ci masa mutunci zatayi, hannu tasa ta dafa window din motar saitin Jalal tana kallonsa, tana iya juyo yadda yake numfashi,
"ABDUL JALAL kaji tsoron Allah kaji, karka mutu mahaifiyarka tana jin haushinka, kome tayi maka kabata matsayinta na uwa, Annabi salallahu alaihi wassalam se da yafadeta sau uku yace abita sannan yace uba, kaji tsoron Allah kadinga yafiya mana, ka tausaya mata kaimata biyayya, kaji dan gidan daddyn sa, ba daddy kawai keda hakki akanka ba, nasan yanzu mashaya zaka tafi, dan ba kunya ce da kaiba naga baka da alamar zaka dena shan giya, kayi a hankali da duniya, sannan ka kiyayi miyagun abokai, u have to focus, ka kiyayi JeJe da Hannah da sauran miyagun abokanka, basa komai banda rusa maka rayuwa, basa nufinka da alkhairi ka kiyaye, jeka Allah ya shiryeka" manyan idanunsa da suka sauya zuwa launin ja ya zuba mata, cikin idonta ya saka nasa, dukda akwai duhu se hasken fitilu be hanashi ganin fararen idanuwan taba masu kama da tana jin bacci, ji tayi kaman an daureta takasa motsawa tabar gurin, itama ta kura masa ido, ji tayi idonta yayi nauyi, ga Jalal yamata wani irin kwarjini, kamshin turarenta duk yacika masa hanci, daurewa yayi, yai mata wani mugun kallo me wuyar fassara, sannaan ya dauke kansa yace
"ki kiyayi haduwata dake, zanyi maganin wannan shishshigin naki, sekinyi dana sanin shigowa rayuwata, zan baki mamaki, bari in tuna miki alkawarin dana taba yimiki, zan maida ke abun kwatance irina, matsa ki bani guri ko in takeki da mota. A hankali ta motsa bakinta, tafara magana a hankali cike da rainin hankali tace
"zaka iya ai, inbaka takeni da mota ba ba sunanka ABDUL JALAL ba, ni bazan fasa fadan gaskiya ba, kome za kayimin, Kuma bazan taba zama abun kwatance irinka ba, dama kwatancen kirki ne da sauki, Allah ya tsareni zama abar kwatance kamar dan giya"
"Haka kikace?" "baka da kunne ne?" Ajiyar zuciya Jalal yayi, ya kunna motarsa, Jalila ta ja dabaya ya ja motarsa da gudun tsiya, Jalila ta juya zata shiga gidansu Jalal, taga Ilham a tsaye a bakin kofa tana mata wani irin kallo na tuhuma, fuskarta na dauke da tsantsar bacin rai, dakuma tsanar Jalila, dan tana hangen abunda yafaru, tsakanin Jalal da Jalila, a hankali Jalila ta karaso, kota kan Ilham bata biba, ta tureta gefe ta wuce cikin palourn, ta tarar da Mummy a palour ta fada mata sakon da aka aikota, Ilham ta shigo palourn taji zuciyarta tana raya mata taje ta dakko wuka ta kashe Jalila ta huta, itako Jalila ko kallon Ilham batayi ba, tacigaba da abunda take.
Jalal kam kaman yadda Jalila ta fada, mashayar sa ya tafi, amma yana tafe tunani kawai yakeyi, yana ta nazarin mezeyiwa Jalila wanda ze bata mata rai, soyake ya bata mata rai yadda zataji zafi sosai fiye da yadda take masa, manyan mutane ma suna shakkarsa, saboda kwarjinin sa, amma yarinya karama tana caza masa kai, wani abun takaicin jinsa yake duk jikinsa ya mutu, kamshin turarenta kawai yakeji, yai kwafa zeyi maganinta ne. Yasamu guri yai parking Ya fito daga mota
Guri yasamu ya zauna, yai shiru dayake ansan abunda yake bukata customer ne sosai, aka kawo masa giyar dayake sha, befi minti shabiyar da zuwansa ba, sega Hannah tazo , dan an kirta a waya an sanar da ita Jalal yazo, guri ta samu ta zauna tana fuskantar Jalal, "Jalal ina kashiga haka, babu ko waya nadena ganinka kwata2 tun a gurin birthday din ka bankuma ganinka ba gashi inason ganinka, nayi niyyar zuwa gidanku amma bani da lafiya ne" kallonta ya danyi yayi shiru ya cigaba da shan giyarsa. Kallonsa Hannah ta kumayi "Jalal ya kayi shiru, kayi magana mana" "mezance miki, inajinki" ta numfasa tace "Jalal dan Allah menene alakarka da wannan yarinyar me iyayin tsiya, ta fadamin sunan ta amma na manta, a zatona itace Ilham amma ranar ta nunamin Ilham tace ita ba itace Ilham ba" ajiye cup din hannunsaa yayi ya kalleta "meyasa kike tambayata wacece?" "ta damu dakai sosai" "hmm ya akayi kikasan hakan?"
"Alamu nagani" "yayi kyau" shine amsan da Jalal yabata, "Jalal dan Allah wacece ita a gurinka" a fusace ya kalli Hannah yace "ke kin isheni, ki kyaleni dan Allah" "meyasa zakace in kyaleka bayan saboda kai nazo gurin nan, Jalal wata alfarma nake nema a gurinka" kura mata ido yayi sannan yace "ina jinki" "Jalal tuba nakeso nayi, na dena abunda nakeyi, dan Allah so nake ka aureni, aurenka ne kawai ze iya cetoni daga halakar danake ciki please Jalal.
" Aurena ze cetoki daga halakar dakike ciki, nikuma ze janyomin halaka, ke kina tunanin zan zabi mace kamarki a matsayin matar aure, Hannah banason yarana suyi irin rayuwar danayi, dan haka uwa tagari zan zaba musu, ina miki murnar shiryuwa da kikayi, naso

Please Login or Register in order to submit comment